Showing 87001 words to 90000 words out of 152002 words
Chapter 30 - AMATULMALEEK COMPLETED BY Mamuhugee.txt
fara qal me taushi ya zira takalmansa Yana qamshinsa me Nutsuwa da sanyi musamman yau din da kusan komai nasa ya sake nutsuwa da Wani irin kamewan class.
Wayarsa ya nufa ya dauki Daya ya kunna,
Tana kawowa wayar massage Kai tsaye ya rubutawa Jameel akan little Abeeda na buqatan likita yanzu yanzu.
Yana tura sakon ya mayarda wayar ya sake kashewa gaba Daya sbd Baya buqatan komai ko damuwa shi kansa kansa na buqatan hucewa daga abinda ya shigesa me girma a daren.
Goshinta ahankali ya shafa tareda kissing lips dinta da suka Dan Bushe mata duk da ruwan Daya ringa dauko mata a palonsa cikin Fridge tana sha.
Gaba Daya Daren Bai rintsa ba hakama itama baccin datake samu a yanken duk da wahala ne.
Bayan ficewansa sallah motsawa tayi ahankali tareda Bude idanuwanta dasuka kumbura sosai ko Gani sosai Batayi,
Babu inda Baya tsananin ciwo sosai a jikinta hakama zazzabinta har Wani fizga jikinta keyi.
Daqyar ta iya dafawa ta tashi zaune tana ganin jiri da radadi sosai a jikinta Amma batajin zata bari ya dawo tana dakin Koda da rarrafe ne dakinta takeson komawa Dan idan ya dawo Babu inda zai bari ta fita kowa zai wayi gari gidan yasan meya faru,
Maamah zata iya shiga mawuyacin halinda zata Sakata a tsaka me wuya Dan haka komai azaban datake ciki zata koma dakinta.
Daqyar ta iya saukowa gadon ta Isa inda wayarta take ta dauka Dan tana tsananin buqatan anty Farha kawai,
Hijab dinta ta Saka ko Gani Bata yi sosai tana dafa Bango ta fito,
Duk taku Daya idan tayi tanajin azaban datafi karfin kanta da kirjinta Amma hakanan ta daure tana rintse idanuwanta tana budewa daqyar ko hanyar Bata Gani sosai ta samu ta Isa bedroom dinta ta shiga ta tura kofan tareda faduwa qasa da rarrafe ta Isa toilet ta shiga ruwan safi tana fashewa da kukan radadi da azaban datake ji sosai.
Kuka takeyi sosai a toilet din takasa ko motsawa cikin ruwan taimako take nema Amma batasan waye zai taimaketa a wannan halin da ita kanta kunyar tinawa da abinda ya farun takeyi bare Wani yaji.
Jajir idanuwanta da farar fuskarta sukai tana kokarin cusa kanta cikin qafafunta taci gaba da kukan taji an Bude kofan toilet din Kai tsaye tareda shigowa.....
Cikin mummunan tashin hankali Daya dakatar da bugun zuciyarta ta dago Dan tasan maamah ce sedai ganin waye ya Sanyata fasa kukan da batasan na Menene ba tana sauke kanta qasa jikinta na tsananta rawa.
Qarasowa yayi ahankali har inda take Yana kallanta da tsananin Jin kukanta har ranta ya na isowa ya cirota daga ruwan gaba Daya Yana kallan fuskanta data qi kallansa tana cigaba da kukanta.
Daqyar ya iya samun kuzari tasa ya fita tayi wankan tsarkin itama ta daura towel ta kasa fitowa seda ya dawo ya dauketa ya fito da ita ya zaunar da kansa ya Saka mata doguwar Riga mara nauyi ba bra ba komai ta Saka rigar ya Saka mata hijab tayi sallah tana idarwa daga zaunen ta Bude Baki daqyar ta rokesa akan ya tafi.
Kallanta yayi zaiy magana ta fasa kuka tana sake rokonsa akan ya tafi.
Baida alaman tafiya likitan Daya Saka a Aiko yake jiran yazo ya duba sbd sosai take cikin azaban Jin jikin har lokacin rawa sosai jikinta keyi.
Kukan data ringa masa tana Neman shidewa ya sanyasa ficewa ya koma dakinsa dan kiran mr Jameel yaji abinda ya Hana likitocin zuwa har lokacin bayan tana Jin jikin sosai.
Bayan fitansa zubewa tayi qasan kwance tana kuka mara sauti jikinta na Jijjiga komai na jikinta kaman ana niqasa takeji musamman qasanta Jin takeyi azaban datake tai mata girma Dan haka kukanta yake sake tsananta.
Mr Jameel Daya kwana zaune Yana ganin sakon ASH akan buqatan likita take ya ajiye maganar rawar jikin isar masa da sakon Greece ya daga wayarsa ya kira asibitin dasuke komai ya buqaci likita mace da namiji.
Yana gama waya da asibitin Farha ya kira itama kusan kwananta Rabi da Rabi ne Dan haka tana ganin kiransa bayan asubar ta dauka da sauri tanason Jin idan yau zasu wuce kokuwa.
Gaisawa kawai sukai ya sanar mata da Amatu ASH ya buqaci a aikowa likitoci.
Dagashi har ita kowa da tinanin dayake ransa Amma dai sbd tsaro da Hana a Saka Amatun tsaka me wuya yace Farha din ta shirya gashinan yakusa isowa gidanta zai dauketa yakaita ta tsayawa Amatun idanma Wani matsalan ne ya sameta na rashin lfy.
Ko da suka iso Mansion din qarfe 6 da mintina Dan haka har Farha ta shigo ta Isa dakin Amatu Babu Wanda ma yakeda alaman tashi a jamaar gidan bayan su karima da suka fito Dan fara aiki.
Gaisawa kawai sukai ta wuce sama zuwa bedroom din Amatun Kai tsaye daidai ASH din ya fito lokacin ya sake dawowa ya dubata a karo na biyu.
Gaidasa Farha tayi cikin girmamawa idanuwanta na qasa
Ya masa Kai tsaye Yana wucewa tareda barin dakin da qamshinsa.
Shigowa tayi ko zama batai ba Dr beeba ta shigo tareda nurse Daya karima Tayi musu iso zuwa dakin batareda sunsan abinda yake faruwa ba.
Anty Farha kallo daya tayiwa Amatun ta fahimci abinda ya faru da ita Dan haka cikin sanyin Daya cika zuciyarta ta qaraso tana kama Amatun ta tashi zaune Amma Bata iya zama Dan haka Dr beeba ta qaraso bayan anty Farha ta rufe dakin bayan fitan karima.
Ita kanta Dr beeba Babu Shan wuya ta fahimci abinda ya faru Dan haka tace sai sun tafi da Amatun asibiti sun mata stitches.
Kuka mara sauti Amatun ta sake fashewa dashi tana jikin anty Farha wadda ke rarrashinta kada asan halinda take ciki musamman Husnah Dake kusa.
Anty Farha ce ta sanar da ASH abinda dr beeba ta ce.
Ga mamakinta shine da kansa yazo ya dauko Amatun bayan sun fice ya fito da ita ta kofan palonsa da Babu me ganinsa idan zai fita Yana fitowa mota na kofan palon yake shigewa
Itama ta Nan ya fito da ita ya shigar da ita mota Mr Jameel ne yau yaja motan suka Isa asibiti cikin qanqanin lokaci.
Isansu asibiti Babu Bata lokaci Akai mata dinkin Wanda ya sumar da ita bayan kukan azaba da wahalan datasha.
Allurai Akai mata tareda daura mata ruwa Bai dadeba ya qare sai lokacin ta dan farfado suka dawo gida lokacin karfe 8 na safe ya wuce Dan haka Koda suka iso ta kofan da aka fita da ita ta Nan suka ya shigo da ita tana hawaye ta nuna masa dakinta zata harya kaita ya kwantar ya rufeta ya fice Babu Wanda ya fito.
Kai tsaye bedroom dinsa ya koma Shima ya kwanta sbd baccin dazai samu ya koma shima wanda gaba Daya Bai rintsaba tin jiyan.
Wanka yayi da ruwan zafi sosai jikinsa ya sake hakama shi kansa Saida akai dressing na hannunsa.
Kaya marasa nauyi ya Saka ya shige bargon ya kwanta yaja sauke ajiyan zuciya da numfashi me sanyi.
A can dakinta kuwa baccin wahala ne ya dauketa itama anty Farha brush tayi ta sauko qasa taci abinci a kitchen ta nufi dakin maamah ta tarar da ita Bata tashi ba har lokacin Dan haka ta qyaleta ta koma dakin Amatun itama ta Haye gadon ta kwanta tayi baccin da bata samu yi ba Tin dare da Jameel ya sanar mata da sakon tashin Madame Abeeda Wanda haryanxu Bai sanarwa da ASH dinba ganin tashin hankalin da suka tashi dashi yanzu Kuma yabarsa ya huta musamman ganinsa da nasa raunin a hannu zai bari sai sun Isa office cikin Nutsuwa ya sanar masa da sakon duk da ya kamata ace an isar da wuri.
Kowa bacci yakeyi cikin mutanen gidan tsit kakeji bayan su karima da khaltume Dake aikinsu na tsaftace gidan da aikin breakfast kafin mutanen gidan su tashi,
Maamah ce ta fara tashi qarfe Tara da mintina ta shiga wanka tayi ta fito ta shirya tana kokarin fitowa Palo Farida ta shigo da breakfast dinta ta jiye mata a palo tareda gaidata ta juya ta fice.
Zaunawa tayi tana duba wayarta da sakwannin MTN sukai mata yawa tana son ragewa ta ajiye kafin ta gama karyawa tukuna idan Amatu ta dawo makaranta ta goge mata su ta dakatar mata da shigowansu.
Abincinta tafara ci hankali kwance tana Dan kallan tv da Farida ta kunna da tana sharan palon da safe.
Yau kusan kowa lattin fitowa yayi Se kusan 10 Husnah ta fito shirye cikin qananun kaya skinny jeans da black Fendi sweatshirt kanta daure da veil tana kokarin kunna wayanta Daya kwana kashe.
Sosai tayi mamakin ganin fitowan anty Farha daga bedroom din Amatu a lokacin dan kuwa garesu safiya ce karfe goman.
##MAMUH#
*_AMATULMALEEK_*
By Mamuhgee
And
*_YANCI DA RAYUWA_*
By Hafsat Rano
Na kudi ne
For more page ku biya
500 for littafi Daya
1k for duka books din biyu
at👇
0022419171 access bank Maryam sani
09033181070
YouTube channel and Meerah Herbs present you the sweetest story#
AMATULMALEEK
Mamuhgee
#ZafafaBiyar
49
*INA MATA,MANYAN MATA,MATAN DASUKA SAN KANSU,MATA MASU DARAJA,MATA MASU BUQATAN GYARA DA KULAWA DA KANSU???*
*SHIN KUNSAN SHAHARARRIYAR ME MAGANIN KUSAN DUKA MATSALOLIN MATA DASUKE FAMA DASU HARMA DA WASU DAGA CIKIN NA MAZAN WATO MEERAH HERBS* 100% Natural herbs💯🔥👍
*Amarya,budurwa,uwargida,bazawara da duk ma macenda take buqtaan gyara da ingantattun kaya karki wuce kayan Meerah Herbs sbd mun tabbatarda ingancinsu kafin tallata muku💯👍*
MAGANIN SANYI
MAGANIN NONO
MAGANIN HIPS
MAGANIN SLIMMING
MAGANIN NANKARWA
GYARAN AMARE
SET MAIJEGO
MALLAKA
SUBULU DA MAYUKA NA GYARAN JIKI
TURAREN WUTA
MATSI
MAGANIN NI'IMA
BACK TO VIRGIN SET
INFECTION FLUSHER
08142800199
07068558096
*****************
Kallan da Husnah takewa anty Farha ya Saka anty Farha din kallanta tana sake fuska da kulawa tace
"Husnah kinfito kenan,barka da safiya,Yaya gidan?"
Cikin Dan kokarin boye mamakinta ta amsa da cewa
"Barka da safiya anty Farha,yau sammako kikai kenan keda ya kamata ki huta anty Farha kinyi hidima jiya"
Dariya anty Farha tayi tana qarasa zama a palon daukeda cup din custard me zafi data Saka karima ta hada mata tace
"Wlh Hutu Nan Ina buqatansa haryanxu Amma matar gidan Nan taku ce ba lafiya sosai shiyasa kika Ganni da sassafe a gidan,Amma inshallah tana Dan warwarewa zan tafi Nima na huta"
Kofar bedroom din Amatu Husnah ta kalla cikin takaici da mamakin yanda anty Farha din ta ambaci Amatun wai da matar gidan da Dan mamaki tace
"Me ya sameta ne?
Lafiya kalau fa ta kwanta jiyan da daddare.
Murmushi anty Farha tayi zatai magana kenan mum Aisha ta shigo palon maamah na bayanta dukkaninsu kallan Farha din sukeyi da mamaki dakuma ganin yanda Husnah itama take tsaye da mamakin tana jiran amasan anty Farha din.
Ita kanta kallansu tayi duk da mamakin ganin yanda kowannensu ke kallanta kaman wainda Basu taba ganinta ba.
Tamkar zakunan dasuka ga nama haka suke kallanta kafin maamah ta Dan juya ta Kalli hanyar dakin Amatu tana sake dawo da kallanta kan Farha wadda ta nutsu ta hadiye maganarta ta saki murmushi tana kawar da tinaninsu duka akan koma me suke tinani da son jin duk da Babu Wanda ko a giyar hauka acikinsu ya kawo tinanin da itama takeyi din akan nasu tinani ta Bude Baki fuska a sake Kuma cikin girmamawa ta gaida maamah kafin ta gaida Mum Aisha tana cewa
"Amatu ce ta kwana ba lafiya shine nayi sammakon zuwa sbd jiya Koda muka rabu Daman tana Jin zazzabi sosai da ciwon mara shine nayi sammakon zuwa da likita ta dubata Amma taji sauki"
Gaba dayansu a tare suke sake juyawa suka kalli kofan dakin Amatun maamah ma abinda Husnah ta fada ta maimaita cewa
"Lafiya kalau fa na rabu da ita jiyan da dare,wane ciwon mara Kuma a tsakiyan wata?
Mum Aisha dakin ta zubawa idanuwanta Bata ce komai ba kafin ta juya ta nufi bedroom din Kai tsaye sbd ganewa idonta ciwo da jikin Amatun.
Husnah ma kusan Daman dakin take kokarin nufa Dan gaba dayansu Hakanan sukaji ciwon nata na Neman Hana zuciyarsu nutsuwa.
Maamah ce a bayansu lokacinda suka Bude kofan bedroom dinta suka shigo dakin idanuwansu akan Amatun Dake bacci sosai fuskarta ta kumbura sosai alaman tayi kukan ciwon Kokuma kukan Wani abin.
Rarraba idanuwa kowannensu a fakaice yakeyi a dakin batareda sunga komaiba sedai hancin Husnah dayake Dan shaqar mata qamshin Dad dinta a dakin zuciyarta na harbawa Amma tana sake bawa kanta tabbacin ba Hakan bane shedan ne kawai da ke Sakata Jin qamshin dan haka Allah ya Bata lafiya kawai sukai mata fata suka fice Banda maamah data qaraso har bakin gadon na Amatu ta zauna a hankali tana kallanta cikin tausayawa ta dawo da kallanta kan Farha Data zauna kan sofa tace
"Menene ya sameta a dare Daya haka?
Likitan me sukace yana damunta?
Shiru Farha tayi tana shiga nazarin abinda zata fadawa maamah wadda ya kamata ace ta sanarwa gaskiyar maganar abinda ya samu Amatun Amma Kuma tasan fadawa maamah gaskiar zai kawo babban tashin hankali da baraka me girma tsakanin uwa da 'ya Wanda bazataso Hakan ba musamman yanzu da Amatun take cikin wannan halin.
Numfashi ta sauke me sanyi wanda ya Saka maamah sake zuba mata idanuwanta tana jiran amsarta.
Kallan maamah din tayi ta Bude Baki a natse tace
"A yanzu dai taji sauki Se Dan abinda baa rasaba,ciwon mara ne kawai Se Kuma damuwa da sukace tana ciki tana buqatan kulawa.....
"Damuwa Kuma?
Damuwan me?
Akwai abinda yake damunta ne Wanda ban saniba?"
Cikin sanyi da damuwa Maamah ta jerowa Farha din tambayoyin wainda suke kashe jikinta da son fadawa maamah Amma Kuma tana danne zuciyarta da Hana kanta
Tace
"Damuwa bazai wuce na karatu da Kuma yanda kike kasa yarda da ita wasu lokutan maamah akan abinda ba laifinta bane,ba ita ta zabawa kanta Hakanba, a gabanki gaban kowa lamarin ya fada kanta Wanda kaman yanda kikaji haka tajisa maamah Amma kina ganin lefinta akan Hakan lokuta da dama,
Maamah Amatu na buqatanki sbd ke kadaice uwa Kuma abokiyar shawara da walwalanta,
Dan allah maamah ki Dena nesanta kanki da ita akan auren da Allah ne ya daurasa Dan kuwa shine ya qaddara ASH TALBA ne mijinta ba Itace ta kaddarawa kanta Hakanba.....
Kalmominta na karshe ne suka Saka maamah data fara yin sanyi da nasihar Farha din sauya zancen tareda dakatar dashi ta hanyar miqa hannunta ta dafa goshin Amatun daya huce Babu zafi a jikinta sbd alluran datasha da magani a asibiti ta Bude Baki tana cewa
"Allah ya Bata lafiya dai."
Amin"Farha ta amsa dashi lura da maamah Bata son ko zancen auren Amatun da ASH tsaban zuciyarta ta bushe qyam akan auren batada Kuma niyar amsar auren.
Wayoyi anty Farha ta fara cikin nutsuwa da sakewa Wanda aket ayi mata na barkan waliman jiya
Maamah kuwa tana zaune tana kulawa da Amatun duk da bacci takeyi sosai batama San waye akantaba.
*****Qarfe goma sha Daya ya fito shirye tsaf cikin navy blue yadi me tsananin tsadan gaske hannunsa daure da agogon Rotary men's Regent watch qamshinsa na tashi a cikin sanyin fuskansa fresh Wani irin nutsuwa ne ya bayyana a tareda shi duk da Shima a sanyaye yake baa ganewa sbd kasalan daya samu kansa acikinta.
Fitowansa yayi daidai da ihun da Husnah ta buga acikin gidan dukkaninta jikinta na tsananin rawa da farin ciki da rudewa harma da firgicin abinda bata taba tinanin zata ji ba arayuwartaba sbd tashin mahaifiyarta Wani abu ne da kusan kowa ya cire ya debe tsammani idan aka cire Dad dinta da Bai taba cire daga tashin matar tasa ba.
Aunt labiba Dake can qasar ce ta kirata ta sanar da ita wannan labarin Daya firgitata ta saki ihun da batasan tayi ba.
Ganin Dad dinta a gabanta lokacinda y Sako Kai palon nasu Dan isa dakin Amatun ya Sanyata qarasowa gurinsa ko Gani batayi Dan tasan ihunta ya sanyasa shigowa tana tsayuwa gabansa bakinta na rawa duk jikinta ma rawa yakeyi tace
"Dad,mum ta farfado, your wife is out of coma, she's conscious Dad.....
Bata qarasaba kawai ta yanke jiki ta zube a ya tarota jikinsa komai nasa na dakatawa Shima cikin Wani irin mamaki da shock Dan bazai yiyu Hakan ta faru ba ace a bakin Husnah din yake ji ba batareda asibitin sun nemesa ba.
Maamah da Farha ne da ihunta suka fiddosa da gudu suka ganta some a jikin Dad dinta da sauri Maamah ta kamota tana dawo da ita jikin Farha suka kamata zuwa kujera shikuwa juyawa yayi ya fice idanuwansa na sauya batareda kansa ya dauki zancenba tsaban tashin hankalin idan ba Wani ne zai rikita masa qwaqwalwan 'ya ba Amma tayaya matarsa zata Farka bayan shekaru a kwance ace ba shine na farko da zaa sanarwaba.
Mr Jameel Dake jiran saukowarsa a guest Palo Dake gefen security room da sauri ya fito ganin Kiran ASH din akan wayarsa.
Yana fitowa Babu mota Kai tsaye ya Bude masa ya shiga da sauri Shima ya shiga suka kama hanyar office Dan vcall yake buqata da Personal attendant na room din da Abeeda take.
Daga securities har mr Jameel take suka fahimci yau din yanayinsa a bayyane yake na bacin Rai da rashin sanin gaskiyar maganar.
Suna isowa office da sauri mr Jameel yabiyo bayansa cikin office dinsa kafin ASH din ya qara taku biyu cikin sanyi da damuwar jinkirinsa da Dan shakku yace
"Tin dare kanada pending call Daya Greece madame is conscious nayita Kiran.......
Dakatawar da ASH din yayi zuciyarsa na daukewa daga wutan bugawa ya Sanya Mr Jameel din yin shiru Yana qasa da kansa cikin damuwa.
Hannunsa Dake nade da bandage yakai ahankali ya dafa table Dake gabansa Dan jiri da nauyin da zuciyarsa ta Dan dauka da abinda Jameel din ke fada masa yanzu.
Ganin hakan Mr Jameel ya dago cikin son isar da sauran bayanin yace
"Nayi booking komai na tafiya zuwa can din komai a shirye yake ticket kawai za'a Siya"
Rintse idanuwansa da sukai jajir ASH din yayi kusan sanyi da Wani irin nauyi dayaji Yana sauka daga zuciyarsa yaji suna gangara jikinsa.
Qarasa zaunawa yayi Yana Bude laptop din da Mr Jameel yayi saurin kawowa ya ajiye gabansa Kai tsaye yayi Saka Kiran Kai tsaye me zuwa dakin Abeeda.
Mintina kafin Kiran yayi connecting aka basa Daman miqa Kiran zuwa dikinta Kai tsaye.
Abinda ya Gani ne ya sanyashi rintse idanuwansa Wani abu me nauyi da tarwatsewa daga kirjinsa idanuwansa sukai sauya take zuwa ja a Karan farko Dayaji yana kasa riqe yanayinsa na farin ciki da mamakin Daya girgizasa ganin Abeeda idanuwanta a Bude aunt labiba na tareda ita da nurse a dakin duk da kwance take Amma idanuwanta dasuke a Bude Kuma itama shi din Daya bayyana tv Dake dakin take kalla hawaye na gangaro gefen idanuwanta suna saukowa.
"Abeedah" ya furta cikin sautin Daya qarawa hawayenta gudu tana Dan motsawa ahankali.
Motsawanta ya Sanya aunt labiba fashewa da sabon