Showing 30001 words to 33000 words out of 155363 words
Chapter 11 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
kenan ba za kiyi shiru ba ko?," cewar Auntie sa'adah tana hararar Deejarh ɗin.
"A"a Yasin nayi shiru bazan ƙara cewa komai ba, tunda na lura bakya so ina faɗar gaskiyar" ita Deejarh ta ba gwaggon nata amsa tana ci gaba da yanka Albasar hannunta.
Ita dai Afeefah tana jin yadda Deejarh gwaggon nata suke kwasar drama, ita kuma tana kwasar dariya, kwando kwando🤣.
Haka dai suka ci gaba da aikin, suna taɓa fira kuma shan dariyar Dije ta ƙauye da ta rikiɗe ta koma Deejarh a Birni🤓.
Har suka kammala haɗa haɗaɗɗen breakfast ɗin tare suke jerewa a dinning room har suka kammala jerewa duka sannan Afeefah ta wuce bedroom ɗin domin yin wanka da Shirin school, ita kuwa Deejarh a faffaɗan plate ta ɗi ba duka kalolin abincin breakfast da suka haɗa, babu kalar da bata ɗi ba san ranta ba, sannan takai ɗakinta, kana ta dawo ta kuma ɗiban juice ɗin da Afeefah ta haɗa ta koma ɗakinta dashi.
Sai da ta cinye abincin data ɗi bo tas ta kora da ruwa game da sassanyar juice sannan ta tashi ta shiga bathroom wanka tayi ta fito ɗaure da towel, kalolin expensives lotion ɗin da ta gani a saman dress mirror ta shafa abinta ba ruwanta, bayan ta gama shafa lotion ɗin wardrobe ta buɗe inda ta shirya kayanta ta ɗauki wasu riga da zani na atamfa da suka ga jiya suka ga yau, ta saka sannan tasa hula da alama kayan basu da kallabine.
Ɗukar plate ɗin da taci abinci a ciki tayi, ta fito haɗaɗɗen palon gidan da bata gajiya da kallon shi, kitchen ta shiga ta wanke plate ɗin, sannan ta mayar dasu ma'ajinsu ta fito daga kitchen ɗin tana bin palon da kallon ƙauyenci.
Sam bata lura da mutanen dake a dinning table suna cin breakfast ba, don a nata shirmen bedroom ɗin Afeefah take nema, amma batasan ko wannene ba ciki ƙerarrun bedroom's dake zagaye da palon, zata wuce ta koma ɗakinta kenan tunda bata ga ɗakin Afeefah ɗin ba, saidai me?, turus taja tunga ganin mutane a dinning room suna cin abinci, cikin nutsuwa da rashin hayaniya, lura da tayi kamar basu lura da'ita ba yasa tayi sauri zata wuce zuwa ɗakin, karaf taji muryar Afeefah tana kiran sunan ta.
A hankali ta juya ta nufa dinning ɗin, ƙarisawa tayi, gaisar da mutanen gurin tayi, bata jira sun amsa ba, ta kalla Afeefah tana washe baki ta ce "Balarabiyar india gani, naji kamar kina kira na ko?," Murmushi Afeefah tayi ta ce "kinci abincin kin ƙoshi kuwa?," "E, naci sosai plate ɗin ma, na mayar kitchen na wanke tas don nasan gidan ƴan gayu nake, Deejarh ta bata amsar amma hankalin ta yana akan kallon Haleesat da Zaynerb da suke mata mugun kama, bata ganesu ba dan jiya bata gansu ba tadai gane Lailah da su fareeda da fadeela.
Mister mai kyau, Daddyn su Afeefah ne ya kalla Deejarh kallon nutsuwa da nazari irinnasu, sannan ya ce cikin muryarsa mai sanyi da taushi da kuma girma, "ɗiyata ya sunan ki, kuma daga wani gari kike?," A hankali kamar mai tsoron magana ta ce "sunana 'Nanah khadijatu' amma ana cemin Dije a ƙauye a birni kuma Deejarh😅.
Ɗan murmushin manya Daddy yayi sannan ya kalla Afeefah ya ce "wato dai ita ce kenan?, yayi ma Afeefah tambayar ne, don tuni tayi mishi faffaɗan bayani akan Dije ɗin yadda zai fahimta, kuma ya fahimta ɗin highly.
Afeefah ta ɗaga mishi kai alamar 'E, sannan ta kalla Deejarth tana murmushi ta ce "Malama Deejarh, Let me explain my family to you.
Nuna Nainarh tayi sannan ta ce "wannan sunan ta Auntie Hassana, amma muna kiranta da sister Nainarh ita ce Babba cikin mu, tanada Aure, amma bata haihu ba tukunna, Deejarh ta ce "Allah ya kawo Yaran masu amfani, suka amsa da Ameen, hadda Nainarh wacca da farko ɗaure fuska tayi, amma tanaji ance Allah ya bata Yara ta saki fuska hadda murmushi, don a duniya bata da wani buri da ya wuce ganin ga ta da yaro ko yarinya wata rana, wannan shine burin Nainarh Abubakar Mai Kyau a Duniya.
Afeefah ta nuna Nailah ta ce wannan kuma sunan ta Auntie Hussaina, ita ma muna kiranta da sister Nailah, twins ne ita da Auntie Nainarh ita ma tanada Aure da yaro ɗaya watan shi bakwai a duniya.
Deejarh tayi murmushi ta ce "ae dama daga ganin su anga ƴan biyu yasin, Afeefah ta kuma yi ma ta nuni da Haleesat ta ci gaba da cewa "ita kuma wannan sunan ta Auntie Haleesat ita ma muna ce mata sis leesat a wani lokacin." Da sauri Deejarh ta ce "Yasin kuma tana kama ƴar indiyar nan miye ma sunan ta ne kuwa?, Yauwa na tuna sunan ta 'Krithi Shetty, wannan mai dimples din gata kyawawa, Yasin komai nasu iri guda da na wannan Haleesa ɗin." Dariya sukayi hadda Haleesat ɗin Afeefah ta ce "haka da yawan mutane suke cewa.
Sannan ta nuna Zaynerb tana murmushi ta ce "ita kuma wannan ƴar kyakyawar da kike gani, ita ce my Lovely Aunty sunanta Auntie Zaynerb sannan rana ɗaya aka haifesu ita da Auntie Haleesat."
Deejarth ta ce " ato kice shiyasa naga suna kama, amma sai dai ita wannan, ta nuna Zaynerb ta ce "tafi kama da meliz ta wannan turkish film ɗin 'Elimi Birakma' wato Rayuwata wannan Turkish actress 'Cemre Baysel' Yanayin gashin kanta mai tsayi da sheƙi iri ɗaya da komai ma, Deejarh tayi maganar ne hango gashin kan Zaynerb da ya leƙo ta Hular dake kan Zaynerb ɗin, da tayi.
Sukayi dariya kafin Afeefah ta kuma cewa wani abu Deejarh ta ce "suma sunada Aure ne?," Afeefah ta zaro ido ta ce "Aure kuma?, a'a basu da, Deejarh da mamaki ya kusa kaita zaune ta ce "cabɗi jan ae wa'innan da'ace a ƙauyen mune da yanzu sun kusa Aurar da Yaran su, ma yasin huh, lallai ƴan birni a gaiaheku.
Dariya Zaynerb tayi ta ce "sai dai kuma nan birni ne ba ƙauyen ku ba.
Afeefah ta ci gaba "wannan kuma ta nuna Lailah ta ce sunan ta Lailah kuma ita ɗin, my sweet sister ta ce, kuma ƙanwata ce don na bata wata biyu, Lailah tayi murmushi ta ce "amma kuma idan aka ganni aka ganki sai dai ace ni ce Babba ko, tayi maganar tana yima Afeefah ɗin gwalo.
Deejarh da bakinta baya shiru ta ce "Yasin Auntie Lailah!.
Lailah ta maka mata harara, Deejarh taja bakinta ta ɗinke da allura😬.
Afeefah tayi dariya ta ce "saikuma wa'innan ta nuna su Fadeela sannan ta nuna Fadeelan ta ce sunan ta Fadeela ita kuma wannan ta kuma nuna Fareeda ta ce sunanta Fareeda suma twin's ne suma, kuma yaran ƙanwar momyn mune." Deejarh ta ce "to amma ina momyn naku take banganta ba?," Da sauri Zaynerb ta ce bata jindaɗi ne shiyasa, tana upstairs, Deejarh ta ce "inane kuma upstairs?," Wannan karon Haleesat ce ta magana ta hanyar cewa, "tana nufin tana bedroom ɗinta acan saman bene," Deejarh ta ce "ohooo, au yanzu na fahimta ae. Afeefah ta ce "saini kuma Shalelen Daddynta da Auntie Zaynerb ɗina, Sunana Afeefah Abubakar Mai Kyau," Deejarh ta ce "suna mai daɗi, Afeefah ta ce "ga kuma Daddyn mu, Mister Mai Kyau."
Deejarh ta kalla Daddyn tana murmushi ta ce "ina kwana Daddyn mu, nima ka zama Daddyna.
Lailah ta ce "ba kun gaisa ba ɗazu?," Deejarh ta ce "E' mana mun gaisa amma wannan gaisuwar ta musamman ce😍.
🆂🅷🅰🆁🅴 🅸🆃 🅿🅻🆂🙏
𝑳𝒐𝒗𝒆💘𝑮𝒍𝒂𝒎𝒐𝒖𝒓💋𝑫𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚😼𝑻𝒐𝒍𝒆𝒓𝒂𝒏𝒄𝒆😥𝑹𝒐𝒎𝒂𝒏𝒊𝒛𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏_𝒉𝒊𝒈𝒉𝒍𝒚🌹𝑫𝒆𝒂𝒕𝒉😭𝑴𝒂𝒔𝒕𝒆𝒓_𝒅𝒆𝒗𝒊𝒍👹𝑪𝒉𝒂𝒎𝒑𝒊𝒐𝒏𝒔𝒉𝒊𝒑👑𝑪𝒉𝒆𝒂𝒕𝒆𝒅🤕𝐁𝐞𝐚𝐮𝐭𝐢𝐟𝐢𝒄𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💅𝑳𝒂𝒖𝒈𝒉𝒆𝒅😆𝒂𝒏𝒅_𝒑𝒆𝒓𝒇𝒆𝒄𝒕_𝒄𝒐𝒖𝒑𝒍𝒆𝒔_𝒓𝒆𝒍𝒂𝒔𝒉𝒊𝒐𝒏😇__𝑨𝒍𝒍_𝒊𝒏_S♥a♥r♥a♥u♥n♥i♥y♥a♥r♥K♥y♥a♥u♥____T⋆a⋆k⋆u⋆n⋆_F⋆a⋆r⋆k⋆o
*💋💋S̑̈Ȃ̈Ȓ̈Ȃ̈Ȗ̈N̑̈Ȋ̈Y̑̈Ȃ̈Ȓ̈ K̑̈Y̑̈Ȃ̈Ȗ̈💋💋*
*💥𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛💥*
Đ₳₲₳ ₳Ⱡ₭₳Ⱡ₳₥ł₦
*💘𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖'𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ💘*
*☆𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝐾𝑑☆*
°°°°°°°°°°°°
*💝LAFAZI WRITTER'S ASSOCIATION💝*🤙®
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><><
*page 19&20*
Sannan ta kalla Afeefah ta ce "Balarabiyar india, bari na koma ɗaki, anjima zan fita in ƙara ganin wannan ƙaton ƙerarren gidan, kamar na shugaban ƙasa." Ko kafin Afeefah tayi magana, tuni Haleesat ta riga ta faɗin, "wannan sunan kuma fa?," Deejarh ta ce "wai Balarabiyar india kike magana?," Haleesat ta ce "E,Shi fa," Deejarh tayi murmushi ta ce "sunan Aunty Afeefah ne, ae nina saka mata, Jiya da dare kuma ya kamata a yanka rago gaskiya." Lailah ta ce "Yau nake ganin ikon Allah ganin ido na, wai ma dakata, to ae naga babu larabawa a ƙasar india ko?," Deejarh ta ce "ae saboda tafi ƴan ƙasar indian kyau ne shiyasa, nake ce mata Balarabiyar india, ko sunan bayyi ba, na canza ya koma Balarabiyar America ko London?," "Aikuwa dai sunan yayi mata kyau obaa highly, inaga a barshi a Balarabiyar India ɗin kawai zaifi," cewar Zaynerb, tana ƙumshe dariya.
Deejarh ta ce "kunji ƴar gari, Lallai Auntie Zaynerb zamu je ƙasar India dake," Nainarh ce da surutun Deejarh ya fara isarta ta ce, " wannan kyakyawar baƙauyiyar yarinyar akwai surutu kamar xixi, baki kamar radio cicihhh ceee basa gajiya, Deejarh ta ce "laha'ila wacece xixi?, hala ita ƴar nan gidan ne, Nailah ta ce "E, mana, ƙanwar mu ce ae," "to tana ina?," Deejarh ta tambaya, Afeefah ta bata amsa da faɗin, "tana karatu a outside," "oh oh inane kuma outside?," Deejarh ta kuma tambaya tana qwalalo ido. Lailah wacca Ƙauyancin Deejarh ya dena bata haushi sai ma dariya, ta ce "tana nufin tana karatu a ƙasar waje ne, are you clear," Deejarh ta ce "au au yanzu na fahimta ae, kallon Afeefah tayi ta ce "Balarabiyar india zan tafi," Afeefah ta gyaɗa mata kai, ba tare da ta ce komai ba, don ta fahimci yarinyar akwai surutu obaa.
Ita kuwa Deejarh barin dining room ɗin tayi ta koma bedroom ɗin da yake matsayin nata a halin yanzu.
Bayan Deejarh tabar gurin Fareeda sarkin gulma, ta ce "gata ƴar kyakyawa abin ta," ita ma Fadeela ta amshe da faɗin "gata bata da duhun kai irinna wasu ƴan ƙauyen, sannan abin da na fahimta da ita shi ne, tana da saurin sabo, Nainarh ce wacca surutu, bai dameta sosai ba, ta ce "barin ma dai idan tana zubo turancin ta na ƴan koya, abin har dariya yake bani, sai dai ta burgeni, don tafi wasu." "turanci kuma, ita ɗin?," Haleesat ta tambaya a mamakance, "E, mana" Nailah ta bata amsa, Haleesat ta ce "yaushe tayi turancin, ban sani ba?," Afeefah tana dariyar ganin yadda Haleesat tayi tambayar idanu waje, ta ce "jiya ne fa, da dare," Fareeda ce yanzu tayi magana, "ae wallahi ina faɗa muku, nasha mamaki, duk da cewa ba turancin azo a gani tayi ba, sai dai, nima ta burgeni, ba ƙarya." Fadeela ta ce "ah gaskiya kam, tayi ƙoƙari, ba laifi."
Deejarh kuwa tana komawa ɗakin ta, kai tsaye bathroom ta shiga, brush tayi kamar yadda tasa ma ranta, sannan ta fito ta kwanta a saman gadon da yake matsayin na ta, kamar da wasa bacci ya kwasheta saman bed ɗin.
Bata fi minti goma da kwanciyar ba, Afeefah ta shigo bedroom ɗin, ganin tana bacci ne yasa tayi murmushi sannan ta rufe mata ƙofar ta fita, da ma school zasu wuce ta ce, bari ta shigo ta ga baƙuwar tasu.
Deejarh ba ita ta tashi daga baccin daya ɗauke ta ba, sai wuraren karfe ɗaya na rana.
Addu'ar tashi daga bacci, ɗauke a bakinta lokacin da ta farka, kai tsaye ba tare da wani ɓata lokaci ba, bathroom ta shiga tayi wanka haɗe da alwala, bayan fitowarta doguwar riga tasa a jikinta, bata tsaya shafa kalolin lotions da suke a saman dress mirror ba, sai da ta idar da sallan sannan ta shafa lotion ɗin da ta shafa da safe, bayan kammala shafa lotion ɗin, hular rigar jikinta ta ɗauka ta saka.
Sannan ta fita waje can farfajiyar gidan garden ta fara zuwa tasha kallon bishiyun kayan mar mari kala kala, kuma ko wata bishiya ta gani indai taga zata iya sai ta hau, saman bishiyar ta cinka ƴa ƴan bishiyar saboda tsaban ji da ƙauyanci, daga garden kai tsaye haɗaɗɗen swimming pool ɗin, gidan ta wuce, aikuwa tasha kallon ikon Allah, dan lokacin da ta ga yadda ruwan waterfall da yake launin sky blue, na gurin yake spray yana zuba ƙasa abin ba ƙaramin burgeta yayi ba, nan ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta ƙarisa gurin ta shiga cikin ruwan tana wanka, tafi ƙarfin sama da mintuna ashirin a haka, sannan ta wuce can wani keɓantaccen guri cikin gidan, gabaɗaya gurin haɗaɗɗun kejuna ne wanda cikin ko wannen su, wasu irin wild animals ne, na cikin daji ake kiwon su, a gurin, tun daga kan, Tsuntsaye masu kyau da ban sha'awa, sai faman karkaɗa wing's nasu suke, ga kuma, wasu karnuwa da launin su yake sky brown irinna turawa, da dai dabbobi kala kala, da yawa a gurin waɗanda lokaci bazai bari nayi bayanin su ba.
Daga nan kaf girman gidan da faɗin shi, ba inda Deejarh bata leƙa ba, tasha kallon tsaruwa da kyau, sai dai tasha ƙauyanci, dan baki wangale take kallon komai.
Bayan ta gama ƙauyancin nata da ƙarewa gidan kallo san ranta sannan ta wuce BQ wajen gwaggon ta, Auntie sa'adah ta ɗan daɗe a gurin gwaggon na ta har wajen la'asar, sai da tayi sallan sannan ta bar ɓangaren.
Ta dawo cikin katafaren palon gidan, ko ɗakinta bata shiga ba ta ƙarisa main palon inda ta hango mutane zazzaune, su Nainarh ne suke kallon wani indian drama "Nannaku prematho" can gefe kuma Afeefah ce ita da Lailah karatu sukeyi, da sauri ta ƙarisa gurin su tana faɗin, "lah Balarabiyar india, yaushe kuka dawo gidan bansani ba?."
"Ah to dama, yaushe zaki sani, bayan kina can wajen yawo, da nuna ƙauyanci, nasan zuwa yanzu kaf ma'aikatan gidan nan babu wanda baisan da zuwan ki ba." Lailah ce tayi ma ta maganar tana ɗan hararar ta.
Washe baki Deejarh tayi ko'a jikinta da irinna maganar da Lailah tayi ma ta, taja wata uwar ajiyar zuciya irinna ƙauyanci, ta ce "hum hum humm, ae ina faɗamiki Auntie Lailah yau nasha kallo, ni ce gurin ruwan feshi, ni ce gurin sam pool, {wai fa swimming pool, take nufi} ke na ƙare miki zance ma, ni ce har gurin bishiyar mangwaro na hau na tsinkosu da yawa," kallon ta Lailah tayi da tsakanin mamakin yarinyar da ya kusa kai ta ƙasa, badin ta na zaune ba, ta ce "bishiya fa, kikace kin hau ?," Deejarh ta kuma Washe baki ta ce "sosai ma, Auntie Lailah dan ma na shanye mangwaron ne, lokacin da na je gurin gwaggona da kuke kiranta da "Auntie sa'adah" da kin gansu jajaye ga daɗi, gasu nunnanu yasin."
Lailah ta ce "amma dai kinyi wanka da kika dawo ko?," tayi ma ta tambayar tana bin ta da wani irin kallo. Deejarh ta ce "a'a banyi ba, yanzu fa na shigo, kuma ae nayi wanka ɗazu kafin nafi ta," Lailah da takeji kamar takai ma ta mari, ta daure ta ce "naji to jeki ki ƙarayi indai kinaso mu shirya ni dake."
Tashi tayi saboda bata so ta ɓata musu rai aƙi sakata makaranta, zata bar gurin ta kalla Afeefah ta ce "hala yau Balarabiyar india tana a zumin magana ne?," murmushi Lailah tayi ta ce "wai Afeefah kike magana, rabu da wannan intern ɗin kawai, don karatun exam ya ɗau wuta, obaa highly." Deejarh da bata jin magana ta ƙyale ba tayi magana ba, tana shirin shiga ɗakinta ta ce "Auntie Lailah Menene kuma intern?," Lailah ta ɗaga murya yadda Deejarh ɗin zataji ta ce "ɗaalibar kwalejin likita," Da sauri Deejarh ta tsaya daga shiga ɗakinta da zatayi ta ce "dama Balarabiyar india likita ce?," Lailah ta ce bata riga ta zama likitan ba, tukunnan tana dai karatun," Deejarh ta ce "Yasin kuma likitanci zai mata kyau," ta faɗa lokacin da take shiga ɗakinta.
Lailah tayi murmushi ta ce "wannan yarinyar ƙauyen, aku kenan mai bakin magana, wai ace daga zuwanta gidan nan, jiya har na ɗan fara sabo da surutunta."
Suna zaune can sai gata ta fito yanzu riga ce na material ash doguwa a jikinta, sai hular saƙa irinna sanyi, da ta saka Ita ma ash color rigar taji duniya ba laifi, don harda faji gefan ta, wannan karon ba gurin su Lailah taje ba ƙarisawa cikin palon tayi wajen su Nailah tayi sannan ta zauna a saman kujera mai ɗaukar mutum biyu, ba ruwanta, kallon Nainarh tayi ta ce "Auntie Nainarh ina ne ɗakin momyn naku na gaisheta naji ɗazu Antie Zaynerb ta ce bata jindaɗi."
Nainarh da surutun yarinyar baya burgeta ta ce "sama zaki hau room na biyu zaki shiga," ta bata amsa a gajarce. "to" ta ce tana miƙewa ta nufa benen sai kuma ta tsaya tana kallon twin's staircase ɗin dake gaban ta ga kuma wani staircase daga right ɗin ta wanda shi ɗaya ne, bawai twin's ba.
Rasa wanne zata bi tayi, juyowa tayi tana kallon, Nainarh ta ce "Auntie wanne zanbi ne?, naga abin naku kashi uku ne," Nainarh ta ce "kibi Right kawai."
'To ta kuma cewa sannan ta fara taka staircase ɗin, har ta hau sama, "Yauwa yanzu, na wuce room na ɗaya, ta faɗa a lokacin da ta wuce gurin, ɗaki na biyu ta shiga.
Da shigarta wani irin ƙamshi wanda tunda take a duniya bata taɓa shaƙar mai kala dashi bama, balle shi, ya ziyarci duka ƙofofin hancinta, ae ba shiri ta lumshe idanun ta tana kuma shaƙar ƙamshin da kyau, huh mutumiyar taku fa, ita da tazo duba mara lafiya sai ta ɓige da kallon irin kyau da tsaruwar bedroom ɗin, a fili ta ce "cabɗijan wannan ɗakin yasin kona matar shugaban ƙasa albarka, wannan kyau da tsaruwa haka, ah lallai birni ana murewa," haka dai ta dingi sambatu, tana ƙarewa ɗakin kallo, san ranta, Sannan ta fito ganin da tayi matar tana bacci.
Ƙasa ta sauko ta zauna a kujerar da ta fara zama, Nailah ta ce "duba mara lafiyar ne kika daɗe haka?," Deejarh tana ƙumshe dariya ta ce "na tsaya na tayata fira ne ae."
Ta farka ne?, Lailah ta tambaya, Deejarh ta ce "E, mana, amma ta koma, lokacin da zan fito," sannan ta kalla Nailah ta ce "Aunty wai ina waɗannan ƴan biyun?, naga bangansu ba." Nailah ta ce "wai Fareeda da Fadeela kike nufi?," ta ce "E, su," "Allah sarki ae sun tafi gida, tun ɗazu," Nailah