Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 155363 words

Chapter 7 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt

Ads the beginning of article before Image

Nanah Kd   

14 Jun 2024

1007

Ads at the middle of Article

ɗan hasale ta fara magana "waime? ni Haleesat ni ce zan shiga kitchen ɗin huh to akan wani dalili?".
Murmushi Zaynerb tayi sannan ta ce "akan dalilin da yasa kike cin abinci mana" tayi maganar tana kuma bi ta gefan Haleesat zata wuce, "Yauwa kuma kiyi sauri fa, dan kinsan umarnin shalelen Daddy ne ba'a sanya ko jin kiri, Idan kuma akayi tofa rai yana ɓaci kinsan da wannan.
Tana gama faɗin haka tayi gaba abinta.
Tabar Haleesat da cizon yatsa tsaki taja tana bin Zaynerb ɗin da kallon banza dama can basa ga maciji da Zaynerb ɗin cuz indai zasu zauna guri guda tofa saisun raba hali.
Ɗakinta ta shige dayake ɗakunan nasu a jere suke ɗakin Afeefah ne a farko sai na Lailah sai kuma na Zaynerb dake ɗayan Wall side ɗin sannan sai na Haleesat a ƙarshe.


_(The Glam Queen)_ 👑

```Takun Farko```

Story & Written By:
𝔗𝔥𝔢 𝔑𝔞𝔦𝔫𝔞𝔯𝔥 𝔎𝔡

*Page 13&14*

Zaynerb kuwa tana koma wa kitchen, Guri ta samu ta zauna a ɗaya daga cikin chair's na dinning ɗin dake a kitchen ɗin dayake kitchen ɗin babba ne highly.

Kallon Lailah tayi ta ce "Ke Lailah ba haka ake yanka cabbage ba kinje kinayi manya manya keda zaki yanka ƙana na haba, duh Allah ki dinga kula mana.

A hasale Lailah ta juyo, dama da Yayah Afeefah ta samu ta shigo kitchen ɗin gashi tun ba'ayi nisa ba Zaynerb ta fara kushe ta don jan ayi tsiya, ta ce "dan Allah sister Zaynerb zo ki yanka da kanki mana, Haba ni dama na gaji wallahi," Ta faɗa tana dafe goshi duk tabi ta haɗa uban zufa kamar mai amfani da ita ce.

Dariyar ƙetah Zaynerb Tayi sannan ta ce "a'a ba ruwana ae girki sai dai ku Lailah ni dai barni anan inda nake" Ta faɗa tana latsa tsadaddiyar wayar ta, Lailah zata ƙara magana Afeefah tayi mata inkiya da ido alamar tayi shiru qwafa taja kawai ta ci gaba da yayyanka cabbage ɗin da take cikin nutsuwa da rashin qwarewa a fannin.

Jin shiru Haleesat bata zo ba yasa, Zaynerb miƙewa tsaye saboda tsaban rigima irinna ta, Ita ba aikin takeyi ba, Amma don neman magana zata je kiran wata, Tana shirin fita daga kitchen ɗin, Saiga Haleesat ta shigo kitchen ɗin sanye cikin riga doguwa da dogon wando jeans.

"Yauwa ɗiyar albarka kin shigo, To ga rigar girki ki sanya ko sister" Zaynerb ta faɗa tana miƙa mata apron karɓa Haleesat tayi zata ɗaura, Da sauri Zaynerb ta ƙarisa ta bayan Haleesat ɗin ta ɗaure mata igiyar rigar, "Yauwa sis a fara aiki" Cewar Zaynerb tana komawa ta zauna.

Ita dai Haleesat bata kula ta ba, Hasali ma earpiece ta maƙala a kunen ta duka biyun, Kama sumu aikin tayi suka ci gaba da fafatawa dama can ita Haleesat gwana ce wajen iya girki kala kala domin har lecture na koyon girki take zuwa kawai dai shiga kitchen ɗinne ba ra'ayinta ba, A haka suka ci gaba da yi Zaynerb na zaune sai dai idan taga sunyi ba daidai ba tasa baki kuma fah kar kuyi tunanin ta iya ne a'a ko ɗaya ba wani girkin azo a gani ta iya ba kawai tonon tsiwa ne irin nata, Daga ƙarseh ma ɗaukar wayarta tayi tana musu video wai zata ɗaura a Yanar gizo ga ƴaƴan MISTER MAI KYAU guda a kitchen suna girki NEW UPDATE kenan🤣😂😅.

Lailah ce da surutun Zaynerb ya isheta ta juyo tana kallon Zaynerb ɗin ta ce "sister Zaynerb dan Allah zaki iya fita ki bamu guri keba aiki ba sai surutun tsiya haba,"
Zaynerb bata kulata ba ta ci gaba da nuna ma Haleesat wai yadda ake ɓare Maggi mai star, "ke Haleesat na faɗa miki ba haka ake ɓare Maggi ba kin ƙi ganewa, A haka ae zubewa yakeyi haba sis a dinga kula mana," Zaynerb tayi maganar tana miƙewa bayan tayi saving video ɗin data gama ɗaukarsu, Ƙarisawa tayi gurin Haleesat ta karɓa ɓare maggin, "Yauwa to ɗauka wani aikin bari na tayaki wannan🤔.

Ita dai Afeefah sai daɗi takeji Zaynerb ta fara dawo walwalarta kamar da, Bayan lokaci mai tsayin gaske don shekaru biyar baya da Rayuwarta ta shiga tasko farin ciki yayi ƙaranci ciki kuma ya rushe, Bata irin waɗannan abun, Amma yanzu da takeyi hakan na nufin ta manta komai kenan ta barma Allah zaɓinta?.

Haka suka ci gaba da aikin su Zaynerb nayi musu gyara kamar itace boss.
Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci suka kammala haɗa haɗaɗɗen breakfast mai rai da lafiya sannan na Alfarma.
Jerewa sukayi a dinning Room sannan ko wace ta shige haɗaɗɗen bedroom ɗinta domin shiryawa.

Zaynerb tana shiga bedroom ɗin ta bathroom ta shiga takai minti talatin sannan ta fito ɗaure da towel blue color a chest ɗinta, Cikin sauri sauri ta shirya cikin kayan hausawa Atamfa pink mai ratsin fari anyima Atamfar zanen flowers doguwar riga ce mai dogon hannu, Sannan ta kafa ɗaurin ture kaga tsiya kayan sunyi masifar yi mata kyau kamar kamar me, Dama kuma gata mai kyau, Ɗiyar mai kyau, Jikar kyawawa, Feshe Jikin ta tayi da perfumes kala kala masu tsada da sanyin ƙamshi.
Sannan ta fito daga bedroom ɗinta tana baza ƙamshi, dukansu suna zaune a dinning room ɗin suna cin breakfast hadda Daddy MISTER MAI KYAU da Momy Rafi'at, ƙarisawa tayi taja kujera ta zauna tana greetings ɗin Daddy da Momy Rafi'at fuska sake Daddy ya amsa mata gaisuwar har yana tambayar lafiyarta duk da kasancewar lafiyarta ƙalau.
Ita kowa Momy Rafi'at da kyar ta amsa kamar anyi mata dole wai danma taga mijinta MAI KYAU yana gurin ne, Zaynerb kuwa ko a jikin ta da irin amsa gaisuwar ta da Momy Rafi'at tayi, Murmushi ma tayi dan kuwa ita kaɗai tasan irin tsiyar da ta shirya mata, Jira take taga yadda za'ayi aje china a Yau.

...

Bayan sun kammala cin breakfast ɗin palo suka dawo suka zazzauna dayake yau su Lailah basu da lectures Haleesat ce ma take da lectures ɗin a yau amma sai zuwa ƙarfe uku na Yamma.
Lailah da Haleesat ne a palon sai Afeefah suna jiran Mister mai kyau ne dayake zasu rakashi airport zai wuce germany a yau.
Yayinda Zaynerb ta koma ɗakinta bayan ta ce tana fama da headache sama sama, Sai da Zaynerb ta tabbatar da sun fita raka Daddy airport ɗin, Sannan ta fito palon ba kowa dan gabaɗaya Ma`aikatan gidan da masu gyara palon ma sun gama sun koma ɓangaren su, Wanda hakan ba ƙaramin daɗi yayima Zaynerb ba, Don zatafi samun aiwatar da shirinta in carefully.

Upstairs ta hau bedroom ɗin Momy Rafi'at ta nufa kanta tsaye ɗan buɗe ƙofar bedroom ɗin tayi, Ta leƙa kanta a ciki ba kowa shiga tayi dukanta, Ƙaran ruwa taji a toilet da alama wanka takeyi dube dube ta fara a ɗakin amma bata ga komai ba jin alamar an taɓa ƙofar toilet ɗin za'a fito ne yasa ta fita da sauri daga ɗakin.

Kitchen dayake anan Up ɗin ta shiga da sauri sauri bayan wani lokaci ta fito hannun ta ɗauke da robar mai.
A bakin ƙofar ɗakin Momy Rafi'at ta tsaya, Aje robar man tayi a gefe sannan ta ɗauko mopper ta aje a gefe shima, wannan robar man data fara ajewa, ta ɗauko ta juye shi tas a ƙofar ɗakin momyn sannan ta ɗauko moppern ta fara gogewa ta yanda ba za'aga alamar mai ba a gurin ba.
Cikin sauri sauri take aikin don bata buƙatar Momy Rafi'at ta fito ta sameta gurin, Saida ta kammala tas sannan ta mayar da moppern ma'ajiyar ta, roban man ma ta mayar kitchen da sauri sauri ta koma bedroom ɗinta.

AFTER SOME MINUTES

Jin Ƙarar shigowar motar su Afeefah da alama dai har sun dawo daga airport ɗinne.

Palo suka zauna suna ɗan taɓa fira ita ma Zaynerb ɗin ta sauko Down ta dawo palon ta kwanta a saman three sieter tana dafe kanta kamar ciyon kan gaskiya su Afeefah sai sannu suke mata cike da tausayi dan kuwa suna ƙaunar junan su highly.
Haleesat ce ta kalli Zaynerb cike da kulawa ta ce "ki shiga medical room mana ki ɗauki magani kinji sis,"
Ƙasa ƙasa Zaynerb take kallon Haleesat ɗin sannan ta maƙale murya ta ce "karki damu sister nasha fa", T a faɗa da kyar kamar mai ciwon baki, Lailah ta ɗan yi murmushi ta ce "Lallai su Aunty Zaynerb an buɗe file kenan baki ya mutu kamar ba kece mai surutu game da ɗaukar video ɗazu ba,"
Zaynerb bata kulata ba don tafi kowa sanin halin Laila da tsokanar ta, "Sannu kinji sister" cewar Afeefah tana taɓa goshin Zaynerb ɗin taji koda zafi, "Yauwa ƙanwata" Zaynerb ta amsa tana lumshe ido.

𝔐ℜ𝔖_𝔐𝔄ℑ_𝔎𝔜𝔄𝔘

Momy Rafi'at ta gama shirinta tsab na zuwa china da mummunar ƙuduri ta shirya tsab cikin expensive material fari tas da mayafi mai tsada, Ga jakarta shima fari tas ta fito sai baza ƙamshi takeyi, Tafiya takeyi bata kallon gabanta sauri take don saura mintuna goma jirgin su ya tashi ita bata masan ya akayi ta ɓata lokaci haka bata shirya ba.
Cikin tafiyarta batasan ya akayi ba haka zalika bata lura da mai ta taka ba, Sai dai kawai taji wani uban zamiya game da zantsi ya kwashe ta, Aikuwa sai dai tim tittim tim akeji ta faɗi saman tiles, Bata dandara ba ta miƙe da kyar tana dafe ƙuƙurunta saboda wani uban azaba da takeji aikuwa miƙewan data kuma yi santsi ya kuma ɗibarta fiye da farko, Saiga Momy Rafi'at tana faɗowa daga saman staircases gabaɗaya bata dena juyi ba saida tayo kasa tun daga saman bene saida ta dangana da ƙasa.

Da gudu su Haleesat sukayo kanta suna kiran sunan ta amma ina Momy Rafi'at tayi sumar wucin gadi, Dan kuwa ba ƙaramin buguwa tayi ba, Ƙunƙurunta da bayan ta dama sauran jikin ta sai faman kiran sunanta suke cikin tashin hankali, Amma ina Momy Rafi'at bata ma jinsu dan a sume take.
Dq sauri Lailah ta ɗauko ruwa a fridge ta yayyafa mata shiru bata farfaɗo ba, Haleesat hadda kukanta ganin haka yasa Afeefah ƙara yayyafa mata ruwan sai gashi ta farfaɗo tana ihu tana faɗin bayan ta zai ɓalle jikinta ciwo maganar take kamar bata hayyacinta.
Ganin ta kasa tashi yasa Afeefah ta kalli Lailah "Sister mu kaita hospital kawai zaifi, don na fahimci ba ƙaramin buguwa tayi ba," Cewar Afeefah tana kuma kallon yadda Momy Rafi'at take ihu kamar wata karamar yarinya, Da sauri suka taru su ukun banda Zaynerb wacca take kwance a three sieter tana baccin ƙarya, Da kyar suka iya cicci ɓarta suka nufa waje da ita a mota suka sakata sai faman haki suke, Ko tsayawa jiran driver da escort basuyi ba, Afeefah ce taja motar da gudu suka bar gidan zuwa hospital dan ma sunsa mayafan su tun kafin su fito.

Zaynerb kuwa tana tabbatar da sun bar gidan ta fashe da dariya hadda riƙe ciki, A fili ta furta Allah ya ƙara Yasin banji tausayinta ba, Don bata da imani wannan matar har kisan kai zata iya yi tama yi bama zata iya ba, Tsaki taja tana tuna yadda tasha azaba a hannun Momy Rafi'at kafin abin ƙaunar su mahaifin su MISTER MAI KYAU ya ɗaukesu ya mayar dasu Germany.

Zama tayi tana tuna wani lokaci shekaru GOMA SHA ƊAYA baya da Momy Rafi'at take dukan Afeefah, Zaynerb tana kuka tana roƙonta ta dena duka mata ƴar uwanta amma Momy Rafi'at taƙi ji tohm ana cikin haka saiga Daddy yayi dawowar bazata yayi kyakyawar gani kuwa Momy Rafi'at tana dukan shalelen shi da wayar wuta aikuwa a lokacin saida ya saki Momy Rafi'at, Sannan ya ƙwace Yaran shi duka amma banda su Lailah ya bar ƙasar dasu a lokacin sai da kyar aka samu ya mayar da Momy Rafi'at.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta tashi ta hau Up da sauri sauri ta goge duk gurin da ta tabbatar tasa mai sannan ta dawo palo tayi kwanciyar ta abinta.

Koda su Afeefah suka isa asibiti an duba Momy Rafi'at an tabbatar da ta samu goje war ƙashi da wasu gurare a jikin ta da ta sama karaya basu suka baro asibitin ba sai wajen ƙarfe biyu, Gida suka dawo da ita tayi jinyar anan don ita ta zaɓa hakan, Nanfa ƴan uwa da abokan arziki da suke a kusa suka fara zuwa duba jikin ta, Gashi daddy baya ƙasar dole sai Afeefah ce ta kira shi a waya a faɗa mishi Halin da ake ciki.

*°°*

Kwance take saman royal bed ɗin ta, Daga ita sai riga shirt na bacci pink color sai wando short shima pink color.
A hankali ɗan bakinta yake motsawa da alama mafarki takeyi murmushi ta saki ta kuma gyara kwanciyar ta kafin wani lokaci kuma ta buɗe kyawawan idanun ta.
Saukowa tayi daga zaman bed ɗin toilet ta nufa, Tun kafin ta ƙarisa shiga toilet ɗin ta cire short ɗin jikin ta tayi jifa da dashi ita ma rigar cireta tayi, ita ma tayi wurgi da ita gabaɗaya gashin kanta mai uban yawa da tsayi ya rufe mata fuskar ta ya warwatse, Toilet ɗin ta shiga takai minti arba'in ciki.

A hankali ta turo ƙofar toilet ɗin ta fito chest ɗinta ɗaure da towel White color, Da sauri ta ƙarisa gurin expensive wayarta dake kawo wuta, Alamar kira ne ya shigo, Ganin mai kiran nata yasa saida ta fara zauna saman mattress, Sannan tayi picking call ɗin ta kara a kunen ta, Daga cikin wayar mai kiran ya fara magana cikin harshen hausa.

"Hello Madam ansamo brief history na Yarinyar hotunan nan kamar yadda kika nema, Sunanta "Haleesat Abubakar Mai Kyau! Shekarunta Ashrin da uku a duniya, Ita ce ƴa ta hudu a gurin mahaifin su Alhaji Abubakar mai kyau wato dai {Mister mai kyau} wata gila zaki sanshi saboda shi ba ɓoyayyen mutum bane a ƙasar nan, Dama duniya baki ɗaya, Sannan kakanta shine mamallakin wannan shahararren company na magani wato S.L pharmaceutical industry!,"

Ɗan lumshe idanun ta tayi tana jinshi ya civgaba da cewa "tana karantar micro biology anan American University dake a nan Abuja, Sanin da yayi ba sosai take fahimtar hausa ba, Yasa ya ɗanyi full stop da maganar nashi sannan ya ci gaba da cewa.

"Ƙawayenta huɗu ne kacal, Feenah, Zuree, Sai Jennifer, Sai kuma wata da ake kira da Maryam ita ɗin Irregular Friend ɗinta ne.

A halayya kuma ta kasan mace mara son surutu sosai kamar dai ke madam, Ya faɗa cike da zolaya, Ɗan murmushi tayi a gajarce "uhumm" Ina jinka tayi maganar tana kuma gyara zaman wayarta a kunen ta.
Magana ya ci gaba, Sannan kuma bata shan kayan maye sai dai kuma tana busa shisha da sauran su, Amma banda sigari, kana bata kula maza dan zan iya ce miki ma bata da saurayi ko ɗaya, Nan dai ya ci gaba da kwararo mata bayani akan Haleesat yadda zata fahimta da kyau.
Mayar da expensive wayar tayi saman mattress bayan sun kammala wayan ta aje.

Cikin nutsuwa take shirinta tsab ta shirya cikin business suit pink color, Sannan ta ɗauki space pink color shima tasa, Kana ta ɗauki shoes glitter stilettos shima pink color tasa, Hair ɗinta kuwa ta gyara shi in straight style, Hular ta mai wani kalar style da kuma qwal biyu ta saka, Wanda hakan yaba dogon gashin kanta mai tsayi da santsi ga yawa damar fituwa ya sauka a gadon bayanta sannan ta ɗauki coat ɗinta pink wanda aka qawata gaban ta da wasu buttons Golden color masu shaining komai pink color, Tayi kyau highly highly harta gaji kyau gata kamar a wanke hannu a taɓa.

Fitowa tayi harabar hotel ɗin data ke, Zata shiga motar ta ƙirar BMW pink color kenan taji ankira sunanta a bazata.

"ⒽⒺⒶⓇⓉ_ⒸⒽⒺⓃⒼ_ⒿⓊⓃⒼ!!

Fasa shiga motar tayi, A hankali ta juyo domin ganin mai kiran nata, Ɗan waro ido tayi da tsananin mamaki ɗauke saman kyakyawar fuskar ta, Na ganin wacca take a gabanta, Sam bata manta ta ba duk da cewa sun ɗauki shekaru masu ɗan yawa basu haɗu ba.
"Harper David" ce classmate ɗinta da sukayi karatu tare a ƙasar "MALAYSIA" da sauri Harper ta ƙariso gurin ta, "HEART kece kuwa kodai idanuwa nane basa gani da kyau" Ta faɗa tana murza eye ɗinta dan tabbatar da wacca take gabanta.
Sannan kuma duk cikin turanci take mata maganar. Murmushi "HEART" tayi ta ce "ni ce mana,"
"Ohoo to me ya kawo ki Nijeriya nidai nasan baki da wata connection da ƙasar" Cewar Harper, "Business mana" Heart ta bata amsa cikin Hausa, Wannan karon ƙara waro ƙanan idanun ta Harper tayi "oh gosh Ashe har Hausa kike ji?,

"E' mana highly highly ma, Ae ko wata bahaushiyar bata faɗamin Hausa ba" Heart tayi maganar da hausa a bakinta raɗau.
"Harper David ke to meya kawo ki Naija tunda dai kema nasan baki da wata alaqa da ƙasar."

"Yawon buɗe ido mana," Zaro ido HEART tayi cike da mamakin Jin abinda Harper ta faɗa mata "yawon buɗe ido kuma?,"
"E' mana Harper ta bata amsa, "Yanzu dai ba wannan ba, Sauri nakeyi Anyway ga Room card ɗina kawai," HEART tayi maganar tana miƙawa Harper card, Karɓa Harper tayi ta ce. "Okay ni ma dai yanzu akwai gurin da zani dama".
"Okay to shiga motata na rage miki magana mana HEART ta ce ma Harper.

"Ok let's go" cewar Harper shiga motar sukayi suka bar hotel ɗin suna taɓa fira.

[Menene asalin su Afeefah, shin wata kalar ƙiyayya ce a tsakanin Momy Rafi'at da mahaifiyar su Afeefah ne, wacca bata ma a duniyar. Wacece "HEART" wacece Harper ga Jieddarh a gefe duk amsosin waɗannan tambayoyin suna a cikin wannan ƙayataccen Labarin mai suna SARAUNIYAR KYAU]💋👰💋

🅜🅐🅛🅛🅐🅚🅘🅝

🄺🄷🄰🄳🄴🄴🄹🄰🅁🅃🄷
ⓉⒽⒺ ⓃⒶⒾⓃⒶⓇⒽ ⓀⒹ}


🅺🅰🅽🅾

Zaune suke a dinning room suna lunch, Yayinda ƴan aikin gidan ke jere musu lafiyayun Abincicika kala kala masu rai da lafiya wasu kuma na aikin serving ɗinsu cikin nutsuwa, dukansu ƴan gidan ne suke a dinning ɗin, Jieddarh, Humaira sai Heesham da Auntie sai kuma Abba wato Alhaji Jafar Komai Naka.
Dayake dinning table ɗin mai mazaunin mutum takwas ne, cikin nutsuwa suke yin lunch ɗin abinsu.

Bilkisu ce ƴar aikin su budurwa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads