Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 57539 words

Chapter 6 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

557

Ads at the middle of Article

na Baba Bashir, irin part d'in su ne dai, se de kayan ciki da ya bambam ta da na su, Shiga falon su ka yi da Sallamar su su ka gaishe da matar Baban na su Hajara wanda su ke ce mata, momin Teemah, kasancewar ta na da yara bakwai Teemah itace ta shida tana da yaya ana kiran shi, marwan, se ƙannen su, Fatima wanda su ke cewa Teemah ita sa'ar su Hindatu ce kuma 'kawar su.


"Momi Teemah na nan" cewar, Meenal "Ehh wannan wacece?", "Safnah ce" cewar Hindatu, "Allah sarki Safnah ce ta yi girma haka sosai, ko da ga ku ma ai duk sa'anni ne gara da akace ku fito da miji kuyi aure ma", "kai momi kina goyon bayan su kenan", "Ehh mana", "shikenan", d'akin Teemah su ka nufa, da sauri ta na falon d'akin ta zaune ta na karatun wani littafi, TRUE LOVE su ka shigo da sallamar su, Teemah aje littafin ta yi tana murmushi tace "'yan raini wayo na zaci yau ma baza ku zo bane, ni sedai na dinga zuwa part d'in ku amma ni kun kyale ni baza ku zo ba shiyasa jiya na 'ki zuwa", "ai nace ki dawo part d'in mu kin 'ki", "lallai!, ai wallahi ba ku isa ba, kar ma ku bari Daddy ya ji ma wallahi", "to shikenan" "Bakuwa muka yi ne?", "Safnah ce fa ba ki gane ta ba?", "oyoyo sis, zo ki zauna", hannun Safnah Teemah ta ja ta zauna kasancewar tun da su ka shigo ta na tsaye ne, Safnah kece ki ka yi haka ji ki kin zama wata 'katuwa kin yi kiba, murmushi kawai Safnah ta yi, "Ke ya maganar Baba Babba yace fa ku fito da mazaje a satin nan ba?" cewar Teemah, "aini nawa na nan khalid ke ma kin sani" cewar Hindatu, Meenal kuma cewa ta yi, "nima dai jira na ke yi, ina da nawa", "Lallai yaran nan, ni dai karatu zan yi" cewar Teemah "sannu biro da takarda", cewar Hindatu, ita Safnah jin su kawai ta ke yi.


"Safnah ana ta hira ko kin manta mu? ne?" murmushi Safnah ta yi, don duk ba wanda ta manta duk sa'annin ta ne, su na wasa kafin ta tafi, "ta so ki raka mu Part d'in Baba mudan", "to muje" cewar Teemah ta shi su ka yi su ka fito momi lokacin ma bata falo, d'ayan part d'in su ka shiga, shima dai duk irin d'aya ne se kayan ciki, shi kuma yana da yara, tara, Babban d'an shi shine, Ummar, wanda yana, India ya na karatu se kuma, mujahid, se Kamal, se kuma, Sa'adatu, wanda su ke sa'a da su Teemah se ƙannen ta, da Sallama su ka shiga falon, sa'adatu da mujahid su ka tarar a falon, Teemah ce tace "ya mujahid yau ba'a fita ba kenan?" "Ehh zan yi ba'ko ne" "ok ya yi kyau, Sannu 'yar rainin wayo wato ki na nan ko ki zo ki gaishe da mu ko", "ni kuna bani mamaki kuna so a zo muku amma baza ku zo ba, to kowa ya zauna a nashi wajen" cewar Teemah, "Umma bata nan ne?" "tana d'akin ta", "to bara mu gaishe ta" cewar Meenal, d'akin maman sa'adatu su ka nufa wanda su ke cewa Umma, gaishe ta su ka yi su ka fito, ko da su ka fito falon ba sa'adatu, se ya Mujahid da wani, Teemah ce ta 'karasa tace "a'a boss kai ne a gidan namu?", wanda aka kira da boss ya d'ago yana murmushi, Safnah jin an kira boss yasa da sauri ta d'ago don sunan da ake kiran Safwan kenan 'yan makarantar su, idon su ne ya had'u da Boss, d'in ta yi saurin kawar ta kan ta don wani kallo ta ga yana mata, Hindatu ne tace "dama 'kanana na ganin ku?", "to ba gani na zo ba", ya yi kyau ai cewar Meenal sannan yace "kun yi bakuwa kenan?" "A'a 'yar Baban mu marigayi ne" "Allah sarki dama tana ina ne?" "tana Kaduna ne", "yayi kyau", d'akin sa'adatu, su ka nu fa don sun san can ta nufa, aiko nan su ka sameta su ka zauna suna ta hirar su Safnah dai se dai ta yi musu murmushi,
Har wajen sha biyu 12:00 na rana su Meenal na part d'in su sa'adatu, Safnah ko bacci ma ta ke yi, don bata saba da irin hirar nan ba kasancewar bata da wa su kawaye, kawar ta d'aya maryan ita ma ba me surutu ba ne, se kuma Safwan kusan ma shine abokin hirar ta, se kuma anty da yaran ta, se da su ka tashi Safnah kafin su ka nufi part d'in su, a hanya su ka ga, Baba Salihu wanda su ke cewa Baba Babba gaishe shi su ka yi, yace "anjima ku shirya ku kai Safnah gidan 'yan uwa, don su gaisa" "to Baba" cewar Meenal, sannan ya wuce, d'akin su su ka nufa don su yi wanka su shirya, Meenal ne ta fara shiga bayin yayin da, Hindatu ta ke d'auko musu kaya, Kujera Safnah ta samu ta kwanta, jakar ta 'yar 'karama da ta zo da shi ta d'auko, ta bud'e wayar ta ta ciro, bud'e wayar ta yi ba layi se memory, kunna wayar ta yi ta ga taci screen sosai don ko fuska ba'a gani, kamar ta kurma ihu, ga layin ta ba'a gani ba, memory ta ajiye a cikin aljihun jakar ta, sannan ta mayar inda ta ajiye, wayan kuma ta aje da niyar zata kai gyara.


Karfe, 2:00 su ka fito cikin shirun su sun yi masifar kyau du ka kasancewar su jinin Fulani, Hindatu da Meenal kyawawa ne sosai, amma Teemah ta fi su kyau kuma ta fi su haske ma sosai gashi suna masifar kama da Safnah se dai tafi Safnah haske ne, sa'adatu ma, fara ce amma ba sosai ba ita ma ta na da kyau, sosai kai tsaye d'akin kaka su ka shiga tun da dama a wajen ta su ke ita Hindatu ta kasance 'yar Baba Aminu ce, se kuma Meenal 'yar Inna Aisha, mahaifin ta ya rasu, se ta 'kara aure shi ne ta bar ta a gidan su.


'Dakin kaka su ka shiga tana zaune a kujera, Meenal ce ta karasa da sauri, ta zauna ku sa da ita ta dafa kafad'an ta tare da cewa "tsohuwa mai ran 'karfe kina hutawa ne?" dariya kaka ta yi tace "Ehh se ina haka, naga kun d'au wanka?" "Wallahi yau ziyara ce ta tashi", "ai gara ku dinga ziyara sosai", "to 'yar tsohuwa za'a dinga" cewar Hindatu, Safnah gaishe ta ta yi, ta amsa da fara'ar ta, tace "ki zo ki zauna mana!", "A'a kaka barta sauri mu ke yi wucewa zamu yi muka ce se mun ga kaka don yau bamu had'u, ba" "to sannun ku, waye ze kai ku ziyarar?" "ya mujahid ne don shi ne a gidan", "to ku gaishe da su", "to kaka" cewar, Meenal, sannan su ka fita dining table su ka nufa don har an jere musu abinci kasancewar akwai me musu aiki, wataran kuma su su ke abun su, don komai sun iya, abincin su ka ci sosai Safnah dai bata wani ci ba, ita kan ta ta na mamakin kan ta kamar ba gidan su ba ta ka sa sake wa, amma ita har ga Allah ta fi son gidan Kawun ta, waya Hindatu ta ciro tace "bara na kira Teemah na ji tace zata je", "to" cewar Hindatu, Safnah ce tace, "Hindatu ina wayar ki ki ara min?" "ki je d'aki tana kan kujera na bar ta" ta shi ta yi ta nufi d'akin don dama ta koshi wayar ta d'auka, ba security, Safwan ta ke son kira, amma kuma ta manta number kasancewar sabon la yi ya yi d'ayan kuma ta kira a kashe, sosai ta shiga tashin hankali kuma tana ji ajikin ta yau idan bata ji muryar Safwan ba akwai matsala number anty ta had'a ta kira tana ta ringing bata d'auka ba, dama ta sani don bata d'aga bakuwar number, wani katutun ba'kin ciki ne ya tokare mata zuciya wanda idan bata yi kuka ba ma ba ze daina ba, wa su zafafan hawaye ne su ka wanke mata fuska, ta rasa mafita yanzu ya zata yi ne, muryar su Meenal ta ji za su shigo d'akin da sauri ta share hawayen ta, Mi'ka ma Hindatu wayar ta, gyale su ka d'auko su ka sa ka Meenal ne ta ce "Safnah Hijab za ki saka ko gyale?", "Hijab" tace musu, don ita ba ma'abociyar sa ka gyale bace "to ki za'bo wanda zaki sa ka", wajen kayan nasu ta nufa, d'aya sif d'in na kayan meenal ne shi ta sa ma don meenal ma tana da jiki kamar Safnah, se d'ayan na Hindatu, d'ayan kuma gyalulluka ne, da Hijab, kayan kwalliya da dai sauran su don 'yan matan Familyn su ba dai wanka ba shi yasa Baba babba ma ya sa mu su ido, da ya hana su ma saka gyale ko yanzu ma wataran se yace su cire, Sallamar Teemah su ka ji itama ta shirya tsaf Wani hijab sky blue, Safnah ta d'auko, ya yi mata kyau sosai, "ke wai Hijab za ki saka dama haba dai, kin gan mu fa duk gyale muka saka a'a dai ki cire ki saka gyalen ki" cewar Teemah, tare da bud'e sif d'in wani gyale ta za'bo mata mai masifar kyau, tace "don Allah ki saka shi", Safnah bata so ba haka nan ta kar'ba tare da cire hijab d'in, ta sa gyalen "ku yi sauri ya mujahid na jiran mu, ai se da naje part d'in su na ta so shi tsabar takura wai ace mutum baze yi draving ba se dai a kai shi wallahi haushi abun ke bani ga motoci kuma agida", fita su kayi su ka shiga motar, "ya mujahid boss ya tafi kenan?" cewar, Hindatu, "Ehh tun d'azu ma ya tafi", "yayi kyau" cewar Teemah, gidan Baba Aminu su ka fara zuwa, gidan su Hindatu kenan, Gida ne Babba shi ma mai kyau sosai, Ya na da yara bakwai shi ma, Saddiq shine Babba wanda su ke cewa yaya sadiq shima yana India tare da ya Abdul, se shamsudden, se Majid, se Hindatu, se kanwarta, Fatima, se Rahama, se Hauwa'u ita ce ƙarama a falo su ka tarar da momin Hindatu da ka ga Hindatu ka ga Momin ta don su na bala'in kama da gudu Hindatu taje ta rungumeta, tana cewa "momi na nayi miss d'in ki", "d'aga ni kar ki karya ni" cewar momin, Majid da ke falon dariya ya yi yace, "idan an girma dai asan an girma" "to in ruwanka" cewar Hindatu ta na 'kara ri'ke momin na ta, su Teemah gaishe da momin su ka yi ta amsa cikin fara'a, tace "a ina ku ka samo wannan?", ta na nu na Safnah, "momin 'yar Baba 'karami mai rasuwa ne" "oh! naga kama kuwa wallahi gata nan kamar Shamsiyya", murmushi Safnah ta yi, waje suka samu su ka zauna, sun d'an taba hira sosai musamman Hindatu da 'kannen ta da idan su ka had'u ba su son rabuwa kamar ta dawo gida ta ke ji wataran, amma idan ta dawo zata bar, Meenal ita kad'ai ne.


Gidaje da yawa su ka je kuma duka gidajen 'yan uwawa ne, Safnah har se da ta yi mamakin yawan 'yan uwan na su, har se magrib su ka dawo gida a haka ma ba su gama ba se gobe za su sake zuwa, sosai ta ga soyayya awajen 'yan uwan na su, wa su kuma ta ga tsantsar kiyayya, don dama ko a 'yan uwa akwai wanda ba ku cika yi da shi ba.


A màtukar gajiye Safnah ta dawo don bata saba irin wannan tafiya ba iyakan ta school se inda ba'a rasa ba se kuma idan ta je garin su kaka, wanka su ka shiga su ka yi su ka fito cikin riga da wando ban da Safnah da ta saka wasu doguwar riga acikin kayan Hindatu.


Falo su ka fito bayan sun shirya, dining su ka nu fa su ka cika cikin su,kafin su ka zauna zaman hira, Safnah ne ta 'kara kar'bar wayan Hindatu, anty ta sa ke kira, kira d'aya aka d'auka, " Hello, ta ji ance, muryar khalil ne kuma, tsalle ta da ka ta fita d'akin da gudu tare da cewa, "Khalil Safnah ne" shima ihu ya yi daga can bangaren yace "Halima! Fatima! Ku zo ga anty Safnah", da gudu su ka nufo shi, Safnah ne tace, "Khalil ina anty?" "Bata nan ta je wani waje ne tabar wayan" "to ya kuke ya school?" "lafiya lau Anty mallam Usman na ta tambayar ki", "ka gaishe shi, kace mai ina katsina, Khalil Safwan fa", "Anty yana nan amma tun da ki ka tafi ban gan shi ba" "to kace ina gaishe shi, ka yi Save sannan idan Anty ta zo kace ta kira ni ka ji" "to Anty yaushe za ki dawo?" "Bazan dad'e ba da yardar Allah", "to Allah ya yarda", "Ameen Khalil, seanjima" tace tare da yan ke wayar wani 'bari na zuciyar ta na jin farin ciki, najin muyar 'yan kannen ta da ta yi, wani 'bari kuma na cikin ba'kin ciki na jin tun tafiyar ta Safwan be neme ta ba, falon ta dawo ta bawa Hindatu wayar ta tare da ce mata "na yi Save wani number da Anty na, idan an kira se ki min magana", "to" cewar Hindatu, tana ajiye wayar kira ta shigo, da sauri ta d'auka don daga jin ringing d'in ta ga ne, "yaya Abdul ta fad'a da ƙarfi tare da cewa yakake ya aiki kuma", "aiki ba dad'i" cewar shi, tace "wani irin ba dad'i ya Abdul se kace ba Namiji ba, ko kai ma zaka gudu ne?" dariya yayi yace "wani irin guduwa 'kanwata ai muna nan har 'karshen rayuwa", "to Allah ya baku Nasara", "Ameen 'kanwata", Meenal da tun da ta ji an ambaci ya Abdul ta aje wayar da take chart ta nufo wajen Hindatu, Hindatu ta na cikin waya ta ji an kwace ta na juyowa ta ga Meenal ta ruga da gudu cikin gida, tana fad'in "ya Abdul abun na fifiko ne ni baza ka kira ni ba se Hindatu?", "ki yi hakuri ba haka ba ne na fi samun number Hindatu kinsan inda muke wataran ba service" "to na ji yaushe za ka dawo gida?", "Bazan fad'a muku ba zan mu ku surprises ne amma na kusa" "don Allah ka fad'a mana", "naƙi" cewar shi Hindatu ne ta sake kar'bar wayan tace "ya Abdul tsarabar mu fa kar ka manta", "to bazan manta ba insha Allah" "yawwa" cewar meenal ita ma ta na jaddada mai tsarabar su, Hira su ka yi sosai don sabo ne sosai tsakanin su da Yayan na su, duk da Soja amma be cika d'aure mu su fuska ba sosai, amma kuma akwai tsanani akwai horo idsn su ka yi lefi don manta wa yake da su ne ma.


Zaria


Washe gari Safwan ya tashi yayi wanka kamar yadda ya saba ya yi shirin school ya fito ya gaishe da Dad shi sannan ya nufi motar da ze tafi da ita ya shiga tare da kunnawa yayi waje, ya so ya fara zuwa gidan su Safnah amma se wata zuciyar ke fad'a masa za su had'u a school, hakan ya sa ya wuce kawai makaran ta, ko da ya isa jama'ar sa na nan zaune su na jiran zuwan sa kafin shiga Class za ma ya yi cikin su su ka gaisa, yace "Safnah fa bata zo ba?" "Ehh bata zo ba" cewar Kamal, sosai hankalin shi ya tashi don yasan indai Safnah ta wuce tara9:00 bata zo ba to baza ta zo bane don bate late gashi tara ta gota. ta shi ya yi bayan ya zube musu kud'i ya nufi can wata kujera da su ke zama, Salmah ya hango ta nufo wajen tsaki yaja a fili sannan yace "wannan kuma fa?", 'karasowa ta yi tare da gaishe shi sannan ta zauna, "Safwan jiya kace min za ka zo gidan mu har na fad'a wa momi na amma kuma ka 'ki zuwa gashi na kira baka d'auka ba" "banajin dad'i ne" ya bata amsa a takaice "Allah ya ba ka lafiya amma idan ka ji sau'ki zaka zo ko?" "Nace miki ban ji sau'ki ba ne, ai idan ban ji sau'ki ba baza ki ganni ba, ina ne anguwar ta ku?", Ta ji haushin tambayar don tun ba yau ba ta ke fad'a mai amma ya manta, "Jushi" tace mai ba tare da ta sake kallon shi ba, "ok anjima zan zo", "dagaske?", "Ehh mana", "amma naji dad'i sosai", tashi su ka yi su ka nufi Class don sun hango Lecturer zai shiga.






??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*15&16


Ko da aka tashi school Safwan gidan su Safnah ya fara zuwa don ganin lafiya?, Anty ya samu ta shaida mishi ta tafi Katsina, baza ta dawo ba kad'an ya rage ya fad'i da jin wannan lamari ta shaida mai kuma wayar ta ta fashe, amma bata fad'a mai ta kira ba don Khalil be fad'a mata ba, da'kyar ya iya komawa gida.


Bayan sallar la'asar ya yi wanka ya shirya don zaman gidan ma ya ishe shi motar shi ya hau ya nufi Jushi se da ya isa kafin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads