Showing 48001 words to 51000 words out of 66367 words
Chapter 17 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
ma kukan take, Mama Tace "Rahila Kinga Ni ko zurfin ciki baiyi ba na Sha fad'a Miki Ni mahaifiyar kice ki daina b'oye min abu, In da na San da hakan bazan tab'a Bari prince ya Auri rose ba, Yanzu yayi riba biyu" sai ta sake fashewa da kuka Mai cin raai, Rahila cikin kuka Tace "Mama am sorry please forgive me it was a mistake"
Amma Mama bata saurare ta ba Asali ma kukan ta kara,dakyar Nnna ta rarrashe ta, tayi shiru.
"Yanzu gobe zan tafi da ita gida Dole yasan abinda ya aikata da dukkanin Yan kauyen mu"
Nnna Tace "Ahhh bakya ganin Zaki tona wa Yar ki asiri?"
"Wani asiri ya rage Nnna, gara Muje kawaii kowa ya sani"
Iska ta hura sannan Tace "Toh shikenan tunda kince haka"
*WASHE GARI*
Mama tasa Rahila a gaba suka koma kauyen su, ko Zama basuyi ba suka nufi fada.
Mama ta Sanarwa Sarki da sarauniya komai, sarauniya taci kuka Sosai sarki ya aika aka Kira Prince, prince na Jin cikin dake jikin Rahila nasa ne Bai Musa ba don yansan aika aikan da yayi Kuma shi ya b'are ta aleda, yayi murna sosai, ya bawa mahaifiyar sa da Daddyn sa hakuri sannan ya nemi yafiyar Mama da Rahila, sannan ya roki alfarma a bar Rahila a fada sabida a bata kulawa na musamman, Mama da farko Taki Amma da iyayen sa suka sa baki sai ta amince, Rose ji tayi kamar ta had'iye ran ta tsabagen bakin ciki gashi Babu yanda ta iya, amma ta d'auki aniyar kawar da ita da abinda ke cikin ta.
*KANO*
Nan da Nan jama'a suka cika gun, ji nayi wani yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wannan ai baya Numfashi" Yana nuna Mubarak da aka Ciro da ga cikin mota dakyar, ji nayi wani yace "A'a yana Numfashi Amma ba Sosai ba"
Wani yace "Mu Kai su asibiti kaga d'ayan motar Kam ta Kama da wuta,sai dai a Kira fire service" haka kuwa akayi Rai a hannun Allah aka Kai Mubarak asibiti, suna Shiga asibitin emergency aka kaishi Kan likita yazo har ya cika.(Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,Al Mautul hak mutuwa gaskiya ce, kullu Nafsin za'ikatul Maut, Allah ya jikina musulmai mu da muke raye idan tamu tazo yasa mu cika da imani, ameeeeeeeeeeeen).
Sageer na kwance yaji karar Wayar sa Yana dubawa yaga number Mubarak ne, a fili yace "Oh naga jaraba wannan wani irin ango ne" Yana picking yace "Kai Dallah malam Kai wani iri ne kawai don kayi aure....." Sai yaji muryar mace Tace "Hello Dan Allah da Sageer nake magana?"
Cikin sanyin murya yace "Eh nine"
"Okay to kaxo Muna bukatar ka a medical center abokin ka yayi hatsari"
A firgice ya tashi ya zauna sai ambatan Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un yake Nan take ya Kira wayar Ra'ees ya Sanar Masa halin da ake ciki ya razana Sosai sai yace "mu had'u a asibitin"
"Okay" a tare suka katse wayar.
A tare suka Shiga asibitin suna Shiga suka nemi ganin sa, likita yace "Kuyi hakuri Rai yayi halin sa ya zub da jini da yawa"
Kan na Ankara Ra'ees ya shake kwalar rigar likita yace "Toh munafuki Kai baka da abin fad'a sai Labarin mutuwa ko? Toh Wallahi Kai ma sai na kashe ka"
Sageer na kokarin cire Masa hannun Amma ina ya rike shi da karfin gaske Sageer yace "Ra'ees ka sake shi, ka sake shi Mana kana cikin hayyacin ka kuwa?"
"Sageer kyalleni na kashe mutumin nan, shine fa Wanda ya fad'a min Rumana ta mutu,Shima sai yaje in da ya Kai su"
"Ka sake shi, ya kamata ka rungumi Kaddara Rumana lokacin ta ne yayi Mubarak ma haka babu Wanda ya Isa ya kashe wani sai Allah yaso Kuma idan kwana ya Kare babu Wanda ya Isa ya Hana Mutum mutuwa, shi aikin sa kawaii yake yi, please be a Man"
A hankali ya sake shi, tsaki likita yayi ya bar gun, wata nurse ce tazo Tace "Zaku iya tafiya da gawar" tana Kai Nan ta tafi.
*KAUYE*
"Baba ina so ka kashe min ita bana so ta kwana, infact karta Kara minti d'aya a duniya"
Wata iriyar dariya yayi irin tasu na mugayen bokaye yace "Anyi angama" cikin katuwar murya yace "Amma Zaki ajeyi Mana dubu d'ari biyar Kan a yi aikin, ba b'ata lokaci ta ciro Yan dubu dubu ta Mika Masa a tsawace yace "Keeeee!!" Har sai da ta Fad'i daga Kan kujerar da ta zauna, yace Mata "Ba a Mana haka sa kud'in a wanchan kwaryar" Yana nuna Mata wata katuwar kwarya Wanda zai iya cinye Ruwan jarka biyar, tana sa kud'in, kud'in ya b'ace a zabure ta tashi ta Tsaya Dariya yayi yace "zauna babu abinda zai same ki"
Jiki na rawa ta zauna.
Wata Yar karamar kwarya ya d'auko da ruwa fari sal a cikin ta, wasu irin magana yake yi Wanda na kasa gane me yake fad'a nan da Nan Ruwan ya Fara canza kala ya koma blue sannan ya fari kamar nono chaan ya koma jaaaa daga Nan ya koma kalan asalin ruwa.
Yace Mata "Matso ki gani" Yana nuna Mata cikin kwaryar tana lekawa Tace "Itace itace" dariya yayi.
Nima nace Bari na leka Kar a yi bani Rahila na gani tare da Mahaifiyar prince suna Hira tare da wasu bayi guda biyu suna danne Mata kafa.
Ihu Mai Karfi Rahila tayi sarauniya Tace "What is it?"
Ihu ta sake kurma wa tana ciza leb'e tana rike cikinta, Tace "Ko dai nakuda ce?"
Kai ta d'aga mata, Nan da Nan aka Kira nurses aka kaita d'aki, duk abubuwan da ake yi Rose na gani a cikin kwaryar sai Murmushi take irin na mugunta.
Tun Kan Rahila ta haihuwa Allah ya d'auki abarsa Amma ta haihu 'ya ta mace.
Rahila na ganin hakan ta b'ata raai tace "Ya naga kamar abinda ta Haifa bai mutu ba?"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Mu had'u a page na gaba
Milhaat
Yar Terawa
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu''' .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
Follow me on Wattpad
@milhaat🙏🏻
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
'''PAGE''' 2️⃣4️⃣0️⃣↪️2️⃣5️⃣0️⃣
'''PREVIOUSLY'''
Tun Kan Rahila ta haihuwa Allah ya d'auki abarsa Amma ta haihu 'ya ta mace.
Rahila na ganin hakan ta b'ata raai tace "Ya naga kamar abinda ta Haifa bai mutu ba?"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
.............."Eh bata mutu ba Dole sai tazo duniya"
Rai a 'bace Tace "Ina so ka kashe ta yanzun Nan"
"Keeeee!!!!" A tsawace wannan karon bata tsorata ba ya d'aura da fad'in tashi ki fita,tashi ki fita" ganin idon sa ya Fara canza kala tayi saurin fita daga bukkar.
Prince ne durkushe a kasa Yana rike da hannun Rahila yana kuka Yana ta fad'in "Please forgive me, forgive me please."
Mahaifiyar sa sai hakuri take ta bashi Amma kamar ce Masa take ya kara.
Rose Sam bata ji dad'in ganin yar Rahila a raye ba, hakan yasa tun da aka haife ta,ta d'aura Mata tsanar duniya a kanta.
*KANO*
"mummy gobe insha Allahu zamu fara fita IT" Aniya ke magana da mummy dake yanka kayan Miya Aniya Kuma na wanke wanke.
Murmushi Mummy tayi Tace "Masha Allah,Allah ya taimaka Yanzu da ga IT Kun Gama ko?"
"A'a Mummy sai munyi final Exam tukunna"
"To Masha Allah,Allah ya taimaka" ta amsa da "Ameen"
*Washe gari*
Ta shirya tsaf sai asibiti, asibitin da Hafeez yake aiki, ganinta a gun ba karamin dadi ya ji ba har sai da ya kasa nuna hakan, hakan yasa suna tare a kowa ni lokaci idan Basu da abin yi.
*Bayan Sati biyu*
Aniyah na tafiya acikin asibiti sai taji ance "Yan Mata ji Mana"
Tsaki tayi ta cigaba da tafiyar ta ba tare da juyo taga ko wane ne ba tana tafiya tana latsa wayar ta, da saurin gaske ya Sha gaba ta.
Cikin b'acin raii ta d'ago kanta Tace "Malam ya haka baka da....." Ganin Wanda ke gaban ta yasa ta kasa Karasa maganar dake bakin ta, zaro Ido tayi cikin Rawar murya Tace "Kaaaai..kaaai ne?"
Murmushi yayi yace "Eh Ni...Ni ..Ni..ni ne"
Kara zaro idon ta tayi Tace "Sabir dama kana Nan?"
Dariya yayi yace "Gashi kuwa kin ganni"
"Oh ikon Allah yaushe ka dawo?"
Murmushi yayi yace "Zamu iya Zama Dan Allah? In yaso sai ki cigaba da tambayoyin naki?"
Murmushi ita ma tayi Tace "Toh mu zauna, ga chan kujera" tana nuna Masa wasu plastic chairs da aka jera a gindin wata bishiya, suna Zama tace Masa "Uhmn ina sauraron ka yaushe ka dawo?"
"Na fi wata biyu da dawowa ai"
Tab'e baki tayi Tace "Oh Allah Amma mutuncin ka dayawa yake shine ko ka neme mu ko?"
"Kin San Dole na neme ku ai, na dawo na samu Kun tashi ina tambayar hajiya ta Amma Tace min Bata San unguwar da kuka koma ba"
"Ayya hakane Kam, mun tashi ba Shiri sannan lokacin Bata Nan munje da Daliyah akace Mana tayi tafiya shiyasa, so ya karatu da fatan an gama lafiya?"
Yar karamar huci yayi yace "Well Alhamdulillah komai normal, ya naki fa?"
"A Nan BUK nake ina karantar medicine yanzu IT muke anan"
"Masha Allah Kinga nima shi nayi, Allah ya taimaka ya sa a gama a sa'a"
"Ameen Nagode sosai"
"Ina Labarin Liyah?"
Murmushi tayi Tace "Tuntuni nake jira naji ka tambayi Labarin Mutuniyar ka Amma baka tambaya ba, to tana lafiya Lau"
Tsotsa keya yayi yace "Ai abokiyar fad'a tace dole na tambaya,kin tuna sanda tace sai ta dake Ni Wai na fad'a wa Aunty cewar kunyi swapping class?"
Aniyah dariya ta Shiga yi Tace "Eh na tuna ai bazan manta ba Amma a wanchan lokacin ka tsorota fa"
"Haba haba tsoro? Ni d'in? Liyah mace ce fa Kuma yarinya ce akaina duk da ban Baku shekaru dayawa ba"
"Eh hakane Kam, Ai Liyah sai a hankali ko da kafi hakan zata ce zata dake ka karfin tsiya ne da ita"
Ya kyal kyale da dariya sannan yace "Wai kina so kice min haryanzu Liyah bata canza ba, Bata daina wannan shegen rashin jin nata ba?"
"Ina kuwa ai sai abinda ya Karu, Amma tunda yanzu ka dawo zaka saita Mana ita ko?"
Da Karfi yace "Ni?" Yana nuna kansa, sai ya d'aura da fad'in "Wane Ni kin fa San yanda ta tsane Ni,Kuma kice haka?"
Murmushi tayi Tace "Tsana kuma Kar kace haka Mana"
"Toh Daniya mene ne in ba tsana ba?"
Murmushi tayi kawaii ganin tayi shiru yace "Khadeeja tayi aure na Taya ta murna sosai"
"Eh wallahi tayi aure Yanzu kusan shekara take nema in ban manta ba"
"Naga Pre Wedding pictures din ta ai a Insta sunyi kyau sosai Allah ya Basu zaman lafiya"
Ta amsa da ameen.
Nan suka Shiga hiran yaushe gamo sunayi suna dariya, Hafeez ya nufo inda suke ganin ba ita kad'ai bace ya kauda kansa kamar bai ganta ba ya canza hanya, tana ganin sa ta Shiga Kiran sa "Yaya Hafeez!!! Yaya Hafeez" Amma Bai kulata ba Kuma Yana Jin ta, Murmushi Sabir yayi yace "Saurayin kine ko?"
Da sauri Tace "A'a ba saurayina bane d'an makarantar mune"
"Hmmm lallai in ma ba saurayi ki bane to yana sonki, sabida Nan ya nufo dake flower chan ta tare Ni Amma da ya ganmu tare sai ya juya"
"Kaaai Sabir kaima dai baka canza ba wallahi har Yanzu sa idon ka na Nan baka daina ba"
Yar karamar dariya yayi yace "Ki tashi kije kiyi biko,nikam zan tafi" had'e da Mika Mata wayar sa "sa min number ki please" ba musu ta karb'a ta sa Masa, yace "Ki gaida su Mummy idan na samu lokaci zan shigo na gaishe su" ta amsa da "To insha Allah zasu ji sai mun ganka" yace "Okay" sukayi sallama kowa yayi hanyar sa.
Har office d'insa ta Shiga da sallama a bakin ta ta nemi wuri ta zauna Tace "Yaya tun d'azu fa nake jiran ka, ka fito daga tiyatar da kuka Shiga Amma ina Kiran ka kaki kulani"
Fuska ba Wal Wala yace "Sorry banji bane,ya akayi?"
Ta amsa da "kalau"
Babu Wanda ya sake cewa komai Aniyah ganin Shirun yayi yawa Tace "Yaya Anya kana lafiya kuwa me yake damin ka na ganka wani iri ko dai ba ayi nasarar aikin bane?"
"Lafiya ta kalau Kuma babu abinda yake dame Ni, Kuma aikin anyi shi successful"
"To mene ne matsalar?"
"Babu" kawaii yace Mata a takaice, "okay ko dai baka bukatar magana dani ne?"
Kallon ta kawaii yayi baice Mata komai ba.
Jiki a sanyaye ta tashi har ta bud'e kofa taji yace "Aniyah!!!" A hankali ta juyo Tace "Na am"
"Da wa na ganki d'azu?"
Murmushi tayi Tace "Dama wannan shi yasa ka b'ata Rai?"
"Baki bani amsar tambaya ta ba"
"Sunan sa Sabir, tare muka tashi tun muna yara, makwafcin mune tunda muka gama secondary School ya bar kasar Nan tunda ga Nan bamu sake had'uwa ba, sai d'azu da na fito zan shigo office d'inka muka had'u dashi, to fa shine kaga muna gaisa wa ban San me ka d'auka ba"
Iska Mai zafi ya hura, sannan ya tashi ya nufo ta sai da ya iso daf da ita ya tsaya sannan yasa hannun sa duka biyu a aljihu yace "Na d'auka saurayin ki ne ai, Baki ji yanda zuciya ta take min zafi ba da na ganki dashi kina ta Masa Murmushi harda dariya hmm"
Kallon sa tayi, tayi Murmushi sannan Tace "Yaya Hafeez to meyasa zaka ji haushin hakan don ka ganni da wani?"
Murmushin takaici yayi yace "Haba Aniyah Yanzu ke Baki fahimci komai a tattare dani ba? Ashe dama haukata nake kawai ni kad'ai?"
Cikin rashin fahimta Tace "Hauka kuma? Dan Allah me kake nufi da hakan Yaya?"
Da Karfi yace "sabida Ina sonki Dole ne naji bakin ciki da 'bacin raai duk sanda na ga wani ya kusance ki bayan ni Aniyah kece Wacce nake mafarkin Rayuwa ta dake, tun ranar da na Fara ganin ki naji na kamu da son Ki na d'auka kin fahimce Ni Ashe ba haka" ya Karasa maganar cikin sanyin murya jikin sa mace ya koma ya zauna ya dafe kansa.
A nitse take tafiya ta Karasa inda ya zauna ta sunkuwa Tace "Yaya Hafeez" cikin sanyin murya, a hankali ya d'ago kansa idon sa yayi jajir , Murmushi tayi Tace "Yaya Hafeez ba ka Soni a banza ba sabida kamar yanda kake kaunata nima haka nake Kaunar ka Ina ganin Soyayyar da kake min bai Kai Wanda Ni nake maka ba sabida a kullum da Soyayyar ka nake kwana Kuma nake tashi, sannan ko wani safiya farin ciki marasa misaltuwa yakan ziyarci zuciya ta sabida nasan zan had'u da Kai, Amma naji tsoron fad'a maka sabida Ina ganin kamar Kai ba da hakan ka d'auke Ni ba"
Gyara Zama yayi yace "Dan Allah dagaske kike Aniyah kina Sona? Kuma Zaki aure Ni?"
Tashi tayi ta nufi kofa sai da ta bud'e kofar sannan ta juyo Tace "Eh Ina son ka Kuma kasa a Ranka Aniyah matar kace" tana Kai Nan ta fita da sauri.
Hafeez tashi yayi ya Fara tsalle Yana hamadalah ga ubangijin sa sai washe Baki yake.
Tun daga wannan ranar Soyayya Mai Karfi ya Shiga tskanin Hafeez da Aniyah kamar zasu cinye junan su.(asha love lafiya😘)
"Kiyi hakuri Fareedah, ki rungumi kaddara, lokacin sa ne yayi"
Ra'ees ke wannan maganar yayin da Fareedah kuka take Sosai kamar ranta zai fita, Sageer tausayin ta ne ya kamashi shiyasa ya fita daga d'akin.
Cikin kuka Fareedah Tace "Shikenan ko Ra'ees? Mubarak ya tafi ya barni meyasa mutuwa zata min Haka a dai dai lokacin da na shirya zaman Jin dad'i da masoyi na, meyasa mutuwa zata d'auke min shi bayan ga mutane Nan dayawa?"
"Kash subhannallahi haba Fareedah kina Yar musulma kike fad'in hakan? Ya kamata ki sani duk Mai Rai mamaci ne duk ita muke jira Mubarak Ubangi yayi Kiran sa Dani dake duk babu Wanda ya Isa ya hana shi tafiya Dan Allah kiyi hakuri ki daina kuka ki rungumi kaddara, kukan Nan bazai amfana Masa komai ba ki yi ta Masa addu'a"
"Ra'ees Kenan ba ka San yanda nake ji bane shiyasa kake fad'in hakan"
Murmushin gefen baki yayi yace "Ni ko nasan yanda kike ji, babu Wanda ya kamata yasan yanda kike ji sai Ni, karki manta fa biki na da Rumana saura two weeks ta rasu a gaban Ido na ta fad'i ta mutu Kuma kice min ban San yanda kike ji? Ina Jin zafin rashin Rumana, sai Kuma gashi mutuwar Mubarak ta sake fama min ciwon da ke damina, Amma babu yanda muka iya hakuri ya Zama Dole, na sani wannan jarabawa ce da mahallicin mu ya d'aura Mana Allah ya bamu ikon cin sa" mikewa yayi yace "Ni zan koma gida Dan Allah ki Rika yi Masa addu'a,sai da safe" sai yayi ficewarsa.
Fareedah kwana tayi tana kuka, taji duk duniyar ta fita Mata akai, kuka tayi sosai har Saida hawayen suka kafe.
Karfe goma na safe aka Masa wanka aka sallace shi sannan aka kaishi gidan sa na gaskiya, Liyah naji Labarin abinda ya faru suka shirya ita da Aniyah suka je gidan ta, tun safe suke gidan sai yamma suka koma, Fareedah na ganin sun tafi ta bud'e sabon shafin kuka, mahaifiyar Fareedah ganin halin da take Ciki ta d'auke ta suka koma gida, a chan a ka cigaba da karb'an gaisuwa.
(Allah ya jikan musulmi)
Sageer alkwari yayi wa kansa tunda yaga irin Soyayyar da Liyah take Masa ya kudiri a aniyar Zama da ita Zama na har abada duk da yasan cewar ba sonta yake ba.
School d'insu ya Shiga don yin wasu abubuwa Wanda ya shafi karatun sa,sai ya Kira ta don su had'u, ya Sanar da ita ya shirya zai turo iyayen sa, zaune suke a restaurant suna cin snacks suna hira sai mummy ta Kira ta, Tace masa "Ina zuwa Bari na fita nayi picking call" yace "okay" bayan ta fita wata student ta Zo ta zauna bayan sun gaisa Tace "Irfan Ina bala'in son wakokin ka"
Murmushi yayi yace "Nagode sosai"
Tace "No need ai yabon gwani ya Zama dole, birthday na ya kusa Ina so ka rera min waka please"
"Okay Yanzu dai Kinga bani kad'ai bane akwai abinda nake yi yanzu" hannu yasa a aljihu ya d'auko card din sa yace "Ga card Dina idan kin Samu lokaci sai ki kirani mu tattauna ko?."
Tace "Toh na gode" tashin ta ke da wuya sai Taji saukar mari a fuskar ta tass, a razane Sageer ya tashi ya na fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Liyah?"
Yarinya ta Kama kuncin ta Tace "Ke!!! Kika mare Ni?"
"An mare" tana magana ta huci, Liyah Kan ta Ankara taji saukan Mari yarinyar ta