Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 66367 words

Chapter 12 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

Nan suka Fara hira, Liyah mamaki ne duk ya rufe ta "Ashe dama Yana magana haka? Lallai guy d'in Nan miskili ne Amma ko ba komai naji dad'i sosai"
Fareedah da Kuma sai rawar Kai kawai take yi, Liyah a ranta Tace "yau kowa ta kansa yake in dai Sagheer zai soni ba ni da wata matsala"


"Liyah!!!" Jin an kira sunan ta da Kuma Wanda taji ya Kira sunan ta, da sauri ta kalli Sagheer a nitse Tace "Na'am" Murmushi yayi ya shafa sajen fuskar sa sannan yace "Muryar ki na da dad'i please taimakon ki nake nema"
Gyara Zama don mamaki ya bata sosai sai ta nuna kanta Tace "Ni? Taimako a wurina?"
Ra'ees yace "Eh ke kina mamaki ne?"
"Eh sosai,Amma wani wani irin taimako?" Tana maganar tana kallon Sagheer, Murmushi yayi "Ina fatan Rumana ta fad'a Miki cewar muna waka?"
"Eh ta sanar min"
"Good so muke mu bud'e sabon band Kuma muna bukatar muryar mace da Rumana take Mana so muna so mu samu at least Mata biyu aciki ina fatan Zaki bamu had'in Kai?"
Murmushi tayi tace "Ai ba matsala shi yafi komai sauki"
Ra'ees yace "Ai na fad'a maka ba matsala insha Allah gashi ta amince"
"Eh na yarda yanzu"
Fareedah Tace "To Ni Kuma fa ya zakuyi dani?"
Ra'ees yace "Kar ki damu Kema za'a yi dake, Babe zamu tafi" Yana maganar Yana kokarin mikewa.


Ta amsa "Da okay take care"
Ya amsa da "You too,sai anjiman ku"
Sagheer eye glass d'in sa ya d'auka ya saka a fuskansa sannan ya d'auki makullin motar sa da ke Kan tabur ya d'aga musu hannu yace "Bye" Suma hannun suka d'aga suka amsa da "bye."


Suna barin gun Fareedah tace "Yauwa Ruman please aramin wayan ki man duba applications masu kyau, sabuwar waya ce"
Ba musu ta Mika Mata, Fareedah na karb'an wayar received calls ta Shiga last call ta duba taga last call d'in ansa Life Partner Murmushi tayi ta Shiga ta d'auki number, sannan ta Shiga xender ta Fara tureren karya sai da ta gama ta Mika Mata.




Da gudu ta fito daga d'akin ta nufi compound na gidan amai take yi sosai kamar zata Amar da kayan cikin ta, da sauri Nna ta bi bayan ta tana fad'in "Sannu Sannu" ta dafe ta a kafad'a, Nna Tace "Chidinma ki d'ebo ruwa da sauri" ba b'ata lokaci ta fito da gudu hannun ta rike da Kofi,Nna ta karb'a sannan ta Shiga wanke wa Rahila Baki "Sannu Rahila me ya same ki?"
Rike cikinta tayi alamun Yana murd'arta jiki ba Karfi Tace "Nna I don't know tun jiya nake Jin zazzab'i"
"Me Kika ci ne?"
"Ba komai fa Nna bana ma iya cin Abinci ina Jin kamshin abinci sai naji zuciyana ya na Tashi"


Nna mikawa Chidinma kofin tayi sannan Tace "Muga hannun ki" ta Mika Mata d'aga kanta tayi Tace "Muga idon ki" ta duba, Nnna Tace "Rahila ciki?"
A razane Rahila Tace "Ciki?"
Ta dafe kirjin ta had'e da fad'in "Na Shiga uku"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau Kam da Allah Zan had'a ku min comment please😂🙏🏻


🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_




```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```



*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE``` 1️⃣6️⃣0️⃣↪️1️⃣7️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
Rike cikinta tayi alamun Yana murd'arta jiki ba Karfi Tace "Nna I don't know tun jiya nake Jin zazzab'i"
"Me Kika ci ne?"
"Ba komai fa Nna bana ma iya cin Abinci ina Jin kamshin abinci sai naji zuciyana ya na Tashi"


Nna mikawa Chidinma kofin tayi sannan Tace "Muga hannun ki" ta Mika Mata d'aga kanta tayi Tace "Muga idon ki" ta duba, Nnna Tace "Rahila ciki?"
A razane Rahila Tace "Ciki?"
Ta dafe kirjin ta had'e da fad'in "Na Shiga uku"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............."what do you mean kin Shiga uku, how on Earth do you got pregnant? Oh is that why you came back to my house?"
Kad'a Kai take ta yi, hawaye ne masu zafi suke gangarowa daga fuskar ta, Nna dake mutumce Mai tausayi sai ta Shiga rarrashin ta Tace "Tashi mu Shiga ciki" da taimakon Nna suka Shiga cikin gida a parlor suka zauna, Nna Tace "Rahila tell me ya akayi hakan ta faru who is responsible for this pregnancy?"


Rahila kuka take a hankali, tana Wasa da yatsunta, sai ta d'ago Kan ta idon ta sunyi jajir hancin ta duk majina, Tace "Nna it's the prince"
A razane Nna Tace "Ennn! Which prince?"
Had'iye yawun da ya tsaya Mata a wuya tayi Tace "Prince of our Village, Prince Steven"


Murmushi Nna tayi tace "Ta kwana gidan sauki, ai na d'auka irin Yan iskan gari ne masu yaudaran emmata su gudu sabida Basu da kud'in kula da yaran, to yanzu Zaki Fara shiri gobe goben Nan zamu je kauyen ku sabida mahaifiyar ki tasan halin da ake ciki"


Rahila gwiwowinta ta zuba a kasa ta had'a hannayen ta guri guda tana kuka wiwiwi tace "Nna please Kar ki fad'awa mamana, baza taji dad'i ba don ba tarbiyar da tamin ba Kenan"
"To Banda ke da abunki Rahila ai shi ciki baya b'uya do zai fito"


"I know Nna, dalilin da yasa nace Kar ki fad'a mata shine.......
Nan ta Shiga Sanar Mata da komai yanda akayi ta samu cikin da kudirin Prince sai ta fashe da kuka.


Nna Tace "Chaaaaai fiya kwa" ta tufar da yawu, sannan ta d'aura da fad'in "Men!! Men, yanzu bayan ya Miki fyad'e ya Auri kanwar ki? Amma Prince d'in Nan d'an iska ne"


Chidinma Tace "Sosai fa Nna abin ya bani mamaki sai kace a Shirin film wato Shi yayi riba biyu kenan ko?" Sai ta Maida kallon ta ga Rahila tace "Amma sis, Rose Bata San abinda ya faru tsakanin ki da prince bako?"
Kai kawai ta d'aga Mata alamun "Eh" Chidinma tace "I knew it ai da baza ta yarda ba"


Nna tace "Zata yarda, me banbancin a yanzu? Ta Riga ta San suna Soyayya da 'yar uwar ta Amma ta amince ta aure shi, Amma bakomai My dear God is with you oo,ki dai na kuka tashi kije ki watsa ruwa Zaki ji dad'in jikin ki"
Godiya Rahila tayi mata sosai,sannan tayi wankan tana gama wankan ta kwanta bacci Mai nauyi ya sace ta.


*OXFORD UNIVERSITY*
"Wow Maryam Kinga yanda kikayi kyau kuwa Wallahi Atamfa sunfi Miki kyau akan wannan Yan iskan Kaya da kike sakawa" Rahina ne ke wannan maganar tana kallon Maryam dake kallon kanta a madubi.


Murmushi tayi tace "Rahina gaskiya kina da abinda dariya tun d'azu fa kike ta rurutani Kuma nasan ba wani kyau nayi ba tsokana ce irin Taki"
"A'a Wallahi am damn serious nasan kinyi kyau Kuma Zaki Sha mamaki idan muka fita don nasan ba kowa ne zai gane ki ba"


"To naji naji ya Isa haka Zaki tashi mu tafi lectures d'in ne ko kuwa Baki gama surutun naki ba"
Dariya Rahina tayi tace "Muje ban gama ba, Zan takaita shi zuwa wani lokacin"
"Whatever tashi mu fita"
Tafiya suke suna Hira, har suka Isa LT, suna Shiga idon ta ya fad'a akan Sabir har sai da taji kirjinta ya buga, Rahina ta lura hankalin Maryam ba a jikinta ya ke ba hakan yasa ita ma ta kalli inda take kallo, Murmushi tayi Tace "Maryam Sabir ne Zaki iya samun Soyayyar idan Kika Zama mutuniyar kirki Kai ba ma shi kad'ai ba duk wani d'a namiji na gari Wanda ya ganki a irin shigar Nan Dole ya ji wani Abu a ransa, yanzu ne ya kamata ki sace zuciyar Sabir"


Murmushin gefen baki tayi tace "No Rahina, no more love na hakura da Soyayyar Sabir don na lura akwai Wacce yake so, son maso wani nake ance koshin wahala, gaskiya na wahala shekaru biyu fa Kenan nake bibiyar sa, Haba is enough"


Dariya Rahina tayi tace "Allah Mai iko jiya jiyan Nan fa Kika Gama kuka akan baza ki daina son Sabir ba baza ki iya daina son sa ba Amma ji abinda kike cewa?"


Itama dariyar tayi tace "ke dadina dake mutunci kad'an ne, ai idan Kika duba jiya sanyi akayi yau weather ya canza Ana zafi kad'an alamu an shigo wata Rana, yau daban jiya daban, bazan daina son shi ba Amma dole na rabu dashi, Zan tinkare shi da friendship har Allah yasa mu Gama karatun mu yayi kano Ni Kuma na koma adamawa"


Iska Rahila ta hura sannan Tace "To Allah ya sa ki iya because the love you have for these guy is extraordinary"
Murmushi tayi tace "Kar ki damu insha Allah , Allah zai dafa min idan shi d'in rabo na ne sai kiga anyi auren"
"Toh shikenan ina Miki fatan Alhairi"
"Nagode muje ko?"


Bayan sun gama lectures, Sabir na tafiya zai koma hostel sai yaji ana Kiran sunan sa ya gane muryar ta shiyasa ma yayi banza da ita ganin ta dage Kiran sunan sa sai kallon sa ake ya juyo Rai a b'ace a tsawace yace "Wai ke Maryam ke Wace irin jaka......." Kasa karasa maganar yayi Baki a bud'e yake kallon ta, Murmushi tayi sannan Tace "Kayi mamaki?"




Shiru yayi Yana Kare Mata kallo daga sama har kasa yace "Maryam kece?" Cike da mamaki, "Eh nice" gyara tsayuwar sa yayi yace "ikon Allah, Kinga yanda Kika canza kuwa? Kamar bake ba, Allah Mai iko yau Maryam ce da hijab har kasa da safa"


Dariya ta Shiga yi garin irin kallon da yake Mata mamaki ne karara a rubuce a fuskar sa, sai da tayi Mai isarta sannan Tace "Sabir Kai da Rahina bani da bakin gode muku Sai dai ince Allah ya saka da Alhairi,ke Kuma Rahina fatana shine Allah ya bar mu tare, da ace ana samun kawaye irinki da Rayuwar mu tayi nagode Sosai"


Murmushi kawai Rahina tayi, Sabir kuma kasa cewa komai yayi gyaran muryar da Maryam tayine yasa shi ya dawo daga tunanin da yake Tace "Yaya Sabir Dan Allah in Neman wata alfarma Wanda baxa su wuce biyu zuwa uku ba"


Mamaki ne ya kama shi, "Wai Yaya Tace min" Murya chan ciki yace "Mene Ne wannan?"
"Kaga nayi Wasa sosai so nake ka Fara min extra lesson ko zanyi catch up, Abu na biyu Kuma ina so mu kulla abota da Kai ko Zan d'auki Kyakkyawan halayyar ka"


Murmushi yayi yace "ba matsala in dai wannan ne,amma naji dadin ganin ki a haka but ina fatan dai ba tuban muzuru kikayi ba?"
Maryam da Rahina duk Saida sukayi dariya sannan Tace "A'a Yaya Sabir wannan karon dagaske nake tuban tsakanin da Allah"
"Toh Masha Allah, dama abinci zanje ci kuzo Muje"


Jiki na rawa Maryam ta ce "to Muje" sai ta riko hannun Rahina, a jere su uku suke tafiya suna Hira irin na students"


*KANO*
"Sagheer ka gani ko? Ai na fad'a maka komai zai Zo maka da sauki idan ka aje wannan girman Kan naka, gashi ba tare da mun Sha wahala ba Liyah ta amince"


Murmushin gefen baki yayi yace "Koma dai mene ne ka fad'a Ni Wallahi badon ka dage ba babu abinda zai sa nayi wa yarinyar Nan magana"


"Hmmm Sagheer Kenan ka bi duniya a Sannu, Wallahi idan baka daina wulakanta Emmatan da suke son ka ba Soyayyar wata ne zaiyi ajalin ka"
Hannu ya d'aga Masa "Kaga ya ishe ka haka, ina dai ka samu abunda kake so? Liyah ta amince ko? To ka daina min surutai kasan bana son hakan"
"Gaskiya ce Sai na fad'a maka Wallahi idan ban fad'a maka ba wa zai fad'a maka?"
Tsaki ya yi sannan ya jaaa motar suka bar gun yace "Sai Kuma kayi."


*DANIYAH*
Daniya karatun ta take bata da wata damuwa idan Abu ta shige mata duhu Hafeez take Kira ya nuna Mata hakan yasa suka shaku da juna sosai.




Kamar kullum tana bukatar ya nuna Mata abinda bata fahimta ba bata tsaya b'ata lokaci ba ta Shiga Kiran layin sa yana d'agawa ta Sanar dashi bukatar ta ba b'ata lokaci yazo bayan sun gama suka Fara Hira yace "Daniyah kin San ina da kanwa a makarantar Nan?"
Ajiye wayarta tayi ta fuskance sa tace "Haba? Amma baka tab'a fad'a min ba"
Sosa keyansa yayi sannan "I'm sorry hiran ne bai zo ba kin San komai sai Allah yayi"
"Hakane a wani department take?"
"A law take 100lv"
"Aaaah kaga Nima akwai sister na a department d'in gaskiya ya kamata ka had'a mu"
"Insha Allah Zan had'a ku, kin San mene ne?"


"A'a sai ka fad'a"
"Gaskiya sunan ki wahala yake bani baki da wani suna ne?"
Murmushin gefen baki tayi Tace "Babu Daniyan daai"
Yace "Toh gaskiya Zan sa miki suna"
"Seriously? Wani suna Kenan?"
"Aniyah"
"Wow sunan yamin dad'i"
"Dagaske kike?"
"Eh sosai wannan sunan Insha Allah har gida"
Dariya kawaii yayi suka cigaba da hirar su.




Karatu yayi nisa, students sai karatu suke don suna daff da Fara exam.


A yaune a ka kawo wasu Liyah motocin su, murna sosai, motocine na gani na fad'a iri d'aya ne Amma kaloli daban, Liyah Jaa, Daniyah Pink, khadija Baki.
Wannan Kennan


Abokan su Sagheer da su Liyah zuwa yanzu sun Saba sosai sabida tare suke practice sai dai Sagheer bai fiye kula su ba hakan bai tadawa Liyah hankali ba tunda kusan kullum sai ta ganshi.


Yau Aniyah da safe take da lectures hakan yasa ta shirya da wuri ta fito ba tare da sunyi Sallama da Liyah ba don a lokacin da ta fito ta na wanka, hakan yasa tana gama lectures d'inta ta farko ta nufi department d'insu Liyah tana Shiga ta duba bata ganta ba, ba don taso ba ta koma LT, karfe d'aya ta fito masallaci ta nufa Kan ta koma ta dubo Liyah har yanzu bata ganta ba layin ta Shiga nema Amma busy a ranta tace "Ko lafiya, Yauwa bari na Kira Fareedah" Fareedah na picking bayan sun gaisa Tace "Dan Allah Liyah nake nema"
"Oh Liyah Kam bamu da lectures yau Amma akwai abinda zasu yi kije bayan Law department Zaki ganta a gun"
"Ok nagode Sosai"




Tafiya take a nitse har ta Isa gun group nasu Sagheer ta gani a nitse ta Karasa gun Ruman Tace "Sannu Dan Allah Yar Uwata nake nema"
Rumana tace "Liyah tun d'azu ke ake jira har ran Sagheer ya Fara b'aci"


Murya na rawa Tace "A a ni suna na Daniyah, Daliyah Twin sister na ce"
Sagheer ne ya karaso gun yace "Ina Kika Shiga ne kizo mu Fara please"
Murmushi tayi tace "please Daliyah nake nema"
Dariya yayi yace "Oh yau Kuma da irin salon da Kika Zo Kenan?"


Kan ta amsa sukaji muryar d'aya daga cikin abokan sa yace "Sagheer ana Neman ka"
"Waye?"
Nuna Masa mutumin yayi da d'an yatsa, Sagheer na ganin Wanda aka nuna Masa ya b'ata raaai kamar bai ta'ba Dariya Rai a 'bace ya nufi inda yake, Rumana Kuma ta riko hannun ta tace "Ki zauna Mana kina Abu kamar bakuwa Bari na sayo Mana ruwa" sai ta fita.


Sagheer yace "Kaine me kazo yi anan?"
Murmushin takaici yayi yace "Haba My Son for how long zakayi fushi da ubanka Kar ka manta fa duk lalaci nine Mahaifin ka"


"Allah ya sauwake suna kawaii kaci na uba Amma Sam Kai ba uba bane ba"
Murmushin takaici yayi sannan yace "Irfan bazan daina rarrashin ka ba, nasan na cutar da kai Dan Allah ka yafe min ka dawo gida"


Murmushin gefen baki Sagheer yayi yace "Dalilin da yasa kazo Nan Kenan?"
Sa hannun sa yayi a aljihu sannan yace "Naji labarin wakokin ka a gun mahaifiyar ka shiyasa Nazo na duba ka me zai Hana na bud'e maka studio?"


A tsawace yace "ban bukatar komai naka, idan inaso da gumi na zanyi"
Jiki a sanyaye mutumin ya fita ganin zai Tara Masa jama'a, Daniyah duk maganar da suke a kunnen ta a ranta tace "ji yanda yake magana da Mahaifin sa kamar bashi ya haife shi ba."


Ganin Sagheer ya fita sai ta bi bayansa Zama yayi ya had'a Kai da gwiwa, zuwa tayi ta Tsaya a kansa Kai tsaye Tace "Iyaye ba abun rainawa bane"
D'ago Kan sa yayi idanun sa sunyi jajir murya na rawa ya tashi ya tsaya "Ke waya Baki izinin shiga cikin Rayuwata da har Zaki Zo Nan kina min magana?"
"Kayi hakuri idan na maka shisshigi gani nayi Kai musulmi ne Kuma Allah ne da kansa yace mu bi iyayen mu,musamman ma Kai na miji ne aljnnar ka na karkashin kafan su"


Jikin sa ne yayi sanyi tabbas maganar ta gaskiya ce Zama yayi cikin sanyin murya yace "Baki San me yamin bane shiysa kikace haka"
Itama zama tayi a gefen sa Tace "Eh ban sani ba Amma inaa so ka sani iyaye suna da hakki Akan 'ya 'yan su haka ma muna da hakkin a Kan su, Amma hakan ba Yana nufin mu Raina su bane, find it in your heart to forgive him ka yafe Masa laifin da ya maka"
Tana Kai Nan ta tashi ta koma inda su Rumana suke, ita dai burinta taga Liyah.


Maganganun Liyah ya ta'ba Masa zuciya har sai da yayi kuka zuwa yayi ya wanko fuskar sa Kan ya dawo in da Sauran suke, Daniyah tayi kokarin ta gudu Amma duk sun tsare ta su a ganin su Liyah ce, tunda suka Fara rera wakar yake kallon ta wani irin kallo yake Mata Wanda yake nuna tsantsar so, Rumana ganin Haka ta Shiga yi musu hotuna da videos.


Liyah Kuma na gida tana ta sharb'an baccin ta Bata San Ma ana yi ba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Naji dad'i sosai Kun Fara comment, Amma Dan Allah ku Kara sabida na samu na gama muku typing Dan Allah idan kina bibiyar labarin Nan ki daure kimin sharhi kamar yanda sauran sukeyi ko min Kankantanshi zanji dad'i.


Mu had'u a page na gaba


🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_




```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```



*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```PAGE```1️⃣7️⃣0️⃣↪️1️⃣8️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```


Maganganun Liyah ya ta'ba Masa zuciya har sai da yayi kuka zuwa yayi ya wanko fuskar sa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads