Showing 1 words to 3000 words out of 66367 words
Chapter 1 - DALIYAH da DANIYAH By FADEELAH YAKUBU MAHDI (Milhaat) (1).txt
✨✨ *DALIYAH* ✨✨
*DA*
✨✨ *DANIYAH* ✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_*(A Sympetic,Love and Funny Story)*_
```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```
*Daga Marubuciyar*✍🏻
*MATAR AURENAH*
*SAIRA DA SARAH*
*AND NOW*
*DALIYAH DA DANIYAH*
_(Cigaban Sairah da sarah)_
*DALIYAH* da *DANIYAH* , ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya, tausayi,fad'akarwa, nishad'antarwa gami da ilmantarwa.
```
*Note_* ```bamu yarda wani ko wata su juya Mana labariba tare da izinin mu ba.```
Ya Allah Ina rokon ka da ka bani ikon gama Littafin Nan kamar yadda na ra.Ameen
Labarin *Daliyah* da *Daniyah* k'ageggen labarine ban kirkirin Labarin Nan don cin zarafin kowa ba.Allah ubangiji ya datar da mu.
Ameen....
*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu (Milhaat)*✍🏻✍🏻
🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.
🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*BISMILLAIR RAHMANIR RAHIM*
*PAGE* 1️⃣↪️1️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY ON SAIRAH DA SARAH
```
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Idan baku manta ba sairah da Sarah ya Kare ne a dai dai inda Sarah ta rasu sannan Sairah ta Auri John Wanda a yanzu ya musulunta Wanda sanadiyar musuluntar da yayi ne aka sa Masa Suna Hafeez, Mama Larai ta musulunta, yayin da aka sawa Yaran da Sairah ta Haifa Suna Daliyah da Daniyah, bayan rasuwar Sairah, Hafeez ya auri Yar Laraba mai Suna Husnah in baku manta ba Laraba qawar Mama Larai.
Mama Larai mahaifiyar Sairah da Sarah, Hafeez, Husnah, Daliyah da Daliyah, Sai Kanwar Husnah Mai Suna Uwani, Sai Huzaifa da Yusuf sune 'ya 'yan da Yusrah ta Haifa wa Hafeez zaune suke duk a gida d'aya hakan ne yasa Hafeez, Yusrah da Uwani suke Kiran Mama Larai da Mama, Daliyah da Kannen ta Kuma suke Kiran ta da Granny, sannan suna Kiran Mahaifan nasu da Mummy da Daddy.
*Wannan Kenan*
Zuwa yanzu Daliyah da Daniyah sun girma suna da shekaru 16 a duniya, a yayin da Huzaifa yake da shekaru 14 Yusuf Kuma 12.
Daddy na gani Yana saukowa daga steps da shigar sa irin ta alfarma, tafe yake Yana gyara babbar rigar sa, a bayan sa kuma Mummy na gani rike da brief case d'insa da alama fita zeyi suna tafiya suna irin hirar su ta masoya.
Uwani na gani sanye da uniform tana zaune a dining table tana breakfast, ganin su Daddy yasa ta suguna har kasa ta gaida su, suka amsa ba yabo ba fallasa.sai daddy yace "Uwani!!! Ina yaran Nan suke?"
"Yusuf da Huzaifa school bus ya Zo ya d'auke su"
Mummy tace "Twins d'ina Kuma fa?"
"Suna d'akin su"
Daddy yace "Wai har yanzu basu gama shiri ba? yaran Nan dai ban San yaushe zasu Fara son makaranta ba, musamman ma Daliyah wacce itace babba Amma bata ji duk ita ce take b'ata kanwar tata"
Yana idar da maganar da yake ya nufi d'akin su, Daniyah, na gani a zaune sanye take da uniform d'inta, skirt d'in maron sai farar short sleeve, gashin kanta a tsefe ta Kama shi da farin ribon, sannan tasa farin canvas, Kamar su d'aya da Sarah Kai kace ita ce ta haife su, duk da dai dama Sairah da Sarah identical twins ne.
Daddy yace "Kaai uban me kuke jira baku gama shiri har yanzu ba?" Cikin tsawa
Daniyah a tsorace ta kalli kofar don ita Sam Bata San Daddy ya shigo ba, rarraba ido ta Shiga yi baki na rawa don ta San halin Daddy sarai karamin aikin sa ne ya zane ta.
"Ke don ubanki ba magana nake Miki ba Kinyi min shiru"
"Umm umm, dama....dama..."
"Da ma me?" A tsawace
"Dama Daliyah nake jira bata gama ba"
Karan bud'e kofa, Daliyah na gani ta fito kanta ba d'ankawali gashi ba a gyaree ba, Daddy kallon sama da kasa ya Shiga yi mata, yace "Ke" a tsawace Daliyah ta tsorata hanjin cikin ta suka kad'a har ji tayi kamar tayi fitsari a wando, har ta bud'e kofar ban d'akin da niyar komawa ciki, yace "Ina kuma Zaki? Will you come back here?" murya na rawa Tace "Daddy Good morning"
Daddy yace "What is Good about Morning?"
Tayi shiru bata ce Masa komai ba.
Ya sake Mata magana a karo na biyu, "am asking you, what is good about the morning?, Daliyah ba da ke nake ba?"
"Daddy me Kuma nayi?"
"Okay tambaya ta ma kike? Bari ki gani"
Kalle kalle ya Fara a d'akin idon sa ya fad'a akan wani belt, d'auka belt d'in yayi ya nufi Daliyah, Daliyah na ganin hakan ta fita a guje, tana neman agajin Granny, Shima Daddy da gudun gaske ya bi bayan ta, ihun Kiran sunan Granny take Amma Kash Kan ta Kara sa Daddy har ya karaso ta, duka ya Fara Kai Mata ta ko ina tana ihu tana neman agaji, Daniyah ita ma tana chan tana ihu, mummy tayi kokarin ta kwace ta Amma ta kasa, ita tsoro ma take Ji don Bata manta sanda tazo karban ta ba, Daddy Yana sane ya shaud'a Mata har Saida gun ya Tashi shiyasa Bata karban su.
Mama naji, ta sauko da sauri tana ta zuba uban masifa "Hafeez!!! Hafeez baza ka bar dukan yarinyar Nan ba, ko so kake sai ka kashe su?"
Daddy ko a jikin sa don Baya ma jinta har Saida Mama tazo ta kwace belt d'in "Hafeez a Koda yaushe Ina fad'a maka duka baya gyara yaro Amma kaki ji, dubi yadda ka ji Mata ciwo, Kai Kan ka dubi yadda ta yaga ma Riga, ta wani chakume Ni sai kace Ni sa'anta ko da ma niyar ta ta dake ni" ya kara maganar kamar numfashin sa zai d'auke, ran maza ya b'aci.
"Mama ai yagan min rigar da tayi shiyasa na Kara Mata dukan akan Wanda nayi niyar yi Mata jiya jiyan Nan fa na karb'o d'in kin nan, Kuma yadi d'aya dubu goma Amma ki duba Kika yadda ta yaga min Riga ta min asara"
Mama Tace "Yooo ai ka Taki sa'a tunda akan garen ta tsaya"
Mummy da Uwani kuwa Dariya suke kasa kasa, kallon da ya musu ne ya sa sukayi shiru, Daliyah jin Mama na masifa sai Kara ihu take tana birgima tana buga kafanta a Kan tiles, muryar Daniyah suka jiyo da sauri mommy da Mama suka haura d'akin, Daddy ya Riga ya San dukan da yayi wa Yar uwar tace ita ma ya shafe ta duk sai yaji ba dad'i.
Maida kallonsa ya yi ga Daliyah "ke Tashi kiyi kneel down" jiki ba kwari ta yi kneel down, kallon ta yake ya ma rasa yadda zeyi da Daliyah, bata tsoron duka ko fad'a Yar karamar tsaki ya jaa sai yace "Maza kije ki shirya Kar ki kuskura na fito baki Gama Shiri ba"
Ya wuce d'akin sa, Dalilyah na Shiga ta samu Mama da Mummy na rarrashin Daniyah, Daliyah Bata Jin Dad'in irin halittar Nan nasu, Wai ace duk abinda akayi wa d'aya sai d'aya taji, jiki ba kwari ta Shiga ban d'aki tayi wanka, ba ta dad'e ba ta fito ta shirya, Mama da Mummy sukayi ta mata fad'a, "Haba Daliyah ke kulluma a dalilin ki Yar uwar ki take kuka, ke yanzu baza kiyi wa kanki fad'a ba?"
"Mummy nifa na Ce muku bana son makaranta, wallahi takura ni yake lokacin da ya kamata mutum yayi bacci sai a wani ce school"
Mama Tace "Ke ko islamiyar ba son zuwa kike ba, Ni banga Rana d'aya da zaki ce ga abin da kike so ba, ke komai bakya so"
Mummy Kama hab'ar bakin ta tayi Tace "Oh ni Yar su Daliyah Ni kike fad'a wa haka?"
Mama Tace "Daliyah fa sai gyaran Allah"
Tsotsa keya ta Fara yi tace "Am sorry mummy, Sisto tashi mu tafi" a tare suka fita, Daddy da Uwani suka tarar a dining, Nan suka shiga cin abinci, Daddy ya fita don dama tafiya zeyi, zashi lagos, Uwani, Daliyah da Daliyah makaranta d'aya suke, Uwani na ss 1, Daliyah da Daniyah Kuma jss 2 Daliyah na Jss 2A Daniyah Kuma 2B, suna fita already driver na jiran su, Driver d'insu dabane ne Wanda shi aikin sa kawaii ya Kai su makaranta in Lokacin Tashi yayi ya Koma ya d'auko su.
Suna Isa ko wacce ta nufi ajin su, Daniyah na Shiga akasa ta kneel down, Daliyah Kuma ta window ta zaga taga Malamin Yana rubutu a allo, Mikawa yarinyar Dake kusa da window jakar ta tayi sannan ta haura tana Zama, Sai Malamin yace "Daliyah sannu da zuwa ko?" Yana maganar ba tare da ya kalli inda take ba, turo baki ta Fara yi tana wurga Masa harara.
Saida ya Gama rubutun sannan yace "Daliyah fito Nan" Tashi tayi tana tafiya kamar kwai ya fashe Mata a ciki tana jaan kafa, Yace Mata yi kneel down, "Meyasa kika makara? Me yasa baki gaishe Ni ba? Meyasa Kika shigo min ta window?"
Tace "Chaaap lallai ma Uncle duk tambayoyin Nan Ni kad'ai Zan amsa maka su?"
"Eh kuma yanzu nake so ba anjima ba"
Saida ta Harare sa sannan tace "Ni wallahi bazan iya ba , ai ko tambayoyin kabari iya ka Kenan"
"Okay tunda kince haka Zo ki kwanta a Kan table d'in nan"
A zuciyar ta Tace "Yama fi sauki, Daniyah Kuma sai dai tayi ta hakuri da Ni"
Uncle yace "Kiyi min sauri I have a lot to do"
"Uncle Wallahi Ina da maruru"
"Maruru a Ina haka?"
"Uncle a mazauni na" duk Yan class d'in sai da sukayi dariya, yace "Kar ki damu bulala na zai fasa Miki"
Tana kwanciya yayi ta shaud'a Mata bulala, ganin fa Malamin Bai da niyar bari sai Tace "Uncle ya fashe, wallahi ya fashe" "A'a Daliyah bari dai na Kara Miki" sai da ya Mata bulala kusan 50, sannan ya kyaleta taje ta zauna Yan class Kuma duk dariya suke Mata, Daliyah Tace "Zaku sani ne Allah ya had'a mu" sai naji wuri siit kamar ba kowa, da alama tsoron fa suke.
Wannan karon Daniyah Bata ji zafi ba sai hawayen da ke kwararowa daga Idon ta, Aunty Maryam malamar su Daniyah na kallon ta don inda sabo ta Saba ganin hakan, Daniyah Kuma tasan cewa Yar Uwarta ta sake yin wani abun.
Bayan Sun fita break, Daliyah da qawarta wacce ta Mika wa Jaka,Mai suna Fareedah, Fareedah Tace "Daliyah ke meyasa baki da tsoro ko kad'an ne?"
"Mtwwws tsoro ai sai ku Kinga na Miki Kama da Matsoraci ya ne?, Ni fa babban Burina Na shine naga nayi maganin Uncle Ameer"
"Kike so ko nake so? Daliyah Baki San yanda nake Jin haushin Uncle Ameer ba, Kuskure kad'an sai duka mtwss"
"Allah ko mutuniyar, Ina da plan matso kusa na fad'a Miki yanda zamuyi"
Kus kus naji sukeyi tana Gama fad'a Mata, sukayi shewa har da tafi, Daniyah na gani ta Zo ta zauna a kusa da Daliyah, Tace "Dariyar me kuke haka?"
Daliyah tace "Ke dai bari kawaii"
Biscuits suka Ciro da gorar ruwa suka sha, Basu dad'e ba suka Koma class.
*Bayan an tashe su*
Uncle Ameer na tafiya Daliyah da Fareedah na biye dashi, ba tare da ya sani ba, Staff quarters yake da Zama, Bai da nisa da school d'in su, Fitsari yake ji sosai da niyar sa sai ya Isa gida zaiyi Amma ya matsu, Wani uncompleted building ya hango da sauri ya Shiga sai ya aje test books d'in hannun sa a nesa dashi, Bai Ankara ba Daliyah da Fareedah suka kwashe test books d'in cikin sand'a Suka fice.
Bayan Uncle Ameer ya gama ya dawo don d'aukan test books d'in ga mamakin sa yaga wayam babu ya duba Amma Babu ya fito ya tsaya a bakin titi Amma ba kowa yace "Ikon Allah, da hannu na aje test books d'in Nan, Amma ace Babu ko dai wani ne ya shigo? Kaai Babu Wanda ya shigo ko dai aljnu ne, Kai Amma na Shiga uku Test books 5 ko wanne dubu hamsin,Allah ka fid Dani."
Yana tafiya Yana suratai, har ya Isa gida jiki ba kwari, Bangaren Daliyah da Fareedah Kuma, bakin gate na makaranta suka Koma, Daniyah duk ta damu sabida rashin ganin Yar Uwarta, gashi driver yazo Uwani sai kana Nan surutai take, Dalilyah Tace "Toh gani ana Nan ana ta gulma" Uwani Tace "Ke Daliyah Ni kike fad'awa haka, sai na fad'awa Daddy"
Daliyah Tace "To sai me in kin fad'a Masa iya ka ya dake Ni ne"
Daniyah Tace "Please Aunty Khadee Kar ki fad'a masa, Kinga duk mu biyun muke Shan azaba dazu ma Ina ga an dake ta"
Iska ta hura Mai zafin sannan Tace "Shikenan Daniyah, bazan fad'a masa ba, ke Kuma Daliyah Allah ya shirya Mana ke"
Daliyah Tace "Ameen Uwani"
Daniya Tace "Haba Dan Allah Wai ke yaushe Zaki daina kiranta da sunan Nan, Daddy fa ya Mana warning mu Rika Kiran ta da Aunty Khadeeja"
"Wannan Kuma ke ta shafa."
Fareedah Tace "Daliyah Zan tafi da Books d'in na ajiye ko?"
"Eh ki tafi da su"
Daniya Tace "Wani books?"
"Kaai Kaai Daniya dad'i na dake shishshigi"
Tab'e Baki kawaii Daniyah tayi tana kallon ikon Allah
Driver yace "Ku Shiga mutafi mun b'ata lokaci" fuska a tamuke
Fareedah ta musu bankwana Ita ma ta shige Motar Gidan su.
*Washe Gari*
Yau da wuri Daliyah ta shirya don har ta Riga Daniyah.
Daliyah ta ce "Daniyah belt d'in jiyan Nan na wane ne?"
"Ina ga kamar na Huzaifa ne"
"Toh wallahi zai gane kuren sa, akan me zai aje Mana belt a d'aki ba su da d'aki ne?"
"Allah sarki Daliyah Shekaran jiya da na Masa home work ne ya manta anan kin San bazaiyi hakan ba da gangan ba"
"Whatever wallahi yanda naji zafi Shima haka zaiji sai jikin say ya gaya Masa"
Daniyah tun da ta lura Daliyah da gaske take sai ta yi shiru ta kyaleta.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
Mu had'u a page na gaba
MIILHAAT CE Yar Terawa🥰
✨✨ *DALIYAH* ✨✨
*DA*
✨✨ *DANIYAH* ✨✨
_(Cigaban Sairah da Sarah)_
_*(A Sympetic,Love and Funny Story)*_
```Story and written by Fadeelah Yakubu (Milhaat)```
*Daga Marubuciyar*✍🏻
*MATAR AURENAH*
*SAIRA DA SARAH*
*AND NOW*
*DALIYAH DA DANIYAH*
_(Cigaban Sairah da sarah)_
*DALIYAH* da *DANIYAH* , ```Labarine Wanda ya kunshi Soyayya, tausayi,fad'akarwa, nishad'antarwa gami da ilmantarwa.
```
*Note_* ```bamu yarda wani ko wata su juya Mana labariba tare da izinin mu ba.```
Ya Allah Ina rokon ka da ka bani ikon gama Littafin Nan kamar yadda na ra.Ameen
Labarin *Daliyah* da *Daniyah* k'ageggen labarine ban kirkirin Labarin Nan don cin zarafin kowa ba.Allah ubangiji ya datar da mu.
Ameen....
*Daga Alkalamin*
*Fadeelah Yakubu (Milhaat)*✍🏻✍🏻
🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
*M.W.A*
Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da aiki da ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.
🥰
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*BISMILLAIR RAHMANIR RAHIM*
*PAGE* 1️⃣0️⃣↪️2️⃣0️⃣
```PREVIOUSLY```
"Whatever wallahi yanda naji zafi Shima haka zaiji sai jikin say ya gaya Masa"
Daniyah tun da ta lura Daliyah da gaske take sai ta yi shiru ta kyaleta.
💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫💫
A Kan hanyar su ta komawa Gida, naga wani d'an saurayi a tsaye Wanda daga ganin sa sa'ar su Daniyah ne, da alama motar su ce ta b'aci, Daniyah tace "Uncle please ka tsaya, naga kamar motar su sabir" parking yayi sai ya fito yaga tabbas Sabir ne, Sallama sukayi da Driver d'in su Sabir yace "Hassan Lafiya me ya Sami motar ta ku?"
Hassan yace "Wallahi muna cikin tafiya motar ta tsaya"
Daniyah da Daliyah suja fito, suka gaida Uncle Hassan cikin girma mawa ya amsa, Daniyah Tace "Uncle to me zai hana Sabir d'in ya Shiga motar mu tunda duk hanyar d'aya ce"
Daliyah Tace "hakan yayi Kinga dama lokacin islamiya ya kusa"
Hassan yace "A'a Kar ku damu na Kira mechanic Yana hanya"
Sai driver d'in su Daniyah yace "Haba Kai kuwa Kar ka manta mu makwafta ne mun Zama Yan uwan juna"
"Toh Shikenan tunda kunce haka, Sabir ka Shiga sai na dawo"
Sabir ya amsa da "Toh Uncle"
Nan Suka shiga motar, suka nufi gida, suna Isa gida bayan sun Ci abinci sunyi sallah, sannan sukayi wanka sukayi Shirin zuwa islamiya.
A hanyar su ta zuwa islamiya, bayan driver yayi dropping d'insu, Daliyah ta Kama kunnen Hafeez tace "Kai don Ubanka kaje ka ajiye belt d'inka a d'akin mu don Daddy ya daken dashi ko?"
Nan muryar Hafeez ya Fara rawa ya ma rasa ya zai Kare Kan sa don "yasan halin Aunty Liyah, ba ta da mutunci ko kad'an shiyasa ya fi son aunty Daniyah ba ruwanta" Yana cikin wannan tunanin ne sai yaji tass tass maruka 2 masu zafi ta Masa, Bai San sanda ya Saki kuka ba don yaji zafin Marin sosai.
Daniyah ji tayi kamar ta Rama Masa Amma baza ta iya ba sabida tana girmamata duk da Yan mintuna ne a tsakanin, hakuri kawai ta Shiga bawa Hafeez a yayin da shi kuma kamar Ce Masa tayi ya Kara kukan.
Daliyah Tace "Kuttumelessi wato ma ka samu tana baka hakuri shine kake Mana ihu sai kace na yanka maka wuya, toh wallahi in baka yi shiru ba sai ka karya maka hakori, sai ji nayi yayi tsiit kamar anyi ruwa an d'auke, Daniyah dariya ta Shiga yi Tace "Ido wa ka Raina?"
Yusuf yace "Wanda na Saba gani kullum" duk sukayi dariya har da Mai kukan
Daniyah Tace "Aunty Khadee Kinyi shiru kina kallon mu Baki ce komai ba"
"Daniyah me zancen? Lamarin Liyah sai gaba gaba yake yi Yanzu nayi magana ta zage Ni, don kin San karamin aikin ta ne"
Daniyah murmushin takaici tayi sannan ta ce "Hakane Allah ya shirya Mana ita"
Duk suka amsa da amin, Amma Banda Daliyah sai Tace "Iko sai Mai Up, Yanzu gulman ma abun ya Kai ya kawo har a gaban idon ka ake yo taaaab"
Yusuf yace "Aunty Liyah gulma fa sai in a bayan idon ki ne shine Gul......"
Kan ya karasa Tace "Yusuf har da kai? Kai da nake ganin Kai nawa ne Ashe ba haka ba, toh wallahi Kai ma Zanyi maganin ka"
Yusuf yace "Haba My one and only Aunty Kar ki sa a Mana dariya Mana"
"Toh sai me ayi d'in mana."
A Haka har Suka karasa cikin islamiyar ko wanne da ga cikin su ya Shiga ajin su, Daniyah da Daliyah ajin su d'aya, Yaran suna da kokari sosai don duk sunfi yan ajin kokarin sai dai Daliyah an Mata shaida da