Showing 69001 words to 72000 words out of 92878 words
Chapter 24 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt
duk da tana son sa son Sabir a ranta amman kuma ita tana son Aslam fa.
Ga shi lokacin biki sai karatowa yake yanzu sauran sati biyu.
Yau tin da ta tashi take jin faduwar gaba amman ta rasa ko ta macece.
A haka tai wanka ta shirya ta tafi aiki.
A wajen aikin ma ba wani aiki tayi ba sai kwanciyya.
Tana tashi kuwa taiwa Mami waya ta tafi ganin Dady.
Gidan Yaa Buhari ta tafi can ta zauna tana tai wa Aiman wasa.
Yaro ya fara girma kyakyawa dashi. Dan farin Baban sa ya dauko.
Yau tin safe Aslam yayo wa kano linkaya.
Da wajen karfe biyu ma yana cikin kano.
Gidan su Asma'u ya wuce kai tsaye. Yana zuwa Mami ta tarbe shi kamar yadda suka saba.
Zama sukai suna hira, yana tambayar Buhari.
Mami take fada masa haihuwa yaron da akayi ma.
Sosai ya taya shi murna dan Aslam akwai son yara.
Shiru yayi kafin ya dago ya ce,
"Mami! Husnah fa."
Murmuahi Mami tayi ta ce, ta tafi aiki daga can kuma tace zata gidan Buhari."
Kai ya gyada ya ce,
"Mami daman akan Husnah nazo."
Gyara zama Mami tayi ta ce,
"To ina ji."
Kasa yayi da kai ya ce,
"Mami wallahi ban san ya akai har na auri Pretty ba bayan duk duniya ba wacce na tsana sama da ita, wallahi Mami bansan me ya raba ni da Asma'u ba, sai kawai tsintar kai na nayi da rasa ta. Mami ki taimake ni ki bawa Husnah hakuri ta zo muyi aure."
Tinda ya fara magana Sabir da ya ke tsaye bakin kofa yake jin sa.
Juyawa yayi ya shiga motar sa yayi gidan Buhari.
Mami ganin hankalin sa ya tashi yasa ta ce,
"Kaga Aslam ka kwantar da hankalin ka, kasan komai mukadari ne, ni kai na zan so Asma'u ta aure ka. Amman in haka Allah ya tsara zan fi kowa murna, haka nan in akasin haka ne ma bazan yi bakin ciki ba tinda nasan kana tare da ita a matsayin dan uwa. Yanzu dai ka kwanar da hankalin ka kaji."
Kai ya gyada. Mami ta kawo masa abinci ya ci sannan ya hau sama
Dakin Asma'u ya fara shiga, kamshin ta da ya missing shi ya fara sheka yana lumshe idanu.
Kan gadon ta ya fada yana shinshinar sa
Ya jima a Kwance sanna ya mike yana kurawa wani hoton ta kallo.
Ba karamin kyau tayi ba, ita da wani jariri.
Ga dukkan alama yasan 'dan Buhari ne.
Murmushi yayi ya ce,
"Su Husnah da 'da."
Mikewa yayi ya fita ya sauka kasa. Mami ya sama ya ce,
"Mami A wanne gida Buhari yake?"
Mami ta ce,
"Can Rijiyar zaki ne!"
Kai ya gyada ya fita da yake yasan duk gidan jen su.
Can ya nufa kai tsaye da zumudin ganin Asma'u.
Asma'u da tinda tazo tana dakin ta da Dady dan har bacci sukai suka tashi sukai wanka.
Kwalliya tayi sosai wacce ta dade bata yi ba.
Haka ma tai wa Aiman kwalliya dan fita take son suyi.
Tana fita falo ta samu Sabir a zaune.
Dan murmushi tayi ta zauna daga nesa dashi.
Ta ce,
"Yaushe kazo?"
Ya ce,
"Maman Baby kenan tun dazu. Ina zaku kukai wannan kwalliya haka."
Murmushi tayi ta ce,
"Unguwa zamu ni da Dady nah."
Kallon ta yayi a ransa ya ce,
"Kar dai ace Aslam taiwa kwalliyar nan."
Mikewa tayi ta shiga dakin Zainab bata nan.
Kitchen ta shiga, ta ce,
"Mumyn Dady mu xamu tafi unguwa."
Juyawa Zainab tayi ta ce,
"Au daman zuwan da Sir yayi kenan."
Hararar ta tayi ta ce,
"Ba tare zamu fita ba."
Baki Zainab ta kama ta ce,
"Oh wai ke ki ta fita da yaro sai kace matar aure ai sai ya kashe miki kasuwa. Oh ko da yake an siyar daman."
Dariya Asma'u tayi ta ce,
"Kinyi kidan ki kinyi rawar ki."
"To a dawo lafiya. Kema nan da yan wattan ni dai zaki rike kanin Dady."
Zainab ta fada tana dariya
"Allah ya isa sis ke kin fiya abu wallahi."
Ta fita tana cewa.
"Ba za mu kawo miki tsara ba ba."
Inda ta bar shi anan ta same shi.
"Sir sai mun dawo!"
Ta fada tana yin gaba.
Mikewa yayi ya ce,
"Nima gida zan tafi."
Ta shiga mota ta saka Dady a abin zaman sa.
Sanan ta koma driving sit din ta. Ta zauna.
Taga ya leko, ya ce,
"Gobe zasu kawo lefe fa amarya ta."
Murmushi ta dan yi ta ce,
"To Allah ya kaimu."
"Ameen! Yau an kai na Nusaiba."
Ta ce,
"Masha Allah Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya."
"Ameen a dawo lafiya."
Ya mike yana daga mata hannu.
Hannu itama ta daga masa ta tada motar ta fice.
Motar sa shima ya tada ya bi bayan ta.
*MS Indabawa*
[1/18, 14:36] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*
By *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
Dedicated to *My Life. My momy*
76-80
*Manzon Allah(ﷺ)* Yana Cewa: *"Kuyi Aiki Domin Kowwa Ana Saukake shi ya Zuwa Abinda Aka Halicceshi Donshi ne"* (Bukhari da Muslim).*
Ranar alhamis da wuri ta gama komai ta shirya tayi dakin Dady.
Karfe takwas da arbain ta gama komai ta shiga dakin Yaya Buhari.
Gaisawa sukai kawai ta fita duk dan kar ta makara.
Shi kansa yau yasha mamakin ganin Asma'u bata tsaya jan magana ba.
Baba ma da ya gama shiryawa ita kawai yake jira tana shiga ya tada mota suka nufi makaranta.
Suna cikin tafiya motar ta tsaya. Fita Baba yayi Ya taba motar ya dawo amman shiru.
Sai da yafita sau uku ana hudun Asma'u ta ce,
"Baba me ya samu motar."
Baba ya ce,
"Asma'u kinsan ance karfen nasara bai da tabbas motar nan lafiya muku fito amman kinga ta tsaya taki tashi."
Fitowa tayi ta duba agogo tara saura minti biyar.
Waya Baba ya dauka ya kira mai gyara motocin gida ya fada masa inda yake
Kallon sa Asma'u tayi ta ce,
"Baba bari na hau napep dan na makara gashi zanyi submitting aasignment "
"To bari na tsayar miki da Napep din.'
"Aah Baba na gode."
Ta fada tana dan matsawa.
Mamaki take ganin karfe tara amman ji yan makaranta sai zirga zirga suke bama maza yan makarantun gwamnati.
Duk Napep din da zai zo a cike yake zuwa.
Wata Mota ce ta tsaya a gaban ta. Matsawa Asma'u tayi.
Kara binta akai ta kuma matsawa. Fitowa yayi daga cikin motar.
Wani hadaden saurayi ne ya fito. Fari ne, yana sanye da Ash kalar shadda kafar sa da bakin takalmi haka hannun sa daure da bakin agogo.
Kansa bbabu hula sai gashi dake kwace luf luf. Yana da idanu, haka nan hancin sa dogone har baki.
Karasawa yayi gun ta cikin nutsuwa ya ce,
"Assalamu Alaikum."
"Wa'aikulum salam!"
Ta fada tana dan matsawa daga wajen.
Kara bin ta yayi ya ce,
"En mata ina zaki?"
Ko kallon sa batai ba ta fara tsaida wani Napep.
Bai tsaya ba sakomakon cikar da yake.
"Naga kamar makaranta zaki kizo na rage miki hanya."
Dagowa tayi ta watsa masa wani irin kallon sannan ta matsa wajen wani napep da ta tsayar.
Kallon ta yayi har ta shige ciki sannan yayi murmushi ya shiga motar sa ya tafi.
Tana zuwa ta tadda har an yi submitting ga wani malamin yana musu lacturrle.
Kuka ta saka. tana zaune har lecturer ya fito.
Ta shiga ajin ta kifa kanta a benci tana cigaba da kuka.
Zainab ta matso gun ta tana bata hakuri sai ga. sir Sabir nan.
A haka ya shigo har ya gama lecture Asma'u bata dago ba.
Sai da zai fita ya dan matso gefen ta ya ce yana son ganin ta. Sannan ya tafi.
Asma'u duk ta tsure dan tasan akan bai ga assignment din ta ba.
"Zainab Allah bazani ba ni nagaji da kullum complain wallahi."
"Kiyi hakuri kije baki san me zai faru ba."
Da haka Zainab ta lallabata ta tafi office din nashi.
Da sallama ta shiga bayan tai knocking an bata izinin shiga.
Kai daga kallon ta ma zaka san ta sha kuka dan idon ta yayi ja dashi.
Sir Sabir ne zaune a wata kujera sanye da Wata brown shadda. Gefen sa gayen da ta gani dazu a hanya ne yaso ya rage mata hanya.
Waya taji Sir sabir yana yi yana cewa,
"Ki nifa ban san ta ba a ranar nima na taba ganin ta."
Shiru yayi sanna ya ce,
"Sai kinzo. In kuma na fita ne shikenan."
Ya kashe wayar.
Kallon sa ya maida kanta ya ce,
"Mene?"
Kallon sa ta tsaya yi ta ce,
"Uhmm uhmm!"
Sai ku a tayi shiru. Fauwaz dake, gefen sa ya dago dan ganin da wa yake.
Ido ya zaro ya ce
"Kai kece?"
Kallon sa tayi ta dauke kai ta ce,
"Sir kace nazo."
"Me yasa banga assignment dinki ba."
Shiru tayi.
Sai da ya kara nanata tambayar sannan ta dago ta kalle shi
Fauwaz ne ya dago ya ce,
"Friend ita ce wacce nake baka labarin na hadu da ita fa dazu. Motar suce ta lalace,"
Hararar sa Sabir yayi ya kalle ta ya ce,
"Ke me yasa kullum kina da matsala ne, in tayi baki makara ba yau abu kaza ya faru me yasa ne *Husnah* "
Fauwaz ya ce,
"Haba aboki kayi hakuri man."
Ya kalli Asma'u ya ce,
"Beauty mene matsalar ki yanzu?"
Banza tai masa tai kasa da kai idon ta na cikowa da kwalla dan ita da kai mata fada gara ka dake ta. Bata son fada a rayuwar ta yanzu zata fara kuka.
Kallon ta Sabir yayi ya ce,
"Mikon Assignment din naki kuma ki kara samun matsala na rashin submtting ko makara ki gani."
Da sauri ta dauko ta mika masa. Ta ce,
"Nagode!"
Tayi hanyar fita da sauri Fauwaz ya mike zai bita Sabir yai saurin riko hannun sa.
kafin ta bude kofa aka bude. Maryam ce ta shigo cikin shigar ta mai kyau ta saka doguwar rigar atamfa a mata dinkin mai dogon hannu.
Mayafin ta dan yafa kai ba dan kwalli sai jaka dake kafadar ta.
Tana ganin Asma'u ta saka dariya ta ce
"lah Asma'u!"
Sai kuma ta kama hannun ta. Ta kalli Sabir ta ce,
"Uncle kace, baka santa ba a ranar ka taba ganin ta."
Sai a lokacin Amsa'u ta tuno da statement din sa da ta shigo taji yana waya.
Kamo hannun ta tayi suka shigo office din ta ce,
"Ke nazo nema muyi sallama gobe zan koma garin mu gashi ban da number ki."
Murmushi Amsa'u tayi wanda Fauwaz ya kasa dauke ido daga kallon ta.
Hannun Maryam ta kama suka fita kallo Fauwaz da Sabir suka bisu da shi.
Wajen Zainab suka karasa ta zauna sannan sukai musayar number sai hira ta balle.
Dan har lecture tare suka shiga suka fito sukaje sallah sannan suka je cafteria suka ci abinci.
Sai karfe biyar sannan suka rabu shima dan an tashi.
Har bakin office din Sabir suka rakata suna daga mata hannu sannan suka juya.
Sabir da ya zata ma ta tafi ta shiga ta zauna akan kujera ta ce,
"Wash! Wallahi Uncle na gaji haka nima zan sha fama in na fara karatu."
Kallon ta yayi ya ce
"Daman baki tafi ba."
Kai ta daga masa ta kalli Fauwaz ta ce,
"Uncle Fauwaz ya kake?"
"Ni ba ruwana da ke. Kin tafi kin barni."
dariya tayi ta ce,
"Ayi hakuri wallahi Uncle Fauwaz. Asma'u ce ta burge ni na dawo amsar number ta kasan gobe zamu shige."
Kai ya daga ya ce,
"Dan bani number na gani."
"Tab ta ce, kar na bawa kowa wallahi."
Sai lokacin Sabir ya ce,
"In ba kwana zamuyi ba mu tashi mu tafi dare na yi biyar da rabi fa."
Mikewa yayi ya dauki jakar sa da basket ya mikawa Maryam Amsa tayi suka fito tana ta basu labarin Amsa'u in ka kalli Sabir zaka zaci ba jin ta yake ba amman gaba daya hankalin sa na ga ita yana jin abubuwan da take fada.
Da haka suka je gida haka tai ta bawa Mamah labarin Asma'u ranar dai har dare bata da magana sai Asma'u daga ta ce, tayi kaza sai ta ce tayi kaza.
Ta ce,
"Mamah baki ga ba yarinya karama ta na karanta medicine kuma a final year wallahi ta burge ni ga kokari da muka shiga lecture ita ke bada asma."
Mamah ta ce,
"Sai ki koyi da ita to."
"Ai insha Allahu Mamah kuma nayi 'kawa."
Shi dai yana zaune yana ji yana kara jin Asma'u na kara burge shi.
Asma'u ma da taje gida sai da ta bawa Mami labarin yarinyar.
Mami ta ce,
"Daman haka rayuwa take wani na son ka wani kuma kin ka yake yanzu dai ita kince daga haduwa Allah ya sa mata son ki. To Allah ya bar mu ga masoyan mu."
"Ameen!"
Ta mike ta hau sama.
Yaya Aslam ne ya kira ta bayan sun gaisa yake tambayar ta makaranta ita ma take tambayar sa wajen aiki.
Soyayyar Asma'u da Aslam abin sha'awa ce da burge wa dan ba karamin son juna su suke ba kowa da son dan uwan sa son da basa son su taba rabuwa da junan su.
Kowa na kula da tarairayar juna. Ga shi soyayyar su mai tsabta da kyau suke.
*Haka rayuwa yake wani daya ganka yake jin son ka a zuciyar sa. Son Allah kenan wanda wani dabi'un ka su suka burge shi. Wani kuma halayar ka abubuwa da yawa dai. Allah ka bar mu da masoyan mu,*
*Ameen!*
Mutane na tambayata wai *Sabir* Mijina ne ko saurayi nane to daga *Sabir* har *Aslam* da *Fauwaz* all are my lovelly children. Really love then.
*Husnah* kuma ina son sunan ne.
*Masoya na nagode nagode Allah bar soyayya.*
*Muje zuwa ga wani ya dadu a masoyan Asma'u shin ya kenan*
*Ina mai bada hakuri na jina shiru da kukai jiya da night da na morning da ban ba. Nagode*
*INDABAWA*
[1/18, 14:36] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
*HAJOW*
*Hakuri da juriya Online writer's*
Dedicated to *My lovelly Mum*
*81-85*
Yau tin safe Zainab ke bugawa Asma'u kofa amman ko mostin ta bata ji ba.
Abinda ya daga mata hankali kenan. Ta dau waya zata kira Buhari kenan sai taji shigowar sa.
Da sauri ta karasa wajen sa ta na ce masa
"Kaga Asma'u can kwana hudu taki bude daki yanzu na buga ma ko motsin ta bana ji."
Da sauri yayi cikin gidan kofar yake duka amman sam ko motsi.
Da gudu yayi dakin sa ya bude wata durowa ya dauko dayan key din
Fita yayi da sauri yana budewa yaga ta kwance akan sallaya tana fitar da numfashi a hankali.
Dago ta yayi yaga jkin ta duk a sake yake.
Da gudu ya dauke ta ya nufi mota da ita.
Asibiti yayi da ita da gudun gaske. kafin ya karasa ya kira Sabir ya fada masa gashi nan tare da Asma'u.
Yana karasa wa aka kawo gado aka dauke ta kai aka yi wani daki da ita.
Ruwa Sabir ya fara saka mata sannan ya fara duba mai ke damun ta.
Ya gano har da rashin cin abinci sannan kuma jinin ta ya hau.
Ya tabbata zuwan Aslam ne ya sata a wannan hali.
Shi kan sa yasan Asma'u na mugun son Aslam.
Dan ta sha fada masa. Sosai ya tausayawa mata dan ba karamin jin jiki take ba.
Aslam dake can kwance shima ya ce da Mami yana son ya koma gida.
Mami cewa tayi ya bari jikin sa ya kara kwari dan ko tafi sai da kyar yake taka kafar tashi.
Rigima ya sawa Mami dole shi sai ya tafi.
Da kyar ya bari ya kara kwana biyu, dan washe gari Buhari yana tafiya massalaci ya mike ya tafi gidan sa.
Motar sa ya dauka ya dau hanyar Abuja, duk da jikin sa ba kwari.
Tafiya yake yana tunanin halin da yake ciki.
Wai shine zai rasa Asma'u. Hawaye ne ke zuba a idon sa.
Dai dai zai shiga Abuja motar ya kwace daga hannun sa yayi cikin jeji.
Asma'u kuwa tana kwance. jiki dai yaki yayiyu.
Sam jiki ba samun sauki duk maganin da take sha.
A gaskiya tasan tana kaunar Aslam kauna kuwa ba ta taba dainawa.
Tana kwancen nan ba wanda take son ta gani inba Aslam ba.
Kuka kam ita kadai tai tayi. Ta tabbata a yanzu tai rashin Aslam ba a da ba.
Bikin ta da ya rage kwana biyar.
Ba dan taji sauki ba aka bata sallama sai dan bikin ta da ya karato.
Har gida aka kira akai mata maj lallai da gyaran kai.
Rama kuwa ta kara ramewa tayi fari da ita.
Ba abinda take iya ci. Da ta zauna ita kadai sai kuka.
Zainab duk tai rabon katin bikin nata.
Ita dai komai da akeyi nata ido ne.
A bangaren Aslam kuwa Buhari na dawowa bai ga Aslam ba ya tafi gida.
Motar sa yaga ya dauka nan da nan ya kira Momy ya sanar da ita Aslam ya taho.
Haka ma ya kira ya sanar da Mami. Addu'a Mami tai masa Allah yakai sa lafiya.
Momy kuwa tun karfe biyu take zuba idon ganin Aslam amman bata ganshi ba.
Hankalin ta ne ya tashi. Can kuma sai ga sshi an kira ta da wayar sa wai yana asibiti.
Asibitin taje a lokacin aka fito dashi daga emergency aka tafi dashi inda za'a bashi daki.
Gun su tayi aka basu daki sannan likita ya kira ta.
Bayanin abinda ya same shi yai mata cewar ya bugu ne sosai a bayan sa. Sai yan raunika da ya dan daddauje.
Takardar magunguna ya bata ta amsa ta tafi ta bayar aka siyo mata.
Lokacin da Momy ta buga waya tana fadawa Buhari abinda ya faru Suna tare da Sabir.
Sosai Sabir ya tausaya masa. Haka su ka rabu jikin Sabir a sanyaye.
Tunani kuwa har ya rasa wane iri zai yi.
A ransa kuwa cewa yake yanzu yana ji yana gani zai raba farin cikin mutun biyu.
Ya tabbata duk son juna su ke jefa su a halin da suke ciki.
In har ya auri Asma'u yasan ya raba ta da farin cikin ta kuma Aslam ma bai da sauran farin ciki.
Sai yanzu yake tunani anya da Aslam yana cikin haiyacin sa ya juyawa Asma'u baya
Gaskiya da kamar wuya. Dan ya gano irin son da yake mata zai iya rasa rayuwar sa.
Haka ya koma gida duk baida sukuni.
A bangaren Aslam ma yana farkawa ya farai wa Momy kukan wai dan Allah ta taimaka a bashi Asma'u.
Momy kam Mamaki ta dinga yi saboda sai da ta fada masa kar ya soma sawa ransa abinda ya riga da yai masa nisa.
Da bata bashi amsa ba haka ya dinga kuka sai kace karamin yaro.
Ganin numfashin sa na neman daukewa yasa ta ce, yayi hakuri za tai san yadda zatai.
Duk da haka bai samu sukuni ba. shi dai ba wacce yake son gani sai Asma'u.
Momy kam bata fadawa Mami abinda ya faru da Aslam ba.
Kuma sai da ta hori Buhari da shima kada ya sanar da ita.
Ita tunanin ta ma rashin zuwan ta bikin.
Sai Allah yasa kuma ana jibi kamu aka sallamo Aslam daga asibiti.
A gida ta barshi da Dady kan cewa jibi zata dawo.
Haka Momy ta tafi tana tausayawa dan ta.
Sai ta tuna lokacin da take cewa sai ya auri Asma'u amman yaki yac"e sai Preety zai aura amman shine har da suma gashi kuma yanzu ya dawo da son ta.
Bangaren Su Mommah pretty kuwa ba karamin tashin hankali Ta shiga ba.
Ganin Pretty har wata