Header Ads
Showing 24001 words to 27000 words out of 66367 words

Chapter 9 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

suka rubuta jamb, bayan awanni ashirin da hud'u results zai fito duk hankalin su a tashe yake sai Addu'o'i suke hade da nafiloli, washe Gari,kwasam Liyah Taji Karar SMS ya shigo wayar ta zaro Ido sukayi suna kallon juna.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
MILHAT CE
YAR TERAWA
PLEASE COMMENT AND SHARE


🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_




```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```



*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE``` 1️⃣1️⃣0️⃣↪️1️⃣2️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
A yaune suka rubuta jamb, bayan awanni ashirin da hud'u results zai fito duk hankalin su a tashe yake sai Addu'o'i suke had'e da nafiloli kwasam Liyah Taji Karar SMS ya shigo wayar ta zaro ido sukayi suna kallon juna.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............ Daniyah tace "Ki d'auki wayar Mana bakiji Karan text ya shigo bane?"
"Wallahi Daniyah tsoro nake ji Kar ban ci ba"
"Kinga d'auki ki bud'e da addu'a idan kinci ko kin fad'i babu abun da zai....." Ita ma taji Karar ya shigo wayar ta, Liyah Tace "Yauwa Fara bud'e naki mugani"


Sosa keya tayi tace "To..ai..ai naki ya fara shigowa ki Fara bud'e wa"
Dariya Liyah tayi tace "Kya ji ki da wayo Ni Zaki yi wa wayo?"
"A'a Wallahi ba wayo Zan Miki ba ai kece babba dani"
"Malama da mintuna biyar fa kachal na girme ki"
"Ko da ace minti d'aya kin girmenin ai"


Murmushi Liyah tayi Tace "Toh Zan irga uku sai mu bud'e a tare kin yarda?"
Da sauri Daniyah tace "Na yarda"
Liyah tace "One Two Three" sai suka bud'e a tare kallon juna suka yi dukkanin su suka Fara tsalle suna ihu, suka d'ale Kan gado suna ihu, mummy na kitchen Granny kuma na kallo a Parlor Jin ihun su yasa ta mike a tsorace, Mummy Kuma ta fito da sauri tana ambatan "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Mama me yake faruwa ne? Kinji ihuun da Naji kuwa? Kuma har yanzu ina ji"
"Kinga Ni kaina ban sani ba Amma kamar ihun daga d'akin su Liyah ne"


Granny da Mommy sai kallon sama suke a hankali suka Fara taka steps d'in har suka Isa kofan su Liyah Granny ta nunawa Mummy da Akan ta bud'e ta Shiga, Mummy Kau da kanta tayi, Granny tayi ta maza ta tura kofan a hankali tana leke sai ganin su tayi suna ihu suna rawa suna tsalle da karfinta ta Shiga d'akin Kare musu kallo tayi da kyau a tsawace tace "Kaaai me Haka?" Chaak suka tsaya basu Ce Mata komai ba ta kuma cewa "Wannan wani irin rashin hankali ne Kun Zo kunayiwa mutane ihu a cikin gida sai kace wasu masu aljanu?"


Mummy jin Granny na masifa sai ta shigo a hankali ta hango su a tsaye akan gado suna Wasa da hannayen su.
Mummy tace "Kai me kuke yi Haka?"


Liyah ta sauko da gudu har sai da Granny da Mummy suka jaa da baya, rike hannayen mummy tayi Fara tsalle tana dariya sai juya mummy take, Daniyah ma hakan tayi wa Granny, Granny Tace "Wayyo na shiga uku, hajijiya ki Bari" Amma sai Kara yi da Karfi suke sai da sukayi Mai isan su kan suka sake su, a tare sukace "Albishirin ku"


Ina ai mummy da Granny kasa magana sukayi suna kallon wuri bibbiyu a daddafe suka Nemi gurin Zama sun d'auki kusan mintuna biyar Kan Granny Tace "Kunga Jairan Yara so kuke ku kashe Ni ko? Bayan tada Mana hankula da kukayi kuma kuka Zo Kuna waina mu, Wallahi jiri nake ji Ina kallon Abubuwa bibbiyu"


Mummy Kam har yanzu kasa d'ago kanta tayi, Liyah ta zo ta durkusa a gaban su, Tace "kuyi hakuri Granny Wallahi farin ciki ne yasa mu kayi hakan"
Daniyah Tace "Please Kuyi hakuri murna muke sosai mun ga jamb results d'in mu"


Mummy d'ago kanta tayi da sauri Tace "Haba dai nawa kuka Samu?"
Nan suka Shiga Sosa keya Liyah tace "Daniyah nawa Kika samu Ne?"
Daniyah Tace "Ke d'in nawa Kika samu?"
Granny Tace "Au dama duk ihun Nan baku San results d'in junan ku ba? Yaran Nan akwai ku da shiririta"
Mummy Tace "Kaai baza ku kashe Mutum ba Kuna girma Kuna sake Shiga jeji mtsssw." Ta Tashi da niyar fita Daniyah Tace "Mummy yi hakuri Wallahi ba mu yi hakan don b'ata muku ba, naga scores d'ina 259 Kuma dama medicine 250 suke bukata"
Liyah tace "Ikon Allah Kinga Ni ma nawa hakan ne 259, kin gani?" Tana nunawa Daniyah wayar ta, Granny Tace "Masha Allah, Alhamdulillah gaskiya naji dad'i Wallahi Allah ya taimake ku"
Duk suka amsa da "Ameen."


Mummy Tace "Allah ubangiji ya taimake ku nasan Daddyn ku yau ba karamin farin ciki zaiyi ba idan yaji kunci jamb don Shima kamar ku Ina ga kamar ma yafi ku son yaga Kun ci jarabawar Nan"
Daniyah Tace "Mummy ke dai bari ai duk addu'ar ku ce tasa muka ci Kuma kin San dama jamb Sa'a Ce ba ilimi ba"
Liyah tace "Hakane Kam ba ilimin ka bane Bari ma na Kira Fareedah Naji nawa ta samu don itama ta fad'a min law d'in ta cika" ta Shiga dialing layin Fareedah duka biyu ta d'auka da Sallama a bakin ta, Tace "Qawata ya akayi ne?"
Liyah tace "Kalau fa Alhamdulillah sun turo mana scores d'in mu kefa?"
"Ai kuwa dama Nima yanzu nake so na Kira ki sun turo min tun jiya dake kin San na Riga ku yi"
"Eh haka nawa kika samu? Hope akwai joy"


Dariya Fareedah tayi tace "Eh Wallahi Alhamdulillah Ina da 250 dai-dai"
"Masha Allah na tayaki murna sosai"
"Nagode, ke nawa Kika samu?"
"Dani da Daliyah muna da 259"
Zaro Ido Fareedah tayi tace "Haba dai? Kina nufin scores d'in ku d'aya?"
"Eh d'aya ne muma abun ya bamu mamaki"
"Masha Allah congratulations to all of us"
Dariya Liyah tayi tace"Yess oo congratulations to all of us, sai anjima"
"Ok bye"
A tare suka kashe wayan.


Mummy Tace "Da alama kawar taki ita ma ta wuce ko?"
Murmushi tayi tace "Eh mummy ta wuce ba karamin dad'i Naji ba wallahi"
Granny tace "Toh dai Ina muku fatan Alhairi"
A tare sukace "mun gode."


Mummy dafe kanta tayi tace "Laah kunga na manta Ina girki"
Da sauri ta fita Suma suka rufa Mata baya, suna Shiga kitchen d'in duk hayaki, har Saida suka toshe hancin su, Daniyah Tace Kai "Mummy mene ne haka bayan ya konen ma kamar yaji?"


Mummy na tari Tace "Pepper chicken ne fa, kin San yau Daddyn ku zai dawo Kuma Kun San yanda yake son pepper chicken"
Granny Tace "Ai duk laifin takadiran yaran Nan ne kuka tada wa mutane hankali, Kinga Asma'u Zo mu fita ki bar su da girkin tunda dai su suka sa Kika Kona"
Murmushi Mama tayi tace "Aaaah! Mama idan na fita sukayi kwab'a kin San halin Daddyn su"
Tsaki Mama ta jaaa tace "Wai ke baza ki daina tsoron sa bane?"
"Mama ba tsoro bane ba gudun b'acin Rai ne, idan nashi ya b'aci to sai na kowa ya b'aci"
"Mtsww Ni wallahi lamarin Yan gidan Nan ya Fara Isa na, idan yaran Nan basu iya girki ba ke Zaki bi su gida Jen su ki musu girki?"


"A'a haba Mama bazaiyu ba naje gidan su Kuma, tunda kince a bar su suyi sai a bar su d'in, Liyah idan kuna bukatar sanin wani abu ina parlor ku min magana kunji?"
A tare suka amsa da "Toh Mummy."
Sai suka fita, Liyah Tace "Daniyah kin San yanda ake yi ne?"
Dariya Daniyah tayi Tace "Au Ni na d'auka kin iya ai tunda Naga baki yi magana ba"
Sosa keya tayi tace "Chakwakiya yau ake yinta,Ni wallahi wani lokacin Granny b'ata min Rai take, Wai a bar mu muyi girki mtsww"


Dariya tayi tace "Ke dallah me abun b'ata raaai kin manta muna ganin yanda take yi sai muyi hakan,bari na d'auko kazan a Fridge na gyara ke Kuma ki daga kayan Miya"
"okay to."


Daniyah ta d'auko Kazar ta Fara yankawa Liyah Kuma ta Fara daka kayan miyan, Su citta,albasa, garlic da dai sauran su, bayan sun gama suka d'aura Akan wuta bai d'au lokaci ba ya nuna dake kazar Agric ne Kun san baida wani Karfi, Suka sa kayan had'in Nan da Nan kitchen d'in ya d'au kamshi suna gamawa suka kashe gas cooker sannan suka fito, mummy na ganin su Tace "Yaya akwai matsala ne?"
A tare sukace "Mummy mun gama"
"Har Kun gama? to Muje na gani"
Ta yi gaba suka bi bayanta, tana bud'e tukunyar Tace "Allah yasa yayi dad'i kamar yanda yayi kyau a Ido"
Basu ce Mata komai ba, ta d'auki d'aya tasa a plate, ta d'an gusura kad'an Tace "Ashe dai Twins d'ina good cooks ne yayi dad'i Kun d'ana kuwa?
Kai suka d'aga Mata alamun "A'a" Tace "Ya kamata ku d'ana, Miko min food flask d'in Daddyn Ku"
Liyah ta miko Mata, mummy ta zuba Masa sannan ta d'auki plate ta sa musu sannan ta d'auki wani tasa wa Mama, duk suka nufi parlor, Mummy ta mikawa Mama nata, sannan ta zauna,Mama Tace "Yauwa ko kufa bari dai naji taste d'in abincin" tana sawa a baki, batace komai ba sai ta hau ci kawai, Liyah ganin Mama ta dage ta mike ta d'auko Mata ruwa a fridge ta Mika Mata, Bata Ce komai ba ta kafa Kai Tasha, sai da ta cinye tas Kan tace "baiyi dad'i ba ko kad'an" tana tab'e Baki.


Liyah tace "Ohh Allah ai shiyasa Naga kin cinye har da tauna kasusuwan"
"Ke yunwa ce tasa na ci ba komai ba"
Daniyah Tace "Hakane Kam shiyasa Naga kin ajiye spoon d'in"
Dariya Mummy tayi Tace "Dan Allah ya Isa haka Kun Sa min Uwa a gaba"
Liyah tace "Mummy ba ki ga cin mutuncin da take mana ba?"


"Liyah ke ko? Kin San Allah ki kiyaye ni" Granny Ce ke wannan maganar
Liyah Tace "Kan ki ake ji malama girki ya Miki dad'i ki fad'a kawaii"
"Anki a fad'a d'in"
Nan suka Fara Hira suna cikin hakan sai Daddy ya shigo da Sallama a bakin sa, da gudu sukaje suka rungume shi sannan Daniyah ta karb'i jakan hannun sa, Daddy Dariya yayi yace "Tooh bana ma a tab'a nasan dai wannan farin cikin ba na gani na bane ba, me ya faru?" Yana kallon su d'aya bayan d'aya, Mummy tace "Toh ku barshi ya shigo Mana Kun tsare shi a hanya sai kace ba gidan zai shigo ba" riko hannayen su yayi suna tafiya har suka iso sitting room, bayan sun gaisa ya gaida Mama ta amsa ba yabo ba fallasa, yace "Ina sauraron ku mene ne yasa Twins d'ina farin ciki haka?"
Nan Liyah ta Sanar dashi labari Mai dad'i tunda ta Fara maganar Daddy yake Murmushi, yace "Kaai Amma Naji dad'i Allah ya muku Albarka sannan ya Albarka ci karatun ku"
Duk suka amsa da "Ameen"


Mummy Tace "Yallab'ai ya kamata Muje ka watsa ruwa ka samu kaci abinci nasan ka d'ebo gajiya"
Yace "Gaskiya dai Kam Ina bukatar wanka ga yunwar da nake ji" Yana maganar had'e da mikewa ya hau sama mummy Kuma ta karb'i jakar sanan ta bi bayan sa.


Yana Gama wankan ya sauko yaci abinci yayi ta yabon girkin sai da ya gama mummy ta Sanar dashi Twins ne sukayi girkin baiyi mamaki ba a fad'in sa training d'in ta ne.
Khadija na dawo wa suka Sanar da ita tayi murna sosai, zata daina zuwa school ita kad'ai"
Haka ma Yusuf da Huzaifa sunyi murna sosai.


Alhamdulillah Liyah da Daniyah sun samu admission Suma a B.U.K, sannan abinda sukayi applying, Liyah a faculty of Law Daniyah Kuma medicine, Fareedah itama law d'in aka bata Nan da Nan suka Fara attending lectures, komai yana tafiya dai-dai, , Liyah ta kasa sake jikinta da kowa, zaune take a LT tana duba handout d'inta wata Yar budurwa na gani Fara ce Mai dogon hanci Amma Kuma gajera Ce Hijab ne a jikinta baka dogo har kasa, da sallama a bakin ta ta Karasa inda Liyah take , a hankali Liyah ta d'ago kanta had'e da amsa sallamar don ganin Wace Ce take sallamar, hannu ta mikawa Liyah Tace suna na "Ummu Ruman Amma ana kirana da Rumana Nice to meet you" Murmushi Liyah tayi ta Mika Mata hannu Tace "Barka Ruman suna na Daliyah Amma ana kirana da Liyah Nice to meet you too."
Ruman Tace "A wani department kike please?"
"Law" Tace Mata a takaice
"Wow Amma Naji dad'i yau na Fara shigowa Kuma Nima a law d'in nake ina Neman kawa please can we be friends?"


Murmushi tayi tace "Ba matsala Nima bakuwa ce ai" Tace "Nagode" Nan suka Fara Hira suna tambayar juna address da dai sauran su, dake Ruman da Liyah duk masu surutu ne Nan da Nan suka Saba.


Wasu samari na hango sunyi Shiga irin ta manyan Yara dukkanin su kananun kayane a jikin su, sai Mutum d'aya wanda shi Kaftan ya saka, milk color an mishi zubi da zare brown Haka ma hular Sa da talkalmin sa Brown ne, Liyah na ganin sa ta kasa motsi hankali ta duk yayi kansa, Ruman juyowa cikin sauri don ganin abin Liyah ke kallo , Murmushi tayi Tace "Sagheer sunan sa, d'an gidan Alhaji Mubarak Dalha"


Sosa keya tayi tace "Ruman Kema dai da Sa Ido kike ya akayi Kika gane shi nake kallo?"
Murmushi tayi Tace "Haka yake Yana da farin jinin Emmata, Emmata rushing din sa suke Amma tunda nake dashi ban tab'a ji yana da budurwa ba shi Sam baya Soyayya a fad'in sa bai yarda da Soyayya ba, Wasu har kiransa suke da *Sagheer no* *love* "


"Amma gayen ya burge Ni tunda nake ban tab'a ganin Wanda ya min irinsa ba, ki duba kiga gashin kan sa baki a kwance gashi ba fari bane Kuma ba Baki bane, ga d'an karamin lips d'insa da Dara daran idanu Kaaii Ruman sauran abubuwan baza su fad'u ba"


Dariya Ruman tayi Tace "kina da abin dariya hakane gaskiya Sagheer Mai kyau ne, Kinga wanchan na gefen hannun daman sa?" Tana nuna Mata wani d'an saurayi fari ne tass Kuma dogo ne, Mai dogon hanci Yana da kyau sosai sai dai duk kyaun sa s be kamo kafan Sagheer ba. Liyah tace "Eh na ganshi"
"Yauwa sunan sa Ra'ees saurayi na ne, Kuma abokin Sagheer ne ko ince aminin sa, shiyasa nasan shi ma idan kina so sai na gabatar Miki dasu ki Zama abokai"
"Gaskiya Zan so hakan please ki had'a Ni dasu"
Murmushi Ruman tayi tace "Kinga ma Nan suke zuwa"
Liyah manta kanta tayi da kallon sa, har sai da ya buga desk d'in yace "Malama ya dai? Bashi ko Tara?"


Murmushi tayi Tace "ko d'aya"
Tab'e baki yayi yace "Rumana ya kike? congratulations Naji Kema kin samu admission a makarantar mu"
Murmushi tayi tace "Eh wallahi nagode sosai"
Ra'ees yace "Babyna har kin fito?"
Cikin muryar shagwab'a tace "Ehh"
Dariya ta bashi yace "Ke ko Allah ya shirya min ke, Naga har kinyi 'kawa"
"Eh sunan ta Liyah"
Duk kansu suka kalle ta Ra'ees yace "Hyy kawar mu" Yana d'aga Mata hannu, ita ma hannu ta d'aga Masa tace "Hyy" duk suka gaisa Amma banda Sagheer dake ta chatting abinsa, sai yace "Guys ya kamata mu tafi fa Kun San Malamin Nan ba mutunci ne dashi ba,Rumana dama zuwa mukayi mu gaida ke"
"Allah Sarki nagode sosai Allah ya bar zumunci"
Ya amsa da "Ameen"
Ba musu suka nufi hanyar fita, Ra'ees yace "Babyna idan kin fito call me"
Ta amsa da "Okay take care"
Yace "Bye, kawar mu bye"
Suka amsa da "bye."
Liyah tace "Amma guy d'in ki Yana da saukin Kai da son Wasa"
"Eh shiyasa nake mutuwa akansa, shi physics department yake, Sagheer Kuma a law yake dukkanin su a three hundred level suke, Kuma Sagheer da Ra'ees mawakane"
"Wow kice abun nayi ne"
Kan Ruman tace wani abu sai lecturer ta shigo hakan yasa suka dakatar da hirar tasu.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
MILHAT CE
YAR TERAWA
PLEASE COMMENT AND SHARE




🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_




```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```



*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE``` 1️⃣3️⃣0️⃣↪️1️⃣4️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
"Liyah har kin tsorata Ni,wane irin matsala?" "Ra'ees fa saurayin Rumana ne, in takaice Miki ma an musu baiko Yana kammala aji Hud'u za'a d'aura musu aure"
D'an Jim Fareedah tayi sannan tace "Naji ba dad'i Amma ai wannan ba matsala bace ba, tunda Allah ne yace suyi Hud'u, uku ko biyu, in dai zai amince idan ya aure ta ya aureni daga baya"
Muryar Rumana sukaji tace "Auren Waye? Wa zai aure ki" had'e da Zama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............ Murmushi Liyah tayi tace "bar Fareedah da shirme wani Tsohon saurin ta ne sun rabu da dad'e wa babu irin wulakancin da bata Masa, yanzu Kuma tazo take fad'a min shi take so Kuma already an Masa baiko da wata shine fa Wai ta yardan in ya Auri wanchan sai ya aure ta daga baya"
Dariya Ruman tayi tace "Ai shiyasa a rayuwa Kar ka wulakanta Mutum, gara ku rabu lafiya, Amma na tambaye ki mana?"
Tana kallon Fareedah, Fareedah Tace "Ina sauraron ki"
Gyara Zama Rumana tayi tace "shi saurayin naki me yasa Kika ki shi daga farko? Sannan me yasa kike son sa yanzu?"


Fareedah shiru tayi don ita Sam ba ta zaci irin tambayar da Rumana zata Mata ba Kenan,inda inda ta Shiga yi Mata daga karshe tayi yake tace "Ruman it doesn't matter, all I know shine Ina son sa, sannan bana so na tuna baya idan na tuna na Kan tsinci kaina a cikin damuwa da tashin hankali,a yanzu abinda nake bukata daga gun ku shine addu'a da shawarawari tunda yanzu mun Zama friends ko?"
Yar karamar Murmushi Rumana tayi sannan tace "Shi yafi komai sauki, idan Alhairi ce Allah ya tabbatar in Kuma akasin Haka ne Allah ya musanya Miki da mafidiciyar Alhairi"
Ta amsa da "Ameen Amma Ni gaskiya Alhairin shine ya aure Ni don a gaskiya nayi gamo da katar idan fa bai aure Ni ba Zan iya samun matsala ba"


"Ko Kuma kin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads