Showing 9001 words to 12000 words out of 66367 words
Chapter 4 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
Bayan Kun San abin da kuke aikatawa babban lafine a garin nan, Ngozi da ekenna, Hmm Rest in peace" tana wani irin dariya take tana wurga musu harara.
Ekenna yace "Please Nkasi ki rufa Mana asiri Kar ki fad'awa Sarki kin San kashe mu zai sa ayi"
Ngozi Tace "please Nkasi ki dubi girman abun bauta karki fad'awa kowa, Ke qawata ce fa"
"To sai me in ni kawar ki Ce?nice nace Miki ki Zo Nan ki sab'a doka? Kin bari Yana tab'a ki harda Shan baki ko? In ba kazanta ba ma mtwwws, Toh Ku d'aura daga inda kuka tsaya kuyi na karshe don na tabbata yau baza ku kwana a duniya ba sai dai a lahira,Kinga tafiyata" tafiya tayi ta bar su suna Mata magiya Amma Taki sararon su, Kai tsaye ta nufi cikin fada.
Wani bakin mutumi na gani zaune yake a kan kujera da alama shine sarkin, bakine ga tumbi kamar mace Mai cikin wata tara, fuskar sa d'auke yake da gemu ba kyaun gani,fuskar sa tamuke kana ganin sa Kasan Mara Imani ne baida tausayi zaiyi mugunta.
Nkasi na Shiga ta gaida shi sannan ta Sanar Masa Nan take ta ba da izinin a kawo Masa Ekenna da Ngozi, kuka suke sosai suna rokon sa ganin Basu da niyar yin shiru ya daka musu tsawa Wanda yasa ba shiri sukayi shiru.
Yace "Wato Kune marasa kunya Kuna sane da doka na amma kuka banzartar da abin,karshen rainin wayon ma acikin fada ta, Kaii Ina kuke?" Yana maganar Rai a b'ace.
Wasu maza na gani guda biyu suka shigo dogi ne sosai karfafa hannun su Kuma rike yake da adda, yace "Ku tafi dasu ku Tara mutanen gari a jefe su a bayan gari har sai sun mutu, Kuma a bar gawan a wurin kamar yanda akeyi wa sauran"
Zuwa akayi aka Tara mutanen gari aka d'aure Ngozi da Ekenna Yan uwan su da abokanan arziki suna Ji suna gani aka jefe su har suka mutu wasu kuka suke wasu Kuma cewa suke Allah ya Kara, da na bincika na gano ashe masu kukan Yan uwan sune bayan an tabbatar sun mutu duk suka watse suka bar wurin,gawar Kuma na yashe a wurin farin rigar duk ya Koma jaa sabida jinin da suka zubar.
Kad'an daga cikin abinda ke faruwa a fada Kenan.
Bayan sati biyu, Twins sun Saba da Emmatan gidan sosai harda matan gidan don kusan komai tare suke yi, akwai wata Mata a gidan da suke Kiran ta da grace tun lokacin da su Daliyah Suka shigo garin Jinin su ya had'u da Daliyah hakan yasa wasu lokutan take kwana a d'akin Grace idan mijinta baya gari,fitsari Daliyah keji sosai ta kasa jurewa, da sauri ta Tashi ta Shiga ban d'aki bayan ta Gama ta dawo d'akin Grace da niyar kwanciya ga mamakin ta sai taga mutane biyu Akan gado gashi dai tana ganin Grace na bacci Amma Bata gane waye D'ayan ba, Kuma mijin bai dawo ba a ranta Tace "To Ina d'an nata yake?"
Tana cikin Wannan tunanin ne taga mutumin da take gani ya Koma karamin yaro d'an wata shida, zaro ido tayi don ta tabbatar da abinda take gani sai ta ga ya sake komawa babban mutum d'an shekara arba'in cikin ta Ne ya fara kugi, a Hankali ta fita ta Koma d'akin da Daniyah da Granny suke, Granny taga shigowar ta murmushi tayi Tace "Nasan za'a rina dole ki dawo" ta Koma baccin ta, a ranar Daliyah Bata rintsa ba tayi duk addu'o in da zata iya yi Amma Ina tsoro ya mata yawa.
Washe gari bayan sun Gama share share da wanke da wanke duk aka zauna domin a karya, duk Yan gidan sun gane Bata da walwala, Kaka yace "Ke Yar birni me ya same ki na ganki haka kamar an Miki mutuwa na lura yau baki da walwala"
Kirkiran Murmushi tayi Tace "Bakomai kawaii dai yau bana jin na magana ne"
Yace "Toh Shikenan" aka cigaba da cin abinci ana Hira.
Bayan sun gama Daliyah ta Shiga d'aki ta kwanta da zaran ta rufe idon ta sai taga wannan mutumin yana Mata gizo, a zabure ta Tashi ta Shiga d'akin Grace ta tarar B bata Nan a ranta tace "Toh Ina Kuma taje", Bata tsaya b'ata lokaci ba ta fito ta Koma ta kwanta, Granny duk ta lura da abinda takeyi Kuma tasan me yake damunta, Tashi tayi ta bi bayanta tana Shiga Tace "Liyah me ya faru?" A zabure ta tashi ta zauna ta dafe kirji sannan ta maida kallonta ga Granny tace "Granny kin tsorata Ni wallahi"
Murmushi tayi tace "Ke kuwa tsoron me zakiji kina cikin d'aki?"
"Ai Granny d'aki ke da abun tsoro, don jiya na ga abin da ya tada min hankali" Nan ta Shiga Sanarwa Granny abun da ta gani, shiru tayi na d'an wasu lokaci sannan tace "Nima na ji Labarin yaron Nan, haka fa yake yi lokaci zuwa lokaci Yana canzawa hatta kamannin sa sai ya canza"
"Kuma take zaune dashi haka? Ni wallahi bazan iya ba,Amma Granny me yasa yake canzawa?"
"Sai Allah,Kuma ai Zama Mata dole ta zauna dashi uwace fa, yanzu an Kai shi gun mai maganin gargajiya ko za a gane inda matsalar take"
"Okay ai na Shiga d'akin ban ganta ba"
Muryar grace suka jiyo cikin gida da sauri suka tashi suka fita, grace ne take yi wa Kaka bayanin yanda sukayi " Naje gun sa yace min ba mutum na Haifa ba, idan Ina so na tabbar da hakan na Kai shi bakin kogi sannan na saya farin kyalle,gero,doya, da dabino na aje a tare dashi, sannan na b'uya Zan ga abun mamaki"
Kaka yace "To Babu wani abun kuma kin tabbata iya abinda yace kenan?"
"Eh na tabbata, ya ce indai ba a yi yanda yace ko da ya tafi zan sake haifan sa, sabida a lokacin da na samu ciki tun yana wata biyu ya Shiga jikina"
Kaka yace "Toh Shikenan duk abubuwan Nan da Kika Lissafo akwai a gidan Nan, kawaii dai farin kyallen ne Babu, Ina mijin naki yaje ne? Yaje ya sayo"
"Baba ai yayi tafiya har ka manta"
"Na manta tabbas tsufa yazo"
Granny tayi dariya tace Kai sai yanzu ka sani?"
"Na sani yanzun na sake tabbatarwa" duk sukayi Dariya grace tace "Baba Ni fa Zan tafi Kasuwar yanzun Nan"
Charaap Daliyah tace "Zan raka ki Kinga tunda mukazo Babu inda muke zuwa"
Kaka yace "ba matsala sai Kuje d'in Amma fa ku kula, ke kurma"
Yana kallon Daniya don haka yake kiranta yace "Ke bazaki bi su bane?"
"Zan bisu" a takaice.
Gyallen su suka d'auko da niyar fita, sai wata Yar karamar yarinya Yar wata goma ta Fara kukan zata bisu sunan ta Nne,kuka take sosai sai Daniyah ta d'auke ta, sai mamar ta tace "kunga ni d'in ma so nake naje nayi sayayya bari mu tafi kawaii tare"
Daliyah tace "to kuje kawaii sai wani lokacin Zan biku"
Maihaifiyar Nne tace "zamu iya tafiya dukan mu fa, Muje kawai"
Daliyah tace "A a wallahi naji na fasa zuwa ne"
Sai wata tsohu da tun d'azu suke magana tana kallon su tace "Ai itace ya kamata ku kaita gun Mai magani yarinya sai kace mayya"
Duk sukayi Dariya "Daliyah tace yau naga tsohuwa Mai sa Ido, kece dai ya kamata a kaiki ko za ki daina sa ido" shiru kawai ta Mata don ta lura yarinyar Nan Mara kunya, ce ganin Daliyah dagaske take baza ta bisu ba hakan yasa sukayi tafiyar su, suna fita suka shiga Keke napep, suna Isa suka yi sayyyar su sannan suka sake Hawa wani keke napep d'in suka tarar da wata Mata a ciki suka gaisa sannan suka Shiga grace,Maman Nne da matar a baya Daniyah Kuma a gaba, ko wacce tana rike da d'an ta, suna Isa kofar gida Daniyah ta sauka ta d'auki sauran kayayyakin da niyar shigar dasu ciki, mahaifiyar Nne Kuma tana rike da Nne a hannun ta, Grace kuma tana goye da d'anta hannun ta Kuma rike yake da Kaya, ganin hakan Matar dake zaune a cikin napep D'in Tace kawo d'an na rike Miki shi ki sauke sauran kayan"
Ta Mika Mata tare da yi Mata godiya, tana cikin sauke kayan na ga matar Nan ta shafa bakin Nne da yatsa biyu cikin sauri, sanan ta yi Murmushin gefen baki wanda ita kad'ai ta San dalilin yinsa, bayan ta Gama sauke kayan ta karb'i yarta sukayi Mata Sallama sannan suka bawa Mai napep hakkinsa.
Bayan sun Shiga gida ana zaune ana Hira aka jiyi ihun wata yarinya tana kuka, Kun San baban gida ya gaji haka musamman ma lamarin yara sai hakuri, Da sauri Maman Nne ta mike ta karasa inda suke Nne ta gani tana cizon Yayarta Yar shekaru biyar Kuma ta ki ta sake Mata hannu dakyar ta samu ta finciko ta, har Saida hannun ya zub da jini sannan ga alamun hakoranta Nan, ajiye Nne tayi ta d'aga Yayarta Amma sai taji jikinta a sake Kiran Sunanta take Amma shiru cikin sauri duk suka nufu su, Granny ce ta karb'i Yar ta Shiga duba ta, sai tace "Innalillahi wa Innalillahirraji'un,ta mutu meyasa meta ne?"
Mahaifiyar Nne ihu ta Shiga yi tana kuka tana fad'in "daga cizo? Sai ta mutu na Shiga uku?"
Kaka yace "Ba dai don cizo ba dai akwai wani abun na daban Ina aka tab'a haka?"
Granny tace "Nima haka dai na gani"
Duk sun Shiga rud'ani cike suke da mamaki, Daliyah da Daniyah duk sun tsorata sabida basu tab'a ganin gawa ba sai yau.
Wani ihu suka Kara ji, suna dubawa Suka ga d'an kanin Mijin su na ihu Nne na cizin say kafa Kan su karasa inda suke har ya mutu.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
_Mu had'u a page na gaba_
*Milhaat Ce* YAR TERAWA
Please Share 🙏🏻
✨✨ *DALIYAH* ✨✨
*DA*
✨✨ *DANIYAH* ✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_*(A Sympetic,Love and Funny Story)*_
```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```
*Daga Marubuciyar*✍🏻
*MATAR AURENAH*
*SAIRA DA SARAH*
*AND NOW*
*DALIYAH DA DANIYAH*
_(Cigaban Sairah da sarah)_
*DALIYAH* da *DANIYAH* , ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya, tausayi,fad'akarwa, nishad'antarwa gami da ilmantarwa.
```
*Note_* ```bamu yarda wani ko wata su juya Mana labariba tare da izinin mu ba.```
Ya Allah Ina rokon ka da ka bani ikon gama Littafin Nan kamar yadda na ra.Ameen
Labarin *Daliyah* da *Daniyah* k'ageggen labarine ban kirkirin Labarin Nan don cin zarafin kowa ba.Allah ubangiji ya datar da mu.
Ameen....
*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu (Milhaat)*✍🏻✍🏻
🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.
🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*BISMILLAIR RAHMANIR RAHIM*
*PAGE* 5️⃣0️⃣🔄6️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
Granny tace "Nima haka dai na gani"
Duk sun Shiga rud'ani cike suke da mamaki, Daliyah da Daniyah duk sun tsorata sabida basu tab'a ganin gawa ba sai yau.
Wani ihu suka Kara ji, suna dubawa Suka ga d'an kanin Mijin su na ihu Nne na cizin say kafa Kan su karasa inda suke har ya mutu.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Mahaifiyar Nne kuka take sosai kamar ranta zai fita, a yayin da duk Yan gidan sun tsorata sosai da lamarin Nne, aciki awa 2 an rasa yara 6 acikin gidan d'aya Kuma duk sai Nne ta cije su, d'aure Mata baki akayi aka
Kaita gun Mai magani, bayan ya gama duba ta yace "wata Mata ce ta shafa mata baki da hannunta, ta shafa Mata maita idan ta ciji Mutum sai su shanye jinin"
Mahaifiyar ta Tace "Hakane akwai matar da ta ce na mika Mata ita a napep duk yanda akayi itace ta Mata wannan abun" ta karasa maganar cikin kuka"
Yace "Good tunda kintuna a Ina ta sauka?"
"Mun Riga ta sauka"
"Kashh Kinga inda matsalar take, bazan iya karya asirin nan ba, dole sai an samo matar, ita kad'ai ce zata iya karyawa, Kuma ko da kin je gun wani hakan zai fad'a Miki"
Cikin kuka Tace "Toh Me mafita?"
"A Nemo ta don ita kad'ai ce zata ita karya asirin ko kuma a kashe ta don zata Rika kashe mutane, har ke kanki baki tsira ba"
Kukan take sosai Granny Kuma na rarrashin ta, don dama da ita aka aje, Granny tace "Tashi mu tafi kukan Nan bazai Mana amfanin komai ba"
Suna Isa gida suka tarar da dogayen sarki da Kaka a tsaye a kofar gida, mahaifiyar Nne na ganin su tace "Na Shiga uku har an fad'awa sarki"
Granny tace "Kar ki damu mu karasa muji"
Kaka yace "sarki ya Aiko ana neman mu don haka chan zamu wuce yanzu"
Ba musu suka Kama hanya dogarayen sarkin Kuma na biye da su a baya tunda suka Fara tafiyar babu Wanda yace wa wani komai, suna Isa suka tarar da mutane a cike a fada, sai maganganu ake kasa kasa
Sarki yace "Me yake faruwa naji mun samu mayya" Rai a b'ace.
Kaka yace "Rankashi dad'e ba mayya bace jika ta ce"
A tsawace sarki yace and so what? Bazan bari tana kashe min mutane na ba" Ya nuna wani mutum a zaune yace "ga Malamin da kukaje gun sa nasa a kawo min shi, ya fad'a min komai don haka dole a kashe ta"
Kuka Granny da Mahaifiyar Nne keyi, suna magiya Amma yaki sauraron su, Kaka ma haka ya kasa magana son yasan halin sarkin nasu babu abunda zai sa ya fasa, sai yasa aka kwace ta daga hannun Uwarta, aka kaita bayan gari aka harbe ta da bindiga.😭
Babu Wanda baiyi Kuka a gun ba ganin yanda yarinyar ki jikin ta bata San ma me ake Shirin yi Mata ba, har Saida aka harbe ta ta Fara kuka tana Kiran sunan mahaifiyar ta har Allah ya d'auki ranta.
(Gare ku iyayen yara ya kamata ku lura ku daina bawa bako 'ya 'yan ku Duniyar ta lalace ba amana kowa macuci ne naka ma ya cutar da Kai balle ace bare, duk rintsi rike d'an ki a hannu Kar kiyi kuskuren bawa kowa d'an ki, Allah ubangiji ya Kare mu da kariyar sa ameen)
Daliyah da Daniyah sunyi kuka sosai har hawayen su ya kafe sabida komai a gaban su akayi, duk Yan gidan sunfi sati suna jimamin abin da ya faru.
Grace ganin anfi sati da rasuwar Nne da Yan uwanta yasa yau ta shirya tsaf ta d'auki duk abubuwan da Malamin yace ta saya, Granny Tace "bazan barki ki tafi ke kad'ai ba tare zamu tafi"
Grace ta ji dad'in hakan don dama duk a tsorace take da zuwa gun don Bata San me zata gani ba.
Daliyah da Daniyah Suma Suka ce zasu bisu Granny ta Hana, kaka yace "ki kyale su suje d'in ai ba komai"
Granny tace "Su Kenan ko Ina sai suce zasu je"
Grace tace "bakine fa Kuma kinga kullum suna gida Babu gun zuwa domin garin namu ya zama abun da ya zama, kawai ki kyale su"
Granny Tace "Toh Shikenan"
ta amince ne kawai don tana Jin nauyin Kaka Amma ba don ta so ba, suna Isa bakin kogi grace ta kunce shi ta aje, Shi a bakin ruwa da duk abubuwan da suke bukata, sai suka b'uya a bayan wata babbar bishiyar kuka, ya Kai kusan awa d'aya a zaune a gun, Yana ta kalle kalle, Grace tace "Mama Zanje na d'auko shi, Kinga fa har yanzu bai canza ba, ga Rana yayi yawa" ta marairaice kamar zata Yi kuka.
Granny tace "Mu d'an Kara hakuri"
Daliyah tace "Granny nifa na d'auka muna aje shi zai canza ina ga kawaii mu tafi yaron Nan ba aljani bane ba"
Granny tace "Shegen manyace Liyah Allah ya shirye ki"
Daniyah tace "Ameen fa don Wallahi Daliyah sai addu'a"
Daliyah ta Kai Mata duka ta kauce, kwasam sai suka ga ya zama babban Mutum harda furfura a fuskar sa ganin babu Wanda ke kallon sa, wani mutumi ya fito daga cikin ruwa ya kwashi kayayyakin da grace ta aje sai Suka shiga ruwan tare.
Duk sun tsorata Daliyah tace "Ya tabbata, d'an ruwane kawai ba aljani bane"
Daniyah tace "Liyah ai Yan ruwan Suma aljanu ne tunda ba mutane bane"
Granny tace "Ya Isa haka ku Tashi mu Koma gida" dakyar suka samu suka d'aga grace a gun grace tace "Mama d'ana Dana San zasu tafi min dashi da ban kawo shinan ba"
Granny tace "Kiyi hakuri amma kina gani da idon ki ba d'an ki bane, gashi Nan fa Kinga tsohi ne futuk, shi yake sose ki kice kina jin zafi a bakin Nonon ki"
Daliyah tace "Amma Anya mara kunya Wallahi kato dashi ya sha Nono babbar mace"
Daniyah Tace "Kaii Liyah"
Daliyah tace "Nayi shiru" sai ta rike bakinta.
Nan suka rirriketa har suka Isa gida.
Tun da Kaka ta gan su ba d'an ya tabbar da maganar Malamin gaskiya ce, duk akayi ta rarrashinta rasa d'a ba karamin Abu bane ba, ko da kuwa yau Kika Haifa, bare ace Wanda ya kwashi watanni dake"
Grace taci Kuka har sai da idanuwan ta suka kankance, duk tabi ta lalace, Kanwar Grace Mai suna Veronica na zama tare dasu a gidan tun tana karama, Daliyah da Daniyah sun Saba sosai kasantuwar sa'annin juna ne, hakan yasa duk inda zataje suna tare, yau sun shirya cikin shigar gona Granny da Kaka sukayi ta musu dariya Amma ko a jikin su Daliyah tace "Yau dai sai munje munga yanda gonan doya yake"
Daniyah Tace "Eh Mana, Mutum sai dai yaci Amma bai San ya ake samo shi ba.
Kaka yace "Toh dama me zaku iya yi ko da kunje ma sai dai kuyi kallo"
Grace tace "Baba baka ga harda rike fartanyu ba sai kace zasu yi abun kirki"
Daliyah tace "Ba ruwan ku naku Ido idan Kuma akwai Wanda zai Hana mu Kuma to naji"
Granny tace "ai dama bamu Ce komai ba, a dawo Lafiya"
Suka Kama hanyar su, su uku suna tafiya suna Hira kan hanyar su ta tafiya gona suka had'u da wani saurayi, Yana ganin Veronika ya Fara Murmushi ita ma ta maida Masa, bayan sun gaisa yace "Nayi kewar ki masoyiya ta"
Veronica Tace "Nima Nayi kewar ka sosai"
Kallon su kawaii su Daniyah keyi, Daliyah Kuma duk a tsorace take don gani take kamar za'a Zo a Kama su a tafi dasu, Kuma daga ganin su kasan suna tsananin kaunar junar su.
Murmushi yayi sai ya maida kallon sa ga su Daliyah yace "Amma wa'annan baki