Header Ads
Showing 126001 words to 129000 words out of 152002 words

Chapter 43 - AMATULMALEEK COMPLETED BY Mamuhugee.txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

867

Ads at the middle of Article

ya sauke tareda numfashi me tsananin dumi daya furxo nauyin da kirjinsa ya dauka tareda juyawa qatuwar jacket me tsayi sosai da kauri ya Sako akan kayan jikinsa ya fito Mr Jameel ya biyo bayansa a sanyaye jikinsa gaba Daya a mace.


Daga shi har mr Jameel Babu Wanda ya iya magana mota kawai suka shiga Mr Jameel din na satar kallansa cikin damuwa shikuwa Babu abinda ya iya furtawa asibitin kawai yake buqatan Isa.


Suna Isa asibitin Kai tsaye dakinta ya nufa bugun zuciyarsa na qaruwa tareda nauyin kirjinsa yana Isa ya Bude dakin Kai tsaye ya shige da saurin ya Isa kanta sedai hannunta kawai ya kama da nasa ahankali tareda kallan idanuwanta data Bude ahankali ta kallesa da ganinta Daya fara bacewa cikin Wani hali me sanyi ta Dan motsa hannunta Dayake cikin nasa ta Dan kama nasan itama.


Qanqame hannunta yayi ahankali zai Bude Bakinsa da yayi masa tsananin nauyi Bai furta abinda zai furta ta rufe idanuwanta.


Likitan dasuke kanta ne Basu saddakar ba zasu cigaba da Jan numfashinta Rai yayi halinsa.
##MAMUH#




*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070


YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar




70
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*


MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER


08142800199
07068558096


************
"P name Ms ABEEDA TALBA,
Time of dead 10:26 4th Dec"


shine abinda yake shiga kunnuwansa ahankali ya rufe idanuwansa ahankali hannunsa har lokacin Yana riqe da nata kafin ya Bude idanuwansa dasuka qarasa rikidewa ya zuba mata duk Wani jarumtarsa ta ciki tana tarwatsewa Dan kuwa Abeeda nata matsayi me kyau da girma a zuciyarsa na zamtowarta mata Kuma uwar yayansa hakama respect din dayake Jin tana dashi a gunsa yanada girma.


Hannunta aka zare ahankali daga nasa tareda ajiye mata shi straight gefen jikinta aka rufeta akan idanuwansa aka kashe komai na naurorin da duka suke jikinta bayan an zaresu Daya bayan Daya.


Mr Jameel Dake daga bakin kofa duk zamansa namiji kasa riqe hawayensa yayi Ms Abeeda mutum ce mai zuciya me kyau da sanyi daga karshe dai bayan jinyar shekara da shekaru ta rasu tabar mijinta da yayanta da duniyar gaba Daya.


ASH TALBA wannan Daren dare ne Daya girgiza duniyarsa tareda jijjiga zuciyarsa datake da tsananin jarumta sbd rashin Abeeda uwar yayansa dayake Jin tsananin tausayi da radadin jinyar datasha tareda azabar ciwo dakuma azabar dasu Husnah suka dandana mata a cikin Mafi azababbiyar hanya Dan kuwa ko daurirrikan da Akai mata na fadowar a jikinta sunkai biyar,Tasha wuya Tasha azaba gashi Babu karfi ko iKon motsawan da zata rage Mata azaban datake ciki.


Fitowa dashi Akai daga dakin aka bar gawan ta gama mintinan da ake diban mata kafin zuwa da ita inda zaa ajeta.


Mr Jameel Bai Taba ganin abinda yayi breaking ASH TALBA ba sai a ranar sbd har cikin ransa yakejin azabar da Abeedan ta shiga ciki a kwanakin na jinyarta data dawo sabuwa,
Daga shi har Abeedan sunsan tin farko bazatai surviving ba sbd stage na cancer dinta Amma Abeeda dashi kansa suka zabi Takoma gida cikin familynta ta qarasa jinyarta acan tayi spending days dinta ka karshe cikin yayanta da Yan uwanta Ashe batada Rabon ganin Hakan.


Basu baro asibitin ba sai kusan asuba suka dawo sallah yayi ya ringa yimata adduar samun Rahama Saida yazo shafa adduar wasu irin hawaye masu zafi suka tsinke masa ba zato kuka mara sauti ya kufce masa Dan kuwa nauyin zuciyarsa ya kasa riquwa.


Tausayin Abeeda da rashinta da tausayin yayansa sune suke yanka zuciyarsa suna tarwatsata.


Kafin safe zuciyarsa ta jigata sosai sedai Kuma haka Allah ya qaddara masa Yana fatan mutuwa gareta ta zama Hutu da Rahama Dan haka ya riqe jarumtarsa ya Saka Mr Jameel afara shirye shiryen yanda zasu iso da gawar Nigeria.


Shi kansa Mr Jameel Bai sanar da kowa ba sbd tinda Mai gidan nasa ya shige Shima yake cikin tsananin sanyin jiki da nauyin zuciya na rashi da Akai.


Asibiti suka tafi aka fara Shirin komai Dan tafiya yakeson suyi da ita ba Bata lokaci sbd a samu suturtata kan Lokaci.


Anty dinta dake qasar Greece din tareda ita dayake tinda ASH yazo qasar itama tayi tafiya ta huta bataji rasuwar Abeedan ba Saida aka gama komai na taho da gawarta ya kirata ya sanar mata take ta Yanke jiki ta Fadi sbd batama San Abeedan ta koma asibiti ba tinda tasan dai an koma gida da ita.


Ko data farfado aka fara Neman numbern ASH din sun Riga sun taso suna jirgi Dan haka baa samunsa take maganar rasuwar ta fara yaduwa zuwa porthcrt aikuwa take kowa jikinsa yayi sanyi duk da doguwar jinyarta tasa ake Saka ran rasuwar tata koyaushe Amma Kuma rasuwar ta daki kowa sbd Tasha wuyan jinya, ta tafi batareda ta dawo cikin Yan uwanta da yayanta ba datake ta fata da buri.


Kasa sanarwa Husnah rasuwar Akai sedai kawai aka aika musu cewan su koma Abuja dukansu Banda Naufal da suka bari gidan.


Dayake duk a matse suke cikin qunci a gidan take washe gari suka tattara Faisal ne da kansa yazo har yolan ya siya musu tickets suka wuce abuja.


Tinda suka baro jikin maamah yayi sanyi sbd abinda takeji a jikinta na ba lafiyan ba,
Ita kanta Husnah jikin nata a sanyaye yake sedai Kuma baro wancan gidan datai Yana Sakata Jin nutsuwa sbd kullum Bata iya bacci yanda Taga Rana haka take ganin dare Sam Kwanciyar hankalinta ya qare a qunci take wuni a qunci take kwana Se mafarkin mum dinta datake yawan yi gashi ba daman waya da Dad din bare taji Yaya take.


Koda suka iso Mansion din mutanen porthcrt sun rigasu isowa Dan haka take maamah jikinta fara Bata
Ita kanta mum Aisha zuwa lokacin jikinta yayi sanyi Kuma itama take tinanin Abeeda ta rasu yazo kanta
Husnah kuwa ganin dangin mum dinta a gidan ya Sanyata tsayawa cak tana kallansu tinanin dalilin zuwansu na tsinkar da zuciyarta sbd Basu taba zuwa dubasu ba tinda mum din tabar qasar sedai su suje duba su,Basu taka Tako kafarsu inda suke ba sedai idan sune suka je to meyasa sukazo dukkaninsu yanzu?


Maamah kasa riqeta qafafuwanta sukai ta zame qasa tana zauna qasan palon tana kokarin riqe abinda take ji a zuciyarta sbd fatan ba abinda tinaninsu yake Basu bane.


Mum Aisha ma a silale ta zauna tana kallan su mommyn porthcrt din da dukkaninsu suka kasa dagowa su Kalli Husnah.


Husnah dauke jajayen idanuwanta tayi daga kansu tareda Maidasu kan maamah sbd maamah dince zuciyarta kawai ke buqatan magana da ita bayan tsowan lokacinda maamah din ta dauka ko kallan inda take Batayi bare ta Bata Daman kare kanta ko musawa zancen mum Aisha data fada wanda kusan Hakan ne yake qara zarar da ita.


Qafafunta kasa daukanta sukai ta zube da rarrafowa ta iso gaban maamah ta kama qafafunta muryarta na rawa tace


"Maamah meyasa kike kokarin yin kuka bayan Babu abinda aka fada daga shigowanmu?


Gurin mummyn porthcrt ta rarrafa ta koma cikin murya me rawa tace


"Mummyn porthcrt me yake faruwa kuka taho?
Wani abu ya faru?
Kunyi waya da Dad dina ne??


Kasa magana mummyn tayi sai kokarin riqota datake yi zatai magana Amma Husnah din ta janye tana cewa


"Ku fadamun abinda yafaru kuka taho ni shi nakeson fara ji"


Faisal Daya shigo lokacin jikinsa a mace kallan Husnah din yayi zaiyi magana ta qura masa idanuwanta dasukai jajir Bata ko kyaftawa sbd tabbatarda abinda zai fada din.


Ahankali ya Bude Baki zaiyi magana jiniyar motan data dauko gawan ta shigo mansion din alaman su ASH din sun iso.


Gabaki dayansu kofa suka kalla Husnah jikinta Yana saki gaba Daya maamah kuwa kukan daya danne zuciyarta ne yake kokarin fitowa tareda idanuwanta Dake zuba mata radadi me zafi.


Juyawa Faisal yai ya nufi kofan palon ya fice da zuwa harabar gidan.


Husnah kuwa mummy ce ta riqota jikinta ahankali hawaye na gangarowa kowa Dake palon.


Isowar gawar matar ASH TALBA ya qara yada zancen rasuwar da jana'izan da zaayi Dan haka duk Wani abokin huldansa da muaamalansa suka shiga alhini da jimamin rasuwar.


Kusan Yan uwansa na kusa da dangin Abeedan tini suka iso duk suna mansion din Wanda hatta securities da masu Aiko kowa jikinsa a mace yake har aka shigo da gawar palon qasa aka ajiye take Husnah ta saki jiki a jikin mummyn porthcrt din a sume.


Maamah ma take zuciyarta ta fara Hawa sama numfashinta na kokarin daukewa khaltume ce sukai kanta suna kokarin ganin Bata shiga halinda take Neman shiga ba.




AmatulMaleek anty Farha Bata sanar da ita rasuwar ba sbd itama Saida su ASH din jirginsu ya sauka Mr Jameel ya sanar mata take ta shuga mummunan tashin hankali Dan haka Kai tsaye shagonta ta bari ta wuce school ta dauko Amatu data gama exams dinta a ranar.


Amatu kallo daya tayiwa anty Farha din ta fahimci damuwa da sanyin da jikinta yayi.


Jin tayi nata jikin yayi sanyi bare Daman ba Wani kuzari ne da ita ba Dan haka ta Dan sauke numfashi me sanyi a hankali tace


"Anty Farha lafiya dai kuwa?
Wani abu ya faru a spa ne???


Anty Farha din kasa juyowa tayi ta kalleta sai hanyar TALBAs mansion data dauka a hankali cikin sanyi tace


"Su maamah sun dawo suna mansion zamuje gurinsu ne"


Juyowa tayi ta Kalli anty Farha din da idanuwanta dasukai laushi cikeda mamaki da fargaban lafiya..


Kasa cewa komai tayi sbd tinanin data shiga tanajin jikinta na sanyi hakama anty Farha din ma jikinta a sanyaye yake.


Shiru sukai Babu me magana sai anty Farha din da ake kira Akai Akai tana amsawa Wani Kiran Kuma Bata ma iya amsawa sbd batajin dadin zuciya.


Yanayin anty Farha din ya sake Sakata cikin yanayin tinani da fargaban dole Wani abu ya faru kenan tinda tayi waya da maamah da jiya da safen Nan ne kawai basuyi waya ba sbd tinda safe ta fita exams dinta Kuma Bata sanar mata zasu taho Abujan ba,
Hakama idan sunzo anty Farha bazatai sanyi haka ba,hakama tayaya zata fuskanci kowa da ciki kwatsam a jikinta.


Harbawa zuciyarta tafara yi tanajin gefen cikinta Daya fito duk da ba sosaiba kana gani zakasan ciki ne na haihuwa a jikinta Yana daurewa.


Waiwayowa anty Farha tayi ta kalleta cikin kulawa tana Maida kallanta kan gefen cikin data Dan riqe cikin cikin kokarin kawar da damuwarta tace


"Lafiya dai?
Me kikeji?
Cikin na ciwo ne?
Karfa ki daga hankalinki sbd Kinga yanayinki.


Kasa magana Amatu tayi sbd zufan data fara hadawa lokacinda suka shigo street na gidan take taga alaman akwai abinda yake faruwa sbd securities din gidan kusan duk suna waje sbd motocin da suke harabar gidan.


Suna isowa aka Bude musu gate suka shigo Tin anan Amatu jikinta ya Dan fara rawa ganin Mr Jameel ya fito hanyar zuwa palon ASH na qasa Yana waya idanuwansa jajir take ta tabbatarda ASH ya dawo kenan.


Nauyi idanuwanta da zuciyarta suke sake shiga sbd fara fahimtar abinda ya faru,
Anty Farha dole riqe hannuwanta tayi suka nufi ciki suna Saka Kai a palon qasa din akan gawar da aka gama shiryawa ta Madame abeeda idanuwan Amatu suka fara sauka
Cak ta tsaya anty Farha na sake riqeta da kyau sbd jirin Daya dibeta idanuwanta na kan gawar.
#MAMUH#


*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070


YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#


AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar


71
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*


MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER


08142800199
07068558096


************
Cikin qarfin hali anty Farha ta sake riqeta da kyau tana Bata kariya daga jirin dayakeson dibanta tana Jin itama firgici Yana kamata sbd ganin gawa kwance gabansu.


Kama Amatu tayi suka qaraso cikin palon dakyau Wanda yasa wainda keda Dan sauran karfin hali juyowa suka kallesu Amma su maamah Kam da Husnah Babu me qarfi bare hankalin juyowa su kallesu.


Hawaye ne suka ciko idanuwan Amatun suna gangarowa rawar jikinta na bayyanuwa sosai sbd a take tasan Mum Abeeda ce ta rasu itace a kwance a shirye.


"Innalillahi wainna ilaihirrajiun" take furtawa daga bakinta Amma Sam kalman taqi fita sbd kasa tsayuwa da qafafunta datai sbd shock da tashin hankali Dan haka ta silale a gurin jikin anty Farha wadda itama ta bita qasa tana rungumota cikin tsoron kada Wani abun ya sameta sbd firgitan rasuwar.


Mum Aisha da tinda suka shigo ta zubawa Amatun idanuwanta tana kallan cikinta Da suna shigowa akansa Idonta ya fara sauka tini ta taso Dan tabbatarwa ta kamawa farha Amatun tana cewa


"Ciki ne ita??
Idan ciki ne Kam to kuyi sama dakinta ku zauna kada ya bare sbd tashin hankalin ganin gawa.


Anty Farha Bata iya amsa mum Aisha dinba kokarin bawa Amatu data rikice gaba Daya hakuri da kalaman da zasu dawo da ita daidai takeyi Amma gaba Daya Amatun ta rude sbd Daman kafin isowarsu a rude da tashin hankalin take sai gashi ta tadda abinda ya qarasa rikitata ga kukan Husnah Dana maamah dayake tashi cikin palon cikin Wani sauti me yanka zuciya Dan dukkaninsu ganin sukeyi sune silan rasuwar nata,
Maamah ganin takeyi da Bata biye tashin hankalinsu ba ta tsaya ta tare Abeeda da Kila Bata fado ba,
Husnah kuwa Kai tsaye tasan itace sanadin halakan mahaifiyartata hakama a lokacinda ya kamata ace ta tsaya ta gana sosai da mum dinta kafin lokacin rasuwar tata Amma gashi ta rasu batareda sun sake ganin juna ba.


Amatu Sam ta gagara taruwa gabaki daya ma Neman sumewa takeyi Dan haka dole mum Aisha din anty Farha ta Saka ta kama mata ita sukai sama zuwa bedroom dinta sauran mutane na binsu da kallo cikin tausayawa Amatun sbd ganin juna biyu a tareda ita duk da basu ganeta ba Basu San itace 'yar maamah din da ASH yake aure ba.


Suna wucewa sama aka shigo daukan gawar Abeedan Dan ficewa da ita sbd anriga anmata sitira,


ASH dinne da kansa Se Haydar da Abdulhameed Wanda isowarsu kenan ko zama beyiba suka fito da gawar.


Husnah Wani irin kuka takeyi da ko fitowa ya Dena yi sbd wahala da tsananin Wanda taita yi tinda suka iso,
Maamah ma kusan siqewa take Neman yi kafin kace me zuciyarta ta riqe sedai aka kwasheta daga gurin da sauri itama Akai dakinta da ita su khaltume suna mata firfita kafin agama jana'izan a kira mata likita ko kaita asibiti sbd abin yafara Basu tsoro ma.


Husnah ma birkicewan tayi a gurin take ta sake somewa Akai kanta itama ana Neman cetan ranta.


Haydar kuwa kuka ne yakeyi sosai da da sosai sbd bayan tashin mum dinsu baa sanar masa komaiba hakama ko dayaje ganinta Greece yaga alaman sauki a tattare da ita harya tafi yabarsu Husnah da maamah baiga alaman ciwonta zai tashi ba sai kawai rasuwarta kwatsam.


Shi kansa Abdul yayi kukan rasuwar sbd tausayin Haydar da Husnah wadda kusan itace ma tafi basa tausayi tinda yasan depression datake fama dashi.


Anyi jana'izan Madame Abeeda Talba ankaita an rufeta aka dawo Karban gaisuwa Wanda akeyi a mansion din din cikin babbar palon ASH din Dayake qasa Wanda yake ganin baqi.


Acan cikin gidan ma a palon qasa ake karban gaisuwan,
Maamah da Husnah dole aka kira musu likita ya dubasu sbd suna dakunansu a kwance jikin ba sauki.




Amatu kuwa tinda suka kwantar da ita a gadonta hankalin anty Farha ke sake tashi sbd yanda gaba Daya jikinta ya rikice ga Mum Aisha ma ta tsaya tana nuna damuwanta sbd a yanzu data tabbatarda tasu ta qare a gurin ASH so zata nunawa Amatun da cikinta ko zata samu sassauci a gurinsa.


Kokarin saukar mata da zazzabinta anty Farha ta ringa yi kafin a gama jana'izan ta kira likita itama sbd yanzu ko ta kira Likita ana kokarin jana'izan ne bazata samu shigowa ba.


Mum Aisha ma haka ta ringa kaida kawo tsakanin palon qasa gurin karban gaisuwa da bedroom din Amatun har anty Farha ta gaji ta rufe dakin Dan mum Aisha din ta isheta bayan damuwan datake ciki na Amatun.


Dr beeba ta kirawa Amatun Se data Dan jima kafin tazo sbd tana asibiti ko da aka kirata Dan haka Koda ta iso Amatun ta gama galabaita harda ciwon mara har tayi baccin wahala Dan har kusan yamma ma tayi.


Dayake ba mutane sosai Tinda gaisuwan duk Wanda yayi ba zama yakeyiba wucewa yakeyi sbd kowa bayason zaman gaisuwar daga masu karban har masu zuwan tinda Wani lokacin zaman baida Wani amfani gwara kayi ka wuce.


Mum Aisha ce tayiwa Dr beeba jagora zuwa sama har dakin Amatu sukai knocking anty Farha ta taso ta Bude tana ganin Dr beeba ta saki ajiyan zuciya sbd ta fara saddakarwa da kawai ta dauki Amatun su tafi asibiti,
Bata kira Mr Jameel ba ta sanar amsa sbd kada a sanar da ASH a daga hankalinsa ayau dayake buqatan a barsa yaji da abu Daya tukuna.


Qarasowa ciki sukai Dr beeba na musu gaisuwan rasuwar tana nufar Amatu Dake kwance tana bacci a wahalce.


Zaunawa tayi tareda kallan Amatun tana kamo hannunta Daya Dayan Kuma tana Dan yaye rufarta ta Kalli Dan qaramin cikin tana dawo da kallanta kan Farha tace


"Meyasa Baki fadamun tana da ciki ba da bazan Dade haka ba ai zanyi kokarin zuwa kan time gaskia."


Kasa cewa komai anty Farha tayi sai numfashi me dumi data sake jiki duk a mace sbd yunwa da damuwa dakuma ciwon Amatun.


Fara dubata Dr beeba tayi tana Ciro wayarta Dan Kiran asibiti akwai abinda zaa kawo mata.


Mum Aisha fita tayi Takoma qasa duk an watse sbd sallan magrib da Kai kusan duk Yan gidan ne suka rage Dan haka itama dakinta ta nufa ta shige

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads