Showing 42001 words to 45000 words out of 66367 words
Chapter 15 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
a Sa'a"
Suka amsa da ameen ya d'aura da fad'in, "Daga Nan sai aure ko?"
Murmushi tayi tace "Aure Kuma Yaya Sabir?"
"Eh man aure"
"Toh Allah ya kawo na gari"
Ya amsa da ameen.
Rahina tace "Sabir Kai Kuma fa? Kaima auren zakayi ne?"
Murmushi yayi yace "To me zanyi Rahina in ba auren ba"
"Hakan na nufin kana da Wacce zaka aura Kennan?"
"Eh sosai ma"
Wayar sa ya d'auko ya nuna musu hoton Liyah da Khadeeja ta turo Masa.
Maryam kallon hoton kawaii take, ta Rasa abin fad'a sabida ita a ganin ta ta had'u Amma ganin Liyah yasa ta Raina kanta, Murmushi tayi tace "Haba no wonder Ashe shiyasa na kasa d'aukan hankalin ka"
Dariya yayi yace "Meyasa kikace haka?"
"Gani nayi kyakkyawa ce, ga kyau ga diri,Kuma sai Naga kamar su biyu anan"
"Eh Twins ne Daniyah da Daliyah"
Sai Rahina Tace "Amma kin San wannar tafi kyau?"
Tana nuna Daniyah, Maryam ta kure musu Ido Tace "Eh Kinyi gaskiya kamannin su d'aya Amma wannar tafi kyau" sai ta Maida kallon ta ga Sabir Tace "Itace budurwar taka ko?"
"A'a ba ita bace wannan kanwartace Daniyah"
"Ashe na dad'e ina son maso wani Allah ya barku tare"
Ya amsa da "ameen thanks"
Amma a zuciyar sa yace "Anya Nima ba son maso wani nake ba? Anya kuwa Liyah Zata karb'i Soyayya ta kuwa? Ya Allah ka dafa min"
Nan suka cigaba da hirar su.
"Khadeeja ki shirya yau zakiyi bako" Abba ne ke wannar maganar Yana kallon Khadeeja dake zaune a kasa suna kallo, Dukkanin Yan gidan sune zaune su Liyah da sauran su, a nitse Tace "Daddy bako?"
Yace "eh, yazo Neman izinin Neman ki ne a wurina Kuma na bashi sabida haka ki shirya idan Kun dai daita ba b'ata lokaci sai a d'aura"
Kai a kasa tace "to Daddy" sai ya haura sama, kirjinta ne yake duka uku uku, yau ita zatayi bako? Ita dai M.I take so koma wane ne wannan Wallahi sai dai ya hakura."
Liyah Tace "Aunty Khadee ya dai Naga kamar mood dinki ya canza?"
Aniyah Tace "Nima na lura da hakan, ko dai akwai Wanda kike so ne?"
Murmushi kawaii tayi Tace "A'a kawaii dai nayi mamakine abinka da baka Saba ba"
Duk suka yi dariya, Huzaifa yace "Aunty Khadee mu dai ki bari ayi dashi da alama mutumin kirkine shi don na ga zuwan su"
Liyah gyara Zama tayi Tace "Dan Allah dai dagaske ka ganshi?"
"Eh Mana ki tambayi Yusuf kiji ai a lokacin muna tare suka Zo" Liyah Tace "dagaske yake Yusuf?"
"Eh dagaske ne"
Tace "Wow shafa min inji karanto Mana suffar sa"
Yusuf dake ba Mai yawan magana bane ba yace "Ni bazan iya aikin Nan ba Wallahi sai dai in Huzaifa"
Liyah Tace "Huzaifa muna sauraron ka"
Gyaran murya yayi yace "Ai ta kwana gidan sauki, Dogo ne, wankan tarwad'a Yana da dogon hancin da idanu madai daita sannan Yana da saje" Maida kallon sa yayi ga khadija yace "Aunty Khadee Wallahi ki yarda ko da yake nasan idan kin gansa Zaki kyasa"
Mummy da Granny sai dai su kalli wannan su kalli wanchan, Mummy Tace "Dan Allah ku kyale ta haka"
Granny tace "kina Wasa da yaran gidan Nan,Kinga laifin su? Duk sharrin Mai kwalakwalan idon Nan ne Liyah"
Duk suka tunzure da dariya Amma Banda Liyah, Nan aka cigaba da Hira ana dariya, Khadija Kuma duk hankalin ta na gun Wanda zaizo,Daddy yayi d'awainiya da ita tun tuna Yarinya yanzu ya dace ta Masa biyayya dole ma ta koyawa kanta Soyayyar say ba don taso ba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Please comment and share
Milhaat ce
Yar Terawa🥰
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
NOT EDITED🥱
Afwan zaku had'u da errors dayawa.
```PAGE``` 2️⃣1️⃣0️⃣↪️2️⃣2️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
Duk suka tunzure da dariya Amma Banda Liyah, Nan aka cigaba da Hira ana dariya, Khadija Kuma duk hankalin ta na gun Wanda zaizo,Daddy yayi d'awainiya da ita tun tuna Yarinya yanzu ya dace ta Masa biyayya dole ma ta koyawa kanta Soyayyar say ba don taso ba.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
...........bayan sallan Isha huzaifa har d'akin Khadija ya shigo da Sallama ya Shiga sannan yace "Aunty Khadee ana Sallama dake"
Wani rasss taji sannan Tace "Bakon da Daddy ya ce zai Zo ne ko?"
Tab'e Baki yayi yace "I don't know zai iya yiwuwa shi d'in ne"
Tace "Yana ina ne?"
"Yana Parlor Baki"
"Okay Bari na je"
Mayafin ta kawai ta d'auka dama a shirye take tasa Atamfa Holland an Masa d'inkin Riga da skirt yayi dai dai da jikin ta ya Mata kyau dake Khadee irin matan nan ne masu jiki ta kasa Wanda ake Kira da coca cola shape.
Da Sallama ta Shiga parlor ya amsa tarar da mummy tasa an Kai Masa ruwa, fruits da drinks ganin ta yasa ya ajiye cup d'in dake a hannun sa had'e da amsa sallamar ta, a ranta Tace "Ikon Allah yanzu Soyayyar da nake yiwa M.I har ya Kai haka? Ina Jin Muryar wani kamar ya Allah ka taimake ni."
Tunda ta Shiga kanta a kasa ta nemi guri ta zauna tana Wasa da hannunta Tace "Sannu da zuwa ina wuni"
Murmushi yayi yace "Lafiya Lau ya mutanen gida" da sauri ta d'ago kanta Jin Muryar da ta sake ji a Karo na biyu, ga mamakin ta sai taga M.I ne zaune Yana kallon ta Yana Murmushi, Baki a bud'e Tace "K...kkk.....kaaaa...kaaaine?"
Murmushi yayi yace "Eh nine Kinyi mamakin gani na ko?"
Kallon sa kawai take ta kasa magana, a ranta Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un har gizo yake min na Shiga uku"
Yace "Khadija ya naji Kinyi shiru" sai Tace "Dan Allah dagaske ne ko mafarki nake gani nake kamar mafarki nake"
Yar karamar dariya yayi yace "Ba mafarki kike ba Khadija Ni ne dagaske Mr M.I lecturer d'in ku"
"Dagaske ba mafarki nake ba?"
Dariya yayi Sosai yace "Wai meyasa kike mamakin zuwana gidan ku? Khadija na dad'e in dakon Soyayyar a zuciya ta tun ranar da na Fara ganin ki naji na kamu da sonki, tunfa Kuna aji d'aya gashi yanzu Kuna aji uku zaku Shiga hud'u soon kusan four years"
A fili Tace "Alhamdulillah Allah na gode maka ka karb'i addu'a ta a lokacin da banyi tsammani ba"
Kallonta yake cikin rashin fahimta yace "Kamar ya burin ki ya cika"
Shiru tayi don ita ta d'auka a zuciya take maganar Ashe ya fito, Murmushi yayi yace "Kar dai Kema kin dad'e da Sona a zuciyar ki?"
Murmushi kawaii takeyi Kanta a kasa, murmushin Shima yayi yace "Shirun ki ya bani amsar tambaya ta,Amma gaskiya naji dad'i Sosai hakan na nufin na samu karbuwa ko?"
Kai kawai ta d'aga Masa alamun Eh, dariya yayi, Nan ya Fara jaan ta da Hira sai dai Tace Masa eh ko A'a ganin a takure take Yasa yace "Bari na koma gida idan kin Shiga ki gaida gida"
Tace "To gida zaiji" sai yace "Amma kamin Nan ga wayata ki sa min number ki idan na koma gida sai muyi waya ko?"
Murmushi tayi tace "Toh" ta karb'i wayar ta sa masa.
Tun daga wannan ranar suke Shan Soyayyar su ba gani babu ji abin gwanin sha'awa sai Wanda ya gani.
A yaune Khadija, Sageer da Sauran abokanan su suka gama makaranta sai bautar ka sa, Amma Daddy yace Bai yarda taje camp ba gara ayi musu auren Kan ta tafi bautar kasan, haka kuwa akayi aka d'aura auren Khadija da M.I biki yayi biki Yan Uwa da abokan arziki sun halarci bikin an Kuma gama biki lafiya. (Ni ko nace Allah ya bada zaman lafiya sai mun Zo suna💃🏻💃🏻💃🏻).
Ra'ees na Gama bautar kasar sa aka Fara shirye shirye bikin, mahaifiyar sa ta nace Akan sai sun je an musu test a fad'in bakin ta duk yarinyar da tayi jami'a Yar iska ce gara ayi test gudun Kar tasa wa d'an ta kwanjamo.
Ba don yaso ba ya nemi izini gun Mahaifin Rumana sukaje aka d'ebi jinin su, Akan washe gari su Zo su karb'a.
*Washe gari*
Bayan sun koma asibiti, kikita ya nemi su zauna a office d'in sa Bai d'au lokaci ba ya dawo hannun say rike da paper, gyaran murya yayi yace "Results ya fita Kuma duk Negative ne, ma'ana Baku da cutar, Amma akwai matsala"
Gyara Zama Ra'ees yayi yace "Dr wata iriyar matsala Kuma?"
Rumana kirjinta duka yake uku uku, ganin likita yayi shiru Tace "Dr kayi shiru wata matsala muke dashi?"
Iska ya hura a hankali sannan ya ce "am afraid auren ku bazaiyu ba"
Murya na rawa Ra'ees yace "Kamarya? Meyasa kace haka mene ne matsalar?"
"Kai da ita duk genotype d'inku AS ne so kaga auren mu bazaiyu ba idan Kuma kukayi auren zaku haifi Yara masu sickle cell, ma'a zaku haifi yaran da suke da sickler"
A firgice Rumana ta tashi ta Tsaya ta dafe kirjin ta Tace "Na Shiga uku"
Hawaye masu zafi ne suka zubo Mata, Ra'ees Shima mikewa yayi yace "Rumuna please clam down Kar ki tashi hankalin ki kinji?"
Kad'a Kai tayi Tace "Taya za'a yi na kwantar da hankali na kana ji fa yace aure da Kai bazaii...." Kasa Karasa maganar tayi Numfashin ta na kokarin yankewa sai ji nayi daram ta yanke jiki ta fad'i a sume cikin sauri likita da Ra'ees sukayi kanta Ra'ees na Kiran sunan ta Yana d'an bubbaga, da sauri likita ya fita Bai dad'e ba suka shigo tare da nurses guda biyu a Kan Keke suka d'aura ta sai emergency room.
Su Liyah Kuma suna shekarar karshe kullum Sageer d'aure Masa Kai take yi sai dayawa sai ya Rika fad'in "Anya kuwa itace Wacce na fad'a Soyayya da ita?"
Ya shirya tsaf da a yaune zai Fara zuwa gidan su Liyah, already Liyah ta Sanar a gida Daddy ya nemi ya gansa,bayan sun gaisa da Daddy Sageer ya tabbatar Masa da gaske yake Kuma zai turo magabatan sa nan ba dad'e wa ba,Daddy yaji d'adin hakan ya musu fatan Alhairi, bayan fitan Daddy ba da dad'ewa ba Liyah ta shigo da Sallama bayan sun gaisa Tace Masa "Ya kamata mu Shiga kaje ka gaida su Mummy ko?"
Zaro Ido yayi yace "Kaaai su Mummy kikace fa?"
"Eh su mummy akwai matsala ne?"
"A'a kawaii dai ban shirya bane ba"
Murmushi tayi Tace "Ka had'u da Daddy mummy ne zaka tsorata?"
"A'a fa ba tsoro bane ba kawaii dai...?"
"Kawaii me?"
Yar karamar dariya yayi yace "Muje d'in to"
Tace "yauwa ko kaifa"
Murmushi kawai yayi, bayan sun Shiga parlor suka tarar da su Mummy da Granny na zaune suna Hira cikin girmamawa ya gaishe su suka amsa cikin sakin fuska, Granny Tace "Kice yau kin kawo min angona, to inaa goron?"
Dariya yayi yace "Afwan an d'an Samj matsala ne Amma insha Allah next time za'a kawo Miki"
Tace "Toh Allah ya tabbatar da Alhairi"
Ya amsa da "Ameen"
Mummy ta tashi ta shiga d'akin ta, Granny ma haka.
Ruwa ta d'ebo ta mika masa sai suka cigaba da hirar su.
A hankali take saukowa da ga step idon ta na Kan wayarta Murmushi takeyi da alama abinda takeyi na matukar nishad'antar da ita, Sageer ya Kai ruwa bakin sa Kenan ya ga saukowar ta, Ruwan da Ke bakin sa ya kasa had'e wa, sai ji nake siiiiir Yana zub da Ruwan a jikinsa ba tare da ya sani ba, tashi yayi ya tsaya Yana kallon ta, Liyah dake kujerar da ta zauna akai ta bawa Aniyah bayane sai tayi saurin juyo bayan ta gane abin da yake kallon a tsawace tace "Sageer!!!" Har sai da ya tsorata yace "Naa...naaaaa...naaaaam" Yana kokarin Zama, Aniyah Jin tsawa da sunan wanda Liyah ke Kira tayi saurin juyo taga Irfan cikin sauri ta sauko Tace "Laaaah Irfan, Liyah Baki fad'a min Irfan d'inki zai Zo ba"
Sageer yace "Ashe dama ki biyu ne?"
Ya kalli Liyah ya kalli Aniyah, Murmushi tayii Tace "Eh mu biyu ne sunan ta Daniyah Amma and kiranta da Aniyah"
"Ikon Allah Amma baki tab'a fad'a min ba"
Murmushi tayi Tace "Ehh hiran ne fa bai Zo ba"
"Amma kamannin taku tayi yawa muryar ku ma d'aya fa"
Aniyah Tace "Ina wuni Irfan?"
Sake kallon ta yayi a zuciyar sa yace "Irfan? Anya wannan ba itace Wacce nake so ba? Mun Kai almost 2 years bata tab'a cemin Irfan baz idan ban manta ba tun a Havilla"
Muryar Liyah ce ta dawo da shi daga tunanin da ya lula Tace "Tana gaishe ka Kuma ka tsaya kana kallon ta"
"Am sorry ya kike ya gida ya boko?"
Tace "Alhamdulillah ya naka? Naji kunyi graduating har ka na kokarin Zama lawyer Mai zaman kansa, Allah ya tabbatar da Alhairi"
Ya amsa da "Ameen thank you"
Sai ta bar gun, Hira suke Amma Sam ya kasa samun kwanciyar hankali,a hakan har ya tafi gida, a haka ya kwana cikin tunanin abinda ya gani Amma sai ya sawa ransa duk yanda akayi da Aniyah ya fad'a a Soyayya ba Liyah ba sai ya d'auki a niyar gano gaskiya.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ta rasu? Have Dr ya zaka ce min haka dogon Suma tayi Dan Allah kaje ka sake duba ta"
"Am sorry Mr Ra'ees Amma Rumana ta rasu sai dai muyi fatan Allah ya jikan ta"
"Kaaai bakada hankali ne" a tsawace yake maganar "ya Za'a yi yanzun Nan ki Shiga da ita ciki kace min ta mutu bayan ita da kanta ta shigo asibitin Nan, bai Kai mintuna biyar ba" sai ya kwantar da murya yace "Please Dr kace min Wasa kake Rumana Bata mutu ba" ya Karasa maganar cikin kuka, rarrashin sa ya Shiga yi yace "kullu Nafsin za'ikatul Maut every Soul shall test death, Jin cewar jinin ku AS ne shiyasa ta had'iyi zuciyar ta ta mutu tun a wannan lokacin ta mutu, kayi hakuri kaji addu'a zaka Mata" Yana kai Nan ya tafi.
Ra'ees Zama yayi ya rasa abin yi sai aikin kuka yake kamar karamin yaro, waya ya zaro ya Kira mahifin ta cikin kuka ya Sanar dashi komai, sallati Mahaifin ta yayi ya Shiga rarrashin sa da nuna Masa cewar lokacin ta ne yayi ya katse wayar, ya kira umman sa duk jikin ta yayi sanyi don ji take kamar itace silar mutuwar Rumana mahaifiyar Rumana taci kuka Sosai, Mahaifin ta yazo asibitin aka d'auki gawar aka Maida ita gida aka Mata sutura aka kaita gidan ta na gaskiya.
Tsaye yake a jikin motar sa wayar sa ya Kara a kunnen sa yace "Gani a kofar gida"
"Hana dai dagaske?"
"Eh zuwan ba zata na Miki hope kina gida?"
"Eh ina gida" Tace
"okay gani Nan fitowa"
Giftawar Aniyah ya gani yace "Aniyah!!!"
A nitse ta Juyo ganin Wanda yake Mata magana Tace "Na'am Ashe Kaine?"
Murmushin Shima yayi yace "Eh nine sai ki wuce love gaisuwa babu?"
"Am sorry ban lura bane ba"
"Okay ba matsala ya su Mummy?"
"Lafiya lau, Bari naje na Kira maka ita" har zata tafi yace "A'a karki damu ai na kirata"
"Okay to shikenan" zata tafi a Karo na biyu yace "Aniyah d'an tsaya Mana please dan Allah wata Yar tambaya nake so na Miki"
'dan dawo wa tayi da baya had'e da fad'in Allah yasa na sani"
"Dan Allah ki fad'a min gaskiya kece Wacce muka rera waka tare ko?"
D'an shiru tayi Tace "A'a bani bace"
Murmushin gefen baki yayi yace "Sam karya bata Dace da fuskar ki ba, Dan Allah ki fad'a min gaskiya"
"Nace maka bani bace ko" ta yi saurin juyawa don ta Shiga gida, da sauri ya riko hannun ta yace "Please Aniyah ki fad'a min gaskiya Nasan kece, Amma Meyasa kike b'oye min?"
"Jaaar Uba me Zan gani haka?"
Liyah ke maganar Nan tana tsaye a bakin gate tasa hannayen ta biyu a kwankwason ta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
PLEASE COMMENT AND SHARE
MILHAAT CE
YAR TERAWA
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu``` .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
```Story and Written by```
```Fadeelah Yakub (Milhaat)```
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
NOT EDITED🤭
PAGE 2️⃣2️⃣0️⃣↪️2️⃣3️⃣0️⃣
PREVIOUSLY
"Nace maka bani bace ko" ta yi saurin juyawa don ta Shiga gida, da sauri ya riko hannun ta yace "Please Aniyah ki fad'a min gaskiya Nasan kece, Amma Meyasa kike b'oye min?"
"Jaaar Uba me Zan gani haka?"
Liyah ke maganar Nan tana tsaye a bakin gate tasa hannayen ta biyu a kwankwason ta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............cikin sauri Aniyah ta Fizge hannun ta, Tace "Liyah it's not what you're thinking"
Liyah ta Karo so inda suke sai ji nayi tasss tass maruka biyu ta shafa Mata, Aniyah rike kuncin ta tayi Tace "Kika mare Ni?"
"An mare ki"
Liyah ta hau Aniyah da kokuwa har ta kaita kasa tana dukan ta, tana dukan nata Kuma ita kanta tana Jin zafin dukan da take Kai Mata.
Sageer yayi kokarin rabasu Amma ya kasa, Liyah ta kwance wa Aniyah d'an kwalin ta kanta a tsefe jaaan gashin take tsakanin ta da Allah harda ciza leb'e.
A daily dai Nan Daddy ya fito mummy na biye dashi sun nufi parking area, sai ji sukayi ana fad'in "Liyah ki kyale ta Zaki ji Mata ciwo"
Daddy yace "Wai me ke faruwane? Kamar hayaniya nake ji ko?"
"Eh Nima naji"
Yace "Zo Muje mu duba"
Aikuwa suna fita suka ga abin mamaki, Liyah na dukan Aniyah saki kace ta samu jaka, da sauri abba ya nufo gun yayin da mummy ta tsorata ganin jini a hannun Liyah sai Kai Mata naushi take jakan da Ke hannun ta ta Yar da gudu ta Karasa gun har ta Riga Daddy Isa, da karfin ta ta fimciko Liyah yayin da Daddy ya ke kokarin d'aga Aniyah.
Cikin rashin fahimta ta gigicewa Daddy yace "Yau me zan gani haka? Liyah kece kike dukan kanwar ki a bakin titi? A gaban bako?"
Sai ya Maida kallon sa ga Sageer yace "Kana ganin su,suna kokarin kashe kansu baka Shiga tsakanin su ba?"
"Wallahi Abba nayi kokarin rabasu su na kasa"
Daddy yace "Kai ina magana baza ku amsa min ba? Me ya had'u ku fad'a?"
Liyah na huci Tace "Daddy Wallahi sai na kashe ta, idan bata fita daga harkar saurayi na ba,Taya za'a