Showing 21001 words to 24000 words out of 155363 words
Chapter 8 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
mai kimanin shekaru sha tara ta ƙariso da saurinta har ta kusa faɗi saboda sauri gurin Heesham ta ƙarisa cikin rawan jiki take serving ɗinshi yayinda ta kafeshi da ido kamar zata cinyeshi ɗanye saboda so da ƙauna, Shi kuwa baima kula da irin kallon da take mishi ba gabaɗaya yafi mayar da hankalin shi wajen kaima cikin shi haƙƙin da.
Ganin ta gama serving ɗinshi amma bata bar gurin ba yasa shi dakatawa da cin abinci da yakeyi ya ɗago da kanshi yana kallon ta.
Ae bilkisu sai da ta kusa sumewa ganin yau ta ciri tuta ya kalleta, "malama baki gama bane ko dai kina jiran wani abinne?,"
Ya tambaye ta cikin tsare gida da ɗan faɗa ganin yadda ta ƙureshi da ido, Da sauri ta ce "na gama oga," gurin Jieddarh ta ƙarisa tana serving ɗinta amma gabaɗaya hankalinta yana kan Heesham wanda shi baimasan tanayi ba.
Kaf gurin ba wanda ya kula da irin kallon da take mishi sai Jieddarh cikin zuciyar ta ta ce " Wow kaga wani kalan love aikuwa sun dace da juna ,Allah ta biyo ta hannuna zan taimaka mata", Ganin yadda Bilkisu ta wani ƙurawa Heesham ido kamar yau ta fara kallon shi dama ta lura da take taken Bilkisu kwana biyu akan YaYannata Heesham tunda ya dawo daga karatu ta ganshi gabaɗaya bata cikin nutsuwar ta.
Ɗan gyaran murya jieddarh tayi sannan ta kalli Bilkisu ta ce "please Bilkisu ɗan ɗaukomin maltina mai sanyi a fridge mana," Kallon Jieddarh Bilkisu tayi kawai saboda, ta katse mata jindaɗinta shine zata wani ce, Ta ɗauko mata maltina mai sanyi a fridge bayan ga wasu drinks ɗin a gabanta daɗin daɗawa kuma ae tafi ta kusa da fridge ɗin.
Tana ƙunƙuni taje ta buɗe fridge ɗin ta ɗauko mata, "gashi" ta miƙa mata ba tare da ta buɗe mata ba, "Ɗan buɗe min mana" jieddarh ta faɗa tana kallon yadda Bilkisu ta ɓata fuska ga Heesham ya kusa barin gurin bata gama ƙare mishi kallo san ranta ba😂.
"Buɗe mata mana Bilki ko ba ƙyaji ne" Cewar Auntie ganin yadda Bilkisu ta zuba ma jieddarh ido tana kallon ta kamar bata fahimci mai take nufi ba.
Da sauri ta buɗe miƙa mata tayi tanaji kamar ta mari jieddarh ɗin dan haushi, Tana shirin barin dining Area ɗin Jieddarh tayi saurin cewa "please Bilki ɗan dafamin noodles mana na kasa cin wannan abincin na gaba na," Tayi maganar tana ture plate ɗin gabanta.
"Ba Ƙya jin daɗine mamana naga yanayin ki kamar baki da lafiya" Abba ne ya tambayi jieddarh cikin kulawa, Lafiya qalau Abba kawai bana cin wannan abincin ne gwara a dafamin ko noodles ɗin naji ko zan iya ci.
"Okay Toke Bilki kinji don haka jeki dafa mata noodles ɗin mana kin tsaya kina kallon ta kamar baki santa ba," Auntie tayi maganar tana hararar Bilki danta tsana talaka.
Jieddarh fah ta rantse saita hana Bilki kallon Heesham cike da takaici Bilki ta wuce kitchen tana tsaki cikin ranta sai dai ba yadda ta iya, Cikin minti biyar ta kammala girka mata noodles ɗin zubo mata shi tayi a plate ta kawo mata, A lokacin Auntie bata a gurin ta kammala Humaira ita ma ta tashi jieddarh ne da Abba sai Heesham a gurin, Aje mata tayi a gabanta " To gashi nan.
Ɗan murmushin rainin wayo jieddarh tayi ta ce "to gashi naga kamar kinajin yunwa malama Bilkisu mai gadon zinare zauna muci kawai dan naji na ƙoshi."
Ɗan waro ido Bilki tayi jin abinda jieddarh ta ce, Yo ae ita ko karen hauka ne ya cijeta ba zataci wannan girkin ba, "kici mana naga fa tun safe kike zurzurga baki samu kinci abinci ba" muryar jieddarh ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, Ganin yadda Abba Alhaji Jafar Komai Naka da kuma, masoyinta Heesham suka zuba mata ido ne yasa ta zauna a zuciyar ta ta ce "yau na mutu sai dai kuma gawata Yau dai jieddarh ta Rantse saita kasheni🤔.
Aje mata plate na noodles ɗin jieddarh tayi a gabanta "gashi Bilkisu mai gadon zinare muci ko," ƙara gyara zaman ta tayi sannan ta ɗauki spoon ta ɗi ba takai bakinta tana rumtse ido, ae ba shiri ta fito dashi jin wani uban yaji ga gishiri game da uban maggi da yayiwa abincin yawa tari ta fara ba qaqqautawa kamar zata shiɗe, Da sauri jieddarh ta miƙa mata gorar ruwa na Mr. V.
Hannu na rawa ta karɓi ruwan saida ta shanye ruwan tas sannan ta sauke gorar daga bakinta tana sauke ajiyar zuciya da sauri ta ɗauki maltinar data ɗaukowa jieddarh bata shaba, ta kafa a bakinta tas ta shanye maltinar harda karkaɗe kwalbar, Dariya ma taba su jieddarh ganin yadda take karkaɗe robar , na gode Bilki ta faɗa da sauri lokacin da ta ɗauki plate ɗin indomie ɗin tabar gurin kitchen ta shiga da sauri.
jieddarh na kiranta amma ina tayi gaba ko juyowa batayi ba, dariya jieddarh takeyi dama shiyasa taƙi cin indomie ɗin dan kuwa tasan da wuya idan Bilki bata shirya mata mugunta a ciki ba gashi abinda take zargi ya tabbata, Ita ko Bilki koda ta shiga kitchen ta ƙofar kitchen ɗin ta fita ta koma sashen su na ƴan aiki cike da takaicin jieddarh da ta sa ta shan yaji ba tare tayi shiri ba, gashi ko gama kallon masoyinta Heesham ba tayi ba, A fili ta ce Allah ya isa na Jieddarh'
****
Da yamma wuraren ƙarfe biyar dai dai jieddarh na zaune a wasu ƙayatattun kujeru na hutawa daga gefan compound ɗin gidan tana karanta wani English Short Novel Mai Taken The Power Of The Silent, Gown ce doguwa a jikin ta na atamfa brown mai ratsin milk sai mayafin da ta yafa akanta milk color gabanta kayan mar mari ne kala kala sosai takejin daɗin karatun saboda yanayin weather na garin iska na kaɗawa kaɗan kaɗan gashi garin yayi luf luf💔
*Hauwa'u Ma`ana ☆🄺🅈🄰🄺🅈🄰🅆🄰🅁 🅈🄰🅁🄸🄽🅈🄰 🄼🄰🄸 🄹🄰🅁 🄵🄰🅃🄰☆ shi ne cikakken sunanta kyayawar budurwa ce mai kimanin shekaru goma sha tara zuwa ashirin a duniya.
Fara ce sosai hasken ta mai haɗe ja ne, Don zan iya cewa ma Jan yafi yawa akan farinna fatarta, Kyakyawa ce ajin farko duk wani qualities na kyau jieddarh tana dashi gashin kanta dogo mai tsayi highly highly...domin kuwa har mazaunan ta ga santsi sumar kanta mai kala biyu ne daga sama BAƘI ne suɗuq daga kasa kuma brown color ne mai haske idanun ta farare tas gasu dara dara masha Allah ga hancin ta mai tsini wanda Yayi daidai da kyakyawar fuskar ta, Bata da faɗin fuska don fuskar ta is Normalcy ne, Ga ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da launin dark pink tana da gashin gira highly highly gashi baki ga gashin idonta gazar gazar gunin ban sha'awa tana da tabon Allah a kasan gemunta baƙin ƙirin wanda ya ƙarama kyakyawar fuskar ta kyau highly highly😍.....Doguwa ce dirarra gata da duri ba'a magana saboda akwai ta da kayan alatu....Akwai ta da Yawan murmushi gata da dimples a duka gefe da gefen fuskar ta koyaya tayi magana saiya lotsa, Jieddarh akwai ta da son wasa da dariya ba ruwanta...Ta kammala Primary da secondary school ɗin ta a private schools masu masifar tsada a ƙasashe daban daban na duniya, Don bazai yiwu na ce ƙasa ɗaya ba...saidai kuma har wannan Lokaci bata shiga University ba ace war ta secondary School ma ya isheta tunda ta iya turancin ta Shikenan, Jieddarh tun tana da shekaru sha shida tayi saukan alqur 'ani mai girma tana da hazaqa highly highly🤓
Abba Yaya ne agurin mahaifin ta mahaifin ta ya rasu tun tana ciki ba`a haifeta ba..Jieddarh bata taso tasan mahaifiyar ta ba, ko'a hoto mahaifin ta dai wannan ta sanshi a hoto sannan tasan sunan shi "JURAEJ" amma mahaifiyar ta ko tayi ma Auntie ko Abba maganar ta sai suce mata mahaifiyarta bata sonta ta tsaneta bata ƙaunarta tunda ta haifeta ta bar gidan basu sake sannin inda take ba.
Saboda haka ko`a wani lokaci tayi musu magana akan mahaifiyar ta haka suke faɗa mata, Wannan ne yasa bata ma musu maganar mahaifiyarta ta saboda ta lura idan tana musu maganar ta ransu ɓaci yakeyi, Jieddarh ta taso sam batasan Menene soyayyar iyaye ba duk da cewa su Auntie ba takura mata suke ba amma soyayyar iyaye na daban ne, Burin Jieddarh ɗaya a rayuwa shi ne a wayi gari ta zama SARAUNIYAR KYAU sannan kuma tana son wasan golf obaa da kuma gasar tseren🤐.
.......................................................................................................................
𝕎𝕒𝕟𝕟𝕒𝕟 𝕜𝕖𝕟𝕒𝕟 𝕒 𝕥𝕒𝕜𝕒𝕚𝕔𝕖 𝕟𝕒𝕟 𝕘𝕒𝕓𝕒 𝕫𝕒𝕞𝕦 𝕛𝕚 𝕕𝕒𝕝𝕚𝕝𝕚𝕟 𝕕𝕒 𝕪𝕒𝕤𝕒 𝕞𝕒𝕙𝕒𝕚𝕗𝕚𝕪𝕒𝕣 𝕁𝕚𝕖𝕕𝕕𝕒𝕣𝕙 𝕥𝕒 𝕥𝕒𝕗𝕚 𝕥𝕒 𝕓𝕒𝕣𝕥𝕒 𝕕𝕒 𝕜𝕦𝕞𝕒 𝕕𝕒𝕝𝕚𝕝𝕚𝕟 𝕕𝕒 𝕪𝕒𝕤𝕒 𝕁𝕚𝕖𝕕𝕕𝕒𝕣𝕙 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕤𝕠𝕟 𝕜𝕒𝕣𝕒𝕥𝕦 𝕕𝕒𝕞𝕒 𝕕𝕒𝕚 𝕤𝕒𝕦𝕣𝕒𝕟 𝕤𝕦
.......................................................................................................................
{ 🅺🆄 🅳🅰🅸 🅺🅰🆆🅰🅸 🅺🆄 🅱🅸🆈🅾 𝕿𝕳𝕰 𝕹𝕬𝕴𝕹𝕬𝕽𝕳 𝕶𝕯 }
***
Ji𝖊ddarh Bilkisu ta hango zata shiga ɓangarensu na ƴan aiki da alama daga garden take ƙwala mata kira tayi da ƙarfi juyowa Bilki tayi jin ana kiran ta kuma tasan ba kowa bane sai Jieddarh, ƙarisowa gurin tayi, " Malama Bilki zauna mana" Jieddarh Ta ce tana murmushi, zama Bilki tayi a ɗaya daga cikin kujerun gurin harda ɗaukar Tufa tana ci.
"Gani kiran me kikamin aiki zanyi fah bakiga ɗakina ba kacaca saboda haka faɗi abinda da zan miki ko nayi gaba abina" Bilki tayi maganar tanacin tufa ɗinta hankali kwance, aje tsadaddiyar wayar dake hanunta Jieddarh tayi tana kallon Bilki ta ce "kinason YaYa Heesham ko?."
Da sauri Bilki ta kalli Jieddarh jin abinda ta faɗa dan kuwa batayi tunanin wannan kalan tambayar zata mata ba, ɗan gyara zaman ta tayi tana sosa kanta kamar wata mara gaskiya, Ita kuwa Jieddarh ta zuba mata ido tana kallo, Ɗan ɗagowa Bilki tayi zatayi magana saita fasa ganin yadda Jieddarh ta zuba mata ido tana kallo "ina jinki fah, kiyi magana nifa zan taimaka miki wajen YaYa Heesham ɗinne," ɗagowa Bilki ta kumayi jin abinda Jieddarh ta kuma cewa magana ta fara cikin inda inda "ni nnifa Jieddarh kin zuba min waɗannan idanun naki mai kalar Ash bazan iya magana ba ae."
Dariya Jieddarh tayi ta ce "miye kuma idanu na suka miki da bazaki iyamin magana ba idan ina kallon ki?,"
"Hhmmm bazaki gane bane Yasin Jieddarh," "to ki ganar dani mana cewar Jieddarh.
Hm hum hum hmm Bilki taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta fara cewa "kinga idanun naki kalar su Ash dasu su suke hana mutane haɗa ido dake dan kuwa ina faɗamiki ko mijin kine kika zuba ma wannan idanun naki mai kalar Ash mai Shaining to Yasin ina faɗamiki baisan lokacin da zai baki kuɗin Lalle ba kona anko ba Yasin."
Dariya Jieddarh tayi har jejarrun teeth ɗinta farare tas suka bayyana cikin dariyar take cewa "Allah da gaske kike ki rantse Bilki ta ce kicema ya mallaka miki gabaɗaya dukiyar shi tofah da gudu zayyi hakan.
Bilki hadda kuma gyara zaman ta a kujera ta ce "Allah kuwa ae ina faɗamiki keɗin mai sa'a ce a rayuwa."
Jieddarh ta ce "to mudawo topic ɗin mu kinason YaYa Heesham ko a'a?.
Bilki ta ce "kema dai Jieddarh kinsan ba kunyar ki zanji ba, ko E' ina son shi," ta faɗa hadda rufe ido wai kunya bayan kuma yanzu ta gama cewa bata jin kunya ta ci gaba da cewa amma fah karkiga na rufe fuska kije ina jin kunyar ki a'a duk acikin soyayyar da nake mishi ne, To in ma ji kunyarki akan me bayan nasan ke sa'a tace dan kuwa nasan bazaki girmeni ba sai dai muzo sa'anni amma dai yanzu ba wannan maganar ce agaba na ba.
"Na Menene" Jieddarh ta tambaya "ah ae kema kinsani kawai dai ni bansan ta yadda zan janyo hankalin YaYa Heesham ya dawo kaina bane gashi ɗan gayu ina faɗamiki idan naje kusa da shi har wani shiɗewa nakeyi na manta kaina na manta wacece ni gabaɗaya a duniya."
"Tofah kice abin ya girmama?," cewar Jieddarh Bilki ta ce kedai Jieddarh ba zaki gane bane kawai amma na miki uzuri saboda baki taɓa soyayya ba, Bakisan Love bah amma duk ranar da kikasani zaki tuna abinda nake faɗa miki amma yanzu mu aje maganar ki a gefe aji da matsala ta ki faɗamin abinda yafi so da kuma wanda bayaso da sauransu.
Jieddarh ta ce "na farko dai abinda zan faɗa miki ki dena mishi wannan mayen kallon da kike mishi kamar zaki cinyeshi idan kinganshi saboda bayason kallo, Ke bamashi kaɗai ba akwai mutane da yawa basu cika son a kalle su ba haka suke su, Na biyu kuma ki dinga tsafta highly highly saboda YaYa Heesham yana son tsafta highly highly ke bama shikaɗai ba duka maza suna son mace mai tsafta daɗin daɗawa kuma tsafta cikon addini ne.
Jieddarh ta ɗan yi shiru tana ganin yadda Bilki ta zuba mata ido tana kallo "kina fahimta kuwa?," Jieddarh ta tambaya, ajiyar zuciya Bilki ta sauke ta ce "ina fahimta sosai ma", "yauwa haka akeso ae" cewar Jieddarh nan dai Jieddarh ta dinga koyawa Bilki yadda zatayi Heesham ya sota acewar su.
Wasu danƙararrun motoci ne masu kyau da tsada suka shigo gidan guda biyu Yayinda Bilki ta saki baki da hanci tana kallon mutanen da suke fitowa daga motocin a fili ta ce "cabɗi jan yau muke ganin ƴan gayu anan gidan nan Yasin Yasin😇.
"Kalle su Mata su huɗu masu kama da Hajiya Jamila Wato Auntie da alama ƴan uwanta ne" cewar Bilki ta ci gaba da cewa gasu da yaransu suma ƴan gayu kamar su saidai ɗaya ce naga ba Yaro a tare da ita wata gila bata haihu ba ta tsaya tsarin iyali aikuwa za'a tsareta da kishiya duk ranar da mahaifarta ta sama problem "😅😂🤣.
Ɗan murmushi Jieddarh tayi bayan matan sun shiga ainihin gidan ba tare da sun kula su Jieddarh dake zaune a gurin ba, Bilki ta kalli Jieddarh da fuskar ta ya nuna alamar rashin jindaɗi ta ce "Jieddarh su kuma wa'innan fah kamar basu ga mutane a guri ba suka wuce hadda binmu da kallon banza hala ƙanin Hajiya Jamila ne naga suna kama da ita.
"E' ƙanin Auntie ne," Jieddarh ta bata amsa a gajarce "To ikon Allah amma kuma bansan suba ae gashi ina shirin zama IN LAW ɗinsu na miki na turawa.
Cewar bilki, "Oh Bilki ke komai sai kin sanine wai" cewar Jieddarh, Bilki ta ce "eh mana ba dole na sansu ba ƙannin suruka tace fah ae dole na sansu Yasin," Dariya Jieddarh tayi ta ce "to dai na farkon mai sanye da shigar hausawa YaYar Auntie ce uwa ɗaya uba ɗaya sunan ta Hajiya Nusaiba sai kuma ɗayar mai ƙaramin yaro sunanta sister Na'ima ɗayar kuma wanda kika ga ta riƙe hannun wannan kyakyawar yarinyar sunanta pretty Nafisah bazawara ce mijin ta ya rasu tun kafin Ta haifa ɗiyarta khausar, Duk tafi su kirki Yaranta biyu, Sai kuma na ƙarshen budurwace ita batayi Aure ba sunanta Ni'ima beauty shekarun ta Ashirin da biyar ita ce Babbar ƴar Auntie Nusaiba a mata YaYa Heesham takeso shiyasa batayi Aure bah🤣😂😅.
💓*SARAUNIYAR KYAU*💓
*Page 15&16*
Da sauri Bilki ta kalla Jieddarh hadda dafe ƙirji ta ce "wani YaYa Heesham ɗin, Badai masoyina ba?,"
"Of course yes, shi fa," cewar Jieddarh, miƙewa Bilki tayi zata bar gurin, Da sauri Jieddarh ta ce "ina zaki je ne, Haka?," "Hmm ke dai Jieddarh barni kawai zanje naga mai son masoyinane," Da sauri Jieddarh ta ce "to ki tsaya na faɗamiki wani abu mana.
Dawowa da baya Bilki tayi to gani faɗamin halayenta ina sauraronki," "haba malama Bilki toki nutsu mana saina faɗa miki yadda kema zaki fi fahimta," zama Bilki tayi cikin ƙosawa ta ce "to faɗamin ina sauraro," Ajiyar zuciya Jieddarh ta sauke sannan ta ce "kedai Bilki na farko dai ko shekara bakiyi a gidannan kina aiki ba watan ki bakwai ne, dan haka baki gama sanin halayyar ƴan gidannan ba ma balle kuma ƴan waje," ɗan shiru Jieddarh tayi sannan ta ci gaba cewa "ita wannan Ni'ima beauty da kika ganta ba'a shiga harkar ta, saboda bata da kirki ko kaɗan sannan kuma tanason YaYa Heesham highly highly kuwa," Jieddarh tayi maganar tana dariya, Ɗan kallon ta Bilki tayi cike da takaici da kishin Ni'ima ta ce "Yasin Jieddarh da nasan wannan shirmen zaki faɗamin da ban tsaya ba, Yo ni Allah na tuba kar tayi kirkin mana ina ruwa na da ita," Da sauri ta miƙe ta shige palon, Jieddarh ta bita da kallon tausayi kawai, Eh mana dole ta tausaya mata saboda wannan makauniyar soyayya da takewa Heesham, Jieddarh tasan halin Auntie yadda ta tsani talaka fiye da yadda ta tsani mutuwar ta da wuya wannan Auren ya yuwu gashi kuma soyayyar ɓangare ɗaya ne sai dai kawai Bilki ta sha wahala.
Bilki tana shiga palon ta samesu zaune sunyi ɗaiɗai saman Royal sofa's ɗin dake palon sai fira sukeyi da Auntie.
Kai tsaye kitchen ta shiga bayan wani lokaci ta fito hannun ta riƙe da Tray mai ɗauke da cups guda huɗu a saman, ciki juice ne mai sanyi, Ƙarisowa gurin su tayi ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana raba musu wannan juice, Saida ta gama raba musu tas sannan ta dawo gurin Yarinyar Nafisah tana mata wasa ita kuwa Yarinyar sai ɓangale baki takeyi tana dariya, Dama ance mai ɗa wawa ganin haka yasa Nafisah cewa "Hi young lady what is your name?," Da sauri ita ma Bilki ta harhaɗa ɗan turancin da ta koya a makarantar gwamnati da tayi ta ce "year Aunty My name is Bilkisu Adam Mai gazon Zinare."
Dariya Nafisah tayi ta ce "aikuwa sunan ki mai ɗadi it's deserved to you beauty.
"Na gode highly highly" cewar Bilki a lokacin da take ɗaukar Yarinyar zata fita da ita, Harta kai ƙofa taji Ni'ima na faɗin "Yanzu fisabilillah Mamy Nafisah wannan bagidajiyar Yarinyar zaki bari ta ɗaukar miki ƴa kamar bakisan zafin haihuwa ba kwata kwata Yarinyar nan naki ko shekara batayi ba haba adai duba lamarin," Nusaiba ta amsa da faɗin barta Allah yasa a kwaso mata cutar talakawa babu ruwanmu ciki," ita dai Bilki fita tayi tanajin Nafisah na basu amsa ita kuwa tayi tafiyar ta a zuciyar ta ta ce "wannan Ni'imar anyi shegiya tayi da baki kamar mariƙin lema saina koya mata hankali soon na lura bata da wani cikakken hankali akanta.
Ƙarisawa gurin