Header Ads
Showing 57001 words to 60000 words out of 66367 words

Chapter 20 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

cikin tsand'a tazo ta bud'e kofar.
Da sauri ya bi bayan ta, tana kokarin bud'e kofar Amma yaki bud'ewa, ganin ta na wahala yasa hannu don ya tayata Amma Shima ya kasa a tare suka sunkuya don jaan kasar kofar, tsarkan dake wuyan ta sai ya hard'e da aninin rigar sa.




Liyah na Jin karar anyi parking na mota a waje ta leke ganin motar yasa Tace "Good shine" cikin tsand'a tazo ta bud'e kofar.


A tare suka Mike tsaye shi ya sa hannu Yana kokarin cirewa kwasam sukaji an turo kofar ga mamakin su Daddy(Mahifin su liyah) suka gani, zaro Ido sukayi a tare, Daddy shi kansa mamaki yayi ganin su a haka cikin b'acin Rai yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Aniyah me zan gani haka?"


Cikin Rawar murya Tace "Daddy ba abinda kake tunani ba ne wallahi I can explain"
A tsawace yace "Shut up, na Riga na ga komai Aniyah, kin bani mamaki sanda aka kirani na karyata Mai shi Ashe gaskiya ne"


Sageer yace "Daddy wallahi ba...." Ka tse shi yayi da fad'in idan ka sake kirana da Daddy wallahi sai na fasa maka Baki marasa mutunci" Yana Kai Nan ya riko hannun ta ya jaa ta da karfin gaske har sai da tsarkan ya tsinke a jikin rigar sa, suna fita yace "ki Shiga motar ki Kai tsaye gida Zaki wuce ina biye dake"


Jiki a sanyaye ta Shiga motar ta Daddy kuma ya Shiga nashi Yana biye da ita.


Ganin duk sun fita, ta fito daga inda ta b'uya Tace "Yarinya wa ya ce Miki borni gabas take kad'an Kenan daga cikin abubuwan da na shirya Miki."


Tana Kai Nan ta fice da sauri don Kar wani ya ganta, ta dad'e tana tafiya Kan na hango motar ta,( oh wato Liyah ta San Kan tsiya shiyasa ta aje motar ta da nesa to Allah ya shirye ki).


*KAUYE*
Kasantuwar mutuwar Rahila shiyasa ba'a yi hidima ba a sunan abinda ta Haifa duk da hakan dai an d'an yi shaye shaye da ciye ciye a kasa Mata suna Anastasia Amma suna kiran ta da Princess.


Princess ta taso cikin gata, Mahifin ta da kakanin ta sun d'auki Soyayyar duniya suka d'aura Mata yayin da Rose ta d'auki tsanar duniya ta d'aura mata, in prince na kusa har goyon ta take ta rika nuna Mata so kamar zata cinye ta Amma da zaran baya Nan sai ta Rika dukan ta ba dalili, hakan yasa ta tashi cikin tsoron ta.




*BAYAN SHEKARU Takwas*
Rose na ganin farfajiyar gidan sai kaiwa take tana kawo wa a fili Tace "Na rasa wani irin so yake yiwa yarinyar Nan, na samu na juya hankalin Sarki da matar sa Amma shi na kasa, ko dai na shirya naje gun matar Nan da nake Jin Labarin tane? Bari dai naje yanzun Nan ma kuwa" ta shige cikin d'aki ba ta d'au lokaci ba ta fito hannun ta rike da makullin mota driver d'in ta na ganin ta da sauri ya nufe ta da niyar karb'an key d'in hannun ta d'aga Masa Tace "bana bukata yau Ni ka dai zan fita"


Sai yace "But My Princess, prince yace Kar ki Rika fita ke kad'ai"
"Na sani shiyasa nace maka Ni kad'ai zan fita"
Tana kai nan ta nufi parking area, da sauri ta Fizgi motar ta bar gidan.


Wata Mata na gani, farin kyalle ne a jikinta tayi d'aurin kirji ta d'aure kanta da wata Yar karamar farin Dan kwali, idon ta d'aya ta fari ne tass ba alamun baki ko kad'an,zaune take cikin wata Yar karamar bukka, an d'aure wasu fararen kyalle acikin ta it
"Oroko please help me, I hate my sisters daughter, please ki Shiga tsakani na da ita in so samune ki kashe ta"
Rose ke wannan maganar.


Murmushi oroko tayi Tace "Bazan iya wannan ba Amma zan iya sa wa Mahaifin ta tsanar ta a zuciyar sa"
Gyara Zama tayi Tace "Yauwa anzo gidan sauki kimin hakan Ni Kuma na Miki alkawarin baki kud'i masu kauri"


Wata iriyar dariya tayi Tace "Consider it done my princess, me Kuma kike so?"
Ciki i'ina Tace "Kuma Kuma Ina son haihuwa Yanzu kusan shekaru takwas Kenan ban tab'a 'batan wata ba"


"Zan taimaka Miki, Amma ga wannan" wata farin kyalle ta Mika Mata ta d'aura da fad'in "Akwai wani itace aciki karfe Sha biyun dare ki sa a gaban ki zan tura Miki aljani d'aya ya Miki Ciki"


A tsorace Tace "aljani kuma? Why not a Sa'a jikin mijina?"
Dariya tayi Tace "Sabida babu rabo tsakanin ki dashi Kar ki damu baza su cutar dake ba, baza ma kisan anyi ba, zai Rika kusantar ki har zuwa lokacin da Ciki zai Shiga"


Chan kasa ta amsa da "Toh"
Sai ta Mika Mata wata Yar karamar kwalba Tace "ki sa Masa a abinci Yana ci shikenan zai daina Kaunar ta"

Godiya ta Shiga yi mata Kud'i masu uban yawa ta aje Mata sannan ta tashi ta tafi.
Bayan an gama girkin dare a ranar ita da kanta ta shirya abinci a dinning shi kansa yayi mamakin ganin hakan Amma Bai kawo komai a ransa ba, sai da tabbatar ta sa maganin yanda akace Kuma taga yaci hankalin ta ya kwanta, bayan ya gama cin abincin ya sumbaci Princess dake kusa da shi yace "Goodnight My Prince sleep early gobe Monday ko?"
Murmushi tayi Tace "Okay Daddy" ya shige d'aki, suna had'a ido da rose ta wurga Mata wata iriyar harara da sauri ta tashi ta bar gun.




Karfe Sha biyu nayi ta farka tasa wannan itacen da girman sa ya Kai Yar karamar yatsa tana sawa ya shige a saukake kamar an ja shi tana kwanciya bacci Mai nauyi ya d'auke ta.


Wani kyakkyawan saurayi ta gani Yana romancing d'inta har ya Kai ga ya shige jikinta.
Washe gari da ta shi taji jikin ta duk kasala, ban d'aki ta fad'a tayi wanka, tana fitowa ta tarar da prince a zaune a parlor Yana kallon TVC News , sumbatar sa tayi a goshin sa Kan ta zauna ita na ta Shiga kallon.


Princess na gani sanye take da uniform Riga da skirt ne iya gwiwa, rigar navy blue rigan Kuma light blue kanta Kuma tasha kitso cuku an zubo sauran a gaba, kafanta Kuma sanye yake da farin canvas da fararen socks tayi matukar kyau, wata maid na gani biye da ita hannun ta rike yake da jakar ta da alama itace ke kula da ita.


Tana ganin Daddyn ta ta nufe shi da gudu tana Kiran sunan sa, tasa hannun zata rungume shi yayi saurin ture ta har Saida ta Fadi wani Kara tasa Mai Karfi sabida ta buge bayan ta, har sai da ta kasa tashi, da sauri ta Yar da jakan dake hannun ta,ta d'ago ta.


Prince cikin kuka Tace "Daddy good morning"
a tsawace yace "what is good about the morning? Wannan ya Zama shine Karo na farko Kuma na karshe da Zaki sake zuwa inda nake kin ji abinda nace Miki ko?"


Cikin Kuka Tace "Daddy please am sorry na maka laifine ban sani ba"
Tashi yayi sai ji nayi tass "ke don ubanki Ni sa'an kine Zaki Zo kina tambaya ta, ke ki saurare Ni da kyau idan kika sake min magana sai na karya ki" ya Maida kallon sa ga maid d'in yace "Ke ya sunan ki?"
Cikin Rawar murya Tace "Esther"
Yace "whatever ki fita da ita daga Nan ko na had'a dake" da sauri ta d'aga ta chak ta sata a baya ganin baza ta iya tafiya ba, ta d'auko jakan ta suka fice.


Gun driver suka nufa a hankali ta sauke ta sai rarrashin ta take Amma Princess ta nuna abun bai dame ta ba driver d'inta Jin abin da ya same ta hankalin sa yayi matukar tashi sabida duk suna son yarinyar sabida tana girmama na gaba da ita Amma yayi mamakin Jin prince ne ya Mata haka har da Mari shi da baya son komai ya tab'a ta gaskiya Akwai abin duba.


Princess tace "Uncle Mike mu tafi Kar na makara"
Yace "No Princess muje asibiti tukunna"
Tace "No Uncle am okay bugewa ne kawaii zanji sauki"
Ta shige motar ta d'gawa Esther hannun shi Kuma ya jaa motar ya kaita makaranta.




Tun daga wannan ranar princess take ganin abubuwa kala kala na mugunta Wanda prince da matar sa suke Mata Amma dake yarinya ce Mai hakuri bata damu ba gata karama sai wayo.


Rose kuma kullum sai aljanin mijinta ya kawo Mata ziyara kwasam ranar ta tashi da matsanicin zazzabi cikin Rawar jiki prince ya kaita asibiti Ana gwada aka tabbar Masa da Ciki take dashi har na tsawon Watanni hud'u it's kanta tayi mamaki da akace wata hud'u ita da kwata kwata wata d'aya Kenan sa zuwa gun oroko, a ranta Tace "Ko ma dai mene ne bukata ta ta biya."


Prince sai rawan Kai yake da rawan jiki a kanta, Princess ganin tsanar da Mahaifin ta ke Mata yasa idan Yana gida Bata zuwa inda yake in Bata makaranta tana tare da driver da Esther suna Hira ko Kuma taje gun kakanin ta duk da Bata samun sakin fuska a haka ta gwammaci Zama a gun su da irin kyarar da prince yake Mata.




*BAYAN WATA BIYAR*
Rose ta haifi 'ya mace suna Kiran ta da Angel.
Angel tun tana yar shekara uku ta tashi da rashin kunya, raini da rashiin ganin girman ba gaba da ita Daddy da mummy ta kawaii take yiwa biyayya suma d'in sai sunyi dagaske.


*KANO*
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Aniyah Meyasa kikayi haka? gaskiya nayi mamaki da ba don Mahaifin Kune ya fad'a min hakan ba zan karyata ko ma waye ne, haba Aniyah a kirjin Sageer fa ya ganki duk rashin Kunyar Liyah bata tab'a yin hakan ba"


Granny Tace "Hafeez nifa ban yarda ba babu yanda za'a yi Aniyah tayi hakan sabida kowa shaida ne tana da nitsuwa"
Murmushin takaici yayi yace "Ni kaina gani nake kamar mafarki nake Amma da idona na gani so ki daina mamaki don ni da girmana Bazan mata karya ba"


Mummy Tace "Toh Yanzu in ma gaskiya ne in ba gaskiya bace ba idan Liyah taji wannar maganar zargin da take Mata ya tabbata Kenan tsakanin su Kuma sai yanda Allah yayi"


Muryar Liyah suka jiyo Tace "Mummy naji komai" a hankali take tafiya har ta Karasa ta zauna a Kan gujerar dake fuskantar Aniyah dake durkushe a kasa sai aikin kuka take.


Liyah tace "Mummy an dad'e da fad'a muku Aniyah Munafuka ce yau kam Kun tabbatar da hakan ko?"
Granny Tace "ke Kar ki Mana rashin kunya anan kina jina ko?"
Sai ta Maida kallon ta ga Daddy Tace "Hafeez kamata ai ka saurari Yarinya kuje me zatace baku barta tace komai ba"


Daddy yace "Mama me zatace bayan abinda na gani" tashi yayi hade da fad'in "ni kaina sarawa yake Bari naje nasha magani na d'an kwanta don na tabbata jini na ya hau" ya haura sama mummy ta ce "Allah ya kyau ta Dole sai an tsananta bincike akai don Ni kaina ban yarda Aniyah ta aikata abinda ake zargin ta dashi ba." Itama ta bi bayan ta tashi Granny tayi ta d'ago Aniyah Tace "Ki daina kuka kinji Allah ya tonawa Wanda ya Miki hakan yasa Shima ya samu dai dai dashi Zo Muje d'akina na Baki panadol kinyi kuka sosai Kanki zaiiyi ciwo" d'akin Granny suka haura suka barta ita kad'ai a zaune sai Murmushi take ganin zaman ba zai mata komai ba ta shige d'aki.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Mu had'u a page na gaba
Please share and Comments


Masu amfani da Wattpad please kuyi following d'ina, vote and Comment.




Milhaaat ce
Yar Terawa


🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu''' .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_


'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
Follow me on Wattpad
@milhaat🙏🏻


*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Not edited
```PAGE``` 2️⃣8️⃣0️⃣↪️2️⃣9️⃣0️⃣
Granny tayi ta d'ago Aniyah Tace "Ki daina kuka kinji Allah ya tonawa Wanda ya Miki hakan yasa Shima ya samu dai dai dashi Zo Muje d'akina na Baki panadol kinyi kuka sosai Kanki zaiiyi ciwo" d'akin Granny suka haura suka barta ita kad'ai a zaune sai Murmushi take ganin zaman ba zai mata komai ba ta shige d'aki.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............"Fareedah ya kamata ki daina kukan Nan ya Isa haka yau kimanin wata biyu Kenan da rasuwar Mubarak Amma kullum cikin kuka kike, ya kamata ki Sani addu'a yake bukata daga gare ki ba kuka ba"
Cikin kuka tace "Mama Ina Masa addu'a Amma kullum ji nake kamar tafiya yayi, a ranar daren farkon mu ya rasu fa"


"Na sani Fareedah Amma fa ki Sani kukan Nan baida fa'ida Ina so ki cire komai a ranki ki Rika masa addu'a Kuma kin ga ya kamata ki Fara zuwa school don next week zaku Fara exam."


"Mama na yafe bokon bazan iya fahimtar komai ba wallahi"
"Na sani, na sani Fareedah Amma ki Kwantar da hankalinki ki Rika Masa addu'a ki yawaita yin azkar komai zai zo da sauki kinji,Kuma idan kin hakura da karatun ya kike so nayi Kar ki manta irin kudin da aka kashe ya kamata kiji tausayin Mahaifin ki Kar ki zama Mai son Kai"


"Toh shikenan Mama insha Allah zanyi yanda Kika ce, zan yi iya bakin kokarina Amma bazan iya manta Mubarak ba" ta Karasa maganar cikin kuka, Mama ta rarrashe har ta samu tayi bacci.


"Aniyah Ina so ki fad'a min gaskiya tsakanin ki da Allah me ya Kai ki studio na yaron Nan bayan ranar da kunne na naji Mahaifin ku ya hane ku da ganin sa ko da Wasa ne Amma Kuma kinje har ind a yake har ta Kai ta kawo ma Ke Kika Kai Kanki haba Aniyah"


Cikin kuka Tace "Granny wallahi is just a misunderstanding, Granny in fad'a Miki gaskiya Zaki yarda da Ni?"
"Ina sauraron ki"
"Granny Liyah ce na ta nemi alfarma ta Akan naje na roke shi ya cigaba da Soyayya da ita, shine na karb'i number sa na Kira shi na nemi mu had'u, bayan naje gun ne mun gama maganar zan fita sai mukaji an rufe mu ta waje"


"Toh Kuma daddyn ku yace ya rungume ki ya akayi haka?"
"Granny ba haka bane a lokacin da sunkuya zan bud'e kofar ta kafa Shima ya sunkuya shine fa sarka na ya rike aninin sa yana kokarin cirewa ne Daddy ya shigo, Amma nayi mamakin yanda Daddy ya sani"
Murmushi irin nasu na manya tayi Tace "Liyah Kennan wato sharri tayi niyan Miki ko ince ta Miki, Kar ki damu tashi Muje"


Kallon Granny tayi Tace "Ina zamuje?"
"Tashi ki biyo Ni kawaii" ba musu ta bita, suna Isa parlor Granny ta Shiga kwalawa mummy da Daddy da Daddy Kira ba b'ata lokaci suka fito kusan a tare.


Granny Tace "Duk kuzo ku zauna Ina da magana daku"
Mummy da Daddy Akan koshin suka zauna Liyah da Aniyah Kuma aka kasa.


Mummy Tace "Hafeez idan Rai ya b'aci hankali baya gushewa na tambayi Aniyah dalilin zuwan ta gun Yaron Nan me ma yake da suna? Sa.. saa...yauwa Sageer, tana da laifi tun farko Bai kamata taje gun ba tunda ka Hana ta Amma Kuma dake tana tare da shaid'aniya sai ta juya Mata tunani Ni da ku duk Kun San Aniyah na tsoron b'acin ran mutum"




Cikin rashin fahimta Daddy yace "Kamar ya Mama tana tare da shaid'aniya wace ce shaid'aniyar?"
"Yooooo Waye in ba Daliyah ba itace ta shirya komai"
A razane Tace "Granny Ni Kuma?"
A tsawace Tace "Imin shiru Munafukar banza Munafukar wofi Wacce Bata San ciwon kanta ba, Ke don wawanci da rashin sannin ya kamata sai kiyi wa Yar uwar ki sharrii sabida wani Kato Wanda ko sonki baya yi? Liyah kin bani mamaki mahaifiyar ku da Yar Uwarta ba haka suke ba suna Kaunar junar su har suka koma ga mahallicin su"


Mama kuka ce ta kufce Mata sai da tayi Mai isarta sannan ta Kama bakin zanin ta ta share hawaye ta face hancin ta sannan Tace "Sairah da Sarah sun kasance Yan biyu kamar ku, kamar yanda kuke Amma halayyar ku sun banbanta duk da dai nasan Sairah tafi Sarah hakuri Amma hakan Bai sa anji Kan su ba sau dayawa nayi kokarin Shiga tsakanin su sabida akidar da suka say ransu na sai sun Auri miji daya hatta kayan su na Kona don na had'a su fad'a na kasa, Amma ke Liyah bayan mugun ta kina da bakin Hali da son kanki" ta Maida kallon ga Daddy Tace "Hafeez Aniyah laifin ta zuwa studio d'in ne Amma Liyah itace ta shirya komai don ta sa kuyi fushi da Aniyah" Nan ta fad'a musu abinda Aniyah ta fad'a Mata.


Kai Daddy ya girgiza yace "Hakane naso na ga motsin wani sanda na nufi kofan d'akin da suke sannan naso Naga motar Liyah gaba kad'an da studio d'in"
Mummy Tace "Kira layin da aka Kira ka dashi tukunna Kar mu yanke hukunci"


Zaro wayar sa yayi daga aljihu yayi dialing Amma switch off.


Mummy Tace "Maybe an saka a Black list ne Bari na gwada nawa" ta karb'i wayan Liyah tunda mummy ta karb'i wayan ta Fara zaro Ido Nan da Nan zufa ya keto Mata.


Ji nayi mummy Tace "Ikon Allah, Alhaji duba ka gani wannan ai sabon sim da na saya ne na dad'e Ina nema ban gani ba,inaga kamar na fad'a maka ma"


Shiru yayi kad'an da alama Yana kokarin tunowa ne, yace "Eh anyi Haka kin fad'a min hakan na nufin acikin gidan Nan aka kirani" tashi Daddy yayi yace "Liyah!!! Liyah!!" Chan Ciki ta amsa murya na rawa.


Yace "Meyasa Kika d'auke Sim na mummyn ku sannan Kika yi wa Yar uwar ki sharrii?"
Kasa magana tayi tasa kai a kasa, huci yayi yace "sa'an ki d'aya idan na tab'a ki zanjiwa Aniyah ciwo Amma da ba don Haka ba Wallahi Wallahi da sai na lahira yafi ki Jin dad'i, laifin ki biyu kinyi sata sannan kin Zama Munafuka, da zan biyewa zuciya ta da na dad'e da tsine Miki kin bi Duniya"


A tsawace Granny Tace "Kul Kul Kar ka Fara tsinuwa ka dawo cikin hayyacin ka"
Hawaye ne ya gangaro Masa Wanda shi kansa Bai Sani ba yace "Mama yazanyi Meyasa Meyasa a ko da yaushe damuwar da muke samu a gidan Nan Daliyah ce ta Zama

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads