Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 66367 words

Chapter 5 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt

Ads the beginning of article before Image
Ads at the middle of Article

ne ko?"
"Eh Baki ne"
"Sannu ku da zuwa Baki"
Murmushi sukayi sannan suka amsa a tare "Yauwa sannu d'an gari"


Dariya yayi sosai sannan yace "Ya haka am I safe? Bayan kaminnin da kuke, maganar ma tare kuke furtashi, dakyau"


A tare suke ce "Haka Allah ya halicce mu"
Kallon su ya sake yi a Karo na biyu yace "Allah? Kuna nufin ku musulmai ne?"

A tare suka sake amsawa "eh mu musulmai ne"
Tab'e Baki yayi yace "Yayi kyau nice to meet you you"
Suka amsa da "Nice to meet you too"


Veronica Tace "Surutun ya Isa haka as you can see we are on our way to the farm"


"Yes I can see, bari na muku rakiya"
Veronica taji dad'i sosai yau zata zanta da masoyin ta na tsawon Lokaci.


Daliyah tace "Anya don't you think it's a risk?"
Daniyah Tace "It isn't zaku iya Shiga matsala Kila ma ya shafe mu, so ka bari kawaii ba sai ka raka mu ba, by the way har mu uku baza mu b'ata ba"


Elisha yace "Ai Nima bance zaku b'ata ba, kawai so nake na taya ku it has been long ban ganta ba"


Daniyah tace "Mun hutar da Kai, nifa ban shirya mutuwa ba"
Veronica da Daliyah mamaki suke, Veronica Tace "Daniyah Wannan shine Karo na farko da naji Kinyi magana mai tsawo maganar ki baya wuce eh ko a'a"


Murmushi tayi Tace "Toh so kuke nayi shiru, kawai na samu chanjin yanayi ne, Kuma ina tare da Liyah Dole na Koyi surutu ko da kuwa bana so"


Daliyah Tace "ehh ba shakka yimin sharri, malama dama da surutun ki munafurci ne kawai, Kuma kin hango mutuwa by hanging ba"
"Sai kuma kiyi ai, Liyah nasan Kece Kika koya min surutu,Kuma ai mutuwa dole ko da baza a yi hanging d'ina ba in lokaci yayi sai mun tafi"


Duk sukayi dariya, Veronica Tace "Elisha Mu tafi ko?"
Elisha yace "mu tafi"
Daliyah da Daniyah Basu so hakan ba,amma babu yanda suka iya da garen da ba wuya tafiya suke suna hira, har suka Isa gonan Veronica ta nuna musu yanda ake yin kunya, Veronica tayi kunya sama da biyar Amma Daliyah da Daniyah sun kasa yin ko da guda d'aya ne, gashi sun gaji, Veronica Tace "kuje Ku huta ga inuwa chan" tana nuna musu wata bishiya ba b'ata Lokaci suka nufi bishiyar suka zauna.


Elisha yayi dariya sosai yace "a hakan dama zakuyi aikin?"
A tare suka ce "Eh Mana ai Koyo muke"
Veronica tayi dariya suka ci gaba da aikin su, suna Hira Elisha Nayi itama tana yi, muryar wani suka jiyo daga bayan su yace "Chineke Vero, Elisha" Yana nuna su da Yar yatsa, "me kuke yi a Nan?"


Elisha yace "Kamarya me muke yi anan are you blind? baka ganin aiki muke yi ne?"


"Am not blind I can clearly see everything, so you are here helping your girlfriend"


Cikin Rawar murya Veronica Tace "am not his girlfriend"


Yace "Shut up he is not your boyfriend Kuma yake taya ki aiki?"


"He is just a friend"
"Okay zanje na fad'awa Sarki cewar na gan ku a gona kana taya ta aiki Kuma ba kanwar ka bace, baku da gona ne Elisha? Da har sai kazo Nan kayi noma? Why not kaje ka taimakawa tsohuwar ka"


Da sauri Daliyah suka taso suka Zo inda suke Daniyah Tace "Young Man they are just friends, can't you see?"


Kallonta kawaii yayi, ya yi tsaki sai yace "Rest in peace ko"
Yayi tafiyar sa, Daniyah Tace "Wai Dan Allah dagaske yake ne?"


Elisha yace "dagaske yake, dama abokin takara na ne, ya so Vero amma ta ki shi ta zab'e ni kinga zai Sanar da sarki, Vero mu gudu kawai mu bar garin Nan, Daliyah kuje Ku fad'a a gida zamu dawo Nan gaba idan komai ya dai daita"


Vero kuka take sosai Elisha ya riko hannun ta yace "Vero ki Zo mu tafi na tabbata yanzu ya kusa ya Isa fada, Kuma kinsan baza su b'ata lokaci wurin zuwa Nan ba"


Daliyah Tace "Vero ku tafi kawai" suka rungumi juna, Elisha da Vero suka nufi hanyar barin gari Daliyah da Daniyah Kuma sukayi hanyar gida, suna Isa gida suka sanarwa mutanen gida, Hankalin kowa ya Tashi musamman grace da bata da kowa sai ita, Granny tace "Grace my daughter ki kwantar da Hankalin ki tun da sun tafi babu abinda zai same su, Kuma wannan yaron Yana sonta bazai cutar da ita ba"


Grace Tace "Mama I pray so" cikin kuka, suna cikin maganar sukaji ana Sanarwa an Kama Elisha da Veronica sabida haka kowa ya fito bayan gari.


Da gudu Grace ta fita, taga Veronica da Elisha a d'aure ana jaan su a wulakance.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Mu had'u a page na gaba
*MILHAT CE*
*YAR TERAWA*
🥰


✨✨ *DALIYAH* ✨✨
*DA*
✨✨ *DANIYAH* ✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_


_*(A Sympetic,Love and Funny Story)*_




```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```




*Daga Marubuciyar*✍🏻


*MATAR AURENAH*
*SAIRA DA SARAH*
*AND NOW*
*DALIYAH DA DANIYAH*
_(Cigaban Sairah da sarah)_


*DALIYAH* da *DANIYAH* , ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya, tausayi,fad'akarwa, nishad'antarwa gami da ilmantarwa.
```


*Note_* ```bamu yarda wani ko wata su juya Mana labariba tare da izinin mu ba.```


Ya Allah Ina rokon ka da ka bani ikon gama Littafin Nan kamar yadda na ra.Ameen


Labarin *Daliyah* da *Daniyah* k'ageggen labarine ban kirkirin Labarin Nan don cin zarafin kowa ba.Allah ubangiji ya datar da mu.
Ameen....


*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu (Milhaat)*✍🏻✍🏻


📞08111791471


🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*


Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.
🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________


*BISMILLAIR RAHMANIR RAHIM*


*PAGE* 6️⃣0️⃣↪️7️⃣0️⃣
Grace Tace "Mama I pray so" cikin kuka, suna cikin maganar sukaji ana Sanarwa an Kama Elisha da Veronica sabida haka kowa ya fito bayan gari.


Da gudu Grace ta fita, taga Veronica da Elisha a d'aure ana jaan su a wulakance.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Grace ihu take tana birgima tana rokon su Kar su cutar dasu
"Please Kar ku Kashe min ita, she is the only one I have"


Amma basu saurare ta ba, Granny Ce ta Zo ta riko ta tana kuka tana cewa "Grace kiyi hakuri Zaki ji wa kanki ciwo"


"Mama gara na mutu kawaii Nima na bita, ya zanyi da raina bai Kai sati biyu da na rasa d'ana ba, Yanzu Kuma Kanwata d'aya tilo, sannan miji na tun da ya tafi shiru bamu San inda ya Shiga ba, bamu San a wani Hali yake ciki ba, Mama Kuma kice min Kar nayi kuka"


"Na sani grace it is not easy but please try to calm down"


Daliyah da Daniyah suma kuka suke Sosai, gashi Dole sai sunje don idan baka je gun da ake Kashe mutane ba kaima Kashe ka za'a yi, ba don sun so ba sukaje gun, Vero na kuka tana Kiran Sunan Auntyn ta amma baza ta iya taimaka Mata ba.


Bayan an Kashe su, kowa ya watse, grace taci kuka har hawayen ta sun kafe, Daniyah da Daliyah Suma sunci kuka Sosai sannan sukayi fatan Allah ya jikan ta.


Daniyah Tace "Kaka yaushe zamu Koma wallahi na gaji da Abubuwan da yake faruwa a garin Nan daga wannan sai wanchan tun da muka Zo ban tab'a Jin kyakkyawan labari ba" ta karasa maganar cikin kuka.


Granny Tace "Daina kukan kinji" tasa hannun ta share Mata hawaye sai Tace "Daniyah kad'ai ba Ni kaina na gaji, Insha Allah next week zamu Koma, munyi waya da Daddyn ku ma yace ya kamata mu dawo don an koma islamiyya"


"Amma Granny kina ganin next week baiyi Nisa ba?"
"A'a ai kamar Yanzu Ne a gun Allah, Ke dai mu Kara hakuri"
"To Granny Allah ya nuna Mana"
"Ameen"


Daliyah ne zaune da Kaka suna hira duk da ba dad'in hiran suke ba sabida suna kewar Vero, Liyah Tace "Kaka Wai Dan Allah meyasa sarkin ku baida Imani baida tausayi ko kad'an"


Kaka yace "Bai samu Wanda zaiyi magani al'amarin bane"
"Yanzu kana ganin akwai yanda za'ayi?"


"Eh akwai, don har mun tsara komai"
Tace "Kai da wa?"
"Ni da Veronica"
Tace "Allah sarki Vero ina missing d'inta Sosai wallahi"


"Ya muka iya lokacinta ne yayi"
"Allah ya jikan ta,Kaka ka fad'a min abunda zakuyi ko zan taimaka maka"
"A'a aikin Mai sauki ne Amma Yana da had'ari"


"Na yarda Kaka I'm willing to help, in dai zai kawo karshen Al'amarin Nan"


Iska Mai zafi ya fitar sannan yace "Nasan Zaki iya sabida Baki da tsoro,amma ki sani sirrine tsakani na dake"


"Toh Kaka insha Allah bazan fad'a wa kowa"
"Okay good" gyara Zama yayi yace "Kina jina"


"Eh ina jinka"
"So nake ki Shiga gidan sarki"


Daliyah tayi mutukar tsora ta, tayi kokarin saita kanta Kar ya gane Amma sai da Kaka ya gane.


Kad'a Kai ya yi yace "baza ki iya bako?"
Dakyar ta had'iye yawun bakin ta sannan Tace "a'a zan iya,Kaka me zanyi a gidan sarkin?"


Tashi yayi ya d'auko wani bakar Leda ya Mika Mata yace "Ki bud'e ki gani"


Bayan ta bud'e Tace "Kamar Uniform na bayin sarki ko?"
"Eh shine, Zaki sa uniform din Nan ki Shiga gidan sarki, ki Shiga part d'in Yarima ki Sanar wa Mai gadin cewar kece yau zakiyi Masa gyaran d'aki"


Cikin rashin fahimta tace "Amma Kaka in Kuma wacce aka sa aikin ta rigani Isa gun fa?"


"Kar ki damu sun San Shirin, don kowa a matse yake, had'in kanki kawaii muke bukata"
"Okay, Amma me zanyi a part d'in sa?"


Yace "Zan had'a ki da wacce zata fad'a Miki abinda za kiyi, yanzu ki Tashi ki shirya akwai inda zamuje"


"Ai a shirye nake Kaka hijab kawaii zan d'auka"


Murmushin gefen baki yayi yace, "Ina nufin kije kisa Uniform d'in, naga kina sa wani katon hijab in zakiyi sallah ko?"


"Eh"
"Yauwa to, idan Kika sa Uniform d'in sai kisa hijab d'in Kar Yan gidan su gane"


Tace "Toh" sai ta shige d'akin su, taci sa'a Ba kowa a d'akin tayi saurin sa kayan sannan ta sako hijab ta fito a dai dai lokacin da Daniyah ke kokarin kusa kanta cikin d'akin, Daniyah kallon Daliyah take Tace "Liyah har lokacin sallah yayi?"


Hararar ta tayi Tace "kina nufin bana sa Hijab sai in zanyi sallah Kenan ko me kike nufi?"


"A'a maida wukan me yayi zafi shi ba wuta ba? gani nayi sai zakiyi sallah kike sa wannan hijabin Amma Allah ya huci zuciyar ki"


"Ameen"


"Toh ko fita zakiyi ne na rakaki?"
"Innalillahirraji'un, Daniyah Wai ke Dan Allah yaushe Kika Koyi surutu haka ne haba Dan Allah"


"Daga tambaya sai cibi ya Zama Kari"
Murya Kaka suka jiyo yace "Ke Yar Birni Kin Gama Shirin ne?"


Daliyah Tace "Wai Kai Dan Allah har yanzu baza ka iya Kiran sunan Mutum ba? Muna Neman wata fa a garin Nan"


Kaka yace "Bazan iya ba gaskiya suna kaman sunan Aljanu"


Daniyah tayi Dariya Tace "Kaka Arabic name ne fa"


Yace "No wonder Mana Kinga Ni ba iya Kira zanyi ba sai ku, Ina Kakar ku take?"


Daniyah Tace "Granny ai ta fita yanzun Nan"
"Okay mu d'in ma fita zamuyi"


Daniyah tace "Kai da wa?"
Yace "Ni da Mata ta Yar larabawa Mana"


Daniyah Tace "kana nufin Liyah?"
"Eh Mana waye in ba ita ba?"
"Nima Zan biku"
Cikin saurin yace "A'a baza ki bimu ba yanzu zamu dawo"


Daniya tace "Haba Kaka Ni kad'ai zaku bari fa"
"Ga Nan mutane a gidan kice Ke kad'ai ce?"
"Gaskiya Kaka Sai na biku"


'bata fuska yayi kamar bai tab'a dariya ba, a tsawace yace "na fad'a Miki yanzu zamu dawo, wani lokacin sai mu fita dake, Ke Zo mu tafi"


Sai suka fice da shi da Daliyah, daniya mamaki ne yakamata a fili Tace "Anya lafiya kuwa? Tunda nake ban taba ganin Kaka ya b'ata rai ba kullum cikin Dariya yake, Liyah ma duk jikinta a sanyaye, Allah dai ya Sa lafiya."


Suna fita Kaka ya zaro wayar sa daga aljihun sa yayi dialing wata Number kara wayar yayi a kunnen sa duka biyu aka d'aga, yace "Mary kina ina?"


Daga d'ayan b'angaren naji ta ce "Ina gida Kaka"
"Okay to ga munan zuwa"
Tunda suka Fara tafiya babu Wanda yace komai, sun d'au lokaci Kan su Isa, suna Isa Kai tsaye suka Shiga gidan.




Mary na ganin su tace su shigo parlor tana leke leke, Kaka yace "Hope ba kowa a gidan?"


"Eh ba kowa, ku shigo mu Gama maganar Kan wani ya shigo"


Cikin sauri suka Shiga Basu ko gaisa ba, Kaka yace "gata Nan itace zata yi abinda Vero ya kamata tayi"


Mary Tace "Ya sunan ki?"
"Daliyah" a takaice, "Okay Kaka ka Sanar da ita ne?"


"A'a ban Sanar da ita ba, So nake ki fad'a Mata komai sanan ki kaita"


"A'a Kaka yau Kam bazaiyu ba"


A razane yace "Meyasa?"
Tace "Sabida a ranar da ya kamata ayi aikin ne aka kashe vero, na gama nawa sai wata na gaba"


Jiki a sanyaye Yace "Kina nufin yanzu shikenan har sai watan gaba"
"A'a Kaka sai gobe dai"


Dafe kirjin sa yayi ya jaa dogon Numfashi sannan yace "Thank God, toh yanzu me abunyi?"


Ta maida kallon ta tayi ga Daliyah Tace "Karfe shida Zaki Shiga gidan sarki, Zan had'a ki da wata don itace da aikin gobe, in Kika Shiga part d'in Yarima ki Fara gyara parlor Kan ki Shiga bedroom Karfe bakwai zai Shiga wanka zai d'au lokaci Mai tsawo a ban d"akin don wasu lokutan ya Kan Kai awa d'aya kiyi kokarin gyara komai Kan ya fito,Kinga Kenan zai kai Karfe takwas Kan ya gama komai, Karfe takwas sarki da matar sa suke fita don Shan iska suna har kusa da part na Yarima, Zaki dai dai ci wannan lokacin ki yi duk yanda zakiyi ki rungumi Yarima ki tabbata Sarki yaji ihun ki dole zasu shigo ya gan ku haka"


Daliyah cikin rashin fahimta tace "to Amma Meyasa? Amma kin San in sarki ya ganmu zai sa a kashe Ni ko?"


Murmushi tayi Tace "A'a ai cewa Zaki kin Zo gyara Masa d'aki ne ya nemi ya Miki fyad'e, Kinga dole zai sa a kashe yarima tunda ya sab'a doka"


Murmushi Daliyah Tayi Tace "Sai yanzu na fahimta Idan aka kashe Yarima komai zai dai daita, Amma Kuna ganin sarki zai kashe d'an sa?"


Kaka yace "Dole ya kashe shi in ba haka ba za mu Masa tawaye"


"Toh shikenan, zanyi"
Kaka yace "Nasan Zaki iya, tashi mu tafi gobe da safe sai ki fito"


Mary Tace "Zan jira ki a kofar gidan ku Karfe shida"


"Toh shikenan"
Nan suka Tashi suka tafi.


Wasu Emmata su biyu na gani suna tafe suna Hira d'aya daga cikin su Tace "Gaskiya Rose abinda sarki yake yi yayi yawa akan wannan Yariman da shi kansa baya tausayin kansa"


Rose Tace "Haba Meyasa kuke ganin laifin Yarima bayan Kun San cewa dokan sarki ne ba nashi ba"


"Amma ai sabida yaki yin aure shiyasa muka Shiga wannan takurar, do ke baza ki tab'a ganin laifin sa ba tunda saurayin ki ne shi in da gaske ya ke ya fito Mana ya aure ki ku hutar damu, haba sama da shekaru ashirin ake Abu d'aya shi Kan sa Yarima ya Fara tsufa"


"A haka nake son Kayana, Rahila baza ki gane bane sabida baki San mene ne so ba"


Tsaki Rahila ta jaa Tace "sai kuma kiyi I swear da ba don Ke Yar Uwata bace ko....." Sai ta fasa karasa maganar


Rose Tace "Rahila kin San Nice gaba dake Amma kike Gaya min magana son ranki har tsaki kike min?"


"Ai gaskiya na fad'a Miki, Ya fito ya aure ki mu huta"


Shiru kawaii Rose tayi don ita dama ba Mai surutu bace,sai suka wuce gida.




Bangaren Daliyah, tunda suka koma gida ta kasa samun nutsuwa, addinin ta bai halasta Mata tab'a Wanda ba muharramin ta ba, Amma tunda ceton Raine tasan Allah bazai kamata da laifi ba.


A cikin wannan tunanin ta kwana.


Washe gari


bayan ta idar da sallan asuba, ta d'auki uniform d'in ta Shiga ban d'aki ta sako su a jikin ta, ta Shiga d'akin Kaka ta iske shi a zaune tace "Kaka har ka Tashi?"


Daniyah tun jiya ta San
Ido akan shige da ficen Liyah, hakan yasa duk motsin ta Akan idon tane, shiyasa tana fita ta bi bayan ta ba tare da ta sani ba.


"Ina Daliyah ai ban samu damar yin baccin bama kwatakwata"


"Meyasa"
"Hankalina ya kasa kwanciya Sam, gani nake kamar hakan da na Saki yi Kuskure ne"


"Kar ka damu Kaka babu abinda zai same Ni insha Allah"
Yace "Daba don aikin na bukatar sabon fuska ba ai da Mary ce zatayi"


"Hakane ba komai da yardan Allah, yanzu naga shidan ma ya kusa, Zan fita Kan mutanen gidan su tashi"


"Tare zamu tafi ai, bazan bari ku tafi ku biyu ba"
"Amma Kaka idan mutanen gidan suka tashi basu ganmu bafa?"
"Karki damu baza mu rasa yanda zamuyi ba, a yanzu dai bukatar mu shine plan d'in mu ya tafi dai dai"


"Toh Kaka tunda kace haka"
Yace "Tashi mu fita"


Daniya Jin hakan yasa tayi saurin komawa d'akin su, don Kar su ganta.


Fitan Kaka da Daliyah yayi dai dai da isar Mary kofan gidan jikinta a sanye yake da uniform, Basu 'bata Lokaci ba su ka nufi gidan sarki.


Daniyah hankalin ta yayi mugun Tashi a ranta Tace "Wai me ke Shirin faruwa ne? gashi idan na fad'awa Granny baza taji dadi ba tana da hawan jini, Ya Allah ka Kare min Yar Uwata kasa ba cutar da ita zasuyi ba"
Ta koma ta kwanta cike da fargaba.


Suna Isa gate d'in suka tarar da wata ita ma uniform d'in ne a jikinta, Mary Tace "Chioma everything is ready right?" Murya kasa kasa


Chioma ta amsa "Yes everything is cleared" sai ta riko hannun Daliyah tace "zo mu tafi, Amma ya naga Bata da uniform?"


Daliyah Tace "Sorry, I forgot to take off my Hijab" kallon Daliyah Chioma tayi mamaki ne ya kamata Tace "Oh so you can speak English? I thought you hausa people can't speak English"


Daliyah Fizge hannun ta tayi, Tace "Why do you people always underrate us? You consider us as illiterates which is very Wrong"


Kaka Yace "Calm down Daliyah take it easy this is not the right time for this"


Rai a b'ace Daliyah Tace "When is the right time? you are here hearing her insulting me you didn't take any action, you didn't even say anything,in fact I quit I'm not doing this look for a literates like you."




Tafiya ta farayi da niyar barin wurin, Mary ta riko ta tace "Daliyah please don't take this personally, I think you are over reacting"


Daliyah Tace "over reacting right? So be it I'm not doing this"


Kaka Yace "Please

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads