Showing 63001 words to 66000 words out of 66367 words
Chapter 22 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
bata da aiki sai kuka Daddy kuma ya daina kula ta ko kallonta baya son yi Sai dai idan ya ganta ya Kan ji tausayin ta ganin yanda ta lalace ta rame tayi baki.
Granny kuwa tayi tayi mummy ta Sanar Mata inda Liyah taje take kakkauce mata hakan yasa ta hakura.
*BAYAN SATI*
Aniyah na zaune da Hafeez tace "Ya Hafeez kayi hakuri nasan baka San komai a kaina ba, sannan baka san dalilin yasa nake yawan komawa gida a cikin tashin hankali ba"
Gyara Zama yayi yace "Hakane"
Murmushi tayi Tace "Nasan ka San suna Nan Daniyah Hafeez Amma baka san cewa Ni Twins bace"
Gyara Zama ya sakeyi yace "Twins?? Kina nufin ke biyu ce?
Ganin yanda yake Maganar Yana zaro Ido yasa ta dariya tace "Identical twins for that matter"
Zaro wayar ta tayi ta nuna Masa gaban wayan ta karb'a yayi Yana sake kallon hoton dakyau yace "Wonders shall never end kamannin tayi yawa ai idan na ganta zan d'auka kece"
Murmushi kawaii tayi sai da ya gama kallon hoton Kan ya Mika Mata wayar yace "Ina sauraron ki"
Nan ta Sanar masa da yanayin haliattar su Dariya yayi yace "Aniyah Kenan please tell me something more sensitive, sam ban yarda ba hakan ba zaiyu ba"
Murmushin gefen baki tayi Tace "Na Sani dama baza ka yarda ba amma zaka iya wani Rana dakace min kaga jini a bakina?"
Yace "Eh"
'Zaka iya tuna ranar da Ina dariya Amma Kuma idona na zubda hawaye?"
Yace "Eh"
"Zaka iya tuna ranar da kaga jini a hannu na?"
"Eh"
"To haka muke Amma idan baka yarda ba shikenan"
Shiru yayi Yana kallon ta yace "Na yarda sabisay duk maganganun hakan ne, amma abin da abin mamaki"
"Eh Dole ai"
Nan tayi ta bashi labarin Yarintar su yayi ta dariya suna cikin hiran ne Tace "Albishirin ka?"
Yace "Goro"
Tace "Fari ko jaa?"
Yar karamar dariya yayi yace "Fari Kal Kal"
Dariya tayi Saida tayi Mai isarta tace "Daddy fa ya matsa"
"Ya matsa dame?"
Rufe fuskar tayi tace "Cew yayi ya bamu one month mu fito da miji" tashi yayi ya tsaya yace "Dan y dagaske kike"
Turo Baki tayi Tace "Eh man dagaske nake kasan bazan maka Wasa da Wannan ba sabida nasan buri ka Kenan"
Zama yayi Yana washe Baki yace "Hakane hakane, gobe goben zan turo magabatana"
Dariya tayi Tace "lallai Amma zaka iya Bari na Sanar Masa tukunna ko?"
Tsotsa keya yayi yace "Auu hakane fa Ashe Allah ya kaimu to Ina sauraron ki"
Ta amsa da Ameeen,wayarsa ya d'auka ya duba yace "Karfe biyar ya kamata ki koma gida ko?"
Turo Baki tayi Tace "Ya Hafeez har ka gaji da gani na?"
"Aaaah haba gimbiya sarautar Mata na Isa nace na gaji ke Kanki kin san ko kwana nayi bazan gaji da ganin ki ba"
Murmushi tayi Tace "To muje ka rakani"
"Okay tashi muje"
Suna Isa parking area taji Ana Kiran sunan ta, a nitse ta juya hafeez na ganin shi ya b'ata Rai (Oh sarkin kishi)🤭
Ganin shine ta b'ata raai tace "Kaine?"
Yace "Eh" Tsaki tayi Tace "Ya Hafeez sai munyi waya" wani dad'i yaji ganin Taki kulashi, tanaga mota da sauri ya ture Hafeez ya rike kofan motar.
A tsawace Hafeez yace "Kai malam baka da hankali ne?"
Sageer yace "Malam ba da Kai nake na tunda nazo Nan kaga na maka magana" Rai a b'ace Tace "Sageer duk abinda zakayi kayi shi a wani gun Amma wallahi bazan lamunci cin mutuncin Wanda nake so daga gare ka ba"
Cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri Dan Allah ki saurare ni wallahi Soyayyar zata yi min illah Dan Allah ki so ni"
Hafeez ji yayi kamar ya shake Masa wuya, murmushin takaici tayi tace "Sageer bayan abin da kayiwa Yar Uwata ko ka d'auka ban San abinda ka Mata bane?"
"Wallahi Aniyah na d'auka kece"
Gyara tsayuwar ta tayi Tace "Masha Allah kaga Kenan ba Sona kake ba jikina kake so"
Sageer yace "Aniyah wallahi...."
A tsawace Tace "Dakata malam Kar ka sake kulani na tsane ka na tsane ka mugu azzalami" ta Maida kallon ga Hafeez sannan tayi Murmushi tace "Ya Hafeez zan tafi take care of yourself for me please"
Murmushi yayi Wanda Bai Kai Ciki ba yace "You too"
Ta shige motar ta, ta nufi gida.
Hafeez Kuma ya shige Ciki ya bar Sageer a tsaye a gun.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
NA YI TYPING DAYAWA FANS DA FATAN NA WANKE KAINA😁
Please comment and share
Milhaat ce
Yar Terawa🥰😘🥰
🏻: 🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu''' .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
Follow me on Wattpad
@milhaat🙏🏻
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
PAGE 300-310
Not edited
PREVIOUSLY
A tsawace Tace "Dakata malam Kar ka sake kulani na tsane ka na tsane ka mugu azzalami" ta Maida kallon ga Hafeez sannan tayi Murmushi tace "Ya Hafeez zan tafi take care of yourself for me please"
Murmushi yayi Wanda Bai Kai Ciki ba yace "You too"
Ta shige motar ta, ta nufi gida.
Hafeez Kuma ya shige Ciki ya bar Sageer a tsaye a gun.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............Hafeez na Shiga office d'insa ji yayi ransa na b'aci a fili yace "Wai meyasa ma na kyaleshi,Kasshh gayen Nan ya Raina min hankali"
Shiru yayi na d'an wasu lokaci Murmushi yayi sannan yace "Ko da Aniyah ta Riga ta nuna na fishi muhimmanci akansa" Nan ya zauna ya cigaba da harkar gaban sa.
KAUYE
"Ke princess Ni sa'an ki ne? Sau nawa na fad'a Miki ki daina zuwa inda nake?" Prince ne ke wannan Maganar, cikin kuka Tace "Daddy please ka fad'a min laifina, Daddy tun da na taso na taso cikin gata Amma lokaci d'aya ka canza min, gashi yau na cika shekaru Sha takwas, Daddy kiyayya kake nuna min Karara,Amma nagode sosai da ba ka daina kula da maranta,cina,Shana da tufafina ba, Amma please ko ma mene ne na maka ka yafe min"
Tana kai Nan ta tashi ta fita.
Prime Shiru yayi ya rasa me zai ce sai hawayen da ya zubo Masa ba tare da ta San dalilin hakan ba, a zuciyar yace "Ban San dalilin da ya na sane ki ba My Princess Please forgive me"
Princess d'akin Rose ta Shiga ta gaishe ta cikin girmamawa, wata muguwar harara ta Mata sannan Tace "Dama my Lovely daughter ce kayan ta sukayi gasu chan kije ki d'auka ki je kogi ki wanke su Tass" tana maganar tana nuna Mata kusuwar d'akin kayane makil an d'aure a zani, princess kallon kayan tayi cikin sanyin murya tace "Mummy Amma masu wankin gidan suna Nan, ko Kuma ga washing machine tayi amfani dasu"
Princess sai saukar Mari kawaii taji "ke don uwar ki Ni sa'ar uwar kice? Da har ke Zaki fad'a min abinda zanyi? Maza Kan na rufe idona na bud'e ki tashi kije ki wanko kayan Nan"
Cikin kuka Tace "Zanyi mummy Amma Dan Allah ki Bari na wanke Mata a gida kinsan gun da nisa"
Maruka biyu ta mata sannan ta nuna Mata hanyar fita ba tare da furta komai ba.
Cikin tsoro ta mike ta d'auki kayan ta fita.
Tana Isa kogin ta Fara wanki gun Shiru ba kowa sai iska da Kuma kukan tsuntsaye, tana cikin wanki kanta a kasa na hango wata Yar budurwa kyakkyawa Wacce baza ta wuce shekaru ashirin ba ta fito daga cikin Ruwan ina ganin ta na tsorata sabida kyawun ta ya zarce tunani ba bazan iya kwatanta muku kyawunta ba, gashin ta har Yana tab'a mazaunan ta, jikin ta sanye yake da Atamfa Riga da skirt Wanda ban tab'a ganin kalan sa ba, d'aure kanta tayi da d'ankwalin kayan sannan naga ta sa hannu a cikin ta d'auko wasu kullin kaya jikin ta a jike yake sharaff Amma ga mamaki na Kan ta karaso inda princess take kayan ta ya bushe, a hankali ta karaso inda princess gyaran muryar da tayi ne yasa a firgice ta tsaya had'e da yatsar da zanin da ke hannun ta kallonta tayi had'e da dafe kirjin ta, Murmushi tayi
Tace "Am sorry na tsorata ki ko?"
Ganin tayi Murmushi ita ma Murmushin tayi "suna na ummu Salma ke fa?"
Kallonta princess ta sake yi sama da kasa Kan Tace "Suna na princess Amma ke musulmace ko?"
Murmushi tayi Tace "Eh Ni musulmace ke Christan ce ko gargajiya ce?"
"A'a am a Christian"
"Nice to meet you"
"Nice to meet you too"
Salma Tace "zan iya Zama a kusa dake?"
"Eh me Zai Hana? Kiyi kawaii"
Salma Tace "Nagode sosai, Amma please Zaki iya ara min roban ki guda d'aya Kinga na manto nawa a gida"
Bata ce komai ba Mika Mata kawaii tayi,ta Mata godiya, salka rero karatun al'qurani ta Fara yi suratul Maryam, har sai da ta Kai karshe princess Tace "Wani yare ne wannan naji yamin Dadi?"
Murmushin gefen baki tayi Tace "Arabic karatun al'qurani ne"
"Amma yamin Dadi how I wish na iya"
"In dai kina so zan koya Miki ai"
Murmushin takaici tayi tace "Ta Yaya Kenan bayan ba fita nake ba Kuma ba a Bari azo guna idan Kinga na fita to makaranta naje Kuma in na dawo sai aikace aikacen gida"
"Amma alamu sun nuna me Yar sarki ce sabida sarkan wuyan ki na sarauta ce Amma ya akayi na ga kina wanki alhakin kece ya kamata a yi wanki?"
Princess kasa magana tayi Zama tayi a Kan want dutse dake bayan ta, ta shiga share hawaye tana shessheka, cikin tausayin princess Salma ta karasa inda take ta dafe ta a kafad'a tace "Princess kin yarda Dani?"
Kai ta d'aga alamun eh had'e da share hawayen ta, Murmushi Salma tayi tace "In dai kin yarda Dani ki fad'a min matsalae ki Ni Kuma in Sha Allah zan taimaka miiki"
Cikin kuka ta Shiga Sanar Mata da komai da ke faruwa a Rayuwar ta sosai taji tausayin ta duk da dai tasan komai ta San Kuma wace ce princess ta Kuma San wace ce princess.
Wace ce salma???
Ummu Sallama Ziyad Yar sarkin aljanin da ke yanki kauyen su princess ce, kuma kanwa ga Malik ziyad, Malik ziyad Mahaifin ta ne ya turo ta akan ta taimakawa Anastasia princess Kenan, Sarki ziyad Yana fushi sosai da Malik sabida shid'in tamakar shaid'ani yake baya Jin tsoron Allah sabida kullum cikin tsab'a Masa yake hakan yasa ya Kore shi da ga cikin a halin sa, shi Kuma malik ya d'auki alwashin mugunawa Mahaifin Nasa da duk wani abinda ya shafe shi sai dai Yana matukar son Salma dake itace take binsa, Sarki ziyad ganin hakan me yasa ya turo ta don Yana da tabbacin bazai cutar da ita ba.
Wane ne Malik ziyad??
Idan Baku manta ba Rose a gun boka ta samo ciki ta dalilin aljanin da ake turo Mata, Malik ziyad shine wannan aljanin, sannan shine uba ga Angel ( Yar rose).
Wannan Kenan
Cigaban Labari
"Kiyi shiru Anastasia ki daina kuka kinji?"
Da sauri ta d'ago kanta tana kallon ta, kallon cike da tamabaya Murmushi Salma tayi sannan Tace "Kina mamakin yanda akayi na San sunan ki ko?"
Kai ta d'aga alamun eh.
Murmushi ta kumayi a Karo na biyu Tace "Ki daina mamaki ke princess ce ai babu Wanda Bai San sunan ki ba a garin Nan ba so ki daina mamaki"
Murmushi tayii Tace "har na tsorota
Don na San ban fad'a Miki suna na ba"
Murmushi tayi Tace "Kinyi kuka sosai ya kamata ki kwanta ki huta"
"Idan na kwanta wa Zai min wankin?"
"Zan Miki Kar ki damu"
"A'a naki Kuma fa?"
"Princess Kenan duk zanyi"
"A'a dai ki bari kawaii nayi nawa kiyi naki wankin nawa Yana da yawa"
"Kar muyi jayayya dake, Bari na Kama Miki Kan ki ciwon Kan yayi sauki"
Yatsunta ta sa Akan ta, ta Kama kan ta Fara karonto fatiha kafa Bakwai sannan ta zare hannun ta, zare hannun ta ke da wuya princess bacci Mai nauyi ya d'auke ta, gyara Mata kwanciya tayi sannan ta Fara wanki tana yi tana Shanya su, bayan ta gama ta kwashe su ta nad'e su ta aje Mata su guri guda, shafa Kan Princess Salma tayi sannan ta Koma cikin ruwa.
Cikin nitsuwa ta tashi tana goge idonta da hannayen ta duka biyu, ga mamakin ta ba taga Salma ba tashi tayi a ta Fara dube dube ta had'e da Kiran sunan ta mamaki ne ya kamata ganin yanda ta shirya kayan gasu sun fita a hankali ta karasa inda kayan take, wani farin paper ta gani Mai kyaun gaske sai sheki yake da sauri tasa hannu ta d'auka sabida tasan babu Wanda Zai ajiye paper Nan sai Salma cikin sauri ta bud'e ta Fara karanta abinda aka rubuta kamar haka.
"Am sorry princess na tafi bamuyi ban kwana ba sabida naga kina bacci, sannan ga Nan wankin na gama Miki su, ki daina zuwa kogin Nan ke kad'ai don akwai mugayen abubuwa dayawa a kewaye dake, sannan kince kina son koyon karatun da nake d'azu idan Kina so zan Rika zuwa gidan ku kullum ina koya Miki Amma Sai dai idan Zaki karb'i musulunci"
Princess Shiru tayi a fili Tace "Toh Taya za'ayi tazo gidan mu bayan an Hana kowa zuwa guna?"
Sai ta cigaba da karanta wasikar "Hmm nasan zakice Taya za a yi nazo gidan ku ko saibida an Hana Kar ki damu idan kin amince wannan Abu Mai saukine" zaro Ido princess tayi sannan ta Cigaba da karanta shi, "Kar ki tsorata kin San kece Kika fad'a min an Hana kowa zuwa gunki shiysa nace haka, and idan Kika karb'i addini I assure you that Daddyn ki Zai warke sabida asiri aka Masa kisa ranki Daddyn ki Yana son ki Kuma Yana kaunar ki deep down, sannan akwai wani bairo da na ajiye Miki a gefen kayan ki d'auka ki Adana shi da pepper hannun ki, duk sanda kike neman wani taimako ko Kuma Wacce kike so kiyi magana da ita ki rubuta bukatar Akan paper insha Allah Zaki ganni"
Tana gama karanta shi rubutun ya b'ace a tsorace ta yatsar da paper ta Jaa da baya tana kallon paper ta dad'e a Haka tana kallon paper Kan tasa hannun ta d'auka sannan ta duba ta d'auko biron ta Maida kallon ta ga paper hannun nata sai taga an rubuta "Princess kiyi saurin barin gun Nan ki Koma ki gida Bazan iya taimakon ki ba sabida ya fi karfina" sai rubutun ya b'ace cikin sauri Tasa paper da biron a hulan dake kanta ta d'auki kayan ta bar gun a Guje.
Tana barin gun na hango Salma ta fito daga cikin Ruwan tana Murmushi amma wannan karon kayan dake jikin ta kamar kayan sarauta irin Wanda Matan saraukuna ke sawa Amma nata duk zinari ne sai sheki suke, a hankali ta fito ta tsaya a gab'an Ruwan wani guguwa Mai Karfi nake hangowa daga nesa sai da ya Zo daf da Salma sannan ya tsaya nan take ya Koma wani tsayayen mutum dogo Fari Mai farfad'an kirji, zaro Ido nayi ganin yanda yake Kama da Angel tabbas Mahaifin tane shi, huci yake cikin b'acin Rai yace "Salma me kike Anan gun?"
Murmushi tayi Tace "Yayana na fito Shan iska ne"
Ga mamaki na Murmushi Naga yayi Shima yace "An turo Ni ne Nan na Shiga jikin wata Kuma an tabbatar min da tana Nan Ni da kaina Kuma na ganta"
"Yaya Wai Kana nufin princess?"
"Eh ita"
"Haba Yaya me ta maka kawatace fa?"
"Ina kika tab'a ganin jinsin aljanu da bil Adama sunyi abota Kanwata?"
"Kamar yanda kaima ka Auri bil Adama Yaya Dan Allah ka dawo gida ka bawa baba hakuri nasan zai yafe maka ka daina aikin shaid'an cin Nan Haka, Yaya yanzu Kai baka ganin amfani kawaii take da Kai taya za'a yi kana Yarima wata banza chan sai yanda tayi da Kai?"
Rai a d'an b'ace yace "Kar ki sake ce Mata banza uwar 'ya 'ya na ne Kuma ina son ta,da ace wani ne ya fad'i haka ba ke ba da tuni na raunata shi"
Kai a kasa Tace "Kayi hakuri Yaya Amma Kayi tunani akai" tana Kai Nan ta b'ace na neme ta na rasa Shima guguwa ya Koma tun ina ganin sa naga ya b'ace.
Princess na Isa gida, ga mamakin ta Rose ta ganta ta shigo cikin farin Ciki da Wal Wala Kuma jikan ta babu alamar gajiya, zata wuce a tsawace Tace "Anastasia" a hankali ta Juyo ta kalle ta hannun ta d'ga Mata alamun tazo, ba b'ata lokaci ta Koma ta gaishe ta Baki a bud'e take kallon ta Tace "Kinyi wankin?"
Ta amsa da "Eh nayi" "biyo Ni"
Rose na gaba princess na biye da ita kanta Kuma d'auke yake da kayan wankin, side d'inta suka nufa Zama tayi ta d'aura kafa d'aya Akan d'aya tana tauna chewing gum Tace "kwance kayan na gani idan bai fita ba sai kin koma kin sake wanko su" a hankali ta kwance rose d'aya bayan d'aya take duba kayan wani haushi da bakin Ciki taji da Jin haushin bokanya a zuciyar ta Tace "Ya zata min haka ta tabbar min da yarinyar Nan baza ta dawo da Rai ba Amma Kuma gashi ta dawo Kuma har ta gama wankin"
Sannan a fili Tace "kinci Sa'a sun fita tashi kije ki jera Mata kayan a cikin Waldrop din ta"
Tashi tayi ta fita a hanyar ta tafi suka ci Karo da Granma, a jiye kayan tayi da gudu ta rungume ta tana fad'in "Granma you're welcome" ita ma grandma taji Dadi sosai don ta kwana biyu bata ganta ba, shafa kanta tayi tace "Ya na ga duk kin dafe kin rame Kinyi baka" Murmushi tayi tace "Na d'an yi zazzab'i ne"
Kallonta kawaii tayi Amma Bata yarda ba Maida kallon ta tayi ga kayan wankin da princess d'in ta yatsar Tace "Wanchan kayan fa?" Tana nunuwa da Yar yatsa, Sosa keya tayi Tace "Kayan angel ne"
"Ehen me kikeyi dasu?"
"Zan Kai Mata d'akin tane"
"Ita Kuma me take?"
"Tana d'akin ta"
Kai ta girgiza Tace "Wato rose har yanzu tana azabtar dake Kuma kin ki fad'a min sai da nace ki Rika fad'a min ,Amma banga laifin ki ba laifin lusarin uban kine Bari na Shiga na Sami rose d'in" fuuuu ta sa kai ta shige Rai a b'ace, tana Shiga Bata amsa gaisuwar ta ba sai fad'a take ta Mata har da kuka, rose ko a jikin ta fad'an da take Bai dame ta, Granma ta juya da niyar zata fita, da sauri ta riko jakar hannun ta ta zube please