Showing 54001 words to 57000 words out of 66367 words
Chapter 19 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
Allah ina so ka fad'a min Meyasa baka sona? Ko dai akwai Wacce kake sone?"
"Eh akwai Wacce nake so"
Liyah ji tayi kamar zuciyar ta zata fashe Amma tayi kokarin rike kanta Tace "Wace ce?"
Murmushi yayi yace "ce Miki akayi ban da hankalin da zan fad'a Miki don ki Samu damar illa ta min ita ko?"
Gujeran da ke gaban ta ta jaa ta zauna sannan Tace "Ko kad'an wallahi ba haka bane ko ba komai anyi zaman mutunci kawai so nake na San Wace Ce"
Huci yayi yace "Liyah tunda nake ban tab'a son ki ba dai dai da kwayar zarra bake kad'ai ba ban tab'a son wata 'ya mace ba sai mace d'aya Wacce ta canza Ni ta Maida Ni mutumin Kwarai"
Cikin Rawar murya Tace "Wace ce haka Kuma me ta maka?"
"Kyakkyawa ce son kowa kin Wanda Bai samu ba, Haki ka Allah ya Mata hallita Mai kyau gami da kyawawan Hali, Wanda halayen ta masu kyau ne suka sa na fad'a Soyayyar ta,sannan ita ce sanadiyar samun kwanciyar hankali na da family na"
"Naji naji yabon ya Isa haka nidai so nake na San Wace ce"
Murmushi yayi yace "Aniyah nake so"
A zabure ta mike Tace "What? Wace Aniyah?"
Shima tashi yayi yace "Aniyah d'aya Wacce Kika sani na sani ita nake so Kuma na ke kauna"
Cikin kuka Tace "Meyasa Sageer mene ne Wanda take dashi Dani bani dashi Kar ka manta kamannin mu d'aya"
"Fuskar ku d'aya hakane Amma Aniyah na da abubuwa dayawa Wanda Kika rasa"
A tsawace Tace "Mene ne wannan Dani bani dashi?"
Shima ihun yayi yace "Zuciya Mai kyau Aniyah tafiki da zuciya Mai kyau, Amma ke Kanki kawai Kika sani, Aniyah tafi damuwa da damuwar wani akan nata"
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un har Kai Sageer kowa Aniyah Aniyah Aniyah"
"Eh harni sunan Aniyah Yanzu Kika Fara ji sabida ita Yar halakce"
Tasss tasss maruka biyu masu zafi ta shafa Masa sannan Tace "I hate you" sai ta fice da gudu tana kuka.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ya dai Fans na daina ganin comments dinku, ko dai ya daina burge ku ne, Ni don ku nakeyi idan Baku so sai na dakatar dashi😔😢
Please wa anda suke wattpadd ku daure ku Rika min Comments da Vote
Taku a kullum Milhat
Yar terawa
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu''' .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
Follow me on Wattpad
@milhaat🙏🏻
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Not edited
```PAGE```2️⃣6️⃣0️⃣↪️2️⃣7️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un har Kai Sageer kowa Aniyah Aniyah Aniyah"
"Eh harni sunan Aniyah Yanzu Kika Fara ji sabida ita Yar halakce"
Tasss tasss maruka biyu masu zafi ta shafa Masa sannan Tace "I hate you" sai ta fice da gudu tana kuka.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
............a tsawace Tace "Ina take? Ina take munafuka yau asirin ki ya tonu"
Cikin sauri Mummy ta fito daga kitchen hannun ta rike yake da cokalin miya sa alama girki take Tace "Liyah lafiyan ki kuwa? Meyasa kike Mana ihu a gida?"
Rai a b'ace tace "Mummy Ina munafukar yarki take?"
Cikin rashin fahimta mummy take kallon ta Tace "Munafuka kuma? Liyah Ni ban haifi Munafuka ba"
Murmushin gefen baki tayi ta d'aura hannu a kwankwaso Tace "Mummy Baki dai sani ba wallahi kin haifi Munafuka"
A tsawace mummy Tace "Ke Liyah ki shiga taitayinki Kar ki kuskura ki Raina min hankali, me yake faruwa?"
Liyah ta fashe da kuka cikin sauri ta rungumi mummy tana fad'in "Mummy Sageer ta rabu dani yace min Aniyah yake so ba Ni ba"
Mummy ta d'an dage ta d'aga jikin ta tana kallon cikin kwayar idon ta Tace "Liyah na Sha fad'a Miki ki daina yiwa Yar uwarki kazafi ya kamata ki daina zargin ta"
"Haba mummy Meyasa baza ku yarda da magana ta bane, wallahi wallahi Umma shi da bakin sa ya fad'a min cewar Aniyah yake so"
"Ikon Allah wata gaskiyar Mahaifin ku da yace Sageer na so ya rusa Masa iyali, shi Kuma ya zai Mana Haka? Ya soki ya so Yar Uwar ki?"
"Hmmm mummy ba laifin Sageer bane duk laifin Liyah ne"
"Subhannallah liyah ke baza ki daina d'aura wa Aniyah laifi ba yanzun Nan fa Kika ce min shi yace Miki Yana son ta Amma Kuma kice laifinta ne? Ko itace tace Miki tana son sa?"
"Mummy Amma....."
Sallamar Aniyah ce ta katse ta, Aniyah Tace "Mummy lafiya ya na ganku haka kunyi curkocurko?"
Kirkiran Murmushi mummy tayi Tace "A a bakomai cewa tayi na bata magani kanta na ciwo"
"Kanta na ciwo Kuma Ni banji komai ba? Ko Shiyasa ki kuka d'azu?"
"Eh" kawaii Tace Mata, Aniya Tace "Ayya sannu Allah ya sauwaka" ta amsa da ameen.
Aniyah Tace "Mummy munyi bako fa?"
"Bako da yamman Nan? "Amma wane ne?"
Murmushin tayi Tace "Mummy Bari na ce Masa ya shigo is a surprise"
Liyah kokarin barin gun take Aniyah Tace "Liyah ki tsaya Mana kiga bakon namu?"
Tab'e baki tayi Tace "Toh" ta nemi wuri ta zauna.
Mummy Tace "Bari na aje spoon din Nan to"
Aniyah na fita Bata dad'e ba suka shigo tare da wani saurayi Wanda na kasa ganin fuskar sa dakyau.
Shigowar su yayi dai dai da shigowar mummy, mummy ba ganin su Tace "Wai Wai kice babban bako mukayi Sabir Kaine ka Zama Haka?"
Tsotsa keya yayi ya durkusa ya gaida ta cikin ladabi da biyayya ta amsa cikin farin Ciki da walwala sannan Tace "ka tashi man ga wuri Nan zauna"
Tashi yayi ya zauna, tunda ya shigo Liyah ke ta kallon sa a zuciyar ta Tace "duk kyawun Sabir da su Aniyah ke kod'a wa batayi tunanin ya Kai haka ba gaskiya ya hadu iya had'uwa, duk kyawun Sageer Bai kamo kafan sabir ba in ko Haka ne ya canza ko Kuma a baya ban Kare Masa kallo bane?"
Sabir yace "Our future Lawyer ba magana ne?"
Amma tayi nisa a tunani tana kallon sa, Aniyah dake a kusa da ita take sai ta tab'a ta, ta d'an razana kad'an cikin i'ina ce "na am"
Aniyah Tace "Sabir na Miki magana"
"Afwan please Ina wuni?"
Ya amsa da "lafiya kalau ya kike
"Alhamdulillah Ashe ka dawo naji baka kasar?"
"Eh na dawo"
"Toh ya karatun da fatan an gama lafiya?"
"Lafiyaa Lau ya naka?"
"Alhamdulillah muna Nan saura kad'an"
"Toh Allah ya taimaka"
Nan akayi ta Hira har Liyah ta manta da abinda Sageer ya Mata har Saida Sabir ta musu Sallama ya tafi.
Aniyah na kokarin Hawa saman su, Liyah tayi saurin jawo gashin ta wani Kara ta saka da sauri mummy ta fito ta na ambatan "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Liyah me haka ki sake"
Amma Liyah sai Kara jaan gashin ta take, ihun da Aniyah ke yi yasa Granny ta fito ganin suna fad'a abin ya Bata mamaki da sauri suka shiga tsakanin su, Aniyah na kuka Liyah Kuma sai huci take duk da ita kanta tana Jin zafi gashin ta, hakan bai Hana ta yi Mata mugun ta ba.
Granny Tace "Yau me zan gani Haka? Fad'a Liyah fad'a kike da Yar uwarki Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, me ya faru?"
Mummy Tace "Mama bar su shirme ce kawai irin nasu ku wuce ki Shiga daga Ciki"
Granny Tace "Kamarya su Shiga Ciki ku zo muje mu zauna ya sai naji me ke faruwa a tsakanin ku duk tsarin Rayuwar ku ta canza kun daina cin abinci tare Kun dai na Sa Kaya iri d'aya hatta Yar hiran Nan da kuke Kun daina"
"Mama ki rabu da yaran Nan Dan Allah"
"Husnah na lura Kuna b'oye min abubuwa da dama a gidan Nan da ke da Hafeez ko don ban haife ku bane oho"
Da sauri Mummy ta karaso inda Granny take tace "Haba Mama ya zakice haka? Nasan ke ba mahaifiyar mu bace Amma kin Mana abunda mahaifan mu Basu Isa su Mana ba, Dan Allah kiyi hakuri ki daina fad'an haka Ni da Kai na zan fad'a miki, akwai wani yaro d'an makarantar su sunan sa Sageer....."
Nan ta jero Mata komai tun daga farko har karshe, Granny wuri ta samu ta zauna tana jinjina wannan al'amarin Tace "Liyah Meyasa? Umm Meyasa kike haka haba Dan Allah ki duba kiga kina d'aukan alhakin Yar uwarki Karki bari so ya rufe Miki Ido"
Liyah tace "Granny ba wannan ba naji kince baki haife su ba, kina nufin ke ba mahaifiyar Daddy ba Kenan ko kuwa me? Na kasa fahimta?"
Aniyah Tace "Nima tunanin da nake Kenan"
Granny rarraba Ido kawai take don ita Sam Bata San lokacin da ta fad'in hakan ba tabbas idan Rai ya b'aci hankali yana gushewa.
A tsawace Mummy Tace "Ashe Baku da hankali ban sani ba? Akan me zaku sata a gaba Kuna interrogating d'inta?"
Murmushin gefen baki Liyah tayi Tace "Toh Mummy mun sa ta a baya, Amma Ina so ke ki fad'a Mana gaskiyar me ke faruwa"
Shiru mummy tayi ta rasa me zatace har Saida zufa ya Fara keto Mata, Aniyah ganin hakan Tace "Liyah is okay tunda Basu shirya magana ba ki Kyale su idon lokaci yayi zamu sani"
A tsawace Tace "Ke Munafuka Ni ba dake nake ba ki daina Shiga harkata kin gane ko?"
Tana Kai nan ta haura sama, Granny da Mummy jikin su duk yayi sanyi Aniyah Bata bar gun ba har sai da tabbatar sun Zama normal.
Tana Shiga d'aki ta zauna a bakin gado tace "Liyah Dan Allah ki tashi muyi magana ta fahimta Dan Allah" da farko Taki kulata ganin ta nace yasa ta tashi Amma ba don ta so ba.
Aniyah Tace "Liyah please ina so ki sani Ni bana son Sageer ko kad'an Asali ma bai tab'a burgeni ba, Kuma kamar yanda kike son shi Nima Ina da Wanda nake fiye da tunanin ki, ya kamata ki rabu da Sageer d'in Nan ki rungumi Sabir wallahi Sabir Yana matukar Kaunar ki Kuma idan ya aure na tabbata baza ki Sha Wahala ba"
Tafi Liyah ta Shiga yi a fuskar Aniyah har sai da tayi Mai isanta Tace "Wow bravo, gaskiya kin wuce in da nake tunani ke duk mutanen gidan Nan suna Miki kallon mumina, Mai ilimi,Mai tausayin Ashe ba haka bane? Wato na rabu da Sageer sai ki samu ya aure ki ko?"
Rai a b'ace Aniyah ta tashi ta Tsaya "Liyah ya kamata ki sani ba tsoron ki nake ji ba Kar kiga Ina yin shiru ki d'auka Ina shakkar kine ina so mu zauna lafiya ne dake Amma na lura ke bakya ganin hakan"
Tashi Liyah tayi Tace "lallai Kam wuyanki ya Kai na yanka, Ni kike yi was tsawa?"
Tana nuna kirjin ta.
Murmushin Aniyah tayi Tace "Kina mamaki ko? Sabida ban tab'a Miki haka ba ko? To ki sani daga Yanzu idan Kika min sai na Miki tunda dai ba tsoron ki nake ji ba"
"Bance kiji tsoro na ba, Kuma da kina so muyi sulhu kamar yanda Kika fad'a Zaki same Sageer kice Masa bakya son sa ya Soni ba ke ba"
"Zan tabbatar Miki da hakan yanzun Nan, bani number sa"
Ba musu ta b'ata duka biyu ya d'auka da Sallama ta amsa, Tace "Sageer Aniyah ce"
Sageer dake kwance yayi saurin tashi ya zauna cike da mamaki yace "Aniyah kece dagaske kece?"
"Eh nice ina so mu had'u mu tattauna wata magana"
"Okay kina Ina ne Yanzu nazo na same ki?"
"A'a ba yau na sai gobe zan Zo studio d'inka"
"Okay to shikenan sai na ganki"
Bata ce komai ba ta katse wayar ta fita daga d'akin.
Shi Kuma ya bi wayan da kallo, wata iriyar murmushi Liyah tayi Wanda yake cike da manufofi sannan Tace "hmmm Yarinya idan kin San wata Baki San wata ba"
Ita ma ta bi bayan Aniyah.
A dai dai sanda ta sauka taji Aniyah na fad'in "A'a Mummy Dan Allah ku raba Mana d'aki nikam na gaji don wallahi ta Fara turani bango"
Granny Tace "Aniyah yin hakan fa zai sake b'ata komai ne kiyi hakuri"
"Granny please Kar ku Hana mu raba d'aki idan na biye Mata wallahi za muji wa juna ciwo ne"
Muryar Liyah suka jiyo tace "To saime a raba d'akin Nima ba fi son hakan"
Mummy kasa cewa komai tayi takalli wannan ta kalli wanchan, Daddy da Huzaifa da Yusuf ne suke shigo da Sallama hannun su rike da ledoji, da alama shopping sukaje.
Daddy tsayawa yayi chak ganin duk su hud'un a tsaye kallon sunya Shiga yi d'aya bayan d'aya Kan yace "lafiya ya na gan ku haka?"
Aniyah ne tayi saurin fad'in "Daddy so nake a raba Mana d'aki"
Daddy mamaki ne ya rufe shi yau Aniyah ce take neman a raba musu d'aki tabbas akwai gagarumar matsala, yace "Aniyah ke da Kan ki me aka Miki?"
Nan ta jero Masa komai, Daddy ransa yayi mutukar b'aci yace "Baza a raba d'akin ba in yaso ku kashe Kan ku, Aniyah ke da nake Miki kallon Mai hankali Ashe duk kanwar jaa ce, to Bari kuji wannan ya Zama shine na farko Kuma na karshe da zan ji an ambacin sunan ja'irin yaron Nan a gidan Nan, Kuma Kar ko Wacce daga cikin Ku ta sake had'uwa dashi, idan kunne ya ji" Yana rike kunnnen sa, Yana kaina ya bar palor fuu sai uban garen dake bin say baya, mummy ta bi bayan sa, Huzaifa da Yusuf suma suka shige d'akin su, Granny ma haka, sai ya saura Aniya da Liyah, tsaki Liyah tayi ta haura sama, Aniyah Kuma jikin ta ne duk ya mutu da kalaman da Daddy yayi mata "Ina Miki kallon Mai hankali Ashe duk kanwar jaa ce"
Jiki a sanyaye ta fita ta zauna a garden Bata shigo ba har sai da Taji Ana Kiran sallaar Maghriba ta shigo cikin gida.
*WASHE GARI*
Aniyah ta shirya zata wuce asibiti Liyah da sauri ta biyo ta parking space Tace "Zakije ganin Sageer d'in ko?"
Zaro Ido tayi Tace "Baki ji abinda Daddy yace bane yace Kar mu sake ganin sa?"
"To sai me ai ba zai Sani ba ko ke Zaki fad'a Masa, kin San daini bazan fad'a Bako? Kawaii kije duk yanda ake Ciki ki fad'a min"
Huci tayi tace "kaaai A'a Liyah bazan je ba"
Rai a b'ace tace "Dama na San ke Munafuka ce to wallahi ko kije ko Kar ki sake kulani kinji na gaya Miki"
Tana kokarin barin gun sai ji tayi Tace "Zanje" da sauri ta Juyo Tace "Dagaske kike Zakije?"
"Eh da gaske Zanje"
Murmushi tayi Tace "Karfe nawa kin San Bai cika Zama a studio ba"
"Karfe biyu zamu tashi Kan three zan Isa ai"
"Okay by then Zaki same shi"
"Okay to"
Tana kokarin Shiga motar ta Liyah ta rungume ta Tace "Thank you"
Sannan ta shige Ciki.
Murmushi Aniyah tayi Tace "Oh Liyah halinki sai ke" ta shige motar ta, ta fice daga gidan.
Liyah na ganin Aniyah ta fita ta tunsure da dariya, tasa hannun ta duka biyu a kwankwaso tace "Yanzu aka Fara wasan sai kin Raina Kanki"
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Mu had'u a page na gaba
Milhaaat ce Yar terawa yawan comments yawan typing😤
Masu using Wattpad bana ganin comments dinku da vote Dan Allah ku Rika min.🙏🏻
🌎 *MANAZARTA WRITERS* *ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
'''Kungiya d'aya tamkar da dubu''' .
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
✨✨ *DALIYAH*✨✨
*Da*
✨✨ *DANIYAH*✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_(A Sympetic,love and a funny Story)_
'''Story and Written by'''
'''Fadeelah Yakub (Milhaat)'''
Follow me on Wattpad
@milhaat🙏🏻
*DALIYAH da DANIYAH* Labarine Wanda ya kunshi Soyayya Tausayi, fad'akarwa, nishad'antar gami da ilmantarwa.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Not edited
```PAGE```2️⃣7️⃣0️⃣↪️2️⃣8️⃣0️⃣
Murmushi Aniyah tayi Tace "Oh Liyah halinki sai ke" ta shige motar ta, ta fice daga gidan.
Liyah na ganin Aniyah ta fita ta tunsure da dariya, tasa hannun ta duka biyu a kwankwaso tace "Yanzu aka Fara wasan sai kin Raina Kanki."
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
.............."hello gani Ina waje"
"Okay ki shigo Mana"
Ba ta d'au lokaci ba ta shigo, Yana ganin ta sai washe baki yake Aniyah Kuma bata na San yanayi ba, wani d'aki ya nuna Mata su Shiga ba musu ta bi bayan shi.
Suna Shiga juyowar da zanyi sai na hangi Liyah na leken su a hankali ta shigo ta rufe kofan ta baya sai ta shige wani d'aki dake kusa da Wanda suka Shiga, Murmushi Naga tayi ta zaro waya ta cire sim d'inta ta d'aura wani sim d'in, ta dad'e tana Kira Kan akayi picking handkerchief tasa ta d'aure wayan ta canza murya banji me ta ce ba na ga ta katse wayar had'e da cire sim d'in Nan take ta karya sim d'in, sai leke take ko wa take jira sai Allah.
'bangaren su Aniyah Kuma sun Shiga ya ce "Bismillah ki zauna" Yana nuna Mata kujerar dake gefen ta, kallon kujerar tayi sannan Tace "Ba Zama nazo yi ba Irfan, nazo ne mu yi magana da Kai"
Shima kasa zaman yayi ya tsaya Yana kallon ta yace "Toh Ina sauraron ki Amma maganar ta mene ne haka?"
Gyara tsayuwar ta tayi Tace "Irfan I never expect this from you Meyasa zakayi haka?"
Cikin rashin fahimta yake kallon ta yace "Look Aniyah ban fahimce ki ba maganar da kike ba, me kike nufi ne?"
Langwabe Kai tayi tace "Maganar Liyah nake yi me yasa zakayi Mata haka? Bayan kasan irin Kaunar da take maka haba Irfan"
Murmushi yayi yace "Hakane nasan tana Sona Ni Kuma ke nake so, laifina ne da Allah ya d'aura min sonki?"
Dafe Kai tayi Tace "Oh Allah na nikam na rasa yanda zanyi da Kai, Kai da Liyah Kuna kokarin haukata Ni, ban Zo Nan don Jin wannar maganar ba, Dan Allah ka yi hakuri ka aure ta dan Allah, na roke ka, ta d'auki laifin duk ta d'aura min alhalin ba laifina bane ba"
"Zan so ace wata alfarma kike nema da na Miki Aniyah am sorry bazan iya Soyayya da ita ba"
Cikin sanyin murya Tace "but why? Why Irfaan"
Ya marairaice yace "sabida halayyan ta basu min ba, tana da son kanta da yawa ga kishi kamar Wacce batayi makaranta ba, Amma ke kinfi fifita damuwar wasu Akan ki, Aniyah Ina Kaunar ki ne ba don komai ba sabida kece silar shiryuwata kin zama tamkar hasken fitila acikin Rayuwa ta bana tunanin zan iya son wata bayan ke Kuma a shirye nake na zauna ba tare da nayi aure ba har karshen Rayuwa ta"
Aniyah iska Mai zafi ta hura sannan Tace "Nasha fad'a maka cewar bani bace Wacce kake tunani it's just an misunderstanding please ka Auri Liyah"
A tsawace yace "nooo I won't" har Saida ta tsorata Tace "Toh shikenan na barka lafiya"
Liyah na Jin karar anyi parking na mota a waje ta leke ganin motar yasa Tace "Good shine"