Showing 51001 words to 54000 words out of 92878 words
Chapter 18 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt
11-15 ayi hakuri wannan shine 11-15 wancan 6-10 ne nagode*
MASOYA MASU BIBIYAR WANNANN LABARIN NAGODE KWARAI DA GASKE. ALLAH BAR ZUMUNCI. COMMENT DIN KU NA DADA MIN KWARIN GWIWA NAGODE.
*11-15*
Kuka ta kuma fashewa da shi ta ce,
"Meyasa? meyasa? Meyasa yaa Aslam? Me nayi maka da na cancanci haka."
Ta kuma fashe wa da kuka dan har numfashi ta na sarkewa.
Mami ce ta fito ta tadda ta a hankalin da take ciki.
Da sauri ta karassa gun ta. Ina har numfashin ta ya dauke
Da sauri Mami ta kira suka tafi da Asma'u asibiti.
Aslam kuwa ana can yau daurin aure. Duk da yau take ranar farin ciki a gunsa amman sai akasin haka.
Dan damuwa sosai ya shiga na tinawa da tini da Asma'u ake daura auren nasu.
Duk yadda yaso yai farin ciki ya kasa. Abokan sa kuwa dayawa duk basu je daurin auren ba dan ya riga ya koya musu son Amsa'u.
Dukkan su mamaki suke sosai. Wasu kuma haushin Pretty suke ji.
Wasu daga cikin abokan sa su suka hallaci daurin auren.
Bayan an gama reception ya koma gida ne ya kwanta a daki.
Ba abinda yake gani sai Asma'u da ke masa murmushi.
Ido ya lumshe, ya rasa me yake damun sa.
Gani yake kamar a mafarki wai ya auri Pretty. Mamaki yake sosai amman kuma sai wani abu ya dauke hankalin sa daga wannan.
Haka da dare aka kai amarya gidan ta. Dan Mami ta ce bazai saka kowa a gidan da ya gina dan Asma'u ba.
Wani daga cikin gidan shi yasa aka gyara akai wa Pretty kafin kayan ta.
Amarya kamar ba amarya ba dan mayafi ma a kafada ta yafa aka raka ta gidan ta.
Aslam kuwa lokacin yana gida a kwance ya rasa me zai yi.
Mami da kanta taje ta same shi a daki.
Duk da ganin yanayin da yake ya bata tausayi amman hakan bai sa ta ce,
"Ka tashi ka tafi gidan ka. Ga amaryar ka can an kai maka ita."
Shiru yayi kamar bazai yi magana ba. Sai kuma ya sauko daga kan gadon ya durkusa a gaban ta ya ce,
"Momy dan Allah ki yafe min. Momy wallahi ban san abinda yake damu na ba."
Kai Momy ta dauke, Kuka ya saka yana nema yafiyar Momy.
Kallon sa tayi ta tausaya masa ta ce,
"Ba komai kaje Allah bada zaman lafiya. Amman har ga Allah bana son auren nan naka."
Kin sakin ta tayi sai da Momy ta daga sa tace,
"Kaje ka shirya dare nayi."
Mikewa yayi ya shiga bandaki. Ya fito ya shirya cikin sky blue din shadda. Yayi masifar kyau.
Wanka da turare yayi sannan ya fita falo.
Momy bata nan dan haka yayi bangaren ta. Ko da ya taba kofar a rufe take.
Dan haka ya juya ya fice, motar sa ya dauka ya fice daga gidan.
Gidan shi ya wuce kai tsaya. Gidan ne babba wanda yake dauke da babban falo sai kofa da take kallon gabas ita ce in an bude za a shiga bangaren Pretty, Da katon falo sai bed room guda biyu da kitchen da bandaki.
Gidan yayi kyau sosai. Sai dayar kofar dake kallon ta Pretty shine bangaren Aslam benene.
Shima katon falo ne sai Bed room guda biyu kamar yadda bangaren Pretty yake.
Sai wajen gidan kato ne, dan bayan gidan da an shakatawa ba kamar dayan gidan da yake da komai dan har garden da swimming pool ne a shi.
Zama yayi dadi tsakanin ango da amarya sai dai sabin halaye. Da yadda ya same ta.
Ta maida Aslam kamar bawan ta dan sai abinda ttace shi yake mata.
In ta ce, kaza dole yayi shi. haka in ta aiki shi da gudun sa yake zuwa.
Duk da wani lokacin yana mamakin sa in ya kudurce a ransa bazai ba sai ya kasa.
Kamar ko da yaushe yau ma gefen karfe biyun dare ya zame jikin sa daga na Pretty.
Bandaki ya shiga yai wanka ya dauro alwala.
Sallah yazo ya dinga yi dan sai gab da asuba ya zauna yana karanta alkur'ani.
Ana kiran asuba kuma ya mike ya tafi massalaci.
Bai dawo ba sai karfe bakwai. Amman har lokacin Pretty ko mikewa batayi ba bare ta yi sallah.
Gidan dai yan aiki suna ta gyara shi. dan yan aikin da tazo dasu sunfi hudu kowa da aikin sa.
Daga mai gyara mata turaka sai mai gyara mata kitchen da girki.
Sai mai mata gyaran jiki da mai mata wanki under wears din ta.
Sai wani yaro dake mata sharar harabar gidan.
Ita ba abinda take sai dai a kawo mata taci ta koshi ta kwanta.
Dan ba abinda ttake yi. Daga zama sai kallo sai kuwa fita yawo.
Dan wani lokacin ta fice tin safe sai dare take dawowa.
Aslam kuwa da yake ba gwanin cin abincin masu aiki ba sai dai yaje gida ya ci.
Haka yake rana da dare. Duk ya rame ya zama wani iri da shi.
Ita Momy ma tausayi yake bata. Haka shi da baya son hayaniya dan gayu ya tsara yadda zai na jin dadi da matar sa.
Sai dai ya dawo ya tadda uwar lalaci a kwance yan aiki suna mata tausa.
Ko wani lokacin ya dawo ya tadda bata nan.
Bangaren Asma'u kuwa sai da tayi jinya sosai a makkah dan sai da Buhari da sir sabir suka je duba ta.
Sai da tayi sati biyu a asibiti sannan aka sallamo ta.
Ranan tana daki a kwance. Mami da Sir Sabir da Yaa Buhari suna falo suna hira.
Sir Sabir ne ya tambayi mene ya jawo wa Asma'u hawan jini haka.
Shiru Mami tayi kafin ta bashi labarin komai.
Sir Sabir sosai ya tausayawa Asma'u duk da yana mai godiya da Allah wata kila rabon sa ce shiyasa Allah yayi ba ai auren ta ba.
Daman ance, *Matar mutum kabarin sa* in Allah yayi rabon sa ce shikenan.
Sir sabir ya ce,
"Mami yanzu kina nufin Aslam yai aure?"
A kunne Asma'u kenan lokacin da ta fito daga daki.
Faduwar ta kawai suka ji. Da gudu sukayi wajen ta.
Nan da nan suka kara daukar ta sai asibiti.
Da kyar suka samo numfashin ta ya dawo dai dai.
Dr sai fada suke dan zuciyar ta da kamo da ciwo. Banda jinin ta da ya hau. Ya ce,
"Allah yasa ta tashi lafita dan ba karamin hawa jinin ta yayi ba."
Kuka Mami ta dinga Sir Sabir ne mai lallashin ta dan Yaa Buhari ma ya rasa me yake masa dadi.
Abinda baya so Asma'u taji kenan ya baro ta daga kano amman dai da taji.
Wata zuciyar kuma ta ce,
"Shikenan yanzu ai komai jjuj zo da sauko tinda ta san komai."
Sai da tai kwana uku a kwance kamar gawa.
Dan likita yai mata allurar da zata sa ta sami hutu ko nutsuwar ta zata dawo.
Kwanata hudu sannan ta farfado shima da kuka.
Dan sai a lokacin ta samu damar kuka. Ba karamin tashi hankalin ta yayi ba.
Asma'u kuka take kamar ranta zai fita. Mami ce ke lallashin ta.
Asma'u ta ce,
"Mami me nai wa Yaa Aslam? Anya Mami. Mami wallahi ba Yaa Aslam dina bane sai dai wani Yaa Aslam bazai taba yi min haka ba. Mami Yaa Aslam da ya ce min 'yai min alkawari bazai guje min ba. Ya ce, In dai soyayyar sace na gama samu, kuma insha Allahu babu kishiya. Mami amman kuma shine yayi aure ya manta da duk alkwarin da ya sabar min dasu. Mami ce min yayi fa, 'in bar tsoro, in sanya a rai na za ayi auren mu. In Allah ya yadda zamuyi rayuwa, matsayin ma aurata za muyi shakuwa. Ba gudu ba ja da baya sona zai tayi zai zauna dani har karshen rayuwa. Mami amman ji ya guje ni. Mami shiyasa nace miki Yaa Aslam bazai taba bari na ba."
Sai kuma ta fashe da kuka. Dan har numfashashin ta ya fara dauke wa dan sai da aka kira Dr yai mata allurar bacci sannan aka samu tayi shiru.
Sosai Asma'u ta kuma ramewa. Ta kuma zama shiru shiru da ita dan magana ma ba sonyi take ba.
Yau kamar kullum tin da aka sallamo su a asibiti take kuka su koma gida kawai tinda abinda aake boye mata ya fito fili.
Sosai take rigima dan yanzu rigima ta dada yawa haka kawai sai ta tasa Mami a gaba tana mata shagwaba.
To yanzu ma tana kwance a falo sai tunani take, bama lokacin da suke zaune da Dadyn ta,
Dadyn ta ya fado mata da inda yake Tambayar ta abinda take bukata na bikin ta. Ta ce.
"Dady da sauran lokaci fa."
Dadyn ya ce
"Haka ne, amman na fison komai na gama shi da wuri dan bamu san me lokaci zai bayar ba "
"Haka ne Dady. Amman ni bana bukatar komai."
"Kin tabbata?"
"Eh Dady."
"Shikenan na miki transfer din kudi ta account din ki kingan su."
Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"
"Ki duba wayar ki, zaki gani. Dan haka ki ajiye in lokacin bikin yazo in kina bukatar kudi ki huta ba sai kin hau tambayar Mami ko Yayun naki ba."
Murmushi tayi ta ce,
"In ban tambaye su ba ai ina da Dady ko?"
"haka ne! Kina da Ni amman in ina nan ba."
Murmushi tayi ta ce,
"Dady tafiya zaka yi ne?"
Kai ya girgiza ya ce,
"Ko daya in na mutu nake nufi."
Damuwa ce ta sauka akan fuskar Asma'u sosai har ta kasa furta komai.
Dady ya ce,
'Haba *Husnahn Dady* mene na bata rai dan na fadi abunda dole ne ya faru. Ki daina sa damuwa aranki nasan ko na mutu kina da masu rike ki amana. Amman mutuwa tana kan kowa. Kowa lokaci yake jira da tazo kuma bata jira dauka kawai take. Gara duk abinda zamu nayi muna tunawa da ita. Kuma muna sawa a ran mu a ko da yaushe zaata iya zuwa ta dauke mu. Ki daina damuwa. Allah shi ya tsara mana rayuwar mu kuma in yai nihar mutun ya rayu sai kiga ya shekara nawa ma bai mutu ba. Ina iyayen mu duk sun mutu to muma haka wata rana zamu tafi. Fatan mu da addu'ar mu Allah yasa mu cika da imani kuma Allah yasa can ta fi nan
Hawayen idon ta ta goge ta ce,
'Allah sarki ashe Dady mutuwar kuwa zakai da gaske ke."
Sai maganar sa ta karshe da ya ce,
' *Husnah* dan Allah kar ki manta kina sa ya'yan ki suna min addu'a.'
'Insha Allahu. Dady ka daina sa wannan a ranka. Kai ma zaka rayu da su. Su sanka insha Allahu.'
Tana tunawa ta goge hawayen idon ta ta ce,
"Dady Yaa Aslam ya juyan baya bansan me nai masa ba."
Sai wani kukan jin kanta na ciwo yasa tai shiru ta lumshe ido kawai.
*Allah sarki Husnah
Brodas nd sisters ya kk na sameku lpy. Kuyi hakuri kuci gaba da kasancewa dani.
Komai na duniya yana da darko da karshe. Ko wane tsanani yana tare da sauki.
Bawa bay gujewa kaddara ubangiji. Sai dai muyi ta addu'a Allah daura maba abibda zamu iya.
Nagode da kaunar ku. Nima ina kaunar ku.
Ina barar addu'ar ku. Kwana biyu kai na na matsamin da ciwo. Dan Allah kusani a addu'a Allah ya yayewa musulmai baki daya.
Ameen.
Nagode
*INDABAWA*
[1/18, 14:28] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
*part 2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*
Dedicated to *My Lovelly Momy*
*21-25*
Tana kwance Sabir ya shigo. Zama yayi ya zuba mata ido.
Sunan ta ya kira ganin alamar ba bacci take ba.
Ido ta bude wanda sukai jajir dasu.
"Subhanallah!"
Ya fada da sauri yana matsowa wajen ta.
Kallon ta yai ya ce,
"Jikin ne?"
Kai ta girgiza. Ya ce,
"Kuka ko?"
Kasa tai da kan ta. Shiru yayi kafin ya ce,
"Haba *Husnah!* "
Da sauri ta dago kanta. Tinawa da mutum biyu ke yawan kiran ta da sunan gashi basa tare.
Daga Dadyn ta sai Yaa Aslam. to Dady ya mutu, Yaa Aslam baya tare da ita.
Ashe zata kara samun wanda zai kira ta da wannan sunan da tafi jin dadin sa akan ko wanne.
Kallon ta shima yake ido cikin ido. Kasa tai da idon ta, tana kokarin mai da kwallar da ta fito mata.
Magana ya farai mata cikin sanyi wanda taji kamar Yaa Aslam ne ke lallashin ta.
Ya ce,
"Ki daina kuka. Kina godewa Allah akan duk abinda ya faru dake. Jarrabawa d Allah ke miki in kika cinye baki san wane tukwici ne zai biyo gare ki ba. Kina sa hakuri da dangana a zuciyar ki Allah zai miki sauyi da mafi alheri da izinin Allah.
Kai ta daga. Tana jin sanyi a ranta kamar yadda Yaa Aslam ya sabai mata.
Ya ce,
"Walalhi in na gan ki cikin halin damuwa ina finki shiga damuwar."
Da sauri ta dago ta kalle shi. Dan sai taji kamar Yaa Aslam dan shi yake fada mata wannan kalmar.
Kasa yai da kai dan baisan lokacin da ta fito daga hakin sa ba.
Hira ya dinga bata. Dan har da su dariya tana rike ciki tsabar dariya.
Mami ce ta fito ta same su a haka. Dadi taji ganin yadda Sabir ke sa mata auta tayi dariya.
Zama Mami tayi ita ma ana yi da ita har Buhari shima ya fito aka dinga yi da shi.
Sosai ta rage damuwar da take ciki.
Amman da magariba kuma sai ta sawa Mami daru kan su koma gida ta fara aiki a asibitin ta.
Sosai Mami taji dadi da taji Asma'u na son fara aiki dan da ko maganar sa batayi.
Ai kuwa cikin satin su ka daga suka yo Kano.
Gidan ssu a gyare dan masu aikin su sun gyare masu shi.
Kowa dakin sa ya shiga yai wanka suka fito suka ci abincu.
A falo suka bbaje ana hira. Can Asma'u ta ce,
"Bro saura wata nawa bikin ne?"
Murmushi yayi ya ce,
"Wata daya fa!"
Ido ta zaro ta ce,
"Wallahi da ba dan Anty zee zaka aura ba da ba inda zamu kara tafiya. Kiji fa Mami da ya fada mana muje mu hado kaya kafin mu dawo amman yaki ko?"
Murmushi Mami tayi. amsa'u ta ce,
"Mami nan da sati fa zamuje mu hado wani sati mai zuwa kuma akai kaya."
Mami ta ce,
"Duk yadda kika ce."
Asma'u ta kalli Mami ta ce,
"Na kuwa bude asibiti na hau tafiya kuma."
Mami ta ce,
"Me zai hana."
"Shikenan. Allah Yaya ina kara fada maka dan Anty Zee ce da ba inda zani."
Murmushi yayi ya ce,
"Godiya nake? Nawa kuke bukata."
Hararar sa Asma'u tayi ta ce,
"Ai ATM zaka bamu kawai sai yadda kaga saura."
Dariya yayi ya ce,
"Mami dan Allah a dan tausya min dan naga wannan kanwar tawa so take ta sa na rasa ko na shinkafa ne."
Dariya Amsa'u tayi ta ce,
"Ai da sauki in dai na shinka fa ne, zan dire maka kayan abincin shekara ma."
Sukai dariya gaba daya.
Cikin ikon Allah a satin akai bikin bude asibitin.
Inda suka dauke kwararun ma'aikata.
Sosai ake aiki dan asibitin ya karbo. Sunan Dady ta saka wa asibitin aka saka masa. *Suleiman Specialist Hospital*
Taimako sosai yake a asibitin dan har ragi take na kudin marasa lafiya.
Sati daya da bude asibitin tafiyar su ta kama.
Komai ta bari a hannun Yaa Buhri. Inda suka tafi ita da Mami.
Sosai ta dinga jidowa Zee kaya masu kyau da tsada.
Set biyu suka hado mata sannan suka hado na fitar bikin su.
A lokacin ne Asma'u ta sha kuka tinawa da tai ita ma fa wai nata na nan ko.
Sai ta tuna lokacin da take gwada kayan da zasu yi fitar biki da Momy ta kawo mata.
Kuka sosai take sai da Mami ta shigo ta tadda ta. Mami tasan me ya sata kuka dan haka hakuri ta dinga bata.
Kwanan su shida suka juyo suna dawowa suka sanar da Uncle Abubakar shi ya sanar da Dadyn Aslam da uncle iliyasu akafadawa Gidansu Zainab.
Aka kai laife aka sa biki sati biyu masu zuwa.
Tinda Asma'u ta dawo ta kuma komawa shiru shiru.
Daga wajen aikin ma sai ta kulle a office tai ta kuka.
Haka biki ya dinga karatowa. Ta dibi dinkinsu takai musu.
Sir Sabir ne ya ce, zai na taya ta yin aiki.
Wanna yasa ya koma asibitin ta. Yana dan taimaka mata in bai da aiki da yawa.
Tana zaune a office din ta. Ta saka wani yellow material sai blue din mayafi da tayi rolling dinshi.
Tayi kyau sosai ta saka blue din sandal da blue din jaka.
Aiki take yana duba abu a system din ta.
Kamar kullum yau ma Yaa Aslam ne ya fado mata. Kai ta kifa kanta a benci tana ta kuka.
Da sallama ya shigo office din nata. Wanda ya haduwar kai ba zaka ce office bane.
Sai kamshi da sanyi AC ke ratsa shi gefe TV na aiki.
Sanye yake da blue din shadda yayi kyau dashi.
Kansa ya saka hula hannun sa daure da bakin agogo. Kafar sa sanye da bakin takalmi.
Yayi kyau sosai duk wacce ta kalle shi sai ta so shi.
Har ya zauna bata san da shigowar sa ba. Ganin bata san ya shigo ba yasa ya mike ya matsa kusa da bencin ta.
Dan bubbugaga table din ta take, yayi tai saurin dagowa idon ta da hawaye.
Kallon ta ya tsaya yi. Ran sa abace. Ganin sa yasa ta fara kokarin goge hawayen ta.
Zama yayi ya ce,
" *Husnah* ke fa bakya ji ko? Wai bakya son lafiyar ki ne, kita sa damuwa a ranki. To in ba ki damu da rayuwar ki ba ni na damu da ita. In bakya son cigaba da rayuwa ki ina son kici gaba da ita dan wani ne farin cikin ki ni kece farin ciki na. kece farin ciki na. Kece buri na."
Sai kuma yai shiru. Kallon da take da mamaki a fuskar ta.
Kai ya gyada mata ya ce,
"Eh! Wallahi *Husnah* tin san da na fara ganin ki naji ina son ki. Son ki tin a lokacin ya shige ni. Na rasa ta yadda zan sanar dake ne. Ki bani dama *Husnah* zan yaye miki dukkan damuwar ki zan maye miki gurbin Aslam da yaddar Allah."
Kai ta girgiza ta ce,
"Sir baza ka iya ba. Kasan waye Yaa Aslam a guna kuwa. Duk da abinda yai min jin sa nake har yanzu yana zuciya ta. Jin sa nake a rai na. Kasan tin ban san kai na ba Yaa Aslam ke so na. Da son sa na girma da son sa na san wace ni. Da shi kadai na taba soyayya. Sir ko ban auri Yaa Aslam ba to nasan bazan kara soyayya ba. Bazan taba daina son sa ba. Son sa ya riga ya zama jinin jiki na raba ni da shi bazai taba yiyuwa ba. Kayi hakuri nagode da soyayyar ka."
Ta mike tana goge hawayen ta tana gogewa yana kara zubo mata.
Jakar ta, ta dauka ta fita daga office din da sauri.
Yanzu ita tasan soyayyar maso wani take.
Tinda ita