Showing 39001 words to 42000 words out of 66367 words
Chapter 14 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
na tuna abinda Mahaifina yamin sai naji duniyar duk ta fita a kaina"
Murmushi tayi tace "Kayi kokari ka cire abin a Ranka koma mene ka Rika tuna Alhairin da ya maka a Rayuwa, kasa a Ranka shine sanadiyar zuwan ka duniya komai zai Zo da sauki"
Murmushin takaici yayi sannan yace "Ko da kuwa shine sanadin mutuwar mahaifiyata?"
Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi hannun ta rike take da spoon tana Masa kallo irin Wanda take nufin Karin haske murmushin takaici yayi yace "Yess ko da kiwa shi ya you silar mutuwar ta? Don da ace Bai d'auki aikin sa da muhimmanci fiye da mu ba da har yanzu tana Raye"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
PLEASE IDAN KUN KARANTA KU RIKA MIN SHARING TA HAKAN NE LITTAFIN ZAI YAD'U KU KAD'AI NE ZAKU TAIMAKA MIN
Milhaat ce
Yar Terawa
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE``` 1️⃣9️⃣0️⃣↪️2️⃣0️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
Murmushin takaici yayi sannan yace "Ko da kuwa shine sanadin mutuwar mahaifiyata?"
Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi hannun ta rike take da spoon tana Masa kallo irin Wanda take nufin Karin haske murmushin takaici yayi yace "Yess ko da kiwa shi ya you silar mutuwar ta? Don da ace Bai d'auki aikin sa da muhimmanci fiye da mu ba da har yanzu tana Raye"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............"Please Irfan ka ganar da Ni me Kake nufi da hakan? Mahaifin ka ne silar mutuwar mahaifiyar ka? Amma kasan Mutum baya mutuwa sai idan lokacin sa yayi ko? Tunda kaga duk ita muke jira"
"Yes I know Liyah Amma mafi akasarin mutune suna mutuwane da dalili wasu rashin lafiya wasu had'ari wasu Kuma Haka kawaii to Ni Mahaifina shine silar mutuwar ta"
Hannu ta hard'e gu d'aya Tace "Ehenn Ina sauraron ka"
"Alhaji Mubarak Dalha shine Mahaifina ya kasance irin mutanen Nan ne masu son abin duniya, baida wani buri illa yaga ya tara dukiya safe da Rana baida abinyi sai aiki,shine shaye shaye shine biye biye Yan Mata tun ina d'an shekara biyar na gane zaman su ba na dadi bane,ifan akayi jarabawa aka bamu report card da murna make dawowa gida don na nunawa abbana Amma sai ya koreni wasu lokutan harda duka daga Nan karatu ya fita kaina, mahaifiyata ce take kokarin rarrashin a duk sanda babana ya b'ata Mata raai,idan Bata da lafiya bbu Ruwan sa da tambayarta ya jiki iyaka ya ajiye Mata kud'i yayi tafiyar sa, akwai watarana,bazan manta da wannar ranar ba,ranar shi ya kasance mafi munin rana a cikin tarihin Rayuwata"
Hannun yasa ya share hawayen da ya gangaro Masa, sannan ya d'aura da "A lokacin ina d'an shekara Sha biyu, na tashi da masanancin zazzabi tun safe take binsa a kaini asibiti Amma yaki kulata Kuma yaki bada kud'i ta kaini daga baya ya shirya zai fita ta tunkare shi da maganar yace idan ta damu ta jira sai ya dawo da ta nemi tayi Masa gardama a ranar duka ya Mata na fitan hankali abin ba dadin gani yayi tafiyar sa, har karfe Sha d'aya da rabi Bai dawo ba ta Shiga kiransa Yana picking muryar sa buge Ashe Yana club ne suna holewar su"
Hawayen da Ke fuskar sa yaje kokarin gogewa a Karo na biyu Aniyah tayi saurin Mika Masa pieces na hannunta yace thank you sannan yace "Mahaifiyata ranta yayi matukar 'baci ta d'auki makullin mota dake akwai motoci dayawa a gidan sannan ta d'auki ATM d'in sa, ta d'auke Ni ta ajeyi ni bayan motar ta ta'ba jikina Taji zafin jikin nawa ya Kari sai rawar sanyi nake hakan ya yi matukar tada Mata hankali ta Fizge motar muka nufi asibiti a hanya bbu abinda take ambata sai Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un tana cemin Sannu Irfan hannun ta tasa don taji zafin jikin nawa Bata Ankara ba ashe wata babbar mota ta nufo gaban motar mu Kan ta Ce zatayi wani Abu har motar sunci Karo Nan take ta rasa ranta" ya Karasa maganar cikin kuka Aniyah Tace "Tabbas Dole kaji haushin Mahaifin ka kadaina kuka addu'a zaka Mata Allah ya jikanta yasa ta huta,Amma Mahaifin ka da yaji mutuwar ta me yayi?"
"Ya Shiga tashin hankali don he kuka Saida yayi Yana Neman gafararta Wanda a gani na karya yake yi"
"Kar kace Haka na tabbata yayi nadama tunda na gani da idona shi yake baka hakuri, Amma wani abun da ban fahimta ba anan shine ranar yace mahaifiyar ka ta Sanar dashi Kuma kace ta rasu"
"Eh bayan rasuwar mahaifiya ta da shekara d'aya yayi aure ya Auri Salma, Salma mace ce ta gari Mai tsoron Allah ta rike Ni tamkar ita ta haife ni hakan yasa mutane da dama Basu sanin ba itace ta haifeni, Mahaifina ya auro ta da Yar karamar yarinya Wacce ba zata wuce five years ba Ina matukar Kaunar ta duk da ita din ba jina na bace"
"Masha Allah Amma Zan so ganin ta Jin yanda kake sonta Sosai"
Murmushi yayi yace "Zaki ganta soon Maryam, Maryam sarkin rigima ai bata karatu a kasar Nan ma, a Oxford University take sabida Mahaifin ta Mai kud'i ne"
Dafe kanta tayi Tace "Kashh Kaga na manta tare nake da kani na bari na dubo shi, ya kamata ka kira gida kaji ya Mai jiki sannan ka saki Ranka Naga ka damu, duk da hakan ya Zama dole ka d'auki komai a Sannu kaji?"
Murmushi yayi yace "Okay"
A hanyarta tafita Sukayi kicibis da Liyah, Aniyah na ganin ta Tace "Yauwa Alhamdulillah mutumin ki Yana cikin Nan duk ya d'auka nice ki Shiga ki same shi Ni Zan tafi gida"
"Okay Amma me kika Zo yi anan?"
"Wallahi Yusuf ne yace zai Sha ice cream Bari na je na duba shi mu koma gida"
"Okay sai na dawo"
Har Aniyah tayi nisa sai ta dawo da sauri Tace "Liyah d'an tsaya" bayan ta karaso Tace "Yana cikin damuwa Mahifin shi baida lafiya maganar da mukeyi dashi Kenan na fito Yana bukatar ki a yanzu" Nan ta shaida Mata komai dake faruwa gudun Kar a Samo matsala.
To kawaii Tace Mata, tana tafiya Liyah a ranta tace "Yarinyar nan tana nema ta min shisshigi Ni gani nake ma kamar tana sane take bari su had'u da Sageer Amma bakomai I know what to do" sai ta shige.
Da Sallama ta Isa idan yake ya amsa kallon ta ya tsaya yi na d'an wasu lokuta Kan yace "Amma d'azu kamar gyalle pink na gani a Kan ki ko? Yanzu Kuma Naga ya koma jaa"
Yar karamar dariya tayi Tace "No jaa ne maybe baka lura bane ba"
Yace "Okay" Amma fa hankalin sa bai d'auka ba.
Tace Masa "Ya Mai jiki ka Kira gida kuwa?"
Yace "Eh yanzu mukayi waya da umma"
"Okay Allah ya sauwaka"
Ya amsa da "Ameen Ina kanin naki?"
"Yana waje Yana lilo"
"Okay yayi kyau"
Sai yayi shiru, Liyah Tace "Kayi shiru Kar fa ka d'aura damuwa a ranka, dama su iyaye Zama dasu sai hakuri, Amma idan ka tsaya ka d'aura wa kanka damuwa shi kwance Kai ma Hala yazanyi da Raina idan wani abu ya same ka"
Kirkiran Murmushi yayi a ransa Kuma cewa yake "Anya Yarinyar Nan tana da hankali kuwa maganganun ta na d'azu da yanzu ba d'aya bane d'azu ta nuna min mahaifina Yana da muhimmanci a Rayuwata yanzu Kuma ta nuna na min naso kaina fiye da kowa what is wrong with this girl" Yana wannan tunanin Yana kallon ta fuskar ta da walwala ba kamar d'azu da Tausayin sa ya bayyana a fuskar ba, gyaran murya yayi yace "Liyah karfe Tara ta wuce ya kamata ki koma gida"
Zaro Ido tayi Tace "Haba yanzu zuwana fa, Kuma kace na tafi, ko fushi Kayi ne? Wallahi go slow ne ya rage Ni"
Cikin rashin fahimta yace "go-slow? Naga mun Kai almost one hour dake anan Kuma kina maganar go slow?"
Sosa keya tayi ta Fara kame kame Tace "ai duk Kaine kasa na rikeci it has been long fa bamu had'u ba"
Murmushi yayi yace "Kar ki damu zamu had'u Insha Allah har gida Zan Zo"
"To shikenan ka kular min da kanka"
Kad'a Kai yayi alamun okay, zuwa sukayi ya saya Mata ice cream biyu a fad'in sa d'aya nata d'aya na kanin ta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Please comment and share
Milhaat ce
Yar Terawa🥰
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE```2️⃣0️⃣0️⃣↪️2️⃣1️⃣0️⃣
Not edited
```PREVIOUSLY```
Tsosa keya tayi ta Fara kame kame Tace "ai duk Kaine kasa na rikece it has been long fa bamu had'u ba"
Murmushi yayi yace "Kar ki damu zamu had'u Insha Allah har gida Zan Zo"
"To shikenan ka kular min da kanka"
Kad'a Kai yayi alamun okay, zuwa sukayi ya saya Mata ice cream biyu a fad'in sa d'aya nata d'aya na kanin ta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
..........."Hello!! Gani a kofar gidan ku"
A razane ta tashi ta zauna murya na rawa Tace "Wayyo Dan Allah dagaske kake?"
Yar karamar dariya yayi yace "Eh, dagaske nake"
"Okay gani Nan zuwa"
Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta fito, tun daga nesa yake kallon ta mamaki ne ya Kama shi hakan yasa ya bud'e motar ya fito had'e da cire eye glass d'in sa,da Sallama ta karaso inda yake Ra'ees kasa amsa sallamar yayi cikin inda inda yace "Fareedah!!! Dama kece?" Yana nuna ta da eye glass d'in dake hannun sa.
Murmushi tayi Tace "Eh nice kayi mamaki ko?"
Baice Mata komai ba, Murmushi tayi Tace "Kar kaji mamakin hakan so ne sanadin hakan"
Baki a bud'e yace "A tunani na ke kawar Rumana ce ko? Ko dai Baki San Soyayyar dake tsakani na da ita bane?"
"Na sani Mana Amma ai hakan Bai sa na daina sonka ba, kuma ai Kai na miji ne kana da ikon auren Mata hud'u"
Tsaki ya ja yace "Amma ban tab'a sanin ke shasha bace maras hankali so kike naci amanar Ruman? Wallahi Kinyi kad'an idan mafarki kike tun wuri ki farka"
Murmushin takaici tayi tace "Aure ne cin Amana? Ra'ees Raya Sunnah ne fa, shine harda zagi Ra'ees? Idan baka Sona ko ban maka bane sai ka Sanar dani ba ka nemi kaci mutunci na ba, na bar ka lafiya" ta juya zata tafi yace "Fareedah dakata" tsayawa tayi ba tare da ta kalle shi ba, yace "Am sorry please ba halina bane wulakanta Mutum musamman ma ace mace, na shiga rud'ani Sosai ganin kece Wacce kike bibiyata,abinda Baki sani ba shine Abokina Mubarak Yana mutuwar sonki, baida wani zance sai naki, dalilin da yasa ya kasa tinkarar ki gani yake babu yanda za'a ce kyakkyawa kamar ke baki da Masoyiya, Fareedah kiyi hakuri ki karb'i Soyayyar aboki na sabida Yana kaunar ki Sosai Ni kuma ki d'auke Ni a matsayin yayan ki, ki core Soyayya ta a zuciyar ki sabida Kinga Ni Ruman na keso har an Mana baiko so Dan Allah kiyi hakuri."
Shiru tayi na dan wasu lokuta sannan Tace "Toh Amma wane ne mubarak?"
Murmushi yayi sannan yace "Yana cikin abokan mu Amma nasan ba lallai ne ki gane shi ba, Kuma Wallahi da aure yake son ki Fareedah"
"Toh shikenan zanyi Shawara akai"
"A'a Kar muyi haka dake wani Shawara sai kace yarinya na fad'a Miki ki d'auke Ni a matsayin yayan ki, ki bani izini har Nan Zan kawo Miki shi idan bai Miki ba sai na kyale ki"
Murmushi tayi tace "toh shikenan sai na ganku"
Dariya yayi yace "Yauwa ko kefe Yar Kanwata,sannan maganar Nan ina so ki bari a tsakanin mu daga Ni sai ke, ko kin fad'awa Liyah kina Sona ne?"
Tsotsa keya tayi Tace "A'a ban fad'a Mata"
Yar karamar dariya yayi yace "Anya?"
Dariya ita ma tayi tace "dagaske nake"
Yace "good so let's keep it a secret Kar su Raina min kanwa ko?"
Kai kawai ta kad'a Masa.
Yace Mata ban kwana ya Shiga motar sa ya tafi.
Washe gari ya kawo Mata Mubarak sai Taji ya kwanta Mata a rai, ya tabbatar Mata da shi baya so a b'ata lokaci don haka ta Sanar a gida shi zai fito idan yaso bayan ya kammala karatun sa sai a yi auren ai kuwa ta amince ta Sanarwa Mahaifin ta bai fi sati ba aka nema Masa auren Fareedah Kuma akayi Sa'a an bashi, Ruman da Liyah Jin labarin Nan sunyi matukar farin ciki da musu fatan Alhairi.
*Wannan Kenan*
"Daniyah Wai meyasa nake ji a jikina kamar kina sane kike bari Ku had'u da Sageer?"
Aniyah na gaban mirror tana goge Kan ta da towel da alama daga wanka ta fito, cikin rashin tace "Waye Kuma Sageer?"
"Ke Ni zaki Raina wa wayo kice Baki San Sageer ba?"
"Wallahi ban San shi ba Waye shi? Kuma a ina yake?"
Yarfa hannu Liyah ta Shiga yi Tace "Daniyah me kike son Zama ne? Yaushe Kika Zama makaryaciya d'azu ke da Kan ki Kika ce min Kuna tare a Havilla Amma yanzu kice Baki San shi ba"
Dariya Aniyah tayi tace "Oh oh oh dama sunan sa Sageer ne? Ni wallahi da Irfan na San shi" gyara tsayuwar ta tayi Tace "Ki kwantar da hankalin ki Yar Uwata bazan Miki snatching ba, ko kad'an bana son sa Kuma bazan ta'ba son sa ba Kuma lokaci yayi da ya kamata ki nuna Masa cewar mu Twins ne Kinga daga Nan magana ya Kare"
"Kina nufin na had'a ki dashi never, salon yace Yana son ki?"
"Haba Liyah meyasa Baki da yarda ne me zaisa naso saurayin ki by the way kece kike da lokacin Samari Ni wallahi basu gabana"
Murmushin gefen baki tayi ta matso kusa da Aniyah Tace "Kin dad'e kina min shisshigi a Rayuwa ta Daniya kowa Daniya Daniyah Daniyah Kama daga Kan Granny har izuwa Kan Huzaifa kowa ke yake so ni ba a damu Dani ba tun muna yara"
"Subhannallah ya zakice haka sune fa suka haife mu Taya za'a yi su so d'aya su bar d'aya Dan Allah ki daina irin wannan tunanin"
"Zan daina idan Kika fita daga harkar Sageer in ba haka ba Kar ki sake d'aukana a matsayin Yar uwarki"
Aniyah kallonta take cike da mamaki Tace "Yanzu Liyah Zaki iya yanke alakar dake tsakani na dake sabida wani d'a namiji Kar ki manta ni yar uwar kice fa your own flesh and blood Wanda idan kina kuka ko ina so ko bana so Dole nayi haka ma idan kina dariya haba Liyah" ta na maganar ne cikin sanyin murya da langwabar da Kai.
"Whatever Ni dai na fad'a Miki stay away from my man or else you'll see the other side of me" tana kai Nan ta fice daga d'akin Aniyah babu irin tunanin da batayi ba, a fili Tace "Dole ne ma yasan mu biyu ne, in ba haka ba ya Rika mistaken d'in mu Kenan ya Allah ka sake had'a Ni da Irfan don na warware wannan matsalar" ta cigaba da shafa man ta.
Ha aka koma hutu basu had'u da Irfan ba,ita Kan har ta manta ma, Liyah da Sageer Shan Soyayyar su suke babu abinda yasha musu Kai, sai dai wasu lukutan Yana ji a jikin sa ba itace Yariinyar da ya fad'a a Soyayya da ita bace.
Mubarak da Fareedah Soyayya sai dai ace Masha Allah haka ma Ra'ees da Ruman.
Aunty Khadee suna aji uku Soyayyar Mr M.I kullum karuwa take a zuciyar ta ta rasa yanda zatayi sai addu'a kawai take Allah ya kawo Mata mafita da fatan Allah ya d'aura Masa Soyayyar ko da d'an kad'an ne.
M.I na gani zaune da Mr Sadeeq duk su biyun malamai ne "Abokina Wallahi na kamu da soyyayar Yarinyar Nan na Rasa yanda zanyi ganin ta kad'ai shi yake samin Nishad'i Amma na kasa tinkarar ta" M.I ne ke wannan maganar.
Gyara Zama Mr Sadeeq yayi yace "Wai wace yarinya ce wannan da ta d'auke maka hankali kusan kullun sai kamin zancen ta?"
Iska ya hura yace "Khadeeja sunan ta a department d'ina take"
"Wow a wani aji take?"
"300level take"
"Good! To fad'a min me kake jira har yanzu ka sani fa tana gamawa za a Mata miji, ko Kuma an Riga da an Mata"
"Kaai dan Allah Kar kace Haka an Mata miji Kuma ya zanyi da Raina?"
"Oho ka mutu ma Mana ina Ruwana Ni"
"Haba Abokina na mutu Kuma?"
"Eh Mana ka duba kaga duk abokanan mu munyi aure duk babu Wanda yake da d'a kasa da uku Amma kana Nan auren ma ka kasa yi,Amma ko ba komai naji dad'i yanzu nasan Kai na miji ne tunda kace kana son wata ai na d'auka baka da lafiya ne" ya Kara maganar cikin zolaya.
"Kaga malama lafiya ta Lau Wallahi kawai dai ban samu Wacce tamin bane Amma yanzu na samu, so Dan Allah ya kake ganin za'a yi?"
"Gidan su zamu nema"
"Allah ko abokina? Amma Taya ya ya zamu nema?"?
"Kai dad'i na da Kai kwakwalwar ka bata jaa, bata da qawa ne? Ko Kuma idan an tashi mu bi bayanta"
"Ehh akwai wata a department d'in sunan ta Maryam duk ina bibiyar su"
"Yauwa nuna min ita kawai zakayi an wuce gun"
"To anyi Angama"
Ai kuwa ana tashi ya nuna Masa Maryam baiyi kasa a gwiwa ba ya Sanar da ita tayi murna Sosai Jin Allah ya karb'i addu'ar kawarta Amma Taki Sanar da ita kwatancen gidan ta Masa,ai kuwa washe gari da Isha, akayi Sallama da Daddy sunyi sa'a Yana gari suka Sanar dashi dalilin zuwan nasu Yayi matukar murna Sosai sannan ya basu izinin Neman ta idan ta amince zai aura Mata shi.
( Su Aunty Khadee buri zai cika)🤣
*OXFORD UNIVERSITY*
"Maryam Kinga ikon Allah Wasa wasa har mun kusa gamawa"
Murmushi tayi Tace "Eh Wallahi Rahina abun ba wuya dai a gun Allah"
Sabir yace "hakane Allah yasa mu gama