Showing 45001 words to 48000 words out of 155363 words
Chapter 16 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
taimako, wani cizon da Zuree tayi ma ta a cinya ne yasa, ba shiri Haleesat ta saki ihun da yasa budurwar dake zaune gefe tana kallon komai rufe kunenta da duka hannun ta tana rumtse idanu.
Da ƙarfi ta faɗin "ku rabu da ita, I say Stop It Please,"
Amma ina kamar tanayi da dutse, buɗe murya tayi da wani tsawa take faɗin.
"ku rabu da ita nace," ku wasu kalan dabbobi ne wai, mace ƴar uwanku kuke ƙoƙarin yima fyaɗe, anya kuwa kuɗin mutane kuwa?,"
Da sauri Zuree dake wuya, ta juyo zata ma ta magana a zafafe, wannan juyawar da tayi, yaba Haleesat dama, aikuwa bata tsaya jiran komai ba, ta dage iya ƙarfin ta na bara dana bana ta haɗa ta gannawa Zuree cizo a damtsen hannu😂
ihun azaba Zuree ta saki tana rumtse ido, dan kuwa cizon ya shigeta yadda ya kamata, ko kafin Feenah tayi wani yunƙuri, Haleesat ita ma tayi kukan kura ta buga kan Feenah da headboard na gado da masifar ƙarfi ta ƙara bugawa saida tayi hakan fin sau huɗu, Wanda hakan yasa Feenah sakin ihun azaba nan take ta sume a gurin😅
Huci kurum haleesat take tana faɗin "Shegu ƴan iska kawai, maciya amana condemned kawai Allah yayi wadaran hallinku, ƴan kutmarrr 😳🏃
Gabadaya Haleesat bata cikin hayyacin ta, ga dogon gashin kanta ya rufe ma ta fuska.
Juyowa tayi kan budurwar dake gefe tana kallon ta babu alamar tsoro tare da ita.
A hankali ta sauko ƙasa ta zauna tayi tagumi hannu bibbiyu, tana kallon budurwar, a hankali budurwar ta takai hannu ta cire face mask ɗin dake rufe da fuskar ta.
Nan kyakyawar fuskarta ta bayyana, wanda sai da tasa Haleesat lumshe ido, duk da har yanzu bata gama dawowa hayyacinta ba, sannan ta buɗesu kar akan budurwar da bata taɓa ganin ta ba, ko haɗuwa da ita ba, tsawon rayuwarta sai yau kuma yanzu, a wannan taƙin da suke ciki.
"wato dai idan na fahimta, kece kika sakasu ko?," "to amma meyasa?,"
Haleesat ta jerowa budurwar waɗannan tambayoyin, shiru ta ma ta, kamar ba zata bata amsa ba, sai kuma can ta nisa sannan.
Buɗar bakinta sai cewa tayi, "haka kawai, na sakasu,"
Da mamaki Haleesat take kallonta, sai kuma tayi murmushi ta ce "badai haka kawai ba akwai dai dalili, kuma wannan dalilin nakeson sa ni."
Ɗan murmushi budurwar tayi sannan ta ce "ki yarda dani haka kawai, naji inaso nasan yadda akeyin abin, don naga Al'ummar yanzu ko nace matan yanzu sunfi raja'a akan yin hakan,"
"oh wato shine kuma, kikace bari ki gwada akaina ko?,"
Haleesat ta tambayeta cike da takaici, sannan ta ci gaba da cewa "amma sha re wannan, kinamun kama da wata, amma kuma na manta ko wacece, to komadai wacece matsalar ta, yanzu ki faɗamin, a inda kika taɓa ganina, da har kikaji sha'awar gwada hakan akaina,"
kai tsaye budurwar ta bata amsa da "a Club ne, wata ranar Sunday, idan bazaki manta ba, kinyi ma wani ma'aikacin Night club, ɗin faɗa akan ya kawo miki whiskey ko?,"
"oho kice anan kika ganni ko, yanzu na fara fahimta," cewar Haleesat.
Budurwar ta ci gaba da cewa, shine ni kuma tun daga ranar na saka miki ido, har taƙaitaccen tarihin ki na sa mo."
Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke, duk wannan maganar fa, da sukeyi cikin nutsuwa sukeyi kamar ƙawaye ko kuwa waɗanda suka san juna.
sannan ta ce "shin zan iya sannin sunan ki?,"
"𝖧𝖤𝖠𝖱𝖳 𝖢𝖧𝖤𝖭𝖦 𝖩𝖴𝖭𝖦" budurwar ta bata amsa, Nice name, Haleesat ta faɗa, ta kuma cewa zan iya tambayar ki wani abun kuma?,"
Jinjina mata kai Heart tayi alamar 'E', haleesat ta ce "kin taɓayin lesbian ne?,"
Da sauri Heart ta ce "a'a,"
Haleesat tayi nodding kai, ta kuma cewa "kin taɓayin zina?,"
Yanzu ma da sauri Heart ta girgiza ma ta kai alamar dai 'a'a' sannan ta fara magana.
"Ban taɓa aikata zina ba, ko lesbian, amma anso asakani a hanyar yi,"
"a'ina kuma suwa?,"
Haleesat ta jero mata tambayar, Heart ta ce "a school kuma ƙawayena," ta cigaba da cewa "baso ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba ƙawayena sunsha ɗaureni, suce sai sunyi raping ɗina amma basu taɓa samun dama akaina ba, abin har mamaki yake bani,"
"Saboda me" cewar Haleesat ido waje, Heart ta ce "nima dai bansani ba, amma dai wasu suna cewa saboda kyawuna ne, yayinda wasu suke faɗin saboda diri,"
Dariya Haleesat tayi ta ce "ai sun faɗa gaskiya, shiyasa akeso mace ta dinga suturta jikinta da hijjabi a koda yaushe."
"Menene kuma hijjabi?," Heart ta tambaya, ɗan murmushi Haleesat tayi tama, manta ko wacece a gabanta, ta ce.
"Sanya hijabi bin umarnin Allah ne da annabin sa, kariya ne daga fitina, alamace ta tsarkin zuciya, kyakkyawan ɗabi'a ce, garkuwa ne daga faɗawa halaka, sutura ce daga al'aura, kariya ne da ga mazaje marasa mutunci fasiƙai, kariya ne daga aljanu, kariya ne daga shiga cikin azabar Allah da fushinsa, bautar Allah ne sanya hijabi."
Ajiyar zuciya Heart ta sauke jin Haleesat takai aya, sannan ta ce "to zan iya saka hijjab ɗin?," murmushi Haleesat tayi ta ce "zaki iya mana."
Juyawa tayi tana kallon su Zuree da Feenah da sukayi tsuru tsuru dasu ta ce "me kuka yima Jenny?,"
Da sauri Zuree ta ce "Feenah ce ta saka mata qwayar bacci a lemu."
Girgiza kai Haleesat tayi sannan ta ce "kunyi ma kanku, kuma ban yafe ba, ta faɗa tana miƙewa saman bed ɗin, tahau ta ɗauko ribbon's ɗinta da hularta ta saka.
Kallon Heart tayi bayan ta dawo ta zauna a ƙasan ta ce, "sunana 'Haleesat Abubakar Mai Kyau', am very amazing to meet you," ta ɗanyi shiru sannan ta ci gaba da cewa.
"zamu iya ƙulla ƙawance dake?, tayi ma ta tambayar tana miƙa ma ta fresh hand ɗinta.
Hannun Haleesat kawai Heart take kalla sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"yanzu bakiji haushin abin da naso ayi miki ba?,"
Haleesat tayi dariya sannan ta ce "ko kaɗan banji haushi ba, saima darasin rayuwa dana koya, da ma can tun farko laifi nane da nake zuwa Night club, amma yanzu, na fahimci wani abu a rayuwa, wannan abun shi ne bada kowa ake yadda ba, a duniya, komai dangantakar ka da mutum kuwa."
Murmushi Heart tayi sannan ta miƙawa Haleesat hannunta tana faɗin "kamar yadda na faɗa miki a farko sunana HEART CHENG JUNG' Naji daɗin haɗuwata dake."
Murmushi ita ma Haleesat tayi sannan tasa hannunta cikin na HEART suka ƙulla ƙawance.
Clock ɗin dake manne a wall na ɗakin ta kalla lokaci yaja sosai ƙarfe huɗu na asuba saura.
Kallon su Feenah tayi ta galla musu harara kamar qwayar idonta zai fito, sannan ta kalla Heart ta ce inaga fa saidai mu kwana ana gidan, saboda lokaci yaja sosai,"
"Okay baki da damuwa Heart ta bata amsa, tana murmushi.
Tashi Haleesat tayi ta shiga toilet bata daɗeba ta fito, kan bed ta haye abinta kallon Heart ta kuma yi, tayi murmushi sannan ta ce "saida safe, sabuwar ƙawa,"
Heart da ɗan mamaki ta ce "bakyajin tsoron su kuma yunƙurin yi miki wani abun?," tayi ma ta tambayar iyakar gaskiyar ta, dariya Haleesat tayi ba shiri sannan ta ce.
"Idan na amince da mutum na gama nawa, saura ya rage nasa ya kyautatamin ko ya ha'inceni, Nikam banada matsala shida Allah."
Heart ta ce "kina burgeni sosai fa,"
Haleesat tayi dariya, "da gaske nake fa" cewar Heart, "ai na sa ni," Haleesat ta bata amsa.
Murmushi Heart tayi sannan ta kwanta a saman doguwar kujerar da take.
Lumshe ido Haleesat tayi tana tuno kyakyawan mutumin da ta haɗu dashi ɗazu da kyakyawar surarshi, mutumin da ko ainihin fuskarshi bata sa ni ba, balle kuma sunan shi.
*🩸ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ 🩸*
*☆ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ☆🤙*
Kiran sallah ne ya tasheta da ga baccin da ya fara ɗaukarta, a hankali ta buɗe kyawawan idanunta, bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci saukowa tayi daga kan bed ɗin toilet ta shiga ta ɗauro alwala, sannan ta fito, dagewa tayi iya ƙarfinta ta ɗakawa Zuree duka, a firgice kuma ta gigice ta tashi zaune tana zare ido.
"Bani key ɗin motar ki," Haleesat ta faɗa a dake kuma fuska a ɗaure, ba musu Zuree tasa hannu a trouser pocket ɗinta, ta ciro key ɗin sannan ta miƙa ma ta.
Karɓa Haleesat tayi sannan ta fita can parking lot motar Zuree ta buɗe ta ciro hijjabinta da kuma handbag ɗinta.
Cikin bedroom ɗin ta dawo bata ga Heart ba, da alama toilet ta shiga handbag ɗinta ta buɗe ta ciro wani madaidaicin scarf shimfiɗa shi tayi bayan saka hijjabinta ta tayar da sallah, tana idarwa bata tashi daga wajen ba saida tayi azkhar.
Wall Clock ta kalla ƙarfe bakwai da rabi na safe, kallonta ta mayar kan Heart da tun fitowar ta daga toilet taga tana sallah ta zuba ma ta ido ba ko gyaftawa.
Ɗan murmushi tayi sannan ta ce "barkanki dai madam yanzu zan iya tafiya gida?," murmushi Ita ma Heart tayi sannan ta amsa da "yauwa barka, zaki iya."
Tashi Haleesat tayi ta ɗauka handbag ɗinta, bayan ta saka scarf ɗin aciki.
Waje suka fito dukansu hadda su Feenah da Zuree waɗanda ko sallah ma saida rana ta fito gatsau sannan suka gudundura.
"Ko zan iya rage miki hanya" Heart ta tambaya tana kallon Haleesat ɗin.
Haleesat bata ce ma ta komai ba ta nufi motar Heart ɗin, har zata shiga kuma saita juyo, ta kalla su Feenah ta ce "daga yau nida ku anyi baram baram kar ɗayanku tayi gigin koda kirana a waya ne daga yau nida ku b.s.b.s.,"
Tana gama faɗin haka ta shige motar Heart taja suka bar gidan, ba wanda ya iya magana acikin har suka iso unguwan su Haleesat ɗin, sai kuma lokacinne Haleesat ta fara jin faɗuwar gaba daurewa kawai takeyi.
Guri Heart ta samu a gefen wata tree a unguwan tayi parking, fitowa Haleesat tayi ta zagaya ta ɓangaren da Heart take, ɗan kwankwasa glass ɗin window tayi.
Buɗewa Heart tayi tana kallon Haleesat ɗin, murmushi Haleesat tayi sannan ta ce "nagode fa, amma please karki ƙara tunanin sannin wannan abun,"
"saboda me?," Heart ta tambaya, "saboda babu kyau," Haleesat ta bata amsa ta cigaba da cewa "zan iya samun phone number ɗinki?,"
Heart ta ce "sosai ma, why not," wayarta ta ciro a cikin handbag ɗinta tana rubuta lambar wayar da Heart take karanto ma ta.
Ƙurawa wayar ido tayi bayan ta gama rubuta lambar da Heart ɗin ta karanto ma ta ganin lambar bana Nigeria bane yasa ta kalla Heart ta ce "wannan lambar fa?,"
"Number nane na ƙasata, Ƙasar France yau zan koma na gama abin da ya kawoni nan ƙasar,"
Heart ta bata amsa.
Qura ma ta ido Haleesat tayi ita sai yanzu ma take ƙarewa Heart ɗin kallo yadda ya kamata.
Kyakyawa ce sosai, don bata mayi kalar ƴan nigeria ba, da gani ma bata da wata alaqa da ƙasar, amma kuma meyasa taga kamar tana mata kama da wata?, amma kuma ta kasa tuna koda wa Heart ɗin take kama.
Sha re tunanin tayi, sannan ta kalla Heart ta ce "okay Allah ya tsare hanya, bari na shiga gida," ta faɗa bata jira amsar taba tabar gurin.
Ganin haka yasa ita ma Heart taja motar ta tabar haɗaɗɗiyar unguwan.
Kwankwasa ƙaramar ƙofar gate ɗin Haleesat ta farayi zuciyarta na harbawa jin ba'ada niyyar zuwa a buɗe ma ta ne, yasa ta ƙara ƙarfin bugun amma shiru, can taji alamar za'a buɗe, ɗan matsawa tayi gefe.
Isah ne ya buɗe gate ɗin yana faɗin "bama za'a bar mutum ya samu koda baccin sa fe yayi ba, anzo an takura da bugu nasan ma bazai wuce ƴan maula ba, to ai sai aja please a rungumi sorry domin Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo bayanan kuma ma.......
Sauran maganar da yayi niyyar gasa ma koma waye ne, ta maqale a bakin shi, sakamakon ganin wacca take tsaye a ƙofar, da sauri ya matsa gefe yana goge zufar da ta fara wanke mishi fuska, dan kuwa bai manta wahalar da ya sha ba a lokacin da yayi ma Lailah dariya ba, da tasa aka kusa korar shi daga aiki saida ƙyar ya samu Lailah ta haqura.
Haleesat ko kula sannu da zuwan da Isah yake ma ta batayi ba ta shige ciki gabanta na bugu da qarfin gaske.
Knocking ɗin ƙofar palon ta shiga yi baji ba gani, a zuciyarta kuwa tunanin yadda zazu kwashe da ƴan gidan take, dan ma sauƙinta ɗaya taji Isah na faɗin Daddynsu Mister Mai Kyau baya nan.
Jin an buɗe ƙofar ne, yasa ta ɗago daga tsugunawar da tayi, domin har wani ciwon mara takeji.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin ERINA ce mai gyara palo, hanya Erina ta bata ta wuce ciki, shiga palon tayi bakinta ɗauke da addu'o'i kala kala.
Bata ga kowa a palon ba, dan haka da saurinta ta nufi hanyar bedroom ɗinta, har ta saka ƙafa zata shiga ɗakinta taji muryar Auntie Nainarh tana kiran sunanta.
Rumshe idonta tayi da ƙarfin gaske sannan ta juyo dahm da dahm taji zuciyarta ta bada bugu saboda tsananin tsoro.
Duka Ƴan gidan ne zaune a dinning table hadda Momy da ta warke tsaf tana tafiya abinta.
A hankali ta fara taka ƙafafunta tana ƙarisawa dinning ɗin, yayinda gabaɗaya sassan jikinta babu inda baya rawa kamar mazari, cak taja tunga ta tsaya a tsakiyar palon taƙi gaba taƙi baya, kamar suna jira ta tsaya gabaɗayan su suka taso sukayo kanta da tambayoyi kowa da kalar tambayar da yake jefo ma ta.
Ganin haka yasa Momy Rafi'at ta daka musu tsawa cikin faɗa ta fara magana.
"wai ku wasu kalan mutane ne, a haka ne zata baku amsa koya da kalar tambayar da yake ma ta, taya zata iya baku amsa, ku sama guri ku zauna mana."
Umarnin ta suka bi gabaɗayan su suka zazzauna Nainarh, Nailah, da kuma Zaynerb a Three sieter, sai kuma Afeefah, Lailah a two sieter, sai Deejarh one sieter, sannan momyn ta kamo hannun Haleesat ta riƙe suka zauna a three sieter a tare da ya ke kujeru set biyu ne a palon.
*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*
*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*
*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*
*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*
{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}
💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙
<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>><><><><><><><
*Page 27&28*
Kallon Haleesat dake hawaye, Momy Rafi'at tayi, sannan murya ƙasa ƙasa ta fara ma ta magana, "Haleesat ina kika shiga ne?, yau ba'a ganki ba a gidannan ba, gabaɗaya lungu da saƙo na gidannan babu inda bamu duba ba, amma bamu ganki ba, faɗamin Menene ya faru dake kuma daga ina kike yanzu?, please tell me, everything my dear."
Duk a lokaci ɗaya Momy Rafi'at ta jerowa Haleesat waɗannan tambayoyin kuma ɗaya bayan ɗaya.
Shiru Haleesat tayi taƙi tayi magana sai faman matsar qwalla takeyi.
"wai nace bada ke ake magana bane, da zaki tsaya kina ma mutane kukan banza da hofi," a wannnan taƙin Nainarh ce tayi maganar ranta a mugun ɓace, dan ji take kamar ta tashi ta shaƙe wuyan Haleesat ɗin, har saita faɗa ma ta gidan uban da ta kwana, ta tabbatar da Haleesat ba'a gidan ta kwana ba.
A hankali Haleesat ta buɗe bakin da tsaban tsoro har kakkarwa yakeyi, ta ce "Kidnapping ɗina, akayi jiya da dare."
Tayi maganar a gajarce, kuma ta faɗa ne, tana tauna laɓɓanta na ƙasa.
Gabaɗayan su suka haɗa baki cike mamaki gurin faɗin "what kidnapping, fa kikace, anyi naki, to a'ina kuma su waye."
Dukansu suka haɗa baki wajen yi ma ta wannan tambayar, amma banda mutum biyu, cikin waɗanda sukayi tambayar, wato Zaynerb da Momy Rafi'at.
Zaynerb kwata kwata bata yarda da abin da Haleesat ɗin ta faɗa ba, musamman ma da taga yadda take tauna laɓɓanta na ƙasa, tasan Haleesat farin sa ni bata iya qarya ba, inma tayi sai an gano ta, saboda indai tayi qarya saita dinga cizan laɓɓanta na ƙasa da ƙarfi, shiyasa ma Zaynerb ɗin kwata kwata bata yadda da abin da Haleesat ɗin ta faɗa ba.
Momy Rafi'at kuwa bazan iya cewa ga ainihin abin da ke ranta ba, saboda yadda tayi act, komai qwaqwafin mutum sai dai ya batta kawai😇
"Ki bamu amsar, mana ana tambayar ki, kinyi shiru su waye sukayi kidnapping ɗin naki?, kuma mai suke nema, sannan kuma garin yaya kika kuɓuta idan ma sacekin akayi da gaske?."
Wannan karon Nailah ce tayi maganar ranta a mugun ɓace, da rainin wayon da Haleesat ɗin takeso tayi musu.
Afeefah kuwa kasa cewa komai tayi dan mamaki, haka ma ita Lailah, sai zubawa sarautar Allah ido kawai.
"Dan Allah kuyi hakuri, zan faɗa muku, amma please kubarni, ba yanzu ba, please ku bani lokaci dan Allah na roƙeku," tana maganar ne, cikin haɗa hannaye alamar roƙo, tashi tayi da gudu ta shige bedroom ɗin ta, ta rufo ƙofar da key sannan tabar key ɗin ajikin ƙofar.
Saman bed ta faɗa tana kuma fashewa da wani sabon kukan, saida tayi ma'ishi sannan ta miƙe ta shige bathroom, wanka tayi sannan ta fito wardrobe ta buɗe, ta ciro wata doguwar Gown ta Abaya ash color nd red, ta saka sannan tayi rolling ɗin mayafin Abayar akanta, ko lotion bata shafa ba, ta kwanta saman royal bed ɗinta.
Lumshe idonta tayi tana tariyo abin da ya faru gabaɗaya daga jiya da dare zuwa yanzu, rayuwarta ta sauya akala, cikin brain ɗinta take tuno komai, tamkar lokacin komai ya faru.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buɗe beautiful eyes ɗinta, zumbur ta miƙe tsaye, tana zazzare idanu, ganin wacca take gabanta, a tsorace ta ce "ta ina kika shigo ɗakin nan?,"
Guri Zaynerb ta samu ta zauna fuska a turɓune, sannan ta bata amsa da faɗin.
"Ba wannan tambayar ya kamata kiyimin ba, kamata yayi kice meya kawo ni, bawai 'ta ina na shigo ba."
Gyara zama Haleesat tayi, ita gabaɗaya tension ɗin da take ciki yasa, ta manta da akwai wata ƙofar ta bedroom ɗin Zaynerb, wanda kai tsaye zata kawoka bedroom ɗin Haleesat ɗin.
Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke, da niyyar zatayi magana, da sauri Haleesat ta ɗaga ma ta hannu, sannan ta ce "ba yanzu ba, dan Allah Zaynerb ki rabu dani, nayi alƙawari zan faɗamiki abin da ya faru, amma ba yanzu ba please please please.
Kallon ta Zaynerb tayi da kyau sannan tana nodding kai, alamar gamsuwa, ta ce "na yarda dake Haleesat, kuma nasan kinsan haka, ni nasan ba zaki bamu kunya, Sannan karki manta Daddy yana ƙaunar mu, yana sonki sosai, dan Allah karki bashi kunya Haleesat, shawara na baki a matsayin ƴar uwa ta gari, kuma mai ƙaunar ki, fatan zaki fahimce ni."
Da sauri Haleesat ta kalle Zaynerb ɗin, jin abin da ta ce, ɗa