Showing 3001 words to 6000 words out of 152002 words
Chapter 2 - AMATULMALEEK COMPLETED BY Mamuhugee.txt
Basu abincim da zasuci sbd kowa ta kansa yakeyi kowa na fama da rashi.
Madame abeeda wadda a yanxu matsayinsu da sunansu ya zarce na Baya sbd matsayin da ASH yake dashi a gurin Al'ummar Dake tsananin son ya tsaya musu a matsayin gwamnan jahar Amma baida raayin siyasa duk da Hakan jamaa sosai sukeyinsa Dan haka kusan Babu Wanda baisan the grt ASH TALBA ba.
Rayuwarsa data iyalansa kwata kwata baa qasar yake yinta ba sai dai yakan Fi iyalan nasa zuwa Dan haka jamaa sukeyinsa sbd taimakon dayake bayarwa kaman baisan zafin dukiyar ba Dan haka manya da yawa mutanensa ne hakama talakawan ma mutanensa ne hakama masu kudin Dan haka kowa yinsa yakeyi duk da da yawa baisanma sunayi ba Amma Kam sosai aketa Daman gwagwarmaya da rigimar shi akeso amma Sam Baya raayi.
Ta bangaren matarsa Abeeda kuwa wadda duniya ke kira da Madame abeeda Talba tini rayuwarta data 'yayanta ta zama abin kallo daga nesa sbd tsaron da ake Basu bana wasa bane sbd ASH Bai hadasu da komai nasa ba Dan haka a yanzu tsakaninta da maamah aike ne kawai Shima sai can idan lokaci me tsayi yaja Dan haka itama maaman ta hakura ta rungumi marayun 'yayanta.
*****Bayan rasuwar Babah da shekara biyu kawu bello ya aure Maamah din wadda bayan wahala da ukubar data ringa sha a hannun kishiyoyi Babu abinda suka Qaru dashi itada 'yayanta
Ahakan suka ringa Shan kuncin rayuwa har kawun ya gaji ya saketa sbd yace bazai iyaba lalurar tai masa yawa Dan haka dai anan cikin gidan Akai auren anan Akai sakin taci gaba da gwagwarmaya itada 'yayanta Wanda tanaji tana Gani Abdulhameed yakoma almajiri AmatulMaleek kuwa haka take zaman gidan Bata taba barinta fita ba Koda zuwa cikin gidan sbd yanda gidan yake sake zama hadari sosai ga duk Yan matan gidan da Yara qanana ma Dake tasowa duk da yawa sun lalace a tsakaninsu batareda sanin iyayensu ba.
AmatulMaleek tinda tafara wayo rayuwarta ta zama tamkar kurma sbd rashin magana tinda basuda abin magantuwa akansa Dan bayan tarin kunci Babu komai a rayuwarsu Dan haka ta taso a miskilar gaske Wanda Hakan yafiwa maamah dadi da farin ciki sbd kullum kukan maamah a gaban Allah shine yanda zata bawa 'yayanta kariya daga masifar gidan musamman AmatulMaleek datake mace.
AMATULMALEEK
Regular 700
Vip 2k
0022419171 Access bank Maryam sani
09033181070
#MAMUH#
#LA HOT
#LIFE
#ASH TALBA
#AMATULMALEEK
#NAUFAL TALBA
#MEERAH HERBS
#ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
3
Maamah Bata taba yin qasa ko sanyaba akan tsaro da tarbiyarsu kaman yanda babansu ya dage ya tsaya kafin rasuwarsa duk da ta Wani bangaren dukansu har ita suna cikin hadari a gidan Dan ita kanta ansha shigowa bangarensu da dare da niyar a afka musu ko ita ko AmatulMaleek din Amma dai Allah na tsaresu shiyasa duk tsanani basa fitowa fitsarin dare gudun a keta musu haddi basuda abin yi Dan duk Wanda aka Bata gidan bayan hakuri Babu abinda zaiyi bawai Kuma Dan baa San masuyi din ba kawai dai bakada iKon magana ne ayita rigima da iyayensu ana Allah ya Isa da tashin hankali karshe dai cuta ce anriga an cuceka.
Maamah Bata taba Dana sani da damuwar aure a gidan taro me tsanani ba irin wannan sai yanzu sbd illarsa tafi dadinsa da albarkarsa yawa,
Amma dai tinda Allah yasa rabonta na 'yaya anan yake Babu yanda zatayi da kaddara bayan dagewa.
Ko islamiyya Bata barin AmatulMaleek tafiya ita kadai kullum tare suke zuwa lokacin tashi nayi taje su dawo tare duk da ta Dan girma Amma dai hankalinta baitaba Kwanciyar tabarta taje ita Daya ta dawo ita Daya sbd yawun da samarin gidan suka hadewa 'yartata Dan haka tasan ko a hanya zasu iya binta.
Ita kanta AmatulMaleek tasan rayuwarta a gidan tana cikin hadari Dan haka take kiyayewa tareda kame kanta Babu inda take taba zuwa Dan haka wasu da yawa a kauyen Basu Santa ba sbd Bata fita koyaushe tana dakin maamah ana tsaronta kamar wata gwal me tsadar gaske.
Abdulhameed Daya kasance qaninta shi Kuma sai ya zama kowa shi ya sani sbd shi Kam yawonsa yake zuwa yi tinda bara yakeyi duk da Shima Maamah din na kokari akansa Amma dai tafi Maida hankali akan Amah,
Yaron ya kasance Yana so da shaawan karatun Boko Dan haka kullum saiyaje makarantar bokon kauyen ya shige cikin Yara
Wannan dalilin ne yasa ake yawan kawo kararsa ga kawu bello sbd sunyita korosa Amma Baya Dena zuwa Dan haka kawun keji Asmaun da 'yayanta sun ishesa Daman kuka aure yakeson qarawa duk da manyancinsa sosai Dan haka so yake Asmau ta tattara tabar gidan ya samu bangaren sbd ya aje yar bazawarar da zai auro.
*****
Asmau tayi shekaru sosai rabonta da Abeeda a idanuwanta sedai aike Wanda Wani lokacin har mantawa akeyi dasu kafin su samu Wanda daga Yan Aiken ne da aka aje duk wata sukai musu abinci Amma Sam basa kaiwa sai bayan watanni watanni suke kaiwa ganin madame din Bata qasar sai Suma suke tasu zalamar.
A yanzu da AmatulMaleek tafara zama yar budurwar yarinya tini hankalin maamah yabar jikinta Bata bacci Batada nutsuwa kowane dare Bata iya baccin kirki sbd tsoron rayuwar da 'yarta zata shiga a yanzu da samarin gidan da babu nagari zasu iya cewa suna son aurenta kuma tasan batada abinda zai Bata damar hanawa tanaji tana Gani zaa lalata mata rayuwar 'yarta gashi kowannensu yaga budurwa tafara tasawa a cikin gidan sai suce sunaso gashinan da qananun shekaru sunata Tara mata daga me mace biyu Se uku sbd suna cewa sunaso akeyin wuf ayi auren sbd karfafa zumuntar da Babu so ko jin qai a cikinta.
******
Iyalan ASH TALBA sun sauka a kasar Nigeria a bazata sbd rasuwar mahaifin mom Aysha wanda yake tamkar mahaifin ASH din Shima Dan haka dolensu suka dawo Nigeria.
Saukarsu da labarin rasuwar tasa yasaka Maamah shiryawa dole itada 'yayanta sukai Shirin tafiya duk da batada kudin mota Amma hakanan ta siyar da akuyoyinta guda biyu datake ta Reno sbd auren AmatulMaleek idan zaizo kafin lokacin sun qara hayayyafan da zasu isheta yiwa AmatulMaleek din Wani abu.
A wulaqance aka siyesu sbd anga tanason kudin amma Bata damu ba sbd zuciyarta Sam bamai Saka damuwa bace hakama Allah yayi mata sanyin hali da tsananin hakuri me yawa Dan haka baka gane ko ka quntatar da ita sbd tana hadiye komai da sanyin halinta.
AmatulMaleek da batajin dadin tafiyar tasu Sam Amma Bata nuna ba itama sbd kusan halin mahaifiyarta itace ta dauko sak na boye damuwa da hadiye kowanne bacin Rai da sanyin hali Dan haka itace da maamah din sukai wankin kayansu da zasuce tsumma ne ma Amma Kuma su suke dasu Dan haka dasu zasu.
Abdulhameed kuwa farin ciki yakeyi sosai sbd baitaba barin ko wajen kauyen ba bare zuwa babban birni ba dukda baimasan me birnin ke nufi ba Dan shi Kam asalin bafulatanin kauye ne.
AmatulMaleek din ma dai kana ganinsu kaga fulanin kauye sun fito Amma Kuma nutsuwarta ke Hana duhun kansu fitowa.
Ranar da zasu tafi gidan kaf murna sukeyi su tafi sbd bangarensu da kowa keso saikace ce musu maamah tayi bazata dawo ba,
To sukam Koda zata dawo din to idan ta dawo sedai ta koma zauren gidan da zama Dan kuwa duk Wanda ya shiga baida niyarnta gidan sbd AmatulMaleek dasuka qwallafawa Rai akan tana Isa aure zasu aureta su jefa cikin matansu.
Duk Wani Shirin tafiyarsu sun kammala Dan haka washe gari tinda asuba suka hau mashin Abdulhameed na gaba maamah da AmatulMaleek a Baya suka fita kauyen zuwa kauyen gabansu da acan ake Hawa motar zuwa babbar hanyar titi da acan Kuma zasu hau motar zuwa cikin state din kafin daga can su hau motar zuwa Abuja.
Tinda suka hau mashin din Abdulhameed ke washe Baki cikin tsananin farin ciki sbd Bai taba Hawa ko Keke ba bare mashin sai yau din.
Tafiya me Dan tsayi sukai kafin suka Isa kauyen kurmawa,
Saukowa sukai daga kan mashin din maamah na ajiye jakar kayansu gefe
Ita Kuma AmatulMaleek Abdulhameed Dake zare idanuwa Yana kallan koina ta kamo hannunsa suka dawo gefen maamah din.
Kudinsa Maamah ta Ciro ta basa na mashin ya juya Yana musu Allah ya kiyaye Abdulhameed ne kawai ya amsa da Amin cikin murna da farin cikinsa da Baya boyuwa.
Wata motar a Kori kura suka nufa wadda ita kadai ce Daman a kauyen take fita da mutane Dan haka kusan Tama cika Dan haka ba Bata lokaci aka kama su Abdulhameed din da AmatulMaleek aka Dora a sama kafin Maamah ta miqawa Amatu jakarsu tukuna itama ta tattara zaninta ta kama motar ta Haye ta zauna gefen 'yayanta suna Dan gaisawa da sauran mutanen Dake bayan motar a Bude kowannensu kura ta gama rife koina jikinsu kaman anyi juyen yashi a jikinsu sbd iska da akeyi.
Tafiya suka fara Babu me magana acikinsu sai Abdulhameed Dake kalle kalle har bacci ya daukesa a jikin AmatulMaleek wadda itama tafara komawa kamar bokanya sbd iska da qura Dayake Kara sauya kamannin kowa Dake motar.
Tafiya me tsayi Nan ma sukai sosai kafin suka iso babban titin hanyar shiga kauyukansu masu shegen Nisa.
Saukowa sukai kowa qafafunsa sunyi sanyi gashi zuwa lokacin Rana tayi Dan kuwa sha Daya saura Dan haka komai Basu tsayaba ruwa kawai da biredi kawai maamah ta Siya musu suka fada wata motar da zata kaisu state acan su samu shiga motar Abuja.
Babu Bata lokaci motar ta cika Dan haka suka sake daukan hanya.
Biredin data Siya musu ta rarraba musu suka fara cin abinsu hankali kwance.
Abdulhameed duk rawar murnarsa fara komawa ciki tayi sbd zuwa lokacinda suka Isa babbar tashar yola tsoro kamasa yayi sosai sbd Bai taba ganin mutane hakaba sosai da hayaniya anata ihun Neman passengers ta bangare daya ga masu talla takoina suna ihun azo a Siya abinda suke tallan,
Hakama a Wani gefen fada akeyi sosai a cikin tashar..
Ba Abdulhameed ba AmatulMaleek ma kanta tsoro ne da firgici me tsananin gaske ya shigeta Dan Basu Saba haka da mutane da wannan hada hadarba Dan haka dukkaninsu qanqame hijabin maamansu sukai ita Kuma ta riqe hannuwansu gam tana Basu kariya har suka samu motar da zata daukesu zuwa Abujan suka shiga ta rungume 'yayanta tanajin hakanan zuciyarta na karyewa da tafiyar Kuma a yanzu sbd so da dama duk halinda take ciki a kauyen sai tanajin yafi mata nutsuwa akan zuwa birnin duk da wannan tafiyar taji hankalinta ya kasu kashi biyu zatayi ne sbd magana da Madame Abeeda ta rage nauyin zuciyarta da quncin Daya dabaibayeta akan rayuwar AmatulMaleek da batasan Yaya zatai da ita acikin zuriar Sanda Fulde ba.
Shiru tayi tareda Nisa a tinanin rayuwarta tin kuruciya da irin gatan data samu a Baya da rayuwar data taso aciki har kaddararta ta sauya mata hanya zuwa kauye da auren kauye Wanda ayau ta samu kanta a tsaka me wuya sbd rashi na Miji Kuma uban 'yayanta Wanda da ace Yana Raye da bazata samu Kanta a wannan halin na kakanikayi da 'yayanta.
AmatulMaleek Dake jin tsoro me tsananin gaske a duk Nisan da suke qarawa na tafiyar shiru tayi jikin mahaifiyarta tana Jin zuciyarta na shiga yanayi na rashin murna da tafiyar dakuma yanayi na sanyi Dan haka ta rufe idanuwanta tana barin baccin datake ji daukanta.
Kallansu maamah ta sake bayan dukkaninsu sunyi bacci jikinta ta shafa kansu su dukan tana Bude zuciyarta cikin amincin Allah tace
"Allah ya kawo madaukakin haske da girma a rayuwarki AmatulMaleek keda 'dan uwanki,
Allah yasa ki zama tauraruwar macen alfahari a duk inda rayuwa zata kaiki,
Yakuma Baki mijinda zai Miki Mafi girmamman so me tsaftan gaske..Amin"
Numfashi ta ajiye ahankali itama tana lumshe idanuwanta sbd zuciyarta Dake jin kaman tana gazawa da gwagwarmayar.
****
Tafiya yankin azaba kaman yanda aka fada,
Sai yamma lis suka sauka birnin Tarayya,
Daga maamah har su duka kafafunsu sunyi Wani irin nauyi da riqewa Dan haka daqyar dukkaninsu suka iya tsayuwa bayan sun fito motar zuwa lokacin Abdulhameed da AmatulMaleek sosai suke Jin tsoron mutane Dan haka a maqale suke da maamah wadda itama tasan bazata iya Kai kanta gidan ASH TALBA ba Dan haka numbern Madame Abeeda datake cikin kanta kamar hadda ta karanto aka kira musu ita cikin rashin saa akaita kira baa dagawa sbd basa daga bakuwar lamba Dan haka dole guri suka samu a tashar suka zauna ana sake kira lokaci bayan lokaci.
Yunwa da wahala ta Saka AmatulMaleek ringa Amai a gurin har Saida dole aka nemi guri aka kwantar da ita sbd take zazzabi ya rufeta.
Sanyi jikin Maamah yayi ga Abdulhameed Shima duk yayi laushi sbd azabar tafiya da yunwa Dan haka duk taji hankalinta ya tashi damuwa na rufeta ta zuwan nasu.
Sallar magrib ake kokarin shiga Wanda yaketa kira musu numbern ya ringa mata fada Yana cewa wayace suzo batareda sun sanar da inda sukazo din ba?
Basusan baa zuwa Kai tsaye gidajen manya ba batareda an sanar musu ba sbd basason damuwa da takurar talakawa da dangin kauye.
Shiru Maamah tayi sbd zuciyarta gabaki daya Bata mata dadi jikinta yariga yayi sanyi gaba Daya Dan haka batama San me zatace ba bayan sauke Kai kasa.
AMATULMALEEK
Regular 700
Vip 2k
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
#MAMUH#
#AMATULMALEEK
#ASH
#MADAME
#FRIENDSHIP
#LA HOT
#ROMANCE
#LOVE
#ABOKIYAR NISHADI TV CHANNEL
#MEERAH HERBS
Abokiyar Nishadi YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
4
Duk fada da masifar daya daga cikin ma'aikatan tashar yayi mata akan zuwan nata duk da baisan dalili ba bare Kuma alaqarta da Gidan ASH TALBA din datazo gurinsu Amma dai yasan Hakan datai na zuwan Kai tsaye nada hadari.
Kallanta yayi Kai tsaye yace ta Fadi sunanta ya rubuta Sako ya tura mata ga numbern,
Jiki a mace cikin sanyi ta fada masa tareda Dana 'yayanta wainda yayiwa Wani kallan qyama da takaicin yanda ta kwasosu kaman wasu almajirai sunzo garinda basusan koinaba ko tsoro bataji.
Kai tsaye sunanta Dana yayan nata ya rubuta a cikin sakon da cewan a taimaka a dauki wayar gasunan Tasha a zube harda mara lafiya.
Tafiyar sakon ya sakashi kallanta yace ta zauna ta jira idan ankira to shikenan idan Kuma baa kiraba motar asubar safe su koma inda suka fito.
Gyada masa Kai tayi cikin sanyi da nutsuwa tareda Bude Baki ahankali tayi masa godiya ta juya ta koma inda su Amatun ta zauna tana kallansu har zuciyarta bataji komai ba na haushi ko jin zafin rashin daukan wayar harma da fadan da ma'aikacin tashar yayi mata Dan kuwa Babu lefi a cikinsu saima uzuri datakewa kowa Wanda shine abin dayafi bawa mutane Daman cutatar da ita ko acan kauye sbd komai kayi mata a rayuwa tanai Maka uzuri Bata fushi Komai girman cutar da zakai mata.
Zaune suke cikin duhu da rashin mafita hakanan ta miqe tayi alwala a gurin tayi sallah har lokacin AmatulMaleek a kwance take jikinta yafara tsanani sosai Abdulhameed ma tini Shima yafara kamuwa da zazzabin sbd wahalar yunwa.
Har Akai ishai Babu Wani bayanin biyo sakon da suka tura da kira Dan haka ta Yanke komawarta da bin motar asuba Kila Wani uzurin ya Hana Abeeda ganin sakon Dan haka bazasu cigaba da damunta da Kiran ba akwai takurawa ga Hakan ta sani.
Ruwa kawai ta ringa bawa Abdulhameed da AmatulMaleek har kusan asuba anan suka kwana cikin sanyi a sararin iska ga sauri da duhu harma da qwari kala kala Dan haka asuba nayi sallah kawai tayi suka miqe Dan shiga layin bin motar komawa.
Koda gari ya fara haske AmatulMaleek kaman bazata tashi ba hakama Abdulhameed Dan haka sai hankalinta ya rabu biyu ga tafiyar sbd bazasu iya bin doguwar hanya a Hakan Amma Kuma Babu zabi na yanda zatayi Dan haka tayi shiru a cikin sanyin jiki Dana zuciya idanuwanta sunyi jajir da damuwar Dake riqe da zuciyarta.
Isowar ma'aikacin tashar na jiya ne gurinta Yana qwala kiranta ya Sakata dagowa ahankali cikin sanyi ta Dan kallesa tareda sauke Kai tana gaidasa da girmamawa.
Da farin cikin dayake tareda takaici ya kalleta Yana cewa tayi Maza tazo ana son magana da ita anbiyo sakon da kira yanzu.
Numfashi ta sauke me dumi kafin ta fito layin a sanyaye ta biyosa zuwa inda ba hayaniya ya miqa mata wayar wadda daidai lokacin aka sake kira.
Cikin nutsuwa ta Bude Baki tayi sallama nauyin zuciyarta na raguwa Jin amsa sallamar Abeeda cikin Wani irin nutsuwa ta wainda suke cikin duk wata ni'imar rayuwar duniya.
Jin muryar Asmau ya Saka Madame abeeda sauke ajiyar zuciya a hankali tareda sake Bude Baki tace
"Asmau kece??
"Meyesa Baki kirani da wayarki ba?
Yaushe kikazo?
Sai yanzu nake duba sakon sbd Banda time na duba wayar rasuwar da Akai ya Saka Sam bana samun Hutu yanda ya kamata.
Shiru sukai dukkaninsu sbd kowannensu da Wani girmamman quncin dayake mamaye cikin ransa Amma baisan tayaya zai tinkari Dan uwansa ba sbd Nisan daya shiga cikin kusancinsu da tsananin kaunarsu
Numfashi mara sauti maamah ta sake saukewa ahankali kafin ta Dan saki murmushi me sanyi tace
"Eh nice,jiya nazo sbd labarin rasuwar ta alhaji babba danaji daga bakin Dan gidan kawu bello dayake Dan shiga birni shine yazo ya sanar mun,
Allah yaji qansa yayi masa Rahama,
Munata damunki da kira ga fama da jamaa Anata zuwa gaisuwa."
Numfashi Madame abeeda ta sauke kafin tace
"Ba komai yanzu ku Jira ga driver Nan zan Aiko yazo ya dauko ku keda yaran ai gwara da bakiyi saurin juyawaba Ina buqatan ki Asmau,
Ina tsananin buqatan nawa a kusa Dani"
Shiru suka sake yi jikin Maamah na sanyi ita Kuma acan nata bangaren wasu zafafan hawayen da babu Wanda ya taba ganinta dasu ne suka taru a cikin idanuwanta Amma Bata bari sun taba saukowa kan fuskartaba bare yau din Dan haka ta sake hadiyesu cikin dauriya da karfin zuciya kafin ta kashe wayar ta ajiye gefenta sbd Asmau kamar rauninta ce sbd Bata iya boye mata komai duk dauriya da jarumtarta.
Ita kanta Asmau sanyi jarumtarta ke Neman yi Dan haka ta daure batareda ta dago ba tasake yi masa godiya tana koma gurin yaranta da suka koma kamar mahaukatan almajirai.
Zaunawa tayi tareda zuba musu idanuwanta da suke boye duk Wani abinda yake cin Rai da zuciyarta tana musu fatan hayewa matakin nasara a duk inda suke rayuwarsu.
Zaman jigum tayi tana sauke kanta qasa da jiran tsammanin Kuma Ina rayuwa da kaddara zatai dasu itada yayanta a gaba.
Zaman jiran awa kusan Daya da Rabi tayi zuwa biyu kafin Daya daga cikin Mahaukatan motocin gidan ASH TALBA ta iso tashar daukanta.
Da farko numbern da aka bawa drivern yazo