Showing 45001 words to 48000 words out of 152002 words
Chapter 16 - AMATULMALEEK COMPLETED BY Mamuhugee.txt
din ba Kuma akan mutuncinta zai iya tsaye mata koina,
Amma Kuma a yanzu data zama mallakin ASH TALBA din gaba Daya kusan yamafi Jin nutsuwar zuciya ga yar uwar tasa Dan yanzu itace macen datake saman kowacce mace a TALBAs bayan Madame abeeda tinda sune matan shugaba.
Zazzabin Daya rufeta ne ya Saka Abdul din kamata ta kwanta kan gadon da tin anan sun San anfara samun banbanci Dan kuwa dakin shine matsayin dakin madame Abeeda duk da Basu tare gidan ba bama ta taba zuwa ba Amma dai shine matsayin dakinta Amma yanzu matar me gidan Daya ta shiga.
Fitowa yayi daki bayan rufeta da abin rufar Dake gadon me tsananin laushi ya nufi dakin dasu maamah suke Suma daga maamah har Husnah din zazzabi kowa yakeyi hakama Faisal tini nasa zazzabin yayi karfi yabar Mansion din ya tafi masaukinsa daga can jirgi zaibi a da safe ya koma Abuja.
ASH tinda yagamo sallan magrib din Shima shigewa yayi bangarensa tareda kashe wayoyinsa ya tsaya a dan qaramin closet dakin kayansa ya zare kayan jikinsa a natse tareda janyo towel Daya daga cikin towels Dake Jere a bangare daya kusan guda ashirin duk farare kowannen kalar farinsa da taushinsa zaisa ka bambamtasa da normal towels daka sani masu qarfi.
Toilet ya nufa ya shige hannunsa Daya akan towel din qugunsa Da Bai daure da kyau ba.
Wanka yayo ya fito toilet din gaba Daya ya cike da qamshin Aesop liquid soap daya biyo har dakin sbd jikinsa Dake fidda qamshin fatar jikinsa kuwa kaman wadda Bata taba shiga Rana ba fresh.
Baya Wani shafe shafe bayan body oil na Aesop din me shegiyar tsada sai body perfumes kawai.
Abinci lafiyayye da drinks dasu tea harma da snacks masu zafi aka jere babban dining table din Dake babban dakin cin abincinsu tareda sake tsaftace gurin kaman baa jima da sake tsafatace koina n gidanba.
Abdulhameed ne kawai yazo Palo ya tsaya jiran yanda zai sanar da ASH din halinda duka su Amatu suke ciki.
Masu aiki tini suka bace bat daga cikin ainihin palon cikin gidan sbd sanin kowane lokaci ASH zai iya fitowa.
Babu jimawa sai ga qamshinsa ya fara doso palon Abdul na Jin qamshin ya miqe tsaya Yana Dan saita kansa tareda nutsuwa.
Cikin wata tsadaddiyar silk jallabiyan da basai anfadaba kana gani kasan jallabiya ce ba muna jallabiya ba,
ASH TALBA matashin me kudin da yanzu ne yake kokarin shiga dattijantakarsa sbd auren gata na wuri da Akai masa hakama 'dansa Haydar kana ganinsa kasan shine ya haifesa sbd kyansu ya banbanta Dana Husnah wadda nata mahaifin ta dauko itama Zak a kamanni Amma dayake Yana kama da ASH sai itama take diban kamannin da ASH,
Zuba masa idanuwa Abdul yayi Yana Yaba nutsatsiyar halittar da Allah yayi a gurin,
Mutumin da Babu Wanda zai kallesa baiyi fatan inama shine shi din,
Mutumin da Babu macen da bazata kallesa ba taji Ina Allah zai bata matsayin da zai kalleta da wata siffar sbd shedan da duniya tai masa na mijin mace Daya ne madame Abeeda Talba wadda bayan tafiyarta Allah ne kadai yasan matan da aka ringa basa 'yayan manya da manyan matan Amma Yana dakatarwa sbd baitaba kallan wata macen da sunan macen so ko aure ba bayan matarsa,
Ita kadai ta ishesa a rayuwarsa yake gani hakama duk wuya duk rintse bazai taba iya kulawa ko kallan mace ko wace iri bace da sunan mace matiqar Abeedansa tana raye ba mutuwa tayiba Wanda Baya fatan ta mutu ko ahakan datake kwance yana fatan Allah ya bar masa ita karta tafi tabarsa.
Isowarsa tsakiyar palon yasaka shi dago fararen idanuwansa ya zuba akan Abdul din Wanda yayi qasa da nasa idanuwan Yana Bude Baki cikin girmamawa yayi masa barka da fitowa.
Amsawa yayi a natse Yana nufar dining room Abdul din ya biyo bayansa cikin nutsuwa yace
"Gaba dayansu maamah da anty Husnah basuda lafiya harma da AmatulMaleek,Kuma sosai"
Dago Idanuwansa dasuka Saka Abdul Dan shin shiru yayi ya Kalli hanyar dakunan nasu ya Bude Baki yace
"Ba damuwa likita zaizo ya dubasu yanzu kafin mu tafi da safe sun warware Inshallah"
Ok Abdul yace Yana kokarin juyawa ASH din ya basa izinin zama yaci abinci shikuma juyawa yayi yakoma Dan kira ya Bada umarnin a Aiko musu kwararran likita yanzu a Talba mansion.
##MAMUH#
for more pages joining vip or follow me @Mamuhgee arewabooks
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
atπ
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
27
*Free class! π₯*
*Shin ko kun san zaku iya samun jari online ta hanyar sayar da kayan da ba naku ba ana biyanku commission?*
Idan kuna so ku samu ilimin kasuwanci online ta yadda zaku daura business dinmu gaban mutane da yawa fiye da yadda kuke dashi yanzu...
*Inada Free class wannan satin dan haka ku shiga link din dake Ζasa*
πππ
https://wa.link/1gss1o
****************
Lokacinda likita yazo dubasu AmatulMaleek aka fara dubawa kafin su Husnah da maamah hakama dole aka Aiko da nurse biyu suka kula dasu har safe Daya Amatu dayar Kuma Husnah da Maamah.
Kafin safe ba laifi kowannensu ya samu kulawa me kyau sun samu kansu da sauki hakama Husnah ta riga su warwarewa ta fito da safe taci abinci tareda Dad dinta da Abdul a dining Wanda har lokacin Babu wata fuska ko damar maganar auren data Gani daga garesa Wanda shi bayajin a gurinsa akwai Wanda zaiba damar yi masa maganar auren ko tini akan maganar auren.
AmatulMaleek ma ankawo mata breakfast lafiyayye a dakin tareda jeresu kaman tareda wasu zataci.
Nurse dinta ce ta takurata tareda lallabata taci abincin dole
Tana gama ci taqara Bata magani Ta miqe ta shiga toilet wanka sbd Abdul yazo ya sanar dasu karfe 11 na safen zasu wuce.
Ko data fito wanka ankawo mata kayan sakawa dogayen Egypt abayas masu tsada sosai Huda uku an ajiye mata.
Kallan kayan tayi tareda dauke idanuwanta ahankali tanajin qarfin jikinta na sake tafiya Kuma Batada zabin Daya wuce sakasu tinda ko alamar an taho da kayansu Bata ganiba.
Black daga cikinsu ta Saka tareda mayafinta ko zama bataiba daga Saka kayan ta fito ta nufi dakinsu maamah lokacin Suma sun shirya ta gaida maamah a sanyaye cikin nutsuwa.
Maamah Bata iya dagowa ta kalletaba ta amsa gaisuwar,
Husnah ta kalla Taga yanda ta kafeta da idanuwa tana kallanta tareda fadawa tinani Dan haka sai batama tsaya yi mata magana ba ta fice sbd ganin yanayin maamah data qi ko kallanta.
Ta sani wannan auren duk qin da kowa zai masa qiyayyar da maamah zatai masa daban ce,
Idan kowa ya qi auren da sauki nata qin babbane,
To Amma ita meye laifinta tinda batason auren ita,Bazata iya auren Dad din Haydar ba,mijin mummy Abeeda,tayaya ma maamah zatayi tinanin ita Koda wasa zata iya son wannan auren.
Shigowar Abdul ne ya Saka Amatu dagowa ta kallesa harya iso ya zauna kan kujera Yana kallanta cikin kulawa yace
"Yaya jikin?
Zuba masa idanuwanta da suka fada cikin dare Daya tayi kafin ta amsa masa da taji sauki cikin sanyi.
Ganin yanayinta ya sanyashi tambayarta ko taje gurin maamah ne?
Sake kallansa tayi tareda gyada Kai ahankali zatai magana ya katseta da cewa
"Kowa maamah din Bata iya kalla bake kadai bace,
Bazata iya karban aurenki ba ayanzu sai zuwa gaba ahankali sbd wannan auren shock of her life ne aka Bata,dole zataji damuwa duba da yanda take da mummy Abeeda and shi kansa Dad dinsu Haydar din.
Fadan sunan Haydar dayayi shine ya sake narkar da zuciyarta tinawa da idan yaji wannan zancen kowane hali zai iya shiga Amma Kuma dole zatayi aure yaji Amma dai Bada Dad dinsaba,
Bazata taba so ko kaunar haydar yaji Dad dinsa ne ta zama matarsa ba,ko bayan Haydar dangin mummy Abeeda zasu iya qullatan maamah,
Ita kanta mummy Abeedan Koda Bata tareda su ahakan kaman baayi mata adalci bane.
Nasihar kwantar da hankali subi komai na rayuwa a sannu suga inda zata kaisu Abdul ya ringa wa Amatun tareda tinatar da ita wannan auren bawai shi kansa Dad din yana raayi ko buqatan auren bane,kawai yayi ne sbd biyan maamah alkhairinta garesa,yayi ne Dan kare mata mutuncin 'yarta da akaso ketawa acikin gidansa,
Yayisa ne Dan karbo ki daga masifaffen auren dasu kawu sukaso yi Miki hakama yayi ne sbd Baki sunan matarsa ta yanda Babu Wanda zai Kuma kallanki ya Tina Wani abu hakama Babu Wanda ya Isa ya kalleki da wata manufar bayan ta girmamawa.
Ki kwantar da hankalinki ciki gaba da rayuwarki cikin nutsuwa da Kwanciyar hankali kaman yanda kika Saba Babu abinda zai canja a rayuwar ki bayan wannan auren.
Knocking kofar dakin Akai Abdul ya miqe yaje ya Bude.
Cook din gidan ne ya sanar dashi su fito lokacin tafiyansu yayi.
Abdulhameed ne yafara fitowa hannunsa riqe Dana AmatulMaleek din sbd tsananin sanyin jiki da damuwar datake ciki tana buqatan makusancinta a tareda ita.
Maamah da Husnah mota Daya suka shiga Abdul da Amatu suka shiga Daya Saida sukai zaman minti biyu a mota kafin ASH TALBA ya fito sanye cikin Wani tsadadden navy blue Switzerland cashmere Daya fitarda tsadaddiyar rayuwar Dayake cikinta,
Hasken fatarsa kawai AmatulMaleek ta iya hangowa lokacinda yake takowa cikin nutsuwa da kamewansa ta sauke Kai tana Jin jikinta na sake sanyi auren na dawowa mata cikin Kai da Jin Babu abinda takeso a rayuwarta daidai wannan gabar kaman rabuwar wannan auren.
Husnah kuwa Dad din nata ta zubawa idanuwanta ko kyaftawa Batayi,
A Koda yaushe Dad din ta komai nasa daban ne,
Tin daga kan iyayen mutane data Saba gani,masu kudi da masu kudin kudi sosai,harma samari da matasan da duka take Gani Babu kaman Dad dinta,
Dad dinta tamkar tauraro ne Gani daga nesa ga mata harma da mazan,
Dad dinta class/ajinsa dinsa daban ne,
Kwarjinsa da haibansa na musamman ne,
Kyansa da kyan jikinsa abin kallo ne
Mummy dinta ce kawai macen rayuwarsa,
Ita kadai yake kalla amatsayin macen data Kai,
Ita kadai ce a zuciyarsa
Tayaya Rana tsaka AmatulMaleek zata zama yarinyar da mutane zasu kira matar ASH TALBA bayan mahaifiyarta ce kawai me wannan sunan?
Tayaya AmatulMaleek zata samu girmamawa da mutuntawar da mum dinta ce kawai ta cancanta?
Tayaya AmatulMaleek ta samu mijin da ita tasan duk Wanda zata aura bazai Kaisa ba,
Faisal takeso a rayuwarta Kuma shi takeson aura to Amma Kuma Faisal Tako Ina be kama hanyar Dad dinta ba,meyesa AmatulMaleek zata fita ta wanna bangaren bayan itace a Baya take cire kayan sawarta tana Bata,
Jin tayi gaba Daya zuciyarta ta tsani wanna auren itama,
Sam Bata aminta dashi ba,
Kaman yanda Taga maamah Bata aminta ba Kuma batada niyar aminta dashi har abada yasata Jin zata tsaya a tareda Maamah bazasu taba aminta da wannan auren ba da Babu komai acikinsa bayan rashin kamata.
Hawaye taji suna ciko idanuwanta ta hadiye Wanda maamah ta lura da Hakan takuma San hawayen Menene tinda itama ASH TALBA din tayiwa kallo daya ta sauke idanuwanta sbd Jin abu biyu na danne kirjinta,
Na farko qin auren,.na biyu mijin AmatulMaleek ne tinda an daura kafin a warware batajin zata iya ko kallansa yanda ya kamata yanzu.
ASH da Babu abinda yake ransa gameda auren ko wainda ke tinanin auren Yana isowa aka bude masa mota ya shige aka rufe
take aka tada motocin suka nufi gate da aka wangare musu suka fice tareda Hawa titi sai airport.
Ko isarsu airport dayake Babu Wani Bata time Akai abinda zaayi suka shige jirgi.
*********
Mum Aishi da Naufal da Shima tini ya dawo bayan tashin hankali Babu abinda suke cikinsa,
Tsoro da fargaban Kiran ASH takeyi taji ko andaurawa Naufal din aure da Amatun ne,
Hakama su Uncles din Naufal din Babu Wanda Bata kira numbernsa ba Bata shiga.
Shi kansa Naufal din yayita kiransu Amma Bata zuwa gashi shi harga Allah so yake yaji ance ai andaura masa Amatun shikenan ta zama tasa da hujja zaiyi zaman aure da ita Amma Bai bari mum tasan abinda yake ransa ba Dan haka ya bayyanarda damuwarsa ta qin son auren sosai.
Har dare yayi Babu bayanin komai haka suka kwana Babu kowanne zance Saida safe suna tashi Naufal ne yaci gaba da sake Kiransu cikin saa numbern Uncle Sulaiman dinsa ta shiga.
Ringing takeyi harta katse baa daga ba ya sake Saka Kiran harya Yanke baa dagaba.
Mum ce ta sake Saka Kiran da tata wayar Kiran farko ya dauka ransa a bace Dan Daman fushi sukeyi da Naufal.
Yana dauka mum Aisha daqyar ta iya tsayawa suka gaisa ta musu ya hanya tana dorawa da cewa
"Tin juya kuka baro kauyen ko?
Kun koma ne?ko Kuna yolan haryanxu?
Ya lamarin ya kasance?
An daurawa Naufal yarinyar kuwa?
Allah dai yasa baa daura ba sbd wlh har cikin Raina auren a yanzu Bai kwanta mun ba,Kuma dai daura musu auren batareda suna son juna ba bashine maslahaba......
Katseta uncle Sulaiman yayi da cewa
"Eh aure batareda suna son juna ba bashine maslahaba Amma ai yasan batasonsa Baya Sonta din yaje zai haiqe musu 'ya,sai yanzu da zaayi musu aure yayi abinda yaga Dama da matar bisa ga Sunna shine rashin maslaha a gareki ko Aisha sbd son zuciya,
Yanzu duk wannan abin da yakeyi ke har kina iya ganin rashin maslaha a daura masa aure?
Kinfi shaawan yaje yayita lalata yayan mutane Yana zubarwa Wanda kuke karkashin alfarmarsa da mutunci,
To maslaha da rashin maslaha dai andaurawa yarinyar aure.....
Wani mummunan faduwa gaban mum Aisha yayi zufa na feso mata Dan kuwa qiyayyarta da auren Amatu ga Naufal dinta daga qasan zuciyarta ne,
Ace Danta guda Daya a duniya ya rasa macen da zata zama matarsa sai 'yar me dafa mata abinci tana ci.
Naufal dayake Jin duk zancen na uncle Sulaiman Jin yayi zuciyoyinsa ta cike da Wani farin ciki da sanyi Dan kuwa yanzu da ya zama mijin AmatulMaleek din ko mum zata raba auren kaman yanda tayi rantsuwa wlh kafin ya saketa Saiya kwana Yana dirzan sadakinsa da aka biya kafin ya saketan da safe shi son yake ma yaji yaushe Amatun zaa dawo da ita.
Mum dinsa kaman tasan tambayar datake ransa ta Bude Baki zufanta na qaruwa tace
"To yaushe Amatun zata dawo idan har an daura auren ai dole ta dawo ko?
Dawowanta Kam tana hanya tareda Wanda take mallakinsa ayanzu,ma'ana mijinta,
Idan ba Basu Riga sun iso ba to suna hanyar isowa,
Dan haka saiki fadawa danki ya tattara kayansa yabar gidan Dan yanzu ko kallan matar me gidan yayi da wata manufar aka qwaqule idanuwansa a banza wlh karma ki nememu Dan bamuda da me wannan sunanma.
Kashe wayarsa yayi tareda kashewama gaba Daya sbd karsu damesa da kira Suma uban kudin da ASH ya Basu suke rabawa kafin Suma su dauki hanya Dan sukam motarsu zasu ja su koma ba jirgi zasu hau ba.
Naufal da mum Aisha kuwa juna suka kalla batareda fahimtar me uncle Sulaiman din yake nufi ba,
Naufal kalaman Uncle sun mata kama da bashine aka daurawa Amatun ba,
Wani zufan baqin ciki ne ya tsiyayo masa batareda ya tabbatarda Hakan ne ba,
Mum Kuma duk da Bata fahimta ba itama kalaman sun mata kama da Bada Naufal aka dauraba Dan haka take taji Wani sanyi na gauraya zuciyarta da ruhinta.
##MAMUH#
#ROMANCE
#HOT LOVE
#MARRIAGE
#DESIRE
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
atπ
2k for vip each
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
28
Assalamu Alaikum
Hajiyata kinada labarin kayan Egypt da muke kawowa kuwa to in baki saniba matso kusa kiji,
AINAM DRINKS AND MORE mun kawo muku kaya na gani na fada na gayu wainda sai wance da wance ake gani dasu ba kano made bane kunsan a koda yaushe burinmu mu kawo muku unique abu.
Idan muka ce kayan Egypt muna nufin na Egypt din fa,
kayan manyan mata,manyan Yan mata,mata masu aji,matan dasukasan kayan alfarma,
Available ne ba jira zakiyi akawo ba muna bada sari muna aikawa koina,duk abinda kike bukata hajiyata ki latsoni kawai 08146766440
Ko baki siyaba yanzu kiyi saving number ta murika ganin status din juna sbd idan kina Gani zakisan namu ba irin nasu bane.
Nagode
************
Naufal Jin yayi zuciyarsa na daukan Wani zafi da takaici tareda baqin cikin idan har Wani aka aurawa Amatun ba shi ba bare yasan bazai wuce Barr Faisal uban naci da taurin Kai ba.
Mum Aisha ruwa ta ringa sha tana godewa Allah a Fili da zuciyarta Dan itama tasan bazai wuce Barr Faisal dinba tinda sun San Shima dole bazai iya zama baibi Amatun kauyen ba,.Dan haka itadai koma wanene su je su qarata Allah yasa auren bazai mutu ba sai mutuwa,
Allah yasa auren ya dauru Babu abinda zai tabasa sbd Amatun tayita zamanta acan Babu ranar dawowa rayuwar gidan sun huta
Shi kansa Naufal Daya qwallafa mata Rai tasan ranta yanzu zai samu Nutsuwan Bai ga Amatun ba bare ya Kuma janyo mata maganar da zata kaisu babbar halaka a hannun ASH.
Naufal miqewa yayi batareda yace komaiba zai bar palon mum Aisha ya kallesa da sauri tana cewa
"Ina zaka?
Kasan dai Tinda su Sulaiman sunbaro dole ASH Shima yabaro Kuma inda yake Yana hanyar dawowa gidan Nan ko?
Tinda Bada Kai aka daura ba Maza ka hada kayanka ka koma gidan zayyan kafin komai ya lafa sai na basa hakuri muga idan zaa samu sassaucin da kaima zaka iya zuwa Basa hakurin ya Sauko tukuna ka dawo.
Sai a lokacin Shima fargaban dawowan ASH din ya shigesa Dan haka cikin fargaba ya Kalli mum din yace
"Mum idan ASH ya sameni gidan Nan zai iya miqani inda sai kema kin manta kamanni na kafin a fito Miki Dani ki Ganni"
Miqewa tsaye mum din tayi tana cewa
"Muje kayi sauri ka hada kayanka ka fice sbd jirgi zai biyo kowane time zakaji ya iso."
Fitowa sukai da sauri zuwa dakin Naufal din Shida mum din suna rige rigen Saka kayansa a akwatinansa da duka ya dawo dasu harya Jere kayansa Yana jiran amaryarsa.
Cikin sauri da gaggawa suke hada kayan batareda tsarawa ba Dan haka kayan kusan duk a hargitse suka gama hadasu suka janyo zuwa mota tana sake maimaita cewa
"Wallahi Naufal ka nutsu kafin na cire hannuwana a lamarinka,
idan zaka koyi dangana da iya hadiye kwadayika akan mata kafin mu samu sassaucin fushin ASH Wanda ba magana zaiyiba Amma hukuncinsa abin tsoro ne,
dan kaje ka sake debo Wani abin maganar da zai dawo kunnen ASH wlh fitarda hannuna zanyi tinda Kai bakasan ana koshi da gundura da komai na duniya ba"
Harabar gidan suke kokarin Isa aka Bude makeken gate din Mansion din motocin ASH