Header Ads
Showing 42001 words to 45000 words out of 92878 words

Chapter 15 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

to *My Lovelly Momy*








*146-150*










Kwanan Pretty biyu sannan ta koma gun malamin ta.


Tana zuwa ya hau mata albishir da aikin ta yayi kamar me. Murna ta farayi.


Malamin ya ce,
"Sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba. Shine ki kula sosai sannan kafin aure kiyi kokari ki dawo dan akwai wani abu da za a karayi miki."


Godiya tayi masa, ya ce,
"Kar ki damu da kin je gida zaki tadda abin mamaki."


Kudi masu yawa ta zube masa ta tashi tana masa godiya shi kuwa a ransa tinda ya kusan ce ta yaji a duniya ba wacce yake so kamar ta.


Yayi Alkawari da duk daren dadewa sai ya mallake ta ta zama tasa gaba daya.


Ya bata dama ne ta je wajen Aslam din amman yayi alkwarin shi da kansa zai raba su dan ya same ta.


Ita kuwa Pretty gida tayi tana ta murna.






**********************************************
Aslam ne zaune a dakin sa yana waya da Asma'u.


Duk wayar da suke kara kwantar mata da hankali yake, sosai take samun nutsuwa in tana tare da Aslam.


Sai dai kwanan nan tana yawa mafarkai akan Aslam, wanda in ta zauna ita kadai tai ta kuka ta rasa kukan mene, amman tasan tana tsoron rasa Aslam ne.


Kwanan nan ta dan rame ta kara rage walwala duk da yadda take so ta sake ko dan tana sawa Mamin ta nishadi amman kasawa take.


Bama in da dare bayan sun ci abincin dare. Ba wanda yake fado mata sai dady shi yasa da sauri take tafiya daki ta sha kuka.


In ba Aslam ne ya kira ta ya kwantar mata da hankali ba.


Dan Aslam ko ta chatting yana gane a irin mood din da take bare kuma yaji muryar ta.


Aslam dake kwance idon sa lumshe yana yiwa Asma'u tadi mai dadi da sanya ta nishadi har yaji tayi bacci.


Wayar ya bari a kunnen sa yana jin yadda numfashin ta ke sauka a hankali a hankali.


Yana kwancen nan bai tashi yayi alwala yayi shirin bacci ba bare addu'a bacci ya dauke shi.


Ya jima yana baccin can kuma sai ya mike.


Dakin ya fara kalla. Ba abinda yaji yana so ya ji ko ya gani in ba Pretty ba.


Abokin sa Mohd da Pretty tasan shi ta dalilin sa ya kira a waya.


Abokin sa dake kwance yana bacci dan lokacin wajen karfe uku ne yaga kiran sa.


Dauka yayi dan shi ya zata ma ba lafiya ba.


Aslam ne ya katse masa tunanin dalilin kiran sa ta hanyar ce masa,
"Mohd dan Allah number Pretty nake so yanzun nan."


Mohd cire wayar yayi daga kunnen sa ya kara kallon me kiran nasa.


To kawai ya fada ya kashe wayar. Mamaaki yake me Aslam zai yi da number Pretty bayan ko sunan ta bai son ji bare wani abu da ya shafe ta.


Baki ya tabe ya ce,
"Shi yasani."


Number ya tura masa ya koma bacci. Aslam kuwa yana ganin number yai ta kira amman a kashe.


Ranar har asuba bai kuma ba yana ta kiran wayar. Kiran sallah shi ya sa ya hakura ya mike yai wanka yai alwala ya tafi massalaci.


Yana fita Asma'u ta kira saboda jin bai kira ta ba.


Amman shiru bai dauka ba. Tayi tsammanin yaje masallaci shi yasa ta bar kiran nasa.


Aslam kuwa yana dawowa daga massalaci ko ta kan wayar sa bai bi ba. Ya shiga bayi ya kara wanka ya fito ya shirya cikin Wando baki sai riga ruwan kasa.


Yayi kyau dashi. Turare ya dauka ya feshe jikin sa dashi.


Falo ya fita ya tadda Momy na hada musu wajen karyawa.


Gaisawa suka sannan ya mike ya fita kamar wanda ake hankada shi.


Sauri kawai yake yaje yaga Pretty, gudu yake sosai har ya karasa gidan su,


Horn yayi aka bude masa gate din fitowa yayi bayan yai parking ya akai a kira masa Pretty


Wanda ya aika cikin gidan yazo ya ce, masa Pretty bata nan.


Cikin mota ya koma ya zauna. Wani iri yake jin sa. Ranar ji yake in har bai ga Pretty ba bazai iya rayuwa ba.


Duk ransa yana son yasan halin da Asma'u take ciki da ya fara tunanin Asma'u sai kuma Pretty ta fado masa.


Duk da Asma'un ba gushewa take a zuciyar sa ba amman ya rasa dalili.


Haka ya yini a harabar gidan su Pretty sallah ce kadai ke tayar da shi.


Da ya dawo zai tambaya ko Pretty ta dawo. Cikin lokaci kan kani ya canja ya koma wani iri.


Ranar sai karfe goma ya koma gida bayan ya tabbatar da Pretty bata nan.


Jiki a salube ya dawo gida. Momy kuwa da hankalin ta ya gama tashi na ganin tin safe basuyi waya da shi ba kuma in ta kira ba ya dauka ya daga mata hankali.


Yana dawowa ta hau tambayar ko lafiya. Ce mata yai bai da lafiya, wannan yasa ta kai shi daki ta hada masa ruwan wanka sanna ta kai masa abinci.


Wankan yayi ya ci abinci. A ransa yana tunanin yau ko a wane hali Asma'u take.


Har ya mike zai dauko waya ya kira ta kuma sai ya fasa ya koma ya kwanta.


Tunanin sa daya Pretty. Haka ya kwana ya tashi. Dan ko baccin kirki bai samu yayi ba.


Washe gari ma tin safe ya kuma dirar wa gidan su Pretty.


Pretty kuwa tana hanya dawowa ggida ana sallah la'asar aka kawo ta kofar gidan su.


Motar Aslam ta gani a cikin gidan su. Matsawa tayi wajen motar ta kalla ta kuma kalla.


Tabbas motar Aslam ce kenan da gaske dai abinda Malam ya fada mata.


Wani tsalle ta doka ta yi cikin gidan bangaren ta, ta shiga tai wanka ta fito tayi falon gidan.


Mahaifiyar ta ce zaune cikin shigar kasaita. Tana kallo.


Pretty ce ta shigo ta fada jikin ta. Kallon ta Mahaifiyar tata tayi ta ce,
"Pretty ni ai nayi fushi kwana biyu ko neme na bakya yi."


Kai ta dan sosa ta ce,
"Sorry Mommah!"


"Shikenan waye ne tun jiya yake zaryar neman ki a gidan nan."


Kallon mahaifiyar tayi ta ce,
"Wani ne, shine wanda nake son aura."


Murmushi uwar tayi ta ce,
"Kai Alhamdulilah amman naji dadi amman na bar shi a waje tin jjiya yake zarya fa."


"Kar ki damu Mommah nima nasha wahala akan sa."
Mommahn ta ce,
"Ah ai kam kema gasa abin ki."


Pretty ta mike ta ce,
"Kisa a kawon abinci bangare na."


Ta fice. Dakin ta ta nufa ta zauna. Wayar ta ta dauko ta kunna.


Text din Aslam ne suka dinga shiga wayar.


Sai da ta gama karantawa taga yadda ya hauka ce sannan ta sheke da dariya.


Kiransa tayi. Lokacin yana jikin motar sa dan bai dade da dawowa daga massalaci ba.


Yana ganin kiran ta yai saurin dauka. Ya ce,
"Haba Baby na ina kika shiga ne haka?"


Murmushi tayi ta ce,
"Kana ina ne?"


Gidan ya kalla sannan ya ce,
"Ina cikin gidan ku fa."


"Oh ai ban sani ba yanzu na dawo. Ka sa a nuna maka site dina sai ka shigo."


Nan da nan ya tambaya aka nuna masa ya nufi wajen da sauri dan bai da abinda yake burin gani kamar Pretty.


Tana zaune a kan kujera gaban ta kayan abinci ne kala kala.


Yana shigowa ta mike ya mata masifar kyau. Yana sanye da Brown wando sai milk din riga.


Wajen sa ta nufa ta kamo hannun sa. Murmushi ya sakar mata ya karaso cikin dakin.


Zama sukai a kujera mai daya ta zauna akan cinyar sa.


Fuskar sa take shafawa a hankali kafin ta daura kan ta a kkirjin sa.


Aslam kuwa wata ajiyaar zuciya ya dinga saukewa dan ko ba komai ya samu abinda ransa ya matsa masa ya zo ya nema.


Duk da zuciyar sa tana can ga Asma'u amman wani bangaren tunanin sa yana ga Pretty ya rasa dalili.


Kallon sa ta danyi ta ce,
"Wai da gaske kai ne?"


Kallon ta yayi ya ce
"Ga alama nan kuwa."


Kai ta gyada ta ce,
"Ya batun soyayyar mu."
Wani murmushi ya saki ya ce,
"Sai yadda kika ce."


"Da gaske?"
Ta tambaye shi tana wasa da sumar kan sa.


Kai ya gyada mata. Murmushi tayi ta ce,
"Aure nake so muyi nan da sati biyu."


"Sati biyu kawai "
Ya tambaye ta.


Kai ta gyada masa, ya ce,
"An gama. Nawa ne zai ishe ki siyan kayan lefe da komai da komai."


Kai ta dan daga ta ce,
"Ka bari zuwa gobe zan duba."


"Shikenan! Ki fada min goben fa. Dan nima na matsu."
murmushi tayi ta rumgume shi.


Shima rumgume tan yayi. Kiss ta fara masa, jiki da jini tini shima ya hau biye mata.


Kiran sallah da yaji ana yi shi yasa yai saurin tsayawa daga abinda yake yi.


Mikewa yayi. Kallon sa tayi ta ce,
"Lafiya?"


Nuni yai mata da waje sannan ya ce,
"Kiran Sallah ake."


Tsaki tayi ta ce,
"Ni na zata ma wani abun ne."


Ta koma ta zauna Kallon ta yayi yai murmushi ya ce,
"Bari naje na dawo."


Ya fice ranar dai har goma suna tare da Pretty da kyar ta kyale shi ya tafi.
















*INDABAWA*
[1/18, 14:22] Maryam S Indabawa🥰:  *LABARIN RAYUWAR*


*Asma'u Husnah*






Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*


Facebook @Maryam sulaiman
Wattpad @Msindabawa
Instagram @Maryam S Indabawa




🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*






Dedicated to *My Lovelly Momy*








*151-155*


An Kar6o Daga *Aisha (ra)* Tace: Na Tambayi *Manzon Allah(ﷺ)* Game da Waige a Cikin Sallah? Sai Yace: *"Wata Fisga ce Shedan Yakeyi a Cikin Sallar Bawa"*. (Bukhari)._


_A Hadisin *Tirmizi* Kuma Ya Ingantashi: *"Kashedinka da Yin Waiwaye a Cikin Sallah, Domin Halaka ne, Idan Ya Kasance Babu Makawa Sai Kayi, To Kayi A Cikin Sallar Nafila"*._










Yana shiga gida ya tadda Momy zaune a falo.


Kallon sa tayi ya karasa gun ta.


Gaishe ta yai ya dan zauna. Kallonsa tayi ta ce,
"Aslam lafiyar ka kuwa. Kwana biyun nan ina kake zuwa da har kake kai dare haka a waje."


Kai yayi kasa da shi. Dan ka idar sa da anyi isha'i yana gida.


"Ba magana nake maka ba. Ka fadan inda kake zuwa."
Shiru ya karayi.


"Wallahi Aslam zan batar maka in baka fadan ina kake zuwa ba."
kai ya dan sosa ya ce,
"Daman ina son nai miki maganar ne, wajen wata budurwa ta wacce nake son aura nake zuwa."


Tsaki Momy tayi ta ce,
"Wai ni sa'ar ka ce da kake min wasa bayan kasan ba lokacin wasa bane yanzu."


Shiru yayi yana tunanin ta inda zai fara.
"Wai ba magana nake maka bane, ko so kake na kira mahaifin ka na fada masa."


Kai ya girgiza ya ce,
"Momy da gaske nake."


Momy ta ce,
"Da gaske kake kamar ya?"


Kai ya sosa ya ce,
"Momy daman mun gama maganar aure da 'yar gidan tsohon ministern man fetur ne akan nan da sati biyu zamuyi aure."


Kallon sa Momy take tama kasa cewa komai.


Dagowa yayi ya kalle ta, ta ce,
"Eh ka dago ka kalle ni ai nifa bangane mai kake fadi ba."


"Eh Mami yar sa Pretty ita nake so nake son muyi aure nan da sati biyu dan har nace ta fadawa Mahaifin ta ma."


Kallon mamaki Momy kewa Aslam dan gani take kamar ba Aslam din ta ba.


Aslam din ta mai hankali da nutsuwa amman ji wannan inda yake mata wani shirmen zance.


Amman kuma fa zancen kamar akwai kamshin gaskiya.


Da kyar Momy ta iya bude baki ta ce,
"Asma'un fa?"


Kai ya girgiza ya ce,
"Momy ni yanzu ga wacce Nake son na aura."


Kallon sa Momy tayi ta ce,
"Aslam kana cikin hayyacin ka kuwa."


Kai ya gyada mata. Momy ta ce,
"Me ya hada ku da Asma'un taka."


Kai ya girgiza ya ce,
"Wallahi Momy ba komai."


"Amman saboda me zakai mata haka."
Kallon Momy yayi ya kasa bata amsa.


Shima bai san abinda yake fadi ba. Ji yake kamar bashi yake maganar ba.


"Aslam kasan me kake fadi kuwa. Asma'un taka kake son ka ce min ka fasa aura ko kuwa."


Kai ya gyada mata. Momy ta ce,
"Inna illahi wainna illahir rajiun."


Sai da ta fada sau uku sannan ta dago ta kalli Aslam sosai dan taga ko ya fara shaye shaye ne.


Har mikewa tayi tana shinshina sa da duba sa.


Ganin ba alamar shaye shaye yasa ta kuma mike tayi wajen sa tana duba shi.


Tabbas Aslam din ne dai 'dan ta. Komawa tayi ta zauna tana rike kan ta.


Sanna ta dago ta ce,
"Wallahi Aslam ba da yawu na ba a auren da kake son kayi. Ba ruwana kaje ka nemi wata uwar bani ba."


Ta mike ta bar masa falon. Mikewa yayi jiki a sanyaye yayi dakinsa.


Daki ne guda kai kace dakin wata amaryar ne. Babu abinda babu a ciki.


Kan kujera ya fada, yana dafe kan sa. Ya zai yi.


Wayar sa da tin dazu take kara ya dauko ya duba.


*Soul mate* shine abinda ya bayyana akan wayar.


Ajiyewa Yayi ba tare da ya dauka ba. Dayar wayar sa ce ta hau ringing itama yana dauka naga *My* ya bayyana akai.


Shima ajiyewa yayi bai dauka ba. Haka ta gama kiransa amman bai dauka ba.


Shi kansa wani zafi yake ji, baya son damuwar Asma'u amman mai yake damun sa yake neman sa ta a damuwa.


Dan ya tabbata Asma'u tana cikin damuwa fiye da tunanin mai tunani.


Har ya dau wayar zai kira sai kuma ya fasa ya kira Pretty waya sukai sosai. Dan har sha biyu suna waya sanna sukai sallama yai wanka yazo ya fada gado.


Shi kansa yasan bai da lafiya. Dan rashin Asma'u ba karamin tashin hankaline a rayuwar sa ba.


Pretty kuwa tana can har an fara shirye shiryen aure.


Dan komai da take bukata tai masa list din su.


Haka nan kudaden da za a kashe wajen taro duk ta masa suma list


Sosai ta tsuga kudi dan komai na karya take so yayi mata.


Waya kowa tayiwa kawayen ta kan cewa nan da sati biyu bikin ta. Dan har kalar ankon da za a sak"a ta fitar dashi.


*********************************************************************
Asma'u ce kwance, akan gadon kai daga ganin ta kasan ba lafiya ba.


To rabon ta da abinci kwana biyu kenan.


Hankalin ta ya kasa kwanciyya da rashin kiran da Yaa Aslam bai mata ba gashi ta kira shima bai daga ba. Ta kira Momy ma ita ma bata daga ba.


Tana kwance idon ta jajir dan rabon ta da bacci shima yau kwana biyu ne.


Ga wata faduwar gaba da take yawan yin ta. Ta rasa ta me ce.


Ido ta lumshe hawayen da ya taru suka zubo akan fuskar ta.


Juyi tayi tana me fashewa da kuka. Ba wanda ya fado mata sai Dady.


A duniya ta san indai Yaa Aslam ya na nan ba zatai kukan mutuwar Dady ba.


To yanzu in Yaa Aslam din ya mutu tayi yaya kenan. Ko in ya barta tayi ya kenan.


Tana tunanin taji an bude kofa. Da sauri ta goge hawayen idon ta.


Yaa Buhari ne, ya shigo hannun sa dauke da Leda.


Kan gadon ya karasa ya dan zauna kafin ya dago ta.


Jikin ta ya taba yaji har lokacin da zazzabin.


Kallon ta yayi ciki tausayawa ya ce,
"Sannu Asma'u. Ya jikin?"


Murmushi yake tai masa ta ce,
"Yaya nifa yanzu normal nake ji na."


"Da gaske?"
Ya tambaya yana mata murmushi shima.


Kai ta gyada masa. Murmushi yayi ya mika mata ledar hannun sa ya ce,
"Ungo wannan to ki daure kici kinji Kanwata."


Amsa tayi idon ta na kawo kwalla. Ta ce,
"Tnc bro."


"Ina zuwa. Akwai wani suprise da zan miki "
Ya mike ya fita.


Bayan sa ta bi da kallo yana fita ta fashe da kuka.


Mami ce ta shigo dakin da yake Buhari bai rufe kofar ba bataji shigowar ta ba.


Mami ce ta dago da kan ta ce,
"Oh Asma'u ke haka zaki ta ciwo da kuka. Wai yaushe zaki daina kuka in baki da lafiya."


Hawaye ta goge tana son kawar da damuwar ta.


Mami ta kalle ta sosai ta ce,
"Bayan zazzabin me yake damun ki. Dan ga damuwa nan fal a fuskar ki. In akan Dady ne, dan Allah ki rage damuwar nan Amsa'u kina masa addu'a kinji."


Kai ta gyada.
"Yauwah koke fa, *Husnahn Dady* "
murmushi tayi.


Mami ta dauki ledar da Buhari ya kawo mata ta bude.
Murmushi tayi ta ce,
"To ai ke sai ya narke"


Ta fada tana zaro mata ice cream din daga leda. Daya ta mika mata ta mika.mata kullin naman da ya siyowa kowa nasa.


A firij ta zuba ragowar ice cream din. Sannan ta ce,
"Ina Buharin?"


"Yanzu zai daw......."
bata karasa fadi ba sai gashi ya shigo da sallama.


"Au ina kaje?"
Mami ta tambaye shi.


Kallon Asma'u yayi ya ce,
"Daki fa naje."


Zama yayi a gefen Asma'u ya ce,
"Sis an sa ranar aure na da Zainab fa dan kiji tare za ayi da naku."


Yana fadar haka taji kirjin ta ya buga. Dan har sai da ta dafe shi.


A zahirin gaskiya taji dadi amman kuma bata san me ya haifar mata da faduwar gaban ba.


Murmushi tayi ta ce,
"Kai Alhamdulilah. Amman kuma shine ba a fada min ba."


"Sorry ai kece naga bakya jin dadi."
"Ni ba wani nan Yaya ka sani fada min zai yi sanadiyar samun sauki na. Zan hadu da Anty Zee din ne."


Murmushi Mami tayi ta ce,
"Kaji har baki ya bude ko?"


Daga haka suka ci gaba da hira sosai suka dauke mata kewar Yaa Aslam.


Dan har sha daya suna tare. Sannan. Buhari ya tafi dakin sa. Mami kuma suka. kwana tare.


Washe gari ta dan ji dama dama amman a zuciyar ta ba sauki sai abinda yyai gaba.




Aslam kuwa sai ya tari Dadyn sa da maganar ko kallo bai ishe shi ba.


Dan haka ya tafi gun Wan Dadyn sa. wan Dady kuma ya shige masa akan maganar auren su da Pretty.


Komai da komai akai aka tsaida nan da sati uku za ai biki.


Lokacin da Dadyn Aslam ya samu labari kasa magana yayi.


Dan baisan me zai cewa, Amina ba shi har ga Allah yafiwa Aslam sha'awar Asma'u.


Ko Momyn Aslam kasa mata maganar yayi shi kadai ya dinga juya abin a ran sa.


Aslam ya kira yai masa gargadi akan ya janye batu auren yarinyar da yake son aura amman sai ga Aslam har da su kuka.


Da Dady yaki sauraron sa mma sai ya zube ya suma a gun.


Da sauri Dady ya fita dashi asibiti hankalin sa a tashe.






*Alhamdulilah*
Anan na kawo karshen littafin. *LABARIN RAYUWAR Asma'u Husnah* *Part 1* Sai ku saurare ni dan jin karashen sa.


Anan ne zamuji Shin Aslam yana auren Pretty ko Asma'un yake aura.
Sannan zamuji Yadda Sabir zai kasance.


Anan nake muku fatan alheri tare da cewa mu hadu a *LABARIN RAYUWAR* *Asma'u Husnah PART 2*


Ina son naga comment sosai tukkinna.


And pls don't forget to vote @MSindabawa


*Nagode masoya na. Allah ya bar kauna*


HHHHH YA KUKA JI. FAN ALLAH KUYU HAKURI AKAN YANAYIN LITTAFIN KOMAI A TSARE YAKE ZAKUJI DADIN SA SOSAI


*Muje zuwa*




YANZU AKA FARA.


Godiya ga masoya masu bibiyar littafi na. Bazan manta dake ba *Ummu Ayda, fadeelat, bela'u, sis Kibdiyya, Fatitih, namesake, Asmy, Husnah, and also u Mahee Abdullahi kai kuna da yawa da yawa nagode nagode da bibiyar littaffin man da kuke. Allah ya bar kauna nagode*


Muje zuwa


*INDABAWA*




















[1/18, 14:26] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*


*part 2*


Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*


🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads