Showing 96001 words to 99000 words out of 152002 words
Chapter 33 - AMATULMALEEK COMPLETED BY Mamuhugee.txt
cewa
"Ni kaddarata ta haihuwa acikin zuriar masu tosashen Kai ce,
Babu abinda yake cikin kanka daga mata Se mata,
Dana San haka zaka zama da a hannun ubanka zan barka ka tashi acan sai nasan baqin cikin labarin lalacewanka kawai zan riqa ji batareda nagani ba baqin cikin yamun yawa,
Uban meye ne Amatun take dashi da ka nace ka rufe ido da tosashiyar qwaqwalwanka harka qare da qafa Daya duk akan macen da gata Nan kanajin kana gani Se Hange shi Wanda ya rabaka da qafar Daya Ya mallaketa,
Duk wannan rashin hakurin naka da masifaffen kwadayin matan ya Saka Amatu ta samu Isa ga Daman zama ASH din,
Da ka hadiye kwadayinka da duk bamu zo Nan inda muke ba aynzu......
"Mum wlh yaudarata Husnah tayi nikuma kaya zan dauka a mansion din,wlh Bazan barta ba Husnah din ai......
"Kamun shiru da toshewan basirarka ka barni naji da komai,
Husnah dinma tafika hankali da tinani tinda har tasan ta inda zata cutatar da wadda bataso,
Kai kuwa idonka ya rufe maimakon data tura maka sakon ka tattara komai ka kaiwa ASH ka nuna masa Dan dawo da yardarsa gurinka ya yafe Maka akan abinda ya faru Baya Amma Se Kawai ka kwashi qafafunka kaje lalata masa mata ko? Ta barka da Arziki ka raso qafa Daya gurin rashin danganarka"
Shiru yayi maganganun mum Aisha din na cin zuciyarsa suna qara masa damuwa da baqin ciki me qarfi.
Katse shirunsa tayi da cewa
"Karka kuskura naji kayi Wani abun akan kowa,
Kabarni Daya bayan Daya kowa zaisan ya tabani, Husnah zatasan da was takeyi Dan ko uwarta nafi qarfin iskancinta bare ita,ba ta iya Kai labarin Azo ASH Baya gida ba?itama nata labarin zata samu bayan na fasa bakinta da kanta"
Sai alokacin ya sake dagowa ya Kalli mum din Yana Dan Jin sanyi a ransa Dan yasan ba sauki Husnah zata gurbi abinda tai masa.
Kasa zama tayi asibitin ta tattaro ta dawo gida Dan zuciyarta tafasan datakeyi ko Naufal din zata iya rufewa da duka duk girmansa da jinyar dayake kuwa sbd abinda takeci ya wuce bacin Rai tafasan zuciya takeyi.
Ko data dawo gida Babu ma Wanda yasan ta dawo bayan su khaltume ta shige bedroom dinta tana Ciro wayarta numbern Husnah ta Nemo ta danna mata kira zuciyarta na tsalle Dan kuwa da Husnah na gidan ayau da wlh sedai ASH ya Tararda Rabin Husnah din badai cikakkiyar ta ba Kuma ta fada masa abinda zai Sakasa yiwa shegiya auren Sadaka da duk Wanda ya samu.
Husnah na ganin Kiran mum Aisha taji gabanta ya Dan Fadi kaman bazata dauka ba sai kuka ta daure ta dauka cikin rashin son magana sosai.
Ko gaisuwarta mum Aisha Bata amsa ba tace
"Ki tattara komai naki ki dawo Abuja kafin ASH ya dawo Dan idan ya Riga ki dawowa shine zai fara Jin abinda kikai na turawa Amatu Naufal Dan ya la.......
Tashi zaune Husnah tayi da sauri daga kwancen datake tana satar kallan su mummyn porthcrt Dake tareda ita kafin ta miqe ta nufi bedroom ta shige tareda tura kofar tana cewa
"Mum Aisha ni Kuma?
Ni bangane me kike nufi ba?
Wane Uncle Naufal din?
Tsoki mara sauti mum Aisha ta sake tareda cewa
"Ki zauna porthcrt jiran bayani har ASH ya rigaki dawowa kisha mamakina"...kashe wayarta tayi tareda jefar da wayar Dan kuwa saita Maida Husnah abin tausayi da wannan maganar da ita zatai amfani ta juya kusan kowa a gidan yanda takeso.
*********
AmatulMaleek kuwa jikinta ya sake warwarewa kaman ma Bata taba yimata komaiba harda dinki Dan haka ta koma zuwa school Kuma ta Dan sakewarta sbd anty Farha na gidan Sam Bata barinta shiga damuwa ko tinanin dayake sanyaya jikinta duk da ta fahimci sosai maamah ta sauyawa Amatun takuma San dalilinta Dan kusan yanzu itace sirrin Amatun da maamah Dan ita kanta maamah din zuwa yanzu dole ta yarda Farha na kaunar Amatu da gaske haka Kuma hankalinta ya kwanta da alaqarsu sedai Sam taqi yarda da duk wata nasiha ko maganar da Farha ke Mata akan auren Amatun qarshe ma doka da rantsuwa tayi akan kar a sake Mata maganar duk da Amatu batama San anty Farha na kokarin yiwa maamah nasiha akan lamarin ba.
Ganin yanda Farha ta dauki auren Amatun da mahimmanci sai ta sauya mata kwata kwata ko fuska ta Dena sake mata Kuma daga Farha din har Amatun sun fahimci sauyin maamah din sai jikin Amatun yayi sanyi ta sake shiga damuwa.
Duk zata school tare suke fita da anty Farha su ajeta spa dinta su wuce idan sun dawo saisu biyo su dauketa su dawo gida.
A kwanakin duk da tana cikin damuwan maamah wasu lokutan Hakan Bai Hana hutun datake samu bayyana ba ga Kuma kulawa sosai da anty Farha ke Bata,
Komai nata ya sake upgrading zuwa babban matsayi Dan komai nata kusan an sauya ya sake zuwa babba,
Designer ne take bugu yanda ya kamata,kudinsu maamah Bata saniba da sai ta kusan kwanciya asibiti sbd damuwa,ita kanta Amatun bawai kudaden da ake kashe mata din ta saniba komai haka ake kawowa anty Farha ta jerasu inda ya kamata komai ya zauna.
Har wannan lokacin tinda ya tafi basuyi magana ba Dan batama kunna wayarta Se dare Kokuma idan zatai magana dasu Abdul ko Haydar Dake cikin farin cikin tashin mahaifiyarsa.
Tana kunnawa zataga text dinsa zata karanta ta rubuta masa lafiyanta kalau da thank you kawai ta sake kashe wayar.
A zuciyarta Babu ranar da tinaninsa Baya azabtar da ita Amma Kuma tana Jin jikinta na sanyi tareda mutuwa tinawa da a gurin matarsa dayake tsananin so ya tafi Dan murna da farin cikin son kasancewa da ita.
Ita kanta anty Farha Bata damu da rashin son kunna wayan da Amatun keyi Dan haka suka share suna abubuwan Dake gabansu kawai.
A wannan gabar maamah tafara matsuwa da Farha ta tafi sbd ta samu cikakkiyar Daman magana da Amatun akan abinda takeso tai mata magana kafin ASH ya dawo.
*****Husnah a porthcrt ta shiga tsananin tsoro da firgicin maganar mum Aisha Dan haka ta tattara zat dawo Amma su mommyn can din suka hanata dawowa Dan haka hankalinta yayi mummunan tashi Amma ba Daman fadan abinda yasa takeson komawan,
Tayita Kiran numbern mum Aisha Amma Bata dauka idan kira 100 zatai mata,
Hankalinta Bai tashiba tafara Neman haukacewa sai datai magana da Dad dinta taji a satin ze dawo Dan haka ta tattara ta Siya ticket sedai su mummyn suka wayi gari ta gudu Abuja Dan kuwa hankalinta ma Baya jikinta idan ba Isa tayi Abujan ba.
Ko data iso gidan ba kowa Se maamah da masu aiki Dan haka ko zama batai ba ta sake kiran mum Aisha Amma Bata dauka ba Dan haka ta zauna bakin gadonta jikinta na rawa ta tura mata sakon cewan ko dawo tana gida.
Tafiyar sakon befi da mintina biyu ba mum Aisha Tayo mata reply da sunan asibitin da suke.
Kallan sakon tayi a karo na babu adadi tana tinanin mezataje tayi acan din.
Shiru tayi tana Jin zuciyarta na shiga damuwa da tsoron maganar ta Isa kunnen Dad din duk da tasan bazai iya fushi da ita ba ko mata Wani hukuncin akan Amatu da ba 'yarsa ba Amma Kuma batason yaji sbd Haydar ze tsaneta, Haydar ze iya fushi da ita Yama shareta.
Miqewa tayi tana daukan wayarta kawai Se qaramar chain handbag ta nufi kofa ta fito ta sauka ta fice batareda Maamah ma tasan ficewanta ba.
Da kanta ta karbi key taja motan sbd Bata buqatan kowa da zai iya ji Ko da tsautsayi cewan tanada Saka hannu a cikin maganar fyaden Amatu.
Tana ficewa mansion din su Amatu motansu na shigowa Amma Sam Batama lura dasu ba kaman yanda Suma Basu dauka itace ta dawo harta fita dinba.
###MAMUH#
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
54
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER
08142800199
07068558096
************
Ko data Isa asibitin room number din dake tareda sunan asibitin cikin text din mum Aisha ta nufa gabanta na Dan faduwa tana Kuma fatan mum Aisha dince tayi hadarin motan da bama zata iya magana ba bare fadawa Dad dinta abinda takeson fadan.
Tana tsayawa kofan dakin Kai tsaye knocking tayi tareda Bude kofan dakin ta tura ta shiga idanuwanta na fara sauka kan Naufal Dake zaune Shima kofan yake kalla idanuwansa jajir da zafin zuciya da baqin cikin ganinta kaman zai tashi ya raba da ranta yakeji.
Rawa hannuwanta suka fara ta shigo tareda rufe kofar tana kallan Naufal jikinta na sake daukan rawan tashin hankalin ganinsa da qafa Daya.
Tsoro ne me qarfin gaske ya kamata ganin qafarsa Daya yanda take din Dan haka tayi saurin juyawa bazata iya kalla ba tsoro me tsananin gaske takeji Dan bata Saba ganin irin wannan tashin hankalinba.
Damqota mum Aisha tayi cikin zafin Rai tareda dawo da ita ta jefata gadon Naufal din gurin qafar Dan ta Gani da kyau.
Hawaye Husnah tafara jikin na sake daukan rawa sosai hakama bugun zuciyarta na tsananta har cikin zuciyarta tsoron ganin qafar takeyi hankalinta ya tashi sosai har ta kasa magana sai cewa tayi
"Mum Aisha banason Gani Ina tsoron ganin qafar uncle Naufal,tsoro nakeji banson Gani,Ina qafarsa Daya take Dan Allah karki…....
Cikin zafinta daya kasa dannuwa da tsananin bacin Rai Mai hade da baqin ciki mum Aisha ta falla mata Wani gigitaccen Marin Daya Saka Husnah fadawa kan qafar Naufal din jikinta na rawa tayi saurin janyewa daga qafar a rikice da azabar Marin sedai kafin ta qarasa janyewa mum Aisha ta sake dafe kanta a gurin kafar tana cewa
"Ki Kalli qafar da kyau yanda tsoro ze juyar Miki da qaramar qwaqwalwanki kafin ki fuskanci hukuncin abinda kikai daga Wanda ya Yanke masa qafa akan abinda kece kika haddasa komai"
Rawar masifaffen tashin hankali da firgici jikin Husnah ya dauka tana hawaye tana rintse idanuwanta daga kallan dungun qafar Naufal din dake fuskarta ta fashe da Wani irin kuka tana cewa
"Mum Aisha Dan Allah kiyi hakuri wlh zan Suma idan Ina ganin wannan qafar Dan Allah ki barni na tafi gida"
Cikin baqin ciki da takaici Naufal ya motsa qafar ya tura mata a fuska Yana buge bakinta da dungun duk da Yana Dan Jin zafi Amma baqin ciki ya hanasa Jin zafin sosai.
Kuka sosai Husnah keyi tana Neman shaqewa kafin mum Aisha ta dagota ta zubar qasa tana kallanta cikin zafin zuciya tace
"Yanda kika ga ya rasa qafarsa Daya akan abinda yayi to idan ASH din yaji kece kika turasa me kike tinanin ze Miki?
Kinsan ASH ne da kansa ya yankewa Naufal din kafa akan zuwansa mansion gurin Amatu kawai,
To idan shi ya Yanke kafarsa Dan yaje mata ke da kika aikasa kika ringa kiransa kina cewa yaje gidan me zaayi Miki?
Ke harma rigimar farko ta zuwan Naufal din dakinsu Amatun kece kikai mixing drink dinsa ma Dan yajewa Amatun........
Cikin masifaffen tashin hankali Husnah ta dago jajayen idanuwanta ta Kalli mum din muryanta na rawa tace
"Wallahi tallahi banyi Hakan ba,ba nice ba,ban.....
"Kece kikasan ba kece ba mu bamu San Hakanba, ASH ma baisan Hakan ba..."
Rawa jikinta ya sake dauka hawayenta na qafewa tace
"Mum Aisha wlh banyi Hakan ba, Dad dina ba bazai taba yarda da zanyi Hakan ba,
Wannan na bayan ne kawai nasan na cewa uncle Naufal din yaje mansion ba kowa Se Amatun ya mata abinda yakeso....
Muryarta taji tana maimaita abinda ta fada yanzu a wayar Naufal din yayi playing recording din maganar tata.
Juyowa tayi ta kallesa idanuwanta na sake cikowa da wasu hawayen jikinta na mutuwa gaba Daya,
Kan mum Aisha ta dawo da kallanta hawayenta na saukowa ta Bude Baki a sanyaye tace
"Mum Aisha Dad dina bazai yarda da na aikata Hakanba,
Dad dina bazai iya yanka qafana ba kaman na uncle Naufal,
Dad dina bazai iya ko ganin bacin Rai na na bare yanka qafana....
Katseta mum Aisha din tayi da cewa
"Idan shine ya haifeki ba,
Idan shine ya haifeki daga tsatsonsa shine bazai iya Miki Hakan ba Amma tinda mijin uwarki ne kawai Kuma qanin mahaifinki mezai Hanasa ko aurar dake ga Daya daga cikin securities dinsa idan har bazai iya yanka qafarki ba bayan kin tura namiji yayiwa matarsa fyade,matarma wadda yakeso fiyeda Taki uwar Daya rufe babinta a rayuwarsa.......
Zuru Husnah tayi tana kallan mum Aisha da idanuwanta batareda ta fahimci Kalma ko Daya datake fada ba daga kalmominta na farko dasuka shiga kunnuwanta.
Naufal ne ya miqa hannu ya jijjigata daga zaunen dayake Yana cewa
"Abinda ake nufi ana shine ba ASH ne Wanda ya haifeki ba auran mamanki yayi dake a hannunta Dan rufa muku asiri ya Baki sunansa....""
Bata gane abinda suke fada ahankali taji jinta na daukewa bakinsu kawai take ganin suna motsawa suna fadan maganganun da Sam batajin komai.
Maimaita mata kalmomin suka ringa yi Daya bayan Daya har sai da jinta ya dawo zantukan suka ringa shiga kunnuwanta suna ratsasu zuwa cikin kanta,
Maimakon su Isa ga zuciyarta cikin kanta suke wucewa suna juya kan ahankali.
Zubewa tayi qasa take Neman yi mum Aisha ta tareda tareda kama hannunta kaman makauniyar da akewa jagora.
Harabar asibitin ta fito da ita Babu mutane sosai kowa abinda yake gabansa yakeyi.
Motarta ta Bude tareda kamata ta shigar da ita ta zaunar a mazaunin driver tareda saka key ta tada motar ta kama hannunta ta Dora mata kan steering ta kalleta tace
"Kije gida"
Rufe mata kofar motar tayi tareda juyawa ta koma ciki Dan tasan Babu yanda Husnah din zata iya Kai kanta gida a wannan halin itama yau zata dandani abinda ake nufi da azaban hadarin data saka Naufal a ciki ya rasa qafa ita Kuma kila ran zata rasa gaba Daya.
Tana juyawa Husnah taja motar a cikin mummunan gudun Daya Saka securities din asibitin tareta suka hanata fita sbd tsaro suka hau bincike motarta tana zaune kaman wadda Babu komai a tareda da ita bayan numfashin datake shaqanta kaman tana shaqan gas take ji sbd ficewa hayyaci.
Suna gamawa suka hanata fita Saida ta Dan dawo hayyacinta suka Bude mata gate ta ja motar cikin Wani irin tsananin gudun gaske me qarfi ta hau titi ko ganin gabanta Batayi sosai.
Ko data Isa mansion din TALBAs ganinta yafara qaranci sosai Dan haka parking dinma Bata qarasaba ta fito motar tana hada hanya ta nufi cikin gidan.
Step din farko na stairs data Dora kafarta zata hau Sam sakon Naufal ya shigo wayarta Wanda yasata dubawa da idanuwanta Bata Gani sosai.
"Idan har kin samu Isa lafiya karki manta wadda ta fada Miki waye babanki itace takeda abin fadawa ASH TALBA abinda ya samu matarsa waye sanadi"
Qurawa sakon idanuwanta tayi hannuwanta na rawa sosai sbd idan ta fahimci abinda suke nufi shine idan ta fada Wanda ya fada mata ita ba yar ASH bace zasu fada masa abinda tayi.
Da dafa Bango ta Isa palon saman seda zuciyarta Dake kokarin bugawa ta kasa riqe abinda takeson riqewa ta Isa dakinta ba shiri Bata saniba ta zube tsakiyan palon tareda fasa Wani irin ihun Dayake dauke da tsananin girman baqin cikin da zuciyarta ke Neman fashewa akansa...
Gaba Daya mansion din sautin ihun nata ya dauka Wanda ya Saka kowa fitowa hankali tashe musamman Amatu da anty Farha da bedroom din Amatun yake palon sosai ihun yafi shiga kunnuwansu.
Maamah ma dasu khaltume duk a rikice sukayo saman sedai Koda kowa ya iso Husnah din ta sume a gurin hawayen Dake cikin idanuwanta suna gangarowa Babu abinda yake motsi nata.
Amatu ce tayi kanta cikin kulawa ta fara tabata tana ambatar sunanta cikin fargaban abinda ya sameta.
Maamah dasu khaltume kuwa harma da anty Farha Babu abinda yazo ransu Se Madame abeeda lokaci yayi ta cika kawai Dan haka kowa jikinsa ya dauki bari musamman maamah dataji zuciyarta na Neman tsayawa daga aiki tayi Baya Amatu ta miqe da sauri ta tareta tana kiranta a tsorace cikin damuwa da tsananin kulawa.
Zaunar da maamh din tayi su Kuma su khaltume suka kama Husnah din itama suka Kai kan kujera tareda debo ruwa suna zuba make Amma Sam ko motsawa Batayi.
Rawa jikin maamah ya sake dauka ta miqe da kanta ta karbi ruwan tana zubawa Husnah din Amma Sam Babu alaman zaa sameta.
Farha ce cikin tashin hankali ta dauko wayarta ta kira likita Amma Sam Bata shiga dan haka kawai suka kwasheta zuwa asibiti.
Maamah da Husnah dinne a Baya anty Farha na gaba Amatu ke driving sbd Basu tsaya cewa driver yakaisu ba.
Asibitin da suke zuwa aka nufa da ita suna Isa aka amsheta da gaggawa sbd kusan lamarin ya sake tsananta Dan numfashinta ma ya tsaya cak.
Maamah ma kusan dole suka buqaci likita ya dubata Dan kuwa itama zubewan take Neman yi Dan itama Amatun zuwa lokacin ta saddaqar da cewan Wani abu ya samu Madame abeeda ne.
Bayan an duba maamah itama an Bata gado ta huta na awanni hakama Husnah gadon aka Bata
Shiru Amatu tayi sai alokacin jikinta yayi sanyi da damuwan halinda ASH yake ciki idan Wani abin ne ya samu Madame abeeda.
Numfashi ta sauke ahankali tana kallan wayar anty Farha dake hannunta tanajin tanason Jin muryarsa Dan sanyaya damuwansa sedai zataso da tata wayar zata kirasa Dan haka ta danne abinda take ji a zuciyarta idan ta koma gida ta kirasa.
##MAMUH#
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
55
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK