Showing 33001 words to 36000 words out of 92878 words
Chapter 12 - Asma'ul-Husnah Complet Book by Indabawa .txt
Ya Kasance Idan Rana Ta Fito Yana Cewa:_
*{ﺍﻟَﺤْﻤَﺪُ ﻟِﻠَّﻪ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﺟَﻠَّﻠَﻨَﺎ ﺍﻟْﻴَﻮْﻡَ ﻋَﺎﻓِﻴَﺘَﻪُ ، ﻭَﺟَﺎﺀَﻧَﺎ ﺑِﺎﻟﺸَّﻤْﺲِ ﻣِﻦْ ﻣَﻄْﻠَﻌِﻬَﺎ ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﺻْﺒَﺤْﺖُ ﺃَﺷْﻬَﺪُ ﻟَﻚَ ﺑِﻤَﺎ ﺷَﻬِﺪْﺗَﻪُ ﻋَﻠَﻰ ﻧَﻔْﺴِﻚَ ، ﻭَﺷَﻬِﺪَﺕْ ﺑِﻪِ ﻣَﻼﺋِﻜَﺘُﻚَ ﻭَﺣَﻤَﻠَﺔُ ﻋَﺮْﺷِﻚَ ﻭَﺟَﻤِﻴﻊُ ﺧَﻠْﻘِﻚَ ﺃَﻧَّﻪُ ﺃَﻧْﺖَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻻ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻ ﺃَﻧْﺖَ ﻗَﺎﺋِﻤًﺎ ﺑِﺎﻟْﻘِﺴْﻂِ ، ﻻ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻ ﺃَﻧْﺖَ ﺍﻟْﻌَﺰِﻳﺰُ ﺍﻟْﺤَﻜِﻴﻢُ ، ﺷَﻬَﺎﺩَﺗِﻲ ﻣَﻊَ ﺷَﻬَﺎﺩَﺓِ ﻣَﻼﺋِﻜَﺘِﻚَ ﻭَﺃُﻭﻟِﻲ ﺍﻟْﻌِﻠْﻢِ ﻭَﻣَﻦْ ﻟَﻢْ ﻳَﺸْﻬَﺪْ ﺑِﻤِﺜْﻞِ ﻣَﺎ ﺷَﻬِﺪْﺕُ ، ﻓَﺎﻛْﺘُﺐْ ﺷَﻬَﺎﺩَﺗِﻲ ﻣَﻜَﺎﻥَ ﺷَﻬَﺎﺩَﺗِﻪِ ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺃَﻧْﺖَ ﺍﻟﺴَّﻼﻡُ ﻭَﻣِﻨْﻚَ ﺍﻟﺴَّﻼﻡُ ﻭَﺇِﻟَﻴْﻚَ ﻳَﺮْﺟِﻊُ ﺍﻟﺴَّﻼﻡُ ، ﺃَﺳْﺄَﻟُﻚَ ﻳَﺎ ﺫَﺍ ﺍﻟْﺠَﻼﻝِ ﻭَﺍﻹِﻛْﺮَﺍﻡِ ﺃَﻥْ ﺗَﺴْﺘَﺠِﻴﺐَ ﻟَﻨَﺎ ﺩَﻋْﻮَﺗَﻨَﺎ ، ﻭَﺃَﻥْ ﺗُﻌْﻄِﻴﻨَﺎ ﺭَﻏْﺒَﺘَﻨَﺎ ، ﻭَﺃَﻥْ ﺗَﺰِﻳﺪَﻧَﺎ ﻓَﻮْﻕَ ﺭَﻏْﺒَﺘِﻨَﺎ ، ﻭَﺃَﻥْ ﺗُﻐْﻨِﻴﻨَﺎ ﻋَﻤَّﻦْ ﺃَﻏْﻨَﻴْﺘَﻪُ ﻋَﻨَّﺎ ﻣِﻦْ ﺧَﻠْﻘِﻚَ ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲ ﺩُﻧْﻴَﺎﻱَ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻣَﻌِﻴﺸَﺘِﻲ ، ﻭَﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲ ﺩِﻳﻨِﻲ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻫُﻮَ ﻋِﺼْﻤَﺔُ ﺃَﻣْﺮِﻱ ، ﻭَﺃَﺻْﻠِﺢْ ﻟِﻲ ﺁﺧِﺮَﺗِﻲ ﺍﻟَّﺘِﻲ ﻓِﻴﻬَﺎ ﻣُﻨْﻘَﻠَﺒِﻲ}*
_*"Alhamdulillahil Lazi Jallalanal Yauma Ãfiyatahu, Wa Jã'a Bish Shamsi, Min Ma'dli'aha, Allãhumma Asbahtu Ash'hadu Laka Bimã Shahidta Bihi Li Nafsika, Wa Shahidat Bihi Malã'ikatuka Wa Hamalatu Arshika Wa Jami'a Khalqika, Innaka Antallahu Lã'ilaha Illã Antal Qa'imu Bil Qisdi, Lã'ilãha Illã Antal Azizul Hakeem, Aktub Shahãdaty Ba'ada Shahãdati Malã'ikatika Wa Ulul Ilmi. Allãhumma Antass Salãm wa Minkas Salãm Wa Ilaikas Salãm, As'aluka Yã Zal-Jalãli Wal Ikrãm An Tastajiba Lanã Da'awatana, Wa An Tu'u'diyanã Ragbatanã, Wa An Tu'u'diyana Amman Agnaitahu Annã Min Khalqika. Allãhumma Aslihli Deeni Allazi Huwa Ismati Amri, Wa Aslihli Dunyayal Laty Feeha Ma'ashy, Wa Aslihly Ãkhiraty Allaty Ilaihã Munqalaby".¹*_
Asma'u kuwa tana komawa ciki ta hau daukar kayan da ta siyo tana nunawa Yaa Aslam.
Hiran suka sha sannan ta mike tayi alwala.
Aslam ganin karatun su Asma'u yazo gangara ya sa yayi takakiya yazo har kano.
Asma'u bata san da zuwan sa ba. Sai da ta dawo daga gidan su Zainab sannan ta ganshi.
Murna kamar me taji dadin ganin sa.
Daki ta shiga danyin wanka. Amman tindata fito vata sake ganin sa ba.
Sai da su Dady ta ganshi da ta sauko da akai sallah isha'i.
Sai kus kus taga suna yi da Dady wannan yasa ma batayi wajen su ba.
Tare duk suka ci abinci, suna gamawa tayi dakin ganin akwai maganar da suke da Dady.
Tana shiga dakintai wanka ta haye gado. faduwar gaba taji tana yi, da haka har bacci ya dauke ta.
Can cikin bacci taji karar wayar ta. Mikewa tayi tana salatin annabi. sannan ta dauko wayar.
Number Yaa Aslam ce. Dauka tayi cikin sanyin murya ta masu bacci.
"Baby na har kinyi bacci?"
Ya tambaye ta.
Kai ta gyda masa ta ce,
"Eh kai fa?"
Ya ce,
"Yanzu dai zan kwanta na ce bari naji ya Baby na take."
Murmushi tayi ta ce,
"Ina lafiya "
"To sai da safe ko?"
Kai ta gyada nasa ta ce,
"Allah tashe mu lafiya. "
Ta kashe wayar ta kwanta.
Washe gari kuwa tana gama abinda zatai ta kule a daki.
Mami ce ta shigo ta ce, Dady na neman ta.
Wata faduwar gaba ta ji. Haka ta mike ta dauki mayafin rigar dake jikin ta ta nufi falon Dady
A hanya ta hadu da Yaa Aslam shima zai je dakin.
Kallon sa tayi ta dauke kai sannan ta durkusa ta gaishe shi.
Amsawa yayi yana binta da wani kallo mai cike da tsantar kauna.
Kai ta kawar tai saurin shigewa dakin Dady
Bayan ta yabi yana murmushi wanda shi kadai yasan ma'anar sa.
Asma'u na shiga tayi gefen Dady, gaishe shi tayi sannan ta kalli Yaa Buhari dake dakin shima ta gaishe shi.
Mami ce ta shigo ta zauna. Gyaran murya Dady yayi sannan ya ce,
"Ayi salati ga Annabi (SAW)."
Bayan anyi akai addu'a ga wanda da suka riga mu gidan gaskiya sannan.
Ya kalli Asma'u ya ce,
" *Husnah* ba komai ne ya tara mu anan gun ba sai wani abun da nake son na sanar dake, abin nan kowa ya sani ke kadai ce kawai baki sani ba."
Shiru yayi yana kallon Asma'u wacce duk ta gama tsorata bata san me zai faru ba.
Dady ya ce,
"Kafin nan ina son na tambaye ki shin *Husnah* kina da wanda kike so ne?"
Faduwar gaban ta ce ta tsanan ta, wani gumi ya karyo mata. A gaskiya tana jin kunyar Dady dan ji take baza ta iya ce masa akwai wanda take so ba.
Shiru tayi Dady ya kuma tambayar ta tayi shiru sai da ya tambaye ta sau uku bata bashi amsa ba sanna ya ce,
"Wannan ya nuna min baki da wanda kike so kenan."
Da sauri ta dago kai ta kalli Dady sai kuma ta kalli Yaa Aslam da ya zuba mata ido.
Kasa tayi da kanta. Murmushi Dady yayi ya ce,
"To Alhamdulilah! Akwai wani alkawari da na dauka tin kina shekara shida. Ba wani alkawari bane sai na bawa Aslam auren ki,"
Da sauri Asma'u ta dago tana kallon Ya Aslam.
Murmushi ya sakar mata ya kanne mata ido daya. Dady ya ce
"Aslam shi ya hana a fada miki ya ce, sai ya nemi soyayar ki gashi kuma ba tambaye ki ba Wanda kike so kinyi shiru."
Fuska Amsa'u ta rufe da tafin hannu. Dady ya kalli Aslam ya ce,
'To kai har yanzu baka nemo soyayyar taka ba dan haka ka sake zage dantse."
Dariya dakin sukai gaba daya. Dady ne ya kara yin gyaran murya ya ce,
"To yanzu Aslam yazo akan batun auren ku. Ya ce, so yake da kinga gama karatu ayi komai a gama, dan haka na kira ki na shaida miki an bada ke ga Dan uwan ki Aslam."
Kai tayi kasa dashi tana jin wani sanyi kamar zai me murnar ta taki ta rufu. Kamar yadda Aslam ma bakin sa ya kasa rufuwa.
Dady ya ce
"dan haka muna addu'a Allah ya tabbatar da alherin sa a cikin wannan al amarin."
Dakin gaba daya suka amsa da
"Ameen!"
Dady ya ce,
"Yau nafi kowa farin ciki da na sauke wannan nauyin a kai na da kaina. Allah yasa Asma'u ta zama matar ka ta sunna."
Suka kara amsawa da
"Ameen!"
Dady ya ce,
"Zan fi kowa farin ciki ko a yau na mutu nasan *Husnah* ba zatai maraici mai yawa ba dan na tabbata Aslam da Buhari zasu kula dake iya kar iya yawar su. Ina fatan *Husnah* ki zama mace ta gari ga mijin ki. Aslam yana son ki so tsakani da Allah nasan duk wanda zai zo ya so ki bai zai kai kamar yadda Aslam ke son ki ba. To Alhamdulilah kema kina son nasa naji dadi. Allah yai muku albarma."
"Ameen!"
duk suka amsa
Dady ya ce,
"Shikenan kuje daman kiran kenan."
Asma'u ce ta mike ta fice duk kunya ta kamata.
Dariya Dady yayi ya ce,
" *Husnah* kenan."
Mikewa Aslam yayi shima yayi dakin sa. Waya ya bugawa Dadyn sa yana cewa ya shirya, auren sa ya kusa fa.
Dariya yabawa Dadyn sa Dadyn sa ya ce
"Allah tabbatar da alheri,"
"Ameen!"
Ya amsa
Tin lokacin Asma'u ta kasa fitowa falo sai bayan la'asar da taji gidan shiru shine ta mike ta shiga wanka.
Fitowa tayi ta shirya cikin bakin dogon siket sai wata riga mai dogon hannu Ash kala wacce akai mata ado da bakaken stone. Hula kawai ta saka ta fita daga dakin.
Mami ta gani zaune a falo. gefen ta ta zauna ta ce,
"Mami sannu da gida"
"Yauwah!"
Mami ta amsa. ta mike ta fice.
Garden ta nufa ta zauna a inda suka saba zama ita da Yaa Aslam.
Ido ta lumshe kamar me bacci ta tafi can duniyar tunani.
Aslam kuwa tin da ya dawo daga massalaci ya nufi garden din shima.
Da farko zama yayi sai da yaga ba kowa sannan ya mike yana zagaye garden din. Iska mai dadi tare lumlume na ratsa sa.
Yanzu haka gajiya yayi, ya juyo ya dawo dan ya zauna.
Kamar a mafarki ya hangonta kwance ta lumshe idon ta.
Wani dadi yaji ya lulube shi. A hankali ya karaso inda take.
Zama yayi a kujerar dake gefen ta sannan ya hura mata iska a kunnen ta.
Ido ta bude da sauri Yaa Aslam ta gani zaune a gefen ta sai murmushi yake sakar mata.
Mikewa tayi zaune ta kasa dauke idon ta daga kallon sa.
Murmushi yayi ya hure mata idanun ta da iskar bakin sa.
Murmushi tayi ta dauke kanta daga kallon sa cikin jin kunyar sa.
Ya ce,
"Baby ya kamata muje naga asibitin ki,"
"To muje."
Ta fada tana mikewa.
Kamo hannu ta yayi ya ce,
"Ina kuma zaki?"
"Mami zan fadawa."
Sakar ta yayi ya ce,
"Ina jiran ki a mota."
Cikin gida ta shiga ta dauki after dress sannanta sanar da Mami inda zasu.
Adawo lafiya Mami tai musu suka fita.
A hanya ba wanda yace da dan uwan sa kala.
Ita Asma'u sai yanzu take jin kunyar Yaa Aslam dan yanzun ta tabbatar da gaske dai shi zata aura.
Shi kuma ya rasa me ya hanashi jan ta da hira sai da lokaci kadan kadan ya kalle ta ko ya kamo hannun ta ya murza.
Da haka har suka karasa asibitin. Katon Asibiti wanda Dady yasa akai mata ginin zamani mai kyau.
Komai na cikin asibiti mai kyau da tsada ne.
Har office din ta sai da suka shiga.
Ya Aslam sai yaba wajen yake. Duk da nashi asibitin yafi nata girma amman tsarin nata ya burge shi sosai.
Sai da suka gama kalla ya ce,
"Baby na kince dai in munyi aure yau muna kano gobe muna Abuja ko?"
Kallon sa tayi dan bata gane maganar tasa ba. Ya ce,
"Eh man ai dole muna zuwa duba asibitin mu ko?"
Murmushi tayi ta daga masa kai,
Gida suka koma ana kiran sallah magariba.
Asma'u ce kawai ta shiga ciki shi kuma ya tafi massalaci.
*Muje zuwa*
*INDABAWA*
[1/18, 14:20] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*
Dedicated to *My Lovelly Momy*
*121-125*
An Ruwaito Daga *Abdullahi bn Mas'ud (ra)* Ya Kasance Idan Ya Samu Labarin Fitowar Rana Yana Cewa:_
*{ﺍﻟْﺤَﻤْﺪُ ﻟِﻠَّﻪِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻭَﻫَﺐَ ﻟَﻨَﺎ ﻫَﺬَﺍ ﺍﻟْﻴَﻮْﻡَ ، ﻭَﺃَﻗَﺎﻟَﻨﺎ ﻓِﻴﻪِ ﻋَﺜَﺮَﺍﺗِﻨَﺎ}*
_*"Alhamdulillahil Lazi Wahaba Lanã Hazal Yauma Wa Aqãlanã Min Atharãtinã²".*_
Yana dawo daga massalaci ya kira ta awaya kan ta same shi a garden.
Mikewa tayi ta fita ta kofar kitchen ta shiga yana zaune akan kujera ta karasa gun sa.
Zama tayi ba tare da ta ce kala ba.
Kallon ta yayi yai murmushi ya ce,
"Baby na ya kika ji batun Dady dazu."
Murmushi tayi ta ce,
"Me Dadyn ya ce?"
Murmushi yayi ya ce,
"Wallahi baza ki kunna ni ba. Kinji komai da ya fada yanzu kin kara tabbatar da irin son da nake miki."
Kai ta gyada ta ce,
"Daman can na yadda da son da kake min."
Murmushi yayi ya ce,
"Alhamdulilah nagodewa Allah Zuciya ta ke kadai takewa na amince ki rike ta har abada."
"Ya Aslam kenan!"
ta fada.
Yace,
"Eh! Man kada ki taba zaton zan yaudare ki"
Tace,
"Nasan baza ka taba bama."
Yace,
"Yauwah Love."
Sukai murmushi a tare, Asma'u ta ce,
"Nima Zuciya ta kai kadai take yabawa dan tasan ka riketa ba da yaudara ba."
"Da gaske."
"Eh!" Ta fada tana dage masa gira.
ya ce,
"So hadi na Allah ne Asma'u, Zuciyata ke kadai ta nuna min. Na riga na sanarwa da Momy da Dady da Dady da Mami, da duk wanda muke mu'amala dasu in babu ke sai dai na rasa rayuwa ta."
Ido ta zaro,
"Su Momy,"
Yace,
"Eh! Mana ai kowa yasan son da nake miki in aka raba mu zan iya rasa rayuwa ta."
Murmushi tayi ta ce,
"Allah ma ya kiyaye."
Ya ce,
"Ameen!"
Tace,
"Tin da Dady ya bayyana, min son ka akan kai ne, mijina baka ji yadda naji ba. Saboda Allah yasa ga wanda nake so aka hada kaga yafi dadi ko."
Ya ce,
"Shiyasa nacewa Dady kar a fada miki sai na kama bakin zaren!"
Murmushi tayi, ta ce,
"Wane zaren kuma"
Ido ya kashe mata.
"Zuciyar ki man. Hmmm *Husnah* baki san yadda na riki soyayyar ki a raina ba. Ta zama abin yi dare da rana. Soyayyar daraja ne da ita. Samun irin taki shine burin ko wane me hankali. Bana son na taba yin nesa dake. Kin shiga zuciya kinyo kafuwa. Ni dake babu rabuwa koman dadewa."
Kallon sa ta tsaya yi.
"Kai ma kasan kaine zabin rai na. Zuciya ta, ta adana soyayyar ka ba wanda ze maye gurbin ta. Sa'a ni na sama tinda na samu gwarzon masoyi kamar ka. Kai ka ke sani addu'ar neman miji na gari, kuma nasan Allah ya amsa min da ya aikon da kai a matsayin masoyi wanda nake fatan shine miji na."
"Gaskiya ne. Dace da masoyi shine ribar soyayya. Nasan sabon da mukayi ni dake sai dai a kira mu tagwaye, ko yaushe in na tina ki nakanyi murmushi da jin farin ciki a cikin zuciya ta."
Murmushi tayi, ta sauke ajiyar zuciya me karfin.
Ya ce,
"Lafiya?"
Ta ce,
"Ya Aslam in na tuna da rabuwa ne sai naji zuciya ta tayi min rauni"
Kallon ta yayi ya ce,
"Haba *Husnah ba mun kashe wannan maganar ba ne."
Kai ta gyada masa ta ce,
"Eh!"
Ya danyi murmushi shima. Ya ce,
"To Bazamu rabu ba sai dai mutuwa itama insha Allahu tare zata dauke mu."
Kai ta langwabar tace,
"Allah yasa!"
Ya amsa da
"Ameen."
Dan shiri sukai sai kuma yace,
"Yauwah kinga tin yanzu sai mu fara tsara yadda bikin mu zai kasance ko?"
Murmushi Asma'u tayi tace,
"Kai Yaa Aslam tin yanzuu."
Yace,
"Eh man. please My love, let's talk about ourselves, our future My dear, sbd managers sun ce, he who failed to plan he plan to fail."
Kallon ta ya yi sannan ya cigaba da cewa,
'My love, ni yanxu bani da wata agenda da ta wuce naga mun gina rayuwa me kyau ni da ke my dear.
My yanxu misali nan da yaushe ya kamata ace mun fara shirin auren my?"
Asma'u ta dan ja numfashi ta ce,
"Ni ban sani ba."
Dariya yayi ya ce,
"Toh Ashe kuwa abin xai xo muga bamu tanadi komai ba my.
Indai haka xakina cewa my."
Asma'u tayi murmushi ta yi kasa da kai ta ce,
"Haba To ni me zance?"
Dariya Aslam ya karayi ya ce,
"ke kuwa kike da abinda xaki ce, My just ra'ayin ki xaki fada da abinda kike ganin ya dace musa acikin tsari Wanda may be ni hankali Na be kawo kai ba."
Asma'u ta ce,
"kamar me?"
Ya ce,
"Kamar ace a ra'ayin ki, May be akwai wani event da kike ganin kina bukata ayi."
Kan Asma'u a kasa ta ce,
"fadin ra'ayin ka naji."
Ya ce,
"My ina so if possible ace ran Friday xa'a daura mana aure after mosque."
Murmushi Asma'u tayi dan itama tana sha'awar daurin auren ranar juma'a.
Kai ta daga ta ce,
"Yayi kyau nima ina son haka."
"Yauwah koke fa. Sai batun sauran event me da me kike ganin za'ayi."
Dariya tayi ta ce,
"Duk yadda My yake so haka za'ayi."
Numfashi yaja ya ce,
"Kinsan sauran Event duk naku ne, daurin aure da dinner sune kadai namu."
"To ni dai nasan Mami zata yi yini da kamu daga haka bansan me kuma ba."
Murmushi yayi ya ce,
"Shigar da zamuyi kuma fa?"
"Wayoo Ya Aslam ni bansan yadda za ayi ba."
Ta fada yana turo baki.
Aslam ya yi dariya ya ce,
"Wallahi *Husnah* zamu bata, sai kace bakya son maganar auren tamu. Oya fada min wane kalar dressing kike so muyi ran dinner."
Baki ta turo tana kun kuni. Dariya yayi ya ce,
"Eh sai kin fada. Kaji yarinya daga an mata maganar aure ta maidani sirikin ta. Maza fada min ko na fadawa Dady ayi auren ending month din nan."
Dariya tayi ta ce,
"Ayi man."
"Haka kika ce?"
Kai ta girgiza ta ce,
"A'ah!"
Ya ce,
"To fada min."
Shiru tayi sannan ta dago ta ce,
"Ran Dinner ina son dressing din gloding kala. Ran Daurin aure kuma farar shadda zaka sa ko blue?"
Kallon ta yayi ya ce,
"Ke nake son ki zabar min. Amman gani nake fara zata fi saboda ranar farin ciki ce kamar yadda zuciya ta take fara haka nake komai nawa ya zama fari."
Murmushi tayi ta ce,
"To kaga ka zabi abin ka."
"Haka ne, sai na ranar yini."
Dariya tayi ta ce,
"Duk kalar da ka zaba."
"Ok ranar zan saka blue din shadda dan haka kema ki saka something da zai hau dashi."
Kai ta daga ya ce,
"Gobe zan sa Momy ta tanadar mana kayan."
Kallon sa tayi tana dariya. Ta ce,
"Ya Aslam duk saurin nan fa."
"Kedai bari wallahi ji nake kamar na matso da kwanan nan kusa "
Dariya tayi ta ce,
"In kana wannan zumudin sai ina jin tsoro kar wani abu ya faru."
"Kefa haka kike. Dan Allah ki daina sa haka a ranki za'ayi komai lafiya a gama lafiya da izinin mazon Allah (SAW)"
"Allah yasa to!"
"Ameen!"
Kallon ta yayi yai.murmushi.
"Lafiya?"
Ta tambaye shi. Murmushi ya karayi ya ce,
"Wai ya zanji ranar da My ta zama mallaki na."
Kasa tayi da kai. Ya ce,
" *Husnah* duk ranar da kika zama tawa wato mallaki na sai nayi azumi guda bakwai na godiya ga Allah da ya mallaka min ke."
Dariya tayi. Ya ce,
"Ranar zan yi abinda ban taba sanin me zan yi ba har yanzu amman ranar zata zama rana mafi soyuwa a rayuwa ta."
"Yaa Aslam kenan!"
Murmushi yayi ya girgiza kai ya ce,
" *Husnah* kenan amman dai baza kizo kina min kuka ba ko? Tinda gaki a gun life partner din ki."
Murmushi kawai tayi. Aslam ya ce,
"Wannan murmushin naki make me go crazy."
"Allah ko Yaa Aslam kana kashen bakin magana ne."
Murmushi yayi ya ce,
"Plz don't u ever forget I love u. (Dan Allah kada ki taba mantawa ina son ki.)
Plz promise to never leave me even if there are thousand and one reason to. (Dan Allah ki min alkawarin baza ki taba bari na ba ko da akwai dubun nan dalilai da huja da zaki)
Plz promise to stay with me no matter how hard or difficult the relationship might be. (Dan Allah kimin alkawarin zaki kasance dani duk rintsin yanayin da zamu tsinci kan mu a ciki.)
Do u konw why am saying all this? (kinsan saboda me nake fadan duk wannan)
Because I never ever want to loose u My,
If I loose u, I have lost a grate part of me (saboda bana son na taba rasa kine tawan, in na rasa ki na rasa wani babban bangare daga gareni.)
Idan na rasa ki
Nayi mummuna rashi My
To me u are the perfect wife and I just want to make u mine. (A waje na, ke ce cikakiyar mata. Kuma kawai ina son na mai dake tawa.)"
Kasa tayi da kanta. Mikewa yayi ya dawo gaban ta. Kan ta ya dago idon ta a lumshe.
"Dan Allah ki amshi alkawari na."
Dagowa tayi ta ce,
"Yaa Aslam komai naka ina son ya kasance gaskiya dan nima shine duk burika na. Ina addu'a Allah yasa duk abinda ka ambata ya zama gaskiya da nafi ko wacce mace farin ciki da samun soyayar gaskiya."
"Nagode *Husnah* Nagode Allah mallaka min ke."
"Ameen!"
Ta amsa. Mikewa tayi ta ce,
"Mu shiga ciki ko?"
Kai ya gyada mata yabi bayan ta.
*INDABAWA*
[1/18, 14:20] Maryam S Indabawa🥰: *LABARIN RAYUWAR*
*Asma'u Husnah*
Na *Maryam S Indabawa*
*Mans*
🌐 *HAJOW* 🌐
*Hakuri da Juriya Online writers*
*Gidan Amanci da albarka*
Dedicated to *My Lovelly Momy*
*126-130*
An Kar6o Daga *Abi-Hurairah (ra)* Yace: “ *Manzon Allah(ﷺ)* Ya Hana Mutum Riqe Kwankwasonsa a Cikin Sallah”. *(Bukhari da Muslim)* a Lafazin Muslim: *“Shine Mmutum Ya Sanya Hannunsa a