Showing 51001 words to 54000 words out of 66367 words
Chapter 18 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
Rama Tace "Idan ke Mahaukaciya ce na fiki hauka wallahi"
Liyah Tace "Kai Kai Kaaaai Kika mare Ni?"
Yarinyar ta ajiye Jakarta akan tebor Tace "an mare ki, ko Zaki Rama Ne?"
Liyah ta Kamata da kokuwa kitir kitir Nan da Nan gurin ta kaure da ihu daga masu dariya sai masu kokarin raba su cikin masu rabiyar harda Sageer da kyar aka raba su, bakin Liyah duk jini.
"Aniyah lafiya ya Naga jini a bakin ki?"
"Jini kuma?" Tasa hannun tasa taga tabbas jini ne da gaske, tana gani ta zaro Ido Tace "Daliyah" ta mike tana kallon hannun ta.
Hafeez cikin rashin fahimta yace "Daliyah? Wace ce ita?"
Gani yayi ta Fara tattare dakardun ta, tana sawa a jaka yace "Aniyah lafiya ina zakije?"
"Gida" tana kokari fita da sauri ya riko Jakarta yace "Aniyah ki tsaya Mana kimin bayani"
"Maganar tana da tsawo zamuyi maganar daga baya please as for now I really need to go home"
"To ki tsayaa Bari na d'auko car key na kaiki gidan"
"No Kar ka damu yau na fito da tawa tana kai Nan ta fita.
Ta barshi a tsaye a gun Baki a bud'e.
Tunda ta Shiga motar take kokarin Kiran Liyah Amma Bata picking, Kiran layin mummy ta Shiga yi Mummy na picking bata tsaya gaida ta ba Tace "Mummy Ina Liyah?"
Cikin rashin fahimta Tace "Lafiya me ya faru? Ya naji muryar ki haka?"
"Mummy ki amsa min mana tana gida ne?"
"A'a Bata gida, ta na makaranta,me ya faru?"
"Mummy jini na gani a fuskana Ina tsoro kar wani abune ya same ta, Amma Bari zanje makarantar na duba ta"
"Toh duk yanda ake ciki call me"
"Okay" sai ta katse wayar.
Mummy a fili Tace "Oh Allah Allah ka kawo Mana karshen abin Nan" sai ta haura sama.
Rai a b'ace Sageer yace "Ke Wace irin Mahaukaciya ce?meyasa Baki da hankali kin san ita d'in wace ce? Kin San me tazo yi a wurina kin San maganar me muke tattaunawa?"
Liyah mamaki ne ya Kama ta Tace "Sageer kasan da wa kake magana kuwa? Liyah ce fa Liyah d'inka yau Ni kake cewa mahauciya?" Tana nuna kanta.
"Na sani dake nake, to me hankali zaiyi abinda kikayi ne? Liyah na gaji na gaji bazan iya ba daga Yanzu Kar ki sake kirana idan Kika ganni a hanya ki nuna Baki sanni ba"
Ya juyo ya kalli yarinya yace "am sorry please Mu fita waje please" ba musu ta fita, zai fita Liyah tayi saurin rike Masa Riga tace "Sageer please am sorry Kar kamin haka Dan Allah please don't break up with me"
Fincike hannun ta yayi yace "To hell with you Liyah am fade up, am breaking up with you Kar ki sake nema na, na gaya Miki" Yana Kai Nan ya fita, ita Kuma ta zube a gun sai aikin kuka take students na gun sai kallon ta suke wasu na Jin tausayin ta wasu Kuma suna magana kasa kasa Wanda suka ga abin ya faru Kuma dariya suke da fatan Allah ya Kara.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Please wa anda suke Wattpad please ku daure ku Rika min vote please
Please and please
Milhat ce
Yar terawa
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu''' .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
Follow me on Wattpad
@milhaat🙏🏻
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Not edited
'''PAGE'''2️⃣5️⃣0️⃣↪️2️⃣6️⃣0️⃣
'''PREVIOUSLY'''
Fincike hannun ta yayi yace "To hell with you Liyah am fade up, am breaking up with you Kar ki sake nema na, na gaya Miki" Yana Kai Nan ya fita, ita Kuma ta zube a gun sai aikin kuka take students na gun sai kallon ta suke wasu na Jin tausayin ta wasu Kuma suna magana kasa kasa Wanda suka ga abin ya faru Kuma dariya suke da fatan Allah ya Kara.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............. A tare suka Shiga gida, Aniyah na parking motar ta ta nufi In da Liyah tayi parking.
Zaune take acikin motar babu abinda take yi sai kuka ganin Aniya yasa ta fito, cikin nuna kula da tausayawa Aniyah Tace "Liyah me ya same ki? Na shiga tashin hankali ganin jini a fuskata bayan hakan Kuma na fi awa in ganin hawaye a idanuna meya same ki?"
Shiru Bata ce Mata komai ba, a Karo na biyu ta ce "Please Liyah answer me, me ya same ki"
Cikin muryar kuka Tace "Shikenan hankalin ki ya kwanta ko?"
Cikin rashin fahimta Tace "Kamarya hankali na ya kwanta ban fahimce ki ba?"
Murmushin takaici tayi Tace "Hankalin ki ya kwanta Mana ,Sageer ya rabu Dani yace kar na sake kula shi"
Dafe kai Aniyah tayi Tace "To Ni Kuma me Hadi na da shi da har Zaki ce hankali na ya kwanta, Liyah is high time da ya kamata ki daina d'aura min laifi"
A tsawace Tace "Karya kike munafuka nasan komai kina son Sageer shiyasa yace mu rabu"
Murmushin gefen baki tayi Tace "Ina son Sageer shiyasa yace ku rabu? Does that even make sense to you? Ki sani ke yake so ke ya Fara sani ba Ni ba, Ni dai Dan Allah ki daina d'aura min laifi akan abinda ban sani ba, mu koma kamar da please"
"Abu d'aya Zaki min mu koma kamar da"
Da sauri Aniyah Tace "Mene ne? ki fad'a min zanyi Miki shi sabida na gaji da abinda ke faruwa"
"Kije ki dai daita tsakani na da Sageer idan Kika min haka zan manta komai na yafe Miki"
Cike da mamaki Aniyah ke kallon Liyah sannan Tace "Hakan kuskure ne Liyah zai samu damar Raina ki, ki Bari in dai Yana son ki zai dawo gare ki"
"Hmm na sani dama haka Zaki ce, zargina ya tabbata Kenan"
"No wallahi ba haka bane ki fahimce ni"
"Zan fahimce ki ne idan Kika yi yanda nace" tana kaina Nan ta rufe kofar motar da karfin gaske har Saida Aniyah ta tsorata, ta shige gida ta bar Aniyah a tsaye cikin tunani.
*ADAMAWA*
"Daddy Dan Allah ina neman wata alfarma ne a gunka" Maryam ke wannan maganar tana kallon wani tsoho da zai haura shekaru arba'in, farin glashin idon sa ya cire sannan ya rufe news paper dake hannun sa ya aje Akan tebur d'in dake gabansa, sannan ya Maida kallon sa gare ta ya ce "Ina sauraron ki my daughter"
D'an Jim tayi Kan Tace "Daddy please ka taimaka min naje na ga mummy na Kai kusan shekaru goma ban ganta ba"
Jin hakan yasa duk annurin dake fuskar sa ya gushe, Rai a d'an b'ace yace "Sau nawa nace Miki ki daina min maganar ta, na Sha fad'a Miki ki daina tambaya ta zuwa ganin ta don bazan bar ki ba"
Cikin kuka tace "Daddy please....."
'daga Mata hannu yayi yace "Bana son jin komai daga gare ki tashi ki bani guri"
Zubewa tayi a durkushe a gaban sa ta had'a hannayen ta guri guda Tace "Daddy Dan Allah kayi min wannan alfarmar ko da kuwa itace alfarma ta karshe da zaka min Dan Allah"
Tashi yayi ya tsaya ya hard'e hannayen sa duka biyu ta baya Yana kaiwa Yana kawo wa sannan ya tsaya chaak Yana kallon ta yace "Meyasa a lokacin da na Baki zab'i ko Ni ko ita Kika zab'e Ni? Bayan hakan munyi yarjejeniya dake Akan baza ki tab'a zuwa gun ta ba"
"Haba Daddy ko Allah ma muna Masa laifi ya yafe Mana Amma Daddy Kai ka kasa yafewa mummy Kun Sani a tsakiya Daddy shekaru dayawa sun shud'e kamata ai ku manta komai"
A tsawace yace "Ke!! Lallai yarinyar Nan wato don Kinga ina son ki Ina shagwab'a ki fiye da Sauran 'ya 'ya na shiyasa kike fad'a min maganar da ranki yake so ko?"
"Kayi hakuri Daddy idan maganar da nayi ta b'ata maka raai ko kad'an ban fad'i hakan don na b'ata maka Rai ba, Allah ya huci zuciyar ka" ta tashi da niyar tafiya sai Taji ance "Haba Abban Maryam ya kamata kaji tausayin yarinyar Nan ka barta taje ta ga mahaifiyar ta Dan Allah"
Cikin sauri Maryam Tace "A'a Umma Dan Allah Karki sa baki a maganar duk sanda Kika sa baki ba ku kare maganar da dadi"
"Kyaleni Maryam dole na fad'a Masa gaskiya ko Yana ko baya so haba, Meyasa kake son kanka dayawa? Anan fa kullum sai kaje ka duba mahaifiyar ka don ganin ya Laifiyar ta take Amma yarinyar Nan tun tana da shekaru biyar aka raba ta da Uwarta kullum cikin rokon ka take Amma kaki bata izini Gashi yau harta gama jami'a har ta Fara aiki Amma Shiru kake ji idan zaka daina son Kan ka ya kamata ka daina kayi abinda ya dace"
"Iyeeee lallai saudat Ni kike yi wa tsawa? Sannu Uwata,To ko Zaki sa hannu ne?"
Ya na nuna Mata bayan sa, "A'a me yayi zafi daga fad'an gaskiya Sai cibi ya Zama kari? A matsayina matar ka Dole ma fad'a maka gaskiya ko kana so ko ba ka so"
Huci yayi yace "Ehh hakane, to ki sani ki dab da barin gidan Nan"
"Toh sai me don ka sakeni a kaina a kafara? Dama d'aya ya rage kaga shikenan" tana kaina ta haura sama Yana Mata magana tayi burus dashi yace "Saudat ki dawo Nan ban gama magana dake ba"
Juyo wa tayi ta kalle shi Tace "Sai ka Bari idan naje na fad'a wa Wacce zaka ji maganar ta in yaso sai na dawo mu cigaba"
Rai a b'ace yace "toh wallahi ba da izini na ba, idan Kika fita a gidan Nan ban yafe ba"
Yar karamar dariya tayi tace "kwantar da hankalin ka alhajina ba fita zanyi ba, ka manta Yanzu muna cikin zamanin technology wayata zan d'auko na Sanar Mata abinda ake ciki" tana Kai Nan ta shige d'aki da sauri.
Ganin hakan yabi bayan ta fuuuu, Maryam ganin hakan ta shige d'akin ta, Yana Shiga ta samu har ta kirata yana ringing da sauri ya kwace wayar ya katse had'e da fad'in "Ashe baki da hankali ban sani ba?"
Hannun a kwankwaso tayi d'aurin ture kaga bala'i tana bubbuga kafa d'aya wani irin kallo ta Masa Tace "Kai hankalin naga kake dashi shiyasa kake Abu kamar Wanda ya gudo daga gidan mahaukata"
Kama Baki yayi yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Ni Ni Saudat gidan mahaukata?"
Wani irin harara ta Masa Wanda yasa ya Sha jinin jikinsa, karar Wayar yasa shi saurin dubawa yaga lambar hajiyarsa ce, Mika Mata wayar yayi yace "Dan Allah Karki fad'a Mata komai kinji?"
Murkuda Masa Baki tayi Tace "Sai na fad'a" da sauri ya Fizgi wayan yayi picking da Sallama daga d'ayan b'angaren Tace "Ha ahhhh Kaine dama? Ina saudatun?"
"Emm emmm ta Shiga wanka"
"Toh wane ne ya kirani naga missed call?"
"Itace ina ganin gaisuwa ce kawaii"
"To too Kuna lafiya dai ko?"
"Eh lafiya kalau"
"Kace lafiya Kuma nake Jin muryar ka wani iri?"
"Daga bacci nake hajiya"
"Toh shikenan, yauwa idan Allah ya kaimu gobe ku turo min yarinyar Nan Mairamu"
"Toh hajiya insha Allah" sai ta katse wayar.
Dariya Umma tayi Tace "Ta ma fi sauki kaga sai ta Sanar Mata Baki da Baki sai yafi dad'i ma"
"Saudat wallahi ki kiyaye ni, toh shikenan na amince taje d'in"
Umma Murmushin had'e da dariya tayi Tace "Dan Allah dagaske kake alhaji?"
"Ta shirya jibi taje"
Da sauri ta rungume shi sannan ta sumbace shi a goshi Tace "Shiyasa na ke Kara sonka Alhaji na"
Ture ta yayi a Kan gado ya wurga Mata wayarta yace "Zaki ce haka ai tunda an cuce Ni" sai ya shige ban d'aki,dariya tayi ta fice daga d'akin ta haura saman Maryam.
Umma na fad'awa Maryam tsalle tayi ta rungumeta ta tana kukan farin ciki tayi ta Mata godiya,umma ta tabbar mata da bakomai hakan zata yi wa 'ya 'yan cikin ta.
Tun a Daren ta Fara Shiri, ta Kira mahaifiyar ta ta shaida mata tayi farin Ciki matuka, Bata yi kasa a gwiwa ba ta Sanarwa mijin ta Shima yayi murna don Haka kawai Allah ya d'aura Masa sonta.
MARYAM A KANO
Karar horn d'in da yaji yasa shi saurin mikewa ya fito daga part d'in sa da sauri,mummy na ganin sa ta kad'a Kai tace "Haba Irfan kabi a hankali Mana ai Nan zata shigo"
Murmushi yayi yace "Bari dai naje na taro ta"
Fitar sa yayi dai dai da lokacin da ta sauko da kafarta d'aya a waje tana zaune daga cikin mota ganin sa yasa ta fita da gudu tana dariya had'e da fad'in "Oyoyo Yaya" Shima Dariya yayi yace "Oyoyo Yar Kanwata" rungumar sa tayi kyam da sauri ya ture yaji ya soma Shiga wani irin yanayi, cikin muryar shagwab'a Tace "Yaya lafiya?"
"Lafiya kalau Zo mu Shiga daga Ciki"
Turu baki tayi tace "Ture Ni fa kayi"
Yace "Eh Mana Baki San kin girma bane?"
Rufe fuskan ta taking da hannayen ta tana dariya kasa kasa, rankwashin ta yayi sannan ya riko hannun ta Kai tsaye parlor suka Shiga suka tarar da umma na shirya dinning da gudu ta nufi inda take ta rungume ta.
Kuka Mai sauti ta sake, ta rungumi Umma a jikinta kyam kamar zata shige jikinta, Umma na rarrashin ta yayin da Maryam kamar ce mata ake ta Kara kukan, hakan yasa ummu ta Shiga kuka, Sageer nad'e hannun say yayi ya jingina a jikin bango Yana kallon su sun d'auki kusan mintuna goma a Haka sannan ya Karasa inda suke yace "Mummy and daughter love, Yanzu dai ki fahimtar Dani kukan me kuke? Nasan it has been long Baku had'u ba Amma kukan Nan ya Isa haka mana Kar hawayen ku ya Kare"
Rankwashin sa Umma tayi Tace "Kaga ja'iri Ina ka tab'a Jin hawaye ya kare?"
Tsotsa inda ta rankwashe sa yayi hade da fad'in "Ban tab'a gani ba Amma Idan kuka cigaba da hakan za a Fara a gidan Alhaji Mubarak Dalha."
Gyaran murya sukaji, duk su ukun suka Maida kallon su I zuwa saman steps d'in Murmushi yayi yace "Kai Irfan me Kuma iyalan Alhaji Mubarak Dalha sukayi?"
Murmushi yayi yace "Abba Ashe kana Nan na d'auka ka fita?"
"A a wane Ni My one and only daughter zata Zo ai Dole na aje komai"
Da saurin ta nufi inda yake ta gaishe shi cikin girmamawa ya amsa ba yabo ba fallasa yace "Da alama My Maryam ta girma Yanzu 'yar hug d'in da akeyi wa Abba babu?" Yana bud'e hannayen sa.
Murmushi tayi ta rungume shi,ya Dan shafa kanta yace "Allah ya Miki Albarka" ta amsa da ameen, "Abba Ni kuma fa?"
Umma rike Baki tayi Tace "Oh ni zanga ranar da Irfan zai girma haryanzu kishi kake da ita?"
"To Umma cewa fa yayi Allah ya Mata Albarka kamata ai yace Allah ya muku Albarka"
Maryam tace "Yaya Yanzu duk tsawon lokacin Nan da kake ta kwasan Albarka na yau kawai sai ya tada maka hankali, Amma naji dad'in ganin ku a Haka Abba ban yi tunanin zan ga ranar da Kai da Yaya zaku yi Wasa harda dariya ba"
Murmushi yayi yace "Ni kaina banyi tunanin hakan ba My Daughter Don gaskiya har na cire Rai Amma Yanzu gashi kusan four years Kenan kamar ba a yi ba"
Umma Tace "ai Alhaji har Ni kaina mamaki nake lokaci d'aya ya canza"
Yar karamar dariya yayi yace "Ni kaina banyi tunanin Aniyah zata canza min tunani ba"
Umma tace "me kace?"
Yace "A a cewa nayi ku tayi na da addu'a Allah ya cigaba da Kara shirta muka Ni"
Abba yace "Addu'a Kam muna Kai ai, Allah ya Albarkaci Rayuwar ku"
Duk suka amsa da ameen.
Umma Tace "Maryam je ki watsa ruwa nasan kin d'ebo gajiya hirar Nan ba Karewa zaiyi ba"
Ta ce "To Umma"
Ta nufi part d'in da aka gyara Mata Sageer yace "Ke wa zai d'aukan Miki tarukucen ki?"
Turo Baki tayi tace "Yaya pleeeeassse"
Zaro Ido yayi ya kalle ta yace "Please what?"
Sai ta nuna Masa akwatin ta, yace "Laa ila yarinyar Nan ta Raina Ni Amma bakomai tunda yau ke bakuwa ce zan bauta Miki Amma Zaki ji a jikin ki" da sauri ta bargun shi kuma ya bita da akwatin.
Yana Shiga ya samu harta Shiga ban d'aki ajiye mata yayi, yayi ficewar sa bayan ta gama wanka sukaci abincin a ka zauna zaman hiran yaushe gamo.
"Mummy"
"Subhannallah Liyah me ta same ki? Ki duba fuskan ki duk jini hankalin Yar uwar ki ya tashi Sosai"
"Hmm na munafurci ne abinda take so ke ta samu Akan me hankalin ta zai tashi?"
"Kamarya abinda ta so ta samu, kimin magana ta yanda zan fahimce ki?"
Cikin muryar kuka Tace "Mummy Sageer ya rabu Dani Kuma na tabbata Aniya ce sila"
"Ya rabu dake? To me hujjan ki na cewar itace sila?"
"Sabida duk abinda nake so sai ta nemi hanyar rabani dashi"
"Ya Salam Liyah ki daina fad'an haka Aniyah baza ta yi miki Haka ba ya kamata ki daina d'aura Mata laifi"
Murmushin takaici tayi Tace "Nasani Dama haka zakice na manta Ashe fa Bata laifi ko?" Tana kai Nan ta haura sama Rai a b'ace mummy kuwa kallon bayan ta take har ta shige d'akin.
Jiki a mace Aniyah ta shigo mummy na ganin ta ta gane sun had'u, rarrashin ta kawaii ta Shiga yi Aniyah ta kirki murmushin karya Tace "Bakomai mummy na mata uzuri nasan tana Jin zafin rashin masoyin ta ne Dole tayi hakan"
Mummy Tace "Allah ya Miki Albarka Aniyah tabbas ke 'yace"
"Ameen mummy bari na watsa ruwa"
"Dan Allah ko da zata Miki magana Karki kulata kinji?"
"Tog mummy"
Tana Shiga d'aki ta tarar da ita zata shiga wanka a nitse tace "Liyah na amince zanyi wa Sageer magana"
Da sauri Tace "Dan Allah dagaske kike ?"
"Eh dagaske nake"
Rungumar ta tayi Tace "Nagode" sai ta Shiga ban d'aki, Aniyah mamaki ne ya rufe ta, ta manta ranar da Liyah ta tab'a jikin ta da sunan runguma, tun da Sageer ya Shiga Rayuwar su ya rusa dukkanin farin cikin su Amma taji dad'in hakan.
A ranar tare sukaci abinci sukayi kallo tare, duk kowa sai da yayi mamaki musamman ma Daddy da yasan ya Yanzu yaran shi basu jituwa.
Har restaurant d'in da suke yawan zuwan da Sageer da je da fatan zata ganshi taci Sa'a ta tarar dashi a gun Yana Shan coffee, Yana ganin ta ya b'ata Rai da Sallama ta Isa gun sa, Amma Bai amsa ba tace "Haba Sageer Sallama fa na maka Kuma baza ka amsa ba"
Kauda Kai yayi yace "Wa alaikissalam"
Tace "zan iya zama?"
Yace "Malama nasan ki ne da Zaki ce min Zaki zauna?"
"Haba Sageer Dan Allah kayi hakuri muyi magana please lets fix this"
"Bana bukatar fixing komai da ke kin gane ko?"
"To naji Amma Dan