Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 155363 words

Chapter 14 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt

Ads the beginning of article before Image

Nanah Kd   

14 Jun 2024

1407

Ads at the middle of Article

ai da gaske nake,"

"nifa yau banga wulƙawan Auntie Nailah ba kwata kwata, Zaynerb tayi maganar.

Deejarh ta ce "ai lokacin da kika tafi makaranta ne suka fita ita da wannan ƙawan nata mai kama da jarumar india 'Pooja Hegde' ɗinnan, ni banmasan sunanta ba,"

"amma wallahi baki da kirki sadiqqa ce take kama da Pooja ɗin?," cewar Zaynerb tana dariya.

Dariya ita ma Deejarh tayi ta ce "Yasin Auntie wannan ƙawar Auntie Nailah ɗin, da pooja take kama har tsayin da hasken ɗaya, yanayin gashinta ne, kawai bansani ba."

"ke kuma a'ina kikasan tsayin pooja ɗin?, uwar ƴan sanin kamanni?,"
Lailah ta tambaya, Deejarh ta ce "a cikin film mana,"
"wanne a ciki?," Lailah ta kuma tambayarta.

Ta ce "wannan wanda tayi ita da allu arjun ɗin mana na dai manta sunan shi ne."
"wai 'Alavaikunthapurramuloo' kike nufi?," Afeefah ta tambaye ta bayan ta faɗa sunan film ɗin, da sauri Deejarh ta ce "E, shi nake nufi.

Zaynerb ta ce "ai tafi jaruman india na yankin telugu kyau gabaɗaya."
Lailah tace "a'a wasa dai kikeyi ko amma me za'ayi da wata 'pooja' bayan gasu 'kajal aggarwal' a gefe,"

Zaynerb ta ce "wake maganar kajal, ai wannan ta tsufa,"
" a gurin ki ba, cewar Lailah, Afeefah ta ce "to Ladies a'ina kuka bar Rashi Khanna ɗin, gasu Tamannah Bhatia, Mehreen dasu Samantha duka a gefe,"
"faɗa ma ta dai sister," cewar Lailah ta ci gaba da cewa "ga kuma Shruti Hassan madam ina faɗamiki idanun nata kamar kamar me kyau da kyau aka haɗa fa."

Deejarh ganin suna magana suna haɗawa da turancine, gashi ita ba komai take fahimta ba, a zuciyarta ta ce "bari dai nima nayi turanci nan na haɗa da indian ci😎

Gyaran murya tayi sannan ta kalla Lailah dake kwance a 2sieter ta ce "Auntie Lailah na tambaye ki wani mana?,"
"inajinki da sauraronki cewar Lailah.
Deejarh ta ce "karfa kice bakyajin yaren da zan miki maganar dashi,"
Lailah ta ce faɗa mana baki da problem, to banda abinki Dije ta ƙauye yaruka goma nake ji fa, kuma duka na qware akan jinsu highly.

Deejarth ta kuma gyara zaman ta alamar za'a fara sannan ta ce.
"Menene is poonakaalu ahora?,"

Tashi zaune Lailah tayi tana faɗin, "ban fahimci me kike nufi ba, please ɗan maimaita muji, maimai tawa Deejarh tayi.

"Menene is poonakaalu ahora."

A hankali Lailah ta kuma maimai tawa ita ma, girgiza kanta tayi, "ke bansani ba, wannan ai hauka kawai kika haɗa."

"Ba hauka bane fa, tambaya tayi miki,"
Cewar Zaynerb kallon Deejarh Zaynerb tayi murmushi ta ma ta sannan ta ce.

"na farko dai da ta ce 'Menene' hausa tayi, na biyu kuma da ta ce 'is' turanci tayi, na uku kuma da ta ce 'poonakaalu' yaren telugu tayi, na huɗu kuma da ta ce 'ahora' yaren spanish tayi."

"Nifa wannan dogon bayanin, ba ganeshi nakeyi ba jeki gundarin magana kawai kai tsaye," cewar Lailah.

Da sauri Afeefah ta ce "tana nufin ta ce 'ƙarfe nawa ne' fa, shine ta haɗa yare kala huɗu ko ba, haka bane?," tayi maganar tana kallon Deejarh ɗin, dariya tayi ta ce "E, mana Balarabiyar india haka nake nufi."

Fashewa da dariya Lailah tayi har tana faɗowa daga saman sofa.
Duk suka zuba mata ido, ita ma Zaynerb dariyar takeyi ba laifi.
Saida Lailah tayi dariya ma'ishi sannan ta dakata. Kallon Deejarh tayi cikin dariyar take faɗin, "amma fa, kinyi ƙoƙari waima, ke a'ina kika koya, wannan yarukan kala kala haka?,"

Deejarh ta ce "nima kawai naji na iya ne fa," dariya Lailah ta kuma fashewa da shi.

Afeefah da abin ya isheta buɗar bakinta cewa tayi, "Lailah kodai kin sama taɓuwa ne?,"

Lailah ta ce "lafiyata qalau, kawai dai na manta rabon da, a sakani dariya kalar haka ne,"
"ai saikiyi da kyau an baki aiki cewar Afeefah.

"Lailah zoki rakani gidan Sunainah mana?," cewar Zaynerb tana miƙewa tsaye.
Tsayawa Lailah tayi da dariyar da takeyi ta kalleta "amma dai wasa kike ko?,
Zaynerb tana ƙoƙarin shiga bedroom ɗinta, ta juyo ta ce "da gaske nake, don akwai abin da nakeso ta koyamin, kinsan course ɗin da nake karanta shi ta karanta ko?,"

Tana faɗan haka ta shige ɗakinta, bata daɗe ba, ta fito sanye da hijjab blue black har ƙasa ga folder's rungume a chest ɗinta, kallon Lailah tayi ta ce
"zo mu tafi mana."
"Inason zuwa, amma wallahi ina tsoron karen gidanta," Lailah ta faɗa iya gaskiyar ta.
"ke matsoraciya, indai saboda kare ne, ba zaki ba to kisa ranki a inuwa domin karen yana ɗaure ma kaca."
"ke tayaya kikasani?,"
Lailah ta tambaya, Zaynerb ta ce "ita ta faɗamin, kinsan kuma ba zatamin ƙarya ba ko,"
Tashi Lailah tayi ta ɗauka gyalenta dake a gefen kujera ta yafa a kafaɗarta.

"Nima zan biku kinji Auntie Zaynerb, tunda na shigo gidannan, ban fita ba,"
Cewar Deejarh iya gaskiyarta, "idan bakyajin tsoron kare, kizo muje," cewar Lailah tana dariya, "banajin tsoron shi,"
"to zo muje," Zaynerb ta amsa ma ta.
Da sauri ta miƙe tsaye ɗakin da yake matsayin nata, ta shiga ta ɗauko hijjab ɗinta iya gwiwa fari.

"ke yanzu nanda maƙwabtan ne, saikin saka wani hijjab," cewar Lailah tana kallon Deejarh da koɗaɗɗen hijjabinta. Zaynerb ta kalla Deejarh ta ce "rabu da Lailah kawai don ta iya tonon tsiwa kala kala, ɗunguma sukayi wajen fita daga palon su ukun.

Suna taɓa fira a hanyar su har suka ƙarisa gidan, ƙwanƙwasa ƙaramar kyauren gate ɗin gidan, Zaynerb tayi shiru taji hannu tasa ta tura ƙofar tajita a buɗe.
Shiga gidan sukayi basuga mai gadi a kujerar shi, ta zama ba, basu kawo komai ba suka nufi cikin gidan a tsakiyar palo suka tsaya suna kwaɗa sallama, amma ba amsa.

"Kai kodai bata nan ne?," Deejarh ta tambaya, Zaynerb ta ce wata ƙila, wata ƙila kuma.....zata kuma magana saiga Babah Dije mai aikin ta fito, "yauwa Babah wai Ummyn Farhana tana nan kuwa?,"
Zaynerb ta tambaya, Babah Dije ta ce "aikuwa Ƴar nan bata nan ta fita ita da mai gidan, wato Alhaji Sohailu."
"to bata faɗa miki inda zata ba?," wannan karon Lailah tayi tambayar.
Babah Dije ta ce "eh inaga gidan surukanta suka tafi," "okay ba damuwa, idan ta dawo kawai kice mata munzo bamu sameta ba, Zaynerb ta faɗawa Babah ɗin hakan.
Da 'to' Babah Dije ta amsa musu, su kuma suka fito.

Lailah ta ce "danasani ma, ban biyoki ba, tunda dai batanan....Zaynerb ta ce "ai kin motsa jiki koba komai inagaa!....kasa ƙarisa maganar tayi ganin abin da ke gabansu, "kinaga mene?,"
Lailah ta tambaya jin Zaynerb ɗin ta kasa ƙarisa maganar bakinta.
A hankali takai kallon ta inda taga 𝑍aynerb ɗin ta saki baki da hanci tana kallo.

*~𝑺𝒉𝒊𝒏 𝒌𝒐 𝒎𝒂𝒊, 𝒁𝒂𝒚𝒏𝒆𝒓𝒃 𝒕𝒂 𝒈𝒂𝒏𝒊 𝒅𝒂 𝒚𝒂 𝒉𝒂𝒏𝒂𝒕𝒂 𝒌𝒂𝒓𝒊𝒔𝒂 𝒎𝒂𝒈𝒂𝒏𝒂𝒓 𝒅𝒂 𝒕𝒂𝒌𝒆𝒚𝒊?~*
*~𝒔𝒉𝒊𝒏 𝒅𝒂𝒎𝒆 𝑳𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉 𝒛𝒂𝒕𝒂𝒚𝒊 𝒊𝒅𝒐 𝒉𝒖𝒅𝒖 𝒊𝒅𝒂𝒏 𝒕𝒂 𝒋𝒖𝒚𝒂?~*
*~𝒎𝒆𝒚𝒂𝒔𝒂 𝒎𝒂𝒊 𝒈𝒂𝒅𝒊 𝒃𝒂𝒔𝒉𝒊𝒏𝒂𝒏 𝒈𝒖𝒓𝒊𝒏 𝒛𝒂𝒎𝒂𝒏 𝒔𝒉𝒊?~*

*ᴋᴏᴍᴀ ᴍɪʏᴇ ᴍᴜ ʜᴀᴅᴜ ᴀ ɴᴇxᴛ ᴘᴀɢᴇ's ᴊɪʙɪ ɪɴsʜᴀ ᴀʟʟᴀʜ, ᴅᴏᴍɪɴ sᴀɴɪɴ ʏᴀᴅᴅᴀ ᴢᴀᴛᴀ ᴋᴀsᴀɴᴄᴇ, ᴅᴀsᴜ ᴢᴀʏɴᴇʀʙ, ᴅᴇᴇᴊᴀʀʜ, ʟᴀɪʟᴀʜ, ᴀ ɢɪᴅᴀɴ sᴜɴᴀɪɴᴀʀʜ*

👑🩸ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ🩸👑
💝ᴛᴀᴋᴜɴ ғᴀʀᴋᴏ🤙


*~💅ᴛʜᴇ ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴍᴀʟʟᴀᴋɪɴᴀ ɴᴇ, ɴɪ ᴋᴀᴅᴀɪ ɴᴀᴋᴇ ᴅᴀ ᴅᴀᴍᴀʀ sᴀʀʀᴀғᴀ ᴀʙɪɴᴀ ʏᴀᴅᴅᴀ ɴᴀᴋᴇsᴏ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ɴɪ ɴᴀʏɪ ᴋᴜᴍᴀ ɴᴀsʜᴀ ɢᴡᴀɢᴡᴀʀᴍᴀʏᴀ ᴡᴀᴊᴇɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀɴsʜɪ, ᴡᴀɴɴᴀɴ ʟᴀʙᴀʀɪɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀɴsʜɪ ɴᴀʏɪ, ᴅᴏᴍɪɴ ɪʟᴍᴀɴᴛᴀʀᴡᴀ ᴅᴀ ғᴀᴅᴀᴋᴀʀᴡᴀ ʜᴀʀᴍᴀ ᴅᴀ ɴɪsʜᴀᴅᴀɴᴛᴀʀᴡᴀ, ɴɪ ɴᴇ ɴᴀsᴀɴ ɪʀɪɴ ᴡᴀʜᴀʟᴀɴ ᴅᴀ ɴᴀsʜᴀ ᴋᴀғɪɴ sᴀᴍᴀʀ ᴅᴀsʜɪ, sᴏ ɪɴᴀ ᴍᴀɪ ɢᴀʀɢᴀᴅɪ ᴅᴀ ᴋᴀᴋᴋᴀᴜsᴀʀ ᴍᴜʀʏᴀ ᴀᴋᴀɴ, ʙᴀɴ ʏᴀʀᴅᴀ ʙᴀ, ᴋᴜᴍᴀ ʙᴀᴢᴀɴ ʟᴀᴍᴜɴᴄᴇ ᴡᴀɴɪ ᴋᴏ ᴡᴀᴛᴀ sᴜʏɪᴍɪɴ, ᴀᴍғᴀɴɪ ᴅᴀ ᴡᴀɴɪ sᴀsʜᴇ ᴋᴏ ʙᴀɴɢᴀʀᴇ ɴᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴡᴀɴɴᴀɴ ᴋɪʀᴋɪʀᴀʀʀᴇɴ ʟᴀʙᴀʀɪ '𝐒𝐀𝐑𝐀𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐊𝐘𝐀𝐔' ʙᴀ, ɪᴅᴀɴ ᴋᴜɴɴᴇ ʏᴀᴄɪ ᴍᴀғɪʏᴀ ʏᴀᴡᴀɴ ᴍᴀsᴜ ɪʏᴀ ᴍᴀɢᴀɴᴀ, sᴜᴋᴀ ᴄᴇ ɢᴀɴɢᴀɢᴀʀ ᴊɪᴋɪ ʏᴀ ᴛsɪʀᴀ, 👑ᴛʜᴇ ɢʟᴀᴍ ǫᴜᴇᴇɴ💅 ᴍᴀʟʟᴀᴋɪ ɴᴀ ɴᴇ, ɴɪ ᴋᴀ𝙳ᴀɪ🤙~*

^ɴᴏᴠᴇʟ ᴡʀɪᴛᴇʀ ᴏғ✦

💓sᴀʀᴀᴜɴɪʏᴀʀ ᴋʏᴀᴜ💓

♥︎ғɪʀsᴛ sᴛᴇᴘ

*💋💋ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ💋💋*

*~ƚԋҽ ɠʅαɱ ϙυҽҽɳ~*

*☆ʂƚσɾყ & ɯɾιƚιɳɠ Ⴆყ☆*

*~ƙԋαԃҽҽʝαɾƚԋ. ʂαႦι'υ. ყαԋყαԋ🤙~*

{~✦ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ~}😇

*page 23&24*

Waro dara daran idanun ta waje Lailah tayi ganin abin da ke gabansu, wani ƙaton kare ne, irinna turawa wanda yasha training ya gaji sai faman hura fala falan kunen shi yakeyi ga mai kula dashi a gefe hannun shi riƙe igiyar da ya ɗaure ƙafan karen ɗaya.

Ita Lailah sam bata lura da ƙafan karen dake a ɗaure da sarƙa ba, gabaɗaya a mugun tsorace take ga wani guntun fitsari da ya matseta a mara.

Tattare skirt ɗinta ta farayi, ganin zata ruga ana kare yasa Iliya dake riƙe da karen saurin faɗin.
"hajiya karki gudu karki gudu fa, a ɗaure yake da sarƙa," Amma ina Lailah tayi nisa bata jin kira a three sixty 360 ta ranci na kare.

Shikuma kare dayaga haka ya rama mata baya, Toh abin yazoma Iliya a bazata ne, dan haka baima san lokacin daya saki igiyar hannun shi ba, shikuwa kare yace dama haka nakeso.

Hannu biyu Iliya ya ɗaura aka yana mai faɗin " yau ina ganin bala'i ganin ido na, dan Allah madam ki tsaya ki dena gudu, amma ina wanda yayi nisa bayajin kira.

Jama'a ba saiga Lailah da kare ana zuba tsere a compound ɗin GIDANMU ba, gabaɗaya Lailah ta rikice batama san inda take jefa ƙafafunta ba, ga kare da shegen gudu duk inda ta cire ƙafa nan yake jefa nashi.

Ganin Lailah tasha kwana shima karen ya mara mata bayane yasa su Zaynerb da Deejarh dake faman hawaye da ma Iliya gabaɗaya suma suka mara musu baya.

Lailah idonta ya rufe kawai gudu take ba ƙaƙƙautawa, fitsarin da take riƙewa batasan lokacin da ta kusa saki ba.
Tazo wuce swimming pool santsin gurin ya kwasheta, saiga Lailah saman ruwa kace kace, kare dayaga haka sai juyo zai koma inda ya fito a daidai lokacin kuma Deejarh dasu Zaynerb sukayo kwanar kawai sai aka tsaya kallan kallo a tsakanin Deejarh da kare yayinda Zaynerb da Iliya suke a daga baya ko wannen su ido a zazzare tsaban tashin hankali.

Deejarh kuwa yi tayi kamar zata ruga da gudu, sai kuma taja wawiyar kwana ta zube a ƙasa tayi pretend kamar irin ta suma ɗinnan, shikuma karen daidai lokacin ya taho jama'a saiga kare ya tsallake Deejarh ya wuce, wata wawiyar kuma doguwar ajiyar zuciya Deejarh ta sauke a lokacin da karen ya tsallake ta.

Da sauri Iliya ya lallaɓa a hankali cikin sanɗa da kuma dabara wajen da karen yake dayake ya bashi baya ne, da sauri ya riƙo igiyar da ya ɗaure ƙafar karen.

Gabaɗayan su suka sassauke ajiyar zuciya hadda Lailah dake cikin ruwa tsundum har yanzu, da sauri Zaynerb ta ƙarisa bakin swimming pool ɗin ta riƙo hannun Lailah suka samu ta fito Lailah tana riƙe qugunƙumi ita ma Deejarh tashi tayi daga kwancen da take.

Lailah ko kula Iliya dayake mata sannu batayi ba tsaban takaici, saima kallon ka cuceni da ta jefa mishi tayi gaba abinta, su Zaynerb suka mara maba baya.

A hanya tafe suke bamai magana sun zama kuramen ƙarfi da yaji, sai ajiyar zuciya da kowanen su yake saukewa, wani wawan shura Lailah takai ma ƙaramar ƙofar gate ɗin gidansu, ba shiri gate man yazo ya buɗe don ganin wani mahaluki ne, wata wawiyar dariya ce ta tahoma Isah mai gadi ganin fuskar Lailah da tayi kamar wacca aka qwato daga bakin kura.

Aikuwa bai iyayin juriyar riƙe dariyar ba, dan saida yayi abinshi.
Wata uwar harara Lailah ta galla mishi cike da balbalin bala'i ta ce "wannan dariyar da kamin to, a bakin aikin ka kayita😨

Tana faɗa mishi haka tabi bayan su Zaynerb da sukayi gaba kamar zata tashi sama saboda sauri.

A tare duka su ukun suka kaima ƙofar palon duka su uku ae ƙofar ba shiri ta buɗe suka shiga ciki.

Afeefah, Nainarh da Nailah da suke kallon wani Chinese Drama 'Intrepreneurial age.'

A tare suka juyo dan ganin mahalukin da ya turo ƙofa kamar zai ɓalla haka, sunayin ido huɗu dasu Lailah a tamanin Auntie Nailah tayi jifa da jaririn dake hannunta zata gudu ganin fuskar Lailah da tayi tunaninta gamo tayi da ZOMBIE ko HORROR ko kuma FATALWA 👽, Allah ne kawai, ya tsare Nainarh tayi saurin cafe yaron cike da tsoro.

Su Zaynerb basu kula Afeefah da Nailah da suke rige rigen haye staircase's don neman gurin ɓuya ba, suka sama guri su duka suka zazzauna a saman 3sieter.

"Zaynerb lafiyar ku kuwa, kuka shigo ko sallama babu, sai kace ku ɗin duka ba yaran musulmai ba," cewar Auntie Nainarh tana zama a 2 sieter babu alamar tsoro a tare da ita, don bata ma kula da fuskar Lailah ba, kallonta ta mayar kan Deejarh sannan cike da mamaki ta mayar kan Lailah zumbur ta miƙe tsaye, tanabin Lailah da kallon tsoro da mamaki.

"Lailah kece kuwa, miye haka ya sameki?, kodai faɗa kikayi da kura ne?,"
Nainarh ta jerowa Lailah tambayoyin ko tsayawa batayi ba saida takai aya.

A hankali Afeefah da Nailah suka fara dawowa da baya jin abin da Nainarh take faɗa.
Da sauri Afeefah ta ƙariso tana kallon Lailah "to kodai faɗan taje tayi da kuran bamu sani ba," cewar Afeefah da ta tsaya a gaban Lailah tana ƙare mata kallo cike da tsoro game da mamaki.

Buɗe baki Deejarh tayi zatayi magana sai kawai ta fashe da dariya tunowan da tayi lokacin da Lailah take tafka TSEREN MUTUWA tsakanin ta da kare.

"ah ah menene haka kuma, qalau kuwa kike ke Deejarh?,"
Nailah tayi tambayar tana kallon Deejarh ganin yadda take dariyar na ta na hauka tsakanin ta da Allah, "rabu da wannan mental ɗin kawai, ke Zaynerb menene ya faru ne wai na ganku haka 'So Bleak ne'," cewar Nainarh.

Zaynerb ta buɗe baki kenan da zummar zata musu bayani, ita ma ta tuno abin da ya faru ba shiri, ta fara ƙyaƙyata dariya harda riƙe ciki, ganin haka yasa Lailah dake harare harare ita ma ta fashe da dariyar.

Gabaɗaya su ukun suka haɗu suna ƙyaƙyata dariyar su sai yanzu ma abin da ya faru yake tariyo kanshi a kwakwalwar ko wannensu.

Uban tagumi Afeefah ta rafka hannu biyu biyu tana kallon ikon Allah, idan ta kalla Deejarh sai ta kalla Lailah idanta kalleta saikuma ta mayar da akalan kallon nata kan Zaynerb, dayake akwai kaifin kwakwalwa da basira, kafin ta ankara tuni wani tunani yazo kanta, kawai ita ma saita fashe da dariyar.

Nainarh ta ce "wa'innan yaran fa, sun sama mental illness nake gani,"
"ae ki bari kawai suyi mai isansu, idan suka gaji su da kansu zash dena," cewar Nailah tana karɓar yaron ta.

'𝑭𝒊𝒗𝒆 𝒎𝒊𝒏𝒖𝒕𝒆𝒔 𝒕𝒐 𝒈𝒐'

Saida sukayi dariyar ta ishesu sannan suka tsaya suna sauke ajiyar zuciya a tare kamar wa'inda suka sha gudun fanfalaƙe.

"Okay kun kammala?, yanzu zaku iya faɗa mana abin da ya faru?," Nainarh ta tambaya tana jiran amsa.
Fashewa da dariya Deejarh ta kumayi kamar wata zautacciya.

Da kyar Zaynerb ta samu ta saita nutsuwar ta sannan ta fara basu labari kamar haka.

"Ɗazu ne fa, mun fita mu uku, ni da Lailah da kuma Deejarh zasu rakani gidan Sunainarh, domin ta kowa min wani topic, tohm munje gidan batanan, ta tafi gidan surukanta ita da mijinta, to shine fa, mun fito zamu dawo gida, a daidai compound ɗin gidan muka haɗu da karen gidan, shida mai kula dashi da alama sun dawo daga £vening exercise ne, shine fa, ita Lailah gabaɗaya saboda ruɗewar da tayi na ganin wannan karen, batama lura karen a ɗaure yake da sarƙa ba, ina faɗamuku da ta tattare skirt ɗinta ta ranta da gudu, shi kuma kare yabi ta a three sixty 360.

Nan suka dinga zagaye gidan Lailah tana gudun ceton rai, sai daga ƙarshe ta samu, ta faɗa swimming pool 'In indistinctely, sannan ta samu ta tsira sai kuma kawai ya dawo kan Deejarh dayake tanada wayau sai tayi kamar ta suma shikuma kare da yaga haga yayi gaba abinshi, sannan ne fa, Iliya ya samu ya ɗaureshi da dabara."

*'𝑫𝒂𝒅𝒂 𝒂𝒍𝒌𝒂𝒎𝒊𝒏'*

*~☆ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ☆~*

Tunda ȥaynerb ta fara rattaɓa bayani, Nailah da Afeefah suke ɓaɓɓaka dariya kamar taɓaɓɓu, ita kuwa Nainarh, baki ta saki tana kallonsu su duka cike da mamaki, saida taji Zaynerb takai aya, sannan ta sauke ajiyar zuciya.

Kallonta ta mayar kan Lailah, ɗan murmushi tayi ganin yadda gabaɗaya hallitar Lailah ya canza dan wuya, don komai mazewar ka idan kaga fuskar Lailah a lokacin kuma aka baka labarin abin da ya faru dole kaji dariya tazo maka 😀

Still cikin ɗan murmushi Nainarh, ta ce "au ashe dama Lailah har yanzu kinanan da wannan shegen tsoron karen naki?,"

Lailah tana shafa fuskarta dake ma ta raɗaɗi raɗaɗi ta ce "wallahi Auntie Nainarh bazaki gane bane kawai, dan bakiga yadda karen nan ya biyoni bane kawai, ni harna sadaƙar ma wannan mayen karen sayyayi Bitten ɗina, sai kuma Allah ya tsare, na faɗa pool.
Afeefah tana ɗan saita nutsuwarta ta ce "yanzu tunda kin tsira, sai kije kiyi wanka, ki gurje duka dattin da ƙuran da kare yasa kika kwaso ko?," Afeefah ta ƙarishe maganar da alamar tsokana.
Harara Lailah ta maka ma ta sannan ta ce "ai ko baki faɗa ba, madam yanzu zan wuce."
Kallon Zaynerb tayi ita kanta Lailah ɗin, dariya yana zuwa ma ta amma ta maze ta ce, "wai kuwa Auntie Zaynerb nace ina folder's ɗin, dana gani ɗazu a hannun ki ne, waɗanda sanadin su na shiga halin nan?,"

Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke tana mai ƙoƙarin ta tuna inda ta zubar ta ce.

"ni kaina, banmasan a gurin dana zubar ba, inaji garin gudun ceton rai ne, na zubar."

"Gashi fa, a hannuna na riƙe, ɗazu garin gudu kika zubar, ni kuma na kwashe na riƙe miki, a hannuna," Deejarh ta faɗa tana miƙawa Zaynerb folder's ɗin.
Karɓa Zaynerb tayi tana faɗin, "gaskiya kinyi abin kirki nagode miki obaa highly."
Lailah ta ce "aini da komawa gidan Sunainah kuma sai wani ikon Allah ɗin, dan bazan har abada ba, kuma bazan ce nan nan kusa ba."
Lailah tayi maganar a lokacin da ta miƙe tayi hanyar bedroom ɗinta, tanaji su Afeefah suna kuma ma ta dariya amma ko tsayawa batayi ba.

________***___🎀

𝑾𝒖𝒓𝒂𝒓𝒆𝒏 𝒌𝒂𝒓𝒇𝒆 𝒕𝒂𝒓𝒂 𝒅𝒂𝒊 𝒅𝒂𝒊 𝒏𝒂 𝒅𝒂𝒓𝒆💫

Afeefah ta tura ƙofar bedroom da Deejarh take kwana, a hankali ta shiga, kamar yadda tayi hasashe, kwance ta sameta saman bed tana fuskan tar stylish ceiling na bedroom, idonta a buɗe kamar mai tunanin wani abu ko ƙarisowar wani abun.

Guri ta samu a gefen bed ɗin, ta zauna tana kallon Deejarh wacca alamu ya nuna har yanzu batasan ma da shigowar ta ba.

A hankali ta kira sunan ta 'Deejarh'," juyowa Deejarh tayi tana kallon ta ba ta ce komai ba, murmushi Afeefah tayi Sannan ta ce "mekike tunani ne haka?, na shigo bakisani ba."

"Tunanin abubuwa da yawa, Balarabiyar india ina tunanin abubuwa da yawa da yawa sosai

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads