Header Ads
Showing 60001 words to 63000 words out of 66367 words

Chapter 21 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

tamkar annoba a cikin mu"


Mummy Tace "Subhannallahi haba Alhaji Dan Allah Kar kace Haka 'ya Kane fa Kar ka manta bakin iyaye Kuma gashi har kuka kayi hawayen ka masiface a gare su Dan Allah kayi hakuri ka yafe Mata"


"Husnah Kenan kinyi kokari da yaran Nan Kuma kina Kai Baki tab'a nuna banbanci tsakanin Su dasu Huzaifa ba Allah ya Miki Albarka, Amma Daliyah Kam bazan iya ba tafi karfina tana dab da Samin hawan jini"


Liyah da Aniyah sai kallon junan su suke da sauri Liyah Tace "Daddy kamar ya Bata nuna banbanci kana nufin ba itace ta haife mu ba?"
Kallon ta kawaii yayi ya kauda kansa.


Aniyah a zuciyar ta Tace "Oh ikon Allah Liyah halinki sai Allah Mahifin ki na fushi dake Amma Baki damu ba sai maganar da yake fad'a ne ya Dame ki?"


Tashi tayi ta durkusa a gaban Daddy Tace "Daddy Dan Allah kayi hakuri ka yafe Mana Dani da Yar Uwata insha Allah baza mu sake tsallaka maganar ba Dan Allah Daddy Kar kayi fushi damu"


Gwiwar sa ne yayi sanyi yasa ya zauna Yana kallon Aniyah Murmushi yayi ya dafe kanta yace "Baki min komai ba My angel idan ma kinyi na tabbata cikin rashin Sani ne ba Kya son b'acin Raina"


Murmushi tayi ta rike hannayen sa Tace "Nagode Daddy Amma Yar Uwata fa na roka Mana gafara tare Kuma ba ka ambaci sunan ta ba?"
Kallon Liyah yayi murmushin takaici yayi yace "Aniyah Kinga alamar ya dame ta ne? Bata damu ba da ta damu da itace ya kamata ta Fara neman gafara"


"No Daddy ba haka bane kasan ta tun ba yau ba Haka take ba ta fiye magana ba"
Granny Tace "eeee Amma ta iya had'a munafurci"
Mummy Tace "Duk ba wannan ba yanzu Ke Liyah baza ki tashi ki bawa Daddyn ki hakuri ba?"
Turo Baki tayi Tace "To mummy me na Masa? Aniyah ce ta Shiga tsakani na da Sageer Kuma na Rama Kuma sanin Kanki ne bana barin bashi"
Mummy yarfa hannu ta Shiga yi ta Kama Baki Tace "Oh Allah al'amarin Liyah sai addu'a Ni wallahi kin Fara bani tsoro"


Daddy yace "Kyale ta zanyi maganin ta daga yanzu baza ki sake fita daga gidan Nan ba kina jina ko?"
A razane Tace "Daddy makarantar fa?"
A tsawace yace "Na dakatar dashi"


Granny Tace "A'a A'a baza a yi haka ba ka Mata wani horon Amma Kar ya shafi karatun ta, kaga Saura Yan watanni ne su gama Dan Allah"
Iska ya hura sannan yace "To Mama"
Sannan ya Maida kallon sa ga Liyah tsawa ya daka mata yace "Ke Ina makullin motar ki?"


Tace "Gashi Nan"
"Miko min"
Ba musu ta Mika Masa, yace "had'o da wayar hannun ki"
Shima ta Mika Masa, yace "zan sayar da motar Nan da wayar bake ba waya da mota" tana jin hakan ta fashe da kuka.


Mummy Tace "Ka sayar kuma? Meyasa zakayi hakan Alhaji?"
"Sabida zan Rika biyan driver bani da kud'in biyar da dashi zan biya shi"
Mummy ta rasa me zatace tayi Shiru Daddy yace "Dake da Aniyah na baku Nan da wata d'aya ki fito da miji in ba Haka ba zan aurar daku ga Wanda nake so Yana Kai Nan ya tashi yace "Ni na tafi masallaci" ya yi ficewar sa.


Yana fita Liyah ta tashi fuuuu ta haura sama tana kuka Aniyah ta tashi da niyar bin bayanta Granny Tace "Ina Kuma Zaki?"
"Zan je na rarrashe tane"
Mummy Tace "Ko Kuma ki Sha zagi ba"
Granny Tace "Ahtoh gwamma ki zauna anan"
Aniyah Tace "Bana Jin dad'i idan na ga tana cikin damuwa musamman kukan ta damina yake ki duba kiga Nima kukan nake"


Mummy Tace "Aniyah kina da zuciya Mai kyau duk da irin abubuwan da take Miki hakan Bai sa kin ji haushin ta ba"
"Toh mummy yazanyi jina nace fa ai bazan ki ta"


Granny Tace "Ko kashin awaki kuke da ita baza ki bi bayanta ba sabida Haka wuce Muje d'akina kiyi sallah a chan sai tayi bacci Zaki koma d'akin"


Mummy Tace "Mama ai gara kawaii ku kwana"
"Kin kawo shawara Mai kyau yau tare zamu kwana wuce Muje" Aniyah ba don taso ba ta bi bayan Granny.


Daliyah tunda ta shiga d'aki take aikin kuka, sai Taji ta Kara tsanar Aniyah a fili Tace "Shikenan Sageer zan Zama Aniyah kamar yanda kake bukata" tashi tayi ta Shiga ban d'aki tayi alwala tayi sallar magrib da Isha Akan sallayar ta kwana sai wurin karfe takwas ta farka da sauri ta fad'a ban d'aki tayi wanka tayi sallah sannan ta shirya tsaf yau batayi kwalliya ba hakan yasa kamannin su ya fita sak Idan ba ka gane su ba zaka d'auka Daniya ce don dama yawanci Daliyah ce Mai kwalliya Daniya Bata fiye kwalliya ba.




Har d'akin Daddy ta Shiga da sallama Yana ganin ta ya Kai da Kan sa, durkusawa tayi tace "Daddy Ina kwana" ko kallonta baiyi ba bare ya amsa cikin muryar kuka Tace "Daddy Dan Allah kayi hakuri ka yafe min nasan bana kyautawa Ni ba 'ya ta gari bace Amma Dan Allah ka sake bani wata dama dan Allah"
Bai kulata ba, mummy na gani ta fito daga ban d'aki Tace "Haba Alhaji magana fa take maka baka ce komai ba"
"Toh me zance Mata ai bani tayi wa laifin ba Aniyah tayi wa laifi sai taje ta nemi yafiyar ta"
"Daddy wallahi Zanje na Bata hakuri Amma yanzu Dan Allah ka yafe min Daddy Dan Allah"
Ta dad'e tana bashi hakuri yaki sauraron ta har Saida mummy tasa Baki ya hakura, makullin motar ta da wayar ta ya Mika Mata yace "Gashi Kar na Kuma ji ko ganin wai abu ya had'a ki da Yar uwarki in ba Haka ba Wallahi zan Kore ki a gidana"


"Insha Allah zaka sameni da aiki da maganar Daddy Nagode"
Yace "Kina iya tafiya"
Tashi tayi ta fita "Kai Tsaye d'akin Granny ta Shiga bayan sun gaisa ta bawa Granny hakuri sannan ta nemi yafiyar Aniyah abin nema ne ya samu ba b'ata lokaci ta yafe Mata.


Tare duk sukayi breakfast sannan Liyah ta wuce school Aniyah Kuma ta wuce asibiti.
Bayan ta Shiga schook ta gama duk abinda zatayi ta wuce studio d'in Sageer.


Yana ganin ta yace "Aniyah kece?" Murmushi tayi Tace "Eh nice"


"Naji dadin ganin ki naji tsoron Kiran ki Kar Kuma najaa Miki matsala da Mahaifin ki jiyan Nan banji dadi na na kasa bacci"


"Kar ka damu komai ya wuce na shawo Kan komai shiyasa nace Bari nazo muyi Hira Kan na koma gida"
"Kai Amma naji dad'i"
Fita yayi ya sayo musu abinci sukaci suka Sha suna cikin hiran ne Liyah ta koma kusa dashi ta zauna sai matse shi take.


Gogan naku dake ba mai hakuri bane Nan da Nan feelings d'in sa ya tashi, ta lura da hakan, hakan yasa ta Kwanta a Kan cinyarsa a hankali ya Fara shafa gashin kanta har ya Kai ga ya sumbace ta ganin Bata damu ba yasa har ya wuce gona da iri, har Saida ya kauda budurcin ta ya Kyale ta ga mamakin na bata damu ba duk da taji zafi hakan Bai da ta Hana shi ba, bayan sun gama sheka ayarsu bacci Mai nauyi ya d'auke su.


*WASHE GARI*
A gajiye ya tashi ya duba ya ga jikin sa zigidir haihuwar uwarsa shi a tunanin sa mafarki yayi Ashe ba hakan bane ba, ganin ta yayi jikinta d'aure da towel da alama daga wanka ta fito Murmushi ta Masa Tace "Sageer ka tash?"


A zabure ya tashi ya zauna a Kan koshin d'in yace "Liyah dama kece?"
"Eh nice kayi mamaki ko?"
Dafe kansa yayi yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Liyah meyasa zakimin Haka?"
"Sabida Ina son ka nayi hakan Ne don na tabbatar maka da cewar nice Masoyiyar ta hakika ba Aniyah ba"
"Liyah ban tab'a sanin haukan naki ta Kai har Nan ba, na fad'a Miki Ni Aniyah nake so ba ke ba"


Jiki a sanyaye ta karaso inda yake murya na rawa Tace "Amma abinda ya faru jiya da dare Kuma fa?"
"Am sorry ki tashi ki koma gida"
Maruka masu kyau ta Masa sannan ta sa kayanta ta fita.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
MILHAAT CE
YAR TERWA


PLEASE VOTE AND COMMENTS
Miilhaat Novelist✍🏻: 🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu''' .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_(A Sympetic,love and a funny Story)_


'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
Follow me on Wattpad
@milhaat🙏🏻


*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Not edited
```PAGE``` 2️⃣9️⃣0️⃣↪️3️⃣0️⃣0️⃣
Jiki a sanyaye ta karaso inda yake murya na rawa Tace "Amma abinda ya faru jiya da dare Kuma fa?"
"Am sorry ki tashi ki koma gida"
Maruka masu kyau ta Masa sannan ta sa kayanta ta fita.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............mummy tunda taji an Fara kiraye kirayen sallar Maghriba hankalin ta ya tashi ganin Liyah Bata Kai haka ba ta dawo ba, Daddy ya dawo gun aiki bai zauna ba suka wuce masallaci dasu Hafeez, bayan sun dawo yaga mummy duk ba a hayyacin ta take ba hakan yasa ya ce "Lafiya kuwa na ganki duk bakya Wal Wala"


Cikin damuwa Tace "Alhaji wallahi na damu yarinyar Nan ce Liyah tun safe da ta sa kafa ta bar gidan Nan ba ta dawo ba"
Murmushi yayi yace "Haba hajiya Liyah ai ba yarinya bace ba zata dawo ki kwantar da hankalin ki"


"To ai Alhaji gani nayi bata Kai haka a waje"
"Kinga dama Aniyah bata dawo ba sai ki dami Kanki Amma Liyah Kam ai ta Fara fin karfina kawaii mu bita da addu'a, kin mayi sallah kuwa"


"Eh nayi"
"Toh Masha Allah, abinci fa ko sai mun roka ne?"
Murmushi tayi Wanda Bai Kai har zuci ba Tace "Wane Ni Muje Yana dinning" Zaman su ke da wuya Huzaifa, Yusuf, Granny da Aniyah suka fito duk suka zauna a dinning don cin abinci, Granny Tace "Ina Mai bakin halin Nan take?"


Yusuf yayi dariya sannan yace "Wannar tsohowar da Neman magana kike Wace ce kuma Mai baki Hali?"


Tab'e baki tayi Tace "Waye in na addar ku Mara Kunyar Nan ba"
Huzaifa yace "Gaskiya Granny bamu son haka aunty Liyah kike fad'a wa hakan?"
Tab'e baki tayi Tace "Au Ashe ma kun San tana da bakin Hali tunda ka gane ta" Maida kallon ta tayi ga mummy dake kokorin raba abinci tace "Husnah Ina yarinyar Nan tayi"


Jiki ba walwala tace "Mama ni kaina Maganar da nake Kenan tun d'azu nake zaman jiranta Amma Shiru kikeji"
Granny Tace "Kai Kema dai da neman magana kike zata b'ata ne? Kuma Naga Liyah ba yarinya bace ba"


Daddy yace "Mama Nima Haka nace Mata Amma Taki ji"
Granny tace "To ki kirata Mana kiji inda take tunda kin damu da ganin ta"
"Mama na kirata ya fi sau ishirin Amma a kashe"
Granny Tace "Toh Allah yasa Lafiya" sai ta Maida kallon ga Aniyah dake ta faman Loma, Tace "Ke Kuma fa ana ta magana kinyi Shiru"
Aniyah sai da ta Kai loman dake hannun ta Kan tace "Granny yunwa ce wallahi take damina yau mun wuni aiki"


"Allah sarki Allah ya taimaka ya bada lada"
Ta amsa da "Ameeen" tana kainan tasa wani loman.


Daddy yace "Aniyah Ina fatan baki manta da Maganar mu bako?"
Shiru tayi tana tunanin Wace maganace chan sai ya Fad'o Mata a ranta Tace "Duk yanda akayi Maganar fid da miji yake, Dole na ma na Sanarwa mummy dama Hafeez yasa Ni a gaba da Maganar aure"
A fili Kuma Tace "Eh Daddy ban manta ba"
"Good to ya ake ciki?"
Tsotsa keya tayi Tace "Daddy zan fad'awa Mummy"
Murmushi yayi yace "To shikenan Ina zaman jira."


Bayan sun gama cin abinci Daddy suka nufi masallaci don yin sallar Isha su kuma suka Shiga d'aki don yin sallah, bayan duk sun idar suka dawo parlor don Hira dama hakan ya zama musu kamar al'adar su.


Hira suke suna kallo Amma mummy duk Bata hankalin ta har karfe Tara Shiru Nan ne fa kowa hankalin sa ya tashi, duk kasa bacci sukayi gashi dare yayi ba halin fita don ana curfew a lokacin Granny tace yayi hakuri zata dawo, a ranar a Parlor suka kwana( Oh Liyah kin Shiga Tara kina chan kina sheka ayan ki da Sageer Mahaifan ki Kuma suna cikin tashin hankali)


*WASHE GARI*
Sai da aka Kira sallar asuba suka watse.


Aniyah kasa zuwa makaranta tayi tana kwance a d'aki ta rasa me ke Mata dad'i tana tunanin wani Hali Yar uwarta take Ciki.


Tana kwance ne taji saukan hawaye a fuskan ta da gudu ta Shiga d'akin mummy, mummy ganin hawaye a idon Aniyah hankalin ta ya tashi hakan ya tabbatar ma ta da cewar Liyah na cikin damuwa Amma tayi kokarin b'oye wa tace "Meyasa baki fita aiki ba?"
Cikin Muryar kuka Tace "Mummy wallahi duk na damu da halin da take Ciki shiysa ko naje ma bazan Maida hankali na a akai ba"


"A a ban yarda ba maza ki shirya, idan supervisor d'inki yazo Bai same ki bafa kawai ki je ki shirya yanzun Nan"
"Amma mum....." Dakatar da ita tayi tace "Ba wani Amma ki wuce kawaii"


Ba da taso ba ta shirya ta fita, Daddy ya Sanar da mummy zai je police station tayi Masa fatan Alhairi da Sa a Dace Amma Bata fad'a Masa sunga hawaye ba sabida tasan Shima hankalin shi zai tashi, Huzaifa da Yusuf duk sun damu Amma dai a hakann mummy ta tillas ta musu suka fita.


*BAYAN WASU AWANNI*


Mummy da Granny na zaune a parlor suna kallo suna ne kawaii suna kallo Amma Sam Basu fahimtar abinda akeyi ko Wacce da irin tunanin da take Jin an kira sallah Granny ta shige d'akin ta mummy ma ta Shige d'akin ta, Granny na idar da sallar tayi bacci kasance war kwanan zaune sukayi jiya, mummy ta fito ta zauna a Parlor zaman ta ke da wuya taji an turo kofa ganin Wacce ke tsaye a kofar ta nufe ta da saurin tana kiran sunan ta "Liyah!!! Kece?"
Ta riko hannun ta "Ina kikaje? Ina Kika Shiga Muke ta neman ki?" Zaunar da ita tayi tana kallon cikin kwayar idon ta, cikin kuka Tace "Hakika na zalunci kaina na cutar da Kai naci amanar addini na tabbata Allah bazai tab'a yafe min ba"


Cikin rashin fahimta tace "Kamar Liyah me kike fad'a ne?"
A dai dai Nan Daddy ya shigo gidan ya Kuma ga motar Liyah hakan yasa yaji sauki a ransa sannan yayi saurin Shiga don ya ga Yaya take, zai turo kofan sai yaji muryar Liyah tana fad'in maganganun Nan hakan yasa ya jaa da baya don yaji maganar.


Cikin kuka take maganar tana "Fad'in mummy wallahi Allah nasan Ni Mai laifi ce a gun ubangiji na Kuma na ci amanar ku na zub da tarbiyar da kuka min na biye wa son zuciya ta"


Mummy ta kosa Taji mene ne hakan yasa ranta ya soma b'aci cikin b'acin raai tace "Baza ki fad'a min me kikayi ba ko sai na sab'a Miki?"


Cikin kuka ta Fara Sanar Mata da abinda ya Shiga tsakanin ta da Sageer.


A razane mummy ta tashi tayi saurin dafe kanta don ji tayi Yana tsarawa sai ambatan "Allahumma ajirni fi musibati, Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Liyah yanzu ke rashin hankalin naki har ya Kai nan ban tab'a sanin wayewar ki na banza bace sai yanzu, to yanzu wa gari ya waya? Ya ci muriyar ganga yanzu fa shikenan kin Zama fanko" ta Karasa Maganar kuka.


Durkusawa tayi a kasa Tace "Mummy dan Allah kiyi hakuri ki daina kuka dan Allah"


"Liyah ki fad'a min me zanyi idan ba kuka ba, yanzu ke bakya tunanin gaba? Ya kike ganin Mahaifin ki zaiji idan yaji maganar Nan?"


Da sauri ta taso ta rike hannun ta Tace "Mummy Dan Allah Kar ki fad'a Masa Kinga dama Yana fushi Dani Dan Allah ki rufa min asiri kar ki fad'awa kowa please" sai kuka take kamar idanun ta zasu sauko.


Daddy ya shigo parlor da fad'in "Na yaushe kuma Daliyah na Riga na ji komai naji komai kinyi abinda ranki yake so hankalinki ya kwanta"


Da gudu ta Durkusa a gaban sa tana bashi hakuri hankad'e ta yayi ya haura sama, mummy ce ta taso ta d'aga ta.


Aniyah na zaune da Hafeez suna Hira Taji kamar an buga kanta a zabure ta tashi Tace "Yaya Hafeez zan tafi gida"
Shima tashi yayi yace "haba aniyah meyasa kike min Haka ne duk sanda muke cikin Jin dad'i sai ki ce zagi tafi kuma a gigice kike tafiya why?"


Cikin murya kuka tace "Dan Allah ya Hafeez kayi hakuri nayi alkawarin fad'a maka komai gobe idan muka had'u Amma yanzu Dole na tafi" ta d'auki jakarta ta Shige motar ta ta bar asibitin.


Tana Shiga parlor taji mummy na fad'in "Liyah Ni yanzu babu abinda zance Miki sai dai fatan Shiriya Kuma kema ki dage gun neman yafiya a gun Allah kin yawaita istigfari"


Cikin kuka Tace "Mummy Dan Allah ki roki Daddy ya yafe min wallahi bazan sake ba"
Murmushin takaici tayi Tace "Na yaushe kuma Liyah yanzu fa babu wani d'a na Miji da zai ganki da mutunci sabida kin zubar da mutuncin ki budurcin ki an yi shine sabida ki kaiwa mijin ki shine zai Zama pride d'inki Amma kin bawa wani banza a banza bayan hakan Kuma bai canza komai ba tunda har yanzu baya sonki" Cikin kuka mummy ta d'aura da fad'in "Sageer ka cuce mu bazan tab'a yafe maka ba"


Jiki a sanyaye Aniyah ta karaso inda suke Tace "Mummy kina nufin Sageer ya...." Ta kasa Karasa Maganar shiru tayi a ranta Tace "Tabbas jiya naji zafi a private part d'ina zafin da ban tab'a ji ba wato hakan na nufin Sageer ya shige ta Kenan?" Tana kallon Liyah mummy Tace "Duk tunanin da kike hakane ba garga da"


Aniyah ganin irin kukan da Liyah keyi yasa taji tausayin ta, rungumar ta tayi tana rarrashin ta sannan ita kanta kukan take , mummy sai Taji tausayin su ya kamata sai ta Shiga rarrashin su Tace "Ku yi Shiru bana so kowa yaji maganar Nan daga Ni sai ku Daddyn ku ma banso yaji ba Kar ku sake su Hafeez su ganku a haka,maza ku tashi ku Shiga d'aki zan shigo anjima" Basu musa ba suka haura sama, Liyah dakyar take tafiya sabida Sageer bai Mata da Wasa ba.


Suna Shiga Aniyah ta had'a Mata Ruwan zafi ta Shiga Ciki sannan tayi wanka tana fitowa ta kwanta bacci Mai nauyi ya d'auke ta.


Tun daga Wannar ranar Liyah

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads