Showing 3001 words to 6000 words out of 155363 words
Chapter 2 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
taji haushin ganin yadda zahrah ɗin duk tabi ta firgice da ganin zuwan afeefarh ɗin saikace ba da ƙƴar aka samu tazo ba..
Oh sorry my friend banma kula dake ba,murnar ganin feefarh mai kyau ne,yasa ban gankiba wallahi,zahrah ta faɗa tana kama kunnenta alamar ban hakuri. .
Haleesarth zatayi magana lailah ta rigata da cewa "kunga kuzo muje anata kiran birthday girl fa,wani lokacin a ƙarisa wannan topic ɗin..
Murmushi zahrah tayi sannan tace "okay shall we" ɗunguma sukayi dukansu ukun suka shiga wajen birthday party da yake cike da manyan yara maza da mata masuji da tashen quruciya da dukiya ta iyayensu...
An kammala komai an shirya komai ,anzo wajen yanka cake ,yanka cake ɗin zahrah tayi da wani madaidaicin ATM card dake hannunta sannan taci taba saurayinta abdul a baki shima ya bata nan wajen ya ɗauka sowa samari da ƴan mata ana faɗin "happy birthday to you zahrah. ..
Hakadai abin nasu wallah👯
Ita dai afeefarh tana daga gefe burin ta ayi a gama su koma gida kafin daddy MISTER MAI ƘYAU ya dawo basunan domin kuwa idan ya rigasu komawa da akwai ƙura over highly.
"Assalamu Alaiki Yake ƙyaƙyawa cikin kyawawa, tauraruwa cikin ƙyawawan taurari wacca take haske duk wani waje"
Wannan Maganar ne ya dira mata a kunnenta wanda hakan yasa saida tsigar jikinta ya miƙe saboda batayi tsammani ba taji muryar mai maganar ya dira a kunnenta.
Wata Sansanyar murya ta bayanta akayi mata sallama da yabo lokaci guda.
Bata Juya ba kuma bata amsa sallamar ba saidai ta amsa cikin zuciyarta...
Sallamar aka ƙarayi mata still,a fusace ta juya da niyyar yima ko ma waye masifa,sai kuma me?.
Ido huɗu sukayi dashi yana kallon ta,itama tana kallon shi.
Zata iya cewa gaban ta ya ɗan faɗi kaɗan,sakamakon ƙyawawan idanun shi daya kafe ta dasu..
Shiru tayi tana ƙare mishi kallo from head to toe. ..
Fari ne shi amma ba fari cancan ba,bashi da tsayi highly highly,irin can ɗinnan amma fa,he`s so cute nd beautiful obaa..
Launin kwayar idanun shi Brown color kamar na mage,ya tara suma akanshi baki sidiq irinna fulanin usul gata tasha gyara in stylishly...
SARAUNIYAR KYAU* 💓
_(The Glam Queen)_ 👑
```Takun Farko```
Story & Written By:
*_Ⓣⓗⓔ Ⓝⓐⓘⓝⓐⓡⓗ ⓀⒹ_*
_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._
*ℙ𝕃𝔼𝔸𝕊𝔼 𝕊ℍ𝔸ℝ𝔼 𝕀𝕋 𝔽𝕆ℝ 𝔼𝕍𝔼ℝ𝕐𝕆ℕ𝔼*
*Page 5&6*
Sanye yake cikin ƙananan kaya T-shirt fara da wando crazy Jeans ash color, kansa ba hula, kunnensa ɗaya manne da ɗan kunnen barima irin wannan wanda maza suke sakawa na gayu, shi ɗin cikakken gaye ne mai ji da kuruciya da gayu ga kuma naira.
Cikin sakanin da ba za su wuce uku zuwa huɗu ba, ta gama ƙare mishi kallo ta cikin glashin dake fuskarta, kai ba za ka ce shi take kallo ba saboda yadda ta tsare gida. Shekarun shi baza su wuce ashirin da huɗu zuwa da biyar ba a iya lissafinta.
Muryarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
"Hey babe am Sabbir Salis Mai Naira, amma an fi kira na da S.S Gidan Naira."
Ya faɗi hakan yana miƙa mata hannu alamar su gaisa. Hannun nasa take bi da kallo ita ba ta ba shi nata ba, kuma ba ta masa magana.
Ɗan sosa sumar kansa ya yi ganin ba ta kulashi ba. Sannan ya cusa hannunsa ɗaya cikin aljihun wando, ya gyara tsayuwarsa sannan ya ce, "Please beautiful! A taƙaice dai za mu iya zama abokai?" Ya faɗa yana wani kanne mata ido ɗaya irin na tatattun ƴan duniya.
"Oh da gaske amma saboda me za mu zama abokai?" Ta tambaya ba tare da ta bari sun haɗa ido ba, don kuwa sai ya sa ta ba shi eleven ɗinta ba tare da ta sani ba, da wadnnan shegun idanun nasa.
Murmushi ya yi, "Because you are so beautiful!" Ya ba ta amsa yana ƙara kashe murya.
Za ta iya cewa ya ba ta dariya wannan kashe murya haka, haka ko mace albarka. Ba tare da ta kuma kallon shi ba ta ce, "Hmmm! I'm Lailah Abubakar Mai Kyau!"
Ta faɗa tana yamutsa fuska don ya ta kura mata shi ya sa ta faɗa masa sunan Lailah komai ta fanjma fanjam.
"Lailah, wow nice name! Am so Amazed meeting you."
"Me too!" Ta ba shi amsa tana kokarin barin gurin domin kuwa ta gaji da tsayuwar, da sauri ya sha gabanta sannan ya ce, "Sorry ba ki ba ni eleven naki ba?" Ya faɗa yana marairaicewa tamkar maraya.
Ganin dai zai tara mata mutane ne ya sa ta ba shi lambar Lailah da yake duka wayoyin har da ma na Haleesarth suna hannunta.
Da sauri ya kwashe lambar data karanto masa cikin dankareriyar wayarsa, don bala'i saboda ya tabbatar sai da ya kira ya ji ko tatan ce ko kuwa, ɗauko wayar ta yi a handbag ɗinta ta nuna masa sannan ta ce,"Shi ke nan ko da wani abu?"
Murmushi ya yi ganin ya sama lambarta, ita kuwa Afeefarh ba ta tsaya jin surutun da yake koarin yi mata ba tabar gurin.
Jin an dafa shoulder ɗinsa ne yasa shi jujowa, "Ah Haydar, kai ne ashe."
Murmushi Hydar ya yi sannan ya ce, "To ya an samu nasara ko kuwa?" Ya tambaya yana kallon Sabbir da fuskarsa take ɗauke da ƙayataccen murmushi.
"An samu da ƙyar amma fa..." Ya faɗa yana dafe saitin zuciyarsa.
"To kai Shar Shar, tunda ka samu Haydar." Ya faɗa cikin murmushi sannan ya ci gaba da cewa, "Amma na ji kamar ƴar uwarta ka ce kana so fa, to ya haka?"
AFEEFARH
Ɓangaren Afeefarh fita waje ta yi wajen da suka parker motocinsu, tana jiran su Haleesarth.
A taƙaice dai su Afeefarh ba su suka bar gurin Birthday ɗin ba sai wajen takwas na dare.
Burin su bai wuce ace daddy bai dawo ba,dan sunsan idan ya dawo kashin su ya bushe..
"Oh my God !! Rashin sa`a cewar Haleesarth Lokacin da security gate man ya wangale musu wagameman gate ɗin katafaren Gidan nasu,idansu bai sauka Ko`ina ba sai a parking space...
Da Jerin Motocin MISTER MAI ƘYAU da suke a pake suka yi arba. Ko gama daidaita parking haleesarth datayi driving nasu yanzu batayi ba suka fito dukansu.
Palo suka shiga da Mister mai kyau suka fara cin karo yana kaikawa da qaton palon hankali a tashe....
A hankali suka fara taku saɗan saɗab kamar mara sa gaskiya cikin palon aikuwa kamar ance mister mai ƙyau juyo sukayi four eyes da afeefarh dama itace a gaba.
Da sauri ya qariso gurin hannunta dake rawa kamar mazari ya kamo.
A hankali ya fara magana kamar mai jin tsoron wani abu ya raba shi da ita shalelensa.
"Shalelena ba abin da ya same ki please tell me. Gabaɗaya na shiga damuwa na dawo gida bakunan".
Murmushi Afeefarh ta yi tana kara jin ƙaunar mahaifin nata da wannan ƙauna da yake nuna mata da kulawa.
"Ah Daddy karka damu indai ni ce babu abin da zai same ni muddin kana tare da ni lovely daddy, yanzu birthday party ɗin zahrah classmate ɗinmu muka je mun yi tunanin bazaka barmu bane shi yasa muka yi satar hanya amma muna ba da haƙuri our apologize."
"To amma shalele mai ya sa ba ku tafi da guards ba, kun fa san yadda ƙasar nan ta lalace." Mister mai Kyau ya kuma faɗa.
"Dad! Mu fa ba ma son hayaniya ne shi yasa ba mu tafi da escort ba."
Tun kafin ya kuma cewa komai ta riga shi da kara faɗin, "I need to take shower, na gaji sosai daddy."
Murmushi Mister Mai Kyau ya yi sannan ya ce, "To shi ke nan shalelena, yi sauri ki je ki yi wanka ki huta kin ji?" Ya faɗa yana duban inda su Haleesarth suke sai dai me? Wayam babu ba su sun gudu, ya girgiza kai cikin murmushi irin na manya.
Dariya Afeefarh ta yi ta ce "Daddy ke nan ai tun ɗazu suka shige bedroom nasu ta faɗa tana kuma murmushi.
Daddy Bai kuma cewa komai ba ya wuce dining table wajen Matar Gidan Haj. Rafi'at {Mrs Mai Kyau}Sai dai yaranta sun fi kiran ta da Momy Ko kuma Momy Rafi'at, musamman Zaynerb da Afeefarh sun fi kiran ta da haka a matsayinta na kishiyar mahaifiyarsu Hajara da ta daɗe da rasuwa tun haihuwar Afeefarh.
Momy Rafi'at ta kasance kyakyawar Bafulatana ce kyakyawar ƙarshe ajin farko, ta kasance mace mai son a girmama ta na ɗaya, ta kasance mace mai son mijinta Mister Mai Kyau fiye da komai a rayuwarta na biyu, ta kasance mace mai bala'in saurin fushi da gaza fahimta kuma ita tana so a fahimce ta na uku, ta kasance mace mai Bala`in iya ɗaukar wanka da shiga na kece raini domin kuwa sometimes idan ta ɗauki wanka ta saka mayafi da glass kai ba za ka yi tunanin shekatunta Hamsin da ɗauriya a duniya ba, tunani za ka yi ba ta wuce 30yrs ba, na huɗu ta kasance babu wasu wadnda ta taɓa tsana a duniya ko na ce ta tsana sama da Zainab da kanwarta Afeefarh ta tsane su, sama da mutuwarta, sai dai ba ta taɓa nunawa ko a fuska ba, tun shekaru goma sha daya" baya da ta yi kuskuren yi wa Zaynerb da Afeefarh dukan mutuwa a kan dalilin da bai kai ya kawo ba, ai kuwa lokacin ta ga masifa da bala'i domin sai da mijinta ya sake ta a lokacin, kuma ya ɗauki yaransa Zaynerb da Afeefarh ya bar ƙasar da su tsawon shekaru shida sannan da ƙyar aka samu ya dawo, tun lokacin ba ta ƙara yunƙuri ko gigin sake dukan su ba, sai dai ba wai don tsanar su ta bar zuciyarta ba, a'a sai dai don ba ta so mijinta ya ƙara sakin ta, domin wancan lokacin da ya sake ta ta sha matukar wahala kafin ya dawo da ita don sai da ta shekara guda cur sannan aka samu ya haƙura aka mayar da aurensu.
Shi ya sa take danne tsanar tasu a zuciyarta ba wai don ta ƙyale su ba, a'a ɗaurin talala ta yi musu ya gama nuna musu ƙaunar.
Da yake tana da katafaren asibiti nata na ƙashin kanta a tsakiyar garin Abuja, tana aiki a can shi ya sa mafi yawan lokuta take cikin busy da yake asibitin nata Pediaric ne.
Yau ma around 6:pm ta dawo asibiti a gajiye ta sama mijinta Mister Mai Kyau cikin tashin hankali wai ya dawo gida bai ga shalelensa ba hankalin shi ya tashi yake faɗa mata.
Abin ba ƙaramim sosa mata rai da ba ta haushi ya yi ba, kawai ba yadda ta iya ne ta danne ɓacin ranta ta ki kula shi, sai dai abin yana nuƙurƙusar ta ƙasan rai. To ban da latsinsa ma da rashin son gaskiya, Afeefarh ce kaɗai ba ta gidan, ai har da su Lailah da Haleesarth amma Afeefarh ya tuna saboda ita ce ƴar gold sauran ko oho.
Da ta gaji da abin nasa bayan ta yi wanka ta shirya cikin jallabiya ruwan madara da mayafi shi ne fa ta fito palon ƙasa inda yake tsaye har yanzu, ba ta kula shi ba ta karasa haɗaɗɗen dining room ma'aikata suka yi serving nata ta fara cin abinci hankali kwance.
Tana nan zaune Afeefarh suka shigo palon kuma tana jin duka abin da suka tattauna sai dai ba ta kula su ba, har Mister Mai Kyau ya dawo dining room ɗin ya zauna cikin washe baki.
Ma'aikaciyar ce cikin rawar jiki ta fara kici-kicin serving ɗinsa, ai kuwa cikin zafin nama Momy Rafi'at ta yi saurin miƙewa tana mai daka wa 'yar aikin tsawa a kan za ta yi serving mijinta abinci abin da ko da gigin wasa ba su taɓa ba, tana mata tsiya dan bala'i gefe guda kuma tana antayawa Afeefarh da za ta wuce ta side ɗin hararar tsana.
Ita ma Afeefarh ba ta kuma magana ba ta nufi bedroom ɗinta ko kula momy Rafi'at da ke antaya mata harara ta gefan ido ba ta yi ba.
KANO
Da gudu ta shigo bedroom ɗin tana ƙwala wa Jieddarh kira, "Jieddarh, Jieddarh. Ke Jieddarh!" Hango ta ta yi saman gado ta yi ɗai-ɗai tana ƙwasar barci.
Da sauri ta hau kan bed ɗin tana kiran sunanta, "Jieddarh ki tashi takardar ki ta fito nan da wata ɗaya za ki fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin Jaha.
𝔗𝔥𝔦𝔰 𝔦𝔰 𝔐𝔶 𝔉𝔦𝔯𝔰𝔱 𝔑𝔬𝔳𝔢𝔩 𝔖𝔥𝔞𝔯𝔢 𝔦𝔱 𝔣𝔬𝔯 𝔢𝔳𝔢𝔯𝔶𝔬𝔫𝔢 𝔭𝔩𝔢̨𝔞𝔰𝔢🙏
SARAUNIYAR KYAU* 💓
_(The Glam Queen)_ 👑
```Takun Farko```
Story & Written By:
🅣🅗🅔 🅝🅐🅘🅝🅐🅡🅗 🅚🅓
*page7&8*
A hankali ta buɗe fararen idanunta ta ware su akan fuskar ʜumaira dake mata magana.
maƙalƙale ʜumaira tayi ta miƙe tsaye tana rawa da juyi saman bed ɗin ita ma ʜumaira tana taya ta.
Da sauri ta dira daga saman bed ɗin. ᴛa fita daga bedroom ɗin gabaɗaya. ɪta ma ʜumaira ta rufa mata baya. ᴅa gudu ta ɗare jikin wata ƴar ƙyaƙyawar dumadumar mata baƙa,ᴅake palon wacca ba za ta wuce shekaru arba'in da huɗu zuwa da biyar ba.
Tana faɗin "Auntie nayi nasara zan fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha nanda one month"...
Da sauri ƴar dumadumar matar da jieddarh ta kira da "Auntie tayi saurin yin, rijecting ɗin wayar da takeyi sannan ta juyo da jieddarh gabanta tana tambayarta,abinda ke faruwa.
Cike da farin ciki jieddarh ta ce "Auntie an zaɓeni, zan fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha fa"..
Ƙayataccen murmushi Auntie Tayi,ba tare da tace komai ba.
Ita ma jieddarh bakinta washe yake kamar gonar auduga, ᴢama tayi saman two sieter kusa da ʜumaira tana faɗin "Auntie yau ina cikin farin ciki burina Ya kusa cika zan zama SARAUNIYAR KYAU" ta faɗa tana rungumo hannun ta a ƙirji Tana lumshe kyawawan idanun ta kamar mai jin bacci.
"murnar mai akeyi ne BRITISH QUEEN?" muryar ʜeesham taji yana magana da sauri ta juya tana kallon ƙofar palon ta wajen da ta jiyo muryar shi, tsaye yake jikin ƙofar ya rungumo hannun shi ta baya yana sakar mata ƙayataccen murmushi.
Da gudu ta miƙe tsaye ta ƙarisa gurin shi, ʏi tayi kamar zata rungume shi, sai kuma ta fasa ta tsaya a gaban shi tana sauke ajiyar zuciya, cikin murya mai sanyi tace "Yaa .H. yau ina cikin farin ciki burina zai cika an zaɓeni a cikin waɗanda zasu fito gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha.
"Da gaske take, ku rantse mana" ya tambaya yana kallon ʜumaira dake murmushi ɗaga mishi kanta tayi alamar haka ne.
Gyara tsayuwar sa sayayi a gaban ta kamar wani soja yayi saluting ɗinta yana dariya.
Ita ma salute ɗin shi tayi tana murmushi ta ce "Yaa .H. kaga daga na zama SARAUNIYAR KYAU ta jaha sai ta ƙasa daga ta ƙasa saina duniya ko", ta tambaya tana kallon shi.
Dariyar da ba shiri Auntie Tayi ta na faɗin "yarinya kenan waya faɗa miki daga na jaha saina ƙasa akwai wasu gaba"..
"Wanne da wanne kenan jieddarh ta tambayi Auntien tana zama a kujera, ʙayan ta dawo gurin.
Dukansu gyara zama sukayi suna kallon Auntie murmushi Auntie ta yi a zuciyar ta ta ce "anzo gurin Yarinya Jieddarh GO AHEAD Muje zuwa"...
Muskuɗawa tayi sannan "ta ce na farko dai da ace a ƙauye kike to saikin fara cin na local government sannan azo na State idan shima na state kinci sai azo.
Na state`s talatin da shida na ƙasar nan, shima sai kinyi winning sannan kuma azo na ƙasa, Bayan wasu ƙananu da za`ayi waɗanda su ba dole,bane domin ko anyi ko ba`ayi ba za`a iya shiga na ƙasa.
Kana azo a haɗa ƴan waɗannan ƙasar da wacan ƙasar shima idan kinyi winning akwai wasu da yawa sannan kuma azo uban gayyar na DUNIYA!.
Jikin jieddarh ne yayi sanyi jin waɗannan uban lissafi ita awa na state ɗinma ya aka ƙare balle na duniya Allah yasa taci na jahan ma tukunna, Toh dama Haka Abin Yake Idan akazo maganar sai taji jikinta Yayi sanyi laqwas....
"Aini nasan indai jieddarh ce zata cinye waɗannan tuni, wae bakuga wannan kyau ɗin bane ae ko wata ƴar american albarka come on mana Jieddarh yane wae da rasa qwarin gwiwa haka, haba mana keɗin fa, kece SARAUNIYAR KYAU ta gidan mu", Humaira ce duk tayi waɗannan maganar a domin kwantar ma da jieddarh hankali, fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, "Ko ba haka ba Yaa .H. da sauri yace Haka ne mana na yarda highly.
Ganin yadda jikin jieddarh ɗin har yanzu Yake a sanyaye yasa Auntie faɗin "kuma ae nasan yarinyar tawa kyakyawace zata ciyo mana kyauta na musamman,nasan da wannan.
Washe baki jieddarh tayi dan kuwa a kullum tanaso taji ana yabon ta, ana ƙara mata ƙarfin gwiwa, ana ƙara zugata kanta na hayaƙi😇.
"Kinga yanzu sai a fara shirya shirye ko?" cewar ʜumaira, Da sauri jieddarh ta ce "eh Haka ne to amma dame za'a fara?.
"Ku shirya kawai na kaiku kuyi shopping tun yau kuma yanzu ku zaɓo duk abin da ranku ke so, nauyin payment na ɗauka", Heesham ya faɗa yana kallon Humaira ɗin da ita Jieddarh.
Da sauri suka miƙe tsaitsaye harda ruga ruge "kabamu minti biyar kawai Yanzu zamu shirya no wasting time suka faɗa a tare suna nufar hanyar staircases domin shiga bedroom don shiri domin kuwa a kullum Burinsu a fita shopping basa gajiya sam ko kaɗan da outing🥰.
Sallama suka ma Auntie Bayan sun shirya suka fita shopping mall aikuwa dai sun jido kaya kala kala a gurare daban daban Wani ma, ba amfani zayyi ba,kawai don a kashe kuɗaɗe suka jido.
Basu suka dawo ba sai da suka biya suka sha ice cream cheese Burger e.t.c.
Daga ƙarshe ma sai da aka biya dasu sukayi salon sannan suka dawo gida.
Aikuwa dai a gajiye suka dawo gidan,domin kuwa ko gurin Auntie basu biya ba don ko ba ƙaramin gajiya suka kwaso ba.zuwa lokacin Dare ya lula kowannen su wucewa bedroom ɗinsa yayi domin samun Hutuu...
WANNAN KENAN