Showing 57001 words to 60000 words out of 92878 words
Chapter 20 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt
da juriya tare da kawar da kai, gidan zaman lafiya. Na gaida ku.*
*36-40*
Dedicated to My great *Mamah* Allah ya jikan ki ba dan kin mutu ba.
Allah kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka.
Nagaida ke mahaifiya ta abar alfahari na.
*Manzon Allah (SAW) ya ce,
Idan zaka so mutum kada ka nuna masa tsananin so.
in zaka kisa kada ka nuna masa tsananin ki.
Dukkan su hankalin su ne yayi kan motar, banda *Asma'u* da ta daukar da kan ta, tana wasa da wayar ta.
Khadija ce ta fara magana, ta ce,
"Kai motar nan ta hadu amman."
Amina tace,
"Ai daga duk kan alamu, ma na cikin ta zai fi haka hauduwa."
"Gaskiya kan motar ba karya, ko wane dan gayun ne a ciki."
Hafsat ta fada
"Ni kam ba ruwana da na ciki sai motar da ta burge ni."
Zainab ta fada.
"Kai Allah bani irin motar na."
Hafsat ta fada.
"Hassada kike yi tinda kika ce Allah baki irin ta sai dai kice Allah baki finta."
Amina ta fada.
"Duk karya ne irin haka nan, dan kaga Abu ka roki Allah yabaka irin sa shine haka."
Zainab ta fada tana tabo *Asma'u*
" *Asmy* kalli waccen motar amman tayi kyau wallahi."
Kai ta dago ta kalli motar, ji tayi gaban ta ya fadi.
"Eh tayi kyau."
Ta fada tana mikewa sakamakon kiranta da ake yi.
Can gefe ta koma jikin wata motar, ta dauki wayar.
"Hallo my beauty! (Kyakyawa)"
"Ya Aslam wannan ai tsokana ce."
amsa ta amsa masa da muryar shagwaba.
"Wacce tsokana nayi."
ya tambaya
"Wai beauty!"
ta bashi amsa.
"Oo Ke ba kyakyawar bace."
Ya tambaya.
Ta ce,
"Gaskiya ni ba kyakyawa bace. Wannan ai sai kasa ayi min dariya."
"Ba wanda zai miki dariya kinji, saboda kyan ki ba kowa ke da irin shi ba. Kina da wani kyau wanda kafin a samu mutum me irin sa ake dade wa. Ur skin is fresh with a beauty colour. (Fatar ki a murje, me kala me kyau)."
Ta ce,
"Uhmm please stop dis joking I beg you. (Dan Allah daina wannan tsokanar na roke ka."
Murmushi yayi ya ce,
"Wallahi I am not joking, I am telling the true. (Ba tsokanar ki nake ba ina fadan gaskiya ta ne.)"
Baki ta turo ta ce,
"Naji ya isa, ka karaso ne,"
"Eh! Gani kina ina ne."
Ta ce,
"Ina kofar department din mu,"
"Nima ina wajen."
"Kai ya Aslam!"
ta fada.
"Da gaske ina wajen."
"Ta ina."
"Ina cikin wata Ash marsandi."
"Oh na ganka. Ina ta bayan ka."
"To kizo man."
"A'ah Yaya please kai ka fito."
"To gani nan."
Baya ta juya masa.
Kofar motar ya bude, wani sanyi da kamshi me dadi ne ya fito.
Kafar sa ya ziro kasa. Safa ce da takalmi sau ciki bakake a kafar sa.
Daya ya diro sannan ya fito gaba dayan sa. Suit ce a jikin sa, ruwan kumkumadi.
Ya cire ta saman sai yar ciki da ya rage. Tin daga kafar sa na fara kallon sa inayin sama. har na karasa kirjin sa wanda yake a bude dashi na kirar cikaken namiji me jini a jiki wanda ya cika namiji.
Kan fuskar sa na gangara. Fuskar sa me kyau ce doguwa fari ne tas dashi, sai manyan idanu wadan da suke a lumshe, wanda ake ce musu (sexy eye)
Bakin shi dan karami ne, wanda yake da lebe me taushi gasu pink sai kwalli suke. Kansa cike yake da suma, kamar ta indiyawa.
Sai saje dake gefen fuskar sa, wanda ya kara fito masa da kyaun fuskar sa. Idon sa sanye da farin gilashi.
Masha Allah wannan gayen duk inda ake neman cikaken namiji me kyau da kwarjini ya kai ya ma wuce nan.
Yan mata da yawa kallon sa suka tsaya yi sai gulmar sa akeyi. Dan ya gama haduwa ba karya.
Waige waige ya farayi dan neman inda take, duk da ta juyar da kanta sai da ya gene ita ce. Dan duk jikin sa ya gama shaida masa, *Husnah* sa ce.
Cikin tafiyar kasaita da nuna kalama tare da nutsuwa yake tafiya.
Sannu a hankali har ya karasa gefen ta. Ta bayan ta ya zaro hannayen sa dake cikin alhiju ya rufe mata idanu.
Jin an rufe mata ido da hannu me laushi, ga kamshin turare dake tashi, tasan Ya Aslam ne.
Murmushi ta saki me sauti.
"Haba My Hero, ai nasan kai ne."
Hannun sa ya janye ya maidasu kan kafadun ta ya juyo da ita.
Kasa magana yayi ya kure ta da idanu.
Ido ta kashe masa guda daya.
"Yah dai."
Yawu ya hadiye tare da sauke ajiyar zuciya yana me sakin wani murmushi dake karawa fuskar sa kyau.
Wani kallon soyayya yake aika mata dashi.
Ba karamin kyau sukayi ba.
"Baby nah kinyi kyau fa."
ya fada yana kara kallon ta.
"Zaka fara ko?"
Ta fada tana nuna masa wasu kujeru da aka gina su.
Zama yayi ita ma ta zauna.
"Sannu Yaya nah Ya hanya?"
ta tambaya cikin kulawa.
Ya ce,
"Hanya Alhamdulilah."
"Sannu toh!"
"Yauwah! Naji dadin zuwa na dana ganki Sweetheart, kin kara kyau, ashe duk hoton da nake gani rage min kyaun ki yake yi."
"Yayana kenan yasu Momy."
ta fada tana wasa da yatsun hannun ta.
"Suna lafiya."
Ya fada yaba dago face din ta.
"Bari na karbo maka lemo."
Ta mike.
Kamo hannun ta yayi ya ce,
"A'ah yanzu na gama cin abinci ga naku can ma a mota."
Murmushi tayi,
"Kai Yayah."
"Eh!"
"Zakaje gida ne."
"A'ah! Daga nan zanyi gida."
"Ok."
"Ina sonki Baby nah."
Murmushi tayi ta dukar da kanta.
"Baby kunyar nan taki tana dada miki kyau."
Kai ta kuma dukar wa.
"Bari na wuce kar nayi dare. Tinda naga Baby nah ai nagodewa Allah."
Murmushi tayi.
"To nagode."
"Nike da godiya Baby nah "
Suka mike suka nufi motar. Dai dai karasowar Sir Sabir zai dauki motar sa.
Kallon juna suka yi, ya shige motar sa.
"Waye wancan."
Juyawa tayi,
"Sir Sabir wani lecturern mune."
"Kuna magana ne?"
Ya tambaya fuska a dan hade
Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"
"Ina zee kuwa?"
Ya tambaya.
Kallon gun da suke tayi ta ce,
"Gata can bari na kira ta."
Ta tafi wajen su Zee,
"Zee kizo inji Ya Aslam!"
Ta fada tana kamo hannun ta.
Wajen su suka karasa.
"A bamu waje ko?"
Ya fada yana kallon *Asma'u* baki ta tabe ta bar wajen. Dariya yayi, yace,
" *Husnah* rigima."
Sannan ya dawo da hankalin sa kan Zee.
Bayan sun gaisa yake bata amanar *Asma'u* sannan sukayi sallama.
Wajen *Asma'u* yayi,
"Haba Baby na yanzu da Yayan naki kike fushi. Kiyi hakuri kinji."
Shiru tayi masa. Murmushi yayi, ya koma gaban ta,
"Ko so kike na rumgume ki na rarashe ki."
Ido ta zaro, tana girgiza kai. Ya jawo ta. Saurin janye hannu ta tayi. Tayi wajen motar sa.
Bayan ta ya bi, yana Murmushi ya shiga motar. Leda ya miko mata.
"Gashi ni zan tafi."
Amsa tayi ta ce,
"To Allah kiyaye hanya."
"Ameen nagode!"
Ta rufe masa kofar tana daga masa hannu. Tare da murmushi akan fuskar ta.
Sai da taga bata hango shi sannan ta koma wajen kawayen ta.
Ido suka bita dashi,
" *Asma'u* waye wancan."
Hafsat ta tambaya fuskar ta a hade. Kallon ta *Asma'u* tayi sannan ta dauke kai.
Zainab ce, tace,
"Yayan ta ne."
Khadija tace,
"Amman fa ya hadu. Wai meyasa ke kike baka ne."
Amina ce, tace,
"To ko zaki canja mata halitar ta ne,"
Harara ta Khadija tayi,
"Ni na tambaye ta, ta wani haden rai da dauke kai."
Hafsat ta fada, Mikewa *Asma'u* tayi ta kalle ta.
"kin tambayen an amsa miki ba shikenan ba. ko kin manta wa kike tambaya ne. *Asma'u* da batai miki komai bace kika dau gabar duniya kika daura mata, kin manta in nayi miki magana ko kallo na bakya yi shine kuma yanzu zaki zo kina tambaya ta. Kuma cikin isa sai kace ni yar kice. Ke bama zan fada ba. Kiyi abinda xakiyi."
Ta fada tana kama hannu Zainab suka shige hall.
"Haba *Asma'u* me kenan kika yi ke da bakya fada."
Kuka *Asma'u* ta fashe dashi,
"Ya zanyi kema kinsan dai Hafsat ta kaini bango ne. Duk makarantan nan ba wacce ta tsana kamar ni tin ina dauke kai sannan yanzu tazo tana min gadara. Akan abinda be kai ya kawo ba."
"Ya isah toh mene na kukan!"
Ta fada tana jan ta jikin ta tana rarashin ta.
Ta jima tana addu'a cikin ranta sannan taji sanyi. Kan ta, ta dago ta kalli Zainab.
"Nagode besty."
"Ba komai."
kasa ta duka zata dauki jakar ta. Sai a lokacin ta tuna da abinda Ya Aslam ya kawo musu.
Murmushi tayi ta dauki ledar tana dubawa. Takeaway yayi musu, guda uku sai dayar ledar kuma kaji ne guda biyu a ciki da lemuka na jarka.
Raba su tayi gida biyu ta mikawa Zainab.
"Besty dan Allah mikawa su Amina kayan nan."
Karba tayi tayi waje.
Su *Asma"u* na barin wajen, su Amina suka farayiwa Hafsat fada.
"Haba Hafsat, meyasa kike haka, yarinya bata tsare miki komai ba amman kin tsane ta gaskiya ki daina haka."
Hafsa ta ce,
"Tayaya zakice bata taren komai ba, yarinyar da ta shigo ta same ni sannan tazo tafi ni kokari shine bata fini komai ba."
Khadija ta ce,
"Yo dan tafiki kokari, ai kema dagewa ya kamata kiyi ba ki tsane ta ba."
Khadija ta fada tana bata fuska.
"To ku dake ni mana."
Hafsat ta fada.
"A'ah A'ah ba abin duka anan. Sai dai muyi miki addu'a Allah ganar dake."
Dai dai nan wata daliba da tayi kaurin suna a makarantar ta karaso gun su
"Hae Babies."
"Hae!"
Gefen Hafsat ta zauna.
"Dan Allah wa naga ta tsaya da yaron nan da yazo yanzu. Dan bayan ta na gani banga gaban ta ba."
"Oh ai *Asma'u* Suleiman ce."
Hafsat ta bata amsa.
"Wane department take,"
Suka fada mata tai musu godiya ta bar wajen
Zainab na fitowa Munasha na shiga Hall wajen *Asma'u* ta dosa kai tsaye,
Toh masoya *Asma'u Husnah* naga sakon ku na gode, ba ma yan threestart u always love my story tnc Allah bar kauna.
Hhhh yan facebook comment naku na min dadi ngd
Afternoon yan uwa
Don't forget to vote pls
*INDABAWA*
[1/18, 14:30] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Part *2*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da juriya Online writer's*
Dedicated to *My lovelly Mum*
Pagr *41-45*
Yau Yaa Buhari yana tashi ya fara shirin tafiya.
Mami taso ya kara kwana ki to amman ba lokaci, dole haka ta bashi sakon Asma'u.
Kaya masu yawa ta aiko mata sannan ta bata sakon tayi amfani da kayan laifen da aka hada mata.
Sunyi bakwana kan cewa nan da kwana biyar zata taho Kano ita ma.
Haka Yaa Buhari ya taho yana kewar ta, a ransa kuma yana sa ran sai komai ya gyaru dangane da Yaa Aslam.
Asma'u kuwa washe gari ta tashi lafiya sai dai damuwa dake damun ta sosai.
Da farko akwai damuwar ta, ta rasa masoyin ta sai kuma damuwar, da Sir Sabir, yake ciki.
Tasan matsalar so tasan halin da ake fadawa na rashin samun masoyi. Dan haka dole ta tausayawa Sir Sabir.
Ta sa a ranta zata aminta da Sir Sabir ko da bata son sane.
Da wannan shawar da ta yanke kuma ta tuna wane Sir Sabir wajen kyawun hali yasa ta dan ji dama dama a zuciyar ta.
Dan har waya sukai da Maryam ta ce, mata tare zasu zo da kawar ta Nusaiba.
Asma'u kam murna har tana cewa su taho cikin satin nan.
Sannan ta ce, ta aiko da measurement din su za'a kai dinki. Sosai Maryam tai murna ta ce, mata insha Allah ran juma'a zasu zo kafin sati biki kenan.
Suna gama Waya Mami ta sauko ta ce,
"Asma'u dawa kike waya ne haka?"
Asma'u ta ce,
"Mami da Maryam 'yar yar Sir Sabir muke waya ranar juma'a ma zasu zo biki."
Mami ta ce,
"To fa. Allah dai ya nuna mana bikin nan lafiya."
Asma'u ta amsa da
"Ameen!"
Mikewa tayi ta shiga kitchen ranar ita ta shirya musu abincin rana.
Sannan ta shiga tai wanka ta ce, zata je ta kai musu dinkin dan har da Hafsat da Maimuna za akai dinkin.
Mami ta bata kudin dinkin isashe ta fita.
Zainab ta biya ta dauka sannan suka wuce Zoo road inda zasu kai dinkin.
Kayan ta bashi ta ce, zata turo masa da measurement din su ta waya.
Ta bashi kudin dinki suka wuce wajen da Yaa Buhari ya bada a bugo musu littafi da jaka da calender.
Har ya gama suka amsa suka nufi gida.
Ya Buhari sai Yamma ya dawo lokacin Asma'u bata gida.
Wanka yayi ya bawa Mami sakon ta sannan ya fice yai wajen Sabir.
Asma'u kuwa, suna dawowa ta kai Zainab gida tayo gida a gajiye.
Sabani suka samu da Yaa Buhari dan tana tafiya shi kuma ya nufi gidan su Zainab.
Asma'u na shiga taga motar Yaa Buhari cikin gida ta shiga da sauri tana kwala masa kira.
Mami dake falo ta ce,
"Oh Asma'u!"
Dariya Asma'u tayi ta ce,
"Mami ina Yaa Buhari nane?"
Mami ta ce,
"To ya fita kije ki wanka, kizo ga kaya can Momy ta aiko miki."
Mikewa Asma'u tayi ta ce
"A'ah Mami kayan zan fara gani tukkunna."
Tayi sama da sauri. Dakin ta ta shiga akwati ta gani babba ta bude.
Kaya ne masu kyau da tsada wanda Momy ta saba aiko mata dasu duk karshen wa.
Amman wannan kyan nasu yafi karfin wasa.
Kayan dai fitar biki ne, sai wata shadda da ta gani a dinke kala biyu da ta tata da ta Mami.
Da wani material shima iri daya amman dayan pink dayan kuma green.
Mai pink dine nata green din na Mmai.
Har da takalma da jaka duk da fashion dankunne da sarka.
Sosai taji dadin kayan duk da dinki nan da tayi.
Cikin akwatin ta mayar ta rufe ta zauna ta zuba tagumi,
Murmushi ta danyi ya ce,
"Allah sarki da yanzu muna tare da Momy. To Allah bai ba. Allah yasa haka ne mafi alheri."
Ta mike tana maida kwalar da ta fito mata.
Dady ne kuma ya fado mata. Wanka ta shiga tana yi tana zubar da hawaye.
Har ta gama ta fito, ta shirya sannan ta gaye gado.
Dan bata da walwalar da zata iya sauka kasa dan kar ta dagawa Mami hankali.
Tana kwancen nan take zancen zuci ta ce,
"Ni kam wai haka rayuwa ta xata kare kenan ban da walwala banda farin ciki. In kuwa har haka ne, zancen Sir Sabir zai faru na, zan iya kamuwa da wani ciwon bayan kuma ina da masoyan da zasu damu dani."
Juyi tayi ta rufe idon ta duk dan ta samu tayi bacci.
Asma'u sai karfe tara na dare ta mike, sallah tayi ta kara komawa gado ta cigaba da bacci.
Washe gari tana tashi ta shirya cikin Wata bakar abaya wacce akai mata aiki da golding zare.
Sandal ta saka golding da jaka golding tai rolling kanta da bakin mayafin rigar.
Ba karamin kyau tayi ba duk da ba kwalliya tayi ba. Sai kamshi take tashi.
Dakin Yaa Buhari ta shiga ta tada shi yana bacci, fita tayi ta sauka kasa.
Mami na kitchen ta karasa ta gaida ta, sannan tai mata sai ta dawo.
Fita tayi ta dauki motar ta ta nufi wajen aiki, tinda taje take kwance ta kasa komai.
Tana kwance Sir Sabir ya shigo. cikin shigar sa ya saka bakar suit yayi kyau da shi.
Fuskar sa sai annuri take fitar wa da wani murmushi mai sanyayya zuciyar wanda akai dan shi.
Jin shigowar sa yasa ta Mike da sauri, kallon sa ta yi, tai kasa da kai ta ce,
"Ina kwana?"
Zama yayi a gefen ta, yana kallon ta kafin ya amsa da
"Lafiya ya kike?"
"Lafiya lou!"
Ta bashi amsa.
Shiru sukai, Jin shirun yai yawa yasa, ta jingina kan ta a akan kujerar da take zaune.
Ido ta lumshe kamar me bacci. Kallon ta Sir Sabir yayi. Ta kara kyau da ita.
Ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya ce,
"Bakya jin dadi ne?"
Kai ta girgiza cikin sanyin jiki tai masa murmushi ta ce,
"Lafiya kalou nake, kawai garin ne?"
"Garin ne?"
ya tambaye ta.
Kai ta gyada masa, murmushi yayi ya ce,
"Taso mu fita to!"
Mikewa tayi dan baza ta iyai masa musu ba.
Fita sukai suka dinga zagaye gari shine kai ta can shine kai ta can.
Duk wajen da yasan zai ta ji nishadi ya dinga kai ta.
Har la'asar suna yawo a gari. Abinda yake buri ya samu.
Dan sosai ta sake har hira suke. Daga nan ya dauke hanyar yayi hanyar gidan su.
Sai da suka shiga sannna ta kalle shi ta ce,
"Ina ne nan?"
Ido ya kanne mata ya ce,
"Gidan mune!"
Kallon sa tayi tai kasa da kai. Fita yayi ya bude mata.
Fita tayi tabi bayan sa. Gida ne mai kyau gashi kato.
Ciki suka shiga da sallama. Mamah na zaune kan kujera, tana kallon suka shiga.
Suna shiga Mamah ta mike tana cewa,
"A'ah wa nake gani.kamar Asma'u!"
Ta kamo ta. Sabir ne ya ce,
"Ba kama ba ce ita ce."
A kan kujera ta zaunar da ita Asma'u ta zame ta zauna a kasa.
Gaishe da Mamah tayi cikin girmamawa da kunya.
Mamah ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar ta, yasu mami da Buhari.
Ta bata amsa. Mamah da kanta ta kama Asma'u suka nufi daining tana fadin
"ince daga aiki kike zo muje kici abinci "
Sabir kallo yabi su dashi, ba karamin burge shi sukai ba.
Bayan su yabi ya cewa,
"Mamah ta samu Asma'u yau ta manta dani."
Dariya Mamah tayi ta ce,
"Ai dole na kula da Asma'u na manta da kai."
Suka zauna. Abinci ta zubawa Asma'u. Shinkafa ce da taloya da miya da taji naman kaji, sai hadin kabeji da lemon kwakwa.
Kasa ci Asma'u tayk sai juya cokali da take, sai da Mami ta mike, sannan ta fara ci a hankali.
Sabir kam ido ya zuba mata yadda take cin abincin ma daban ne.
Jin ido akan ta yasa ta dago. Ido hudu sukai, Cokalin ta ajiye ta daina cin abunci.
Da ido da hannu ya tambaye ta
'lafiya'
Kai ta dauke kawai, murmushi yayi ya ce,
"To sorry Baby nah, kici na daina kallon ki"
Ya fada yana dauke ido daga kallon ta, abincin shi yaja gaban sa yana ci.
Itama ci ta cigaba dayi. Sai da suka gama sannan suka koma falo.
A gidan sukai sallah magariba sannan suka mike tanawa Mamah sallama.
Wani hadin turaruka Mamah ta bata, amsa Asma'u tayi tana godiya.
Gida suka tafi tare suka shiga ciki. Mami na ganin su ta ce,
"To kuna tare kenan!"
Kai Asma'u ta daga ta ce,
"Kinga kayan da Mamahn Sir Sabir ta bani."
Amsa Mami tayi ta duba tana godiya ta kalli Sabir ta ce,
"Angode Allah saka da alheri."
Murmushi kawai Sabir yayi ya zauna. Asma'u dake gefen Mami ta kalle ta, ta ce,
"Mami ina Yaa Buhari?"
Mami ta ce,
"Yana gun Zainab!"
Baki Asma'u ta tabe ta ce,
"Yaya ba a kara sauran kwana nawa ta koma gunsa gaba daya."
Murmushi Mami tayi ta ce,
"Asma'u daru."
Mikewa tayi tai sama tana cewa,
"Bari naje nai wanka. Nai sallah."
Tayi sama.
*MS Indabawa*
[1/18, 14:32] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
ASMA'U HUSNAH
BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*
🌐 *HAJWO* 🌐
*Hakuri da juriya Online writers*✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
*46-50*
Dedicated to my love mother. *Momy nah*
Really love u
An Ruwaito Cikin Littafin Ibn Sinni, Daga *Anas (ra)* Lallai *Manzon Allah(ﷺ)* Yace: "Shin 'Dayanku Zai Gajiya Ya Zamo Kamar Abi-Damdama?" Sai Sahabbai Sukace Wanene Abu-Damdama Ya Annabin Allah? Sai Yace: Ya Kasance Idan Ya Wayi Gari Yana Cewa: *{Allãhumma Inni Qad Wahabtu Nafsi Wa Irdi Laka, Falã Yashtumu Man Shatamahu, Wala Yazlimu Man Zalamahu, Wwala Yadribu Man Darabahu}*
*KARASHEN LBRN Munasha*