Header Ads
Showing 24001 words to 27000 words out of 57539 words

Chapter 9 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

559

Ads at the middle of Article

"to yayi, ina Safnah take?" Ɗan kallon Safnah tayi sannan tace "gata nan"


"To kice mata ina jin yunwa"


Dariya sosai Meenal ta tuntsire dashi, wanda ya ja hankali Hindatu da ta yi nisa wajen chat da Masoyin ta, shi ko Abdul yanke wayar ma yayi.


Sai da Meenal ta gama dariyar ta sannan ta kalli Safnah tare da cewa "to Safnah number ki ta fito yaya Abdul fa yana jin yunwa" ita kan ta Safnah maganar ta bata dariya, Murmushi tayi tare da cewa "to ya za'ayi"


"Yadda za'ayin kenan shiga kicin ne ya gan ki" cewar Hindatu
"Ai na faɗa miki kin zama mai girkin shi daga yau" ta faɗa


"Muje to na taya ki koda yanka albasa ne" Meenal ta faɗa tare da yin gaba don tasan idan ba'a yi girkin nan ba akwai matsala don ita yaba saƙon gashi tayi mai dariya a waya abun da ya tsana kenan, tunda taji ya yanke wayar kuma tasan yayi fushi ne.


Dama shi Abdul haka yake baya cin abincin mai aiki, se dai ya siyo a restaurant shima bako wanne ba, don yana daga cikin mutane masu zaɓan abincin wanda zasu ci.


Haka Safnah ta miƙe suka shiga kicin ɗin jallop ɗin cus-cus tayi mai, mai rai da lafiya, yaji vegetable ga kunun aya da ta haɗa mai ta saka ƙanƙara yayi sanyi sosai, don Safnah ba baya ba wajen iya girki don ita take yiwa Anty ma.


Bayan sun gama sun fito ne kiran ya sake shigowa, "lallai ma wannan yana gidan amma ya dinga kiran mutane" ta faɗa a zuciyar ta tare da ɗaga wayan "wai ba'a gama ba ne?" Abinda yace kenan "an gama to ka ƙi fitowa ne ai"


"Kice ta kawo min ɗaki na"


"Kuma dai!" Meenal ta faɗa ba tare da sanin a fili ta faɗa ba ma, hakan yasa tayi sauri yanke wayar.


"Yace ki kai mai ɗakin shi" Meenal ta faɗa tare da yin gaba


Tsayawa Safnah tayi a zuciyar ta tace "lallai ma wannan wai a kawo mai" ɗaukan kulan tayi da filet da kuma jug ɗin ta nufi ɗakin shi.


Da sallama ta shiga don ƙofar a buɗe take a falon ta same shi kwance akan kujera


"Ina wuni" ta faɗa a takaice


Se da ya tashi ya zauna sannan ya amsa, ajiye abincin tayi a kujerar dake gaban shi ta juya zata fita


"Safnah!" Ya kira sunan ta


Tsayawa ta yi cak! Ba tare da ta juyo ba, "ki zo ki zauna za muyi magana ne" ƙarasowa tayi ta zauna can gefe.


"Kina so ki zauna a ɗakin su Hindatu ko kuma a baki naki daban?"


"Nafi son nawa ni kaɗai" ta bashi amsa


"To shikenan akwai ɗakuna se ki zaɓi ɗaya


"Ni ɗakin mu nake so, naga ba kowa a ɗakin"


"To ba matsala zuwa gobe se ku gyara da su Hindatu, ɗazu kin ga kaya ko?"


"Ehh Nagode sosai"


"Kar ki sake min godiya"


"To"


"Shima gobe zasu raka ki, ki kai ɗinki"


"To"


"Sannan muhimmin maganar da yasa na tsayar dake shine: maganar gadon ki tun lokacin da aka raba yana wajena, an damƙa min ne, na ɗibi rabi ina juya miki sauran kuma suna cikin wani account da na buɗe da sunan ki, sannan akwai gidaje da filaye duk idan na samu lokaci zan kai ki ki gansu"


Tunda ta fara magana Safnah kallon shi kawai take yi, har ga Allah ita ta manta ma da wani gado da ake bayarwa don kuɗin basu gaban ta.


"Kinyi shiru!" Ya faɗa, hakan ya dawo da ita daga tunanin da take
"Yaya Abdul duk yanda kayi dai-dai ne, bi bana buƙatar kuɗi"
"A'a ba wani ɗan Adam da zece baya buƙatar kuɗi" ya faɗa tare da miƙewa ya nufi bedroom ɗin shi


"To idan buƙatar hakan ta taso zan yi magana" ta faɗa cikin ƙosawa da maganar don tunda tazo gidan bata yi magana daya kai wannan ba.


Fitowa yayi ɗauke da leda a hannun shi, miƙa mata yayi tare da cewa "zaki iya tafiya" "to Nagode" tace duk da bata san miye a cikin ledar ba.


Hanyar fita ta nufa shi kuma zama yayi ya fara cin abincin shi se santi yake yi.


Koda Safnah ta fito bata samu su Hindatu a falo ba, hakan yasa ta wucewa ɗakin su.


Da sallama ta shiga ɗakin amsawa suka yi tare da cewa "Safnah se yanzu?" "Ehh ya tsayar da ni ne" "to me kika samo mana" cewar Hindatu
Se yanzu Safnah ta tuna da ledar hannun ta don ta manta ma da ita.
"Wallahi bansan meye ba ya bani ne kawai" Safnah ta faɗa, rige-rigen ƙarɓar ledan suka fara inda Meenal tayi nasarar kwacewa ita kuwa Safnah zama tayi a kujera.


"Masha Allah!" Meenal ta furta lokacin da tayi arba da wata haɗaɗɗiyar waya ƙirar iPhone13 cikin kwalin ta, ta haɗu sosai, cirowa Meenal tayi ta haɗa ta saka layin tare da kunnawa, ƙarar wayar ce ta dawo da Safnah daga tunanin da take yi, zaro idanu tayi tana kallon wayar miƙo mata Meenal tayi, ba musu ta ƙarɓa yayin da farin ciki ya cika mata zuciya ɗon koba komai ta samu wayar da zata dinga kiran Safwan da su, Anty.


"Na taya ki murna Safnah" cewar Hindatu "Nagode sosai" Safnah ta faɗa.


Tashi sukayi suka nufi bedroom don ɗauro alwala don kiran Magrib ake yi.


Khadeejerh Ishaq ✍️ ce
More comment
More typing
Share pls






??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*_19&20


Washegari se ƙarfe 9:00 suka fito ƙaryawa, suna gana ƙaryawa Safnah ta shiga kicin don yiwa Yaya Abdul nashi abun karin chips ɗin dankalin turawa da kwai tayi mai, haɗe da shayi, tana gamawa kuwa se gashi ya fito mamaki ne ya kama ta ganin shi da kayan soja, don tana tsoron Soja a rayuwar ta, gaishe da shi tayi tare da yi mai godiyar waya, sannan ta kawo mai abun karin, "kije ki kira min su Hindatu" ya faɗa kasancewar basu falon sun shiga ɗaki.


Cikin minti ɗaya1 suka fito tare zama su kayi a dining table ɗin, "me kuka koma yi a ɗaki, ke baki ce su taya ki gyara ɗakin bane?"


"Ehh babu key ɗin ne ai" Safnah ta bashi amsa


"Ok, idan na fita zan aiko Sadiq ya kawo miki, Hindatu ku taya ta ta gyara ɗakin su nan zata koma, sannan anjima Sadiq se zo ya kai ku wajen ɗinki ku bayar harda naku,
"To yaya muna godiya" Meenal ta faɗa


"Sannan kuma na kira ku nayi muku sallama ne don yanzu zan wuce India"


"Yaya! Yau kwanan ka uku ne fa!" Cewar Hindatu cikin zaro idanu


"Ehh na sani, Baba babba yace lallai se na koma kun san mun samu matsala da Anty, ta kawo min mari na buge hannunta kaɗan shine wai ta samu gocewar ƙashi" Dariya Meenal ta tuntsire dashi tare da cewa "ashe shiyasa muka ganta riƙe da hannu"


"Ehh, ta faɗawa Baba ƙarya da gaskiya shi kuma yace na koma wajen aiki, dama hutun sati ɗaya na samu amma nan da sati biyu zamu sake samun hutu na wata ɗaya nan da sati biyu in sha Allah ina gida"


"Yaya za muyi kewar ka sosai Allah ya tsare hanya ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya" Meenal ta faɗa.
"Ameen" suka amsa da shi.


Miƙewa yayi bayan ya gama cin abincin ya nufi ɗakin shi, cikin minti biyu2 ya fito ɗauke da jakar shi, har wajen mota suka raka shi ya shiga ya bar gidan suna ɗaga mai hannu.


Bayan tafiyar shi cikin gida suka shiga part ɗin su Teemah don yin hira.




ZARIA


Safwan bashi ya dawo gida ba se ƙarfe sha biyu12 na dare Kamal ya kawo shi, don a buge yake sosai, har ɗaki ya kai shi ya kwantar dashi, sannan ya fito ya koma na su gidan.




Washegari se ƙarfe 11:13 kafin Safwan ya tashi don ko Sallar Asuba beyi ba cikin sauri ya tashi yayi wanka sannan yayi Sallah har na Magrib da Isha'i yayi na jiya da be samu yi ba.


Ƙarfe 12:00 ya fito cikin shirin shi a falo ya samu Daddyn shi, ƙarasawa yayi ya gaishe shi, cikin fara'a ya amsa sannan yace "Safwan mun tsayar da ranar aure wata biyu masu zuwa"


Gaban Safwan yayi mummunan faɗuwa, daƙyar ya seta kan shi yace "Daddy nifa bana son yarinyar nan, akwai wacce nake so fa"


"Wacece?" Dad ya tambaye shi, kame-kame ya fara yi


"Safwan tunda nake da kai ban taɓa neman alfarma a gurin ka ba komai na saka ka zaka yi, to amma yanzu wannan alfarma nake nema a wajen ka"


"Haba Daddy wane ni da zaka nemi alfarma a wajena, na yarda" Safwan ya faɗa don baya son ɓacin ran Daddyn shi.


"Yawwa Allah yayi maka albarka, in sha Allah zaka ji daɗin auren tunda kayi min biyayya, anjima zan kira Momyn ka na faɗa mata"


"Daddy yaushe zaka dawo da momy ne"


"Babu rana!"


"Daddy ba rana kuma?"


"Ehh saboda momyn ka tace min baza ta dawo ba, yanzu haka ma ta kusa yin aure"


"Shikenan Daddy zan fita ne dama"


"To adawo lafiya, yaushe zaka je gidan su Salmah?"
"Se gobe Daddy"
"To Allah ya nuna mana, baka gaishe da Antyn ka ba, naga zaka fita"


"Mun gaisa ɗazu" Safwan ya faɗa tare da rufo ƙofar da ya fita, yasan idan yaje wajen anty ƙara mai baƙin ciki kawai zata yi, kai tsaye gidan su Kamal ya tafi.




KATSINA


Yaya Sadiq ya zo ya kai su wajen ɗinkin sun bayar sannan suka shiga ɗakin su Safnah don taya ta gyarawa, ba komai a ɗakin se kujeru a falo da kayan kallo, se ƙaton gado, da manya-manyan sif a Bedroom ɗin, ba wasu tarukuce, gyara ɗakin suka yi tas sannan suka jera mata kayan kwalliya da mayukan shafawa a kan mirror suka zuba kayan ta wanda ba'a kai ɗinki irin su dogayen riguna, riga da siket, da riga da wando, da su gyale don hijaban suna wajen ɗinki kusan goma sha biyu, kaya ne masu yawa kamar na lefen wata, wata ma baza ta samu rabin shi a lefe ba ma.




Wanka suka yi bayan sun gama aikin sannan suka kwanta don huta gajiya.


Safnah kwance a makeken gadon ta hannun ta ɗauke da waya tana ta gwada number Anty amma bata shiga, abinda Safnah bata sani ba, tun ranar da Safnah ta kira Antyn Kawu ya sani ya ƙarɓi layin ya bata wani sabo.


Bayan tayi ta kira bata samu ba, hakan yasa ta shiga facebook domin yin login a account ɗin ta, abun takaici ta manta password ɗin kamar ta kurma ihu haka taji, ta tabbatar indai ta shiga account ɗin zata samu Safwan don suna chart sosai.


Wani sabon account ta buɗe tayi ta searching Safwan amma bata same shi ba, kuma tasan baza ta same shi ba, se dai idan shi ya turo mata friend request.


WhatsApp ta koma shima ta buɗe sabo ba numbers da yawa a ciki wasu number ne guda uku kawai kuma duka bata san masu shi ba, hotunan dake jiki ta WhatsApp ta duba, ɗaya Yaya Abdul ne da kayan sojoji yayi hoto, ɗaya kuma yaya Sadiq ne don ta san shi sosai yanzu, ɗayan ne bata sani ba.


Bayan ta gama abun da zata yi ne ta ajiye wayar tare da kwanciya wani nannauyan bacci ne ya ɗauke ta.






ZARIA


Safwan bayan yaje gidan su Kamal kai tsaye suka wuce wani wajen shaƙatawa don yanzu baya son zaman gida gashi sunyi hutun school.


**********
Kawu ne zaune da iyalen shi ana ta hira cikin nishaɗi "Abban Khalil ya kamata fa muje Katsina domin duba Safnah daga nan akai mata kayan ta"


"Wai so nawa zan faɗa miki ba zamu je ba, kuma Safnah bazata dawo gidan nan ba, saboda dangin mahaifin ta sun nuna sunfi ni iko da ita, kuma haka ne, munyi waya da Baban ta Salihu ya shaida min aure za suyi mata ma, sannan kayan ta yace bata buƙatar su, asan yadda za'a yi da su, ke ma ina so ki manta da wata Safnah ta zauna a gidan nan"


"Amma ya kamata duk da haka muje mu ga gidan, sannan ga Safwan ya dame mu na bashi adireshin gidan ze je kuma ban sani ba"


"Idan ya ƙara tambayar ki ki faɗa masa baki sani ba, kuma Safnah baza ta dawo ba sannan ki faɗa masa tayi aure ma"


"To shikenan tunda haka kace"
Cewar Anty ba tare da ran ta yayi mata daɗi ba, hakan yasa ta barin wajen gaba ɗaya.


Safwan be dawo ba se wajen ƙarfe 9:00 na dare kai tsaye ɗakin shi ya wuce don ba kowa a falon.


Direct bayi ya shiga yayi wanka, ɗaure da tawul ya fito mirror ya nufa ya shafa mai haɗe da turaruka masu masifar ƙamshi sannan ya zura wata jallabiya maroon colour yayi mai kyau sosai, saman gadon shi ya dawo ya kwanta, tare da cire wayar shi da yasa caji ya ɗaura a gefen drawer kira ya ɗanna tare da kara wayar a kunnen shi.


Har kiran ta katse ba'a ɗauka ba, seda yayi wajen kira uku sannan aka ɗauka, "Assalamu alaikum momy na ykk"
Daga can ɓangaren aka ce "Wslm my son ya kake?" "Wallahi momy ba lafiya ba!" "Subhanallahi me ya faru kuma!?" "Komai ma ya faru, momy kin dena son tilon yaron naki ko? Sai da nayi wajen kira uku sannan zaki ɗauka, kuma ko kira na baki yi ma" ya ƙarasa maganar cikin shagwaɓa, dariya momyn tayi tare da cewa"kai Safwan bana son sakarci fa, kai baka san ka girma bane, Dadyn ka ya kira yana faɗa min bikin ka saura two months ma" "Momy ki share wannan maganar, wallahi bana son yarinyar da Daddy ya dage se na aure ta, momy yaushe zaki dawo wai?" "Safwan me yasa ka cika rigima ne, ni bazan dawo gidan nan ba" "What! Momy kar dai abinda Daddy ya faɗa min hakane, Momy yanzu baza ki dawo ba aure zaki sake yi!?" Safwan ya faɗa cikin tsantsar tashin hankali domin yana matuƙar azabtuwa na rashin Momyn shi a kusa da shi sosai.
"Tabbas hakane Safwan bazan dawo ba" Momyn ta faɗa.


"Yanzu Momy ni kaɗai zaki bari kenan?" "Safwan yanzu fa ka girma gashi har aure zaka yi, ka zauna da matar ka lafiya, sannan ka cigaba da yi wa matar Daddyn ka biyayya kaji!" Wasu zafafan hawaye ne suka fara gangara daga idanun Safwan cikin rawar murya yace "Momyna zanyi abinda kika ce amma duk halin da na faɗa kar ki zarge ni, na kira ki domin ki kwantar min da hankali akan matsalar da nake ciki amma kuma kin ƙi saurarana ma to se anjima momy" ya faɗa tare da kashe wayar yayi wurgi da ita Allah yasa akan kujera ya faɗa da yayi raga-raga.


Miƙewa yayi ya nufi firij ɗin dake ɗakin buɗewa yayi ya ɗibo giya har kwalba uku, sannan ya nufo gadon ya zauna tare da buɗewa hawaye nabin fuskar shi, tsurawa kwalbar daya buɗe ido yayi kafin ya fara faɗin "ya Ubangijina kaga halin da nake ciki ka fitar dani, kafi kowa sanin damuwata Allah ka yaye min Allah ka shirye ni, na daina wannan halin, Safnah kiyi hakuri zan ƙarya alƙawarin ki, amma duk lefin ki ne, ki ka yi nisa dani, bayan kinsan bazan iya jure hakan ba.


Maganar yake hawaye na bin fuskar shi idan ka ganshi se ka tausaya mai sosai ɗaga kwalbar giyar yayi zuwa bakin shi cikin abinda be fi minti1 ba ya shanye tare da sake ɗaukan ɗaya shima tas! Ya shanye shi.


Be yi minti 5 ba bacci mai nauyi ya ɗauke shi.




KATSINA


Safnah zaune a falon ɗakinta idanunta nakan Tv suna haska shirin Tarkon Ƙauna a tashar Arewa24 amma a zahiri hankalin ta ba akan Tv yake ba don tayi nisa cikin tunani haka yasa bata samu damar jin ƙarar da wayar ta take yi ba, wanda yake nuna kira ne ya shigo, ga kuma ƙarar Tv.


Ta daɗe sosai sannan ta dawo hayyacin ta, tashi ta yi ta nufi Bedroom don ɗauro alwala don kiran Sallar la'asar da ake yi.


Se da tayi alwala tayi Sallah sannan ta dawo falon wayar ta ta ɗauka, zare idanu tayi gani 2misscall daga Yaya Abdul, mamaki ta shiga yi me yasa kuma ze kira ta.


Bayan ta gama tunanin ne ta danna mai kira, har ya katse ba'a ɗauka ba, zata sake kenan se ga kiran shi ya shigo, se da ta dai-daita nutsuwar ta sannan ta ɗaga wayar ta kara a kunne shiru ba'a yi magana ba, hakan yasa ita ma ta yi shiru, har tsawon sakwanni15 sannan ta daure tace "Assalamu alaikum!" "Wa alaikumus-salam" ta ji ya faɗa daga can ɓangaren, "lallai ma wannan mutumin ya kira ya wani yin shiru to me zance mai Oho!" Ta faɗa a zuciyar ta, har zuwa lokacin be sake yin magana ba, "Ina wuni" ta daure daƙyar ta faɗa "lafiya lau, na zaci ai da kurma nake magana" shiru tayi bata ce komai ba"meyasa baki son sakewa a gidan ku, kina yi kamar wata baƙuwa, ranar da na ganki a lambu kina kuka me akayi Miki" "bakomai Yaya Abdul" "ya kamata ki saki jikin ki, ga ƴan uwan ki kuyi hira, ina su Hindatu suke?" Ya ƙarasa maganar tare da jefa mata tambaya"suna ɗakin su" "ke kuma kina ina?" "Ina nawa ɗakin"
"To kin ga irin ta ko, ki zauna ke kaɗai cikin tunani, to a ina kike kwana ma"
"Ɗakina" ta faɗa kamar zata yi kuka don ta gaji da tambayoyin da yake mata,
"To ban yarda ba kije cikin ƴan uwanki ku dinga kwana tare, da rana ma ki kasance tare da su kin ji ko?"


"Ehh naji" "to tashi ki tafi ɗakin su"
"To seanjima zan tafi" ta faɗa tana shirin yanke wayar.
"Kar ki yanke min waya Malama" taji Muryar shi yana faɗa "to zan tafi ɗakin nasu ne fa" ta faɗa cikin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads