Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 66367 words

Chapter 13 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Kan ya dawo in da Sauran suke, Daniyah tayi kokarin ta gudu Amma duk sun tsare ta su a ganin su Liyah ce, tunda suka Fara rera wakar yake kallon ta wani irin kallo yake Mata Wanda yake nuna tsantsar so, Rumana ganin Haka ta Shiga yi musu hotuna da videos.


Liyah Kuma na gida tana ta sharb'an baccin ta Bata San Ma ana yi ba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
...........suna gama rera wakar suka nemi Aniyah suka rasa, tana barin gun ta koma department dinsu.


Bayan ta gama lectures d'inta ta koma gida ta tarar Liyah da Mummy na kitchen Kai tsaye ta Shiga ta musu Sannu sannan ta Watsa ruwa ita ma ta dawo kitchen d'in.


Bayan sun gama cin abinci kowa ya Shiga d'akin sa, Liyah na Hawa whatsapp tayi viewing status na Ruman, ga mamakin ta taga an rera wakar Kuma ga Sagheer da Mai Kama da ita, a razane ta zauna da karfi Tace "Kuttuman Uba" da sauri Aniyah ta tashi ta zauna tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Liyah me ya faru kike irin wannan ashariya?"


"Wannan kamar ke?" Tana nuna Mata fuskar wayarta, Murmushi tayi tace "Am sorry Wallahi na manta ne na fad'a Miki naje Neman ki ne sai suka d'auka kece nayi nayi na ganar dasu cewar mu biyu ne Amma sunki su saurare Ni"


"Ba zasu yarda ba sabida basu san mu biyu bane Kuma kammanin mu ya b'aci mu identical twins ne, amma ai kin fini kyau Daniyah"


Murmushi tayi tace "Na fiki kyau? Kya jiki da wani zance yanzun Nan kikace we are identical Kuma kice na fiki Neman zancen kike Liyah"


"Daniyah Kenan shi wannan da kike gani ina matukar son sa dan Allah ki nisance shi " fuska ba Wal Wala take maganar, murmushin gefen baki Aniyah tayi tace "Kar ki d'akin know my limit"
"Yauwa ko da naji" tana Kai Nan ta juya Mata baya tayi kwanciyar ta, Aniyah Kai ta kad'a tana jinjina Hali irin na Yar Uwarta.


Sagheer sai juye juye yake ya kasa samun sukuni tambayar kansa yake "Wai me ke faruwa dani ne da zaran na rufe idona Liyah nake gani kunnuwana sautin muryarta suke jiye min" Karan message ya shigo wayarsa yasa hannu y ma d'auko yana bud'ewa yaga Ra'ees ne ya turo Masa hotuna da Videos Yana dubawa yaga hotunan su ne da Aniyah Murmushi yayi ya Shiga kallon hutunan d'aya bayan d'ayan Yana Murmushi Wanda shinkansa baisan yanayi ba.


Wani message ya sake tura Masa yace "Yane mutumi na? Ga ango ga Amarya"
Dariya yayi amma Kuma ya Masa reply da "baka da hankali" a Haka bacci yayi awun gaba dashi, ko sallar dare da yakeyi yau baiyi ba, bayan ya farka da asuba yaji babu abinda yake son gani sai Mahaifinsa bayan ya idar da sallah yana jero addu'o'in da ya saba yaji wayar sa na ringing Queen Naga Ni a fuskar wayarsa Murmushi yayi ya d'aga da "Amincin Allah ya tabbata a gareki ummana da fatan kin tashi lafiya?"
Shesshekar kukar da yaji take yi ya sa shi saurin mikewa tsaye a razane yace "Umma me ya same ki kike kuka?"
"Abban ka Irfan" ta sake fashewa da kuka, murya na rawa yace "Me...me yaaaa Sami abban nawa?"
"Tun jiya da safe Yana shigowa gida ya yanke jiki ya fad'i ban d'auki abun serious ba Amma gani nayi har sun sa shi a ICU" ta Kuma fashewa da kuka.


Sagheer sai ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yake tunda ta Fara maganar "Umma a wani asibiti kuke?"
"Malam Aminu Kano"
Tsit ya katse wayar da jallabiyar da ke jikinsa ya fita makullin motar sa da wayarsa kawaii ya d'auka ya Fizgi motar sa sai asibiti.


Yana Isa ya samu Umma sai aikin kuka take kwantar da its yayi a kirjin sa ya Shiga rarrashin ta, Shima hawayen ne a idanun sa Umma tace "Irfan akwai abinda yake damin Mahaifin ka, b'acin Rai da damuwane yake sa cikin irin wannan halin" tana maganar tana kuka , murya a shake yace "Umma kiyi hakuri ki daina kuka addu'a zamu Masa Wai Umma anan Kuka kwana?"
"Eh"
"Amma Umma shine ba a Sanar dani ba sai yanzu?"
'dago kanta tayi ta kalle shi tace "Nasan ba zuwa zakayi ba, yanzun ma nayi mamakin ganin ka sabida nasan irin tsanar da kakeyiwa Mahaifin ka"


Murmushin gefen baki yayi yace "Umma ban sane shi ba fushi nake dashi Wanda insha Allah daga yanzu komai ya wuce"
Gyara Zama tayi dakyau Tace "Ka yafe masa? Dagaske kake?"
"Dagaske nake Umma na yafe wa Abba......." kukane yaci karfin sa ya kasa Karasa maganar murmushi Umma tayi kana ganin fuskanta kasan ta ji dadin maganar da yayi, rarrashin sa ta Shiga yi da sa Masa Albarka.


Dake yau Sunday ne shiysa ya samu damar kula da Umma, Liyah Kuma wuni tayi tana Jin haushin Aniyah sai dai tana kokarin b'oye fushin ta.


Sagheer yafi sati baya zuwa school sanadiyar rashin lafiyar Abban sa, Liyah duk tabi ta damu hankalinta ya kasa kwanciyar har sai da ta ji dalilin rashin zuwan sa.


Likita ne ya fito fuskar sa d'auke da murmushi ya nufo inda su Sagheer suke yace "Alhamdulillah Hajiya, Alhaji ya farfad'o"
Sagheer ne yayi saurin fad'in "Alhamdulillah zamu iya Shiga mu ganshi?"
"Eh zaku iya zuwa gobe insha Allah zamu iya sallamar sa don yanzu babu abinda yake damin sa kawaii zamu barshi ne don ganin karfin jikin nasa"
Umma Tace "Alhamdulillah mun gode Dr"
"Bakomai bismillah" Yana nuna musu kofar d'akin da Abba yake, da sauri suka nufi d'akin Sagheer Saida yazo daf da kofan ya tsaya da har zaijuya sai yaji ance "Irfan!!! A hankali ya juya Yana kallon hannun Mahifin sa da ya Mika Masa, jiki ba Karfi yake tafiya kamar Wanda kwai ya fashewa aciki hannun Abban sa ya rike cikin muryar kuka yace "Abba am sorry nasan nine silar kwanciyar ka a asibiti"
Umma tayi saurin d'aga kanta Tace "Ka daina fad'an haka Irfan Mahaifin ka rashin lafiya ne ya same shi ba Kaine sila ba"
Murmushin taikaci yayi yace "Wallahi Umma nine sabida a ranar Abba yazo ya same Ni a makaranta na fad'a Masa maganganu marasa dad'i" ya karashe maganar cikin kuka, Murmushi Abba yayi yace "Ka daina kuka My Son naji sauki ai Burina d'aya shine ka yafe min laifin da na maka Dan All...."
Da sauri ya katse shi yace "Abba na yafe maka duniya da lahira kaima ka yafe min Dan Allah"
Murmushi Abba yayi yace "Na yafe maka Irfan duk da ma baka min komai ba nine na maka laifi Allah ya maka Albarka"
Umma ta da Sagheer suka amsa da Ameen.
Bayan kwana biyu aka sallami Abba, washe gari Sagheer ya Shiga makaranta don kawaii yaga Liyah har department d'insu ya Shiga bayan sun gaisa dasu Fareedah da Rumana yace "Liyah Dan Allah d'an Zo Mana Muje mota ina da magana dake"
Murmushi tayi Tace "To" a tare suka fita suna isa motar da kansa ya bud'e motar ta Shiga, Fareedah da Rumana sai leke suke, Rumana Tace "anzo gun"
Fareedah Tace "Ina Kenan fa?"
Dariya tayi Tace "Inda nake so azo Mana Sagheer ya fad'a a kogin Soyayya"
"Oh na gane"
Sukayi tafi da dariya.


Kallon ta yayi yace "Da fatan kina lafiya"
Murmushi tayi tana Wasa da yatsunta Tace "Lafiya kalau Alhamdulillah"
"Kin San dalili da yasa na Kira ki Nan?"
"A'a sai ka fad'a"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Hafsy qawata
Ummu Abdallah
My Ayusher
My Anisa
Ina Jin dadin comments dinku Allah ya bar Kauna.
Mu hadu a page na gaba
Milhat ce








🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________






"✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_




```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```



*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE```1️⃣8️⃣0️⃣↪️1️⃣9️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
Bayan kwana biyu aka sallami Abba, washe gari Sagheer ya Shiga makaranta don kawaii yaga Liyah har department d'insu ya Shiga bayan sun gaisa dasu Fareedah da Rumana yace "Liyah Dan Allah d'an Zo Mana Muje mota ina da magana dake"
Murmushi tayi Tace "To" a tare suka fita suna isa motar da kansa ya bud'e motar ta Shiga, Fareedah da Rumana sai leke suke, Rumana Tace "anzo gun"
Fareedah Tace "Ina Kenan fa?"
Dariya tayi Tace "Inda nake so azo Mana Sagheer ya fad'a a kogin Soyayya"
"Oh na gane"
Sukayi tafi da dariya.


Kallon ta yayi yace "Da fatan kina lafiya"
Murmushi tayi tana Wasa da yatsunta Tace "Lafiya kalau Alhamdulillah"
"Kin San dalili da yasa na Kira ki Nan?"
"A'a sai ka fad'a"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Wow wow wow,yau da farin ciki nake typing d'in Nan Kun faranta min matuka da comments d'in ku ku cigaba da min comment Ni Kuma ina suburbud'o muku labari.
Swt Ummu Abdallah,Hafsy,My Ayusher,My Anisa, Hidima Allah ya bar Kauna ina Jin dadin comments d'inku.


Amma nace ba ya kuke ganin lamarin Sageer,Aniyah da Liyah Zata kasance? Kar ku manta fa shawarwarin da Aniyah ta bashi shiyasa yaji ta burge shi,ya kuke ganin lamarin zata kasance idan Sageer ya gane cewar Aniyah ce ta bashi Shawara ba Liyah ba?
Ku kasance Dani (Milhaat Yar Terawa)
Muje zuwa guys💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻






.............Wani leather ya Miki Mata yace "gashi ki bud'e" tana karb'a ta duba wata Yar karamar kwali ta gani an mishi design Ruwan toka sannan jikin Yana sheki, Liyah kwalin ne ya burge ta ta tsaya kallo Murmushi yayi yace "Ki bud'e Mana kiga me ke ciki" tana bud'ewa agogo ta gani kalan sa kalan kwalin Amma sai dai shi ya fi samun stones masu shining cikin glass d'in Kuma an rubuta Liyah, Liyah kasa magana tayi sai Murmushi take d'agowa yayi ya kalle ta yace "Ya dai ko dai bai Miki kyau bane ba?"


Murmushi tayi Tace "Yayi kyau Sosai shiyasa na kasa magana,gashi har da suna na a cikin agogon"
Murmushi yayi yace "daga Saudi nasan aka miki, Kuma Kanwata dake Oxford University ce ta zab'a Miki kalan"
"Wow amma ta iya zab'e gaskiya kalan ya burge Ni sosai, nagode Sosai,Amma meyasa ka bani kyautan sa"


Yar karamar dariya yayi yace "Na Mika sakon godiya ne ban san ya za'ayi na gode Miki ba,kin dai daita tsakanin da mahaifina"
Cikin rashin fahimta Tace "Ni kuma da nayi me?"
Sajen fuskar sa ya 'dan shafo sannan yace "Maganganun da kike min a ranar ya sanyaya min zuciya ta tabbas iyaye abun girmamawa ne bai kamata nayi fushi dashi har haka ba, gashi Nan ya kusa rasa ransa a dalili na Amma Alhamdulillah yanzu Allah ya tashi kafad'ar sa"


Murmushi tayi Tace "Ai yiwa Kaine Kuma ai baka da laifi gara da ka nuna Masa laifinsa Kaga gaba bazai sake maka hakan ba"
Wani irin kallo ya mata a zuciyar sa yace "Ikon Allah kamar ba ita ce take min nasiha ranar ba Kuma ji abinda take cewa ikon Allah"
Muryar tane ya dawo dashi daga tunanin da ya lula "wow nagode sosai"
Murmushi yayi yace "bakomai" sannan yace "ko zamuje Shan Ice cream?"
Da sauri Tace "Eh" (Ni ko na ce Liyah ba ko irin jaan ajin Nan Allah shi kyauta).


Jaaan motarsa yayi ya bargun, Wasa Wasa zasu Fara exams hakan yasa suka ajiye lamarin waka a gefe, Aniyah tunda daga wannan ranar basu sake had'u da Sageer ba ita har ta manta dashi sai dai Sageer wasu lokutan idan Liyah tayi wani abun sai yaga kamar ba itace ta bashi shawarwari cikin hikima da nitsuwa,a yaune suka gama jarabawar su, hakan yasa Sageer ta d'an shirya musu karamin lunch suna Ci suna Sha sannan suna Hira kwasam suka ji ya ambaci sunan Liyah "Liyah! Ina ma ace na kasance da Ke a duk bugun Numfashi na, Kaunar ki Ce take Kara tasiri a Ruhina, babban burina Naga bayyanar fitar Murmushi a Kan wannan kyakkyawar fuskar ki ya zamana Kuma nine sanadin hakan"


Liyah suman zaune tayi sai kallon sa kawaii take tunda ya Fara maganar har ya Karasa bata d'aga idonta akansa ba, mamaki ne ya kamata Sosai tare da kullewan kaai, muryar Ra'ees ne ya dawo da ita daga tunanin da tashiga yace "Kunga tashi mu basu wuri yau maganar ta manya ce"


Ba musu suka bi bayanshi, Sageer tashi yayi yazo ya zauna a kujerar dake kusa da ita yace "Liyah Kinyi shiru Baki ce komai ba, ko ba Kya so nane?"
Da sauri ta kad'a Kai had'e da fad'in "Ina son ka Mana" sai kuma taji kunya da sauri tasa kanta a Kan table d'in dake gaban ta Yar karamar dariya yayi sai ya jingina jikinsa akan kujera Yana shafan kirjinsa a zuciyar sa cewa yake "Alhamdulillah na d'auka Zan Sha wahala Ashe abin zai Zo min da sauki" a fiili Kuma yace "Gaskiya Allah Yana Sona,kin San meyasa?"


A hankali ta d'ago kanta Tace "A'a Sai ka fad'a"
Iska ya hura sannan ya gyara Zama yace "Sabida ke d'in kyakkyawa ce,Allah ne yayi halitta, halitarki dabam ce cikin jinsin yan mata. Kina da faren idanu tas mai dauke da yalwatar bakin gashin gira, a kan su. Gaki da dogon hanci kamar ke kika wa kanki, dai dai tuwar labban bakin ki akan dogowar fuskar ki shi ya fito da cikar kyawun ki, ta yadda ko bakiyi kwalliya ba kyawun dirin ki hada da kyawun fuskarki zai iya sa gayu karo a kan titi"


Liyah dariya ce taso ta kufce Mata Amma ta rike ta sai saita kanta sannan Tace "Karo Kuma kana da abinda dariya"
Dariya Shima yayi ya ce "No abar batun Wasa sincerely speaking kina da kyau son kowa kin Wanda bai samu ba nazo da kokon bara ta ina baran Soyayyar ki da fatan dai ban makara ba?"
Murmushi tayi tace "A'a baka makara ba,Ina maraba da Kai"


Zaro Ido yayi yace "Dan Allah dagaske kike?"
"Umhmn dagaske nake ko Kaga alamun Wasa a tattare Dani"
Murmushi yayi yace "A'a naji dad'i Sosai Liyah ba tare da b'ata lokaci ba Zan gabatar Miki da Kai sannan na baki amsar tambayar da kika min kwanaki"
Cikin rashin fahimta Tace "Wace tambaya na maka"
"Har kin manta? To maganar mahaifina"


Sosa keya tayi Tace "Afwan Ina sauraron ka"
Sai yace "Na kasance ni kad'ai a gun mahaifiyata da mahaifina, Mahaifina Yana da tarin dukiya hakan ne yasa baya......"
"Irfan Baku Gama bane? Ana Kiran salla fa" Ra'ees ne ke masa wannan tambayar,hannu ya d'aga Masa alamun Yana zuwa, yace "Kinga yamma tayi ana Kiran maghrib muje nayi sallah na Maida ki gida"


Murmushi tayi tace "Nagode Amma Ina da motata"
"Kassh banji dad'i ba amma ba matsala zamuyi waya in yaso daga baya sai muti schedule inda zamu had'u"
Ta amsa da to, Liyah ce tayi dropping na Fareedah a gida sannan ta Kai Rumana gida tayi Mata alkawarin kawo Mata ziyara na musamman Kan a koma school, Fareedah murna take Sosai hutun Nan zai taimaka Mata wurin sace zuciyar Ra'ees Kan su koma. (Anya Fareedah hanyar da Kika d'auko Mai bullewa ce kuwa?)🤔




Bayan hutu da kwana biyu Ra'ees na kwance Yana chat da Ruman, misalin karfe Sha d'aya na dare yaga amsa sallama da bakuwar number, ba b'ata lokaci ya amsa bayan sun gama gaisa Tace "Nasan baka gane Ni bako?"
Yace "Eh please Waye ne?"
"Yar makarantar kuce"
"Okay Amma Zan iya sanin ko Wace ce?"
"Masoyiyar kace"
Sticker na dariya ya tura mata, Tace "please ba da Wasa nake ba na dad'e ina dakon Soyayyar ka, Ra'ees ka ceci Rayuwa ta ka Soni kamar yanda nake sonka"
Ya bud'e ya karanta sai baiyi Mata reply ba ya cigabada chat da Masoyiyar sa inda sabo ya saba da irin wannan sakon, a ransa yace "Wasu matan Basu da hankali Wallahi da kima da mutuncin ki kizo kina bin na miji Allah ya kyauta"
Ta jera kwanaki uku tana Masa magana baya kulata daga baya sai ya Fara kulata ganin ta nace,chat suke Sosai ba da Wasa ba Nan da nan suka Saba duk da Bai San da Wacce yake chat ba hakan bai Hana su waya ba, yayi da ita ta tura masa picture d'inta Taki a fad'in ta sai sun had'u face to face zai ganta ya Mata alkawarin next week zai Zo har gida ta masa kwatance suka cigaba da hirar su.


'bangaren Liyah da Sageer love d'in su suke Sha, waya,chat harda video call sai dai tun ranar da suka tafi hutu basu had'u ba.


Tana zaune kiransa ya shigo wayar ta, bayan sun gama gaisawa yace "Dan Allah kimin kwatancen gidan ku na kosa Ina matukar kewar ki"
Murmushi tayi Tace "Anjima zan fita sayan ice cream a Havilla sai mu had'u a chan ko?"
Murmushi yayi yace "Yauwa Babyna ko kefe horon yayi yawa"


Aniyah na zaune tana kallo a parlor Yusuf yazo yace "Sister Dan Allah muje sayan ice cream please"
Agogon hannunta ta duba Tace "Kai Yusuf karfe takwas saura fa"
'dan b'ata raai yayi yace "Eh ai dare baiyi ba Kuma ai da mota zamu"
"Toh anji je ka tambayi mummy idan ta yarda sai muje"
Ya amsa da to, ai kuwa yayi Sa'a mummy ta amince "Amma Tace Kar mu dad'e"
Ta amsa da "okay"
Aniyah already dama a shirye take tsaf Riga da wando Pakistan ne a jikinta, Baki ne an Masa flowers da pink d'an kwalin ta ma pink Hala ma takalmin ta, nurse d'inta ta d'auko tace wa Liyah "bari mu dawo"
Ta amsa da "Okay."




Aniyah na fita wayar Liyah ta Fara ringing tana picking Tace "Har ka fito?"
Ya amsa da "Eh"
"Okay gani Nan zuwa"




Aniyah na isa suka saying ice cream, Yusuf yace zaiyi lilo ta rakashi sannan ta dawo ta zauna tana Shan ice cream, kujera taga an janyo anzauna , d'ago kanta zatayi sai taga wannan guy d'in nan ne da suka rera waka tare wato "Sagheer" tana ganinsa sa Tace "Irfan!!" Don da sunan taji Mahifin sa ya Kira shi, kallon tayi cike da mamaki sannan yace "Na'am Ashe kin karaso Kuma baki Kiran ba"
Shiru kawaii tayi Masa, yace "Liyah d'azu jikin Mahaifina ya tashi sai da muka Kai shi asibiti"


A nitse Tace "Innalillahi ya jikin nasa? Da fatan ya samu sauki Sosai?"




Liyah tun da ta fito go-slow ya rike ta a hanya sai tsaki take tana turo Baki.


"Eh ya ji sauki sosai Alhamdulillah"
"Masha Allah, Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"
Ya amsa da "Ameen nagode"
Sai Tace "Kar ka damu ba sai ka gode min ba,Amma naji dad'i da kuka shirya da Mahaifin ka"
Murmushi yayi yace "Nima Haka,Liyah idan

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads