Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 155363 words

Chapter 10 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt

Ads the beginning of article before Image

Nanah Kd   

14 Jun 2024

1008

Ads at the middle of Article

take gaishesu su kuma ba kunya sun amsa a zuciyarta ta ce "bala'i Yasin ba shegiyar da zan gaisar tunda ba'a haifeni ba caɓɗijan, gyara tsayuwar ta tayi tana kuma bin mutanen palon da kallo a zuciyarta ta ce wa'innan suba turawa suba larabawa sannan kuma ba chanistawa bah🤣😂😅.

Afeefah dake saukowa downstairs ta hango mutane tsaye a palo kamar masu jiran kota kwana ga wasu abubuwa hannunsu kamar tsummokara🤣.
Ita batama gane su ba saida ta kusa saukowa sannan ta gane kosu waye cike farin ciki ta ce "laha'ila Auntie sa'adah kece?," da ɗan saurinta ta ƙarisa saukowa sannan ta ƙariso gurin su tana faɗin "Auntie sa'adah yaushe kika dawo ne?, yana ganki a tsaye ki zauna mana please, kallon Dije tayi wacca ta zuba mata ido kamar zasu zubo ƙasa saboda kallo.
"Lah Auntie sa'adah wannan fah?, ta tambaya bayan su Dije sun zauna a two sieter ita kuma ta zauna a one sieter. murmushi Auntie sa'adah tayi sannan ta ce "wannan ƴar yaya tace nazo da ita zata dinga tayani girki da wasu ayyukan. tayi maganar a gajarce.
Murmushi Afeefah tayi Sannan ta ƙara kallon ƴar kyakyawar baƙauyiyar yarinyar dake kallon ta har yanzu kamar ta sama television, ta ce "barkanki dai please may i know your name?,"

"Sunana die dee deejarth, eh deejarh." Dije ta faɗa cikin inda inda, game da daburcewa na ganin tsantsan kyau irinna wannan kyakyawar halitta dake gabanta.
"Hala dai kina inn inane" Afeefah ta tambaya.
Da sauri Dije ta ce "a'a banayi 'Balarabiyar india'.
Murmushi Afeefah tayi ta ce "Wacece kuma 'Balarabiyar indiyar?." Dije ta ce "ke mana ae kece 'Balarabiyar india' don naga kinfi wa'incan kyau, ne sa ba kusa ba Yasin. Ta faɗa tana nuna mutanen palon da suke harkar gabansu kamar basusan da wata hallitar a gurin ba inma sun sani to basu damu dasu bah🙄.

Kallon su duka Afeefah tayi yaran ƙanwar Momy Rafi'at ne Hajiya Sailiba, su biyu fareeda da fadeela twins ne sai kuma Lailah dake kwance a Three sieter da alama karatu take bacci ya ɗauketa sai kuma can dinning table Nainarh da Nailah ne suke cin dinner ɗinsu.

"To Ke ma miye sunanki" Dije ta tambaya.
"Sunana Afeefah Abubakar Mai ƙyau", "wow nice name" cewar Dije hadda haɗawa da ɗan turancinta da ta kowa a makarantar ƙauyensu. Ta kuma cewa "i'm very pleasure to meet you.
A wannan karon ba iya Afeefah ba hatta su fadeela, fareeda,su Nainarh da Nailah dake dinning room saida suka juyo suna kallon Dije da tayi maganar dan kuwa basuyi tunanin tanajin turanci ba, tun daga yanayin shigar dake jikin ta, huh to akan mema zasuyi tunanin tana jin turanci bayan kallon irin shigar jikinta,duk wanda ya kalleta lokacin kai tsaye da Villager girl zai kirata.
Dije tayi murmushi dan kuwa da gangar tayi turanci dan ta kankarowa kanta daraja, a zuciyarta ta ce jisu sun ɗauka kowama dusa ne taja qwafa🤓.

Afeefah ta ce "wow you are so cute and adorable."

Nanfa ɗaya Dije ta fara zarar ido tana rabawa dan bataji abinda Afeefah ta faɗa a ƙarshen maganar ta ba, turancin ma da tayi yanzu da yaya ta haɗasu, da kyar ta iya cewa "na gode," amma a ranta ta riƙe kalmar "adorable" ƙam saita bari daga ita sai Afeefah ɗin, zata tambaye ta fasarar kalmar.

Afeefah ce tayi magana, Dare fah nayi ta kallesu ta ce "Aunty bari da safe ma ƙarisa maganar yanzu kije ki kwanta kawai," sannan ta kalla Dije ta ce "follow me na rakaki ɗakin da zaki zauna," tashi sukayi dukansu Auntie sa'adah ta wuce ɓangaren su na ƴan aiki ita kuma Afeefah ta nuna ma Dije wani bedroom dake kusada kitchen, tana murmushi ta ce "bedroom ɗinkine shigo nanuna miki ciki," binta ciki Dije tayi hannun ta riƙe da jakar kayan ta, ɗakin yanada girma sosai ba lefi komai na ɗakin milk and Brown color ne.
Yanayin komai na ɗakin yayima Dije kyau sai faman washe baki takeyi ɗakin tsaf da alama kullum ana gyarashi bathroom suka shiga Afeefah ta nuna mata yadda ake amfani da wasu abubuwan dake ciki wasu kuma ta ce sai gobe, sai da Afeefah ta tabbatar da ta nuna ma Dije yadda ake amfani da komai sannan ta fita ta rufo mata ƙofar.

Afeefah na fita Dije ta daka tsalle ta haye saman gado a fili ta ce "huh saini Dije ta ƙauye a birni kuwa deejarh nake Yasin.
Tashi tayi tana kuma ƙara bin ɗakin da kallo iya yinta saida tayi iyayinta sannan ta cire yamu shashshe hijjab ɗin jikinta wanda yaga jiya yaga yau.

Toilet ta shiga jin ana kiran sallan isha'i alwala ta ɗauro as a muslim girl, bata tsaya ƙarewa toilet ɗin kallo ba ta fito, jakar kayanta ta buɗe ta ciro sallaya da hijjab sabo.
Gurin da taga an tanadar domin sallah taje tayi, bayan ta idar da sallan ta cire hijjab ɗin, jakar kayanta ta ɗauka ta fito da kayan ciki duka waje tayo dasu, saboda tsaban iyayi irinna Dije a wardrobe ta jeresu tas bayan tayi musu ninki irinna guga.
Sannan ta tashi toilet ta koma tana kuma bin ko'ina da kallo yayi kyau sosai gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta saman mirror ta kalla taga abubuwan wanke kala kala sai wanda mutum ya zaɓa.
Ae ba shiri Dije ta zaro ido ganin abubuwa na ƴan gayu iri iri ba'a magana, kayanta ta cire, ta ɗaura towel ɗin da taga anyi hanging ɗinshi in toilet wall.
Ɗaya daga cikin abin wanke kai ta ɗauka taga an rubuta "shampoo" buɗewa tayi tatso a saman hannunta sannan ta murza zuba saman gashin kanta saida ta gama sawa Sannan ta kunna famfo tasa ruwa ta wanke tas, wani ta kuma ɗauka taga an rubuta "All hair conditioner" ba tunanin komai shima ta wanke kanta dashi bayanta gama wanke sumar kanta da shampoo's ɗinne, tayi wanka ta fito ɗaure da towel fari ga wani a hannunta tana tsane sumar kanta dashi hand Drier ta gani da sauri ta jona a charge sannan ta fara bushar da gashinnata bayan ta kammala ko shafa lotion batayi ba ta je wardrobe ɗin data jere kayanta riga doguwa na material ta ɗauka duk taji duniya ta saka bayan ta gama komai ta haye saman bed sai bacci. {Dije anya kuwa wannan daga ƙauye take?, E mana gani nayi ae ta iya komai daya danganci bathroom sai kace wacca dama can ta saba shiga🤔}.




NKD ✍️ ✊

Khadeejarth Nainarh Kd.




𝐴𝑓𝑒𝑒𝑓𝑎ℎ 𝑚𝑎𝑖𝑘𝑦𝑎𝑢

Ɓangaren Afeefah kuwa tana fita daga ɗakin da ta sauke Dije kai tsaye bedroom ɗinta ta koma, system ɗinta ta ɗauka tana karatun exam dayake sun fara ne.
Tana zaune saiga Lailah ta shigo ita ma hannunta riƙe da littafai irinna su na likitoci, zama tayi tana faɗin "a gaskiya na gaji wannan karatun, wallahi karatun likita ba sauƙi saina Allah....kai ina, ni da ma a soke karatu kwata kwata adena a duniya."
kallon Afeefah tayi dake faman aiki da system da alama ma batasan ta shigo ɗakin ba. "Hey miss feefah, duk karatun ne haka ba'asan ma lokacin da na shigo ba." Lailah tayi maganar tana tafa hannunta a fuskar Afeefah ɗin, ɗagowa Afeefah tayi tana kallon Lailah fuskar ta ɗauke da murmushi ta ce "yane likita karatun exam ɗinne, yayi zafi ko?," Aiyar zuciya Lailah ta sauke ta ce "ana fama wallahi, ni fa ko, wani lokacin sai naji kamar nabar wannan karatun likatancin fah." Waro ido waje Afeefah tayi tana ɗan murmushi ta ce "lah lah Lailah aikuwa wannan maganar sai a kunnen daddy, ko dai duk karatun exam ɗinne ya kawo hakan kike saɓa lamba haka."
"Hummm kedai ba zaki gane bane kawai Miss feefah sai dai kawai abar zancen anan," cewar Lailah, "haba zan gane mana idan kika ganar dani Afeefah ita ma ta bawa Lailah amsa tana dariya.ɗaukar littafin karatunta Lailah tayi ba tare da ta ce ma Afeefah ɗin ci kanki ba😂.

**

Sai wajen sha ɗaya na dare, sannan suka kammala karatun nasu wai nanma Lailah ce ta dage bacci takeji shiyasa suka haƙura.

**
Kiran sallah ne da sanyin asuba dake kaɗo curtains ɗin ɗakinne ya tashi Dije daga bacci tashi tayi tana miƙa alamar dai baccin bai isheta ba. Kai tsaye bathroom ta shiga ta ɗauro alwala ta fito ta tada kabbarar sallar asuba bayan ta shimfiɗa sallayar ta da ta zo dashi daga ƙauye.
Tana cikin raka'ar ƙarshe ne aka turo ƙofar ɗakin aka shigo Afeefah ne jikin ta sanye da hijjab fari tas har ƙasa na sallah zama tayi saman bed tana jiran Dije ta idar da sallah.

Juyowa Dije tayi bayan ta idar tana kallon Afeefah ta ce "lah Balarabiyar india kece ashe ina kwana," murmushi Afeefah tayi ta ce "lafiya ƙlau Deejarh ya kike ya baƙunta kuma fatan kina cikin ƙoshin lafiya.
Washe baki Dije tayi ta ce "ae Balarabiyar india ina faɗamiki babu baƙunta don tuni yabi gado, amma wai Balarabiyar india na tambaye ki mana idan babu damuwa?," cewar Dije.
Afeefah ta ce "ina jinki Allah yasa na sani," washe baki Dije ta kuma yi cike da farin ciki wannan kyakyawar Balarabiyar india tana mata magana ta ce, " ah dama Balarabiyar india wannan ɗakin hala na ƙanwar kice?." Dariya Afeefah tayi ta ce "a'a ko ɗaya bana ƙanwa ta bane, amma me kika gani ne?," Dije ta ce "ae naga akwai komai da komai ne, a ciki hadda man wanke gashi fah na gani kala kala a can wajen ta nuna bathroom.
"Okay ae ɗakin baƙi ne idan suka zo sai suke zama anan, kamar dai ace ƴan mata kamar ki, aikin ga ɗakin irinna ƴan mata ne waɗanda basu wuce 15years ba ko," Dije ta ce "E, mana gashi ɗakin mai kyau kuwa, Balarabiyar india wai Menene ma sunan ki na gaskiya sunan akwai daɗi amma kuma sai wahalar faɗa ko miye ma "AFEEF" ne ko "AFFAF" ta tambaya tana kallon Afeefah ɗin.

Yauwa na tuna Afeefah hakane ko?," 'E,' Afeefah ta bata amsa sannan ta ce "follow me muje kitchen Auntie sa'adah na kiran ki zamu haɗa breakfast okay," tashi Dije tayi tabi bayan Afeefah bayan ta cire hijjab ɗin jikinta ta ɗaura ɗan kwalin rigar dake a jikinta.

Dije sai faman kallon kitchen ɗin takeyi tana kallon kyau da tsaruwa, muryar gwaggon ta taji suna gaisawa da Afeefah da sauri ta kalla gurin da gwaggon nata take ta ce "lah gwaggona kece wai, to ina kwana ni yasin na manta dake mah," gwaggo ta ce "toh dama tayaya zaki tuna dani kina can kin sama a.c kina kwasar bacci harda minshari.......washe baki Dije tayi tun kafin gwaggonnta ta ƙarisa maganar da takeyi Dijen ta rigata da faɗin, "Yasin kuwa gwaggo bakiji ba kamar karna fito daga ɗakin domin wani irin madarar daɗin bacci ɗakin yake dashi.
Dariya Afeefah tayi ta ce "to malama deejarh mai ɗaki, ga wannan juyo in ɗaura miki, kallon abinda Afeefah take miƙo mata Dije tayi ta ce "laha'ila wannan kuma Menene wai ku nan birni idan za'ayi girki sai an saga wannan abunne?."
Afeefah ta ce "E, mana ta yadda bazai ɓata kayan ki ba" Dije ta kuma washe baki ta ce "to Balarabiyar india! au Adda Afeefah miye sunan wannan ɗin shi kuma muji idan akwai daɗi.
Saida Afeefah ta gama ɗaura mata sannan ta ce "cikin murmushi sunan shi apron.

Dije ta ce "aikuwa daga yau na riƙe sunan shi don fita kunya, apron ko kika ce ae,"
Gyaɗa mata kai Afeefah tayi Sannan ta bata kayan vegetables ta ce "ina fatan dai kin iya yankawa ƙanana ƙanwata?," Dije ta ce "E, mana Balarabiyar india sosai ma, na iya a ƙauye.
"Okay to yanka mu gani tunda kince kin iya," ɗauka Dije Tayi ta fara yankawa iya qwarewarta, Afeefah tana lura da'ita tana mamakin yadda yarinyar ta iya aikin highly, don ita da farko ma tayi tunanin yarinyar ba za ta iya aikin komai ba, sai kuma gashi yanzu yarinyar ta bata mamaki.
Kallon Auntie sa'adah Afeefah tayi Sannan ta ce "Auntie jiya naji kamar kince zaki faɗamin wani abu koh, ɗan juyowa Auntie sa'adah tayi tana kallon Dije sannan ta nuna ma Afeefah, Dije ɗin ta ce.
"Ita wannan sunan ta khadijatu kuma ɗiyar YaYa na da muke uwa ɗaya uba ɗaya dashi ne, mahaifiyarta ta rasu tun tana da shekaru biyu a Duniya, a lokacin naso YaYa na wato mahaifin ta ya bani ita na ci gaba da rainonta tunda kamar yadda aka sani ne ban taɓa haihuwa ba amma Allah bai nufa ba.

A hannun kishiyar uwanta ta taso, matar ba ƙaramin wahalar da'ita tayi ba, don da kyarma aka samu ta bari aka sakata makaranta na arabic da na boko, to haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Dije tana hannun kishiyar mahaifiyarta har ta kawo wannan lokacin sati ɗaya baya, daya wuce ne wai su isu isu ƴan matan ƙauyen wai suka haɗa gasa wai suna gasar SARAUNIYAR KYAU ? sannan tsarin gasar shine, duk wacca tafi kyau to zasu haɗa kuɗin da ƴan kallon gasar suka haɗa, su ba wacca tayi nasara, to ana haka shine fah, ita ma Dijen ƴar ƙaniya da ita, ta shiga kuma taci shine da aka bata kuɗinta a matsayin wacca taci nasarar, ita kuma ba ta ba Ladidi ba, ta yi harkar gabanta dasu, Ladidi wato matar babanta da take riƙonta, shine ita kuma Ladidi taji haushin hakan wanda dalilin kenan da yasa ta kamata ta ɗaure a ɗaki ta mata dukan mutuwa kuma taƙi ta kwanceta abinci ma taƙi bata saida YaYa na wato mahaifinta ya dawo gidan yaga halin da take ciki, a lokacin ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba, nan dai ya kwanceta ya kawota gurina shine ni kuma na yanke shawarar na kawota nan aikatau saboda na kusa Aure nanda sati ɗaya ne InshaAllah shiyasa jiya kika ganmu da dare, Auntie sa'adah ta ƙarishe maganar tana sauke ajiyar zuciya, duk da cewa yankan kaɗan daga cikin tarihin rayuwar Dije tayi ta ba Afeefah a taƙaice kuma a gajarce don ba duka bane, hasali ma iya labarin da ta ba Afeefah kaɗanne ko na ce kamar talla ne daga cikin labarin rayuwar Dije.

Ita ma Afeefah ajiyar zuciyar ta sauke tana bin Dije da kallon tausayi sannan ta mayar hankalinta kan Auntie sa'adah ta ce "to amma dai hukuma ta hukunta matar ko, dubi yadda duk jikin ta yake a farfashe fa. Tayi maganar tana kuma kallon yadda wasu gurare ajikin Dije suke duk wounds ne.
Hucin takaici Auntie sa'adah ta sauke tana faɗin, "wani hukunci ae ba abinda aka mata hasali ma, shi YaYan nawa da kanshi, ya kasa ko mata kallon banza balle azo maganar hukunci.
Da tsananin mamaki a wannan taƙin Afeefah take kallon Auntie sa'adah ta ce "kamar yaya bayyi mata komai ba kenan kinaso kice min babu abinda aka mata, aka barta ta ci gaba da rayuwa a haka. "E' haka nake nufi" cewar Auntie sa'adah.

A fili Afeefah ta ce "amma wallahi mutumin ƙauye bayyi ba wani lokacin haba dan Allah," Auntie sa'adah tayi murmushi ta ce "gwara dai da kika ce wani lokacin", "sorry for say so, kawai dai abin ne ya bani takaici, Afeefarh ta faɗi hakan ganin yadda yanayin fuskar Auntie sa'adah ɗin ya sauya. Sannan ta ci gaba da cewa.
"Auntie sa'adah amma wallahi, matar nan ta bani haushi sosai, duka duka ita Dijen ɗin nawa take da har zatayi mata abin da tayi," Auntie sa'adah ta ce "ba za ta wuce shekaru goma sha biyar ba, da haihuwarta a duniya," Afeefah taja qwafa tana faɗin, "dama da gani ba za ta haura hakan ba nasani. Oh naji ma kamar kince zakiyi Aure ko?, Yanzu shikenan zaki tafi ki barmu da kewarki?," tayi maganar cike da shagwaɓa da rashin jin daɗi, Auntie sa'adah tayi murmushi tana faɗin "to ba ga Dije ba, ae zata zauna mada dina."
Ita ma Afeefah murmushi tayi ta ce "ae munfi sonki akan ita Dijen ɗin cuz mun daɗe dake highly, don ina ganin kusan six years muke tare dake, ita kuwa kwata kwata jiya tazo, kuma muka fara ganinta.
Da sauri Dije dake yanka onion akan chopping board ta ce "au yanzu, Balarabiyar india kinfi son gwaggo na akaina kenan?," Afeefah ta ce "E, mana nafi sonta akanki sosai ma, kuma sannan sunan ta ba gwaggo bane, ki dinga kiranta da "Auntie sa'adah" daga yau," Dije ta ce "shikenan naji, kuma nima ta dena cemin Dije sunana Deejarh ko kuma ta ce Nanah, ko kuma dai suna mai daɗi, amma ba irinna ƙauye ba. Afeefah ta ce "Okay, to dai kinji Auntie sa'adah, Deejarh ta ce ki dena kiranta da Dije, sai dai kice Nanah ko Deejarh." Auntie sa'adah ta ce "to to shikenan na dena Dije na," Dije kamar zatayi kuka ta ce "kuma dai kin ƙara faɗar Dijen, Afeefah tana dariya ta ce "to ae ba tashi ɗaya bane zata iya dena faɗa, dole sai da kaɗan kaɗan sannan.
Dije ta ce au bari dai alƙalamina ✍ ya kiyayi rubuta wannan Dijen tunda bataso kar tayimin kuka 😢😂.

Deejarh ta kalla Afeefah ta ce "Balarabiyar india, amma dai zakije ƙauye bikin gwaggona Auntie sa'adah ɗinki ko?," Afeefah tayi murmushi tana faɗin, idan Allah ya nufa kafin lokacin mun kammala exam a school zani Insha Allah.
Tun kafin Deejarth ta ƙarayin wata maganar Auntie sa'adah ta rigata da faɗin "a'a, ae bama sai kinje ba abin da ba mutane za'a tara ba kawai ɗaurawa ne da tarewa, rana guda, Afeefah ta ce "Okay to Allah ya kaimu musha biki, kuma Allah ubangiji yasa gurin zama ne," Deejarh ta amsa Ameen Ameen Balarabiyar india ta kuma Allah yasa tana shiga wata tara kuma koma suna.
Dukan wasa Auntie sa'adah ɗin ta kaima Deejarh tana faɗin "na shiga tara na ni, Dije yanzu da tsufa na ne zanje ina wani haihuwa, ae haihuwa yanzu sai yara.
Dariya kawai Afeefah takeyi yayinda take kare Deejarh da ta ɓoya a bayan ta, bakinta bai mutu ba take cewa "ae Yasin gwaggona baki wuce haihuwa ba, kwata kwata shekarunki nawa ne, ae rannan ina jinki lokacin da kike faɗawa Dillaliyar da zaki saya kayan ɗaki gurinta, cewar shekarunki Talatin da tara da watanni ne baki ci ke Arba'in ba, kuma ae ance sai mace takai shekaru arba'in ne ko fiye da haka take dena haihuwa."

"Au

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads