Showing 114001 words to 117000 words out of 155363 words
Chapter 39 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
ta ita ma tana fama da kanta domin kuwa naƙuda take yi sosai.
Ganin har wuraren sha biyu anyi Haihuwa a gidan har ma Ƴan uwan Rafi'at sun fara zuwa, amma Hajarah bata fito ba yasa Dattijuwar matar,
Hankalin ta ya gaza kwanciya hakan yasa ba shiri ta nufa ɓangaren Hajarah domin ganin ko lafiya, aikuwa tana zuwa ta tarar da Hajarah cikin wani hali na naƙuda wanda ba wacca zatasan Yanayin sai macen da ta taɓa ɗanɗanar haihuwa.
Aikuwa nan wannan Dattijuwar mata ta shiga bawa Hajarah taimakon da ya kamata, a taƙaice dai Hajarah ba ita ta hafe abin da ke cikin ta ba, sai Yammaci wuraren ƙarfe uku na Rana, sannan Ita ma ta santalo jaririyarta mace mai kama da ita Tamkar an tsaga kara, komai irin na ta ne sak, sai lokacin ta fara baccin wahala.
Zuwa dare gaba ɗaya dangi Ƴan uwa da Abokan arziƙi sunji haihuwar da a kayi ma Abubakar duka mata, hatta mutanen France sunji ta hanyar wayar tarho ko washe gari mutanen Jigawa State dana Adamawa dana Mai Duguri Kano gaba ɗaya sun hallara a gidan Abubakar cike da farin ciki, aikuwa nan aka shiga kula da masu jego.
A Ranar da suka cika kwanaki uku da Haihuwa Abubakar ya dura Nigeria aikuwa Ya yi kyakyawar gani a cikin gidan sa.
Gaba ɗaya matan da ya bari haihuwa yau ko gobe su ya tarar ko wacce da kyakyawar Ɗiyar da ta haifa masa, saboda tsananin farin ciki a lokacin rasa mai zayyi ya yi aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba ya yi sujadar shukur yana miƙa godiyar sa ga Allah da ya nufe sa da ganin wannan rana.
A lokacin in banda dariya babu abin da su Sakeenah da su Zuwaira suke masa nan ya shiga ɗaukar jariran, idan ya ɗauki na Hajarah sai ya a je ya ɗauki na Rafi'at haka yake ta yi abin gunin burgewa.
Wani ƙarin ikon Allah kuma gaba ɗaya jariran biyu, mugun kama suke da juna tamkar mace ɗaya ce ta haife su, aikuwa nan mutane suka dingi magana a kan wannan abin mamaki.
Ranar suna kuwa ɗiyar Hajarah taci suna Zaynerb a Yayin da Ɗiyar Rafi'at taci suna Haleesat, wato dai har lokacin Abubakar bai manta da Haleesat Rashid Rayyan ba masoyin gaskiya ke nan, Allah sarki Rayuwa a lokacin har da yawa sun manta da ita.😞
Ba ƙaramin daɗin wannan sunan da Abubakar ya sakawa ɗiyarsa dangin Rafi'at suka ji ba, a lokacin wasu daga ciki har sai da suka yi kuka na tunawa da maragayya Haleesat Rashid Rayyan mutumiyar kirki.
Ita ma dai Hajarah sai lokacin take sanin wacece Haleesat Rashid Rayyan a wurin Abubakar.
Rayuwa ta ci gaba da antayewa yayin da Abubakar yake kula da matan sa duka domin kuwa ƙin bari ya yi su Hajiya Harirah su ɗauki Hajarah wankan gida, a lokacin sai dai Hajiya Harirah ce tazo ta zauna dasu tana kula da Hajarah, yayin da ita kuma Rafi'at wannan Dattijuwar mata da ta amsa haihuwar su take kula da ita.
---**
Wani Abun mamaki da ya taɓa faruwa Wanda gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo ba zasu taɓa mantawa dashi ba shi ne.
A wata Ranar Alhamis da safe lokacin Rafi'at da Hajarah suka cika watanni uku da Haihuwa, Ranar Abubakar bai fita Company ba.
Wuraren goma na safe suna zaune a palon gidan shida Rafi'at da Hajiya Harirah da kuma sauran Yaran gidan suna taɓa fira sama sama.
Sai ga Hajarah ta shigo tamkar an jefo ta, sai faman goge gumi take ga fuskar ta ɗauke da matsanancin Farin ciki saboda tsananin saurin da take yi har Ƴarta Zaynerb dake hannunta ta kusa faɗi ƙasa, ta taro ta.
_-_Mgnr Payment da nace. Tabbas Book 2 is paid fa_-_
_Duk Wanda Ya shirya ayi tafiyar da shi, kuma ya shirya Payment_
_-_Just Pay With This Details_
_-_-_-_-_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*
___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Page *77&78*
Qarisowa tayi sannan ta tsaya a tsakiyar palon tana faman sauke ajiyar zuciya game da haki, ganin yadda ta shigo a hargitse kamar wani ya biyo ta yasasu gaba ɗaya tashi suna tambayar abin da ke faruwa.
A hankali ta buɗe kyakyawan idanunta waɗanda saboda tsananin farin cikin da take ciki yasa suka kawo ruwa, ta kallesu dasu sannan ta fara magana.
"Ina cikin farin ciki wanda tunda nake a Rayuwata ban taɓa shiga ciki ba. Yau kuma a dai dai wannan lokaci na tuna WACECE NI, Yau bayan shafe tsawon shekaru ɗaya da wata biyar da kwanaki biyar da mintuna goma sha biyar da sakanni, a Yau ni 'Hajarah Haleed Mai Waje: na tuna Asalina na tuna Ahalina na tuna sunan State nawa, na tuna komai da komai duka...'
Tayi maganar ne a Yayin da wasu siraran Hawayen Farin ciki suka wanke ma ta fuska.
Gaba ɗayansu jama'ar dake a palon kabbara suka saka cike da tsantsan farin ciki, shikuwa Abubakar gaza jurewa ya yi har sai da ya yi sujadar shukur yana kuma miƙa godiyar sa ga Allah wato dai maganar bahaushe ce da yake cewa INDA RAI DA RABO ikon Allah, gashi dai daga ƙarshen ƙarshe, Hajarah zata kuma haɗuwa da Ahalinta a karo na biyu, Allah ke nan buwayi gagara misali.
Da gudu Rafi'at ta ƙarisa wurin Hajarah ta Rungumo ta gaba ɗayanta a jiki tana faɗin
"Na tayaki murna sosai sosai Abokiyar."
Da yake haka suke kiran juna, murmushi Hajarah tayi tana kuma damƙe hannun Rafi'at dake cikin nata Sannan ta ce
"Nagode sosai Abokiyar, Allah ya bar ƙauna."
Hajiya Harirah kuwa tun ɗazu fuskar ta ɗauke take da matsanancin Farin ciki, saboda haka sai ta kasa magana, kawai tana binsu da kallo, ƙari sowa wurin ta Hajarah tayi Bayanta miƙawa Abubakar Zaynerb kana ta Rungumo Hajiya Harirah faɗi take
"Hajiyar mu kita yani murna da farin ciki Yau ina cikin nishaɗi obaaaaa..."
Sai da gaba ɗaya suka sama nutsuwa suka zazzauna sannan kuma Abubakar ya ɗauki waya yana kiran gaba ɗaya dangi yana faɗa musu Abin farin cikin da suka wayi gari da shi.
Aikuwa nan aka dingi tayasu murna barinma dai su Zuwaira, Jawaheer, Jummai Sakeenah waɗanda suka ɗauki Hajarah matsayin Ƴar uwa ba matar ɗan uwansu ba, ai nan mutanen Jigawa State suka ce gasunan ƙarisowa Abujan ayi farin ciki tare dasu.
A Ranar gaba ɗaya Ahalin sun wuni ne cike da farin ciki mara misaltuwa.
Misalin ƙarfe bakwai na Yammaci mutanen Jigawa State tun daga kan Alhaji Sameer Lamiɗo Dr_Raheemah Hajiya Zuwairiya, Zuwaira, Jawaheer, Jummai hatta Sakeenah dake Aure a Adamawa State sai da ta hallara a garin Abuja gaba ɗayansu sun ƙariso.
Wuraren ƙarfe Takwas da Rabi na dare gaba ɗaya sun hallara a Babban palon gidan, suna fira cike da nishaɗi bayan komai ya lafa ne Alhaji Sameer Lamiɗo ya kalla Hajarah cike da kulawa Yake faɗin
"Ɗiyata Hajarah gaba ɗaya nida Ahalina muna tayaki murnar tuno Rayuwar ki da Ahalin ki da kikayi.."
Murmushi tayi cike da jindaɗi ta amsa da
"Ina godiya sosai Abbhee..."
"Tohm ni dai har Yanzu banji sunan State ɗin namu ba."
Cewar Jawaheer cike da zoyala, murmushi Hajarah take saboda farin cikin da take ciki ma haƙoranta sunƙi rufuwa gyara zama tayi kana ta fara magana kamar haka.
"Da Farko dai kamar Yadda kuka sani sunana Hajarah sunan mahaifina kuma Alhaji Haleed Mai Waje, ni ɗin cikakkiyar Ƴar Garin KADUNA STATE ce dake a nan AREWA cikin Nigeria Yankin Africa."🌍
"Alhamdullilah.
Masha Allah..
Hakan akeso..."
Haka kawai gaba ɗaya mutanen da ke zazzaune a palon suke faɗa nan kuma aka ƙara tayata murna daga nan kuma Sabuwar fira ta ɓalle a tsakani daga ƙarshe sun yanke shawarar cewa gobe tun daga kan Alhaji Sameer Lamiɗo da matansa da kuma Zuwaira da Abubakar sai kuma ita Hajarah ɗin zasu wuce Kaduna Garin Gwamna domin haɗuwa da Ahalin Hajarah, daga haka kuma taron ya watse dama lokacin dare Ya yi sai kowa ya sama makwanci, dama kuma Hajarah ita keda girki sai kawai tabi mijinta tura karsa.🤭
*WASH£-GARI*
Wuraren ƙarfe goma sha ɗaya na safe gaba ɗayansu Ahalin tsaye suke a filin ajiye motoci na gidan. Yayin da waɗanda zasuyi tafiyar suna shirye tsaf, Yayin da kuma waɗanda ba da su za'a tafi ba, suka tsaya daga gefe suna musu ban kwana cike da Fatan Nasara.
Bayan sun gama ban kwana ɗin ne gaba ɗaya suka shiga motoci da yake motocin ba kalar na wannan zamanin bane, shiyasa sai da suka yi mota uku sannan gaba ɗaya suka shiga ciki.
*SAIDAI KUMA ME?.*
Wani Abun mamaki shi ne duk Yadda a kaso motar da Hajarah take ciki ta tashi Abu ya cutura.
Abu dai kamar wasa tun ana gwadawa cikin daɗin rai har aka koma gwada mota mota amma wani ikon Allah shi ne, duk motar da Hajarah ta shiga ciki ba zata tashi ba, amma kuma tana fita wannan mota zata tashi.
Abu fa kamar wasa anata abu ɗaya har wuraren ƙarfe ɗaya na rana ana kan abu ɗaya, sai daga ƙarshen ƙarshe ne, bayan Addu'o'i da suka dingiyi aka samu mota ta tashi.
Ajiyar zuciya ko wanen su yake saukewa gaba ɗaya sun haɗa uban zufa barin ma dai Hajarah da takeji kamar me?.
Sallama suka kuma yi da kowa sannan suka ɗauki hanya, Bayan gate man ya wangale musu gate.💃
_____*
Sun bar Garin Abuja wuraren ƙarfe ɗaya da rabi na Rana sannan suka fara wuce garuruwa sun wuce Minna ba daɗewa ke nan suna shirin shiga Garin Kaduna.
Jikin Hajarah ya fara wani irin rawa ta ko'ina haɗa zufa take ga wasu ƙuraje da suka fara fitowa daga ko'ina na jikinta, da yake su uku ne a Motar ita da Dr_raheemah da kuma Hajiya Harirah, da Farko basu lura da abin da ke faruwa da ita ba, sai da suka ji ta fara nishin wahala, aikuwa nan take suka ba driver umarnin tsayawa.
Gefan kwalta ya samu sannan ya tsayar da Motar da yake suna a gaba ne, shiyasa suma sauran motocin da ke bayansu suka sama wuri suka tsai tsaya, sannan gaba ɗaya suka fiffito suna kallon Hajarah dake faman haɗa uban zufa ga wasu ƙuraje da suke feso mata tashi ɗaya, Abin gunin ban tausayi.😰
Da sauri Abubakar ya ƙarisa wurinta kana ya kamo hannunta cike da tausayawa ya kira sunan ta.
Kasa amsawa tayi saivma kallon sa da tayi cikin jin azaba ta ce
"Dan Allah mu koma gida, idan ba haka ba kuma mutuwa zanyi, zafi nakeji ta ko'ina a jikina jina nake kamar bani ba..."
Daga jin irin abin da take faɗa da kuma ganin yadda gaba ɗaya jikinta yake rawa ga wasu ƙuraje, Yasa Alhaji Sameer Lamiɗo Ya yi gyaran murya, gaba ɗaya suka juyo suna kallon sa, suna jira suji abin da zai ce.
"Ina ga mu juya gida kawai domin kuwa na lura wannan lamarin dasa hannun Jinnu a ciki, mu Fara komawa gida a ma ta magani sannan koma menene daga baya a yi."
Gaba ɗaya sun gamsu da maganar sa kuma sun fahimci abin da yake so ya fahimtar dasu, saboda haka ba tare da ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga motocin su suka koma.
Su Rafi'at suna zazzaune a palon gidan suna taɓa fira tsakanin ta dasu Zuwaira suka ji dawowar motocin.
Mamaki ne ya kamasu ganin su Hajiya Zuwairiya sun shigo.
"To kodai har sun dawo ne?."
Jawaheer ta tambaya tana miƙewa tsaye kamar yadda suma sauran suka mimmiƙe suna binsu Hajarah da kallon neman ƙarin bayani.
Gaba ɗayansu zama suka yi a saman kujerun palon jiki a mugun sanyaye, ganin haka yasa suma su Jummai suka zazzauna sannan ne kuma suka lura da Hajarah da ƙurajen da suka fara fiffito mata a jiki.
"Ya Allah.! Menene kuma wannan?."
Sakeenah ta tambaya cikin waro ido tana ƙarisawa wurin da Hajarah take
Ajiyar zuciya Hajarah ta sauke idanunta sunyi jajur na ɓacin rai sannan a fili take faɗin
"Dama nasan haka zata faru, tabbas nasan ba zata taɓa bari na koma gida cikin sauƙi ba, ni na sa ni, kuma nasan komai, nasan ko ita wacece."
Gaba ɗaya mutanen dake palon suka zubo ma ta ido cike mamakin jin abin da take faɗa.
Abubakar da ya gaza jurewa sai da ya magantu.
"Wacece ita haka da kike faɗin kin san ba zata Bari ki koma gida lafiya ba?."
Ya tambayar idanun sa akanta, kamar yadda suma sauran jama'an palon suke ma ta kallon neman ƙarin bayani.
Numfashi kawai take fitarwa da sauri da sauri kana bayan wasu sakanni ta ɗago da kanta tana kallon jama'ar palon, kamar suma yadda ɗin ita suke kallo Sannan ta fara magana kamar haka.
"Alhaji Haleed Mai Waje shi ne cikakken sunan mahaifin mu.
Asalin sa Ɗan Garin Kaduna State ne.
Gaba da baya, su biyu a wurin iyayen su, shi da ƙanin sa Kamaludeen, sunan 'Mai Waje' kuma mutane ne suka saka masa.
A dalilin shiɗin ya kasance yana gudanar da harkokin kasuwancin sa ne a tsakanin ƙasashen waje.
Ya kasance cikakken Ɗan kasuwa kuma Mai Naira Wanda duniya take damawa dashi ta kowani ɓangare.
Matar sa ɗaya wacca ta kasance Baturiyar ƙasar Bulgaria ce, haifaffiyar Babban Birnin ƙasar wato 'Sofia'.
Tabar iyayen ta da Biyuninta a ƙasar su ta biyo sa.
Nigeria ne a dalilin son sa da take yi, kuma a kayi sa'a shima ɗin yana matuƙar ƙaunar ta.
Koda suka zo Nigeria a tare, batare da wani ɓata lokaci ba mahaifin sa ya ɗaura musu Aure, bayan ta karɓa Addinin Musulunci taci suna Haleematul Sa'adiya.
Yaran su huɗu a tare Hasheem shi ne na Farko, sai kuma wasu mata biyu da suka kasance twin's ne Mubashirah da kuma Munira, sai kuma Ni Auta Hajarah.
Mun taso ne cikin Tarbiyar iyaye, saboda duk da cewa mahaifiyar mu ta kasance Baturiyar da ta Musulunta, hakan bai hana ta jajir cewa ba ita da mahaifin mu wurin bamu Tarbiya mai kyau da nagarta. Mun kasance a gidan mu.
Muna zaune ne tare da ƙanin mahaifin mu da matar sa, suma suna da Yara uku a tare.
Matar ƙanin mahaifin mu mai suna Asabe ta kasance ta tsani mahaifiyar mu fi ye da kima, wai saboda ta kasance TUBABBIYA ce, kuma duk da haka surukan su sunfi ƙaunar mahaifiyar mu a kanta, wannan ne Babban dalilin da Yasa ta tsani mahaifiyar mu, a kullum cikin muzguna ma ta take yi, duk da cewa a cikin gidan mu suke zaune, kuma da dukiyar mahaifin mu suke ci suke sha.
Amma hakan bai hana ta neman kai mahaifiyar mu ƙasa ba. Da duka ƙarfinta.
Sai dai kuma duk Abin da take yi cikin salo da dabara take yi domin kuwa kaf gidanmu dama Ahali baki ɗaya babu Wanda Yasan Burinta a kan mahaifiyar mu domin ta kasance mace mai ƙissa da kisisina, a cikin mutane nunawa take tafi kowa ƙaunar mahaifiyar mu, amma kuma cikin zuciyarta ba haka bane.
Kaf gidan ba Wanda Yasan Burinta akan mahaifiyar mu sai ni kaɗai, domin kuwa na kasance tun ina Yarinya ina da matuƙar kaifin basira sosai, Wanda wannan dalilin ne ma Yasa nake karantar psychology ma'ana ilimin Tunani.
Ita da ƙanin mahaifin mu suna da wani Yaro mai suna 'Sama'ila' Wanda ya kasance tun daga tasowar sa mutum ne shi mara imani ko kaɗan domin kuwa ya kashe mutum har lahira ba damuwar sa bane, domin kuwa koda ya kammala secondary school kai tsaye ya wuce ƙasar China ya Karanci Astrology Wato ilimin Bokanci.💀💀💀
Wanda a dalilin baƙin cikin hakan ƙanin mahaifin mu Kawu Kamaludeen zuciyar sa ta buga ya mutu.
Sai dai a maimakon mutuwar sa tasa Ɗan sa Sama'ila ya tuba ya koma ga Allah. A'a saima sabon salon abu da ya fito dashi. Domin tattarawa ya yi ya koma can kudu da zama.
Yayin da ƙannin sa biyu da mace dana miji da kuma mahaifiyar su suka ci gaba da zama a cikin gidan mu.
A lokacin ne kuma Asabe ta fito da nata sabon salon ita ma domin kuwa ta Yanke shawarar Auren mahaifin mu ta ko wani hali.
Nima a lokacin nazo gida hutu ne, sai na je ɓangaren nasu. Wajen ɗiyarta wacca ta kasance sa'ata ce shi ne fa naji abin da Yafi ƙarfina, a lokacin hankalina ya tashi sosai domin kuwa harji nayi tana faɗin, "Lallai zata iya kashe mahaifiyar mu har lahira indai ta nema kawo mata matsala."
"Lokacin ba ƙaramin tashi hankalina ya yi ba, sai dai kuma wani abun mamaki na kasa faɗa wa kowa abin da naji tana faɗa har hutuna ya ƙare na dawo Abuja domin kammala karatuna.
To a lokacin dana kammala karatuna ne a wajen dawowa ta daga wajen taro, na gamu da wannan Hatsarin da harna manta gaba ɗaya memory na akan Rayuwata da Ahalina..."😭
Hajarah ta na kawowa nan da maganar ta tayi shiru, Yayin da wasu zafafan hawaye suka wanke kyayawar fuskarta.
Shiru gaba ɗaya palon ya ɗauka tsawon mintuna goma, babu Wanda ya iya faɗar wani abu, saboda tsananin mamaki da al'ajabi, sai can ne Alhaji Sameer Lamiɗo ya nisa sannan yace
"Tabbas sosai mun tausaya miki fi ye da baya, da jin wannan labari naki mai cike da ƙalubale da chakwakiya game da rikitarwa, wannan yana nufin ke nan zargi na ya tabbata a kan cewa, da saka hannun Jinnu a wannan lamarin, to daga yau Insha Allah, zamu dage gaba ɗaya a haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin ganin an nemo Ahalin ki, sun zo su ganki, tunda zuwan ki can bazai yiwu ba, kuma zamu ƙara dage wa wajen ganin an rabaki da waɗannan mutanen da suke a tare da ke Bi'iznillah.
***
Aikuwa Tun daga wancan ranar gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka ƙara zage damtse wajen kula da Hajarah fi ye da baya, kowa ƙaunar ta yake yi kamar me, hatta Rafi'at ba'a barta a baya ba, domin kuwa ba kaɗan ba labarin Hajarah ya taɓe ta. Ashe dai ko'ina da shegu😕
Ita babu abin da yafi ɗaga ma ta hankali sai ji da tayi wai musamman Sama'ila da yake Ɗan musulmi, ya ɗauki ƙafa wai yaje har can uwa duniya Ƙasar China dangin ifiritai, Karantar ilimin Bokanci ashe haka duniyar ta zama.😔
Zieey Jinjina mara adadi a gareki, ina godiya matuƙa da ƙaunar da kike yiwa wannan book, Allah ya barmu tare🥰