Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 92878 words

Chapter 2 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ya dafa miki Ameen. Amman muna jiran cigaban *Yafi dare dugu* a taimaka mana*


Dole na yabe ki AMRAH A MASHI PrincessAmrah. Gaskiya littafin nan Amrah nake so yayi kina kokari Allah ubangiji ya dafa Allah yasa a gama lafiya


*Ameen.*








Suna shiga mota, Aka kira ta. Dagawa tayi, da fara'a akan fuskar ta.


"Assalamu Alaikum!"
Ta fada dauke da murmushi.


"Wa'alaikum salam!"
Aka amsa mata daga can bangaren


"Ina kwana Yaya nah!"


"Lafiya lou. Kin fita dai ko."
"Gani a hanya."
ta amsa masa"Ina hoto nah?"
y


a tambaya.


"Bari na turo maka. Ina nawa?"
Ta fada tana lumshe ido.


"Naki yana can yana jiran ki."
ya bata amsa.


"Masha Allah ganawa nan zuwa."
Ta kashe wayar. whatsapp ta hau tayi masa sending pics din da ta dauka.


Nasa ta fara budewa, kallon wayar ta zubawa idanu.


Wani hoto ne ya bayyana, akan wayar ta.


Wani hadaden Balarabe ya bayyana, yana sanye cikin bakar suit, idon sa sanye da farin gilashi.


"Masha Allah! Yayanah kayi kyau."
Ta tura masa.


Amsa ya turo mata.
"Tabarakallah! Allah nagode maka da ka bani wannan kyakyawar yarinyar Allah ka mallaka min ita."


"Ameen Ya Allah Yaya na. Ka fita ne."
"Gani a hanya."


"To kaje ka duba mutane sai anjima."
Ta fada.


"Toh ki kular min da kanki kar ki bari kowa ya kalli fuskar ki."


"Hmm ka kular min da kanka nima."
Ta sauka a online. Titi ta kalla.
"Haba Yaya."


"Mene?"
Ya tambaya yana kallon ta. Fuska ta dan bata ta ce,
"Baka sauri fa."


Murmushi yayi ya ce,
"Karbi tukun."


"A'ah yi hakuri. Amman dan Allah ka dada sauri kaga har tara tayi."
ta fada tana marairaice masa fuska.


Sauri ya dada sukayi gaba, yana direta ta bude kofar da sauri.
"Nagode Yayana ka bada sako ga Besty nah."
Ta fada tana murmushi


Hararar ta yayi.
"Ban da wayar ta ne ko baki."


"Allah sarki Yayanah ji zanyi ko da gyaran da zan maka ne dan nasan na fika iya love."
ta fada tana kanne masa ido daya.


Kokarin bude kofa yake ya fito.
"Yi hakuri!"


Ta fada tana yin gaba da sauri.


Kofar ajin ta karasa. Wani kyakyawan saurayi ne a ciki baki ne amman yana da kyau ba kadan ba.


Sai kayi tsamanin irin black american nan ne.


Sanye yake da farar shadda kansa ba kula sai gashi da ya kwanta luf luf akan sa.


Lekawa take yi jifa jifa. Ganin sun hada ido yasa tai saurin dauke kan ta.


Fita yayi ya zuba mata ido. Kai ta dukar kasa. Kallon ta ya cigaba dayi.


"Wa kike nema."
Ya tambaye ta da turanci.


"Uhmm daman yanzu nazo ne."
ta bashi amsa tana in ina.


"Shine kuma me?"
Ya tambaye ya.


"Ba komai."
Ta fada jiki a sanyaye


"Karfe nawa kuke da lecture?"
Magana yake cikin turancin da ya kware a bakin sa.


"Sir karfe tara."
ta fada masa kan ta a kasa.


"What say's d time now (Karfe nawa yanzun)."
"Ban sani ba."


Kallon ta ya tsaya yi. Sannan ya duba agogon hannun sa. Karfe tara da rabi.


"9:30am yanzu ne lokacin zuwan ki."
"I am sorry Sir."


"Naji daga yau kika makara kar ki kara dosan kofar ajina kinji ko?"
Kai ta gyada masa.


Kanta a kasa taki yadda su hada ido dan wani kwarjini yayi mata.


"Shigo ciki."
Ya fada yana yin gaba


A gaban allo ya tsaya tayi hanya zata shige ciki.


"Come here (zo nan),"
Ya fada yana nuna mata wajen da zata zauna. A gaban sa.


Komawa tayi ta zauna, duk dagowar da zatayi idon sa na kanta. Kuma duk tambayar da zaiyi ita yake jefawa.


Sosai take bashi amsa dan *Asma'u* akwai kokari.


Sai karfe sha daya yabar ajin nasu. Tana zaune a inda take zaune sai ga Zainab ta karaso wajen ta.


" *Asma'u* amman fa kinyi sa'a har malamin nan ya bar ki kika shigo."


"Nima nayi mamaki dan kinsan haka yan wacan shekara suka sha fama dashi."


"Dan Allah kina dai kula."
zainab ta fada cikin damuwa dan bata son kawar tata ta rasa aji.


"Kar ki damu yau ma akasi aka samu ne."


Wani malamin ne ya shigo musu, yai musu lectures dan sai karfe daya ya fita.


Yana fita suka shige, masallaci. Sai karfe daya sukai sallah sannan sukayo cafeteria.


Lemo kawai ta karba, sannan ta tambayi Zainab me take so. Ta siya mata.


Suka samu wajen zama.
"Sis wannan gayen fa ya dame ni da maganar ki."


Murmushi *Asma'u* tayi,
"Wane gaye fa."


Hararar ta Zee tayi,
"Wai har kin manta."


Asma'u ta ce,
"Wallahi na manta."


Zee ta ce,
"Wannan Nasir din dan unguwar mu."


Murmuahi Asma'u tayi ta ce,
"Oh na tina. Ya akayi."


Dan hararar ta zee tayi ta ce,
"Wallahi ya dame ni ne."


Kallon Zainab Asma'u tayi ta dan saki murmushi ta ce,
"Ki bashi hakuri kinsan dai irin karatun da muke ciki ko?"


Zainab ta ce,
"Haka ne, amman ai karatu mun gama tinda asibiti zamu tafi, ya kamata ki maka ma miji da mun kammala sai mu shige gidan mu ko."


"Haka ne Zee amman nifa nayi karama da yawa!"
Hararar ta Zee tayi.


"Shekara sha tara din shine kike karama. Da da akewa yan shekara goma aure fa suce me."


"Haka ne, Sis ina tsoron aure ne, kuma dai bari kinji na fada miki. Nayiwa kai na miji kuma nasan shi zai fahimce ni ya kuma gatan tani."


Murmushi Zee tayi,
"Masha Allah wane wannan."


"Ya Aslam mana."
Asma'u ta bata amsa tana lumshe ido.


Dariya Zainab ttayi ta ce,
"Wane ma Ya Aslam."


"Ke Zee har kin manta shi. Dan gidan Yayar Mami nah fa. Ta Abujar nan."


"Oh nagane shi. Abinda har gida sun zo tare da Love dina."


Murmushi *Asma'u* tayi.
"Dan haka ki bashi hakuri. Nasan Nasir nada hankali da ilimi komai dai ya hada. Amman ki bashi hakuri."


"Ba komai zan san yadda zan sanar masa insha Allahu."
"Nagode."


"kar ki damu."
Wayar tace tayi kara,


Tana dubawa ta saki murmushi ta dauka.
"Assalamu Alaikum Baby "
aka dada daga can bangaren


"Wa'alaikum Salam."
Ta amsa masa murmushi dauke a fuskar ta.


"Kina lafiya dai ko?"
Ya tambaya.


"Lafiya kai fa?"
"Lafiya Alhamdulilah da fatan kinyi sallah kinci abinci."


"Yaya duk nayi biyu nake jira tayi mu shiga aji."
"Masha Allah abinda na kira naji kenan."


"Nagode da kulawar ka."
"Ba komai."


"To kai kaci abincin da sallah "
Na dai yi Sallah abinci kuma sai na gama aiki zan ci."


"Kai Yaya!"
ta fada a shagwabe
"Yi hakuri befi mutum uku ba kinji "


"Da gaske."
"Eh!"


"To dan Allah kana gamawa kaci."
"Insha Allahu!"


"Yauwah nagode."
"To sai ajima ko."


"Aha bye."
Ta katse wayar.


Zainab ce ta kalleta.
"Kece kuwa *Asma'u* "


"Me nayi?"
"Soyayya "


"Haba Aunty Zee ina wata soyayya anan. In ma soyayya ce ke kika koya min ai."


"Ni kuma?"
"Eh man yadda ko da yaushe kike yi a gabana."


Dariya tayi,
"Tashi mu tafi."


"Toh!"
Suka tafi hall din da zasuyi lectures.


Tinda suka shiga sai bayan hudu suka fito. Suna fitowa sallah sukayi su.


Lokacin har anzo daukar Zainab dan haka ta tafi ta bar *Asma'u* tana jiran azo daukar ta.


Ba tayi minti biyar da zama ba, aka zo daukar ta.


Tana mota Ya Aslam ya kira ta.
"Baby nah ya makaranta."
"Gani a hanyar komawa gida."


"Sannu kin gaji ko?"
"Wallahi, na gaji jikina sai ciwo yake min"


"Sannu kinji ai da ina kusa da nayi miki tausa ko."
Murmushi kawai tayi.


"Yaya nah kai fa ka tashi."
"Ina fa, aiki ma zan fita yanxu."


"To Allah bada nasara."
"Ameen! Sai anjima."


Ta kashe wayar. Idon ta ta lumshe, gaskiya tayi sa'a samun Yayan ta a matsayin me sonta, wanda tasan tin kafin ya fara son ta yake kula da ita da riritata bare yanzu kuma.


A rana sayi waya sau nawa banda text din safe na rana da na dare. Yayanta na son ta sosai da duk tafiyar da zaiyi tsarabar ta daban ce.


Haka nan Ga soyayyar Dadyn ta da itama take kara sa mata nutsuwa.


Tana shiga gida ta tadda Mami a kitchen dan haka kitchen ta shige ta fara taya ta aiki. Sai gab da magariba suka gama sannan ta mike ta hau sama.


Wanka tayi ta saka kaya mara sa nauyi. Turare ta feshe jikin ta sanna ta hau kan sallaya tayi sallah.


Tana idar wa ta dauko kur'ani ta fara bita sai da ta kai ixifi daya sanna taji kiran sallah isha'i mikewa tayi, tayi sannan ta fita zuwa falo.






pls don't forget to follow and vote @ msindabawa


Nagaishe ki ummu Ayda Allah bar mu tare Ameen


*INDABAWA*
[1/18, 13:56] Maryam S Indabawa🥰: *ASMA'U HUSNAH*




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


Facebook @Indabawa novel
Wattpad @Msindabawa
Insta @Maryam S Indabawa


*HAJOW*


� *HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS* �




*16-20*








DEDICATED TO U *MOMMY NAH*


NO ONE LIKE U IN MY LIFE REALLY LOVES YOU *MY HAPPINESS*






*Manzon Allah (SAW) ya ce, "Kada dayan ku yayi tafiya da takalmi guda daya.
Ko ya saka duka. ko yacire baki daya"








Kamar kullum sai bayan isha'i na sauka. Da fara'a ta na karasa wajen Dady na.


'Barka da dawowa Dady ya aikin?"
Murmushi yake ta zubawa.


"Yauwah *Husnah tah* aiki lafiya Alhamdulillah! Ya makarantar."
"Makaranta lafiya Dady."


"Masha Allah!"
"Dady tashi muje kaci abinci kaxo ka huta."


"Toh yar gidan Dady."
Suka mike.


Wajen Mami ta karasa,
"Mami taso."


Itama mikewa tayi, sai tayi wajen Ya Buhari,
"Babban yaya taso"


Baki ya tabe ya mike. Gefen Dady ta koma ta kamo hannun sa ta hade dana Momy, suka nufi gun cin abinci.


Sai da ta zubawa kowa sannan ta koma gefen Dady,
"Yau tare zamu ci."


Suka fara cin abincin su.


Suna gamawa tayi kitchen dasu ta wanke sannan ta dawo falon.


Tausa takewa Dady a kafafun sa, yana tambayar ta harkar makaranta.


Karfe tara tayi dakin ta bayan ta gama tsokanar yayan ta tayiwa Dady da Mami sai da safe.


Tana shiga wanka tayi tayo alwala sannan ta murje jikin ta da mai, me kamshi tasaka kayan bacci a jikin ta.


Gado ta hau tana me janyo wayarta da ta ajiye.
Ido ta lumshe lokacin da tayi tozali da hoton Ya Aslam akan wayar ta.


Fita tayi daga galleryn ta duba screem din wayar sakon sa ne akai.


Dubawa tayi.
"Love na dawo gida amman tunanin ki kawai nake. Ji nake dama anyi auren nan muna tare da na shigo nayi tozali dake."


Murmushi tayi,
"Yaya nah ina sonka."


Ta fada tana mai kiran number tasa. Bugu daya ya dauka.
"Hello Habibaty."


"Uhmm Honey, ya gajiyar aiki."
"Ruwan zafi ya tafiyar da ita. Kinga da munyi aure ke zaki gusar min da ita."


"Rai dai wani lokacin ni zan gusar da ita."
"Wayyo Allah! Da kuwa naji dadi. Allah nuna min wannan lokacin."


"Ameen!"
"Fadan me dame zakina min in munyi aure."


Ido ta rufe da hannayen ta, dan sai taji kunya.
"Yaya nah sai anyi aure ka gani."


" *Husnah* kenan baki san yadda nake son ki ba. Na miki alkawarin bazan taba rabuwa dake ba."


"Nima na maka alkawarin baxan taba juya maka baya ba duk abinda zakayi min."


" *Husnah* zan gatataki na nuna miki tsantsar soyayyar da nake miki. Baxan taba barin ki kiyi kuka ba."


"Nima insha Allahu zaka same ni mai kula dakai da kuma faran ta maka."


"In kuwa har hakan ta kasance nasan zaman mu zai yi dadi."
"Allah tabbatar mana da alheri."


"Ameen Baby nah. A tashi aje ayi alwala azo ayi addu'a ki kwanta."


A speaker ta mai da wayar, taje tayo alwala ta dawo tayi addu'a duk yana jin ta, ta gama Ta shafe jikin ta.


Kissar Annabi Musa ya ke bata, tin tana ji har bacci ya duke ta.


Sai da ya tabbatar tayi bacci sannan ya kara karanto mata addu'a, sannan ya mike yayo alwala yai sallah ya kwanta yana me karanto addu'ar ya tofe jikin sa da ita.






Kamar yadda ta saba karfe biyar da biyar da kwata ta tashi alwala tayo tazo tayi raka'atanil firji.


A lokacin Ya Aslam ya kirata.
"Baby nah kin tashi dai ko."
"Eh na tashi."


"Kinyi sallah ko."
"Nayi ai tinda ka kara fadan darajar ta ban kara fashin yin ta ba."


"Masha Allah. Sai anjima."
Ya kashe wayar


Sannan ta mike lokacin da ana kiran sallah tayi sallah. Karatun al kur'ani sannan ta dauko littafin makaranta tana dubawa.


Mami ce ta leko ta ganta ta dukufa akan littafin ta,


Murmushi tayi ta juya. Tana son *Asma'u* yarinyar akwai shiga rai da neman ilimi tare da ladabi da biyayya.


Sai karfe shida sannan ta fita.


Falon su a gyare sai kamshi yake da ke Mami da ta tashi take gyara wa. Dan bata yadda da masu aiki suna gyara mata cikin gida ba.


Kitchen ta nufa. Mami ta tadda har kasa ta durkusa ta gaida ta.


Doya taga ta sauke, karba tayi ta fara soyawa sannan tabar kadan tayiwa Dady yamball da ita.


Sai kunun gyada da ta dama masa. Ta kai komai sama.


Sannan ta dawo ta taya Mami gyara kitchen din. Sannan tayi sama.


Dakin ta, ta gyara ta share sanna ta wanke bandakin ta feshe shi da turare ko ina.


Wanka ta shiga tayi ta fito ta shafe jikin ta da mai sannan ta murje jikin ta da humra.


Katuwar doruwar ta. ta bude, Kasa ta duka ta dauko kayan cikin ta. Sanna ta mike ta dauko wata bakar riga me adon ja.


Sai jan mayafi da ta dauko. Babba dashi. Shiryawa tayi bayan ta saka kayan ta kama gashin ta tayi parking nasa.


Jar hula ta saka sannan ta dauko mayafin tayi rolling nashin. Ta dauko turaren ta, ta fesa.


Jakar ta ta dauko ta zuba duk abinda take bukata. Sannan ta dauko wani cover shoe takalmin ta ja tasaka.


Fita tayi ta nufi dakin Dady, yana hango ta ya saki fara'a.
"Dady ina kwana?"


"Lafiya lou *Husnah* kin tashi lafiya?"
"lafiya lou."


"Har kin shirya kenan."
"Eh Dady."


Mami ce ta fito daga dakin Dadyn ita ma taci adon ta tayi kyau.


"Matsa na hada masa abinci."
"Mami bari na hada masa."


Kunun da ta dama ta dauko masa ta zuba sannan ta juye masa madarar ruwa, ta mika masa.


Sai doyar da yam ball da ta zuba masa.


Tea ta hada ta fara sha. Ta dan tsakuri doyar taci.


"Wai *Husnah* baza kina cin abinci ba ko?"
"A'ah Dady wallahi dana fara cin nake jin ciki na ya cika."


"Kina son na fara miki dura ko."
"Ah yoh *Dadyn Asma'u* ai kaima gara ka gane bata son cin abinci."


"Kai Mami."
"Karya zan miki."


"A'ah!"
"Toh ya isa, ke *Husnah* kina cin abinci kinji ko."


"Naji Dady."
"Allah miki Albarka."


"Ameen!"
Hira suka dan taba sannan ta masa sallama ta mike.


Kudi ya kara bata kamar kullun sai taki amsa haka kuma dole zai sa ta amsa dan ko wani zai nemi taimako a gun ta.


Jakar ta, ta dauko, ta shige dakin Yayan ta. Baccin sa yake hankali kwance.


Bude shi tayi ta dinga daukar sa hoto. Sai da ta gama sannan ta tashe shi.


"Ooo *Asma'u* Allah kada ki bari na tashi."
"Haba Yaya ai kai ma kasan bazan iya tafiya ban gaida ka ba."


"Naji nagode dan Allah jeki."
"Please ka tashi kaga princess din taka mana."


" *Asma'u* "
ya kira ta da babbar murya.


"Na'am!"
"Tafi nagode!"


Bargon da ya rufa dashi ta yaye sannan ta fita a guje. Bayan ta yabi da gudu shima.


Dakin Mami ta fada tana.


"Mami kingan shiko."
Tayi bayan ta.


"A'ah fah *Asma'u* kin cika tsokana kin qi dai ki girma ko."
"Mami shikenan bazan je na gaida Yayana ba. Bayan tin muna yara ake cewa muna gaida na gaba damu."


"Oh sai akace in yana bacci ma a tashe shi a gaisar."
"To Mami dan me bazai tashi ya wuce aiki ba ko dan yasan a karkashin Dady yake aiki."


Dai dai lokacin da ya shigo dakin. Kara kamkame Mami tayi tana ihun ta taimake ta


"A'ah a'ah Buhari rabu da ita kayi hakuri kaji."
"Haba Mami kullum sai ta tada ni ina bacci."


"Yi hakuri kaji baza ta sake ba."


Lokacin wayar ta ta fara qugi. Da sauri ta dauka.


"Baby kindai fita ko!"
ya tambaya daga can site din.


"Yanzu zan fita."
Ta fada tana kallon Mami.


"8:30 fa kina kuma da lecture 9 me kika tsaya yi."
ya tambaya.


"Yi hakuri na tafi."
Ta fada tana diba a guje, tana cewa
"Mami na tafi. Yaya kayi hakuri sai na dawo."


"Tafi dai a hankali. Kar ki fadi."
Mami ta fada.


"Allah ya kara kullun sai ta tsaya tsokana taje ta makara."
Yayan ta Buhari ya fada.


"Ya Aslam na fito."
Asma'u ta fada bayan ta fita compound din gidan.


"To daina gudun kada ki fadi."
Ya fada cikin tausasa murya.


"Toh!"
to ta amsa.


"Tsokanar kika tsaya ko?"
ya tambaya dan yasan hali.


"Yaya kaima tsokanar zaka ce ina yi zuwa nayi fa mu gaisa."
Tai maganar cikin shagwaba wacce ta riga ta zame mata jiki kasancewar ta Autah.


"Kuma yana bacci kika tashe shi ko?"
Ya fada daga can barin.


"A'ah fa."
Ta fada masa tana karasawa wajeen motar gidan su,


"Ki daina dai."
"Toh!" ta amsa.


"Bari mayi magana anjima."
"To a dawo lafiya."


Ya ce,
"Ni tin dazu ina office. Ke zan cewa a dawo lafiya ayi karatu."


"Insha Allah!"
"Bye!"


Tana karasawa Baba driver ya tashi ya bude mata.
"Baba nagode."


Ya shiga gidan gaba yaja suka tafi.


Sai daga baya ta samu ta gaida shi. cikin sa'a tara saura minti biyar ta shiga makaranta.


Da sauri ta karasa hall din da suke daukar darasi.


Tana shiga har Zainab ta sama mata wajen zama..








Don't forget to vote @MSIndabawa


*Indabawa*
[1/18, 14:05] Maryam S Indabawa🥰: *ASMA'U HUSNAH*




BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*








🌐HAJOW📝🌐


👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾








*21-25*






DEDICATE TO *MY LOVELLY MOMMY*


UR LOVE IS SPECIAL. MAY ALLAH BLESS YOU
*AMEEN*




*Manzon Allah (SAW) Yace "Zagin musulmi fasikanci ne.
Yakar musulmi kafirci ne"*










Sai bayan sun fito Zainab ta samu damar yi mata korafi.
"Wallahi ke dai kin baci yanzu."


"Da me?"
"Makara mana. Gobe dai Sir Sabir ne."


Murmushi tayi!
"Ki kwantar da hankalin ki da wuri zan fito."


"Allah yasa."
"Ameen!"


*-*-*-*-*-*-*-*-*-*-*


Zaune yake cikin office din shi ba abinda yake sai tunanin ta duk inda ya juya hoton fuskarta kawai yake gani.


"Ya Salam! Allah ka dauran abinda zanyi dashi."


Ya fada yana jinginar da kan sa a jikin kujerar da yake zaune.


Yarinyar tayi min, irin ta nake son aura. Gaba daya ta gama tafiya dani.


Ido ya lumshe yana tuna maganar Mamahn sa.


"Sabir kana girma amman har yanzu kaki ka kawon matar aure ko, ga yan mata nan a family amman duk kaki ka kula su ko."


"Mamah ki kara min affuwa na kusa kawo matar da zan aura."


"Allah nuna min."
"Ameen!"


Ajiyar zuciya yaja.
"Insha Allahu na samu mata."


Ya fada yana bude firij din gefen sa ya dauko lemo.




Haka ya koma gida sukuku dashi duk ba wani karfi a tattarre dashi.


Yana shiga Mamahn sa tasan da abinda ke damun sa.


"Sabir lafiya dai ko?"
Murmushi ya kakalo.


"Lafiya lou Mamah."
"Ka tabbata."


"Eh!"
Ya fada yana daga mata kai.


"Taso kaci baccin ka kaji."
"Mamah sai anjima."


"Sai anjima"
ta tambaya dan tabbatar wa


"Eh!"
Ya amsa mata.


"Allah ya kyauta."
ta fada. Tana kallon sa.


"Abbu ya dawo ne?"
Ya tambaya.


Mamah ta ce,
"Yana dakin sa."


Sabir ya ce,
"Ohk bari naje na dan huta in na fito ma hadu."


Kallon sa ta tsaya yi, saboda tasan indai Abbu na nan ba abinda ke rabasu da gudu zaiyi wajen sa.


Kai ta jinjina Tana me masa Addu'a a cikin zuciyar ta.












Wata kyakyawar farar yarinya ce, doguwa ce, siririya amman sam bata da shape.


Zaune take a katon falon ta kayan marmari ne a cike a zube sai wata kawar ta dake gefen ta.


"Preety wai ya zancen Aslam kin shawo kansa dai ko."
gyara zama wacce aka kira da Pretty tayi. Ta ce,
"Ina fa, abi ya ci tura."


"To yanzu mene abin yi."
"Wajen Malamin nan nake son zuwa. Wallahi bazan iya rasa Aslam ba shi ya nacewa karamar yarinya kome tafini dashi oho. Amman wallahi sai na raba su."
preety ta fada.


kawar tata tace
"Preety ina bayan ki. Amman ina zakije wajen malamin?"
"Kinsan gobe zamu tafi

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads