Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 57539 words

Chapter 12 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

560

Ads at the middle of Article

gani na zo gidan"


Dariya Sadiq yayi tare da cewa


"Kai! Babban yaya ko dai ka na son wata ne a cikin Familyn mu"


"Ina ruwan ka!"


"Ai na riga na ɗano jirgin ka, akwai wacce kake so wallahi, to ni dai Sa'adatu nake so kuma take so na"


Ajiyar zuciya Abdul ya sauke tare da mamaki yace


"Yaushe har ku ka fara soyayya da Sa'adatu?, Ya akayi kuma babu wanda ya sani"
Abdul ya faɗa


"Ai tsohon labari ne, don mun fi shekara ɗaya1 muna soyayya, kasan Sa'adatu bata da surutu baza ka taɓa ji a bakin ta ba, amma Momyn su ta sani, se kuma Teemah to su ne kawai suka sani"


"To yayi kyau ashe shiyasa nake ga kake yawan zuwa gidan ko?"


"Ehh mana, to kai wacce kake so a ciki?"


Murmushi Abdul yayi tare da miƙewa yace "zaka gani ba yau ba"


"Ok kai ta dama"


"Se anjima abinda na zo ji kenan dama" Abdul ya faɗa tare da fita daga ɗakib.




Kai tsaye gidan su ya nufa, a falo ya samu su Teemah Hindu da Meenal, har ma da Sa'adatu sun yi shiri da alama akwai wajen da zasu je ne.


Gaishe da su su ka yi sannan Abdul yace "Sa'adatu bani wayar ki"


Bata yi musu ba ta miƙa mai, ɗakin shi ya nufa tare da faruq.


Yana shiga kuwa ya saka Number Sadiq yayi dialing a wayar Sa'adatu "My Husband to be" yaga sunan ta fito, dariya ce ta suɓuce masa ba tare da ya shirya ba, nuna wa Faruq sunan yayi shima dariya yayi.


Danna kira yayi ringing ɗaya Sadiq ya ɗaga "Hello my sweet" Sadiq ya faɗa


Dariya Abdul yake yi har yanzu, wanda ya tabbatar wa da Sadiq ba sweet bace ta ɗaga wayar.


"To Sarkin soyayya ni ne ba Sweet ɗin ba" Abdul ya faɗa


"Kai! Amma ka Bala'in rai na min wayo, me ya kawo wayar Babyna hannun ka?"


Dariya Abdul yayi tareda cewa


"Lallai yaro baka da kunya ni kake ce wa Babyn ka, ashe zan yi sizin ɗin wayar nan"


"To se mene, zuwa anjima zaka gan ta da wata" Sadiq ya faɗa tare da yanke wayar.
Abdul ma sauke wayar yayi yana dariya


Se yanzu ya kai duban shi wajen da Faruq yake zaune wayam! Ya gani bashi, tasowa yayi ya fito falon Sa'adatu ya bawa wayarta bayan ya goge Number Sadiq da ya kira.


Har a falon be ga Faruq ba, hakan yasa shi fitowa waje.


Can ya hango Faruq shi da Teemah a wajen motar da suka zo gidan, suna hira, sosai abun ya ɗaure mai kai, komawa yayi ba tare da ya bari sun gan shi ba.


Ɗaki ya koma cike da tunani iri-iri, Faruq se da ya ɗauki wajen mintuna 25 sannan ya dawo ɗakin da sallamar shi.


Zama yayi kusa da Abdul yana waƙar "dama dake na fara haɗuwa da nayi aure tun tuni zama dake akwai ƙaruwa, ni dalling kina burgeni, wayyo!"


Abdul idanu ya zuba mai, ba tare da yace komai ba,


Se da Fatuq ya gama sannan yace "abokina gaskiya ni mai sa'a ne wallahi, don na riga da na sace zuciyar Teemah"


"Kai da gaske kake don Allah?"


"Wallahi kuwa ta amince zata aure ni, wayyo daɗi!"


"To na taya ka murna, Allah ya tabbatar da alkhairi"


"Ameen"


"Nima ka taya ni addu'a, Allah yasa Safnah ta ƙarɓi soyayyata"


"In sha Allah" Faruq ya faɗa.


"Gobe zaka wuce Kaduna ko?"


"Ehh wallahi gida an matsa min na dawo, momy bata san na samo mata suruka ba"


"Lallai kam! Kaga da'ace lafiya lau da na bi ka mun tafi, amma kafin bikin Salma ina nan zuwa "


"To shikenan, momy kuwa tana son mu taho tare wallahi"


"Ka bata hakuri kace mata ina nan zuwa"


"To shikenan".
Zan tsaya anan


Ku biyo ni a cikin littafin nan yanzu ma aka fara, shin Safnah zata ƙarɓi Soyayyar Abdul kuwa? To idan ta Karɓi soyayyar shi ya zata yi da Safwan?


Maganar auren Safwan ya matso shin za'a yi auren ko kuwa Safwan ze zauna ya jira dawowar Safnah ya faɗa mata yana son ta?


Shin wai Safwan da Safnah za su sake haɗuwa ma?


Duk amsoshin ku na nan cikin wannan littafi, ku dai ku kasance tare da ni, Nagode


Taku har kullum


Khadeejerh Ishaq ✍️ ce


More comment
more typing


Share pls






??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*_25&26




*****ZARIA*****


Washegari


Faruq sammakon shiri yayi don tafiya gida, kasancewar kwanan shi biyu anan, ƴan gidansu na ta kiran shi, don sunyi kewar shi, watan shi huɗu4 rabon shi da gida.


7:30 su ka fito shi da Abdul, don se sun fara zuwa asibiti sun duba Safnah daga nan se ya wuce.






Zuwa 7:45 su ka isa asibitin, Safnah ta ji sauƙi sosai, har yau Umma ne ke tare da ita a asibitin, yayin da su Hindu kuwa asibitin ya zaman mu su wajen zuwa akai-akai.


Sun samu Safnah ma tana cin dankali ne haɗe da tea, zama su ka ɗan yi na wa su mintuna, Abdul kuwa se satan kallon Safnah yake don baya gajiya da ganin ta, gashi bashi da hoton ta ko guda ɗaya.




Ƙarfe 8:15 su ka baro asibitin, kai tsaye airport su ka nufa kasancewar Faruq jirgi ze bi.


Suna isa ana sanarwar tashin jirgin na su nan da mintuna10 hakan ya basu damar tattaunawa.


"Faruq ka gaishe da Momy da sauran mutanen gidan, ka bawa momy hakuri kace mata ina nan zuwa nan da two days"


"Ok kar ka damu, amma fa idan ka zo se biki zaka dawo ko?"


Dariya Abdul yayi tare da cewa "wata ɗaya fa kenan, ai se ku kore ni"


"A'a fa ba wata ɗaya ba ne, yau saura 17days ni ne ba na lissafi dai-dai ashe nace maka saura 1month, amma jiya Momy ke faɗa min ai saura 17"


"Ok hakanan yayi yawa, se na zo dai"


"Ok"


Faruq ya faɗa tare da juyawa yana ɗaga mai hannu, shima Abdul hannun ya ɗaga mai, har jirgin su ya tashi, sannan Abdul ya juyo cike da kewar Abokin nashi da yake ji tamkar ɗan uwan shi, kai tsaye gida ya nufo don wani irin bacci yake ji sosai.


A falo ya samu su Meenal na hira, gaishe da shi su kayi sannan ya wuce zuwa ɗakin shi.




"Meenal yaushe za mu ko ma asibitin ne?" Cewar Hindu.


"Ai ki bari kawai ayi sallar azahar, Teemah ma tace zata je"


"Ok to shikenan"


"Hindu kinsan menene kuwa?"


"A'a se kin faɗa!"


"Ina wannan abokin yaya Abdul ɗin"


"Ehh, Yaya Faruq ki ke magana"


"Ehh shi, to shine yake son Teemah"


"Keeee! Meenal bana son ƙarya wallahi"


"Billahil azimu kuwa!, Ɗazu da muka yi waya take faɗa min, kuma jiya baki gan su suna hira ba?"


"A'a hankalina bai kai can ba gaskiya"


"To ai Sa'adatu ta gani"


"In dai hakane kuwa na taya ta murna!, Domin daga ganin shi mutumin kirki ne wallahi, gashi ya haɗu wallahi"


"To kinsan dai halin Teemah, ba lallai ta karɓi soyayyar shi ba"


"Ai kuwa da ta yi asara, ai irin shi mata ke rubibin samun, ga kyau ga kyawun hali"


"To mu miye amfanin mu indai bamu sakata taso shi ba"


"Hakane sister, amma kinsan Teemah da kafiya ko?"


"Hakanan dai"


Haka suka cigaba da hirar su kasancewar ba aikin da zasu yi, mai aiki ne take mu su girki yau, kuma iya na su ne se kaka, don yaya Abdul bashi a lissafi daƙyar idan ze ci, asibiti kuma abinci ma yayi mu su yawa, don idan suka kai ma za su tarar da abinci kala-kala.






*****ZARIA*****


Safwan zaune gaban Dadyn shi suna kallon kayan da Anty ta haɗo na lefe,


"Safwan kayan sunyi kuwa?"




"Ehh Daddy" Safwan yace


"To shikenan" amma a zuciyar Daddy har ga Allah ya rai na kaya, amma ya bari a zuciyar shi ne kawai.


"Na so a kai kayan yau, amma a barshi kawai se na dawo, saboda ina son na ƙaro wasu"


"To Daddy" Safwan ya faɗa tareda miƙewa ya nufi ɗakin shi.


Yana shiga ɗakin shi ya faɗa gado, tare da dafe kan shi da yake mai bala'in ciwo, Computer shi ya jawo tareda kunna ta, wajen hotuna ya shiga hotunan Safnah ne birjik! A wajen, kan wani hoto yaje yayi Clicking yana son hoton sosai Safnah sanye cikin Pakistan riga da wando, blue ta yafa farin mayafi, kafarta sanye cikin wani farin takalmi mai ɗan tudu, ta ɗaga hannayen ta duka biyun kamar mai addu'a, ta yi masifar kyau, kamar ba bahaushiya ba.


Safwan ya kasa ɗauke idanun shi akan hoton, baze taɓa manta lokacin da yayi mata hoton ba, lokacin da su ka je gidan kakan ta a Kano.


"Allah ya mallaka min ke Safnah!, Allah ya dawo min da ke! Ya Allah ka ga zuciyata ya Allah ka yaye min damuwar da nake ciki, ya Allah ka canza min halayena, Allah ka shirye ni"


Addu'a Safwan ke ta rero wa, yayin da Zafafan hawaye ke zubowa daga idanun shi, wani irin matsanancin son Safnah ne ke ƙara shiga zuciyar shi, ya rasa inda ze saka kan shi, ya je gidan Anty yafi a ƙirga ta bashi Number Safnah ta faɗa mai bata dashi, kuma ita ce kawai zata iya haɗa shi da Safnah a ganin shi.


Number Safnah kuwa a kullum yana kira sau ba adadi amma a kashe, hakan na ƙara mai matuƙar damuwa, yayi rama sosai yayi duhu duk tsabar damuwar da ta addabi zuciyar shi, yana samun sauƙi ne kawai idan ya sha giya ya fita hayyacin shi.


Hakan ce ta kasance, yana gama tunanin ya ɗauko kwalaben giyar nashi ya dinga korawa, har ya fita hayyacin shi gaba ɗaya, daga bisani kuma nannauyan bacci ya kwashe shi.




*****JUSHI ZARIA*****


Ƙarfe 10:00 a gida ta yi wa Faruq, iyalan shi na cikin farin ciki sosai da dawowar shi, don an daɗe ba'a haɗuba.


Su huɗu zaune a katafaren falon na su na alfarma, Momyn shi, Daddyn shi, se ƙanwar shi Salmah, da ma su biyu iyayen su suka haifa, hakan yasa suke ganin soyayya sosai a wajen iyayen na su, da dangi gaba ɗaya.


"Yaya ina abokin naka kace tare zaku taho?" Salmah ta tambaya.


"Ehh mun so mu taho tare, amma kuma se wani abu ya tsare shi"


"Allah Sarki Abdul, yaron akwai hankali sosai wallahi ga tarbiyya" cewar Daddyn Faruq.


"Ehh wallahi yaron akwai kirki sosai"


"Amma yace min zuwa nan da two days ze zo" Cewar Faruq


"To yaya, Allah ya kawo shi lafiya" Salmah ta faɗa.


"Faruq ka ga ƙanwar ka ta kusa yin aure, kai ma ya kamata ka fito da matar da zaka aura, ka ga ka girma sosai fa"




Momyn Faruq ta faɗa


Murmushi faruq yayi tare da cewa


"Ai momyna ki kwantar da hankalin ki, na samu matar aure"


"Masha Allah a ina take?" Daddy ya tambaya.


"Daddy a Katsina take, ƙanwar Abdul ce"


"Masha Allah, miye sunan ta"


"Sunan ta Fatima!"


"Yaya kace da walakin, goro a miya, shiyasa kaje kayi zaman ka a gidan mutane ashe ka samo budurwa ne"


"Ehh wallahi ƴar uwa, baki ganta ba Masha Allah"


"Nuna min hoton ta na gani yaya" Salmah ta faɗa.


"To shikenan" Faruq ya faɗa tare da ɗauko wayar shi ya lalubo hotunan da yayi wa Teemah gudu biyu kafin ya taho dama yace zai nuna wa ƴan gidan su ne.


Da sauri Salmah ta kwace wayar don ganin Antyn nata.


Gaban ta ne yayi mummunan faɗuwa ganin wacce take cikin hoto, ta yi mata kama da wanda ta sani, cigaba da kallon hoton ta yi, nan taga tsantsar kamarta da Safnan Safwan.


"To ya akayi haka!, Gashi kuma ance Safnah Katsina ta tafi dama"


Maganar da Salmah take yi kenan a cikin zuciyar ta.


Kwace wayar da faruq yayi a hannunta, shi ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, miƙawa momy wayar yayi don su ma su ga Sukikar ta su, sannan yace


"Sister lafiya kuwa, ko bata miki ba ne"


Murmushin dole Salmah ta kirkiro tare da cewa "yaya tayi mana, kuma ta haɗu sosai wlh"


"To amma meyasa naga kin tafi tunani?"


"Yaya tayi min kama da wata wacce na sani ne"


"Tabbas se dai kama kuwa, don baki taɓa zuwa Katsina ba, bare ki san ta"


"Ehh yaya" Salmah ta faɗa.


"Masha Allah Babana yarinyar ta yi kyau sosai, amma kun gama magana ne?"


"Ehh Daddy mun dai-dai ta, maganar aure kawai za'ayi.


"Yaran zamani ba kunya, su ke maganar aure a gaban iyayensu, amma mu a da ai ko maganar aure ba muyi a gaban iyayen mu" Momy ta faɗa tana mamakin wannan abu haka.


"Ki kyale su zamanin su ne, ai kowa da tashi zamanin"


"Hakane kuma" momy ta faɗa tare da miƙewa ita da Daddy su ka nufi ɗaki, suka bar Salmah da Faruq.


"Sister har yanzu ban san Ƙanin nawa ba fa! A ina yake?"


Murmushi Salmah ta yi tare da rufe fuska, sannan tace


"Yaya Safwan ne fa, ɗan gidan abokin Daddyn nan"


"Ok! Alhaji Muhammad ko?"


"Ehh shine"


"Sunan yaron Muhammad ko?"


"Ehh yaya, amma Safwan ake kiran shi ai"


"Ok da nasan yaron sosai, amma tunda na daina zama sosai se na manta shi, ina jin ko a hanya dakyar zan gane shi, amma a ina ku ka haɗu ne sister?"


"Yaya a School"


"To Allah ya bada zaman lafiya, to me kike so nayi miki na gudummawar bikin?"


"Yaya duk abinda ya samu ina so"


"To shikenan bari naje ɗaki nayi wanka na zo na fita naga gari"


"To yaya" Salmah tace tare da tashi itama ta nufi nata ɗakin.




*****KATSINA*****


Jikin Safnah yayi sauƙi sosai hakan yasa ma aka rubuta mata sallama ta koma.


Zaune su ke suna hira a part ɗin su Teemah don tunda aka sallami Safnah yau kwana biyu 2 kenan part ɗin take zai ne, don sunyi wani irin sabo da Umma sosai don ji take kamar itace mahaifiyarta, su Hindu ma anan su ke wuni sosai se dare su koma, Safnah kuwa a ɗakin Teemah take kwana.


A bangaren ya Abdul hakan yasa har yau be furta kalmar so ga Safnan ba, saboda ba su haɗuwa se dai idan ya je part ɗin Umma, kuma a gurguje yake zuwa.




Yau ma kamar kullum Teemah ce da Safnan zaune a ɗakin Teemah suna hira wajen ƙarfe 8:30 na dare, kira ne ya shigo wayar Teemah, cikin sauri ta jawo wayar, don dama jiran kiran take tana jin ringing ɗin kuma ta gane shi ne, wato farin cikin ran ta (Faruq).


Ɗaga wayar ta yi fuskar ta ɗauke da Murmushi "Assalamu alaikum gimbiyar mata" Faruq ya faɗa daga can ɓangaren.


"Wa-alaikumussalam" Teemah ta faɗa da sassanyar Muryar ta,


"Gimbiya ta da fatan kina lafiya?"


"Lafiya lau masoyi na ya Momyna"


"Momyna lafiya lau ya Ummata?"


"Ta na lafiya"


Safnah dai bin Teemah kawai take yi da ido tana sauraren hirar ta su, wanda ka na ji kasan tsantsar so da ƙauna sun zauna a wurin.


Kusan mintuna talatin30 Teemah ta kwashe suna waya da Habibin nata sannan su kayi sallama.


"Safnah kinsan menene?"


"A'a se kin faɗa"


"Wai dama haka so yake, a da ban taɓa tunanin zan faɗa soyayya nan kusa ba, amma wallahi haɗuwana da Faruq ya canza komai, ya canza min tunani na, ina masifar son shi, ta yadda ba na jin zan iya son wani bayan shi"


Maganar da Teemah ta yi ya tono wa Safnah son Safwan da ta samu ya ɗan lafa kwana biyu2 kwalla ne suka cika mata idanu.


Cikin ƙoƙarin kawar da kwallar tace


"Teemah tabbas so babbar cuta ce, kuma lokaci ɗaya take shigar mutum ba tare da son ran shi ba"


Tana ƙarasa maganar kuka ya kwace mata duk da ƙoƙarin da ta yi na danne kukan nata.


"Subhanallahi!, Safnah lafiya kuwa?"


Safnah bata ba Teemah amsa ba, se ma sautin kukanta da ya ƙaru.


Daƙyar Safnah ta samu ta tsayar da kukan da take yi.


"Safnan kin taɓa faɗawa tarkon soyayya ne?, Don nasan maganar da nayi ne yasa ki kuka"


"Teemah tun zuwa na gidan nan nake fama da tsantsar damuwa na kewar masoyin da ban tabbatar da so na a zuciyarsa ba!, A kullum da tunanin sa nake kwana kuma dashi nake tashi"


"Safnan to yaya akayi haka!, Kuma shi ɗin wanene?"


"Teemah zuciyata ta amince da ke hankalina ya kwanta dake kuma ke kaɗai zuciyata ta amince da na faɗa wa sirrin da ba kowa ya san shi ba a rayuwana, shi wanda nake faɗa miki abokin karatuna ne kuma abokin shawarana, munyi shakuwa sosai wanda mutane ke cewa soyayya ce, amma kuma bamu yarda da cewa son junanmu muke yi ba, daga baya ne na fara tabbatar da cewa ina son Safwan saboda ko kwana ɗaya idan nayi ban ganshi ba, ba na jin daɗi, amma shi a ɓangaren shi na kasa fahimtar so na yake ko kuwa kawai abota ce"


Safnah ta tsaya da maganar har yanzu hawaye na bin fuskarta, Teemah kuwa ta cika da mamakin lamarin Safnah, daurewa tayi tace


"Safnan naji labarin soyayyar ki, amma ki sani da ace yana son ki da ze faɗa miki a gani na amma"


"Hakane, amma wani ɓari na zuciyata yana faɗa min yana so na"


"To shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ya kamata mu kwanta dare yayi, da safe se muyi magana"




"To shikenan" Safnah tace tare da kwanciya.


A ranar daƙyar bacci ya ɗauketa se tunane-tunane take yi.


Zan tsaya anan


Kuyi hakuri da wannan in sha Allah gobe zan yi typing da yawa.


Ku kasance da ni a cikin wannan littafin nawa don jin yadda zata kaya, yanzu dai aka fara wasan, ina jin daɗin yadda kuke son wannan littafin nawa sosai ina muku fatan alkhairi da fatan anyi sallah lafiya.




More comment
more typing


Khadeejerh Ishaq ✍️ ce





??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads