Showing 54001 words to 57000 words out of 155363 words
Chapter 19 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
Turanci zaki iya faɗamin, How many part of speech?,"
Shiru tayi sai can ta ce "guda Takwas {8} ne,"
"Da £nglish zaki faɗa," cewar principal.
Gyara zaman ta tayi ta ƙara ƙanƙame backpack ɗinta sannan ta ce.
"£ight ne,"
"Good" cewar principal sannan ya kuma cewa "and what and what."
Ta ce
"Noun, Pronoun, Verb, Adverb, Adjective, Conjunction, Interjection, Prepositions,"
"Good, and What is Noun?,"
Gyara zamanta ta kumayi sannan ta ce.
"A Noun is a Name of Anything.,"
Murmushi principal yayi sannan ya cigaba da jefo ma ta tambayoyi akan £nglish language. Tana bashi amsa, wasu tayi daidai wasu kuma, yana ma ta gyara.
"Angama da £nglish saura basic science" cewar principal.
Ya kalla Deejarh yace.
"a darasin basic science, What is digestion ?,"
Yanzu ma saida tayi jim kafin ta fara kwararo masa bayani, wanda yasa Afeefah da ke gefe zaune, ta saki baki tana kallonta cike da mamakin ilmin yarinyar.
"Digestion is the process, by which injested food, material are broken down in to similar particle's."
"Wow, good, and Define what is Brain?,"
Ta ce, "The part inside your head, that controls your thoughts, feelings, and movements."
Haka principal ya ci gaba da jerowa Deejarh tambayoyi daban daban akan subjects kala kala kamar su.
National Value, Agriculture, £conomic, Computer Science, I.r.s, Civic £ducation, £.t.¢.
Daga ƙarshe ya rufe da faɗin, give me the Ten, word's of £nglish.
T@ ¢£!
1.perfect,
2, Dream,
3, Table,
4, Challenge,
5,Get,
6, Offer,
7, School,
8, chair,
9, office,
10, salute🤭😇
Tunda ta fara Afeefah ta saki baki tana kallonta tasha mamaki sosai, da Deejarh ta iya wannan.
Ashe abin ba haka bane da ake ganin wasu mutanen da ke ƙauye ko kuma waɗanda suke zuwa government school ake musu kallon, jahilai, kodai adinga musu wani kallo na dabam abin ba'a zuwa government school bane, maida hankali da kuma jajircewa ne, dan ba wanda ya taɓa yin ilimi yana zaune sai an tashi an zage damtse, an shiga rana sannan da wuya koda daɗi 👍
Amma tana tunanin ko'a haka ita Deejarh ɗin tana cikin wa'innan mutanen da ake kira da Geniuses a turance kennan, sannan ita ɗin gifted ce.
Murmushi principal yayi yana kallon Deejarh ta burgeshi sosai da hazaƙarta.
"Nice good girl, kin amsa duka tambayoyi sai dai Wanda ba'a rasa ba."
Sannan ya mayar da kallon shi akan Afeefah yana murmushi yace "ta cinye interviewing, duka dan haka za'a sakata a j.s.s.three, she deserved it."
Afeefah tayi murmushi ta ce "okay sir."
Telephone ɗin dake ajiye kusada dashi, ya ɗauka ya danna wasu lambobi sannan ya kira, cikin harshen turanci yake maganar har ya gama, sannan ya kalla Deejarh yace "Nanah khadeejartu, taso na kaiki class da kaina,"
Murmushi tayi sannan suka miƙe dukansu suka fita a ƙofar office ɗin.
Afeefah ta kalla Deejarh tana faɗin, "to Deejarh ayi karatu da kyau, idan an tashe ku, Moses driver zaizo ya ɗaukeki kinji,"
"To shikenan babu damuwa," Deejarh ta amsa, sannan Afeefah ta nufi motar ta, Deejarh na ɗa ga ma ta hannu.
Kana tabi bayan principal elevator taga ya nufa, ita ma tabi bayan shi suka shiga a tare hawa na uku taga ya danna bayan sun shiga.
Ba'a daɗe ba taga ɗofar ta buɗe sannan suka kuma fita.
Ita dai nata ido, don sai ƙarema makarantar kallo, takeyi sosai makarantar ta burgeta ga ɗalibai kala kala farare da baƙaƙe hausawa dama waɗanda ba hausawa ba.
Wani haɗaɗɗen class taga principal ɗin ya shiga, kafin ta ankara, da sauri tabi bayan shi sai kuma ta tsaya cak ganin class mai kyau da tsari gashi duka ɗaliban ciki basu wuce su ashirin ba kai bama sukai hakan ba.
Gaisar da principal ɗin, taga student's ɗin sunyi bayan sun miƙe, ya amsa musu fuska a tsume kamar bashi ke washe baki yanzu a office ɗin shi ba 😅
Nuna musu Deejarh yayi sannan yace "kunyi sabuwar New comer, kallon Deejarh yayi yace, "gabatar musu da kanki, a matsayin sabuwar ɗaliba duk cikin turanci yake maganar.
Ta fahimci wani abu dan haka kallonta ta ɗauke daga kanshi, ta mayar kan students na class ɗin da suka zuba ma ta ido suna kallo.
Qara Riƙe backpack ɗinta dake bayanta tayi sannan ta fara magana.
"Hello class, am Nanah khadeejah Abubakar mai kyau, am New comer, kamar yadda mai girma principal ya faɗa da farko."
Da turanci take maganar tana haɗawa da hausa fa.
Ta ci gaba da cewa "am very Gladness to see you, ina fatan zaku karɓeni hannu biyu biyu ko?,"
Ɗan shiru tayi tana kallonsu, sai kuma ta ce "ina fatan dai ƴan uwan nawa ɗalibai suna fahimtar abin da nake faɗa, saboda ni ɗin ma ƴar koyo ce, ba komai na iya ba."
Gabaɗayan su students ɗin suka haɗa baki wajen faɗin "munajin ki, kuma muna fahimtar ki, sannan kuma muma muna masu Farin cikin haɗuwa dake kuma muna fatan zaki kasance damu har lokacin da zamuyi Candy."
Dariya Deejarh tayi {Ɗalibai kenan, basu daɗe da shiga j.s.s Three ba amma suna tunanin fita daga school ɗinma gabaɗaya, ae haka muke ɗalibai akwai mu da Buri kala kala 🥰🇳🇬}
Ta ce "Nima haka, ina muku fatan nasara a rayuwa, sannan kuma, ku cinye jarabawar j.s.c.e. hadda ma s.s.c.e. gabaɗaya😇
Dariya sukayi hadda ita, principal yace "yanzu tunda kun gaisa kunsan juna saiki sama guri ki zauna."
"To," ta amsa masa, sannan ta nufi gurin zama, da sauri wata kyakyawar matashiyar budurwa ta ce "baki faɗamana wani abu ba."
Lokacin da tayi maganar principal ya fita kuma dama can ba teacher a class ɗin.
Deejarh ta tambayeta, "Menene abun?," budurwar tana dariya ta ce "baki faɗamana, Menene burinki ba, sister,"
Dariya Deejarh tayi sannan ta ce "burina shine naga wata rana, an wayi gari na zama babbar likita wacca take taimakon talakawa da marasa ƙarfi, SO I WANT TO BE A DOCTOR.
Tafi class ɗin ya ɗauka rafraf suna faɗin munayinki wallahi our new comer { kuma kunsan students idan malami baya class 😁 }
Deejarh tayi murmushi a takaice sannan ta ce "nima dai zanso naji Burin ko wannenku ko?,"
Budurwar da tayi magana ne ta miqe dama bencin farko take kuma ita kaɗa ce.
Ta tsaya gaban blackboard kusada Deejarh, Sannan ta miƙawa Deejarh ɗin special hand ɗinta ta ce. "AM FALILAT KHAM££S, AND I WANT TO A DOCTOR TOO."
Murmushi Deejarth tayi sannan ita ma ta miƙa ma ta hannunta dake sanye cikin handglove ash color ta ce "nice to meet you miss Falilat,"
Falilat ta koma ta zauna, wata ma tazo sukayi kamar yadda sukayi da Falilat, haka suka dingi yi har aka gama da ɓangaren mata.
Wani saurayi ya fito ya miƙowa Deejarh hannu, wai su gaisa, murmushi tayi sannan ta juya hannunta ta baya ta karkaɗa mishi ta ce "haka akeyi saboda ni ba muharramarka bace."
Murmushi yayi yana faɗin "na gode da tuni, And am Farhad Khamees, i want to be a perfect £ngineer
Deejarh tana dariya ta ce "amma dai ku, twins ne da Falilat ko?,"
Amsa ya bata da faɗin, "E, haka ne, tayi murmushi haka suka ci gaba da yi mazan suma ba'a gaisawa sai dai a karkaɗa hannu. inji Deejarh.
Bayan sun gama ta sama guri a bencin farko, ta zauna kusada Falilat suna taɓa fira sama sama akan karatu, suna haka saiga wani malami ya shigo, miɗewa sukayi aka gaisar dashi, bayan ya amsa suka zauna.
Deejarh ta kalla Falilat dake ciku cikun ciro littafi a jakarta ta ce "wani darasi wannan malamin yake koyarwa?,"
Falilat ta amsa "£nglish language," jin haka yasa Deejarh ta ciro book ɗinta a jakarta ita ma.
Saida ta tsallake pages ɗin da aka wuce ta sannan ta fara copyn writing ɗin da malamin yakeyi a blackboard.
Bayan ya kammala ne yayi musu dogon explaining saida period ɗinshi ya fita sannan ya bar ajin.
Wani ma ya shigo bayan ya fita, aka kaɗa bell lokacin Break, ganin kowa yana fita, Banda su yasa Deejarh ta kalla Falilat ta ce.
"nace ke banda kene a fita Break ɗin?,"
Murmushi Falilat tayi sannan ta bata amsa, "ki tsaya kiga ikon Allah mana."
Jin haka Deejarh tayi gum, can saiga Farhad da snacks da kayan maqulashe kala kala ya duresu a gaban su, sannan ya kalla Falilat yana faɗin.
"Auntina waɗannan hadda qawarmu," yayi maganar yana kallon Deejarh da ta saki baki tana kallon su, yayi murmushi sannan yace "mamaki kike ko?,"
"Sosai ma," cewar Deejarh, yace "to ai ba abin mamaki bane, auntina ce ita idan kuma baki yadda ba, ki tambaye ta yana faɗin haka ya fita waje, wajen abokanshi.
Deejarh ta kalla Falilat zatayi magana, Falilat ta rigata da faɗin "haka ne ni ce babba awa ɗaya tsakanin mu, kuma yana girmama ni, nima ina bashi girmanshi."
Deejarh ta ce "amma kuma ana ganin shi, aka ganki za'a ce shine babba,"
Falilat ta ce "Eh mana saboda shi namiji ne ae."
Haka suka cigaba da fira suna taɓa snacks ɗin gaban su har aka dawo class.
Wannan karon macece ta shigo ta koyar dasu Hausa language, 'Malama Fateema' bayan ta gama ta fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi sallah bayan sunje sunyi, sun dawo islamic aka koyar dasu dayake haka tsarin makarantar yake.
Ƙarfe uku dai dai aka tashe su, a tare Deejarh da Falilat da kuma Farhad suka fito.
Tsaye suke a bakin gate na makarantar, Falilat ta kalla Deejarh tana faɗin.
"to kodai zamu rage miki hanya ne, tunda drivern naki bai ƙariso ba?."
Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "an karki damu fa, kuje kawai nasan nan bada ɓata lokaci ba zai ƙariso,"
"to shikenan,"
Falilat ta amsa ta sannan ta shiga motar su driver yaja suka tafi.
Akalla takai minti biyar a tsaye sannan ta hango wata farar mota ta parker, a kusa da ita, da sauri Moses driver ya ƙariso yana faɗin.
"am sorry ma'am Mrs mai kyau ce ta aikeni shiyasa ban ƙariso da wuri ba."
Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "ba komai Moses yanzu shiga mu tafi gida, dan Yunwar da nakeji ba za ta faɗu ba, shiga motar tayi bayan shi ma ya shiga yaja suka bar gurin sai gida.
KANO
Da Gudun tsiya ta taho saboda tsananin saurin da takeyi, in twin's take taka staircases ɗin da sauri ta ƙarisa tsakiyar palon tana sauke haki.
"Ke Jieddarh lafiyar ki kuwa?,"
Auntie da Humaira suka haɗa baki wajen tambayar ta ganin yadda ta sauko kamar wani abu ya biyota.
Tana sauke haki ta musu nuni da haɗaɗɗiyar princely gown dake hannunta.
Cike da farin ciki take faɗin Auntie na kammala, a yau na kammala haɗa gown ɗinnan.
Da sauri Humaira ta karɓa rigar tana faɗin.
"nicely Jieddarh barkanki dai, wannan aiki haka, shimfiɗa rigar tayi a tsakiyar palon tana bin haɗaɗɗiyar rigar da kallo ta haɗu sosai ba ƙarya.
Ɗinki ne irinna ƴa ƴan sarakuna, yaran sarakunan ma ba ƙanana ba.
Da wani kalar tsadadden yadi aka tsara ɗinkin rigar, yadi mai masifar kyau da tsada, sky blue color mai haske.
Rigar bata da hannu, daga sama wajen ƙirji an matse rigar, daga ƙasa kuma ta buɗe, amma ba sosai ba, yanayin tsarin dai irinna ɗinkin yaran sarakai.
Wasu kyawawan stones farare da kuma sky blue color da aka jeresu jikin yadin, da aka ƙawata saman rigar dasu sai sukayi kamar sarƙa.
Daga tsakiyar rigar kuma ta wajen ƙirji wasu haɗaɗɗun flowers ne, sirara sosai aka taho dasu har izuwa ƙasa, yayinda wasu guda bibbiyu kuma aka jasu ta baya ko wani ɓangare biyu.
Sai kuma wani haɗaɗɗen yadi fari ta bayan rigar, doguwa ce rigar sosai, dan sai taja ma ta ƙasa, duk da cewa ita ma Jieddarh ba baya ba akwai ta da tsayi ba ƙarya.
Sai kuma wani haɗaɗɗe kuma kyakyawan yadi fari da aka ƙawata shi da stones sky blue color, sannan aka ɗinke, shi aka zagaye ma'ana dai zayyi kamar shine hannun rigar amma shi daban yake ba haɗe da Rigar ba.
Gefe ma ga wasu Beautifuls hand Gloves farare suma masu ɗauke da adon stones sky blue color, suma sak, ko ince fiye da na yaran sarauta suma daban a gefe ba'a jikin Rigar ba.
Kallon Jieddarh Humaira tayi Bayanta kammala ƙarewa gown ɗin kallo obaa highly.
Tana murmushi ta miƙawa Jieddarh hannunta tana mai faɗin "a gaskiya na yaba da wannan haɗaɗɗiyar Rigar tayi ɗari bisa ɗari 100%. Jieddarh tawa sannu da ƙoƙari fa."
Sannan ma zatayi ma wacca ta ɗinka kyau ɗari bisa dubu, dariya Jieddarh tayi tana faɗin.
"wayyo Humaira bakiji yadda nakeji ba, jina nake kamar nayi tsuntsuwa, naje na yanjo Ranar gasar nan ya dawo yau, kuma yanzu sannan kuma adai dai wannan lokacin a wannan gaɓar" 😝
Humaira ta ce "kisa ranki a inuwa kamar kinyi, babban baƙo ya mutu da dare.
Championship day ɗin aita kusa nan da jibi ne ae."
Kallon Auntie Jieddarh tayi tana washe farare kuma ƙananan teeth ɗinta ta ce.
"Auntie ya kika ga wannan Rigar tayi kuwa?,"
Auntie dake zaune a saman three sieter ta ce, "sosai ai saima Ranar gasa ɗiyata zata fito a cikakiyar princess ta fasa Taro da kyawunta mai ban mamaki."
Fashewa Jieddarh tayi da dariya tana faɗin "wayyo Auntie kuna fasamin kai fa, da wannan ya bawar,"
"Yoo ai gaskiya ake faɗa keɗin kyakyawa ce, a cikin kyawawa ina faɗamiki, mutumiyar keɗin, tauraruwa ce, a cikin kyawawan taurarin dake haske guri," Humaira ce take kwararo wannan zancen a yayinda da take ninke haɗaɗɗiyar gown ɗin.
Jieddarh ta ce "wow it's so very very amazing oh my glamorous Time."
Please Humaira can you imagine, yadda zan kasance a ranar gasar kuwa?."
Ta faɗa tana yin zaman ƴan bori a tsakiyar palon tayi tagumi hannu bibbiyu tana lumshe ido, ga fuskar ta har yanzu a sake take, wanda hakan yaba kyawawan dimples ɗinta duka biyun damar bayyana, dama kuma can koda tayi murmushi ko batayi ba a haka fuskarta take koda yaushe dimples ɗinta a bayyane suke.
Humaira ta ce "komai yayi zam zam, sai dai abu ɗaya da kika manta da shi."
Da sauri Jieddarh ta ce "Menene shi wannan abun?,"
Murmushi Humaira tayi sannan ta ce "banga kin nuna mana, wannan ƴar sandar da yaran sarakuna suke riƙewa ba."
Jieddarh ta bata amsa "ina nan da ita, tana bedroom gata ita ma launin ta sky blue ne, nd White color,"
Humaira ta ce "na lura da gaske kike wannan shirin fa,"
"sosai ma," cewar Jieddarh tana washe baki kamar gonar auduga.
Tashi Humaira tayi ta koma saman two sieter tana faɗin "da kikace 'glamorous' ma tunomin da wani chinese drama mai suna 'OUR GLAMOROUS TIME', kikayi, inason dramar sosai,"
Jieddarh ta ce "ni kuma wacca take cikin dramar nake so, Humaira ta ce 'Zhao liying' kike nufi?,"
"E, mana ta iya act sosai da sosai take burgeni I LIKE HER SO VERY MUCH." Jieddarh ta faɗa tana nufar staircase hannunta riƙe gown ɗin.
ABUJA
Da sallamarta ta shiga palon tana cillah school bag ɗinta sama ta cafowa.
Amsa ma ta sallamar Lailah dake zaune saman two sieter gabanta laptop tayi.
Ɗa go da kanta tayi daga kan laptop ɗin, ta sauke akan Deejarh daketa faman washe ma ta baki.
"ah ah barkanki dai ƴar school, to ya ya school ɗin?, ina fatan dai anyi karatu sosai da sosai?," cewar Lailah cike da fara'a kamar ba ita ba.
Zama Deejarth tayi a tsakiyar palon tana amsawa da "yauwa Auntie Lailah, hala ke kaɗai ce a gidan?,"
"Me kika gani?,"
Lailah ta tambaya tana kallon Deejarh ɗin, dan kuwa ba ƙaramin kyau yarinyar tayi ma ta cikin school uniform ba.
"naga kamar banga kowa bane sai ke, " ta bata amsa, Lailah ta ce "Auntie Zaynerb da Haleesat suna school, sai zuwa anjima zasu dawo, su kuma Auntie Nainarh da Nailah suna up, Momy kuma ta fita hospital kinsan bata cika zaman gida ba."
" toh Balarabiyar india fa, tana ina Deejarh ta tambayeta, murmushi Lailah tayi sannan ta bata amsa.
"Balarabiyar indian ki tana garden tana hutawa, yanzu sai ki tashi ki shiga kiyi wanka ki canza kaya sai ki fito kici lunch ɗinki yana jiranki, shalelen Balarabiyar india😃
"To shikenan,"
Ta amsa sannan ta miƙe ta shige ɗakinta, tana shiga aje jakarta tayi a saman bed, sannan ta cire uniform ɗin jikinta, ta ɗaura towel ta shiga bathroom wanka tayi da brush sannan ta fito ko lotion bata tsaya shafawa ba, ta buɗe wardrobe ta ciro kayan da zata saka.
Cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin English wears, riga doguwa wacca bata wuce gwiwarta ba purple color, sai wando pencil fari, Ribbon tasa ta kamo doguwar sumarta kanta na ainihin fulani baki siqiq ta ɗaure ta, in cute ponytail, sannan tasa p-cap fara.
School bag ɗinta ta buɗe ta ciro wasu littafai guda uku, ɗaya £xercises Book na subject ɗin Basic science, biyu kuma Note Books ne.
Palo ta fito ta sama Lailah bata da alama bedroom ɗinta ta shiga wata ƙila.
Dinning room taje ta zauna a kujerar dinning ɗin, sai da taci abinci ta ƙoshi sannan ta miƙe hannunta riƙe da Books ɗin ta fita waje.
GARD£N ta nufa, a hankali ta Tura ƙofar garden ɗin ta shiga akan wasu haɗaɗɗun kujeru, na hutawa ta hango Lailah da Afeefah zaune, Afeefah tana karanta wani £nglish Book 'HOW TO MAKE FALL IN LOVE,' yayinda Lailah take sarrafa system ɗin dake saman lap's ɗin ta.
Akan kujerar dake lilawa ta zauna tana faɗin "Auntie Lailah ashe Nan kika taho?,"
Lailah ta bata amsa "ae nan na gudo nima,"
Kallon littafan hannun Deejarh ɗin, tayi sai kuma tayi murmushi tambayarta tayi, "wa'innan fah ?.
Dariya Deejarth tayi sannan ta ce "kai Auntie Lailah karatu fa, zanyi da Rubuta, kuma akwai wani Assignment da aka bamu yau a school zaki koyamin."
Lailah tana murmushi ta ce "ah lallai Ƴan makaranta daga zuwa yau har an fara baku Assignment?, to wani subject ne?,"
"Hausa language ne fa, kuma zasuyi wahala sosai," cewar Deejarh tana ya mutsa fuska.
In rushing Lailah take faɗin "to tunda Hausa ne, ki bari in anjima kya ba Auntie Nainarh, tunda ita Hausa ta karanta,"
Deejarh ta ce "ke bazaki iya bane?,"
Lailah ta ce "rabani da wahala, Hausa ai akwai wuya yafi Turanci wahala sosai fa."
Dariya Deejarh tayi ta ce haka Ƴan class ɗinmu suketa faɗa, lokacin da malamar ta bada Assighment ɗin, gata akwaita sauƙin kai ga fara'a🤓
*💋💋SARAUNIYAR🎀KYAU💋💋*
______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
*Page 31&32*
"E gaskiya suka faɗa hausa akwai wuya ga wanda bai iya ba, ni kenan" cewar Lailah.
Saidai kuwa idan mutum bai mayar hankali ba," Afeefah ta bata amsa tana mayar da kallonta kan Deejarh.
Lailah ta ce "nidai ban iya ba, "shine kuma kikeyi yanzu?,"
Deejarh tayi ma ta tambayar tana ƙureta da idanu, murmushi Lailah tayi sannan ta bata amsa.
"ae faɗan Hausa a baki daban, haka zalika rubutawa daban, sannan kuma koyan harshen Hausa shima daban