Header Ads
Showing 30001 words to 33000 words out of 92878 words

Chapter 11 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*


*Gaskiya ina jin dadin yadda kuke kkokari wajen zaman lafiya da kula da juna. Ina gaishe lu yan kungiyar mu. Allah kara muki basira da daukaka.*




Dedicated to *My Lovelly Momy*








*106 - 110*


*Karanta Alkur'ani a gida*
*Yana Daga Cikin Dalilan Dake Nuna Haka Hadisin *Abi-Hurairah (ra)* Inda *Manzon Allah(ﷺ)* Yake Cewa:_


*{ﻋَﻦْ ﺃَﺑِﻲ ﻫُﺮَﻳْﺮَﺓَ ﺃَﻥَّ ﺭَﺳُﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻬﻢ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ ﻗَﺎﻝَ ﻟَﺎ ﺗَﺠْﻌَﻠُﻮﺍ ﺑُﻴُﻮﺗَﻜُﻢْ ﻣَﻘَﺎﺑِﺮَ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥَ ﻳَﻨْﻔِﺮُ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﺒَﻴْﺖِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺗُﻘْﺮَﺃُ ﻓِﻴﻪِ ﺳُﻮﺭَﺓُ ﺍﻟْﺒَﻘَﺮَﺓِ [مسلم:٧٨٠]}*


'''Fassara:''' _An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Kada Ku Mayar da Gidajenku Kamar Makabartu, Lallai Shedan Yana Gudu Daga Gidan da Aka Karanta Suratul Baqara a Cikinsa".* (Muslim: 780)_


*Lallai karata Suratul bakara a ggida yana da amfani. Dan akwau wata Mamanah in ta saka a gida har tsorata ta ake. Da ta tambayi wani malami ya ce ta cigaba da sakawa insha Allahu ta daina gani.*


*Ko kunsan cewa in da wani sihiri a tare da kai ko al jannu karanta suratul bakara ko saka karatun ta yana baka kariya.*


*Mu daure da karanta ta ko da aya kadan ke daga ciki*
*Mu daure da son karanta alkur'ani*












Watan Yaa Aslam daya ya fara shirin tafiya.


Asma'u ji tayi kamar me, dan kuka ta sha shi tinda ya ce mata zzai tafi.


Ranar Asabar ya saka tafiyar tashi. Ranar juma'a ya dauke ta ya kai ta shopping yai mata siyayya mai yawan gaske.


Amman duk jikin ta a sanyaye yake da ka kalle ta zaka san bata da walwala.


Haka suka dawo gida duk yadda yaso ta sake kasawa tayi sai dai ta dan yi masa murmushin yake.


Da dare bayan sun ci abinci ta shiga dakin sa dan taya shi hada kaya.


Shima yana kwance ya fito da kayan ya ajiye akan gado.


Tunanin shima rabuwa da ita yake. Kallon sa tayi ta wuce wajen kayan ta fara zuba masa a cikin akwatin sa.


Motsin ta da yaji shi ya sa shi bude idon sa. Kallon ta ya tsaya yi hada masa kayan take cikin sanyin jiki.


Jin idon sa akan ta yasa ta kalle shi, Murmushi ta sakar masa, ta cigaba da abinda taken.


Mikewa yayi zaune ya zura mata ido. Ko kiftawa baya yi.


Har ta gama bai dauke idon sa daga kallon ta ba.


Takalman sa ta fara hadawa ta gama ta koma gefen sa ta zauna.


Kallon sa ya dawo da shi kan ta, murmushi ta kara sakar masa.


"Yaya nah lafiya?"
Ta tambaye shi.


"Baby nah bana son ganin ki a damuwa,"
Ya fada yana kamo hannun ta.


Hannun ta. ta zare ta ce,
"Yaya nah naji sai kuma me?"


"Bansan menene ba. Amman bana son barin ki Asma'u bana son nima na tafi. Ki yadda nayi magana ai mana auren kinji."


Kasa tayi da kanta sannan ta ce,
"To Yaya nah yanzu in mukai auren karatu na fa. Kaga nazo gangara ka bari nan da wata shekara sai muyi aure ko?"


Kai ya gyada ya ce,
"Haka ne, amman bana son na rasa ki bana son nayi nesa da ke."
"Haba Yaya nah kar ka manta fa dazu kai ka gama lallashi na akan nayi hakuri muna tare ko?"


Hannun ta ya kamo ya matse shi a cikin nasa. Ido ya lumshe, sannan ya bude.


Kallon ta ya tsaya yi tin tana kallon cikin idon sa, har ta gaza kalla dan wani abu take ganin yana shiga cikin nata.


Lumshe idon tayi matsowa yayi kusa da ita. Ya ce,
"Asma'u ki riken Alkawari na kar ki taba bari na in dai ina cikin duniyar nan ina son ki yi min alkawarin ke tawa ce."


Idon ta, ta bude wanda suka canja kala zuwa ja, ta ce,
"Wallahi Yaa Aslam na maka wannan alkawarin bazan taba barin ka ba. Sai dai in kai ka bukata."


Ido ya lumshe samnan ya ce,
"Ni kuwa tayaya za'ai na bukaci rabuwa da rayuwa ta."


Murmushi tayi ta ce,
"Bare kuma ni."


Yayi murmushi.
"Bari naje na kwanta!"


Kallon ta yayi ya ce,
"Kamar mu kwana tare."


Murmushi tayi ta ce,
"Allah kawo ranar da zamu kwana taren."


"Ameen!"
Ya fada yana mikewa. A kofar dakin ta suka kara tsayawa sun dauki kusan minti ashirin suna tsaye sannan sukai sallama ta shiga.


Tana shiga daki ta fashe da kuka. Rasa kukan me take tayi amman ta san cewa ba zai rasa nasava da tafiyar Yaa Aslam ba.


Sai da taji kiran sa a waya sannan tai saurin shiga bayi tai wanka ta fito ta shirya sanann ta kira sa.


"Baby na kin kwanta ne?"
Ya tambaya daga can site din.


"Eh yanzu na kwanta."
ta bashi amsa.


Ya ce,
"To kiyi addu"a sai da safe."


Ta ce,
"Allah tashe mu lafiya."
Ta fada tana kashe wayar.


Washe gari tin asuba ta tashi ta yi duk abinda zata yi.


Wanka tayi ta koma gado tai kwanciyyar ta.


Sai karfe sha biyu sannan ta mike ta kara watsa ruwa ta shirya cikin wani tissue pink material wanda akai mata dinkin fitetgown, batai kwalliya ba.


Hoda da man lebe kawai ta shafa sai kwalli da ta saka a idon ta.


Falo ta fito ba kowa a sama a kasa ta dinga jin maganar su.


Sauka tayi a hankali ba ta kalle su ba sai da ta shiga kkitchen.


Ruwan zafi kawai ta hada ta fito falo. Sai da ta gaishe da Yaa Aslam da Yaa Buhari sannan ta nufi daining.


Zama tayi ta kasa shan tea din ma. Yaa Aslam ne ya mike ya shiga kitchen ya dafa mata indomie sai ya soya mata kwai.


Daining ya nufa ya zauna a kujerar dake facing tata.


Kallon sa tayi ta sakar masa murmushi.


Plate din hannun sa ya tura mata gaban ta. Ya daga mata gira alamar 'ta ci.'


Ja tayi ta saka spoon tana ta wasa da shi.


Amsar spoon din yayi ya fara bata a baki. A hankali a hankali har ta ci mai yawa sannan ta ce ta koshi.


Falo suka koma suna hira da Yaa buhari ita kuwa tai shiru sai dai ta kalli.wannan ta kalli wannan.


Kiran sallah aka yi wannan yasa kowa ya tafi dakin sa.


Alwala su Yaa Aslam sukai suka wuce massalaci.


Ita kuma a daki tai sallar tinda ta idar ta kasa tashi daga inda take har karfe biyu tana zaune.


Yaa Aslam ne ya shigo dakin cikin shirin tafiyar sa.


Yana sanye da Milk din wando sai maroon kalar riga mai dogon hannu.


Takalmin kafar sa ma maroon ne. sai tashin kamshi yake.


Tana ganin sa ta mike ta saki fara'a shima murmushin yayi ya kamo hannun ta suka fito.


Mami na falo suka tadda ta. Sallama yai mata suka fice tare.


Yaa Buhari ta gani a cikin mota yana jiran su.


Bayan mota suka shiga daga ita har shi har lokacin hannun ta na cikin nasa.


Wata zoben azurfa ya fito dashi daga cikin jakar sa. Ya zura mata a yatsan ta take hannun ya kara gaske yai mata kyau.


Sumbatar hannun yayi yana kallon cikin idon ta.


Lumshe idon tayi tana mai yin murmushi.


Suna zuwa airport din Yaa Buhari ya fita a motar.


Kallon ta yayi ya ce,
"Baby na zan tafi ki kular min da alkawari na."


Asma'u Ta ce,
"To Yaya nah Allah kiyaye hanya, kar ka manta da alkawari na nima kaji."


Ya ce,
"Insha Alalhu bazan manta ba!"
Yai mata kiss a goshi sannan ya fita.


Ta taga ya leko ya ce,
"Ki zauna ba sai kin ffito ba. Kai ta daga masa sai kuka kuma.


Kuka sosai take ba shiri ya koma cikin motar ya jata jikin sa yana lallashin ta. Amman kamar kara zuga ta yake.


Ya jima yana lallashin ta da kalamai masu sanyaya rai yaji ta daina kuka.


Bai daina shafa mata bayan ta ba da kwantar da hankalin ta. Sai da ya dauki minti goma a haka sannan ya dago dan ya ga me take.


Bacci yaga tana yi sai ajiyar zuciya take saukewa.


Murmushi yayi ya kwantar da ita sannan ya kara kissing nata a goshi.


Waya ya dauko ya dauki pics din ta sannan ya fita a hankali.


Yaa Buhari ya gani suka karasa ciki. Basu jina ba ya tashi. Dawowa mota Yaa Buhari yayi ya ganta tana ta baccin ta.


Motar ya tayar suka tafi gida a hankali yake tukin duk dan kar ya tashe ta.


Yana tausaya musu yana musu addu'a akan Allah ya mallaka musu juna su. Dan son da sukewa juna su shi gani yake kamar yayi yawa.


Kuma yana tausaya musu dan kar wani a bu ya faru bai san wane hali zasu shiga ba.


Har ya isa gida bata tashi ba. Daukar ta yayi ya kaita dakinta samman ya sanar da Mami sun dawo.


Sai magariba ta tashi. Tana bude ido taji idon ta a kumbure.


Taba su tayi sai kuma ta tuna da abinda ya faru dazu.


Wani kukan ta kuma saki ita kadai tayi iya yin ta sannan ta mike ta shiga ban daki.


Wanka tayi tayo alwala ta fito ta saka kayan bacci ta tada sallah tana idar wa ta kwanta anan inda take


Wani bacci ya kuma sace ta. Sai tara saura ta farka.


Bandaki ta shiga tai alwala ta fito tai sallah zata hau gado kenan sai ga Mami da Dady nan sun shigo.


Mami rike da katon tire a hannu. Gefen ta Dady ya zauna ya ce,
"Wannan shakuwar taku Asma'u tayi yawa. Yanzu inda Yayan naki yai aure ai sai Antyn ki tana jin haushi kiyi hakuri da kin gama karatu zaki je ki musu hutu kinji."


Kai ta daga tana masa murmushi sannan tai masa sannu da zuwa.


Abinci Mami ta zuba mata sai da ta ga taci ta koshi sannan suka fita daga daki


Kan gado ta koma ta kwanta kiran sa ne ya shigo.


Dagawa tayi cikin sanyin murya. Ta ce,
"Yaya nah ka isa lafiya yasu Momy da Dady?"


"Duk suna lafiya ya na baro ku?"
"Lafiya Alhamdulilah."


"Wallahi ina kewar Baby na."
Murmushi tayi ta ce.
"Nima haka."


Daga haka suka fara hirar su kamar yadda suka saba.


Sun jima suna hira sannan sukai sallama kowa ya kwanta.




*Uhmmm*










*INDABAWA*
[1/18, 14:19] Maryam S Indabawa🥰: *Asma'u Husnah*






Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*






🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*






Dedicated to *My Lovelly Momy*
Allah kara budi Allah ya daukaki. Ameen.






*111-115*


_Har Wayau An Kar6o Hadisi Ingantacce Daga *Jabir (ra)* Yace Yaji *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa:_


*{ﻋَﻦْ ﺟَﺎﺑِﺮِ ﺑْﻦِ ﻋَﺒْﺪِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ، ﺳَﻤِﻊَ ﺍﻟﻨَّﺒِﻲَّ ﺻَﻠَّﻰ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠَﻴْﻪِ ﻭَﺳَﻠَّﻢَ , ﻳَﻘُﻮﻝُ : " ﺇِﺫَﺍ ﺩَﺧَﻞَ ﺍﻟﺮَّﺟُﻞُ ﺑَﻴْﺘَﻪُ ﻓَﺬَﻛَﺮَ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋِﻨْﺪَ ﺩُﺧُﻮﻟِﻪِ ﻭَﻋِﻨْﺪَ ﻃَﻌَﺎﻣِﻪِ , ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥُ : ﻻ ﻣَﺒِﻴﺖَ ﻟَﻜُﻢْ ﻭَﻻ ﻋَﺸَﺎﺀَ ، ﻭَﺇِﺫَﺍ ﺩَﺧَﻞَ ﻓَﻠَﻢْ ﻳَﺬْﻛُﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋِﻨْﺪَ ﺩُﺧُﻮﻟِﻪِ , ﻗَﺎﻝَ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥُ : ﺃَﺩْﺭَﻛْﺘُﻢُ ﺍﻟْﻤَﺒِﻴﺖَ ، ﻭَﺇِﺫَﺍ ﻟَﻢْ ﻳَﺬْﻛُﺮِ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋِﻨْﺪَ ﻃَﻌَﺎﻣِﻪِ , ﻗَﺎﻝَ : ﺃَﺩْﺭَﻛْﺘُﻢُ ﺍﻟْﻤَﺒِﻴﺖَ ﻭَﺍﻟْﻌَﺸَﺎﺀَ [مسلم:٢٠١٨]}*


'''Fassara:''' _An Kar6o Daga *Jabir bn Abdullah (ra)* Yace: Naji *Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Idan Mutum Zai Shiga Gidansa Sai Ya Ambaci Allah Yayin Shigansa, da Kuma Lokacin da Zaici Abinci, Sai Shaidanu Suce (da 'Yan Uwansu Shaidanu): Baku da Wurin Kwana Kuma Baku da Abincin Dare. Idan Kuma Ya Shiga Gidan Be Ambaci Allah Ba a Yayin Shigansa, Sai Shaidan Yace (da Yan Uwansa Shedanu): Kun Samu Wurin Kwana. Idan Kuma Be Ambaci Allah ba Yayin Cin Abinci, Sai Shaidan Yace da Yan Uwansa Kun Samu Wurin Kwana da Abincin Dare".* (Muslim)


















Haka rayuwa ta cigaba dan gashi har Asma'u sun fara exam.


Murna suke dan baza su dawo skul ba asibiti zasu tafi su zama student doctor.


Sun gama Exam lafiya. Inda suka koma gida suna shan hutun su.


Dady kuwa har ya dawo an gama hada mata asibitin ta.


Bangaren Yaa Aslam kuwa sai wata kulawa da ya dada bata.


Dan shakuwar su ta koma yawa yanzu haka ma zai zo wani aiki zai yi sati daya a kano.


Murna gun Asma'u kamar me?


************
Bangaren Sabir kuwa, duk ya damu bama da akai hutun nan baya samun damar ganin Asma'u.


Mamah ta rasa me yake damun sa dan ba karamin sauyawa yayi.


Duk yadda Mamah taso ya fada mata damuwar sa ki yayi sai dai ya ce ba komai.




Zaune yake akan kujera dake garden din gidan su.


Idonsa a lunshe sai sake saken yadda zai ga Asma'u yake.


Can ya mike zaune da sauri yana lalubar number wayar Maryam.


Kira yayi sai da ta daga suka gaisa sannan ya ce,
"Daughter number wayar *Husnah* nake son ki bani."


"Ohk bari na turo maka."
Ta katse wayar tana murna dan tin da taga Asma'u taji tai wa Uncle din ta sha'awar ta.


Nan da nan ta tura masa, tana addu'ar Allah yasa ta zama matar sa.


Yana ganin number yai saving din ta da. *My Hussy*


Ya jima yana kallon sunan sannan ya tafi kira.


Tana tafiya zai yi sauri ya katse kiran.


Yayi haka fin sau goma sannan ya hakura dan ya rasa me zai ce mata in ta dau wayar.


Ya jima yana tunanin abinda zai ce mata.


Sako ya tura mata da wani sabon sim din sa. sannan ya ajiye wayar.


Can kuma ya dau wayar ya shiga whatsapp din sa.


Searching sunan ta yayi sai gashi yayi appearing.


Nan da nan ya shiga ciki. Last seen nata bata dade da sauka ba.


Profile picture din ta ya bude, Hoton Asma'un ya gani tana tsaye a garden din su.


Sanye take da wata jar doguwar riga tayi rolling da bakin mayafi.


Hannun ta rike da waya fuskar ta ba makeup amman tayi kyau tana murmushi dimple din ta ya lotsa.


Ba karamin kyau tayi ba, da sauri yai saving hoton sannan ya kura mata ido.


Kasa dauke idon sa yayi daga kallon hoton. Ido ya lumshe, Sannan ya bude ya saki wani murmushi.


Mikewa yayi ya shige cikin gidan. Wanka yayi ya shirya cikin Blue din shadda, ba karamin kyau yayi ba.


Mikewa yayi ya fita. Mamah ya gani a falo. Karasa wa yayi ya ce,
"Mamah zan fita."


Kallon sa tayi taga ya canja cikin lokaci kadan.


Kallon sa tayi ta ce,
"To a dawo lafiya."


"Ameen!"
ya asma ya fita.


Kallo Mamah tabi shi da shi har ya fice.


Shoprite ya nufa kai tsaye daga gida. Ciki ya shiga, ya fara shopping hankalin sa kwance.


Kamar daga sama ya hango ta tana dibar kaya ita ma,


Ido ya goge ya ga da gaske dai ita din ce.


Tsayawa yayi da dibar kayan ya dinga binta da kallo. Sanye take da Ash kalar doguwar riga, sai bakin mayafi da ta yafa da jaka da takalmi duk bakake. Binta ya dinga yi da kallo har ta gama tayi wajen biya.


Da sauri shima yayi gun. Yana zuwa ta karasa itama.


ATM card din sa ya mika aka zara, juyowar da zai yi suka hada ido.


Da sauri tai kasa da kai, ta dan durkusa ta ce,
"Sir Ina yini?"


Kallon ta ya dan karayi ya amsa da
"Lafiya lou, ya hutu."


"Alhamdulilah!"
Ta bada amsa kan ta a kasa.


"Masha Allah. Bayar a lisaafa miki."
Mikawa tayi ya tsaya yana jiran a gama ya biya.


Anan gamawa ya mika masa card din sa ya ce, ya dauka a ciki.


Kallon sa Asma'u tayi ta ce,
"Lah Sir da kudi aguna."


Kallon ta yayi ya ce,
"Ai na sani. Na dai biya miki ne kawai."


Dan durkusa wa tayi ta ce,
"Nagode!"


Daukar mata ledar yayi ya dauki tashi suka fita.


A Napep take dan haka ta ce, fita zatayi zata hau mota.


"Muje na rage miki hanya."
Ya fada yana yin wajen motar sa.


Ba dan taso ba tabi bayan sa. Shi ya bude mata mazaunin ta sannan ya koma ya shiga bangaren sa.


Motar ya tayar suka fita sannan ya dan kalle ta ya ce,
"Ina zamuyi?"


"Jan bulo. 3rd gate wajen forestry."
kai ya gyada suka dau hanya.


A hankali suke tafiya kamar baya son tukin duk dan kar su rabu.


Kallon ta ya danyi yaga hankalin ta na kan Wayar ta da take dannawa.


Kai ya dauke ya cigaba da tuki. Kiran ta akai ta daga tana satar kallon sa tayi sannan ta dauka.


A hankali tayi sallama, daga dayan bangaren ya Amsa.


"Baby nah kina ina ne?"
Dan taga missed din sa ganin suna tare da Sir Sabir ne ya sa bata kira sa bba.


"Naje shoprite ne, ya kake ya aiki?"
Ta tambaye shi.


"Lafiya Alhamdulilah! Me da me kika siyo?"
"Uhmm in naje gida zan nuna maka su."


"Ok sai kin dawo. Ki kular min da kan ki."
"To nima ka......."


Sai kuma tayi shiru. Ganin Sabir na kallonta.


Kasa tayi da kanta ta ce,
"Sai na koma"


Ta katse wayar. Sabir kuwa jin tana waya da namiji ba karamin tada masa da hankali yayi ba.


Har suka je unguwar ta nuna masa layin sannan suka karasa kofar gidan.


Horn yayi mai gadi ya bude masa gate suka shiga.


Mami suka gani zaune a barander dake kofar falo.


Fitowa tayi tai masa godiya. Kallon wajen da Mami tayi ta ce,
"Kazo ku gaisa da Mami."


"Ok!"
Ya fada yana fitowa.


A hankali cikin nutsuwa suka karasa wajen da Mami take.


Suna zuwa ya durkusa ya gaishe da Mami.


Bayan sun gaisa ne, Asma'u ta ce,
"Mami wannan shine Sir Sabir lecturer mu ne, mun hadu a shoptite kinga shi ya biya min kudin siyayya ta ma ya rage min hanya kuma."


Kai Mami ta gyada ta ce,
"Kai Sabir har da wahala haka. Angode to Allah saka da alheri "


Asma'u ta kalla ta ce,
"Ki kawo masa lemo man."


"A'ah Mami wallahi Alhamdulilah."
yai maganar kan sa a kasa dan kunyar Mami yake ji sosai.


"A'ah Sabir kar muyi hka da kai."
Ta kalli Asma'u ta ce,
"Je ki dauko masa."


Mikewa Asma'u tayi tayi cikin gida. Bata jima ba ta dawo rike da 5alive na kwali sai kofi a hannun ta da plate da ta zubo cake a ciki.


Ajiyewa tayi akan table din dake wajen. Mikewa mami tayi ta ce,
"Ka saki jiki kaci kaji."


Tayi cikin gidan. Zama Asma'u tayi akan kujera ta nuna masa dayar ta ce,
"Bismillah!"


Mikewa yayi ya zauna ta zuba masa lemo.


Lemon kadai ya sha sanna ya mike ya ce, zai tafi.


Har cikin falo ta raka sa yayi wa Mami sallama sannan suka fito har bakin mota ta raka shi.


Sabir kuwa sosai yaji dadin irin tarbar da Mami tai masa.


Sosai ya dinga murna dan ya ga gidan su Asma'u.


Da haka ya tafi gida ransa kamar takarda dan farin ciki.


Yana komawa ya zauna a falon suka dinga hira da Mamah.


Mamah dai sai mamakin canjin sa take dan ya jima bai zauna sun yi hira kamar haka ba.


Suna zaune Abbi ya dawo. Nan suka zauna suna ta hira har akai sallah magariba suka je sukai sallah suka dawo.


A falo suka zauna suka ci abinci sannan suka ci gaba da hira har lokacin baccin su yayi suka mike suka yi dakin nan su.


Yana shiga daki ya tura mata da sakon sai da safe da kalamai masu dadi.


Ban daki ya shiga yayi wanka ya fito ya haye gadon sa.


Online ya hau ya dinga kallon ta a online amman ya kasai mata magana.


Haka ya shiga gallery ya maida hoton ta kamar TV.


Da shi yayi bacci.














*INDABAWA*
[1/18, 14:19] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*


*Asma'u Husnah*






Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*






🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*






Dedicated to *My Lovelly Momy*








*116-120*


AN Ruwaito a Cikin Littafin Ibn-Sunni, da Sanadi Me Rauni, Daga *Abi-Sa'eedil Khudry (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)*

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads