Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 66367 words

Chapter 16 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

yi Wanda nake so zata so?"


Mummy kad'a Kai tayi Tace "Sai Yanzu na fahimci komai, Alhaji mu Shiga da ga Ciki maganar Bata Nan bace"
Yace "Okay mu shiga"
Har sun Shiga suka bar Sageer a tsaye a gun, Daddy ya leko yace "Kai ma ka shigo"


A Parlor suka zauna, Mummy da Daddy a Kan kujera yayin da Aniyah na zaune a kasa gefen Daddy Daliyah Kuma a gefen mummy, Sageer Kuma na zaune a kasa ta gefe ya wani rakub'e jikinsa a mace.


Daddy ne yayi gyaran murya yace "Sageer Ina maka kallon mutumin kirki, na d'auka ka shigo Rayuwar mu ne da Alhairi Ashe zuwa kayi ka rusa min zurii ta, Taya za'a yi kaso Ya Kaso kanwa?" Rai a b'ace yake maganar Nan mummy Tace "Alhaji kayi hakuri Kar ka tashi hankalin ka Naga Ranka ya b'aci sosai mubi abun a sannu"


"Taya za'a yi na kwnatar da hankali na ki duba kiga jikin yaran Nan" Yana nuna Liyah da Aniyah, ya d'aura da fad'in "Jikin su duk jini suka kokarin kashe Kan su"


Mummy Tace "Ai wannan ba sabon Abu bane ba, ai ciwon da Liyah ta jiwa Aniyah ne ya dawo jikin ta ko ka manta yanda suke ne?"
"Ban manta ba, Banda ke Jaka wawuya baki San idan Kika cutar da ita kin cutar da Kanki bane?"


Liyah sai turo Baki take Tace "Daddy Meyasa kake min fad'a bayan laifin ta ne? Nifa Daddy na Riga na lura tun ba yau ba Kunfi son Aniyah akai na, bata tab'a muku laifi ba Sabi da itace sanyin idanun ku a gidan Nan, hatta Huzaifa da Yusuf sunfi sonta akaina"


Tsawa Mummy ta Mata Tace "Ke Liyah Ashe baki da hankali? Mahaifin kine kike yi wa magana haka?"
Tashi tayi Tace "Dama nasan haka zakuce kullum Ni a Mara hankali kuke d'aukana"
Ta na kaina ta haura sama da gudu tana kuka.


Mummy na Kiran sunan ta Amma Bata tsaya ba bare ta saurare ta ba Daddy yace "Kyale ta, kyale ta ina dab da cire ta a jerin 'ya 'ya na"
Aniyah tayi saurin fad'in "A'a Daddy kayi hakuri Kar kace haka sannan Kar kayi fushi da ita kasan fushin ka akan ta babban matsala ce" ta Maida kallon ga Mummy Tace "Dan Allah kuyi hakuri mummy, duk rashin fahimta ce, Liyah na da kishi sosai shi Kuma Irfan da ya ganni ya d'auka itace, Ina fad'a Masa bani bace sai yaki yarda muna cikin magana ne shine ta fito ta ganmu tare, Amma Irfan baida laifi"


Huci Daddy yayi yace "Ikon Allah, na fahimta, Sageer kayi hakuri da kalaman da nayi a kanka"
Cikin sanyin murya yace "Kayi hakuri Daddy, Wallahi ba da son Raina hakan ya faru ba"
"Kar ka damu,insha Allah Zan San yanda za'ayi"
"Toh shikenan Daddy Ni Zan wuce"
Sai ya fita, Yana fita mummy Tace "Yau naga tashin hankali, wannan wani irin abu ne wannan? Alhamdulillah abin yazo da sauki Mama na bacci yau da kaaam.......hmm, Allah dai ya rufa asiri"
Daddy ya amsa da "Ameen" mummy ta Maida kallon ga Aniyah Tace "tashi kije kiyi wanka ki gyara jikin ki"


Ba musu ta tashi ta turo kofan Amma a rufe, ta Shiga kwankwasa kofar shiru, Liyah na zaune a d'akin a kasa sai huci take, zuciyar ta na tsaka Mata abubuwa masu kyau da maras kyau.


Mummy ta jiyo Karan buga kofar da sauri ta tashi ta haura sama, Tace "Aniyah mene ne haka?"
Langwabe Kai tayi Tace "Mummy tun d'azu nake kwankwasa kofar Amma bata bud'e ba, Ina tsoro kar ta cutar da kanta"


"Mtsww keta ne kawaii irin na Liyah" sai ita ma ta Shiga kwankwasa kofar, Amma shiru,Rai a b'ace tace "Liyah open this door Kar ki Bari na bud'e da kaina" shiru a Karo na biyu ta Kuma fad'in "Liyah baza ki bud'e kofar Nan ba?"


Duk abubuwan sa suke yi tana Jin su, chaan wata zuciya ta Raya Mata ""Tunda kike da mummy Bata tab'a Miki tsawa ba, Amma yau kin b'ata mata raai? Hakan bai dace ba Sam"


A zabure ta tashi ta bud'e kofan sai ta koma da sauri ta Kwanta akana gado tana kuka, Rai a b'ace mummy ta Shiga d'akin Amma ganin ta haka sai Taji duk ba dad'i, Nan fa ta Shiga rarrashin ta, tana fad'a Mata dalilin da yasa Sageer ya rike hannun Aniyah, tashi tayi ta zauna, Tace "Mummy kina wurin ne? Bakya Nan Baki San me na gani ba da idona fa na ga ya rike hannun ta Kuma tun ba yau ba suke had'uwa....." Na ta Fara jero Mata tun daga ranar da Liyah da Sageer suka Fara had'u wa daga farko har izuwa Yanzu da ya rike hannun ta.


Mummy murmushi irin nasu na manya tayi Tace "Magana ai a fili take Liyah ke da Kanki kince it was a mistaky Kinga Kenan ba laifin su bane laifin ki ne da tun farko Baki Sanar masa ku biyu bane so Kar ki d'aurawa kowa laifi, laifi Kam naki ne ki daina tada hankalin ki"


Murmushin gefen baki Liyah tayi ta ce "Na sani dama at Long last zaku ce nice da laifi Ni ban tab'a yin Abu dai dai ba, sai favorite daughter d'in ku" tana wurgawa Aniyah dake tsaye a jikin kofa wani irin mugun harara da Ke cike da na tsana.


Mummy Tace "Na Hana ki fad'an haka Liyah duk d'aya kuke a gun mu babu Wanda bamu so, idan bana son ki ai bazan bari kizo duniya ba tun a ciki zan kashe ki, Amma kin kasa fahimta" riko hannayen ta tayi dukka biyu Tace "Ni mahaifiyar ki ce Liyah na San halayyan ku duka Kama da ga Kanki kece babba har izuwa kanin ku Huzaifa, Liyah matsalar ki d'ayane zuwa biyu, Kina da son Kan ki dayawa sannan baki da hakuri wannan abunne yake damin ki, kiyi koyi da Yar uwar ki Mana"




Liyah Sam Bata ji dad'in Maganar Nan ba ji tayi ta Kara tsanar Aniyah, Dole ma ta San yanda zatayi da ita, Mummy ta katse mata tunani Tace "Nasan ranki zai b'aci sabida na fad'a Miki gaskiya, shi gaskiya d'aci gare ta daga kinta sai b'ata"


Jiki a sanyaye Aniyah ta Zo ta zauna kusa da Liyah Tace "Sis am very sorry please ni Wallahi ba son shi nake ba kamar yanda Kika fad'a ba it's just a big misunderstanding, ki fahimce Ni please"


"Zan fahimce ki ne Idan Kika yanke jikin ki daga nashi"
"Shikenan I promise bazan sake had'uwa dashi ba, Amma Ina so ki sani ba mu tab'a sa schedule Akan zamu had'u ba duk mistake ne at a wrong time"


Liyah Tace "Amma kin San...." Mummy tayi saurin fad'in "Ya Isa haka Liyah ki daina maimaita magana d'aya ta Baki hakuri please komai ya wuce Dan Allah, Dan Allah na roke ku ki had'a Kan ku Kar ku bari wani ya Shiga tsakanin ku" sai ta mike had'e da fad'in "Ki tashi ki gyara jikin ku Kunga an Fara Kiran sallaar Maghriba" tana Kai Nan ta fita, Aniyah ta tashi ta Shiga ban d'aki tayi wanka sannan ta d'aura alwala, Liyah ma hakan tayi.


Sageer na Isa gida ya Shiga side d'inshi dake babban parlor ba kowa sai ya Shiga da sauri don Baya so a ganshi a haka, Yana Shiga ya Kwan ta ruf da Ciki ya dad'e a Haka sannan ya tashi ya zauna yace "Wallahi bazai yu ba duk yanda za'a yi na samu Soyayyar Aniyah zanyi sabida itace ta dace dani ba Liyah ba, halin Liyah ya banbanta da na Aniyah, Kuma Ina da tabbacin Aniyah nake so ba Liyah ba" Yana cikin wannan tunanin ne wayar sa ta Fara ringing, Yana dubawa yaga Ra'ees ne tsaki ya jaa ya cigaba da tunanin sa, Ra'ees sai faman Kira yake, rai a b'ace yayi picking a tsawace yace "Kai Dan Allah malam wani irin Kirane Haka? Ka Kira ka Kira ban d'aga ba sai hakura Amma ka dami muta..." Jin abinda Ra'ees yace ne yasa ambatan "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, what? Rumana ta rasu, look ka daina min irin wannan wasan"


"Haba Sageer Wasa da mutuwa Taya za'ayi na maka Wasa da mutuwa? Mutuwar ma Akan Ruman?"
Shiru yayi sannan yace "Yaushe ta rasu?"
"Tun safe har an kaita"
"Haba ya zaka min haka tun safe sai Yanzu zaka fad'a min?"


"Ka duba wayoyin ka sau nawa na Kira ka baka d'aga ba na Kira karamar Wayar ka yafi a irga yanzun ma mubarak ne yaje gida neman ka ganin mun dad'e Muna Kira baka d'aga ba yazo yaji ko lafiya sai hajiyar ka ta bashi wannan number"


"Am so sorry, na bar wayan a gida ne, Allah ya jikan ta Amma me ya same ta?"
Nan ya labarta Masa, jikin Sageer yayi sanyi matuka, ya Masa ta'aziyya da tabbatar Masa gobe zai Zo insha Allah.




*OXFORD UNIVERSITY*
A yau sukayi graduating, iyayen Maryam, Sabir da Rahina duk sun Zo, akayi Hidima, bayan an gama suka koma gida, bayan Sati Kuma su Sabir suka koma gida (NIGERIA), Sabir dake ya samu results Mai kyau suka bashi aiki a gun amma yaki karb'a "Ni zan koma kasata ne na bauta masa" fad'in bakin sa,Maryam tayi tayi ya karb'a Amma yaki, tare suka koma suna sauka a airport na Abuja Sabir da Rahina sukayi Kano, Maryam Kuma tayi adamawa.


"Aniyah kin kini ko Tunda na bar makarantar Nan Kika daina ne Mata" Hafeez ne ke wannan maganar Yana driving, Murmushi tayi Tace "Wallahi ba Haka bane, Yaya Hafeez Kai ma fa kasan lamarin makarantar Nan sai a hankali Yanzu Muna final exam Dole mu maida hankali Sosai Kar a samu matsala"


"Hakane Kam kina da gaskiya, Albishirin ki?"
"Goro"
"Hmmmm na samu aiki"
"Dan Allah? dagaske a ina? Yashe?"
Dariya yayi yace "duk Ni kad'ai zan amsa wannan"
Tace "Eh"
"Toh Allah dagaske nake, A medical center,jiyayan Nan na samu aikin"


"Wow Masha Allah, na tayaka murna Allah ya yi taimako yasa ka Fara a sa'a"
Ya amsa da "Ameen nagode Sosai" yaga sai Murmushi take yace "Ya naga kamar har kin fini farin cikin samun aikin nan?"


"Eh ai Dole, ai Kai yayana ne?"
Murmushi yayi yace "Hakane, Amma zan so na Zama uba a gare ki na Kare ki daga duk wani mugun Abu, zan so na Zama Yayan ki na soki da dukkanin Soyayya zan so mu zama abokai muyi Wasa da dariya kamar Yara kanana"


Sai kallon sa kawaii take ta kasa fahimta,ganin kallon yayi yawa yace "hajiya mun iso ki fita Kar ki makara"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Mu had'u a page na gaba.
Milhaat ce
Yar Terawa
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_




```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```



*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
NOT EDITED🥱
```PAGE``` 2️⃣3️⃣0️⃣↪️2️⃣4️⃣0️⃣️⃣
Sai kallon sa kawaii take ta kasa fahimta,ganin kallon yayi yawa yace "hajiya mun iso ki fita Kar ki makara"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
........... Har Yanzu dai kallon sa take yi, yace "Aniyah yadai wani irin kallo ne Haka? Lafiya kuwa?"


Murmushi tayi Tace "Na kasa fahimtar maganar kane ai"
Yar karamar dariya yayi yace "Kinga karkiyi tunani dayawa akai fa, kawaii na fad'a ne ba wani Abu ba"


Murmushi tayi Tace "Okay shikenan to, sai anjima" sai ta fita har zata tafi yace Mata "anjima zan sa a taho Miki da motar ki"
"Okay nagode"




Aniyah ranar wuni tayi tana tunanin kalaman Hafeez "maganganun sa sun nuna alamun so, wani b'angaren Kuma Abota na kasa gane me yake nufi, by the way ko ma mene ne with Time zan sani"
Ta cigaba da karatun.


B'angaren Liyah da Sageer Kuma sun shirya kamar babu abinda ya Shiga tsakanin su, hakan yasa ya gaiyace ta suje restaurant daga school yazo ya d'auke ta suka wuce, zaune suke suna cin abinci wata yar budurwa kana ganin ta kasan sa'annin su Liyah ne, tana ganin Sageer cikin sauri ta Karasa gun Tace "Wow Irfaan ko ba Kai bane?"
Murmushi yayi yace "Eh nine"


"Alhamdulillah na dad'e ina son ganin ka I am your number one fan ina bala'in son wakokin ka, Dan Allah zamu iya d'aukan hoto"


Murmushi yayi yace "Sure why not"
Sai ta mikawa Liyah wayarta, Taki karb'a Sageer ya Mata magana a kunne Wanda na kasa Jin me yace Mata gani nayi ta karb'a Rai a b'ace, tsaye suke suna jira ta d'auka musu pic d'in sai ji nayi paaaaassss, yarinyar ta ambaci "Innalillahi baki da hankali ne Zaki Yar min da waya"


Liyah Kama Baki tayi Tace "Wayyo Dan Allah kiyi hakuri ba da sani na bane ya sub'uce min ne"
Tsaki tayi tace "Yar talakawa nasan Baki San kud'in wayar Nan ba shi yasa kike ce haka"


A tsawace liyah Tace "Ke ki iya bakin ki Wallahi in ba haka ba na gyara Miki zama"
Sageer yayi saurin fad'in "Dan Allah kiyi hakuri kije kinji am so sorry nasan baza ta yi hakan da gangan ba"


"Mtswww Irfan Wallahi don Kai ne zan bar yarinyar Nan if not.....hmmm Shawara ka canza yarinyar Nan Sam bata Dace da Kai ba na barku lafiya"


Liyah tabi bayan ta da niyar Kai Mata duka da sauri Sageer ya riko hannun ta yarinyar na barin gun ya saki hannun ta da karfi, yace "Liyah abin naki dama ya Kai har haka, meyasa Zaki fasa Mata waya?"
"Na fad'a maka Kar ka d'auki hoton ka ki Kuma don wulakanci ma kace nice zan d'auka muku? Kasan irin Soyayyar da nake maka da Kuma kishin da nake akan ka Kuma ka min haka?"


Dafe Kan sa yayi yace "Oh my God Liyah!!! Liyah!!! Wai shi so haukane Kam? Ki duba kiga yanda Kika Tara Mana jama'a suna kallon mu"
"Matsalar suce Kai ba ma ta Ni kake ba? Ta mutane kake?"


D'aga Mata hannun yayi yace "ya ishe ki haka"
Ai kuwa Liyah ta fashe da kuka Sageer kallon ta yake cike da mamaki a zuciyar sa yace "Oh Allah Kai ka had'a Ni da ita nasan Kaine kad'ai zaka raba Ni da ita, nayi kokarin koya wa zuciya ta Soyayyar ta Amma na kasa she is impossible" huci yayi ya durkusa a gaban ta yace "Babyna am sorry kinji"
Cikin muryar kuka Tace "Har tsawa fa kamin a kanta"


"Na sani ban kyauta ba shiyasa nake baki hakuri, please ki daina kuka kinji? Bana son ganin hawayen ki please"
Shiru tayi tana shesshekar kuka yace "Zaki Sha ice cream?"
Dake yasan ita d'in mayyar ice cream ce, murya chan kasa Tace "Eh"
Murmushi yayi yace "That's My Liyah tashi ki zauna bari na karb'o Miki ko?"
Ta amsa da "Toh"


Bayan ta Gama Shan ice cream ya Maida ta school dake tana da lectures karfe hud'u.


Yaune ake d'aura auren Fareedah da Mubarak su Liyah sai rawan Kai ake manyan kawaye, tun daga ranar Monday ake ta Hidima both familyn Amarya da Ango, mummy tayi da Aniyah su tafi bikin tare da Liyah Amma Taki Tace "Mummy kin San halinta fa Sarai Yanzun Nan mistake kad'an tayi fushi ta zubar Mana da mutunci musamman ma da naji Angon abokin Sageer ne"
"Kinyi gaskiya Allah ya sa su Gama lafiya"
Ta amsa da "Ameen"


Ranar asabar akayi dinner, bayan an gama dinner aka wuce da Amarya gidan ta.
Bayan salar Isha su Liyah da Sauran kawayen ko Wacce ta koma gida, su Sageer da Ra'ees sune suka rako Ango, bayan sun musu hud'u ba suka tafi.


Bayan tafiyar su mubarak yace "Kasshh nayi mantuwa a mota bari na d'auko"
Yana fita ya bud'e motar ya duba baiga ledan ba, wayar sa ya zaro ya Kira Sageer yace "My man ina kuka aje ledan kazar?"
Ra'ees yace "Kaiiyaaaa kagan shi anan ya akayi muka manta ne?"


Tsotsa keya yayi yace "Yanzu Kuna ina ne?"
Sageer yace "Zanyi dropping d'in Ra'ees a gida ne mun ma Isa gidan"


"Okay gani Nan zuwa na karb'a"
Sageer yace "Ka bari zan kawo maka"
Yace "Inaa ai Wallahi bazan iya jiran ka ba gani Nan zuwa"
D'akin ya koma yace "My D!! Ina zuwa please Yanzu zan dawo, kinyi sallah?"
Ta d'aga Kai alamun "eh" yace "Okay Bari nazo"
Ta ce "To"
Cikin sauri ya fita Yana Isa ya tarar dasu a mota suna jiran sa, Yana karb'a ya juya sai tsokanar sa suke, bai kula su ba, cikin sauri yake tukin dai dai ya Shiga kwana bai Ankara ba sai karar fashewar glass naji, wata mota ce ta shigo da gudu Shima ya shigo da gudu, glass d'in gaban motar da ya fashe duk a fuskar sa jikinsa duk jini.




*KAUYE*
Rahila na zaune a kofar gida sai ji tayi ance "Rahila my daughter"
Tana d'ago kanta taga mahaifiyar Tace "da kyar ta mike" Mama ganin yanda take hakan yasa ta jaa da baya cikin d'aga murya Tace "Jesus Christ, Rahila!!! What am I seeing?"
Nna na Jin hakan ta fito cikin sauri tana ganin ta cike da mamaki Tace "Mummy Rahila it's you?"
Ta amsa da "Yes is me, what is going on here? Could someone please explain what am seeing"


Jiki a sanyaye Nnna tazo ta rike hannun ta Tace "Kizo mu Shiga daga ciki Kinga yanzu daga Kan hanya kike, Biko ooo take it easy please"
"What do you mean I should take it easy?"


Nnna ta kwantar da murya ta ce "ihun da kike fa bazai canza komai ba, it's her fate so we have to accept it ko Muna so ko ba mu so, so please kizo mu Shiga"


Jiki a sanyaye Mama take tafiyar sai kallon cikin Rahila take da ya girma, haihuwa yau ko gobe, Rahila ganin hakan yasa ta sunkuyar da kanta kasa.


Nnna tayi gyaran murya Tace "Mummy Rahila I was also shocked when I found out Rahila is pregnant but da ta fad'a min yanda ta samu cikin sai na Mata uzuri, ke Kanki kinsan yaran ki ba Yan iska bane kin San tarbiyab da Kika musu" Nan ta Sanar Mata da komai, Tun Kan Nnna ta gama bata Labari ta ke ta aikin kuka harda majina bayan ta gama fad'a Mata sai fashe da kuka ta d'aura hannu a Kai Tace "Chineke me wooo, chaaai prince ka cuce Ni I'll never forgive you, you have destroy the lives of my daughters"


Nnna kuwa aikin bata hakuri take tana bubbuga Mara baya, Rahila ita

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads