Showing 54001 words to 57000 words out of 57539 words
Chapter 19 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
shigowar Anty, har uwarɗakar ta shigo tare da zama a gefen Safnah ta ce
"Safnah me ya faru kuma ki ke kuka?"
Kara sautin kukanta Safnah ta yi tare da cewa "Anty komai ma ya faru!, Ina cikin damuwa sosai Anty kuma ba bu wanda zan iya faɗawa damuwata, Anty dama ke ce kawai na ke faɗa ma damuwata kuma ki share min hawayena amma kin yi ne sa da ni Anty ko nema na baki yi!"
Jikin Anty yayi sanyi sosai, har kwalla sun fara shirin zubo mata na tausayin Safnah, goge kwallar ta yi don ba ta son Safnah ta gani sannan ta ce.
"Safnah ki yi hakuri, duk tsanani ya na tare da sauƙi, duk abinda ya dame ki ki cigaba da kai kukan ki wajen Allah domin shi mai ji ne kuma ya na ganin halin da ki ke ciki!, Safnah kinsan ban san gidan ku a Katsina ba, kuma ko na sani Abban su ba ze bar ni na je ba!"
"In sha Allah Anty!, Nagode sosai da tunatarwa ki" Safnah ta faɗa tare da share hawayen da su ka wanke mata fuskarta.
"To Safnan ya kamata ki faɗa min abinda ya ke faruwa"
"Anty kinsan ba ni da burin da ya wuce na ga na yi karatu mai zurfi, amma Anty a can ko maganar karatuna ba su yi se dai maganar aure!"
Murmushi Anty ta yi sannan ta ce "Safnah ai shi ma auren abu ne mai kyau, kuma ko da kin yi aure ai za ki cigaba da karatun ki ba matsala ba ne"
"Anty ba za ki ga ne ba ne!, Kinsan har baiko fa anyi min nan da Three months fa"
Wani iri Anty ta ji a cikin zuciyar ta, amma ta dake ta ce "amma ba mu ji ba, ko Kawun ki na tabbatar shi ma be sa ni ba, amma da waye aka miki baiko?, Ki na cewa ba ki son auren shine daga zuwan ki har kin yi saurayi ko!"
"Anty be fi two weeks da yi ba, kuma ɗan Babanmu Salihu ne fa!"
"To ki ce auren zumunci ne, Allah ya tabbatar da alkhairi!"
Kuka Safnah ta fashe da shi tare da cewa "Anty wallahi ba na son shi, amma shi ya nace wai ya na so na"
"Idan na fahimce ki auren dole za su yi miki kenan?"
"A'a Anty na ce ina son shi, amma Anty wallahi ba na son shi"
Jinjina kai Anty ta yi tare da mamakin wannan lamarin, kallon Safnah ta yi tare da faɗin "amma ba ki faɗa min me ya kawo ki Zaria ba, kuma ke da waye ku ka zo?"
"Anty bikin Safwan mu ka zo!, Amma gidan su Amaryar mu ka zo wa bikin, yayan ta shi zai auri wata ƴar uwarmu a Katsina, kuma wanda aka yi min baiko da shi abokin yayan na ta ne, shi ya kawo ni nan ma yanzu se ya wuce gidan da za'a kai Amaryar ana walima ne"
"To shine ko ya shigo ya gaishe da mu?" "Anty sauri ya ke yi ana ta kiran shi ne, da ƙyar ma na samu ya kawo ni nan, don da gidan walimar mu ka fara wucewa"
"To me yasa ba ki tsaya a wajen walimar ba?"
"Anty ba na son Safwan ya ganni ne!"
"To saboda mene?, Ba se ki ta ya shi murna ba, bayan tafiyar ki Safwan ya zo nan ya fi a ƙirga ya na neman ki!"
"Anty ba zan iya ba ne!, idan na kalle shi baƙin ciki na ke ji sosai a zuciyata!"
"Safnah tun farko ku ku ka yaudari kan ku, ta hanyar ɓoye soyayyar junan ku, da kun bayyana da kun daɗe da zama mallakin junan ku"
"Anty Safwan be taɓa ce wa ya na so na ba, kin ga ba mutunci ba ne ni na ce ina son shi"
"Duk wannan shirmen ku ne!, Amma ko wa ya gan ku zai fahimci soyayyar da ta ke tsakanin ku, musamman Safwan ya na matuƙar ƙaunar ki Safnah, na ji mamaki sosai da aka ce ze yi aure!"
Hira su ka cigaba da yi har kusan Magriba sannan su ka fito zuwa falon Antyn lokacin har su Khalil sun dawo daga Islamiyya, se lokacin Safnah ta ke tambayar Anty ina Kawu? Duk da tun da ta shigo ya ke ran ta, amma se yanzu ta tambaya.
Se da Anty ta gama jere mu su abinci a tsakar falon sannan ta kalli Safnah ta ce "Safnan Kawun ki ya na asibiti, kinsan Mama ba ta da lafiya ta daɗe a gidan nan, amma zuwa anjima za su dawo"
"Allah Sark!, Allah ya ba ta lafiya, ciwon me take yi Anty?"
"Typhoid ne da maleria"
"To Allah ya ba ta lafiya!"
"Ameen!"
Su na rufe baki su ka jiyo sallamar Kawu, da sauri Anty ta miƙe don tarbo mijin na ta, a tsakar gida ta gan shi riƙe da Kaka, da sauri ta ƙarasa ta riƙe kaka ta na mata sannu, daƙyar ta iya amsawa, sannan su ka nufi ɗakin, Kawu kuma ya juya domin zuwa masallaci don an fara kiran sallar Magriba tun ɗazu.
Zaunar da kaka ta yi a kujera tare da ɗauko abinci ta fara ba ta, don ta ɗan ji sauƙi sosai har ta na iya cin abinci.
"Sannu kaka!" Safnan ta faɗa tare da tasowa ta nufo kujerar da su ke zaune"
"Yawwa!, Wa na ke gani kamar Safnah?"
"Ehh Mama ita ce!" Anty ta faɗa.
Ita kuma Safnah murmushi kawai ta yi, don ta ji daɗin ganin jikin kakan na su ya yi sauƙi.
"Yaushe ta zo ne?" Kaka ta faɗa.
"Yau ta zo, Mama ki bar magana ki ci abinci don Allah" Anty ta faɗa, don tasan idan ta cigaba da maganar damuwa ce kawai za ta dame ta, don ta na yawan yin zancen Safnah.
Sosai Kaka ta ci abinci, bayan ta gama ci Anty ba ta ruwa ta sha, tare da sa mata albarka.
Dai-dai lokacin Kawu ya shigo ɗauke da sallama, amsa mai sallamar su ka yi ya samu waje ya zauna.
"Ina wuni Kawu!" Safnan ta faɗa kan ta a ƙasa.
Da sauri ya ɗago daga kishingiɗar da ya yi don jin muryar Safnah, kallon ta ya yi cike da mamaki, don shi kwata-kwata idon shi be kai wajen da ta ke ba ma.
"Lafiya lau Safnah!, Yaushe ki ka zo?"
"Ɗazu na zo Kawu!"
"Kin zo bikin Safwan kenan?"
Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh, sannan ya ƙara ce wa
"Ya garin na ku?, Komai lafiya dai ko?"
"Ehh Kawai, Alhamdulillah!" Safnah ta faɗa don ba komai ta ke iya faɗawa Kawun na ta ba, saboda ta na jin kunyar shi, amma Anty kuwa ba kunya tsakanin su komai ta na iya faɗa ma ta.
"To Masha Allah haka ake so ai, to yaushe za ki koma?"
"Kawu ban sani ba, ba ni kaɗai na zo ba"
"To shikenan"
Wayar Safnah ce ta fara ringing alamar shigowar kira, ko da ta duba Abdul ne, miƙewa ta yi ta nufi ɗakinta don ba za ta iya yin waya a gaban su ba.
Lokacin da ta shiga ɗakin har kira ya yanke, wani kira ne ya sake shigowa ɗaukar wayar ta yi tare da kai shi kunnenta.
"Assalamu alaikum!" Ta ji muryar shi ya faɗa.
"Wa-alaiku-mussalam!" Safnah ta ba shi amsa.
"Barka da dare gimbiyata!"
"Yawwa barka!"
"Ya jikin na ki kuma?"
"Alhamdulillah!"
"Ina nan zuwa bayan isha'i"
"To me za ka zo yi?" Safnah ta faɗa ba tare da sanin maganar ma ta fito ba.
"Ɗaukan ki zan zo yi mana!"
"Haba yaya!, Ka ce se gobe fa!" Safnah ta faɗa cikin muryar shagwaɓa.
"Zan kawo miki maganin ki ne kin manta da shi a can gidan"
"To ka bar shi, ni na ji sauƙi ma!"
"Ni ki ke faɗa wa haka ko?"
"Ka yi hakuri!"
"To shikenan na taho ma yanzu, anjima kaɗan dinner za mu tafi"
"To se ka zo, ina su Hindu?"
"Su na can suna tambayar ki, ana tsaka da biki kin gudu, gobe zamu zo tare da su"
"To shikenan"
"Ok se na zo"
"To" Safnah ta ce tare da yanke wayar, ɗakin Anty ta koma su ka cigaba da hira da yaran don da ta dawo ba ta samu su Kawu ba har Kaka ma ba ta ɗakin.
Bayan mintuna biyar5 kiran Abdul ya sake shigowa, ta na ɗagawa ya ce "ina jiran ki a waje!"
"To" ta ce sannan ta miƙe tare da cewa
"Khalil idan Anty ta fito ka ce mata na je na dawo"
"To Anty!" Khalil ya faɗa, Hijabin Anty ta ɗauka ta saka sannan ta nufo kofar gidan.
A saitin ƙofar ta ga motar shi yayi perking ɗin ta, ƙarasawa ta yi tare da buɗe motar ta shiga bakinta ɗauke da sallama.
"Barka da zuwa!" Abdul ya faɗa kan ta a ƙasa ta bashi amsa da "yawwa ya hanya?"
"Lafiya lau, Masha Allah!, Da dukkan alamu kuwa kin ji sauƙi don ga shi na ga alama, gobe misalin ƙarfe 12:00pm zan zo na ɗauke ki"
"To" kawai Safnah ta ce ba don ta so hakan ba.
Ledar magungunan ya miƙo mata tare da ce wa "mu je na gaishe da mutanen gidan"
Da sauri Safnah ta ɗago kai ta kalleshi tare da ce wa "yanzu wai?"
"Ehh mana!, Ko kar in je ne?"
"A'a mu je" Safnah ta faɗa tare da buɗe motar ta fito, shi ma fitowa yayi su ka jero har zuwa ƙofar gidan.
"To ki shiga ki faɗa mu su zuwa na mana!"
"To" Safnah ta faɗa tare da nufar cikin gidan, Anty ta tarar a falon tare da yaran ta, zama ta yi tare da ce wa
"Anty har kin fito?"
"Ehh tun ɗazu ma, ance kin je ki dawo"
Sunkuyar da kai Safnah ta yi sannan ta ce "Anty yaya Abdul ne ya zo, kuma ya ce zai shigo yanzu ya gaishe da ku"
"To ki ce surukin na mu ne ya zo, to je ki shigo da shi mana!"
"To" Safnah ta ce tare da fita suka taho tare da Abdul, iso ta yi mai har zuwa falon Antyn, Anty na zaune a falon ta saka hijabi, har ƙasa Abdul ya duka ya gaishe da ita, cikin fara'a sosai Anty ta amsa gaisuwar shi tare da faɗin "ya hanya!"
"Alhamdulillah!" Abdul ya faɗa, gaishe da shi sauran yaran su ka yi tare da miƙewa su ka bar falon dukan su.
"Ga waje ka zauna mana ka zauna a ƙasa" Anty ta faɗa ta na kai duban ta wajen da Abdul ya ke zaune a ƙasa.
"A'a Anty nan ma ya isa!" Abdul ya faɗa fuskar shi ɗauke da murmushi.
Cikin mintuna kaɗan Halima ta cika ma Abdul gaban shi da kayan ciye-ciye da na sha,
"Sannu ƴan mata" Abdul ya faɗa yana murmushi don sosai yarinyar ta burge shi, duk da ba ci ze yi ba, amma ya ji daɗin tarbar da aka yi mai sosai.
"Bismillah!, Suruki na, bari na kira mai gidan ku gaisa" Anty ta faɗa tare da miƙewa ta yi hanyar ɗakin Kawu.
"To se ki zauna ai!' Abdul ya faɗa ya na kai duban shi in da Safnah ta ke tsaye tun shigowar su.
Zama ta yi tare da ce wa "yaya yaushe za ku koma?"
"Za mu koma ina?"
"Katsina mana!"
"Ban gane za mu koma ba!"
"Yaya don Allah ka bar ni a nan!"
Kallon ta ya tsaya yi ba tare da ya ce komai ba, ita kuma sunkuyar da kanta ƙasa ta yi don ba ta son kallo musamman ma na Abdul ɗin.
Kafin su sake wata magana su ka ji sallamar Anty da Kawu, waje su ka samu su ka zauna, Abdul ne ya rusuna ya gaishe da Kawu, ba-yabo-ba-fallasa Kawu ya amsa gausuwar ta shi.
"Mun same ku lafiya?" Abdul ya sake faɗa.
"Alhamdulillah!" Kawu ya faɗa.
Sun ɗan taɓa hira kaɗan kafin Abdul ya tafi, bayan ya faɗa mu su maganar sa ranar Safnan, amma be faɗa mu su da waye ba.
Kawu ɗakin shi ya koma bayan tafiyar Abdul, daga Safnah se Anty a ɗakin, don yaran ma sunyi bacci.
"Safnah wannan shine Abdul ɗin?"
"Ehh Anty shi ne"
"Amma Safnah ban ga abun ƙi ta tare da shi ba, ƴan matan yanzu sun fi son saurayi mai kyau, kuma wannan ya na da shi, gashi daga ganin shi mutumin kirki ne Safnah!"
"Gaskiya ne Anty!, Ko ni idan zan yi adalci zan yi wa Yaya Abdul kyakkyawar shaida, amma Anty kawai ba na son shi ne!"
"Safnan ba wai ba ki son shi ba ne!, Zuciyar ki ta na wajen Safwan ne yanzu, shiyasa ba za ki fahimci soyayyar shi ba, amma ki yi ƙoƙarin mantawa da Safwan kwata-kwata, ta haka ne za ki gane ki na son shi.
"To Anty nagode sosai!" Hira su ka cigaba da yi har dare ya tsala sosai, sannan su ka nufi ɗakin Anty, don Anty ta ce ta je can su kwanta.
*****Washegari *****
Duk yadda Safnah ta so tashi ta ta ya Anty aiki hana ta ta yi, hakan yasa Safnah kwanciya ta sha baccin ta, don tun da su ka zo Zaria ba ta wani samun bacci ba, ga tunani ga kuma hayaniyar gidan biki.
Anty ce ta haɗa break fast tare da shirya yaran nata su ka tafi makarantar hadda, sannan ta ta so Kawu don yau bashi da aiki weekend ne, karyawa ya yi shi ma, tare da Kaka, lokacin har ƙarfe 9:00 ta yi, se lokacin Anty ta taso Safnah, wanka ta yi ita ma sannan ta karya.
Safnah ɗakin ta ta nufa, ta samu babban akwatin ta ta shiga shirya kayan ta da take buƙatar su, tun daga kan kayan karatun ta, da kayan amfanin ta da sauran su, ba ta ɗauki kayan sawa ba ko guda ɗaya, se da ta cika akwatin sosai da kaya, daƙyar ma ta iya rufe wa, sannan ta jawo akwatin zuwa falon ta.
Bayan ta gama ne, kiran Abdul ya shigo, kamar ta fasa ihu haka ta ji don dama a cike take kiris! Ta ke jira ta fashe, abinda ta zata kuwa shine, ta na ɗaga wayar ya ce yana hanya, agogon hannun ta ta duba ta ga 12:15 kuka ta fashe da shi bayan sun gama wayar, ta kai mintuna goma 10 kafin ta share hawayen ta ta fito, Anty na kicin ta na aiki, kicin ɗin Safnah ta shiga tare da ce wa
"Sannu da aiki Anty!"
"Yawwa Safnah, har kin gama kwashe kayan?"
"Ehh Anty!, Yawwa Anty an ga sim ɗin nawa?"
"Ehh bari na gama na ɗauko miki"
"To Anty, amma kin yi sauri har kin gama shinkafar?"
"Ehh mana!, Ba ki ga miyar ma saura kaɗan ba?"
"Ehh gashi fa na gani, Anty wai ya na hanya za mu tafi can gidan Amaryar"
"To shikenan!, Daga can shikenan kin wuce ko za ki dawo?"
"Zan dawo mana Anty!, Ga kayana can ba zan tafi da su ba se gobe"
"To shikenan Safnan"
Kafin Safnah ta yi wata magana wayar ta ta fara ringing, tsabar takaici ba ta ma ɗaga ba kawai hijabinta ta saka ta nufi waje.
Ta same su duk sun fito daga mota su Teemah, ita ta ma manta ya ce za su zo tare, ƙarasawa ta yi ta gaishe da shi, sannan su ka gaisa da su Hindu.
"Ku shiga ku gaishe da mutanen gidan se ku zo mu wuce" Abdul ya faɗa tare da komawa cikin motar shi, su kuma su ka nufi cikin gidan.
Har cikin ɗakin Anty Safnah ta kai su, su ka zauna sannan ta zo kicin ta shaida wa Anty zuwan su, sauke miyan Anty ta yi tare da kashe Gas ɗin sannan ta nufo ɗakin.
Gaisawa su ka yi Safnah ta jere mu su drinks sannan ta fito kicin ta karɓo abincin da Anty ta zuba mu su, ta shigo haɗe da jere mu su a gaban su ta ce "Bismillah!, Ga abincin fa"
"Lallai kinsan yaya Abdul na jiran mu shine ki ka wani zubo mana abinci" Meenal ta faɗa.
"A'a fa ni se na ci wallahi don ba mu wuce ta yi" Teemah ta faɗa tare da saukowa daga kujera ta jawo filet ɗaya ta hau ci.
"Shiyasa na ke son ki Teemah" Safnah ta faɗa.
"Ni dai wallahi a ƙoshe nake da na ci" Sa'adatu ta faɗa.
"Don Allah ku sauko ku ci mana miye haka, musamman fa na dafa muku saboda yaya Abdul yace tare za ku zo"
Safnah ta faɗa don su ci abincin
"To ba za mu ba ki kunya ba kuwa bari mu ci!, Amma fa ki je ki faɗawa yaya Abdul mun tsaya ɗa'amun!" Meenal ta faɗa tare da saukowa ita ma.
"To ba damuwa, bari na kira shi na faɗa mai" Safnah ta faɗa tare da barin ɗakin, wajen Anty ta dawo ta tarar ta na share kicin.
"Safnah ya ki ka fito ki ka bar su kuma?"
"Anty na bari su ci abincin ne fa!"
"To shikenan"
"Anty ɗauko min Sim ɗin kar ki manta!"
"To Safnah!, Amma kafin na baki zan miki gargaɗi da ki goge Number Safwan daga ciki!"
"To Anty zan goge" Safnan ta faɗa.
Ɗaki Anty ta shiga, bayan mintuna biyu2 ta fito ta miƙa mata Sim ɗin, karɓa Safnah ta yi tare da nufar ɗakinta ta saka a cikin kayan da ta haɗa.
Ɗakin su ka koma har Anty, hira su ke ɗan yi kaɗan-kaɗan don sun gama cin abincin ma, wayar Safnah ce ta fara ringing ko da ta duba yaya Abdul ne "ku ta so mu je!" Kawai Safnah ta ce ba tare da ta ɗauki wayar ba.
Miƙewa su kayi su fito waje, bayan sun yi wa Anty sallama, Safnah se da ta yi wa Anty sallama sannan ta fito su ka nufi ƙofar gidan.
A jikin motar su ka samu Abdul ya haɗa rai, ƙarasawa su ka yi wajen tare da buɗe motar su ka shiga amma ban da Safnah, don yana jikin ƙofar da za ta shiga,
"Yaya ka yi hakuri, Anty ne ta ce se sun tsaya sun ci abinci"
"To shikenan shiga mu je!" Ya faɗa tare da matsa ma ta ta shiga, zagayowa ya yi shi ma ya shiga tare da jan motar, kai tsaye gidan Amarya su ka nufa.
Mintuna goma10 ya kai su gidan, fitowa su ka yi ba kowa a tsakar gidan se Sadiq da Faruq da su ka tarar a bakin gate da alama tafiya za su yi, perking Abdul ya yi su ka fita su ka nufi cikin gidan shi kuma ya tsaya a wajen su Sadiq.
Sun zo shiga ƙofar falon Safnah ta ga wata ƴar Class ɗin su da alama ta zo wa Salmah biki ne, tsayawa ta yi su ka gaisa, su Teemah kuwa tuni sun shige ciki, Number Safnah ta ba ta sannan su ka yi sallama, tsayawa Safnah ta yi ta