Showing 66001 words to 69000 words out of 92878 words
Chapter 23 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt
a falo tare sa Mami da Yaa Buhari.
Bayan sun gama tsara komai ne, Momy ta kalli Buhari ta ce,
"Buhari kun yi maganar Yayan ka da Mami kuwa."
Dagowa yayi ya dan jima kafin ta ce,
"Wallahi Momy bamuyi ba. Kuma abin na raina kullum. Bama Asma'u da nake son sanar wa."
Kai Momy ta girgiza ta ce,
"Kasan sai a shekaran jiya na fada yadda da ba haka matar Aslam ta bar shi ba. Kaga yadda take masa kuwa ta maida shi bawa fa, ba abinda yyake iya yi sai da izinin sa. Aslam duk ya rame."
Tayi shiru ta ce,
"Jiya da na aika a kira min shi cewa tayi bazai zo ba, sai da ta shiga ciki yake bawa dan aiken hakuri kan ya bani hakuri tinda ta ce, bazai zo ba. Ni da ganin Aslam fa sai nai wata. Kudi kuwa account dinsa na hannun ta. Dan Allah Buhari yazamuyi Na fison muyi abu wanda baza mu.kaucewa Allah ba. Dan ni bana son bin malaman nan su fara juyawa mutun tunani da canfe canfen su."
Kai Mami ta gyada ta ce,
"Innaillilahi wa inna illahir rajiun. Yanzu yadda ta maida Aslam din kenan. To Allah kai mana magani."
"Ameen!"
Momy da Buhari suka amsa da.
Buhari na komawa gida ya samu Asma'u ya ce,
"Asma'u ina son magana da ke!"
Ganin da yadda yai mata maganar yasa ta san magana ce mai mahimmanci.
Kallon sa tayi ta ce,
"To ina ji."
Tana komawa gefen sa. Kallon ta yayi, ya ce,
"Ina son ki sa a ranki duk abinda ya faru da bawa mukaddari ne Allah ya riga da ya tsara, sannan ina fatan duk abinda yya same ki zaki amsa hannu bibiyu"
Kai ta gyada ta ce,
"Insha Allahu."
Ya ce,
"Magana zan miki guda biyu kuma kowa ce ina son ki amshi abinda zan fada miki."
Sai da ta dago ta kalle shi sannan ta ce,
"Insha Allahu zzan dauka."
Gyaran murya yayi sanann ya ce,
"Sabir!"
Jin suna da ya ambata yasa kirjin ta dukan uku. Ta dago da sauri.
Kai ya dauke ya ce,
"Sabir ya same ni da zance yana son ki. Dan haka mun ba shi dama dan nasan in take ce baza ki amshe sshi ba. Yau aka sa ranar bikin ku nn da wata shekara za ayi bikin ku insha Allahu."
Kasa tayi da kai tana zubar da hawaye.
To ita dan ta dan ta auri Sir Sabir mene, tinda ta rasa wanda take so ma.
To amman fa ita Nusaiba take ji. Kuma bazata iya bujurewa maganar su Mami ba.
Tana son Yaa Aslam amman kenan ya zama dole ta hakura dashi. Tinda tasan ba yadda zai tana da aure ta so wani ba kuma.
Duk maganar da Yaa Buhari yacigaba da fadi ba ji take ba.
Sai da taji ya ambaci Yaa Aslam sannan hankalin ta ya dawo kansa.
"Tinda naje Abuja naga halin da yake ciki ba san ba haka matar sa ta bar shi ba. Sai kuma yau da Momy tazo take fadan halin da yake ciki. Asma'u mune kadai yan uwan Yaa aslam dole mu tsaya akan sa da addu'a sannan da wani abun da muka sani na tsarin jiki."
Tinda ya fara magana take kuka har yanzu da ya kare abinda yake fadi
"Kar ki diba abinda yai miki ki 'ki taya shi da addu'a kinsan Yaa Aslma ya so ki a baya to yanzu ma ki dauka kaddara kuce tasa kuka rabu "
Shiru tayi amman sai hawaye dake ambaliya a idon ta.
"Asma'u!"
Ya kira sunan ta.
Dagowa tayi da idanun ta da suka rine da hawaye sukai jajir da su.
"Mene na kuka? Sabir din ne bakya so?"
Kai ta girgiza
"To Yaa Aslam din baza ki taya da addu'a ba?"
Shima kai ta girgiza.
"To yi hakuri ki daina kuka kinji."
Kai ta gyada masa.
Mikewa tayi jiki a sanyaye ta shiga dakin da take kwana.
Kayan ta ta fara hadawa tana cikin hadawa Zainab ta shigo.
Kallon ta ta tsaya ganin tana debo kaya daga cikin durowa zuwa cikin akwatin ta.
"Lafiya?"
Zainab ta tambaya.
"Tafiya zanyi. Sis yanzu a gida an daina so na mai sona a duniya mutum daya ne, kuma ya mutu wanda na dauka shima yana sona din ya daina, to Mami ma da Yaa Buhari sun daina. Wai har sun gaji dani zasu aurar dani ba tare da ina son sa ko an tambayen ra'ayi na ba. Zan bar muku gidan ku ina jin na tare muku wani abu shine yake son nai aure na bar muku gida. Zan tafi gida nasan can Mami baza ta koren ba dan nasan shi zai kai mata maganar Sir Sabir."
Buhari da yana tsaye bakin kofa shima ya shigo. Ya ce,
"Ko daya kanwata. Bazan taba daina son ki ko gajiya da ke ba. Ki fuskance ni. Nasan dai ke ba yarinya bace karama kinsan komai. Bai kamata ace kin kai yanzu ba aure ba. kin gama karatu har kina aiki ai gwara kiyi aure tinda kin samu mai son ki. Kada ki manta da fa tini kina gidan ki wa yasani ma ko da ciki ko 'da. Mutunci 'ya mace gidan mijin ta fa."
Fuska ta rufe saboda kunya. Yaa Buhari ya ce,
"Kiyi hakuri ki karbi zabin mu insha Allahu zaki ji dadi."
Kai ta gyada. Ya ce,
"To ki mai da kayan."
Kai ta make masa, ta ce,
"Ni dai gida."
Murmushi yayi ya ce,
"Husnah daru."
Kai ta gyada ta ce,
"Naji."
Ya ce,
"Kya bari dai gobe ko?"
Kai ta girgiza masa. Duk yadda yaso ta zauna ki tayi.
Da zai matsa mata ma sai ta saka masa kuka.
Dole suka bar ta ta tafi ba dan sun so ba.
Tana zuwa gida ta shige dakin ta ta rufe.
Kwanciyya tayi ta rasa wane tunanin zatai tunanin aure da za ai mata ne ko tunanin halin da Yaa Aslam yake ciki ne.
Mikewa tayi ta fada bandaki alwala tayo ta fito ta dinga yin nafila.
Ta jima tana yi sannan ta dauko kur'ani ta karanta, addu'a tayi masa sosai.
Sannan ta zame agun bacci ya dauke ta.
Buhari ne ya fadawa Mami, Asma'u ta taho wannan yasa ta zo daki ta dduba.
A kwance ta same ta a kasa, idanun ta sun kumbura
Tabata Mami tayi ta bude idanun ta. Jajir suke sai kace gauta.
Mami ta ce,
"Tashi ki hau kan gado."
Mikewa tayi ta hau kan gado. Fita Mami tayi ta kawo mata fura da ta dama.
Kawo mata tayi ta amsa ta sha. Mami na fita ta koma ta kwanta.
Bacci ne yaki zuwa wanna yasa ta mike tana ta addu'a.
*MS Indabawa*
[1/18, 14:35] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
?? *HAJOW* ??
*Hakuri da juriya Online writer's*
Dedicated to *My lovelly Mum*
Page *66-70*
*HAPPY BIRTHDAY PRINCESS AMRAH. WISH MORE YEARS AHEAD+ MIJI NA GARI+ YA'YA MASU ALBARKA+ RAYUWA MAI AMFANI+ RESULT MAI KYAU.*
*AMEEN*
Tin daga lokacin rayuwar Asma'u ta kara komawa shiru shiru, dan daga wajen aiki sai ibada da ta sa a gaba.
Addu'a kuwa kullum yi take Allah ya yayewa Yaa Aslam abinda yake damun sa.
Haka nan addu'a ta daya ce Allah ya zaba mata mafi alheri.
Duk ta rame, Mami ma ta rasa kanta.
Dan ko zaman falo ta daina kullum tana daki kan sallaya.
Wayar ta kuwa ta kashe ta gaba daya.
Duk yadda Sir Sabir yake son ganin ta ko kiran ta awaya ba dama
Dan sai ya yini a asibiti bai ganta ba.
In ma a gidan ne haka baya taba ganin ta.
Yau kamar kullum zaman dakin ya ishe ta gashi bata sallah.
Carbi ne a hannun ta, ta mike ta fita tayi garden.
Tana shan kwana Sir Sabir na shigowa. Hango ta da yayi yasa yabi vayan ta.
Tana zama shima ya karasa wajen ya zauna.
Kallon ssa tayi ta dan yi murmushi. Ta ce!
"Ina yini?"
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce,
"Wallahi kina wahalar dani."
Shiru tayi ta kasa ce masa komai. Ya ce,
"Husnah kiyi hakuri wallahi tausayin ki nake ji shiyasa nayi duk abinda na aikata amman kiyi hakuri. Bayan nan kuma Nusaiba da kike magana akai na miki alkawarin tare za'a hada bikin ku."
Dagowa tayi da sauri ya gyada mata kai, ya ce,
"Eh! Tare aka saka ranar ku."
Kai tai kasa da shi. Tin daga lokacin bata kara magana ba.
Tana can tunani wai su biyu za'ai bikin su. A ranta ta ce,
'To mene ni da ba son mijin nake ba.'
Duk maganar da yake mata ma ba ji take ba tana can duniyar tunani.
Haka har ta jiyo kiran sallah magariba.
Wannan yasa ta mike tana ce masa,
"Sai anjima."
Kallon ta yayi ta shige cikin gida. Kai ya girgiza ya rasa ya zai yi ya shawo kan Asma'u.
Tana zuwa ciki ta kunna wayar da wajen sati biyu rabon da ta kunna.
Text din Nusaiba da Zainab da Maryam duk ta gani.
Na Nusaiba ta bude taga sakon akan sa ranar da akai musu ne.
Tsaki tayi najin wai Nusaiba na murna dan zasu auri Sabir tare.
Wayar ta kashe ta jefa ta gefe daya ta saka kuka.
Sai da tayi mai isar ta sanna ta mike ta shiga bayi ta wanke fuskar ta.
Haka rayuwar ta ta kasance, har Zainab ta haihu ta haifi dan ta na miji.
Sunan Dady aka saka masa, Asma'u na kiran sa da Dady. Su kuma suna kiran sa da Aiman.
Sosai Amsa'u ke son Aiman. Dan kullun sai taje ta ganshi.
Duk da, da ta ganshi take tafiya. Ko zainab yanzu ta kasa gane kan Asma'u.
Dan sai taje gidan daga gaisuwa shikenan.
A haka har lokacin bikin su ya rage wata biyu da Sabir.
Amman zan iya cewa ko sun hadu daga gaisuwa shikenan dan ko zai yi magana ba jin sa ma take ba.
Haka nan su Mami da Momy da Zainab suke ta shirye shiryen bikin. Banda ita da ko an tambaye ta abu bata bada asma.
Takanas Nusaiba tazo dan jin me dame zasu yi amman sam Asma'u hata bata amsa ba.
Sai gun Zainab taje suka tsara komai da ita.
Ranan tana zaune tana lalluben littafan isilamiyyar ta sai da lalubo wani littafi.
Littafin da ta dade tana neman dan anan ta rubuta wasu abubuwa ta.
Tana Budewa taga littafan addu'oin da Malamin su ke basu ne tana rubutawa a ciki.
Dubawa ta farayi sai ta gano wani rubutu da ta rubata
'Karya sihiri'
Dubawa tayi ta ga abinda ta rubuta.
'Ya hallata a karya sihiri amman ba ayi ta ko wacce hanya sai abinda ya shafi hadisi ba aje gun wani dan yin wani abu ba.
Da farko wanda akai wa ya jimanci karatum Alkur'ani, Amanarrasuli, Ayatul kursiyyu, Falaki, Nas, Ahad, Bakara,
sannan mutum zai samu habbatus sauda, da zam zam sai a karanta, fatiha, aciki ya shafe jikin sa.
Ya na karanta suratul mulki, jinnu, yusuf, sannan ya samu zam zam, zuma a karanta Wasafati a ciki ana sha. Da yadda Allah komai akai wa mutum zai warke."
Tana gani ta mike da sauri dauki wayar ta.
Kunnawa tayi ta lalubi number Momy ta tura mata da yadda zata yi sannan ta koma ta zauna.
Tana zama sa ga kiran Sabir nan tsaki tayi ta ce,
"Daga kunna waya."
Dauka tayi ta kara a kunnen ta, tai sallama cikin sanyin murya.
Amsawa yayi daga dayan bangare. Ya ce,
"Kina lafiya?"
Kai ta gyada, sai kuma ta tuna baya ganin ta, ta ce,
"Lafiya!"
Ya ce,
"Asma'u yanzu haka kike ganin rayuwa zata tafiyu, aure fa zamu yi amman kwata kwata kin kasa sakin jikin ki dani sauran fa wata daya. Dan Allah ki tausaya min."
Tausayin sa ne ya kamata, ya ce,
"Wallahi Husnah nai miki alkawarin samar miki dukkan farin cikin ki ko da zai zame min bakin ciki. Ki yadda dani."
Shiru tayi dan ta saba da irin wadan nan kalaman wajen Yaa Aslam. Amman yanzu ina kalaman sukai.
Taso ace Yaa Aslam ne ke kara fada mata wadan nan kalaman.
Sai dai kash ba shi bane, to tana fatan Allah yasa hakan.
Alkawarin rikan da ya dinga daukar mata sai take ganin kamar Yaa Aslam ne.
Wannan shi ya dan sasauta mata ta sauko saboda tausayin sa da take ji.
A haka ya roke ta, akan ta daina kashe wayar ta.
Sannan kuma yana son ta fada masa abubuwan da take bukata.
Ba laifi ta dan saki jiki sunyi waya amman fa duk sai dai in shi ya tambaye ta abu.
Suna gamawa ya kira Nusaiba ita ma suka dan gaisa.
A bangaren Aslam kuwa abin ba dadin ji, dan pretty ta zame masa karfen kafa.
Baya iya komai sai da cewar ta. Duk da sai tai wata nawa bata gari amman ko kala baya iya cce mata.
Sai dai in shi zai fita ta hana shi fita.
Yanzu ma tayi tafiyar da ta saba ne, shine ya samu damar zuwa gaida Momyn sa.
Yana zuwa Momy ta bashi hadin abinda Asma'u ta turo mata ya sha.
Sannan ta bashi sauran ta ce, yana amfani dasu
Sosai ta masa nasiha kan ya dage da addu'a da karatun Alkur'ani.
Shi sai a lokacin ma ya tuna da duk ya manta bayayi.
Mutumin da a da sai ya kwana a kan sallaya.
Kwana biyun da tayi bata nan sosai ya samu ya dawo hayyacin sa.
Dan Mami da ruwan da ta bashi ya kare take kara aika masa da wani.
Ba laifi kuma yana tashi yai sallah da addu'oin neman tsari.
Sai gashi ya fara dawo dai dai, duk yadda ya firgice yanzu ya dawo dai dai.
Dan kullum zai je gaishe da Momy, kuma Yanzu yana yawan tunanin ina Asma'un sa.
Sai da Pretty tai sati biyu sannan ta dawo.
Tana shigowa gida ta tadda baya nan. Nan ta tanadi masifar da zatai masa.
Sai wajen karfe goma ya baro gidan Momyn sa.
Yana shigo yai cikin gida. A falo ya same ta kafa daya kan daya.
Kallon ta yayi ya watsar yayi hanyar bangaren sa
"Mallam baka ganni bane?"
Ta tambaye sa
Banza yai mata dan shi bai zata da shi take bama.
Mikewa tayi ganin ya shige ba tare da ya dawo ba.
Bayan sa ta bi, ban san me ya faru ba sai ihun ta na jiyo ta fito daga dakin sa da gudu.
Zama tayi tana defe kunci saboda zafin marin da taji.
Kallon dakin tayi tana tunanin ayyan kuwa Aslam ne wannan.
Aslam har ya daga hannu ya mare ta. Sosai take jin jina Abin.
Shi kuwa wanka yayi yai alwala ya saka kayan baccin sa zama yayi yana mamakin har tayaya ya bari yarinyar nan ta raina shi haka.
Ya jima yana tunani sannan ya mike ya tada sallah.
Ya jima yana sallah sannan ya zauna yyana addu'a, maganin shi ya sha ya dauki al kur'ani yana karanta Suratul Bakara.
Tin da ya fara karantawa yaji kansa na juyawa amman bai dai na ba.
Haka ya cigaba da yi. Har ya daina jin abinda yake ji.
Sannan kuma ya kwannta. Abin mamaki da ya rufe idon sa sai yaga Asma'u,
Mikewa yayi ya dauko wayar sa number ta yai dailing amman a kashe hakura yayi ya koma ya kwanta.
*Hhhh toh fah ya kk ji chapte?*
*MS Indabawa*
[1/18, 14:35] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*
Dedicated to *My lovelly Mum*
*71-75*
*Na gaishe ku yan kungiyar *HAJOW* ubangiji Allah ya kara basira da daukaka. Ina minyin ku irin da yawan. Soyayyar ku bazata misaltu ba. Sai dai Addu'a Allah ya bar mu tare har abada har a gidan Aljanna. Allah ya hada mu kamar yadda muke anan ma. Ameen.*
*Momyn mu, Nafisa Sulaiman (Hajiya Nafeesa) a koda yaushe ina yaba karamci da soyayyar gare mu. Allah ya raya zuri'a Allah dada lafiya da nisan kwana. Ameen*
Haka canji ya dinga samuwa wajen Aslam. Dan har fita yake hana Munasha.
Sosai ta shiga hankalin ta. Dan taga ya dawo Aslam din shi na farko.
Wanda kwarjinin sa ya dadu, shi wani lokacin Mamakin mai ya hada shi da Pretty yake yi
Haka zai je gun Mami yai ta cewa,
"Mami number Asma'u nake nema."
Sai dai Mami ta dauke kai in ya ishe ta. Ta ce,
"Me zakai mata?"
"Mami ina son jin muryar ta ne, ina son sanin halin da take ciki."
Dariya Mami take in ya fadi haka. Tace,
"Aslam sai yanzu kake son sanin halin da take ciki, a kalla shekara biyu rabon ku baka taba tunanin haka ba sai yanzu."
Yana mamaki in Mami ta ce, sun shekara biyu basa tare dan shi gani yake kwana ki ne.
Ganin yadda Aslam ya daina sakar mata dan ba inda take zuwa ma. Kuma duk masu aikin nan ya rage su.
Gashi ya amshi kudin sa dake gun ta.
Wannan ya tada mata da hankali har ta dau aniyar koma wajen Bokan ta.
Shirye shirye tafiya ta fara ba tare da tasanar da shi ba.
Haka ta dauki hanyar nijar. Agidan kawar ta ta sauka daga nan ta nufi gun bokan ta.
Yana ganin ta ya fara dariya dan yasan aiki ya lalace yanzu kuma damar sa ce.
Da ta fada masa damuwar ta yayi dariya ya ce,
"In zaki yadda ki bar Aslam shine yafi miki alheri. Kizo gareni muyi rayuwa mai dadi."
Zabura tayi jin abinda bokan yake fadi.
Mikewa tayi tana nuna shi da yatsa. Ta ce,
"Allah ya kiyaye min na aure ka. na aure ka nace na auri wa? Baka da hankali."
Ta tofar da yawo tayi gaba. Dariya yayi ya ce,
"Dani kike zaki dawo da kafafun ki.'
Haka ta tafi aka rakata wanin wajen,
Malamin bai mata aiki ba sai da ya kusance ta.
Haka taa dawo gida da sa ran ganin canji ammn abinda Aslam yai mata ya kara tada mata da hankali.
Dan takardar saki ya mika mata. Har saki uku.
Sosai ta firgita. zatai masa magana ya zare mata ido yace ta tafi zai aiko mata da kayan ta.
Gida ta tafi tana kuka kai kace babar ta ce ta rasu.
Aslam kuwa ji yayi kamar an dauke masa duk wani nauyi akan sa.
Yanzu damuwar sa daya ita ce Asma'u.
Asibitin sa, da baya zuwa shi ya koma ya tada shi.
Sai da ya dai dai ta komai sannan ya fara shirin tafiya Kano.
Pretty kuwa Momah ta ce ta dinga kwantar mata da hankali kan zasu san abinda zasuyi ta koma gidan ta.
Sosai ta ji dadi. Haka ta koma karuwancin ta duk da ita ta fison tayi aure ta huta.
Duk wanda yazo mata ta ce ya fito baya kara dawowa.
Haka nan ko a cikin yan harkar su haka abin yake.
Ita auren kisan wuta take son tayi. Tunawa da bokan ta da tayi ta ce,
"Bazata gun sa ba tasan ba zai sake ta ba ko ya aure ta."
Shikuwa bata san yana can yana shirye shiryen yadda zai shawo kanta ba.
Rannan tana kwance akan gado ta mike zunbur.
Mayafi ta saka ta fito sai tasha. Motar nigar ta shiga suna sauka tayi wajen Bokan ta.
Da kuka ta ke ce masa ya taimaka ya aure ta.
A haka dai ta zauna a gun sa suna rayuwa banza dan ba aure sukai ba.
Asma'u kuwa abu na kara rikice mata