Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 92878 words

Chapter 14 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*






Dedicated to *My Lovelly Momy*
*Momy nah a koda yaushe addu'a ta bazata taba karewa gareki ba.*


*Kece komai nawa. Ina nufin komai fa.*


*Masoya a ko da yaushe kune silar dariya ta. Bama in ina karanta comment din ku.*


*To Alhamdulilah Da soyayyar ku a gareni. Allah ubangiji ya bar ni da ku.*


*Gaskiya ina jin dadin yadda kuke bibiyar labarin nan.*


*Masoyan Aslam*
*Masoyan Sabir*
Kuna ina ne?








*136-140*


An Kar6o Daga *Anas (ra)*, Lallai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *“Idan Aka Gabato da Abincin Dare, to Ku Fara Dashi Kafin Ku Sallaci Magariba”*. (Bukhari da Muslim)_










Suna zuwa asibiti aka amshe shi. Sun jima akan sa dan har akai sallar asuba.


Sallah Asma'u tayi ta jima tana wa Dady Addu'ar Allah ya bashi lafiya.


Dady kuwa ganin jikin sa sai wasiya yake bayar wa yana cewa,
"A kira masa *Husnah* ku kira min matata da 'da na da Auta tah *Husnah* "


Da sauri Dr ya karasa ya kira su. Asma'u na shiga da gudu ta karasa wajen Dady ta rike hannun Dady tana jijigawa tana cewa
"Dady gani. Dady ga *Husnah* ka."


Dady dake kwance yana fitar da numfashi sama sama, ya kalli Mami da Buhari. Ya ce
"Amina Allah miki albarka. Allah ya baki aljanna madauka. Buhari kai ma Allah maka albarka Allah ya saka a gidan aljanna Allah baka mace ta gari."


Ya karasa maganar da kyar. Cikin sa ya kara rikewa ya kalli Asma'u ya sakar mata murmushi ya ce,
"Ga *Asma'u Husnah* nan ku kula da ita. Ita ce, yarinyar karama kar ku bar ta tai kuka. Amina Allah miki Albarka. *Husnah* Allah ya miki albarka. Allah baki zuri'a ta gari Allah ya saki a Aljanna."


Hannun Buhari ya kamo tare da na Mami. Kallon Asma'u yayi ya sakar mata murmushi.


Kalamar shada ya dinga fadi a hankali. Mami ita take tayasa amsawa. Su Asma'u da Buhari kuwa gaba daya sun rikice da kuka.


Can Dady ya saki hannun su idon sa ya lumshe, cikin firgice, Mami ta kwadawa Dr kira.


Dr ne ya shigo ya duba shi. Kai ya girgiza kawai.


Kallon sa Asma'u tayi ta ce,
"Dr ya jikin nashi ne?"


Kallon su Dr yayi ya ce,
"Sai dai kuyi hakuri Allah ya amshi rayuwar sa."


Asma'u dake tsaye wata juwa taji tana dibar ta. Daga nan duhu ya rufe mata idon ta.


Zubewa tayi a kasa. Mami ma faduwar tayi. Buhari kuwa ya rasa ya za yi.


Da sauri Nurse suka yi wani Daki aka kai Mami da Asma'u aka kwantar da ita. Suna kokarin ceto rayuwar su.


Buhari kuma ya buga waya ya fadawa Uncle Abubakar kanin Dady da uncle ilyasu da kanwar sa.


Sai Momyn Aslam da sauran yan uwa. Cikin minti kadan gida ya cika da jama'a.


Mami da Asma'u kuwa suna Asibiti. Momyn Aslam a lokacin suka taho a jirgi.


Karfe sha biyu aka sa za ayi jana'idar Daddy.


Momyn Aslam na zuwa, ta zarce asibiti. tana zuwa Mami ta farka.


Kuka Mami ta saka. Momy ta kama ta ta ce,
"Haba Amina, me yasa zaki kuka ki sani kukan ki ba abinda zai karawa Abban Asma'u. Addu'a ce kadai zaki taya shi da ita Allah yai masa rahama.dan Allah ki daure kar ki bari ki saba da zubar masa da hawaye. Allahn da ya bamu shi yafi mu son shi dan haka hakuri zamuyi muna taya shi da addu'a."


Sosai Momy tayiwa Mami nasiha mai ratsa jiki.


Kukan ta daina amman fa zuciyar ta kamar zata fashe.


Damuwa karara akan fuskar ta. Da haka suka mike suka yi gadon da Asma'u take.


Tana kwance har lokacin bata san inda kanta yake ba.


Momy ce ta zauna da ita aka tafi da Mami gida dan ganawa da gawar Dady.


Aslam kuwa da suka taho Dadyn sa bai sanar da shi halin da Asma'u ke ciki ba.


Dan haka duk yadda yaso ya ganta ya ga a halin da take ciki bai samu ba.


Momyn sa ya kira ya ke tambayar ta ina Asma'u dan Allah ta fada masa halin da take ciki.


Dan yasan a wannan lokacin Asma'u zata fi kowa jin mutuwar Dady.


Duba da irin shakuwar dake tsakanin ta da shi.


Komai in zatayi Dady ko abu zata yi tace Dady.


Tafi yin shawara dashi akan da Mami. shiyasa yake son yasan a halin da take ciki.


Haka ta ce masa tana asibiti in ta dawo zata duba masa halin da take ciki. Amman ya kwantar da hankalin sa tana lafiya.


Suna cikin waya aka kawo Mami gida. Da sauri ya karasa gun Mami.


Duk tausayin ta ya kama shi. Shi ya kamata suka shiga cikin dakin da aka kwantar da Dady.


Addu'a Mami tai masa sosai, sannan aka zo aka dauki gawar ta shi.


Duk yadda taso kar tayi kuka sai da hawaye ya zubo a idon ta.


Kanwar Dady ita tazo ta shiga ciki da ita.


Jama'a sun cika gidan makil da mutane. kowa sai mutuwar Dady yake ji, Dady mutumin kirki me kawaici da Hakuri da taimako.


Dan haka kowa abin alherin sa yake fada da masa addu'a.


Mami karfin hali kawai take domin tasan ta rasa farin cikin ta. Ta yi asara da baza ta taba maida kamar ta ba.


Dan rashin Dady a garesu ba karamin gibi bane.


Ana ta amsar gaisuwa Mami kuwa ta yi nisa cikin tunani, ga Asma'u, ba wanda tafi ji.kamar Asma'u.


Asma'u kuwa da magariba ta farfado. Tana ta shi tasa kuka ina Dadyn ta.


Sai kuma ta kuma fashe wa da Kuka ta ce,
"Momy dan Allah ku kaini wajen Mami da Dady dan Allah Momy Dady bai mutu ba ko? Momy kada kice min ya mutu."


Sai wani kukan Momy ma sai da tayi hawayen dan ba karamin tausaywa Asma'u tayi ba.


Allura Dr ya karai mata ganin tana neman fita daga hayyacin ta.


Sai da Dady yai kwana uku aka sallamo Asma'u, gida suka taho da Momy dake wajen ta in kaga Asma'u zaka ga ta rame sosai sai kace wacce ta dade tana jinya.


Aslam da tare suke jinya a asibiti shima duk ya rame ya yi duhu.


Tare suka dawo, Asma'u na zuwa gida tayi wajen Mami, ta rumgume ta tana wani kuka mai ban tausayi.


Kuka sosai suka yi sannan Mami ta dago ta tana kallon ta.


Ta rame har abin yai yawa.
Buhari ya ce,
"Mami ga Asma'u nan bata cin abinci ko tea taki amsa ta sha."


Kai Mami ta girgiza ta jata jikin ta tana shafa bayan ta ahankali a hankali.


Zainab da tinda akai mutuwar take zarya daga asibi zuwa gidan yau ma tana gidan.


Dakin Asma'u suka shiga, Asma'u da ta kasa daina zubar hawaye daga idon ta.


Abinci Yaa Buhari ya dauka ya kai mata ya ce taci amman sam taki ci.


Yaa Asalm ya fadawa. Aslam da kansa ya shigo gidan ya shiga har dakin ta ya tadda ta kwance akan gado.


Zama yayi a gefen ta ya dago ta. Tana ganin shine ta fada jikinsa tana sakin wani kuka mai ban tausayi.


Rumgume ta yayi yana lalashin ta da kalamai masu nuni ga ban hakuri har tayi shiru sai ajiyar zuciya da take saukewa.


A hankali ya dinga bata baki har ta yadda ya dinga bata abinci a baki.


Ci take tana yamutsa fuska dan ba dadin sa take ji ba. Har wani daci yake mata a baki.


Idon ta kuwa ya kasa tsayar da hawaye, a haka ta dan ci ta ce ta koshi.


Tin daga lokacin kullum Asma'u na gefen Mami, dan ko bacci ta koma kullum tana gefen ta.


Kullun kuwa Asma'u da zazzafi take kwana ta tashi. Amman da Mami ta ce zata bata da lafiya zata ce ta ji sauki.


Ranar bakwai kuwa Asma'u kamar me kuka ta dinga yi dan har numfashin ta daukewa ya dinga yi.


Yaa Aslam da Sir Sabir su suka tsaya akan ta.


Da kyar suka samu numfashin ta ya dawo dai dai.


Bayan bakwai kowa ya watse sai Momy da Aslam.


Suma ana yin kwana goma Momy ta fara shirin tafiya. Hakuri sosai ta dinga bawa Mami.


Sannan ta zaunar dasu gaba daya, ta kara basu hakuri sannan ta bawa Mami kudi masu yawa.


Haka Momy ta tafi gidan ba dadi daga Buhari sai Aslam da Mami da Asma'u.


Asma'u da ta zama shiru shiru ko magana batayi. In anyi abu sai dai ta kalli mutum ta dauke ido.


Aslam kuwa kullum ya zauna sai ya san yadda zai sa tayi dariya.


Aslam shike sa Asma'u yin hira ta dan sauko.


In kuwa ba haka ba sai dai ta zauna tai ta zubar hawaye.


Yau ma kamar kullum tana kwance akan gado, ba abinda take sai zubar hawaye tana tunanin Rayuwar su da Dady.


Murmushi ta dan saki sai kuma, kuka da ya kwace mata.


Aslam dake tsaye a kofar ya na kallon sanda tai murmushi sannan kuka yazo ya karaso gun ta da sauri.


"Haba *Husnan Dady* yanzu haka zamu ta rayuwa kenan kullum kin ki ki sake, kina tunanin Dady zai ji dadi a halin da kike ciki. Haba *Husnah* a ko da yaushe Dady bai da magana da ya wuce yasan ko bayan ransa *Husnah* baza tai kuka ba saboda yasan damu. To menene amfanin namu da mu na nan zaki na kuka. Haba *Husnah* dady ba abinda yake nema gun ki sai addu'ar ki. Dan Allah ki daina wannan kuka. In ba haka ba ni bazan iya jurar ganin kukan ki ba zan tafi in hakan kike so."


Hawayen ta, ta goge ta ce,
"Na daina Wallahi Yaa Aslam na daina. Kar ka tafi ka barni."


Murmushi Aslam yayi ita kuwa duk da hawayen da take yi gogewa wani ne yake kara daduwa.


Jikin sa ya jata yana lallashin ta.












*Hmmm kulli Nafsin xa'ikatul Maut.*
*wannan haka yake*


*Karki kuce saboda na sa Dady ya mutu. Haka rayuwa take, muma wata rana sai mutuwa.*


*Hmmm kuyi hakuri haka tsarin littafin yake. In ba haka ba wani abu bazai faru ba. Nagode*


*Nusaiba S Indabawa*
Ki daure ki karanta littafin nan.


Lol wai ita indai nayi littafi wani ya mutu bata karantawa saboda tausayi.


*To sisto ki karanta dan nasan kina son karantawa. Mutu a kuma dole ce. Ke yanzu ina Dady, ya rasu. Sai dai muyi masa addu'a Allah ya kara masa rahama Ameen!*


ALLAH KA JIKAN DUKKAN MUSULMAI. KA JIKAN YAN UWAN MU, DA KAKANNIN MU, DA IYAYEN MU DA YAYUN MU DA KANNEN MU DAMU KAN MU IN TAMU. TAZO


AMEEN!




*INDABAWA*
[1/18, 14:21] Maryam S Indabawa🥰:  *LABARIN RAYUWAR*


*Asma'u Husnah*






Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*






🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*






Dedicated to *My Lovelly Momy*






141-145


An Kar6o Daga *Abi-Zarrin (ra)* Yace: *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: *“Idan 'Dayanku Zai tsayar da Sallah Kada Ya Goge Kasa, Domin Rahama ce Take Fuskantarsa”.* (Mutane Biyar Suka Ruwaitoshi) da Sanadi Ingantacce._






Aslam yayi na mijin kokari wajen sauyawa Asma'u rayuwa.


Dan kullum cikin daukar Asma'u ya kai ta wajen shakatawa ko ya kai ta shopping.


Banda fina finen da yake siyo mata na ban dariya.


Sai da yayi wajen wata biyu a kano sannan ya koma saboda wajen aikin sa.


Duk da tafiyar sa duk wata kulawar da yake bata bai daina ba sai daduwa dda ta karayi.


Sabir kuwa har Mamah ya kawo gida tai wa su Mami gaisuwa.


Haka Maryam ma takanas ta zo kano dan Asma'u. Asma'u ma taji dadi.


Haka nan Maimuna ma tazo tai mata ta'aziyya da yan department din su.


Da kyar Asma'u ta koma asibiti, ta cigaba da rayuwar ta.


Sabir ma yana zuwa akai akai yana duba su ya gaida Mami.




Pretty ce zaune kamar an mata allura ta mike ta dauki ATM din ta da kudi ta zuba a jaka.


Fita tayi ta tsaida mai Napep ta shiga. Tasha kai tsaye ta nufa.


Tana zuwa ta hau motar Niger.


Suna sauka Pretty ta tafi hotel.


Sai da tai bacci ta huta tai wanka sannan ta ci abinci.


Mikewa tayi sai kace wacce zata tashi sama.


Fita tayi daga hotel din ta tsaida mai napep. Yana tsayawa ta fada masa inda zata sannan ta hau suka tafi.


Yana tsayawa ta biyashi kudi sannan ta shige wajen.


Waje ne kamar jeji haka ta kutsa kai. Sai da tayi tafiya mai nisa sannan ta karasa wajen


Yar bukka ce, shi kuma yana zaune a gefen ta.


Jikin sa ba komai sai ganye da yayi tufa da shi.


Kalar fatar jikin mutumin baka kirin, haka nan jikin mutumin sai tashin wari yake.


Idanun sa jajir kansa gashi ne yayi yawa dan sai a iya kitso ma akan shi.


Yana zaune gefen sa tukwane ne. Tin da Pretty ta karasa wajen yake binta da wani fiti nan nen kallo.


To kayan dake jikin ta ne kai ba zakai tunanin yar musulmi bace.


Zama tayi nesa dashi dan ita ma tana kyamar sa.


"Sannu boko na kan tudu."
Ta fada tana kallon sa.


Bakin sa ya bude wanda hakoran dake ciki sun zama ja dasu.


"Kinji shiru ko?"
Ya tambaye ta.


Kai ta daga masa, murmushi yayi ya ce,
"Eh kamar yadda na fada miki aikin yana da wahala ne,"


"Toh! Malam......"
Tsawa ya daka mata. Ya ce,
"Kar ki kara ce min Malam."


"Dan Allah ka taimaka min wallahi zuciya ta zata iya bugawa in ban samu Aslam ba ka taimaka min."
Kai ya daga ya ce,
"Na fada miki aikin yana da wuta. Dan Aljannin da zai miki aikin ya ce, sai ya tara da ke tukkuna."


Ido ta zaro ta ce,
"Aljannin."


Kai ya gyada mata. Ya ce
"kar ki damu ki kwantar da hankalin ki. Ta jikina zai yi amfani dake,"


Ya fada yana lashe lebe. Kallon sa tayi a zabure ta nuna shi da yatsa, ta ce,
"Kai!"


Kai ya gyada ya ce,
"Eh ni."


Wani kallo ta watsa masa ta mike tabar wajen.


Tana fita tayi gidan kawar ta wacce ta hada ta da bokan.


Tana zuwa ta zube mata abin da ya faru, dariya kawar tata ta hau yi ta ce,
"Amman wallahi har kin ban kunya, dan aljanni ya neme ki shine me?"


"Ke dallah shine fa zai kusance ni. Haba kinsan fa ya yake, warin jikin sa ma kadai ya ishe ni."
Pretty ta fada tana toshe hanci sai kace a gaban sa take.


"Kinga ki ajiye duk wannan a gefe wallahi in har yayi abunda ya bukata ko to bukatar ki ta gama yi. Kin samu Aslam dan shi da wannan kwailar yarinya har abada dan nasan ko kallo baza ta ishe shi ba."


Kallon ta Pretty tayi. Ta cigaba da magana.
"Muma duk Boka yayi abinda kike tsoron yi dashi. Kuma ya kusan ce kinki zaki ji abinda baki taba ji ba.


Kallon ta Preetty tayi a ranta tana son samun Aslam amman kuma tana kyamar ta yadda zata je wajen Boka.


A haka kawar tai ta zuga ta har taji zata je dan biyan bukatar ta.


Gida ta tafi tana tunanin taje ko kar taje.


Wata zuciyar na cewa taje wata kuma tana hanata zuwa.


A haka ta kwana da tunanin wata haryar da zata mallaki Aslam.


Ganin bata da wata hanya yasa ta amince da zata koma gun sa.


Mikewa tayi ta shiga wanka ta shirya cikin shigar banzar da ta saba yi.


Abin hawa ta hau ya kai ta inda zata je. Ya dire ta tayi cikin jejin.


Yana zaune kamar ko da yaushe, yana ganin ta ya saki fara'a.


Karasawa tayi tana jin damuwar zuwan nata. Kallon ta yayi ya ce,
"Ya kin amince ne?"


Kai ta gyda masa dariya yayi ya ce,
"To ai kin kyauta. Ki shiga daga cikin zan kira shi in zo zaki ganshi."


Mikewa tayi tai ciki. Kallo ya bita dashi yana lashe leben sa.


Can ya mike yayi cikin dakin da ta shiga yana wata irin tafiya.


Sun dauki a kalla fin awa hudu zuwa biyar sannan Bokan ya fito yana gumi. Wajen zaman sa ya zauna.


Can kuma sai ga pretty nan ta fito. Fuskar ta tai jajir da ita.


Kallon malamin tayi ta bar wajen. Gida ta je ta dade tana dirje jikin ta sannan ta fito ta kwanta a kan gado.


Ido ta lumshe tana cewa, Amman Malamin nan yayi. Dama ace Aslam ne.


Ta yi juyi akan gado ta ce,
"Asma'u kike ko Husnah ina tausaya miki duk randa na samu Aslam kin mutu."


Cikin ta taji yana kukan yunwa ta mike ta fita gari dan samun abunda zata ci.








Asma'u ce zaune a garden tana sanye da threequatern wando da riga karama a jikin ta. Sai hijab din ta da yake har kasa. ta rafka uban ta gumi. Ba wanda ta tino in ba Dady ba.


Hawaye taji yana bin fuskar ta da sauri ta goge hawayen tina maganar Aslam da ya ce,
" *Husnah* dan Allah kimin alkawarin ba zaki kara kukan akan Dady ba sai addu'a. wallahi kukan ki yana taba zuciya ta kamar yadda nasan ki cikin wani hali inda nima nake tsintar kai na a ciki. Ki daina kuka dan Allah ko bayan ido na kar kiyi kuka. In kuwa kikai kuka bazan taba yafewa kai na akan amanar ki da Dady ya bani ba."


Murmushi ta dan saki na tunawa da Yaa Aslam. Tana da tabbacin Ya Aslam din ta zai rike ta amana dan tasan yana daga cikin masoyan ta na farko a duniya.


Duk abinda yasan zai sa ta farin ciki shi yake buri shi yake mata. Ko baya son abu in tana so zai san yadda zai yi ya so abin.


Sabir da yana tsaye yana kallon irin murmushin da take sai yaji wani dadi.


Hawaye kuma ya dawo zubo mata tina in kuma ta rasa Aslam fa.


Kuka sosai take yi har Sabir ya tsaya gaban ta bata ganshi ba.


Handkerchief ya mika mata. Amsa tayi tana goge hawayen fuskar ta ba tare da ta ga wanda ya bata ba.


Zama yayi daga gefe ya ce,
"Haba *Husnah* mene na kuka kuma. Ki dauki hakuri kowa hakuri yake ki na wa Dady addu'a."


Kai ta daga tare da kallon sa. Shima kallon ta yake yana sanye cikin dark blue din wando da bakar riga. Sosai yayi kyau.


Murmushi ya sakar mata. Itama murmushin ta sakar masa.


Hira ya fara janta yana bata abin dariya. Sun jima suna tare sannan suka shiga wajen Mami.


Mami dake zaune rike da casbaha, tana ganin Asma'u ta gane tayi kuka.


Murmushi tayi ta mika mata hannu tayi gun ta. Ta ce,
" *Asma'un Dady* kukan ki kayi ko?"


Kai ta girgiza tana murmushi. Murmushin itama Mami tayi ta ce,
"Hakuri dai zamu nayi. Muma Allah bamu wucewa lafiya."
"Ameen!"
Suka amsa.


Hira Sabir da Mami suke ita kuma tana can a whatsapp suna chat da Yaa Aslam.


Hakuri yake kara bata tare da kwantar mata da hankali.


Suna yi tana satar kallon Sabir kamar yadda shima yake satar kallon ta.


Ita dai Sir Sabir yana burgeta, akwai shi da saukin kai ga fara'a.


Haka nan nature sa na burgeta. Ido ta lumshe sai kuma fuskar Aslam ta bayyana yana mata murmurshi


Itama murmushin tayi ya zame ta kwanta akan kujera.












*INDABAWA*
[1/18, 14:22] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*


*Asma'u Husnah*






Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*






🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*






Dedicated

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads