Header Ads
Showing 3001 words to 6000 words out of 66367 words

Chapter 2 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

rashin ji da tsokana.


*NEXT DAY*


Yau Uwani ta Tashi da zazzab'i hakan yasa momy Tace ta zauna a gida, Daniyah da Daliyah ne zaune a bayan motar, Daniyah tana bata labarin Film d'in da ta kalla jiya, Amma Sam Hankalin Daliyah baya tare da ita da ta lura da hakan tace "Sis me kike Dubawa ne haka? Naga Kinyi serious"


"Kedai bari sis, na Manta muna da test banyi karatu ba, sai d'azu na tuna abiyasa nake reviewing"


"Haba reviewing Yanzu b'ata lokacin ki kawai kike, gara dai ki hakura"


"That reminds me, Daniyah ki Shiga kawaii kimin test d'in"
Zaro ido Daniyah tayi, tace "Test Kuma, Amma Wasa kike ko?"
"Wasa kuma Kinga alamun hakan a fuska ta?"


Kallonta tayi tukunna tace "Daliyah hakan fa Malpractice ne, bai kamata ba, in aka Kama mu Kuma fa?"


"Come on Daniyah Babu Wanda zai gane kin manta cewar muna kama"?


Shiru Daniyah tayi tana kallon ta, Daliyah Tace "Okay Shikenan Kar kiyi dama lura dake Burin ki shine su Daddy suka fushi Dani" Rai a b'ace, a dai dai lokacin yayi parking cikin sauri Daliyah ta fita ta bar wurin, da gudu Daniyah ta bi bayan ta tana Kiran sunan ta, Amma Daliyah Bata saurare ta ba, Saida ta Sha gaban ta, Tace "Haba Daliyah Wai fushi kike Dani?"


"Auu tambayata ma kike? Ki haska ki gani man, Kila Zaki samu amsar tambar ki"


"Okay fine, Zan Miki test d'in" cikin murya Mai sanyi, tsalle Daliyah tayi, ta rungumi Daniyah sannan ta sumbace ta a kuncin ta Tace "Shiyasa nake kaunar ki, Yanzu Zan Shiga class d'in ku after break sai muyi switched over"
Kai kawai Daniyah ta d'aga Mata kai, jiki a sanyaye ta Shiga a Jin Bata d'au lokaci ba ta Gama, ta Tashi tayi submitting, uncle Ameer yace "Abun mamaki Daliyah , ko da yake nasan Baki amsa komai ba"


Murmushi kawai ta Masa, duba paper yayi yaga duk amsoshin dai dai ne, ya ce "Bana a tab'a, kya iya tafiya" sai ta fita.


Bangaren Daliyah Kuma, Aunty Ameeah na musu darasi ga mamakin ta tunda ta Fara Daniyah Bata ama tambaya ko d'aya ba, hakan yasa ta sa ta Tashi ta Mata tambaya, Daliyah a ranta Tace "Ohh Daniyah gashi yanzu bazan iya amsa tambayar ba" da bara ce tazo Mata, sai ta rike cikin ta tace "Wayyo cikina" ta rike da hannu biyu, da sauri Aunty Maryam ta Kara sa sit d'in Daniyah Tace "Me ta same ki?"
"Aunty cikina, Dan Allah Zanje naga school Nurse"
"Okay jeki Allah ya sauwaka"
"Amiin" sai ta fita, fitar ta ke da wuya ta tsinkayo muryar Sabir yace "Daliyah me kikeyi a ajin su Daniyah?" D'an yatsar ta tasa a bakin ta allamun yayi Shiru, Aunty Maryam taji abinda Sabir yace, da sauri ta fito Tace "Sabir wace ce wannan?"


"Aunty ai Daliyah ce daga jakar ta da headband d'inta na gane ta, Nata Duk jaa ne na Daniyah Kuma duk pink ne"


"Okay Daliyah wuce Muje principal office, Kai Kuma Sabir ka Koma ajin"


"Toh Aunty"
Sai yayi tafiyar sa
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Mu Had'u a page na gaba


*Milhaat ce* 🥰 YAR TERAWA
✨✨ *DALIYAH* ✨✨
*DA*
✨✨ *DANIYAH* ✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_*(A Sympetic,Love and Funny Story)*_




```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```




*Daga Marubuciyar*✍🏻


*MATAR AURENAH*
*SAIRA DA SARAH*
*AND NOW*
*DALIYAH DA DANIYAH*
_(Cigaban Sairah da sarah)_


*DALIYAH* da *DANIYAH* , ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya, tausayi,fad'akarwa, nishad'antarwa gami da ilmantarwa.
```


*Note_* ```bamu yarda wani ko wata su juya Mana labariba tare da izinin mu ba.```


Ya Allah Ina rokon ka da ka bani ikon gama Littafin Nan kamar yadda na ra.Ameen


Labarin *Daliyah* da *Daniyah* k'ageggen labarine ban kirkirin Labarin Nan don cin zarafin kowa ba.Allah ubangiji ya datar da mu.
Ameen....


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu (Milhaat)*✍🏻✍🏻


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.
🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


*BISMILLAIR RAHMANIR RAHIM*


*PAGE* 2️⃣0️⃣↪️3️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
"Aunty ai Daliyah ce daga jakar ta da headband d'inta na gane ta, Nata Duk jaa ne na Daniyah Kuma duk pink ne"


"Okay Daliyah wuce Muje principal office, Kai Kuma Sabir ka Koma ajin"


"Toh Aunty"
Sai yayi tafiyar sa
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫


Aunty Maryam ta Shiga class d'in su Daliyah ta Sanarwa Uncle Ameer, Nan aka tura su Headmaster office, Yana ganin su ya cire tabarau d'in sa sai dai ya Kare musu kallo sosai sannan yace "Daliyah Hafeez and Daniyah Hafeez, yau ma kune a office d'ina, Mr Ameer nifa yaran Nan tsoro suke bani bazan iya hukunta su ba, kawaii ku Kira iyayen su"


Aunty Maryam tace "Gaskiya ne sir gara haka if not ana tab'a su sai a samu matsala"


Uncle Ameer yace "Kune fa kuke sa yaran Nan suke abinda suka ga Dama, Ni dukan ta nake ba ruwana" sai ya kara kallo su cikin tsawa yace "Kaaai cikin ku waye Daliyah?"


Daniyah na Nuna Daliyah, Daliyah ita ma na nuna Daniyah a tare suka ce "Uncle itace, itace wannan" suna Nuna junan su da Yan yatsa, Nan da Nan Uncle Ameer ya rike ce, a ransa yace "Wannan wani irin kama ne haka kamar ta b'aci hatta muryan su iri d'aya"


Muryar Aunty Maryam ne ya dawo dashi cikin tunanin da ya lula ji yayi Tace "Daniyah ce mai Pink headband Daliyah Kuma Red"


Uncle Ameer yace "Wow Taya Kika gane su?"
Murmushin gefen baki tayi sannan tace "Students d'ina ne dole na gane su"


Headmaster yace "Nice Of you hakan yayi Miss Maryam"


Daliyah ta kyalkyale da dariya har da tafi, su Kuma mamaki ne ya Kama su ko wanne da irin abin da zuciyar sa ke saka Masa, Headmaster ganin Dariyar tayi yawa yace "You are very stupid, Stupid girl why are you laughing like that? Are you in sane?"


Cikin dariya Tace "Sorry sir, Aunty Maryam ta Raina muku Hankali" kallon ta suka Shiga you, sai Uncle Ameer yace "What do you mean?"
Sai Tace "Sir, d'azu ne fa Sabir ya fad'a Mata kallan Jaka da headband d'inmu ita Kuma tazo Nan tana prouding"


Aunty Maryam ji tayi ranta ya b'aci yanda take Ji yanzu da za a barta wallahi sai ta karya ta, Headmaster murmushin manya yayi yace "Allah shi kyauta" Daliyah Tace "Ameen."


Uncle yace "Andai ji kunya"
Hararar sa tayi ta fice daga office d'in, Headmaster ya Kira Daddy ya Sanar dashi Daddy ya Masa godiya, sai ya Kira Uncle Bashir driver d'insu yazo Kai su gida, sannan ya Kira Mummy ya Sanar da ita, Tace "Alhaji please kayi hakuri yaran Nan fa yarinta ce ta musu yawa"


"Yarinta yarinta fa kikace yaran Nan ne Zaki cewa yara da a kauye suke da an musu Aure"


Murmushi tayi sannan tace "Ban da Kai da abunka alhaji ai Nan ba Kauye bane Dan Allah ka yayyafawa zuciyar ka ruwan sanyi"


"Mata Mata, kaiii ba Mai Shiga tsakanin d'a da uwa ke yanzu ba Kya ganin laifin su ko? anyways anjima Zan biyo jirgin karfe hud'u"


"Ahhh Alhaji na zaci tafiyar ta sati d'aya ce"
"Eh Amma na fasa idan ban Zo na gyarawa yaran Nan Zama ba Hankali na bazai kwanta ba"


"Uhmnn Alhaji kenan, sai ka dawo d'in Allah ya tsare ya kiyaye"


"Ameen ya Allah,Dan Allah a dafa min favorite food d'ina"
"To alhaji Kai d'in ne favourites d'inka dayawa wanne daga ciki?"


"Tuwo man, tuwo miyar kuka, Kar a sa manja please"
Dariya tayi tace "Oh mutum ba bahaushe ba Amma ya Koma cin abincin su"
"Eh Mana yafi d'adi ne"
"To Shikenan Alhaji yadda kake so haka za'ayi"
"Yauwa Mace ta gari shiyasa nake Kara Kaunar ki, ke da kishiya sai a aljanna" murmushi tayi tace"A'a Alhaji Kar kashafa min Zuma a Baki ka Hana Ni lashewa"
"Kar ki damu Zan taya ki lashewa" duk su biyun sukayi dariya.


Nan sukayi ta hirar su, suna cikin wayar ne Daliyah suka shigo, Kai tsaye suka nufi d'akin Granny, Granny na ganin su, tace "Ahh Me Kuma kuke yi a gida? Lafiya na ga Kun dawo yau da wuri?"


Daliyah Tace "Granny ba daddy bane ba" cikin muryar kuka, "me Daddy yayi?" Nan ta fad'a Mata dalilin dawowar su, Granny tace "Amma Kun San ba ku kyauta bako? Wannan karon bazan goyi bayan ku ba,sabida Haka ku Tashi KU bani wuri"


Jiki ba Karfi suka nufi d'akin mummy, mummy na ganin su ta katse wayar Nan ta Fara musu fad'a hakuri suka Shiga bata suna Kuka don yau sun san in Daddy ya dawo kashin su ya bushe, da sauki ma tunda baya gari.


Mummy Tace "Gashi kunsa Daddyn ku zai baro aikin sa ya dawo"
A tare sukace "innalillahi mun Shiga uku Dan Allah mummy ki bashi hakuri wallahi wallahi baza mu sake ba" cikin muryar kuka.


Mummy Tace "Kar ki damu bazan bari ya tab'a ku ba, yanzu je ku cire uniform d'in ku kuzo ku Taya Ni aiki a kitchen" suka amsa da "Toh"


Suna Shiga suka cire uniform Basu b'ata lokaci ba suka fito, suka tarar da mummy na kitchen, Daniyah ta Fara taya ta, Daliyah Kuma ta Shiga d'akin daddy ta gyara sannan ta gyara na mummy ta gyara Gidan tsaf a tare suka Gama aikin, Mummy tace "Twins d'ina sun girma irin aiki haka yau ba a yi complain ba" muryar Granny suka ji Tace "tsaya Nan siyasa ce, sabida sun San sun Basu da Gaskiya"


Mummy tayi dariya tace "Haba Mama, Twins Wai haka?" Murmushi kawaii sukayi, Tace "maganar Mama Gaskiya ce Kenan"


Sallamar su Uwani suka ji, cikin girmamawa suka gaida Mama da Mummy, Uwani Tace "Daniyah me ya faru kuka dawo closing hour baiyi ba?"


"Wallahi aunty Khadee akasi aka samu"
"Wani Abun Kaku yi ko?"


Daliyah Tace "Haba Aunty Khadee tsakani da Allah ba Kya kyauta min Daniyah kawaii Kika gani? ko Kuma ita kad'ai ce baki gani a school d'in ba haba Dan Allah" dukkan su mamaki suke, Uwani Kuma bud'e Baki tayi tana kallon ta sannan Tace "Yau wazai mutu? Daliyah ta kirani da aunty"
Murmushi Daliyah tayi Tace "Aunty Khadee Kenan addu'ar da kuke min ne Allah ya amsa so ki daina mamaki"


Granny Tace "Ahh Ahh daai mamaki Dole Liyah Babu Wanda baiyi mamakin hakan ba hatta su Yusuf, ko ba haka ba Mijina?"


Yusuf yace "haka ne"


Mummy Tace "duk dai ba wannan maza kuje ku cire uniform,kuyi sallah kuzo ku ci abinci Kan lokacin islamiya yayi."


Duk suka Tashi granny Tace "Nima bari nayi sallah naji sun shiga"
Mummy tace "a Mana addu'a"
Ta amsa da "Insha Allah"


Bayan sunyi yadda mummy Tace sannan suka fita don zuwa islamiya, suna tsaye a jikin mota suna jiran Uncle Bash sai ga shigowar motan Daddy, kirjin su ne ya hau duka uku uku, motar na parking duk suka gaishe shi, wani irin kallo yake wa Daniyah da daliyah sai da suka tsorata, Kai kawaii ya kad'a yace "Allah ya shirya" yayi wucewar sa, Bayan ya wuce Daniyah tace "Liyah Ina ga mu hakura da zuwa islamiyar Nan Muje mu bawa Daddy hakuri"
Daliyah Tace "Baki ga yadda yake kallo mu ba har yanzu bai huce ba, yasin in muka Shiga Gidan Nan kashin mu ya bushe"


Uwani Tace "Gaskiya ku bari sai mun dawo Kan mummy ta rarrashe shi, kila ya sassauta muku"
A tare sukace "Hakan ma Yayi Aunty Khadee"


Hafeez yace "ganan ma Uncle Bash d'in"


Uncle Bash yace "emmata da samari meeting ake yi ne Banda ni?"
Daliyah tace "Uncle Kai dai bari wallahi Sabir ne, Kuma wallahi sai nayi maganin sa dani yake zancen" ta karasa maganar tana wani iriyar murmushi Wanda ita kad'ai tasan dalilin yin hakan.


"Toh Daliyah sarauniyar fad'a me Kuma ya Miki?"
Cikin zolaya, Tace "Kaidai mantar kawaii"


Hannu ya d'aga alamun ko a jikisa, yace "ku Shiga mu tafi ko, Kar Liyah tace na sa an Zane ku don ita kowa Mai laifine a gunta"
Nan sukayi dariya suka shige Motar.


Bayan sun taso daga islamiya Bayan sallar Isha Daddy ya sa Hafeez ya kirawo su, suna zuwa suka zube a kasa Kai a kasa kamar munafukai, yace "Yanzu ku dai kullum sai an kawo karar ku? Ku duba dai ku gani Hafeez da Yusuf Kannen ku Ne Amma ba a tab'a kawo karar su ba sai ku, Dan Allah ku fad'a min ya Zanyi da ku? me kuke so nayi Muku eh? Laifin me nayi da nayi deserving haka?" Idon Sa yayi jaa jawur.


A tare sukace "Daddy Dan Allah kayi hakuri wallahi baza mu sake ba"


"Sau nawa kuke fad'in haka Amma sai abinda ya karu, tukunna ma waya ba da shawarar yin hakan"?


Shiru Babu Wanda ya amsa sai kallon junar su suke, Daniyah Tace "Daddy Ni ne"
Daliyah tayi murmushi, Daddy murmushin takaici yayi Tace "Okay Daniyah kema kin Fara min karya ko? Yaushe Kika Fara min karya?"


Cikin muryar kuka tace"Daddy kayi hakuri, Daliyah ce tace zasuyi test Kuma batayi karatu ba shiyasa tace na Mata sabida Kar kuyi fushi da ita"


Daliyah Rai a b'ace tace"why did you tell them? Meyasa zaki fad'a musu? Haka mukayi dake?"


Cikin tsawa Daddy yace "yimin shiru munafuka, in kikayi trying d'ina sai in tattaka ki na karya ki"


Mummy Tace "Haba yallab'ai take it easy Mana"
"Dole kice na bi a Hankali, don bake ake zuwa a samu in suka yi b'arna ba"
Daniyah Tace "Daddy Dan Allah kayi hakuri"


Sai yace "Goben Nan Zan Kai ku kauye gun kakan ku, ya nema muku miji kuyi Aure na gaji bazan iya tolerating non sense d'inku ba"


A tare suka sa ihu "Wayyo Allah daddy Aure Kuma Dan Allah daddy kayi hakuri baza mu sake ba"


"Toh naji baza ku sake ba, Amma dole na canza muku school"
Daniyah Tace "Daddy please Kar ka raba mu da Yar da Uwata, baza mu sake ba"


Mama naji duk abinda suke, tana saukowa da ga steps Tace "Haba Hafeez sai kace fir'auna Allah ma muna Masa laifi Kuma ya yafe Mana kayi hakuri haka Mana"


"Mama Amma kina ganin abubuwan da suke yi suna kyauta wa Kenan?"


"Nasan basu kyauta ba, Amma yanzu kayi hakuri, idan suka sake wani Abun makamancin hakan Ni da kaina Zan kaisu kauyen a aurar dasu"


Babu yanda ya iya dole ya hakura, Amma yaso da ya chanza musu makaranta.
Yace "Tashi ku kuje ku kwanta"
A tare suke ce "Mun gode daddy, sai da safen mu Mummy"


"Yauwa mu kwana Lafiya"


*Washe gari*
Class work Uncle Ameer ya bawa su Daliyah, sai yaga wucewar Aunty Maryam, tasha matsastsun Kaya d'inkin Atamfa ce skirt da Riga, gashi tasa wata figyaggiyar gyalle Wanda bai rufe mazaunin ta ba,sai lashe Baki kamar maye yake, a ransa yace "Kamar ban d'aki zata bari na bi bayanta" ya Tashi ya fita, Daliyah Dama ta dad'e tana Jin fitsari tasan ba barinta zaiyi ba shiyasa ba ta tambaya ba, sai tayi amfani da wannan damar ta fita, Toilet na student ta nufa tana gama fitsarin ta fita a hanyar ta na komawa aji, sai ta hango uncle Ameer a kofar toilet na Mata teachers Yana leke, da saurin ta Ta karasa inda yake ya shagala da leken Aunty Maryam Bai ma San da mutum a Bayan sa ba, tab'a shi tayi, wani tsalle yayi kamar zai Tashi sama dariya ta farayi Tace "Uncle Uncle,me kakeyi?"
A tsorace Yace "yi shiru ke me kikeyi anan?" "Haaa ahh Uncle Ina tambayar ka kana tambayata? Kar ka manta Nan Toilet na Mata ne ba na maza ba"


Kan ya amsa Aunty Maryam ta fito Tace "What's going on here? Me ya faru naji Kuna ta surutu"


Daliyah Tace "Aunty, Uncle Ameer ne yake lek...."
Saurin katsera yayi yace "Umm umm dama... Dama....dama"


"Dama me? kayi magana Mana"
"Umm dama.... Dama so nake.... Umm na tamabaye ki ko Zaki ci shawarma, A'a zob'o A'a umm Kunu Zaki Zaki sha?" Yana wage Baki, tsaki taja tace "you're not serious" tayi tafiyar ta.


Zai tafi Daliyah Tace "Uncle ya kamata ka bani wani Abu don nayi shiru"


"Dallah bar Nan ko yanzun Nan na Zane ki"
"Okay na tafi ko? Okay zan tafi Amma daga Nan office na headmaster nayi na Sanar dashi abin da na gani, Kuma ka San hukunci korar ka za'a yi" har ta Fara tafiya yace "Dawo Mana haba Liyah kyakkyawa"
Murmushin mugunta tayi tace "Yauwa ko kaifa"
"Toh Daliyah yanzu ya za'a yi ne?" Yana magana kasa kasa.


Ita ma sai tayi kasa da muryarta Tace "50k kawaii zaka bani, sai nayi shiru da Baki na Babu Wanda Zan fad'a wa maganar"


"Ke Baki da hankali ne? 50k Kud'in albashina ne na wata biyu"
"Ni kuma Ina ruwana 50k kawaii zaka bani"
"Baza a bayar d'in ba"
"Toh ai hikenan" ta Fara tafiya da sauri ya Sha gaban ta, ya zaro kud'i a aljihun sa ya Mika Mata 2k, sai da ta karb'a ta duba da kyau taga 2k tace "Uncle ko dai bakaji da kyau bane 50k fa nace maka"


"Naji naji, dan Allah kiyi hakuri bani da kud'i"
"Uncle ganan kud'i a hannun ka zai Kai kusan duba hamsin d'in"
"Wallahi Kud'in adashe ne, yanzu haka ana Tashi Zan kai wa Mai kud'i Kud'in sa, Gashi text books ya b'ata har uku Kuma ko wanne 15k ne"


Tsosa keya tayi a zuciyar ta Tace "Dankari Ni wallahi ma na Manta mun d'auke Masa text books"
"Ke Banda keta irin naki yanda kike Yar masu kud'i Kuma ina d'an lallab'a salary na ki Zo ki sani a gaba" "Kan ka ake mahaukaci ya fad'a a rijiya yace Ni wanka nake harda soso da sabulu"
Sai ta Fara tafiya Tace "Uncle 2k ka bani saura 48k fa kasa Wannan a ranka, kuma text books d'in Zan kawo maka su gobe Kar ka damu"


"Ke wato Dama Kece kika d'auke min? Lallai yarinyar Nan"
"Jiman Uncle suna na Daliyah ko Kuma kace min Liyah, gobe Zan kawo maka, kawai kazo ka b'ata min lokaci ban Gama test d'ina ba Mtwws"
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
*Mu Had'u a page na gaba*


*MIILHAAT CE* YAR TERAWA
✨✨ *DALIYAH* ✨✨
*DA*
✨✨ *DANIYAH* ✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_*(A Sympetic,Love and Funny Story)*_




```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```




*Daga Marubuciyar*✍🏻


*MATAR AURENAH*
*SAIRA DA SARAH*
*AND NOW*
*DALIYAH DA DANIYAH*
_(Cigaban Sairah da sarah)_


*DALIYAH* da *DANIYAH* , ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya, tausayi,fad'akarwa, nishad'antarwa gami

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads