Header Ads
Showing 15001 words to 18000 words out of 155363 words

Chapter 6 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt

Ads the beginning of article before Image

Nanah Kd   

14 Jun 2024

1010

Ads at the middle of Article

su kuma ko wanne halin sa ya banbanta, especially ma Lailah da halinta yafi banbanta dana sauran Yayyinta ana cewa halin Momy Rafi'at tayo a wasu lokutan.

Ganin kamar Afeefah ta shiga duniyar tunani ne yasa Lailah ɗan tafa hannu a fuskar Afeefah ɗin, "Hey my friend menene kina jina ma kuwa?," Lailah ta faɗa tana kallon yadda Afeefah ta zuba mata ido tana kallon ta.
Firgigit Afeefah ta dawo hayyacin ta daga duniyar tunanin da ta faɗa ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na biyu tana kallon Lailah sannan ta ce "indai akan wannan ne kika shiga damuwa ki kwantar da hankalin ki, Domin zanyi ma Daddy maganar da na tabbatar da zai fahimce ni akan su Aunty Nainarh harma da YaYa maleek ɗin insha Allah zai fahimta kuma zaisa a nemo YaYa maleek ɗin a duk inda ya shiga, Kinga saiki saki ranki ko saiki faɗamin damuwar naki na biyu muji ko zan iya yi miki solving ɗinta," Afeefah ta ƙarishe maganar tana murmushi.

Ita ma Lailah ɗan murmushin tayi tana kallon Afeefah ƙaunar ƴar uwan na ta na ƙara shiganta, "A'a shi wannan ba wani matsala bane sosai kawai dai Uncle Al'ameen ne ya takura min da maganar soyayya kuma ni kinsan tsarina ba soyayya a tafiya ta, Dariya Afeefah tayi "kina bani mamaki Lailah wani lokacin saiki ce wai ba soyayya a tsarin ki to haka zaki dogara ba aure ina tausayin ki duk ranar da soyayya ta shige ki ba zata miki shigan sauƙi ba Allah, Kuma da kike maganar Uncle Al'ameen ae naga ya daɗe yana ƙaunar ki kawai ki bada kai musha biki sister, Afeefah ta ƙarishe maganar tana dariyar shaqiyanci ganin yadda Lailah ta haɗe rai.

"Ke sis feefah bana son wulaƙanci fah, kisani ae idan ma maganar gaskiya za'a bi kece zaki fito da miji musha bikin tunda naga kullum sai an miki layi wajen zuwa fira," Tamke fuska Afeefah tayi ta ce "amma dai kinsan aure lokacin ne ko zan fito da miji soon amma sai buri na cika dan kuwa ae amfanin soyayya aure," Murmushi Lailah tayi dan kuwa tasan babban burin Afeefah shine zama SARAUNIYAR KYAU👰👸

"Sha re wannan topic ɗin kinji ga wani Special Dress fa na samo amma naga alamar nuna tsiraici zayyi yawa ciki amma duba ki gani", Afeefah ce mai maganar tana nunawa Lailah Dress ɗin da ta yi searching a wayarta, Karɓa Lailah tayi tana faɗin "Okay sis let me it, Sannan ma ana bedroom ɗin zan kwana".
Baki da damuwa madam Lailah Mai ƙyau, Cewar Afeefah cikin murmushi.
Murmushi Lailah tayi ita ma haka suka ci gaba da fira har can Afeefah ta ce bacci take ji sannan ta kwanta, Saida Afeefah ta ɗan daɗe da kwanciya da alama ma bacci yayi gaba da ita, sannan ita ma Lailah ta kwanta tana ɗan murmushi a zuciyar ta furta ina ƙaunarki ƴar uwata duk da cewa ba ciki ɗaya muka fito ba amma muɗin JINI ƊAYA NE tunda dai mahaifin mu ɗaya, addu'a tayi ta shafe jikinta sannan ita ma sarkin ɓarayi yayi gaba da ita

🅷🅰🅻🅴🅴🆂🅰🆃♥︎🅼🅰🅸♥︎🅺🆈🅰🆄

Misalin ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare ta shirya tsaf cikin wasu ƴan iskan kaya doguwar riga maroon color mai hannu ɗaya anyima rigar tsagu tun daga cinya zuwa ƙasa, sannan ta ɗauki takalmi heel mai tsini shima maroon color tasa ta ɗaure igiyoyin jiki, Ga gashin kannan nata ya sha gyara in Braid style, Ɗaukar dogon hijab har ƙasa fari tayi tasa da niƙab sannan ta ɗauki jakarta ta fito, A hankali take sanɗa saɗab saɗab saida ta tabbatar da ba kowa a palon sannan cikin sauri ta nufi kitchen ta buɗe ta ƙofar kitchen ta fita sannan tabi ta garden ko tsoron dare bata yi tabi ta ƙofar dake garden ɗin wacca aka mata ado da wasu flowers masu shaining a qawace ta fita.

A hankali Momy Rafi'at wacca akan idanunta Haleesat tayi duka abinda tayi tun daga kan fitowarta daga bedroom ɗinta bin da tayi ta ƙofar kitchen fitarta ta garden, duka abinda ya faru ta gani daga tsayen da take, Zuge curtain ɗin window ɗin tayi sannan ta koma ta zauna a saman Royal bed ɗinta na alfarma, Wayarta ta ɗauko ta kira lambar Haleesat amma a kashe, Murmushi tayi tana gyara zaman ta saman Royal bed ɗin, Still tana kuma sakin murmushi mai ɗauke da ma'anoni kala kala.
Kwanciya tayi abinta kamar ba uwan da taga ɗiyarta ta fita ba cikin dare baccinta tayi hankalinta kwance..............{ Ikon Allah sai kallo 🏃🏃}

🆉🅰🆈🅽🅴🆁🅱♥︎🅼🅰🅸♥︎🅺🆈🅰🆄

Tana so tasha whiskey ko kwalba ɗaya ne amma kuma tana tuna alƙawarin da tayi ma Afeefah na bazata ƙara shan wani abu daya danganci maye ba, Wanda wannan dalilin ne yasa ta tashi ta ɗauro alwala a Bathroom, nafila tayi raka'a huɗu sannan tayi sallama Al qur'ani mai girma ta ɗauko tayi tilawa sannan Batareda ta cire hijjab ɗin dake jikin ta ba.
Ta tsaya gaban window tana shaƙar fresh air, Kamar da wasa ta hango mutum yana sanɗa ya nufi hanyar garden.
Tuni ta fahimci ko wacece Haleesat ce domin kuwa two months da suka gabata ta fahimci Haleesat tana satar hanya tana fita da dare, Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna saman bed tana mai yima Haleesat addu'ar shiryuwa a ƙasan ranta don banda wannan ba abinda zata iya mata.

Ita kuwa Haleesat tana fita ta nufi wata Jar mota ƙirar BMW dake a pake acan gefe, shiga tayi cikin motar ƴan mata ne aciki su uku biyu a gaban mota, Ɗaya a baya duk da Haleesat suka zama su huɗu.

Cire dogon hijab ɗin dake jikin ta tayi tare da Niƙab ɗin tana faɗin, "Oh God zufa huh", Budurwar dake kusa da ita tayi dariya tana faɗin "Baby leesat yau fa kin ɓata mana lokaci wannan tsayawa ɓadda kaman da kikayi".
"Ke dai rabu dani kawai, Kinji ki Zuree babe yanzu ma da ƙyar na fito, Samu nayi ba kowa a palo ma shiyasa kuka ganni, Cewar Haleesat lokacin aka tayar da motar suka bar gurin suna taɓa fira da budurwar da ta kira da Zuree babe da kuma sauran ƴan matan biyu dake gaban motar Feenah da kuma ɗayar budurwar Jenny.

𝔻𝔸𝔾𝔸 𝔸𝕃Ƙ𝕃𝔸𝕄𝕀ℕ✍️ 𝕋ℍ𝔼♥︎ℕ𝔸𝕀ℕ𝔸ℝℍ♥︎𝕂𝔻📲

Isarsu Night club ɗin suka fito a tare, Haleesat ce a tsakiya hannunta riƙe da hannun Zuree sai kuma Feenah ita ma hannunta riƙe da hannun Jenny shiga ciki sukayi, wa'iya zubilla ƴan mata ne kawai ciki kamar yaran arna ba wata suturar kirki bane a jikin su, abin dai ba ƙyan gani ga samari nan iri iri kuma abin da zai kuma ba mutum ta kaishi da mamaki shine zallah gurin Yaran Hausawa ne birjiq😭

Shigarsu wajen keda wuya, nanfa kiɗa ya canza manyan Yaran sun iso nan wajen ya ɗauki sowa da tafi faɗi, Suke ga manyan Yaran masu ji da lokaci sun iso ae dole a basu guri, don masu guri sun ƙariso, haka suke ta faɗi Cikin Yanayi irinna su.

Kujeru masu arnen kyau suka zauna akai Haleesat tare Zuree a kujera mai mazaunin mutum biyu sai Feenah tare da Jenny a ɗayar kujerar ita ma mai mazaunin mutum biyu sai fasa musu kai ake da yabo su kuma suna ƙarajin ba kamar ya su lokacin sune bawai bane😎

Wani ƙayatacen Tray na glass mai ɗauke da whiskey kala kala ma'aikacin gurin ya kawo ya aje saman glass table ɗin dake a gaban su sannan ya koma ya kawo wani tray ɗin kuma daban mai ɗauke da glass cups na zinare ya aje, Sannan cikin nutsuwa yake zuba musu whiskey ɗin acikin cups ɗin Haleesat ya fara miƙa ma dan kuwa ita ce jigon abun mahaifin ta yafi mahaifin su Zuree kuɗi nesa ba kusa ba shiyasa suke girmama ta ba kaɗan kaɗan ba shiyasa ta zama kamar ita ce shugaban su sai abin da ta faɗa ake bi.

Wani irin tsawa Haleesat ta bugawa ma'aikacin wanda yasa saida ya kusa zubar da whiskey ɗin dake hannun shi tsaban firgita da tsoro.
"Bala'i amma Kai wani kalan bagi dajen mutum ne ka taɓa ganin nasha whiskey a gurin nan, Ko shashancine da rashin kulawa yasa zaka bani whiskey saboda ka mayar dani nonsense wacca batasan abinda take yi ba.
Cike da masifa da kuma gadara Haleesat take maganar tana girgiza ƙafa, Game da sakin huci dan ƙiris ya rage ta kai mishi mari...
Gabaɗaya hankulan wasu daga cikin maza da mata na gurinne ya dawo kansu domin ganin abinda ke faruwa.

Shi ko ma'aikacin mai suna Vinood sai faman bata hakuri yakeyi duk yabi ya haɗa uban zufa jikin shi sai faman rawa yakeyi tsoron shi ɗaya shine karya ya rasa aikin shi a gurin.

Ganin Haka yasa Feenah wacca duk cikin su tafisu sanyin hali kuma bata cika san hayaniya ba, Alama tayiwa ma'aikacin daya tafi ya bar gurin, da sauri kuwa ya bar gurin har yana tuntuɓe.

Kamo hannun Haleesat Feenah tayi tana faɗin "please baby leesat ki kwantar da hankalin ki yanzu zai kawo miki abin da kike buƙata kinji?", Feenah ta faɗa hakan ne saboda tasan Haleesat bata shan whiskey ko kuma Wani Abu daya danganci kayan maye...Tafi ganewa ta busha shisha ko wani abun, Amma bata shan kayan ruwa ma'ana abin da ya danganci maye.
Ajiyar heart Haleesat ta sauke sannan ta ce "ba damuwa kawai dai ya ɓata min raine amma ba komai "forget about the pass".
Murmushi Feenah tayi "shiyasa nake son ki ta waje na akwai ki sauƙin hali", Feenah ta faɗa tana komawa ta zauna.
Feenah ƴace ga Alhaji Sulemanu canji, shahararren ɗan canji ne a garin Abuja da kewaye, Yana da kuɗi obaa highly dan kuwa bayan harkar canji da yakeyi ɗan kasuwa ne shi na bugawa a jarida, Feenah itace ƴar shi ta biyar mahaifiyar ta ta rasu tun tana da shekaru sha biyu a duniya a gurin kishiyar uwanta take.

Yayinda Zuree take ƴa ga malam Adamu jama'are mahaifin ta shahararren malami ne a garin Abuja asalin shi ɗan garin jama'a re ne na jahar Bauchi, Kasuwanci ne da kuma malimta ya dawo dashi garin abuja har ya gina family ɗinshi anan yaran shi tara, Zuwairiya wato Zuree ita ce ta fita zakka a yaran malam Adamu dan kuwa ƴar malam ce wacca taƙi halin malam.

Sai kuma Jennifer lopez, wato Jenny mahaifin ta cikake kuma shahararren mai dukiya ne a garin Abuja sannan kuma pastor ne wanda akeji dashi Jenny ta kasance, Ƴar shi ɗaya tilo tsoka ɗaya a miya shiyasa take abin da taga dama saboda a sangar ce iyayen ta suka raine ta bata san wani abu waishi wahala ba a rayuwa dukansu ajin su ɗaya a University sannan kuma course ɗaya suke karanta wato Microbiology.

Dogon tsaki Zuree taja tana faɗin, "Wallahi Baby Leesat kina Bani mamaki da takaici bansan ranar da zaki waye ba wallahi ke ba shan wannan kayan ruwa ba, Bakya taɓa harkar nan ke gabaɗayanki sai aslow wallahi", Tayi maganar cike da takaici.

Haleesat bata kulata ba da dan kuwa idan da sabo yaci ace ta saba da wannan tsoki burushun na Zuree.
Saima cewa da tayi, "Okay guys kuzo mu motsa Jiki mana,"
Gabaɗaya su ukun tashi sukayi gabaɗayan su suka hau kan dandamali nanfa akayi changing ɗin wakar speakers ɗin CLUB ɗin zuwa wani korean song na zamani, habba nanfa suka fara dancing kamar ba gobe cike da kwarewa suke rawan su abinsu ba ruwansu.

Tsaye take can ɗaga wani ɗan korido na club ɗin, Yayinda take ƙarewa club ɗin kallo dama society ɗin dake ciki.

Pin-up dress ne a jikin ta, Riga black color sai belt golden color da ta kama ƙugunta ta ɗaureshi, Rigar iya gwiwar ta tsaya sannan kuma ta kama ta ɗam, ga wani tsinannen takalmi hill a ƙafafunta kanta kuwa yasha kitson attach mai masifar tsada, Hannunta na hagu kuwa zanen tattoo ne brown color.
Doguwa ce sosai dan kuwa a shekaru ba za ta haura ashirin da uku zuwa da huɗu ba, Idonta yana sanye cikin wani arnen glass no respect launin eye balls ɗinta kuwa abin burgewa ne ga mai kallon tsakiyarsu launin Blue color suke.

Hannyenta rings na diamond masu masifar kyau da tsada ne, Ga wata arniyar chain na diamond a neck ɗinta siririya mai kyau da kuma tsada, Ear ɗinta kuwa ba`a magana wasu kalan earings ne a kunnenta na diamond amma kuma Yanayin shape ɗinsu cross ne, Fuskar ta kuwa tasha light make-up launin hair ɗin ta kuwa brown color ne dogo, ta fito sak Like a indian actress RAKUL PREET SINGH fara ce tas fatar ta har wani shaining takeyi saboda haske gashi kuma ya haɗe da jindaɗi Yanayinta tafi kala da mara sa son Hayaniya obaa highly.

Hannu tasa a pocket ɗin rigarta ta ciro wayar ta ƙirar iPhone 14promax daga inda take a tsaye take ɗaukar Haleesat a hoto, Tayi sunkai kala biyar sannan ta turawa wata number wanda akayi saving da MR. AMIGO sannan ta kira lambar cikin sa'a kuwa ringing ɗaya aka ɗauka magana ta fara cikin Harshen
farasanci, "Hello Mr. Amigo ga wasu pics nan na turo maka nan da gobe nakeso a samomin taƙaitaccen tarihin Yarinyar cikin pics ɗin in Tomorrow please."
On the other hand mutumin shima cikin Harshen farasanci ya ce "shikenan madam amma nace!,"
Bata tsaya jin abinda zai kuma cewa ba ta katse wayar ta mayar cikin gown pocket ɗin ta sannan ta fito daga cikin club ɗin gabaɗaya motar ta ƙirar bugatti ta shiga taja motar da gudu ta bar gurin.

A takaice dai su Haleesat basu suka bar club ɗinnan ba sai wuraren ƙarfe biyu da rabi na dare kamar yadda suka saba sauke ta sukayi a gurin da suka ɗauke ta ɗazu har zata fita a motar ta tsaya jin abinda Jenny take faɗa.
"Wai guys baku kula da wata red ɗin mota da take binmu ba tun ɗazu na lura da'ita fah, Tunda muka fito daga club Take binmu."

Ɗan juyawa sukayi a tare suna kallon inda Jenny ke nuna musu motar a daidai lokacin kuma motar dake binsu ƙirar Benz tayi ribas tabar gurin da speed, Tsaki Haleesat taja irin she don't care ɗinan "koma waye ne matsalar shine fa ba wai namu ba" Ta faɗa hakan yayin da take barin gurin bata tsaya jin abunda suke faɗa ba da sauri ta buɗe ƴar ƙaramar ƙofar da take bi ta gurin ta wuce.
Kai idan baka lura ba bama zakace da hanya a gurin ba balle har a sama ƙofar wucewa saboda gurin akwai wasu flowers da suka rufe ƙofar sai suka zama kamar kwalliya.

Cikin sanɗa take taku harta shigo palon gidan sannan in rushing ta wuce bedroom ɗinta.
Zaynerb da har gyangyaɗi ya fara ɗaukar ta, Baiwar Allah ajiyar zuciya ta sauke ganin Haleesat ta dawo cikin ƙoshin lafiya, Miƙewa tayi ta shige bathroom tanajin zuciyar ta ba daɗi, It's Necessary gareta ta sama Haleesat akan wannan satar hanyar da take tana zuwa Night Club, Ba tare da sanin ƴan gida ba.
Bayan wasu mintuna ta fito ɗaure da brown towel a chest ɗinta ko lotion bata tsaya shafawa ba cikin sauri sauri ta shiga cloth set ta shirya cikin sleeping dress riga na saka maroon color doguwa, Saman bed ta hau tayi addu'ar bacci sannan ta lumshe kyawawan idanun ta bayan wani lokaci bacci yayi awon gaba da ita.

Haleesat kuwa tana shiga bedroom ɗinta kai tsaye bathroom ta shige bayan ta cire dogon hijab ɗin dake jikin ta da niƙab da ta qwaqwama.
After some minutes ta fito jikinta sanye cikin bathrobe gaban dress mirror ta tsaya tana ƙara goge sumarta, da ɗan ƙaramin towel ɗin dake hannunta zama tayi akan stool na madubi tana shafa lotion Bayan ta gama busar da gashin kannata saida ta kammala shafa lotion ɗin, Sannan ta miƙe ta shiga cloth set ta shirya cikin pyjamas mai taushi milk color, System ɗinta ta ɗauka ta koma saman mattress ta zauna tana sarrafa system ɗin ta ɗauki lokaci tana amfani da system ɗin sannan ta mayar da system ɗin ma'ajiyar ta, Kana ta koma saman bed ɗin ta kwanta, Pillows ta rungumo a chest ɗinta tana sauke ajiyar zuciya ba batun addu'ar bacci a haka har sarkin masu iya sata yayi gaba da ita.

Can cikin baccinta mai daɗi taji ana tashin ta ana jijjigata ana kiran sunanta.
A hankali take buɗe lumtsatstsun idonta mai cike da bacci, Biji biji ta fara ganin mutum a gabanta kafin idanun ta suka buɗe duka.
Afeefah ce tsaye a gabanta tana sakin murmushi, riga ce short a jikin ta iya ka gwiwar ta sai dogon wando ga apron blue color da ta ɗaura a saman rigar jikinta, Kanta kuwa hular apron ɗinne shima blue color da alama kitchen zata shiga.

"Aunty Zaynerb" "Aunty Zaynerb!! ki tashi mana tun ɗazu naketa faman tashin ki, kitchen zamu shiga kinsan yaufa Aunty sa'adah bata ta tafi garinsu," Afeefah ce ke maganar tana tashin Zaynerb.

A Hankali ta sauko daga saman mattress ɗin miƙa tayi tana karanto addu'ar tashi daga bacci clock ɗin dake manne a wall na ɗakin takalla ƙarfe bakwai na safe da sauri ta diro daga saman gadon tana faɗin "Yah Allah yaushe lokaci ya tafi haka ban tashi nayi sallah ba," Bathroom ta shiga da sauri bayan wani lokaci ta fito ɗaure da towel fari a ƙirjinta dubawa inda tabar Afeefah tayi, Bata da alama ta fita ne, Cikin sauri ta zura doguwar riga, A jikin ta sannan ta saka hijab ta tayar da sallan asuba bayan ta iddar cire hijjab ɗin tayi sannan ta fito kitchen ta Shiga.

A can ta samesu da Lailah suna kici kicin haɗa breakfast.
"Yauwa Aunty Zaynerb please ɗan kira Haleesat tazo muyi mu kammala haɗa breakfast ɗinnan tare", Cewar Afeefah ba tare da kalla Zaynerb ɗin ba.

Fita Zaynerb ɗin tayi ɗakin Haleesat ta shiga bata ciki dubawa bathroom tayi nanma bata, Fitowa tayi zata koma kitchen ɗin a palo sukayi karo da Haleesat Jogging suit ne a jikin ta da alama daga morning Exercise take.
"Good Haleesat ki shirya Yau dai kitchen za'a shiga dan haka ki shiga ki shirya muna kitchen muna Jiranki, Kinsan dai Yau Aunty sa'adah bata nan kuma su Ummi da Elina Basunan".
Zaynerb ta ƙarishe maganar tana bin ta gefan Haleesat zata wuce, Da sauri Haleesat ta sha gabanta a

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads