Showing 30001 words to 33000 words out of 66367 words
Chapter 11 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
so Kuma ku gabatar min da Kan ku sabida mu San juna ko?"
Nan suka Shiga gabatar da kansa Yana musu Barka da shigowa tutorial class d'in sa, Daniyah ta mike tace "Suna na Daniyah Hafeez" cikin sauri ya d'ago kansa ya kalle ta jin sunan Sa d'aya da Mahaifin ta, Murmushi yayi yace "Masha Allah Ashe dai Ina da daughter acikin ku?"
Murmushi tayi ta zauna, bayan sun gama gabatar da kansu suka Fara darasi har na tsawon awanni biyu kan ya sallame su suka tafi gida"
Daniyah na fita ta Ciro waya don Kiran Driver Amma Kash wayar ta ba chaji, d'an tsaki ta jaa tace "Sai da nace was Fadeelah kar ta cinye min chaji Ashe sai da ta karar ta ajiye min, zamu had'u gobe, mtsww yanzu Dole sai na fita na samu a dai daita tsahu"
Nan ta Fara tafiya a nitse har ta Isa bakin gate duk ta gaji gani tayi anyi parking mota a bakanta da sauri ta jaa da baya, sauke glass d'in motar yayi sannan yace "Assalamu Alaiki"
Murmushi tayi ta amsa da "Wa alaikassalam" fitowa yayi ya zago inda take yace "me kike jira baki tafi gida ba har yanzu ga Maghriba ta karato?"
Kai a kasa Tace "Driver mu nake son kira Kuma wayata ta d'auke"
"Ayya to ga tawa ki sa number ki kirasa"
"To ai ban rike number tasa a Ka ba"
"Kashh! To ya kamata ki tafi gida Kinga ke mace ce bai kamata ki Kai war haka ba a waje Kinga Kare Bakwai saura fa"
"Hakane Zan tari a dai-daita nagode da kulawa"
"A'a haba ma Ina Nan d'in Kuma ga mota kice min Zaki tari a dai-daita, Kinga kiyi hakuri ki bani da ma na kaiki har gida Kuma Dan Allah Kar kice A'a please" Yana had'a hannayen guri guda.
Shiru tayi tana Shawara da zuciyar ta a zuciyar tace "Anya Zan aminta dashi na Shiga motar sa? Yauce Rana ta farko da na Fara ganin Hafeez kawai don ya Zama Tutor d'in mu...."
"Kinyi shiru da alama Shawara kike da zuciyar ki to Dan Allah tayi kokari ta baki Mai kyau a kaina don Ni bazan cutar dake ba na d'auke tamkar Kanwata sabida Ina da kanwa kamar ki Kila ma sa'ar kice Kinga bazan so a cutar da ita ba"
Hakan da yace yasa ta d'an ji Sanyi a ranta, sai Tace "Toh muje"
Yace "Yauwa godiya nake My daughter" dariya ta Shiga yi shi kuma ya bud'e Mata gidan gaba ta zauna, ya zaga ya Shiga, suna tafiya suna Hira har suka iso unguwar su, suna Isa layin su Tace Masa ta tsaya, kalle kalle ya Shiga yi yace "Ina ne gidan naku?"
Murmushi tayi tace "yana gaba kad'an"
"To me zai Hana na kaiki har gidan naku?"
"A'a anan ma yayi na gode Allah ya saka"
Ya amsa da Ameen duk da bai so hakan ba, bud'e motar tayi ta d'aga Masa hannu sannan tayi tafiyar ta.
*OXFORD UNIVERSITY*
"Sabir! Sabir! Sabir" da sauri ta Sha gaban sa Tace "Haba Sabir ya za'a yi tun d'azu nake ta binka Ina Kiran sunan ka kana jina Amma kaki kulani ka duba kaga yanda ka sa ake ta kallo na haba don kawai kaga Allah ya d'aura min Soyayyar ka shi yasa kake wulakanta Ni"
Rai a b'ace yace "Ki ka wulakanta kanki dai, ki duba kiga irin suturar dake jikin ki...
Kallon kanta tayi sannan ta kalle shi, yace "Ke yanzu a ganin ki kin burge ko? To Wallahi ko tsirara Zaki yi yawo baza ki tab'a burgeni ba, iyayen ki sun turo ki Nan all the way from Nigeria don kiyi karatu ki taimaki kanki da Yan Uwan ki da makusanta ki, Amma kin Zo Nan kin ballagazar da kanki, kin maida Kan ki Yar iska Wacce bata San mutunci kanta ba,ki duba kiga skirt d'in jikin ki Yan da ya d'ame ki a bar ma maganar d'ameya a iya cinya fa? Kina Yar musulmai tsabagen iskan ci da tantirancin ki Kika canza sunan ki daga maryam ya koma marry" murmushin gefen baki yayi yace "Kaico Kaico da halinki, wannan shine zai Zama first and last time" Yana nunata da Yar tsaya "wannan shine zai Zama kashedi na karshe da Zan Miki idan Kika sake zuwa inda nake ko Kuma Naji Kika ambaci suna na wallahi Wallahi sai na lahira yafi ki Jin dad'i" Yana Kai na yayi tafiyar da ta Barta agun zubewa tayi a gun da gwiwowinta tana kuka Mai cin raai duk Wanda ya Zo wucewa ya tsaya kallonta ya girgiza Kai sannan ya wuce.
Cikin sauri ta riko Tace "Maryam me ya same ki? Wani abun ne ya faru?"
'dago kanta tayi fuskanta ya wanku tass da hawaye, cikin kuka Tace "Rahina kin San zancen"
Dafe Kai Wacce aka Kira da Rahina tayi tace "Sabir Kuma Wai ke Dan Allah Maryam yaushe Zaki sayawa Kan ki mutunci ne?"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
MILHAAT CE
YAR TERAWA
PLEASE SHARE AND COMMENT
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE``` 1️⃣4️⃣0️⃣↪️1️⃣5️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
Cikin sauri ta rikota a gigice Tace "Maryam me ya same ki? Wani abun ne ya faru?"
'dago kanta tayi fuskanta ya wanku tass da hawaye, cikin kuka Tace "Rahina kin San zancen"
Dafe Kai Wacce aka Kira da Rahina tayi Tace "Sabir Kuma? Wai ke Dan Allah Maryam yaushe Zaki sayawa Kan ki mutunci ne?"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
......... Murmushin takaici Maryam tayi Tace "Rahina kin raga kin San komai fa kin San bazan iya rabuwa dashi ba"
"Ubanki ne shi? Ko kanin ubanki ne shi da Zaki Ce baza ki iya rabuwa dashi ba?"
Zata yi magana tayi saurin katseta Tace "Kinga Tashi mu koma hostel Kinga kin Tara Mana mutane maganar Nan Bata Nan bace ba"
Da taimakon Rahina,Maryam ta tashi sabida skirt d'in a takure take baza ta iya Tashi da dad'i ba.
Suna Shiga d'aki, Rahina ta riko hannun maryam Izuwa gaban mirror Tace "Just take a look at yourself Maryam gaki kyakkyawa mace iya mace, Amma ko kad'an Baki mutunta kanki a matsayin ki na 'ya mace ba,Maryam ki duba kiga irin shigar da kike yi da irin kwalliyar da kikeyi kamar a duniyar aljanu,babu na miji Mai mutunci wanda zai ganki ya so had'a zuri'a da ke,Sabir Mutum ne kamili nitsasse Wanda ya San ciwon kan sa, Babu abinda yasa a gaba sai karatun sa ke Kuma akasin Haka, kene night clubs kece shaye shaye,Taya za'a yi so ki a haka? Kiyi wa kanki fad'a tun wuri,tun lokaci bai kure Miki ba"
Murmushin gefen baki Maryam tayi jiki a sanyaye ta zauna a bakin gado tace "Rahina Kenan Kar ki ga laifina Wallahi Soyayyar da nakeyi wa Sabir ce tayi yawa abin takaicin ma a duk sanda nayi kokarin cire shi a Raina saina ji so da kaunar sa ta karu a zuciya ta, Kuma Ni wallahi duk Wanda yace min na rabu dashi kallon makiyi nake masa"
Kad'a Kai Rahina tayi ta zauna a gefen ta, kafad'ar ta ta dafe Tace "Maryam ba cewa nayi ki daina son sa ba, so halitta ne abin da nake so ki gane anan shine ki sani ke mace ce Allah ya d'auka ki ya daraja Amma kin wulakantar da kanki, Maryam ki sani duniyar Nan Mai Karewa ce idan Kika mutu a haka me Zaki fad'a wa mahallicin ki, mutuwa fa gaskiya ce, kaf cikin makarantar nan babu Wanda yake Miki kallon mutuniyar arziki"
"Amma Rahina ke shaida ce bana Wasa da sallah Ina ibada na yanda ya dace Ina sallah Ina azumi me Kuma ya rage?"
"Alot!! Abubuwa da yawa wallahi ko kaffara bazan yi ba a yau idan Kika Fad'i Kika mutu shaidan da Za'a Miki shine ace Miki 'yar iska, ki tuna fa iyayen ki sun turo ki Nan ne sabida kiyi karatu ba iskanci ba"
Shiru tayi sannan ta sa d'an yasan ta, ta shar hawayen da ya gangaro mata Tace "Insha Allah Zan canza Rahina Zan Zama mutuniyar arziki kamar yanda Mahaifina yake so, maganar Sabir Kuma insha Allah na daina shi daga yau"
"Yauwa ko kefe har kin sa naji dad'i Wallahi, Allah yasa da gaske kike don kin Sha fad'a min hakan"
Murmushi Maryam tayi Tace "Zan Baki mamaki wannan karon ba Wasa nake ba, Bari ma ki gani" Tashi tayi ta nufi walldrop d'in su ta Fara Ciro Kaya Niki Niki, top top ne da wando gajeru da dogaye, ta cire kayan jikin ta, sannan ta saka wata doguwar Riga na Atamfa, kerosene ta d'auka sannan Tace "Ki biyo Ni da ashana"
Bata tsaya taji me zata ce ba ta fita, zubda kayan tayi a kasa sannan ta zuba musu kerosene Rahina na Isa inda take ta Mika Mata ashanan, kyatta ashanan tayi a kayan suna tsaye har kayan suka kone tas sannan suka tafi, Rahina Tace "Naji dad'i Maryam da Kika d'auki magana ta ko ba komai nasan Zan samu lada agun Allah"
Murmushi kawaii tayi Tace "Nagode sosai Rahina you're a true friend, Allah ya bar mu tare."
Ta amsa da "ameen"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kuyi hakuri da wannan
Nayi hakan ne ko Zan ga chanji
Plzz sharhi nake so ba thank you ba
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE``` 1️⃣5️⃣0️⃣↪️1️⃣6️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
Murmushi Maryam tayi Tace "Zan Baki mamaki wannan karon ba Wasa nake ba, Bari ma ki gani" Tashi tayi ta nufi walldrop d'in su ta Fara Ciro Kaya Niki Niki, top top ne da wando gajeru da dogaye, ta cire kayan jikin ta, sannan ta saka wata doguwar Riga na Atamfa, kerosene ta d'auka sannan Tace "Ki biyo Ni da ashana"
Bata tsaya taji me zata ce ba ta fita, zubda kayan tayi a kasa sannan ta zuba musu kerosene Rahina na Isa inda take ta Mika Mata ashanan, kyatta ashanan tayi a kayan suna tsaye har kayan suka kone tas sannan suka tafi, Rahina Tace "Naji dad'i Maryam da Kika d'auki magana ta ko ba komai nasan Zan samu lada agun Allah"
Murmushi kawaii tayi Tace "Nagode sosai Rahina you're a true friend, Allah ya bar mu tare."
Ta amsa da "ameen"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*LAGOS*
....... A hankali yake shafa dukkanin jikin ta, a yayinda d'ayan hannun sa ke cikin sumar ta bakin sa Kuma a cikin ta, wani irin Nishi suke sauke a hankali babu abinda zaka ji a d'akin sai saukar Numfashin su, a haka har ya samu ya cire kayan da ke jikin ta cikin sauki ya shige jikin ta, da sauri ya cire Joystick d'insa Rai a mugun b'ace ya ture ta, yace "Ke Ashe dama ke ba Virgin bace?"
Baki na rawa tace "Kamarya? what do you mean? Ban fahimci me kake nufi ba?"
A tsawace "would you shut up your dirty mouth! Ni Zaki Raina wa hankali Ashe dama ke ba budurwa bace? Kuma kin San alkawarin da na d'auka shekara da shekaru Kuma Kika min haka?"
Tashi tayi ta zauna tace "Look Mr Man, ya za a yi kazo ka Rika min tsawa sai kace Kaine ubana, yaushe mukayi haka da Kai? Ka tambaye Ni cewar Ni budurwa ce Kan ka aure Ni? Ba kayi ba so Kar ka kuskura kace zaka min tsawa, idan zaka Zo mu cigaba da inda muka tsaya kazo gaba ki d'aya ka tada min hankali"
Magana take tana kokarin riko hannun sa, a zabure ya sauka da ka Kan gadon ya d'auki gajeren wandon Sa ya sa, tsaki ya jaaa, sannan ya Shiga ban d'aki Rose kuwa haushin sa taji kamar ta shake Masa wuya, gyara kwanciyar ta, ta d'auko wayar ta datar da bud'e sannan ta Shiga Google, searching d'in Fina finan batsa tayi ta Shiga kallon su, tana lashe baki had'e da ciza leb'en ta, (Ni Milhat Naga abinda yafi karfin idona na fita na bata wuri).
"Waye nake gani kamar Rahila" tana Kara kura wa Wacce ta nufo ta Ido" firgit ta mike Tace "Itace" ji nayi ta Fara Kiran Efoma, Chidinma where are you? ku fito ga 'yar uwar ku tazo"
Da gudu na ga Wasa emmata su biyu suka fito baza su wuce sa'an nun Rahilan ba, runguman ta suka yi suka karb'i akwati da jakar dake hannun ta, ita ko Rahila Murmushi kawaii take yi a nitse ta durkusa Tace "Nna good evening" rungumota tayi kyam a jiki Tace "Rahila my daughter yau kin tuna da gogon ki Kenan ko?"
Murmushi tayi tace "Nna ai kullum Kuna raina na Isa na manta daku ne?"
Dariya tayi Tace "You're welcome ya su maman ki?"
"Suna lafiya sunce na gaishe ku"
"Eyya ina amsawa, ina Kika baro Rose? Meyasa Baku taho tare ba?"
"Emm...emm dama emmm Mama ce tace ja Fara zuwa in yaso zata biyo Ni daga baya"
"Okay yayi kyau, Ina fatan dai Zaki kwana biyu anan ba irin zuwan ku na kwana biyu zuwa uku ki koma ba"
Dariya Rahila tayi sai ta nuna Mata akwatin ta Tace "As you can see Nna zuwan Nan daban ne"
Dariya tayi Tace "Yauwa hakan nake son ji"
Efoma Tace "Sister welcome"
Murmushi tayi ta amsa da "Thank you how are you doing?"
Ta amsa da am fine thank you"
Chidinma tace "Sister hope kin kawo min tsaraba"
Rahila Tace "Oooh Chidinma haryanzu Baki chanza ba,Baki ce min ya hanya ba ke ta tsaraba ma kike?"
Tsotsa keya tayi Tace "I'll come to that I just want to be sure in kin kawo min ne"
"Idan ban kawo ba sai na koma ko?"
"Aaaaa no oooo Ni ban ce, ya kike ya hanya yasu Mama, da sister Rose"
"Duk kalau we Thank God"
"You are highly welcome"
"Thank you"
Mama Tace "To ko shigar da kayan nata ciki Mana, ki samu Kiyi wanka kici abinci ki huta in yaso da ga baya sai Ku zauna kuyi hiran ko?"
Duk suka amsa da "to"
Yana fita daga ban d'aki, idon sa ya fada a Kan Rose dake ta Wasa da farjin ta da Yar yatsar ta kad'a Kai yayi bakin ciki da Dana sani yake,a zuciyar sa cewa yake "Dole hakan ma ta faru dani sabida naci amanar Rahila, a tunani Rose Kamila ce Ashe asalin tantiriyace Yar iska ajin farko" a tsawace yace "Ke!" Ga mamakin sa ko kallon sa bata yi ba, sai wasan ta kawaii take duk ta birkice har sai da hakar ta ya cimma ruwa ta Fara sauke Numfashi, kallon sa kawaii tayi,tayi tsaki sannan bangaje shi ta Shiga toilet,
dafe Kai yayi ya tsuguna agun Yana kukan zuciya.
Rahila tun da taje gidan gogon ta bata nuna Mata cewar tana da dumuwa ba sannan Bata Sanar da ita dalilin ta na zuwan kauyen ba, Rayuwar ta duk ta canza hankali ta ya kwanta har ta manta da wani Wai Prince, sai dai lokaci zuwa lokaci takan tuno shi Kun San zuciya da abinda yake so, Rayuwar ta take gwanin sha'awa suje gona, wani lokacin rafi su d'ebo ruwa suyi wanka sannan su dawo gida abun su.
Rose rashin mutunci kala kala take nunawa Prince, Amma babu yanda ya iya don shi tsoron sa d'aya Kar yaje gida da maganar ta Akan zai rabu da ita yasan baza a yarda ba shiysa ya kyale ta take yin abinda ta gadama, ko da Wasa bai sake kusantar ta ba, idan ta nemi shi yaki a gaban shi sai ta biya wa kanta bukuta.
*KANO*
"Ruman!!! Ruman!!" A nitse ta waigo don ganin Wacce ke Kiran ta, Murmushi Naga tayi Tace "Fareedah kin shigo Kenan?"
Murmushin ita ma ta Maida Mata ta Ce "Eh na shigo, Liyah fa?"
"Yanzu mukayi waya tana cikin aji"
"Okay mu Shiga"
Suna Shiga suka tarar da Liyah na ta buga game a wayar ta, shigowar su ke da wuya malami ya shigo, bayan sun gama lectures sai suka nufi commercial area, Hira suke suna cin abinci sai Kira ya shigo wayar Ruman, tana dubawa Naga tayi Murmushi da Sallama a bakin ta ta d'aga, daga 'dayan 'bangaren naji yace "Baby na kina ina nazo inda muke Zama ban ganki ba?"
Cikin muryar shagwab'a Tace "abinci muke ci muna commercial area"
"Okay gamu Nan zuwa"
Liyah tace "wane ne haka?"
Murmushi tayi Tace "Baby Ra'ees ne"
Dariya Liyah tayi Tace "Baby manya Inyaaau"
Dariya sukayi Amma Fareedah ji ta yi wani abu ta tsaya Mata a makogoro, wani kishi Taji ta rasa yanda zatayi abincin ma taji duk ya fita Mata a rai, Liyah na kallon ta duk ta lura da haukan da take gyaran murya tayi tace "Faree!! Ya dai? Ya Naga Baki cin abincin?" Ko chips d'in bai Miki bane?"
Kirkiran Murmushi tayi Tace "A'a yayi dad'i sosai"
"To kici man"
Turo Baki tayi Tace "Toh"
Tun Kan su iso wani kamshi Mai uban dad'i ya bugi hancin Liyah bata gan shi ba Amma tasan kamshin Nan a jikin Sagheer yake tashi "Assalamu Alaikum emmata" Liyah, Fareedah da Ruman d'ago kansu sukayi a tare suka amsa da "wa alaikumussalam"
Liyah na d'ago kanta sukayi Ido hud'u da Sagheer, Murmushi ya mata ita ma ta Maida Masa, sannan ta cigaba da cin abinci jiki ba kwari, Ra'ees kuwa wuri ya samu ya zuna kusa da Masoyiyar tasa Ruman Yana kashe Mata Ido sai Dariya take, Ra'ees yace "sannan ku"
Da sauri Fareedah ta amsa "Yauwa sannu, ya kake" tana fari idanu, ya amsa da laifiya, ya Maida kallon sa ga Liyah yace "Hajiya yau ba magana ne?" Cokalin dake hannun ta tayi Tace "Am sorry ka wuni lafiya?"
Murmushi yayi yace "Laifiya ya studies"
Ta amsa da Alhamdulillah, Sagheer gyara Zama yayi yace "Wato Ra'ees kawaii kuka sani Ni ban Kai a gaishe Ni bako?"
Hakuri suka Shiga bashi had'e da gaishe shi, ba yabo ba fallasa ya amsa,