Header Ads
Showing 105001 words to 108000 words out of 155363 words

Chapter 36 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt

Ads the beginning of article before Image

Nanah Kd   

14 Jun 2024

1038

Ads at the middle of Article

musu Abubakar ya miƙe suka fita daga room ɗin, suka bar Rafi'at tana ma ta sannu haɗe karanto ma ta addu'o'i dan ta fahimci kamar hadda jinnu a zancen.





Kai tsaye office na likita suka wuce bayan sun zauna ne, Abubakar da ya gaza jurewa ya kalla likita cikin son jin ƙarin bayani yace

"Please Dr Khasim ko zan iya samun bayanan Rahoton lafiyar Hajarah kuwa?, danna fahimci akwai abin da yake damunta sosai."





Ajiyar zuciya Dr Khasim ya sauke sannan Ya fara magana


"A gaskiya Mister Mai Kyau akwai abin da yake damun wannan patient Hajarah abubuwa da yawa ma ba abu ɗaya ba."




"Okay Inajin ka kamar mai da mai ke nan?."


Abubakar ya tambaya yana kuma gyara zaman sa sannan ya mayar da gaba ɗaya hankalin sa akan Dr Khasim yana jira yaji abin da zaice.




"To kamar dai Yadda kaji na faɗa Malama Hajarah tana fama da matsaloli daban daban na Farko dai shi ne....


A binkciken da muka gunadanar akan kwakwalwarta shi ne na farko ta manta da gaba ɗaya Ahalin ta da kuma ainihin State da take, sai dai abu ɗaya da ya ba kowa mamaki shi ne....."




Katse sa Abubakar ya yi yana goge zufar da ta karyo masa kana cikin wata kalar murya yake faɗin

"Bangane ba Dr Khasim ban fahimci abin da kake nufi ba kwata kwata wai kana so kace min mutum zai iya mantawa da Ahalin sa ne a dalilin wani hatsari ko kuma taɓin kwakwalwa?."






Murmushi Dr Khasim ya yi sannan ya amsa da


"Of course wannan mai sauƙi ne, amma ka fara dakatawa kaji sauran abubuwan da suke damunta kafin kayi wasu tambayoyin."


Jin haka yasa Abubakar nutsuwa amma zuciyar sa bata bar bugu ba.





Dr khasim ya ci gaba da cewa


"Kamar yadda kaji ne, tabbas ta mance gaba ɗaya memory nata da ya taɓa faruwa a tsakaninta da Ahalinta, sannan kuma ta manta da sunan State da take gaba ɗaya a Brain nata...
Sai dai abu ɗaya shi ne bata manta ko wacece ita ba, ma'ana dai shi ne bata manta sunan ta ba, ko kuma karatun ta ko kuma wani burin ta bata manta dasu ba, sai dai kuma ɓangaren Ahalin ta dai...
A bisa binkciken da muka gabatar shi ne zata iya tunawa da Ahalinta da kuma sunan State nata kamar nanda shekara ɗaya ko fi ye da haka a bisa hasashen wasu manyan likitocin duniya...
Amma idan shekara ɗaya tazo ta wuce wata shekarar ta zagayo bata tuna komai ba, tofah sai dai ayi haƙuri domin kuwa har abada ba zata taɓa tuna komai ba...."





Ido waje wannan karon Abubakar yake kallon Dr Khasim saboda tsananin mamaki ma kasa cewa komai ya yi kawai yana tauna maganganun Dr Khasim ne.






Sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba Wanda ya iya cewa komai, sai can bayan kamar mintuna biyar.
Abubakar ya nisa sannan yace


"Dr Khasim ina da wata tambaya ɗaya fa."


Murmushi Dr Khasim ya yi kana Yace


"Okay Go ahead Inajin ka."



Abubakar Yace "To wai dama can an taɓa samun kalar wannan matsalar ne, mutum ya manta memory nasa da ya taɓa faruwa a tsakanin sa da Ahalin sa a dalilin hatsari ko wani Abun?."



"Eh an taɓa samu a ƙasar China Babban Birnin ƙasar wani mutum ya yi hatsarin mota sai gaba ɗaya ya manta da Ahalin sa da sunan garin sa abin da bai manta ba kawai shi ne shiɗin ɗan kasuwa ne, sannan kuma ƙarin abin mamakin bai manta da harkokin kasuwancin sa ba."







___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆






Page *67&68*



"A ƙasar India an taɓa samun irin haka ba iya nan ba a wasu ƙasashen ma anyi ta samu, amma ni dai a Nigeria wannan ne karo na farko dana tsinci wannan al'amari."

Nan dai Dr Khasim ya ci gaba da yima Abubakar bayani akan matsalolin da suke damun Hajarah.



A taƙaice dai su Abubakar basu suka bar wannan Asibitin ba sai wuraren ƙarfe ɗaya na rana.
Washe gari ma haka suka sake dawowa wurin Hajarah sannan Abubakar ya kuma komawa wurin Dr Khasim ya masa ƙarin bayani akan lafiyar Hajarah.



Sai da suka kwashe tsawon sati ɗaya suna zuwa duba lafiyar Hajarah, zuwa lokacin taji sauƙi sosai, sannan kuma ba ƙaramin shaƙuwa bace ta shiga tsakanin ta da family ɗin Abubakar Mai Kyau dashi kansa dama matarsa Rafi'at, ai ba'a ma maganar Yara su Abdulmaleek domin kuwa wata kalar shaƙuwa ta ban mamaki tayi da Yaran a sati ɗaya kacal.




Zuwa lokacin kuma Abubakar ya gama binkcike akan Hajarah ya gano cewar.
Ita ɗin Ɗalibar psychology ce a wata University dake a nan Abujan, sannan kuma ta kammala karatun gaba ɗaya a Ranar murnar kammala karatun nasu ne ma, bayan an gama, kowa ya watse ita ma tana hanyar ta komawa gidan da take zaune da yake ba'a hostel take zaune ba, shi ne fa wannan hatsari ya auku da ita, Motar da take ciki wasu Ƴan fashi suka tare, ta fito a domin ta gudu wata mota ta bigeta shikuma mai mota yaji tsoron kota mutu ne shi ne ya gudu bai taimaketa ba, shi ne fa su Abubakar suka tsince ta a wurin da abun ya faru hadda jini a jikinta that is all.






To koda Abubakar ya tambaya Hajarah abin da ya faru, anyi sa'a bata manta komai ba, ita ma dai haka ta faɗa masa, a lokacin Rafi'at ta tausaya ma ta sosai domin kuwa abin akwai ban tausayi ace mutum ya manta gaba ɗaya memory nasa wanda ya faru a tsakanin sa da Ahalin sa daɗin daɗawa kuma ace hatta sunan State da yake ya manta abin akwai ciwo obaaaaa.








___*_____*

Satin Hajarah biyu a asibiti mutanen Jigawa State, suka diro Abuja sakamakon kiran su da Abubakar ya yi a waya ya faɗa musu halin da ake ciki.


Kai tsaye Asibitin da aka kwantar da Hajarah suka wuce suma dai bayan isansu suka kuma tabbatar da abin da Abubakar ya faɗa sun tausaya ma ta sosai, musamman da ya kasance suɗin likitoci ne sun san matsalar abin Especially ma Hajiya Zuwairiya da ya kasance ita ɗin ɓangaren ta karanta wato Brain.




___*


Kwanan su biyu suka juya Jigawa State da Hajarah a bisa shawarar da gaba ɗaya suka yanke na qwara ta koma hannun su da zama, kafin asan abin yi tunda ba za ta iya tuna komai ba, indai ɓangaren da ya shafi Rayuwar ta da family nata ne.


Wannan konawa Jigawa State da zama na Hajarah ba ƙaramin faranta Ran Rafi'at ya yi ba, domin kuwa a da sosai ta damu da inda Hajarah ɗin zata zauna tsoro take kar ta barta a gida ita gata ba mazauniya ba wani abu yazo ya shiga tsakanin ta da mijinta. 🤦




Su kuwa ta ɓangaren Yara ba ƙaramin kewar Auntyn su Hajarah suke ba domin kuwa a ɗan sati biyu da suka yi a tare da ita, shaƙuwa ce sosai ta shiga tsakani domin ko Ranar da su Hajiya Harirah zasu koma Jigawa State da ita ba ƙaramin daru aka sha dasu ba.


Shi kuwa ta ɓangaren Malam mai kyau ni dai Nainarh kd ban ma san abin da zan iya rubutawa da alƙalamina ba, saboda Rayuwar sa ya ci gaba da gudanar wa kamar ko yaushe cike da Nasara ta gefe ɗaya kuma ga Ahalin sa.





Sai dai kuma me?.


Sati ɗaya ya wuce, aka zo sati biyu, ita ma ta wuce sai kuma a lokacin Abubakar ya fara jin kewar ta amma dai ya daure, sati ɗaya ya kuma wucewa abu ya kuma girmama, aikuwa ba shiri ya kwashi matar sa Rafi'at da Yaransu suka bi jirgin yamma sai Jigawa State a cewar sa ganin gida zasuje, aikuwa anyi murna da Farin cikin zuwan su sosai barinma dai Hajarah da tayi kewar Yaranta kamar yadda take faɗa, a lokacin kuma Sagir da matar Suwaiba sun daɗe da kammala karatun su, da farko a Rivers State suka fara zama sai kuma daga baya suka koma Kano ɗungurun gun da zama, suma dai sunzo ganin gida da Yaran su biyu a lokacin aikuwa nan aka haɗu.
Kwanan su Abubakar uku a Jigawa State suka koma Abuja saboda yanayin aikin su.







***

Rayuwa ta ci gaba da tafiya Yayin da da Abubakar ya tsiri sabon abu duk bayan wata ɗaya ko sati biyu sai ya uzzurawa Rafi'at sun tafi Jigawa State haka take haƙura suje su dawo.
Da dai taga abin nashi bana ƙarewa bane, wata Ranar lahadi da dare da ya same ta da maganar zuwa Jigawa State gobe sai ce masa tayi.

"Ita fa Wallahi wannan zuwa Jigawa ta gaji dashi, wai tukunna mai yake zuwa yi ne da yake uzzurawa sai an tafi?."


A lokacin murmushi Abubakar ya ma ta sannan Yace

"Nan da lokaci kaɗan zaki sani ko menene..."
Daga haka kuma ya sha re maganar suka dauko wata.



Washe gari kuma ya same ta da maganar zuwa Jigawa aikuwa kai tsaye ta ce masa "ita da Yaranta ba inda zasu sun yafe."




Rayuwa ta ci-gaba da lulawa yau da daɗi gobe babu yayin da Mister Mai Kyau a duk ƙarshen wata sai yaje Jigawa State abin da bayayi a baya.


___*

A wani zuwa da ya yi ne wata Ranar Saturday mahaifin sa Alhaji sameer Lamiɗo ya yi masa wata tambaya, lokacin da suka kaɗaice a palon Alhajin tambayar da ta saka shi yin murmushin jin kunya yana yin ƙasa da kansa

A lokacin kallon Ɗan sa Abubakar Alhaji Sameer Lamiɗo ya yi cike da kulawa sannan ya nisa bayan ya kira sunan Abubakar ya amsa ya ce.

"Wai kuwa nace wannan zuwa da ake mana ba hutu anya ba wani abu ake nema a wurin mu ba kuwa?."


Ya yi maganar mai harshen damo cikin kulawa yana ƙarewa ɗan nasa kallo.



A lokacin ƙasa da kai Abubakar ya yi cike da kunya tabbas maganar Abbhee haka ne daga ƙarshen ƙarshe dai bayan Haleesat Rashid Rayyan yaga wata Ɗiya mace da yaji yana ƙaunar ta fi ye da komai na Rayuwa yana son ta yana ƙaunar ta fi ye da komai idan yace komai tofa koman komai yake nufi.







Ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi sannan ya ɗago yana kallon mahaifin su Alhaji Sameer Lamiɗo kamar yadda shi ma shi ɗin yake kallo, ko kafin ya sama zarafin yin magana Alhaji Sameer Lamiɗo ya riga sa da faɗin


"Iyalinka tasan da maganar kuwa?."


Ɗan waro ido Abubakar ya yi sannan kai tsaye Yace

"A'a bata sani ba, amma dai zata sani nan bada jimawa ba."


Murmushi Alhaji Sameer Lamiɗo ya yi sannan ya kuma cewa ita ɗin ta sa ni kuwa ko kuwa soyayyar ɓangare ɗaya ne?."





"Eh tasani amma dai ta ce wai tana jin kunyar ku, da kuma mata ta."


Abubakar yaba mahaifin nasa amsa Yana dariya ƙasa ƙasa.

Shi ma dai Alhaji Sameer dariyar yake cike da jin daɗi domin kuwa ya yaba da Tarbiyar Yarinyar obaaaaa.



Suna cikin haka saiga Hajiya Harirah ta shigo da yake ita keda turaka, ƙarisawa ciki tayi tana faɗin

"Ikon Allah kace zance ya yi daɗi tunda naga ana faman sheƙa dariya."




Kallon matar nasa Alhaji sameer ya yi "Bayan ta sama wuri ta zauna, har yanzu fuskar sa a washe take yace

"To dai Ɗanki ya sama mata."

"Ɗana kuma wanne a ciki, kuma wacece matar?."


Tayi tambayar tana binsu da kallon jiran amsa.
"Ɗan ki dai Abubakar Wanda yake zaune a gaban ki a halin Yanzu shi ne ya sama mata kuma ita ɗin Ɗiyarki ce."



Alhaji sameer ya bata amsar tambayar ta.



Cike da farin ciki fuska washe Hajiya Harirah ta kalla Abubakar sannan ta rangaɗa buɗa tana faɗin


"Aikuwa muna ta yashi murna, sai dai kuma abu ɗaya har yanzu ban fahimci wacece matar da ya samu ba fa."




"Toh tunda har yanzu baki fahimta ba kawai kije ki kira mana Ɗiyarki Hajarah zaki fahimci komai ai."


Cewar Alhaji sameer, aikuwa ba musu ta miƙe ta fi ce daga palon ba'a daɗe ba.


Sai gata ta dawo Hajarah na take ma ta baya, wuri ta samu ta kuma zama ita kuma Hajarah ta zauna a ƙasa daga can gefe, sannan ta kuma gaisar da Alhaji sameer ya amsa cikin kulawa sannan
Ya kalle ta cikin kulawa ya fara magana



"Hajarah Ɗiyata kinji haka ake yi, kawai sai muji batu waje. Ashe Ɗiyata tayi miji bamu sani ba."


Ya yi maganar ne cikke da Zoyala.


Qasa da kai Hajarah tayi cike da kunya sai dai bata ce komai ba, ganin haka yasa Alhaji sameer ya ci gaba da cewa

"To Yanzu dai Ɗiyartawa tana son Yayan nata ko kuwa dai..."


Sai ya yi shiru bai ƙarisa ba.

Tun daga kan shi kanshi da ya yi maganar har Abubakar mai neman Auren 😋 da kuma Hajiya Harirah dake gefen mijinta gaba ɗaya suka mayar da kallon su akan Hajarah suna jiran amsar da zata bada.






Tsuru tayi idanun ta na kallon lallausar carpet da da take zaune akai Yayin da zuciyarta ke tariyo ma ta abubuwan Alkhairi da wannan family mai tarin albarka suka ma ta tun daga kan rescue nata da Abubakar ya yi shi da matar sa, da kuma ɗaukota da Alhaji sameer shi da kanshi da kuma iyalansa sukayi daga Abuja zuwa Jigawa State, duk da cewa ta manta da memory nata akan Rayuwar ta da gaba ɗaya Ahalinta hatta sunan State da take ba zata iya tunawa ba.

{ kuma dai masu karatu nasan da yawa daga cikin ku zasu ce to me yasa ba'ayi cigiyarta a gidajen Radio ba, to ku sani cewa wancan lokacin ba ɗaya yake da wannan lokacin ba. Yanzu zamani ya sauya ci-gaba yazo sosai, amma kuma wancan lokacin da babanci nesa ba kusa ba🤳 }
**The Nainarh Kd 🔥
Writer 🔥**






Suka ɗaukota daga Abuja suka dawo da ita Jigawa cikin su, suka ci gaba da riƙe ta da gaskiya da amana ba tare da saran zata biyasu da komai ba, wannan shi ne mutun taka ta gaskiya waɗannan Ahali sun kasance masu mutunci.
Ita kuwa idan taƙi Auren Abubakar to ai tayi musu mugun butulci kuwa.


Murmushi tayi tunawa da tayi wancan zuwan Abubakar yadda yake roƙonta akan ta amince ta Aure sa, koma ba haka ba, ai ita ɗin ta daɗe tana ƙaunar sa dama kunya ce kawai ta hanata, kuma dama ta yanke shawarar samun sa ta faɗa masa. Ra'ayin ta a kansa ehee. 🥰







Kallon su tayi cike da farin ciki a zuciyarta a fuskar ta kuwa cike da kunya ta amsa da


"Eh na amince Abbhee ko dan saboda rescue nawa da ya yi aiya cancanta da ya zama shield a gareni na tsawon har Abada."




Tayi maganar ne a lokacin da ta tashi da gudu ta bar palon tana Rufe fuska.🤦

Gaba ɗayan su dariya sukeyi hadda Abubakar ya yi murmushi Mai Kyau kamar yadda shi ma yake Mai Kyau.



Hajiya Harirah ta ce

"Ƴar nema dama can ana so ake kaiwa kasuwa, to dama wata mara sa'arce za'ayi wa tayin wannan haɗaɗden Lu'u'lu'un Mai Kyau taƙi. ai Abubakar ɗina ɗaya cikin Dalas.😎




Dariya suka yi ai nan aka dasa sabuwar fira a tsakani, domin kuwa Abubakar Mai Kyau jinsa Yake ya gama sa'a tunda har zai mallaki wannan kyakyawar fure haka.




Domin kuwa Hajarah kyakyawa ce first class ta haɗu ta ko'ina tunani Yake anya tuwa bata haɗa jini da turawan Yamma ba kuwa, koda kallon Yanayin gashin kanta mai tsayi da sheƙi ga launin shi abin burgewa shi ba baƙi ba kuma ba Brown ba kai duk Yadda kake tunanin kyau tofa Hajarah ta wuce wurin obaaa...




A Ranar Alhaji Sameer Ya kira duka Ƴan uwansa dake kusa. Ya faɗa musu kyakyawar Albishir sannan kuma a Ranar aka saka Ranar Auren Abubakar Sameer Lamiɗo da Hajarah nan da wata Ɗaya tak domin kuwa Alhaji Sameer cewa ya yi "Gwara ayi ayi."






___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙


☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆








Page *69&70*



Abubakar bai sama damar komawa Abuja ba, sai Washe gari ya bi jirgin Safe izuwa Babban birnin Nigeria Abuja, koda ya koma bai sama matar sa Rafi'at da maganar Auren Hajarah da zayyi ba, sai ma harkokin gaban sa ya shiga yi ba ruwansa.




*SATI_ƊAYA_GABA.*



Wata Ranar Sunday wacca Rafi'at ba zata taɓa mantawa da ita a Rayuwar ta ba, ita ce wata Ranar lahadi da Yammaci Abubakar yazo ma ta da maganar ƙarin Aure.

Abin da dai da ya faru shi ne...


A wata Ranar lahadi Rafi'at tana zaune a ƙayataccen palon gidan Wanda yasha kayan ado na duniya ba'a magana, tana sanye cikin shiga ta alfarma hannunta Riƙe da wani Book na Likitoci tana karantawa ga Yaranta a gefe duka sanye jikin shigar Yaran manya suna wasannin su.


Daddaɗar ƙamshin turaren shi ne ya fara kawo wa dogon Hancin ta ziyara, bata iya jurewa ba, sai da ta ɗaga kanta tana kallon kyakyawan mijinta abin alfaharin ko wacce mace ta gari.🥰

Wanda yake tsaye daga tsakiyar staircases sanye cikin kayan shan iska ya ɗaura hannu a waist yana kallon Yaran su cike da Nishaɗi, sannan a hankali ya ƙarisa saukowa daga saman Floor ɗin kana ya ƙariso wurin ta yana sakar ma ta ƙayataccen murmushi Wanda yasa sai da gabanta ya faɗi.

Zama ya yi a 3sieter gefanta ke nan Yana kallonta kamar yadda ita ma ta zuba masa ido tana kallo Like a ta sama TV.


"Matar Mai Kyau Yane ya da wannan kallo haka?."


Abubakar ya yi ma ta tambayar yana dariya.
Murmushi tayi tana faɗin "Mijina Mister Mai Kyau ina son ka, ina ƙaunarka fi ye da Rayuwa ta."

Tsura ma ta ido ya yi yana kallo ya fahimci maganar dake fitowa daga bakinta, ba iya fatar bakinta ya tsaya ba, a'a tunda ga ƙasan zuciyarta take masa maganar, Ajiyar zuciya ya sauke tunani yake anya kuwa ya faɗa ma ta maganar dake a bakin sa kuwa, ko ya fasa sai gaba?.

Kai ina gwara kawai ya faɗa a yau kuma yanzu saboda a kullum lokaci ƙara ja yake yi obaa.




Gyara zamansa ya yi a kujerar yana kuma matsawa kusa da ita, sannan ya kamo hannunta duka biyun kana ya kira sunan ta da wata murya wacca Alƙalamin Nainarh Kd ya yi kaɗan wajen rubuta sufar ta.😘




Amsa wa tayi ita ma cikin faɗuwar gaba maras dalili, ci gaba da cewa ya yi

"Ina so zamuyi wata magana mai muhimmanci dake, shin zamu tsaya anan ne ko kuwa?."


Ya yi maganar idonsa a kanta, murmushin ƙarfin hali ta masa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads