Showing 81001 words to 84000 words out of 92878 words
Chapter 28 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt
zaunar akan kujera.
Hawayen fuskar ta ta goge mata ta ce,
"Hakika kin raba son da ya dade da kafuwa, son da ba'a taba zaton rabuwar sa ba. Asma'u tayi jinya sosai wace banyi zaton zata warke ba duk a dalilin rashin Aslam. Amman ba komai haka Allah ya kaddara kuma bawa baya wuce kaddarar sa. Allah yayi sai sun rabu kuma sun dawo sun yi auren dai. Zan taya ki rokar Asma'u duk da nasan Asma'u na da saukin kai. Insha Allahu zata yafe miki."
Rumgume ta Pretty tayi tana godiya. Da zata tafi har kudi Mami ta bata.
Hakan zaman Asma'u da Aslam yaci gaba da kasancewa, ko kad'an bata sakar mishi fuska idan yazo inda take, amma tana masa duk kan abinda zai sa ta.
Haka nan girki duk wadan da tasan yana so tana masa, amma da ta jishi zata shige d'akinta,
Aslam ma gane hakan yasa wani lokacin baya dawowa gida ko in ya dawo yana bangaren sa, sai dai ya makala nauwara daukar bayani a babban falo kitchen da dakin ta. Wannan yasa ya daina neman takura mata.
Dan kullum yana ganin yadda take gudanar da rayuwar ta in baya gidan.
Ba karamin burge shi take ba. Bama yaga ta ci ado tana zaune kawai.
Ko kuma ta saka kanannun kaya, tai ta juyi ita kadai.
Wani lokacin ta kira gida da su Zaianb tai ta waya, haka zata kira Momy ma.
Wani lokacin kuma ya ganta tana kuka yakan rasa me yasata kuka.
Rayuwa dai kala kala kala take gudanar wa. Abinda yafi burge shi da ita, shine yawan ibadar ta.
Yana lura da yadda take dukufa wajen addu'a da nafufuli.
Wannan na dada masa son ta da kaunar ta.
Kallon rayuwar ta da yake yi, yasa ya daina takura mata da son damun ta. Sai dai yana 'ko'kori wurin kyautata mata sosai da son nuna mata shi masoyinta ne na ha'ki'ka.
Yau watanta biyu kenan babu abinda ya canja tsakaninta da Aslam.
Tana zaune falon d'akinta ya shigo, bata san ma ya shigo ba tana can duniyar tunani, a fili ta furta,
"Allah sarki Dady na ka tafi ka barni cikin wannan duniyar mara dadi. Yanzu banda waji farin ciki."
Aslam ya zauna daga nesa da ita ya ce,
"Ai ke kika ki barin farin cikin ya sameki."
Kamar bazatace komai ba, sai kuma tace,
"Waya fada maka, ai farin ciki na nasan ya tafi kenan bazai taba dawo wa ba dan yanzu na rabu da duk masoya na. Kaga kuwa ina farin ciki."
Yace
"Ni menene naki. Nima masoyin kine na gaskiya wanda ke da burin ganin farin cikin ki a ko da yaushe."
Shiru ta mishi ba tace komi ba, Mikewa yayi yayo wajen ta. mikewa tayi da sauri zata fita a dakin.
Da sauri ya kamo hannun ta ya zaunar. ya ce,
"Haba Husnah ki tunanin zaman mu zaiyi a haka kuwa? Ina mijinki amma bazamu zauna wuri d'aya ba?"
Kasa tayi da kanta tana wasa da zoben hanun ta. Wanda shine ya bata.
Hannun ta ya kama yana murzawa a hankali. Take tsigar jikin ta ta fara mikewa.
Magana ya ke mata cikin wata irin murya mai burkita mai sauraro.
"Husnah ki yadda dani wallahi son da nake miki ba abinda ya ragu a cikin sa."
Ya fada yana shinsinar wuyan ta. Kamshin ta mai dadi da kwanatr masa da hankali ya shaka take hankalin sa ya fara tashi.
Bakin ta yai saurin cafka, yana tsotsa kamar wanda ya samu alawa.
Hannun sa ne ya gangara kan dukiyar fulanin ta. Wasa ya dinga yi da ita.
Jin yana son wuce guna da iri yasa ta sakar masa wani irin kuka.
"Ni dai Yaa Aslam ka kyale ni, wallahi nasan ba sona kake ba. Ka rabu da rayuwa ta dan Allah. Ka koma gun wacce kake so har ka aura. Ni nasan daman Sir ya gama cutata ne da ya bar maka ni. Baza ka taba ganin daraja ta ba."
Ta fada yana kuka mai tsuma zuciya.
Kallon mamaki ya tsaya yi mata, kasa jurar jin kukanta yayi mai tsuma zuciya, duk ya rikice, ya rasa ya zaiyi, ya fara magana cikin sanyin murya.
"waya fad'a miki ina da wadda nakeso bayanke? Wlhy ke kad'ai nakeso Asma'u, ban ta'bason wata d'iya mace a rayuwa ta ba kamar yanda nake sonki, ke ma kin sani ban taba soyayya da wata bayan ke ba. ki bani dama in bayyana miki irin son da nake miki."
Da 'karfi tace
"baka so na Yaa Aslam, baka so na. Ka koma wajen matar ka da kake so, ni ka kyale ni, nasan dan kaji zan aure ne kazo to kaji dadi da ka raba ni da mai so na."
Duk ya rikirkice, ya ce,
'Wallahi banda burin 'bata miki rai 'kanwata, don Allah ki fahimceni, wallahi ina sonki, naayi miki alkawarin faranta miki har iyakar rayuwatah."
Hannu biyu ta sanya ta rufe kunnenta tace
"Bana sonji Yaa Aslam don Allah ka 'kyale zuciyatah ta huta hakanan, duk abinda zakamin don kasan ina sonka ne...."
Kasa karasa maganar tayi ta kifa kanta akan kujera taci gaba da shesshe'kar kuka.
Sosai yake jin kukanta a jikinshi, ya rasa yanda zai rarrasheta, hannu ya saka ya d'agota a jikinshi, da sauri ta fara 'ko'korin zamewa, anma tsam ya rumgumeta a 'kirjinshi sosai, har saida tayi 'kara saboda ba ri'kon wasa ya mata ba,.
Kuka kawai take dan bata da wani 'karfin da zata kwaci kanta.
Aslam kuwa idonshi lumshe, ko lallashinta ya kasayi, duk jikinta ya saki ta fara rage kukan, sun dad'e a haka, kafin ya sassauta mata ri'kon ta zame ta kwanta a hankali ta rufe idonta, shima mi'kewa yayi ya fita ya barta.
Sai da ya fita daga d'akin kuma ta fashe da kukan takaici, Aslam yaa riga ya gama da ita tunda ya gane mahaukacin son da take mishi, kuka take sosai a ranta tana addu'ar Allah ya rage mata son sa
Ina son ganin comment
Follow nd vote @ Msindabawa
*MS Indabawa*
[1/18, 14:40] Maryam S Indabawa🥰: LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
?? *HAJOW* ??
Dedicated to *My lovelly Mum*
*111-115*
Da dare da wuri ta mishi girki kafin ya dawo, ta shige d'aki tana gama sallolinta tayi shirin kwanciya, doguwar riga ta saka iyakar gwiwa pink, mai santsi dabin jiki, tayi kyau sosai, mukulli ta saka ta rufe d'akinta ta haye gado tayi addu'a ta kwanta.
Aslam kuwa tinda ya fita da yamma yaje gidan Momy. Tambayar da Asma'u tayi ya amsa da tana lafiya.
Daga nan Asibiti ya biya, sai da akai magariba ya taho gida.
Yana driving ne amma zuciyar sa na can tunanin halin da Asma'u take ciki.
Bai son damuwar ta bai son bacin ranta. Dole ya san yadda zai dawo mata da farin cikin ta.
Sanda ya isa gidan kamar yanda ya zata, tayi barci ko motsinta bai jiyo ba, d'akinshi ya shiga ya watsa ruwa yayi shirin kwanciya sannan ya fito ya zauna yaci abincin data girka mishi, hankalinshi duk naa wurinta harya gama.
A hankali ya murd'a Kofar d'akinta, jinta yayi a rufe, kamar yadda ya zata. komawa dakinshi yayi ya dauko makullanshi yazo ya bude a hankali ya tura kofar ya shiga.
K'arasawa yayi inda take, kasa d'auke idonshi yayi a kanta, a fili yake furta,
"Alhmdlh, Allah nagode maka da ka mallaka min Asma'u. Ya Allah ka nunamin ranar da Asma'u zata gane irin son da nake mata," tsugunawa yayi saitin fuskarta yana tunanin yanzu da suna zaman lafiya ne zai kwanta da ita ne a kirjinshi yanajin lallausar fatar ta, shi kadai yasan yanayin da yakeji idan yana tare da Asma'u. Abinda ya dade yana fatan ya faru kenan.
Hannunshi yakai ya shafi fuskarta, ya d'aura hannunshi saman lebanta, bakin sa ya kai kan nata ya dan sumbace ta.
Mikewa yayi ya rufe kofar ya koma dakin sa.
Alwala ya kuma yi. Dan Kusan kwanan zaune yayi yana fad'ama Allah damuwarshi.
Washe da wuri ta gama masa duk abinda zai bukata sannan ta koma daki.
Sai da ta tabbata ya fita sannan ta fito ta gyara gidan
Daki ta koma tai wanka tai ado sosai a jikin ta da fuskar ta.
Bata san dalili ba yau dai ta tashi da farin ciki da son yin kwalliya.
Ta zauna ta karya. Kitchen ta shiga ta fara hada hadar abincin rana.
Fried rice tayi wacce ta wadata da hanta, tayi farfesun naman kaji, tayi cislow.
Cake ta kwaba tai baking sannan ta yi meat pie.
A daining ta jere su tayiwa wajen ado mai kyau.
Kitchen ta koma ta hada lemon kwakwa da madara ta saka dabinoi ta sa a firij.
Wanka ta kara tai Kwalliya sosai kamar amarya. ta saka wani papper less mai kyau da tsada wanda duk jikin sa stones ne da suka kara masa kyau sai daukar ido yake..
Red and black kala. Sosai tai kwalliya ta feshe jikin ta da turare mai kamshi sosai.
Dan kunne da sarka ta saka jajjaye, Babban falo ta koma ta zauna tana kallo.
Wajen karfe uku ta jiyo sallamar sa, amsawa tayi ba tare da ta dago ta kalle shi ba.
Shi kuwa tin da ya shigo ya zuba mata ido, dan yaga tai masa kyau.
Karasawa inda take ya zauna a gefen ta. Dagowa tayi ta zura masa manya manyan idon ta masu dimauta shi, kallon sa ta tsaya yi, sosai yayi kyau.
Yana sanye cikin Sky blue din shadda yai kyau da shi.
Fatar sa ta dada yin fresh, ya dada haske kyaun sa ya kara fitowa jikin sa ya murje. Ya dawo cikaken balaraben sa
Iska ya hura mata, wannan yasa tai saurin dawo wa cikin hayyacin ta.
Kai ya daga mata alamar 'Menene?'
Kai ta dauke daga kallon sa. Hannun ta ya kamo wanda tai masa ado da jan lalle.
Saitin bakin sa yayi da hannun ya sumbata. Zai yi magana kenan yaji ana knocking.
"Waye?"
Ya tambaya.
Mai gadi ne ya ce,
"Nine! Bakuwa kayi."
"Cene ta shigo."
Ya fada yana kallon Asma'u.
Mikewa yayi ya ce, bari na shiga na watsa ruwa.
Yana shiga tana shigowa ba kowa bace face Pretty.
Asma'u da bata san ta ba ta amsa mata sallamar da tayi tana mikewa.
Wajen zama ta nuna mata sannan itama ta zauna.
Gaisawa sukai, Pretty ta ce,
"Baki sanni ba. Ko Aslam yana nan?"
Kai Asma'u ta daga ta ce,
"Eh amman yanzu ya shiga wanka."
Ta mike ta kawo mata lemo da snack. Lemon kadai ta dan sha ta zauna jiran sa.
Sai kallon Asma'u take a ranta ta ce,
"Ashe haka Asma'un take ahh lallai doke Aslam yaso ta. Duk da yarinya ce amman tana da sura mai kyau. Allah sarki na cutar dake.'
Duk wannan maganar a zuciya take yin ta.
Sai da tai minti ashirin Asma'u taga Aslam bai shigo ba ta mike ta shiga ciki.
Yana gaban mudubi Daure da towel a kugun sa, yana ta kalkale jikin sa, Asma'u ta shiga.
Ganin sa a haka yasa tai saurin juya baya.
Kallon ta yayi yai murmushi, magana ta fara yi cikin rawar murya,
"Kayi bakuwa ana jiran ka."
Ta fada, tafiya ta fara yai saurin kamo hannun ta ya juyo da ita.
Kin juyowa tayi, shi ya juyo da ita da hannun sa.
Ido tai saurin runtsewa. Murmushi yayyi ya jata kan gado.
Zaunar da ita yayi ya saka kayansa. Sai da ya gama ya ce,
"To matsoraciyya na gama bude idon."
A hankali ta fara bude idon ganin ya saka kayan yasa ta bude su.
Mikewa tayi ta ce,
"Yaya tana jiran ka fa."
"Na sani."
Hanya tayi zata fita ya ce,
"Zo ki gyara ni man."
Ya fada yana mika mata turare.
Amsa tayi ta fefesa masa. Ta ajiye. tafiya ta fara ya ce,
"Oh!"
Juyowa tayi, ya ce,
"Comb my hair man!"
Amsar comb din tayi ta taje masa kai. Tana direwa tayi waje.
Bayan ta yabi, suka fita. Hannun ta ya kama, suka jera har zuwa falo.
Da yake Pretty ta juya ma hanyar da suke fitowa baya bai gane ita bace
Zagayawa yayi ya zauna ba tare da ya kalli bakuwar ta shi ba.
Asma'u kuma tayi hanyar sashen sa. Saboda taga yai bakuwa.
Dagowa yayi ya ce,
"Sann....."
Bai karasa fadin abinda zai fada ba yai saurin mikewa.
"Me kika zo min a gida?"
Ya fada cikin tsawa. Wanda ya janyo hankalin Asma'u.
Juyowa tayi ta tsaya kallon sa. Lokaci daya ya canja.
Fuskar sa tai jajir, da Hannu ya nuna mata kofa alamar tazo ta fice.
Zubewa tayi a kasa tana rokar sa ya tsaya ya saurare ta amman ya kafe akan sai ta fita.
Asma'u ce ta koma dakin ta kama hannun sa ta ce,
"Haba Yaa Aslam ka tsaya man."
Hannun sa ya kwace ya ce,
"Bazan tsaya naji ba. ta fice min da gani."
Kallon sa Asma'u tayi taga ransa a bace yake sosai.
Hannun Pretty ta kama zaunar da ita.
Wajen Aslam ta karasa shima ta zaunar da shi.
Kansa ta shafa masa har ya samu ya sauke ajiyar zuciya.
Kallon sa tayi, ta ce,
"Kiyi hakuri duk da bansan me ya faru a tsakanin ku ba amman ka saurare ta"
Ta fada tana mikewa. Hannun ta ya kamo, ya zaunar.
Kallon sa tayi ya gyada mata kai alamar ta zauna.
Zaman tayi, ya ce,
"Na baki minti biyu ki fadi abinda ya kawo ki, ki bar min gida na."
"Hakuri na zo na baka!"
Ta fada cikim sanyin murya.
"Indai hakuri ne ki tashi ki tafi bana bukata kara ganin kki a rayuwa ta. Rayuwar da nai dake a baya ma ban san nayi ba."
"Nasan da haka Aslam amman ka yafe min, nazo na bawa Asma'u hakuri ne."
Kallon ta Asma'u tayi cikin rashin sani ta ce
"Ni kuma? Ni da ban sanki ba."
"Eh baki san ni ba, amman ni nasan dan har na cutar dake."
Kwalar idon ta ta goge ta ce
"Dan Allah ki yafe min."
Kallon Aslam, Asma'u tayi.
Shima kallon ta yayi ya kama hannun ta. Kallon Pretty yayi fuskar sa a hade ya ce,
"Malama kiyi mana bayani da zamu gane, da me kika cutar min da kanwata kuma matata."
"Aslam tinda na fara son ka kake fada min kana da mata Asma'u ni kuma a duniya na tsani Asma'un nan ganin irin son da kake mata. Duk inda naje ayiwa Asma'u abu sai ace bazai kamata ba dan ba a zaune take ba. Ina shiga damuwa na son ka ga shi kai baka san ma ina yi ba. Wannan yasa naje har nijar na samu bokan da yai min aiki har ka auren ka bar Asma'u."
Hannun sa Asma'u ta saki, tana mai zaro ido.
Hannun ta ya kara kamawa, Pretty ta ce,
"Na maka asiri ka manta da ita da komai nata, sai da naje kano kwanakin baya ake fadan irin halin da Asma'u ta shiga a sanadin rashi ka. Nayi dana sani nayi nadamar raba ku. Dan Allah ku yafe min. Dan naga darasi ga masu bin bokayr yanzu wai ni ke dauke da cutar HIV"
Ta fada tana kuka. Asma'u ma kukan take dan ita da wane ido ma zata kalli Yaa Aslam.
Aslam ne ya jata jikin sa yana lallashin ta.
Amman kuka take kamar me. Ganin ya kasa lallashin ta ya sanya ya kalli pretty ya ce,
"To kinji dadi kinzo kin ta dan hankalin mata. Tashi ki bamu waje."
"Kayi hakuri banyi haka da zumar bata mata ba. Nayi ne dan na wanke ka. Dan nasan ko yaya ne zata rike ka da abinda kai mata."
"Bana son jin komai tashi ki fita." Ya fada yana nuna mata kofa.
Hannun sa Asma'u ta saukar ta girgiza masa kai.
Kallon Pretty tayi ta ce,
"Ba komai na yafe miki haka Allah ya kaddara wa rayuwar mu sai dai kece sila amman Allah ya riga ya tsara. Na yafe miki. Ki nemi yafiyar ubangiji ki."
Sosai Pretty tai mamaki haka ma Aslam duk da yasan halin Asma'u ita komai a gun ta mai sauki ne inda zaka nemi yafiyar ta in ka bata mata.
Jikinsa ya jata yana rumgume ta sam, Da kyar Pretty, ta ce,
"Nagode Asma'u nagode."
Aslam ta kalla, ta ce,
"Kai ma ka yafe min."
Kai kadai ya gyada mata. Mikewa tayi jiki a sanyaye, ta fita.
Aslam kuwa tinda ta fita ya kara matse Asma'un sa a jikin sa yyana jin wani tausayin ta.
Daman yasan dole rashin sa ya sa ta a wani hali. Shima ya shiga halin mawuyaci Allah ne dai yayi da sauran sa.
"Baby nah!"
Ya kira sunan ta
Kasa amsawa tayi sai, 'Uhmm' da ta fada.
Dankwalin kan ta ya zame, yana shafa gashin kanta.
Magana ya fara a hankali ya ce,
"Baby na yanzu kin yadda ban rabu dake dan son rai na ba. Dan Allah kiyafe min. Wallahi ni mai son ki ne, ina kaunar ki Husnah"
Magana Asma'u ta fara a hankali, ta ce,
"ka yafemin don Allah ka yafe mu, muyi rayuwarmu cikin farin ciki, wayyo naa shiga uku na cutar da masoyinah, a rashin sani, duk bacin ran bari na da kayi ne, ka koyamin rayuwa dakai, lokaci daya ka guje ni, a lokacin nayi zaton mutuwa zanyi idan har baka tare dani, nasha wahala Yaa Aslam don Allah ka yafe mun ka gafararka mijina."
Sambatu kawai take ita kadai, tana kuka, kwantar da kanta ya karayi saman kirjin sa, tana shessheƙar kuka, ji tayi yaa kara matseta a kirjinshi, yaa daura hannu saman kanta.
"Baki min komai ba Asma'u duk a rashin sani ne. Na yafe miki Asma'u bazan taba kin yafe miki ba. Ke da abinda kika min da wanda zaki min a gaba duk na yafe miki Asma'u. Ina kaunar ki Asma'u nasan bazan taba iya hada son ki da wata ba. Nai miki alkawarin daga ke ba kari ni naki ne ke kadai. Kamar yadda kike tawa ni kadai. Ina kaunar ki Husnah"
Kuka kawai Asma'u take. Dago da fuskar ta yayi yana lashe hawayen fuskar da harshen sa.
Sai da ya tabbatar da ta daina kukan sannan ya dago ta sukai daining a cinyar sa ya daura ta ya dinga bata abinci a baki.
Sai da ta koshi sannan, ya fara ci yana ci yana santi.
Suna gamawa suka koma falo. Rungume juna suka karayi, cikin wani irin yanayi na so da kaunar juna.
**** ****
Drop ur comment.
*MS Indabawa*
[1/18, 14:41] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*ASMA'U HUSNAH*
PART *2*
BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*
*HAJOW*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
DEDICATED TO *MY LOVELLY MUM*
*116-120*
**************
Da dare nan Asma'u aka kalkale jiki aka sha gyara akai wanka cikin ruwan turare masu dadi da rikita duk wanda ya shaka.
Dan ko da Aslam ya ganta kasa gigicewa yayi. saida sukayi sallah raka'a biyu na godiya ga ubangiji, sun dade Aslam na kwararo musu Addu'o'i, na zaman lafiya da zuri'a dayyiba, sannan suka shafa ya tashi ya barta har lokacin tana addu'ah.
Sai data gama ne yace
"wannan irin dadewa haka? Me aka rokar mana ne?"
Murmushi tayi ta ce,
"Ina roka Allah, ya kare mu da sharin