Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 66367 words

Chapter 3 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

da ilmantarwa.
```


*Note_* ```bamu yarda wani ko wata su juya Mana labariba tare da izinin mu ba.```


Ya Allah Ina rokon ka da ka bani ikon gama Littafin Nan kamar yadda na ra.Ameen


Labarin *Daliyah* da *Daniyah* k'ageggen labarine ban kirkirin Labarin Nan don cin zarafin kowa ba.Allah ubangiji ya datar da mu.
Ameen....


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu (Milhaat)*✍🏻✍🏻


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.
🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


*BISMILLAIR RAHMANIR RAHIM*


*PAGE* 3️⃣0️⃣↪️4️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
"Ke wato dama Kece Kika d'auke min? Lallai yarinyar Nan"
"Jiman Uncle Suna na Daliyah ko kuma kace min Liyah, gobe Zan kawo maka, kazo ka b'ata min Lokaci ban gama test d'ina ba mtsww"
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


Uncle Ameer kasa motsi yayi Yana mamakin yarinyar Nan, "ga rashin ji ga raini ga tsokana duk ita kad'ai Allah dai ya shirya" (Ni Kuma nace Amin Kai ma Allah ya shirye ka Mai leke kawai).😏


Yana Shiga class ya samu sun Gama sai surutu suke , jiki a sanya ye yace "Keep quiet" Daliyah dariya ta Shiga yi, Amma Bai kula ta, Fareedah Tace "Yadai mutuniyar me ya faru ne?"
"Bakomai fa, kawai dai na tuno da wani Abun ne"
"Baza dai ki fad'a min ba"
"Ke dad'i da ke naci wallahi."
"Allah ya Baki hakuri"


Uncle Ameer suka ga ya Tashi har ya fita ya Kuma dawo wa yace "Where is the class monitor?"


Sai naga wata yarinta ta d'aga hannu, sai yace Mata "am going out, right the names of noise maker"
"Okay sir"


"Idan Kuma naga empty list Zan Zane ki"
"Okay sir"


Sai ya fice,Yana fita ajin yayi shiru, Karan buga desk najiyo na juya don naga su wane ne, Daliyah da Fareedah da na gani, Daliyah na buga desk Fareedah na waka, duk ajin babu wanda ya Isa ya musu magana, sai d'aya daga cikin student d'in tace "Mary You are the class monitor talk to them can't you see that they are disturbing us? Karatu fa muke and we can't concentrate on our books"


Mary ta mike ta kalli Fareedah da Daliyah, Tace "Kai Kai Malamai ya haka? Ku Mana shiru or else.."
Daliyah Tace "Or else what? Ki karasa zancen ki"


"Idan bakuyi shiru ba Zan rubuta sunan ku" "bismillah ki rubutu"
Kyale su tayi ta yi zamar ta, Daliyah tace "Ina Miki magana wato shine har da Zama ko"


"Banda lokacin ku" Daliyah Tace "Fareedah tashi muje mu Koya Mata hankali" har sit d'in mary suka je, suna tsaye a gabanta Daliyah Tace "Oya rubuta sunan mu" fareedah tace "Look at this girl o, ke don Ubanki mu sa'annin kine"


Mary tace "Ni dai ku kyale Ni" Daliyah tace idan fa Baki rubuta sunan ba, jiki magayi"



Hannu na rawa ta rubuta Daliyah Hafeez da Fareedah Mukhtar, Daliyah tace "Lallai yarinyar Nan wuyan ki ya Isa yanka, shine har da rubuta sunayen mu?"


"Daliyah Kece fa Kika ce na rubuta me ye laifina?"
"Ina magana kina magana ko" sai saukar Mari Mary taji a fuskarta, sai Tace "Kai Kai Fareedah Kika mare Ni?"
"An mare ki ko Zaki Rama ne ?"


Fareedah bata an Kara ba taji saukan Mari a fuskarta, Daliyah tace "Kutmelessi, Yau sai kin San ki Mari kawata" duka suka Fara Kai mata ta ko ina, ganin suna neman hallaka ta, wata ta fita da gudu,bata b'ata lokaci ba ta dawo aunty Maryam na biye da ita, Aunty maryam na shigowa taga ajin ya birki ce, A dai dai lokacin Daliyah ta yaga paper da ta rubuta sunan su tasa Mata a Baki tana fad'in "Taune sai kin taune shi" matse wuyar ta sukayi suka sa Mata a Baki Bata so Amma sai da ta taune Kuma ta had'iye.


Aunty Maryam tace "What's happening here? Daliyah sake saketa" Daliyah ta ce "Aunty Akan me Zaki rike Ni? Okay so kike ta hallaka Ni ko?"


"Ke Daliyah ki bini a Hankali dama Ina da cikin ki"
"Toh ki haife Ni Mana ki huta" tana wurga Mata harara
"Ni kike fad'awa hakan ku duba kuga yadda Kuka ji Mata ciwo har da yaga Mata Riga"


"Toh Ina ruwana Ni kad'an ta gani" aunty Maryam tayi Kan Daliyah da niyar zata dake ta dorina, da sauri ta kwace ta Fara shaud'a wa Aunty Maryam abinka da farar mace Nan da Nan gun yayi jaa.


Yan aji sai ihu sake, Uncle Ameer na Shiga yace "me ya faru haka? Me kukeyi haka?"
D'aya daga cikin students d'in ya Sanar dashi abinda ya faru, uncle Ameer a ransa yace "Ni ya zanyi ba Hali na hukunta ta"


Aunty Maryam cikin kuka Tace "Kayi shiru baza kace komai ba? Kaine fa Vice principal Amma kayi shiru"


"Em em Miss Maryam Kinga kije school clinic zanyi handling d'insu" ficewar ta tayi Bata ce Masa komai ba, ya ce wa Fareedah da Daliyah suje su zauna.


Zaman su ke da wuya aka fita break, Bayan sun fita break Fareedah da Daliyah na zaune a inda suka Saba Zama, wata student tazo wucewa da bakar Leda a hannun ta, Daliyah Tace "Ke zonan"


Tana zuwa Tace "Gani"
Fareedah Tace " A wani aji kike?" "JSS 1"
Daliyah tace "Ohh Jss 1? Kuma kike tsaye Akan mu my friend will you kneel down?"

"For what Ni bazanyi ba" Fareedah ta rankwashe ta sannan tasa tayin kneel down Dole, daliyah ta kwace ledan biscuits da chocolate sai baban Holandia, Tace "Fareedah kyale ta, barta ta tafi"
Fareedah Tace "ke Tashi ki Barnan"


Tana barin wurin wurin Kai tsaye ta nufi staff room gun uncle Ameer ta Sanar dashi Bayan ta Gama masa bayani yace "Yanzu Kila ma gugguru ne a ka kwace Miki, da zob'o ko Kuma kunun Zaki, kin Zo Zaki Dame Ni"


"No uncle biscuits da chocolate ne"
"Muje ki nuna min su" sai suka fita a ransa yace yaran Nan sun Shiga uku don sai na huce haushina akan su"


Suna karasawa gun ya ga Daliyah sai da ya ji rasss, har ji yayi kamar ya arce a guje, yace "Ke su waye suka kwace Miki biscuits d'in?"


"Uncle gasu Nan" tana nuna su da d'an yatsa, Daliyah Tace "Ke waye sa'an ki da zaki Rika nuna mu da Yar yatsa?"


Sai Tace "Uncle na kawo maka Kara Amma kazo Nan kayi shiru, Kuma kana Jin abunda suke fad'a"


"Umm... Kinsan...kinsan ya za'a yi yanzu?"
"A'a"
"Nawa ne biscuits d'in?"


"Biscuits na d'ari uku, chocolate na d'ari biyar sannan kasan Kud'in Holandia"


Yace "yanzu dai ga dubu d'aya Zan hukunta su"


"uncle masu laifi daban Mai biya daban?"
"Ke in baza ki karb'a tafi ki bani wuri" karb'a tayi tafiyar ta tana tafiya Shima yayi niyar tafiya Daliyah tace "Uncle Zo man" ya dawo sai kace wata Uwarsa ba musu, Tace "Uncle d'an bani 2k Mana yunwa nake ji"


"Ke baza a bayar d'in ba Kar ki Raina min wayo Mana"
"Toh Uncle Ina wayon yake da har Zan Raina maka shi, kawaii ka bani 2k"
"Daliyah kina trying d'ina dayawa fa, ya ishe ki"


"Oh haka ma zakace? faree Tashi ki raka Ni office na principal"


"A'a haba haba Daliyah tsaya tsaya abun bai Kai ga haka ba, yanzu Zan Baki 2k d'in,Amma Dan Allah na roke ki ki daina tsokanar Nan don dole a kawo karar ki wurina Kuma bazan iya Miki komai ba"


"Uncle ka taimaka ka daina nasihar Nan Haka kawaii ka bani 2k"
Sai ya Mika Mata tace "Saura 46k, mun barka lafiya" Nan suka tashi suka barshi a tsaye Baki a bud'e, Fareedah Tace "Daliyah Wai me ya had'a ki da Uncle Ameer ne yake shakkan ki harHaka?"


"Ke dai bari abin sirri ne, yanzu dai gobe ki fito sa Text books d'in sa"
"Okay Shikenan"


Bayan an Tashi suka Koma gida, Daliyah a cikin kwana d'aya ta canxa a gida duk abubuwan da take yi ta daina, baza tayi wa Yan gida ba Amma mutanen waje sai abinda ya karu.


*Washe gari*


Fareedah ta kawo text books d'in Daliyah ta Kai Masa yayi murna sosai, suna tsaye shi da Daliyah sai ya ga giftawar wasu student Mata su hud'u har Manta jiki yayi, Daliyah tace "Uncle Yadai?"


"Daliyah kin San wanchan yarinyar?"
Da Daliyah ta duba sai taga ai Aunty Khadee Ce murmushin gefen baki tayi tace "Uncle Aunty Khadee Kenan ai unguwar mu d'aya"


Ya matso kusa da ita yace "Dan Allah dai? dagaske kike?"
"Eh man Uncle makwafciyar mu ce mun Zama family d'aya shiyasa ma muke kiranta da Aunty Khadee"


"Yauwa komai yazo da sauki, Dan Allah ki had'a Ni da ita"
"Uncle da ake haka fa, yanzu abinda zakayi shine ka kawo 5k anjima naje na Mata sayayya na Kai mata"


"Hakan ma yayi" ya Ciro ya bata, sannan yace "Dan Allah duk yanda ake ciki ki sanar dani"
"Toh Uncle no case, ka kwantar da hankalin ka kamar kana jirgin sama Mai ya Kare"


"Kamarya Daliyah? Me kike nufi da hakan?"
"Uncle Ina nufin in dai Aunty Khadee ce ka samu"
"Amma Kuma meyasa naji kince ina jirgin sama Mai ya Kare? in fa Mai ya Kare akwai tashin sense fa kenan"


"No no haba uncle, yanzu dai kaga an kusa Tashi bari na Koma class"
"Ok to Shikenan sai na jiki"
"Uhmmn"


Daliyah na barin wurin sosai take dariya, har rike cikin ta take tsabagen mugunta, bayan an tashi ta Sanarwa Fareedah sannan ta bata kyautar kud'in, Fareedah Tace "Meyasa kike karb'an Kud'in sa tunda ba amfani zakiyi dashi ba?"


"Mugunta, kema kinsan nafi karfin 5k mema zanyi dasu, Daddy Yana Mana duk wani Abun da muke bukata"
"Hmm Daliyah Kenan baki da dama wallahi Allah ya shirya ki"
"Ameen, Kinga an buga kararrawa mu fita kawaii."


Suna fita ko wacce ta Shiga motar su.


Kamar kullun sunyi shirya tsaf don zuwa islamiya.


Uncle Ameer kullum Daliyah cikin karb'an kud'insa take Kuma idan ta karba fareedah take bawa kud'in.


Yau suke Rubuta Junior WAEC d'insu, bayan sun Gama Granny Tace "ya kamata mu je hutu kauye da yaran Nan, an kwana biyu bamu jeba"


Daddy yace "haka ne Mama, ki tafi dasu duka ko hankalin mu ya kwanta na kwana biyu"
Mama Tace "Ai da Twins kawaii Zan tafi sauran Kuma sai wani lokacin"


Mummy tace "Yauwa Mama amma ace a tafi dasu duka bakyanan ba yaran kad'aici sai yamin yawa"


Daddy yace "ai Ina tare dake"
"Alhaji Kai da idan ka fita sai dare? A'a wallahi"
"Hmm to uwar 'ya 'ya an bar Miki su, Ni dama Daliyah ce matsalata a gidan Nan, duk da yanzu Naga ta Fara Hankali, mama Dan Allah idan kunje a Rika Kai su gona"


Daliyah tace "haba daddy gona Kuma?" Cikin muryar shagwab'a
"Eh Liyah gona" Yana zazzaro Mata Ido, "ai hakan ne zai sa kuyi laushi"
"Manta da Daddyn ku Liyah Ina Nan ba Mai Kai ku gona"
Daddy yace "Mama Ya kamata ki rage Soyayyar Nan Haka"
"Haba Hafeez in ban so su ba wa Zan so su kad'ai bake gani naji dad'i sabida sun maye min gurbin Sarah da Sairah"


Yaran duk suna kallon Granny don tunda suke basu tab'a Jin ance Granny tana da wasu yaran ba, su dai sun San Daddy shine Mahaifin su Granny Kuma mahaifiyar sa, Kuma baida kani ko kanwa, Amma Kuma waye Sarah da Sairah?


Uwani Tace "Granny waye su Kuma?"


Granny shiru tayi ta rasa me zata ce Mata, don itace ta Hana Daddy fad'a musu cewar ba mummy bace ta haife su ganin irin Abubuwan da Daliyah keyi zata iya ba su matsala ko kuma ma ta Raina ta, Mummy ganin Granny ta rasa abin fad'a yasa tayi saurin cewa "Sarah da Sairah Kannen daddyn ku ne Amma Allah ya musu rasuwa tun Kan a haife ku"


Daniyah tace "Allah sarki, Rashin lafiya sukayi ne?"


Daddy yace "A'a accident sukayi motace ta buge su"


Yusuf yace "Daddy Suma d'in twins ne?"
"Eh twins ne, ai Daliyah da Daniyah kamannin su d'aya da auntys d'in ku"


Daliyah Tace "Allah sarki Amma Zan so ganin su"


Granny tace "Ai akwai hotunan su tun suna yara, bari na d'auko muku"
Nan ta Tashi ta Shiga d'akin ta ta d'auko musu tunda ta shi Babu Wanda ya sake magana a gun, har sai da ta dawo tana rike da photo album d'in su, Nan fa kowa ya zauna kusa da Granny suna kallo tana Basu Labarin yadda Rayuwar su ta kasance, Amma Bata Sanar dasu cewar Sairah Ce mahaifiyar su ba sannan bata Sanar dasu dalilin mutuwar su ba, a Ranar zancen Sairah da Sarah a ka wuni yi.


Daliyah sai kallon hoton take Tace "Look Daniyah ki duba kiga yanda muke Kama dasu kamar an tsaga Kara"


Daliyah Tace "Wallahi Nima abin Yana bani mamaki idan fa akace min Mune aciki wallahi bazan Mu sa ba"




Hafeez yace "Nifa har yanzu gani nake kamar Kune a ciki, don babu Wanda zaice ba ku bane ba, ki duba fa kikaga har murmushin ku ma iri d'aya"


Uwani Tace "Allah Mai iko, Allah yasa dai basuyi rashin ji irin na Twins ba"


Granny Tace "ai yadda kikaga kamin nin su haka halin su, Amma Sairah da Sarah har suka Koma ga mahallicin su suna kaunar junar su ba kaman Su ba"


Daliyah Tace "Granny wa ya fad'a Miki? Ina son Yar Uwata sosai fa Kuma ita ma tana Sona"


Daniyah Tace "Hakane kam, Ina sonta sosai"


Murmushin manya tayi sannan tace "Duk da hakan Bai Kai irin soyayyar da Suke wa junan su ba don in dai sun San zasuyi abin da zai sa a musu duka to baza suyi ba sabida sun San ba Akan mutum d'aya zai tsaya ba, Amma ke Daliyah da gangan ma zakiyi don Yar uwarki Taji zafi"


Daliyah Tace "Wallahi Granny na daina yaushe Rabon ki da kiga Daddy Yana Bina da bulala?"


Daddy yace "Aww watau kina sane kike rashin Jin ko?"
"Ah ah fa daddy ai Hira ake yi shiyasa na Ce hakan" tana tsotsa keya.


Mummy tace "Yarinya sai shegen surutu ga tsoro sai kace farar kura"


Duk sukayi dariya, suka ci gaba da hirar su, Daliyah da Daniyah sukayi ta rokon Granny ta basu hoton Sairah da Sarah da kyar Granny ta basu ganin sun dage, ta bawa ko wacce d'aya.




A yaune sukayi Shirin zuwa kauye Daliyah da Daniyah sunyi kuka sosai don zasuyi kewar gida gashi Daddy yace sai sunyi wata biyu zasu dawo gashi kauye fa akace ko ya Rayuwar su zata kasance a kauyen???🤔




*RAYUWAR DALIYAH DA DANIYAH A KAUYE*


Bayan sun Isa kauye, gidan Kakan su, sun sauka ne a gidan Mahaifin Daddyn su, Yayi murnar ganin su don Rabon shi dasu tun suna Yan shekara biyu a lokacin da Daddy ya Auri Mummyn Su.


Bayan sunci abinci sunyi wanka sun huta, Kakan su yace "Kaai yaran Nan Nifa bazan iya Kiran sunayen ku ba suna sai kace sunan Yan lahira"
Duk sukayi dariya sai ya d'aura da "Zan fad'a muku dokokin kauyen Nan tunda kunga Ku baki ne, Abu na farko da nake so ku sani shine Kar ku yarda a ganku da saurayi"


Granny tayi dariya tace "Amma dokan Nan naka ne ko?"


"A'a ba Wasa nake ba, bayan barin ki garin Nan aka muka Shiga tashin hankali sama da shekaru goma"


Granny Tace"Subhannallah wani irin tashin hankali kuma?"


Kaka yace "Me Kuma sub.... Sub me ma kikace?"


Duk suka Fara dariya Granny Tace "Yi hakuri Ina Jin ka"


"Sarkin garin Nan yasa wani doka, idan yarima bai samu budurwa ba bazaiyi aure ba, ma'ana wacce Bata San d'a na miji ba, idan kuma baiyi aure ba Babu Wanda ya Isa ya yi aure a garin Nan shiyasa yace idan aka ga saurayi da budurwa a Kai su fada za a kashe su ta Hanyar jefin su da dutse har sai sun mutu"


Kallon kallon Daliyah suka farayi wa juna ita da Daniyah.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


*Mu had'u a page na gaba*


*MILHAT CE* YAR TERAWA


*PLEASE SHARE* *AND* *COMMENT*


✨✨ *DALIYAH* ✨✨
*DA*
✨✨ *DANIYAH* ✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_*(A Sympetic,Love and Funny Story)*_




```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```




*Daga Marubuciyar*✍🏻


*MATAR AURENAH*
*SAIRA DA SARAH*
*AND NOW*
*DALIYAH DA DANIYAH*
_(Cigaban Sairah da sarah)_


*DALIYAH* da *DANIYAH* , ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya, tausayi,fad'akarwa, nishad'antarwa gami da ilmantarwa.
```


*Note_* ```bamu yarda wani ko wata su juya Mana labariba tare da izinin mu ba.```


Ya Allah Ina rokon ka da ka bani ikon gama Littafin Nan kamar yadda na ra.Ameen


Labarin *Daliyah* da *Daniyah* k'ageggen labarine ban kirkirin Labarin Nan don cin zarafin kowa ba.Allah ubangiji ya datar da mu.
Ameen....


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu (Milhaat)*✍🏻✍🏻


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.
🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


*BISMILLAIR RAHMANIR RAHIM*


*PAGE* 4️⃣0️⃣↪️5️⃣0️⃣


```PREVIOUSLY```
"Sarkin garin Nan yasa wani doka, idan yarima bai samu budurwa ba bazaiyi aure ba, ma'ana wacce Bata San d'a na miji ba, idan kuma baiyi aure ba Babu Wanda ya Isa ya yi aure a garin Nan shiyasa yace idan aka ga saurayi da budurwa a Kai su fada za a kashe su ta Hanyar jefin su da dutse har sai sun mutu"


Kallon kallon Daliyah suka farayi wa juna ita da Daniyah.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Bari mu leka gidan Sarki muga wace wainar ake tauyawa.


Gidan sarkin ya had'u gashi da girma ko ta Ina a cikin harabar gidan ansa flowers ta ko Ina hakan shi ya Kara wa gidan kyau gidan ta tsaru iya tsaruwa, Bayiin gidan Sarki kuwa Kaya iri d'aya ne a jikin su maza Riga fari da wando Baki, matan Kuma farin Riga da skirt iya gwiwa, sannan kitson kansa duk iri d'aya Calabar style.


Wasu bayin na gani suna tsaye mace da na miji suna rungume da juna a wani lungu da ba kasafai ake bin gun ba, hirar su suke yi irin na Masoya Yana fad'in "Na gaji da Zama haka yanzu shekaru biyar Kenan muke Soyayya dake gashi na shirya auren ki Amma abun bazaiyu ba"


"Kai dai bari na rasa wani irin azzalumin Sarki muke dashi Mai son Kan sa"


Sai yace "Abun bautan mu ne kad'ai zai taimaka Mana"


Motsi sukaji a bayan su, a razane ya sake ta Nan da Nan zufa ya keto Masa Yana rarraba ido jikin sa na karkarwa, wata Yar budurwa na gani ita ma da irin shigar su tana ganin su ta Shiga Yar fa hannu tana fad'in "Abomination, me Zan gani haka?

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads