Showing 57001 words to 60000 words out of 155363 words
Chapter 20 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
ne."
Deejarh ta ce "oho shiyasa ake cewa hausan baka, hausan adabi 😳
Ko miye da miye dai, gasunan kala kala,"
"kinjiki bazaki iya lissafowa ba kenan?," Afeefah ta tambaya.
Lailah ta karɓe da faɗin "ai tamayi ƙoƙari tunda har tana ganewa,"
Da sauri Deejarh ta ce "au ke bakya ganewa?, a lokacin da kike a secondary school kenan?,"
Dariya tayi ta ce "jerk kawai akwai ki da surutu fa," Deejarh ta ce "haka ake faɗa, to idan mutum bayyi surutu ba, ɗinke bakinshi zayyi da zare da allura?,"
Lailah ta ce "bawai haka ba, kawai wani lokacin ki dinga yima bakinki linzami."
💅𝐓𝐡𝐞 𝐅𝐚𝐬𝐡𝐢𝐨𝐧 𝐒𝐡𝐨𝐰 𝐒𝐭𝐨𝐫𝐲💅
ʜᴀʟᴇᴇsᴀᴛ
A gajiye ta fito daga practical lab. Chest ɗinta rungume da ma'ajin bayanai.
Tsayawa tayi da tafiyar da takeyi jin ana qwala ma ta kira, bata juya ba saima duba wristwatch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunta tayi ƙarfe huɗu saura na Yamma...
Sannan ta ɗago tana kallon Jenny da ta ƙariso gurin tana sauke haki alamar tasha gudu ba laifi.
"Menene sauri nake faɗa abin da zaki faɗa zanyi gaba,"
Da tsananin mamaki Jenny take kallon Haleesat, sai kuma tayi murmushi ta ce "haba Leesat ai bani na kar zomon ba, dama akwai abin da nakeso na tambaye ki, idan babu damuwa?."
"Okay, ina sauraronki," Haleesat ta faɗa tana gyara tsayuwa cike da gajiya.
"Wai mene ya faru ne, a tsakanin ki da su Zuree naga kamar baku ga maciji, yanzu kuma naga kin dena zuwa Night club, shine nakeso naji ko lafiya?,"
Jenny ta dire maganar tana kallon Haleesat, murmushin takaici Haleesat tayi sannan ta bata amsa "au su basu faɗa miki abin da ya faru bane, kokuwa zakice baki san komai ba?."
Da sauri Jenny ta ce "ba wani abu da na sani,"
"Okay yanzu dai kinaso kicemin bakisan sunyi kidnapped ɗi na ba kenan?, kuma sunyi attempting raping ɗina😓
Qwalalo madaidaitan idanunta Jenny tayi waje baki da hanci sake take faɗin.
"what, mekike nufi kinaso kicemin dai sunyi abin da naji suna shiryawa kenan...." ta faɗa cike da mamaki.
"Of course not! Sunyi attempt haka amma basu sama nasara ba,"
Jenny da taji tsayuwar da take bai isheta ba, ta zauna daɓas zaman ƴan bori a ƙasa, ta kuma miƙewa sannan ta koma ta kuma zama, babu abin da bakinta yake furtawa fa ce.
"jesus oh amma fa, su Zuree sun bani mamaki ba kaɗan ba," Haleesat tana murmushin abin da Jenny tayi ta ce.
"ashe dai kinsan wani abu,"
Kallonta Jenny tayi har yanzu bakinta bai bar faɗin 'jesus' ba ta ce "nasan dai wani abu daga ciki, amma zamu iya zama saboda maganar ba za ta yuwu a tsaye ba,"
"Okay to ga guri can ai, Haleesat ta bata amsar, tana gaba, ita ma Jenny tabi bayanta kamar wacca kwai ya fashewa a ciki.
A wasu kujerun hutawa farare ƙasan bishiya suka zazzauna, suna fuskan tar juna sunyi shiru na ɗan lokaci, kafin Jenny ta katse shirun da faɗin.
"Wata Ranar Saturday misalin ƙarfe uku na Rana. Muna zaune a hostel."
[da yake a hostel suke zaune Jenny, Zuree, Feenah, a tare a]
"Lokacin idan banmanta ba, ni ina daga saman bed ina karanta wani £nglish book 'SAY NO TO CORRUPTION' yayinda Zuree take kwance a saman doguwar sofa mai ɗaukar mutane biyu, tana chatting a wayarta, ita kuma Feenah tana goge wasu kayanta da iron, a lokacin munayi muna ɗan taɓa fira sama sama.
Har ɗan hayaniya yaso ya kaure a tsakanin Zuree da Feenah akanki, saboda bakya shan kayan ruwa ko wani abin da ya dangance maye daɗin daɗawa kuma bakya kula ko wani kalan Namiji balle kuma wani abu ya shiga tsakani.
Zuree ta ce 'ai saboda taba waye bane shiyasa,' ita kuma Feenah ta ce 'ba wani waye wa, ai waye ba shine shashaye ba, ko kuma bin maza da mata kamar busuruwa ba,' jin haka yasa Zuree ta fusata ta miƙe tana nuna Feenah da yatsa, tana faɗin, 'ai qwara ita, kowa yasan tanayin abinta a fili wata kuma bin matan ma a ɓoye takeyi,' da faɗar haka ita ma Feenah ta fusata a miƙe tsaye ita ma tana faɗin, 'ai qwara ita watan, saboda iya mata take bi, wata kuwa har maza tanabi saboda rashin sanin ciwon kai.'
"HABBA!.
Nanfa aka fara bankaɗe bankaɗe kowa yana faɗar sirrin kowa idan wannan ta faɗa wannan ta faɗa.
Nidai ina daga gefe sai haƙuri nake basu ba abinma da yafi ɗauremin kai sai jin da nayi Zuree na faɗin Feenah tana bin jinsinta mata, kamar yadda ita ma Zuree take, abin ya ɗaure min kai, sosai.
Ni aga ganina ba haka abota ko ƙawance yake ba, A ZATO NA idan akace aboki ko ƙawa ana nufin wanda komai ya sameka tamkar shiya sama ne, A ZATO NA idan aboki yana cikin matsala ko wani abun aboki shi zai jajirce da ƙarfin shi ko da wani abu daya mallaka har sayya ceto wannan aboki nashi.
A TUNANINA idan aboki ya faɗi ƙasa da sauri shima ɗayan abokin nashi zai bishi su faɗi tare, ashe nayi kuskure ba haka abin yake ba, ashe abotar yanzu anyinta ne kawai amma ba'a san Menene ainihin 'KALMAR ABOTA YAKE NUFI BA.'
Haka sukayita yi har saida suka gaji dan kansu, sannan suka saurarawa juna, nidai ina daga gefe nayi tagumi hannu bibbiyu ina kallon abin mamaki, tun lokacin da naje janye Feenah na sama nabon naushi a ciki daga Zuree nayi gefe😂
Can wuraren Ƙarfe huɗu da rabi wata 'Hanifa Falalu' wacca ɗakinsu yake ƙasan namu ta shigo tana faɗa mana wai munyi baƙo a waje, kuma mu dukan mu yake kira, da mamaki mu duka muke kallonta, jin abin da take faɗa, Zuree ta ce 'mu kuma?, kodai bamu bane, amma ta ya za'ace mu duka yake kira?, Hanifa ta ce 'haka yace ma ta', Zuree da Jenny da kuma Feenah, sannan kuma mutumin yana daga wajen gate yana jiranmu gate man yaƙi bari ya shigo.'
Jin haka yasa Feenah da Zuree suka miƙe ko wacce ta zara gyalenta suka fita, nidai cewa nayi ba inda zani tunda bansan ko wanene mutumin ba.
'T£N MINUT£S AGO'
Sai gasu sun shigo suna fira hadda shewa kamar basu suke harare harare a lokacin da zasu fita ba.
Nidai ban bi ta kansu ba, saima saukowa daga kan bed da nayi na shige bathroom domin nayi wanka, bayan nayi ne zan fito daga bathroom ɗin kenan harna saka hannuna dake ɗigar ruwa, zan murɗa ƙofar bathroom ɗin naji Zuree tana faɗin.
"yanzu saimu san lokacin da ya kamata mu ɗana ma ta tarko, domin kuwa wannan aikin da aka bamu mai tsokane sosai,"
Feenah ta karɓe da faɗin "kedai bari kawai, a wannan lokacin wazai baka two million's akan wannan ƙaramin aikin, kai kuma ka tsaya wasa, ai da gudu zan amsa, ko kisan kai ne, ai sainayi badai akwai masu motsi ba, suka kuma kwashewa da dariya.
Nidai tsananin mamaki ma ya hanani koda motsi, sai da naji suna ci gaba da tattauna war, sannan na samu na kwashi ƙafafuna waɗanda sukayi sanyi na jin abin da suke faɗa haka na fito daga bathroom ɗin a raina ina saƙe saƙen abubuwa da yawa sosai sosai.
Ganin na fito daga bathroom ne yasa Feenah tayi shiru da faɗin abin da tayi niyya ni kuwa ko kallonsu banyi ba, har na ɗaga kafafuna na nufi closet a domin shiryawa, naji ina ai gwara kawai na taresu a fili ba ɓoye ɓoye, domin naji abin da suke shiryawa budurwar da ko saninta banyi ba, domin a lokacin basu ambaci sunanta ba, idan ma na rabu dasu tsoro ma kenan, bayan kuma naji suna shiryawa wata gadar zare, banga amfanin zaman tare, babu amana ba, indai ban fito na musu magana akan hanyar da suke su jefa kansu ba.
Cike da gwarin gwiwa na juya ina kallonsu dukansu, da idanuna da suka rine da ɓacin rai, wanda ban taɓa shiga ba tsawon rayuwata, domin naji abin da yafi ƙarfin tunanina da lissafina.
Cikin faɗa da hargowa nake faɗin, 'kundai ji kunya wallah, kuna mata bakusan ciwon ɗiya mace sai ɗiya mace ba, akan wata banza two million's zaku jefa kanku cikin masifa.
Shin ko kunsan abin da shi mutumin zayyi da ita budurwar da ya baku umarnin samota?.
Ko kuwa ya faɗamuku ne?, kuka sani ko kasheta zayyi ko kuma yayi Raping ɗinta ko kuma yayi wani aikin asiri da ita, ko ko duka dai bakusani ba, kawai dai akan wata banza two million's kunzo nan kunata wani cika baki menene da menene ku ba Ruwanku. Tur da zama da ƙawaye irin ku, tir da halinku kaico wallah.
Tunda na fara maganar na fahimci jikin Feenah ya ɗanyi sanyi, ko kuwa yanayin hallitar ta ne ya motsa, na yawan sanyi, nidai bansani ba, na nufe ido ina zazzaga ruwan masifa.
Yayinda Zuree ta cika tayi fom fam ƙiris take jira ta fashe duk surutun da nake yana shiga right ear ɗinta ne ya fita ta left.
Aikuwa ban rufe baki ba ta tashi a fusace, dama bahaushe yace da hauka ake naɗe tabarman kunya, aikuwa nanta hau yi kamar bakinta zai tsage dama gata da saurin baki kamar me faɗi take, "to ke ina ruwan ki koma miye zayyi da ita ba abin da ya damemu mudai munji dumus, kuma zamuyi aiki sai naga uban da ya isa ya hanamu banza dake a gurin."
Nima cikin masifa na hayayyaƙo ma ta nace "dubeki shashasha dake a gurin, ke a cikin shashashu ma sai dai a kira ki 'DANKALI' yasin, saboda tsananin shashanci da akuyanci, ki rasa wacca zaki cuta sai ƴar uwanki mace, aikuwa anyi asara."
Cike da kumfar baki Zuree ta ce "E, naji koma miye zakice kin daɗe baki faɗa ba, kuma anjima da dare saina kai mishi 'Haleesat' ɗin idan ma kasheta zayyi ko Raping ɗinta yayi, kawai dama ta isheni a rayuwa."
Tun a lokacin data kira sunan 'Haleesat' jina da ganina na wani lokaci ya ɗauke sakamakon banyi tunanin ke ba ce, ashe ɗan Adam ba'a bakin komai yake ba.
Da ƙyar na samu na dawo da nutsuwata, na kalleta a ƙasƙance nace.
"aikuwa sai dai aniyar ki ta biki domin Haleesat tafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, domin 'she was very £xtraordinary lady' ita ba kalarki bace, ko zuwa Night Club da takeyi jarab tane kuma kema kinsani Haleesat batayi kalar mata masu yawon ta zubar ba."
Shiru tayi domin kuwa a yanzu bata da amsar da zata bani, ganin haka naja tsaki ina faɗin "idiot kawai kina mace bakisan ciwon kanki ba, wai kuma a haka kike yarinya a gurin babban malami shahararre, andaiji kunya ƴar malam taƙi halin malam.
Duk sunaji na amma daga ita har Feenah dake kwance saman bed, sun kasa tankamin, na kuma jan tsaki sannan na nufi wardrobe na ciro kayan da zan saka.
Harna kammala shiri suna ɗakin sunyi gum kamar ruwa ya shanye su.
Dare misalin ƙarfe goma saura a lokacin wayata tayi full charge, ina zaune saman doguwar kujerar ɗakin, ina sipping coffee, na lalubo lambar ki na kira duk a zato na, sunyi bacci shine fa, kina ɗagawa Feenah ta ƙure volume na speakers, ke kuma daga wajen ki bakyaji sosai, na miƙe da niyyar fita waje, nan wani jiri ya kwashe ni mug dake hannuna ya tarwatse a ƙasa, daga nan nima na bishi bansan tayaya kuma meya faru ba.
Kawai dai da safe na farka ne na ganni a saman bed, ɗakin ba kowa alamar dai ba'a anan suka kwana ba, a lokacin kasa tashi nayi saboda kaina dake matuƙar sarawa haka kuma ga jikina ba qwari.
Nafi ƙarfin two hours a haka sai daga baya na samu na tashi da kyar na shiga bathroom nayi wanka na fito, har lokacin ba ɗayarsu da ta dawo a gurguje na shirya cikin sauri sauri.
Bayan na shirya ne fa, wuraren ƙarfe biyu na rana har lokacin dai ba wacca ta dawo, zuwa lokacin hankalina ya fara tashi ina nan zaune, saiga ƙanwar Zuree ta shigo ɗakin wai tazo gurin Zuree yayarta, kuma tarema suke da babban yayansu.
Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba, ma ta bayanin abin da ke faruwa tun daga farko har ƙarshe.
Ita kuma tanajin haka ba ɓoye ɓoye taje ta faɗama babban yayansu dake waje cikin mota yana jira, shima dai kamar ƙanwar yasha mamaki, amma sayya dake ya ciro phone ɗinshi a trouser pocket ɗinshi ya lalubo lambar Zuree, ya danna kira amma waya a kashe ya kira yakai sau goma amma dai abu ɗaya waya a kashe.
TASHIN S£NS£!
Muna tsaye a bakin gate munyi cirko cirko muna jiran tsammani, saiga wata arniyar mota black color ƙirar R.R. ROLLS ROYC£.
Tayi parking a can gefen mu saiga ƙanwar Feenah, wato Fannah ta fito daga ciki da sauri ta ƙariso gurin da muke tana tambaya na ko lafiya, sannan kuma Feenah tanan sun kawo ma ta ziyara ne.
A lokacin duk da bani ce nayi laifin ba, amma wallah saida naji wani fitsarin tsoro ya cika marata.
Da kyar na samu na ce ma ta "Feenah bata nan," zatayi magana saiga Dadynsu da kuma Momyn su matar da Feenah take a hannunta, da kuma wani saurayi da alama yayansu ne sun ƙariso gurin.
Hannu yayansu Feenah yaba Babban yayansu Zuree sukayi misa baha, sannan suma suke tambaya ko lafiya suka ganmu cirko cirko dayake na ɗan saba da ƴan gidansu Feenah ba laifi.
Nanfa babban yayansu Zuree ya gyara tsayuwarshi, yaba su labari kamar yadda na bashi.
Nanfa naga ɓacin rai kalar wanda ban taɓa gani ba, dan kuwa yayansu Feenah yafi Babban yayansu Zuree nuna tsantsar ɓac
cin ranshi akan abin da yaji su Feenah sun aikata ko ince suke akan aikatawa.
Cikin tsananin ɓacin rai yake faɗin "yaushe kuma ta yaya Safeenah, dama haka sunan Feenah yake na gaskiya.
Ta zama haka, kuma mu muna ina, a wannan lokacin da ƙarfi ya damɗe hannun shi yana futar da huci, shikuwa Dadynsu Feenah tsananin mamaki ya hanashi faɗin komai, haka dai munkai kusan minti talatin muna tsaye a gurin kowa da abin da yake saƙawa aranshi.
Can saiga Motar Zuree ta nufo gate ɗin bamu sani ba, sun hago mutane ne a gurin ko miye ya faru, da sauri dai mukaga motar tayi reverse zata bar gurin.
Ai a three sixty 360 yayansu Feenah shida Babban yayansu Zuree suka bi motar wata kalar super Babban yayansu Zuree yayi yasha gaban motar, yayinda yayansu Feenah ya fasa glass ɗin motar da hannun shi, bai damu da jinin da hannun shi yake ba, ya finciko Feenah waje bai tsaya komai ba, ya dingi ball da ita yana marinta ta ko'ina dukanta yakeyi, don koda yaga ta suma ruwan roba ya ɗauko a mota ya kwara ma ta, ba shiri ta farfaɗo shi kuma ya ci gaba daga inda ya tsaya, ganin zayyi kisane yasa ƙanwar Feenah, Fannah ta ruga da gudu tana kare Feenah tana bashi haƙuri, amma ina kamar ma cewa take ya ci gaba, aikuwa ya haɗa da ita yana jibga baya ma gajiya ga mutane har an fara taruwa ƴan kallon qwaqwaf hadda masu ɗaukar video.
Ganin zai kashesu su duka ne yasa Momyn su ta tafi da sauri ta shiga tsakani, sannan fa ya dakata, shikuwa Dadynsu yana gani yaƙi magana sai ma mota daya koma abinshi.
Shikuma Babban yayansu Zuree tun lokacin da ya kamota wani farin gam yasa ya rufe mata baki dashi, sannan ya ɗauko igiya ya ɗaure m ata hannu da ƙafafu duka biyu sannan fa yahau dukanta yana kwallo da ita haɗe da marinta, fuskar nan nata da tasha bleaching tayi wani irin jajir kamar kamar me.
Bai dena dukanta ba sai da yaga bata motsi sannan ya ciciɓeta a haka ya jefa a mota kamar kayan wanki sannan ya dawo wajen yayansu Feenah suka sakeyin misabaha, ya min godiya sannan ya shiga mota ita ma ƙanwar Zuree ta shiga yajasu suka bar gurin.
Shima yayansu Feenah kaɗasu yayi suka shiga mota suka bar gurin suma daga nan kuma kowa yayi gaba, nima haka jiki ba gwari na koma ciki.
Ajiyar zuciya Jenny ta sauke da ta kawo nan sannan ta kalla Haleesat da tunda ta fara maganar ta zuba ma ta ido, murmushi tayi ta ce "in taƙaice miki dai Zuree a ranar mahaifinta ya aurar da ita sadaka ga wani almajirinshi, sannan kuma yace karatun ma an barshi ba ita ba ƙara zuwa school forever...ita kuwa Feenah taci wuya amma dai ita ba'a katse ma ta karatu ba saboda Dadynsu cikaken ɗan boko ne, gaba da baya amma dai yanzu bata kwana a hostel sai dai ana tashi driver yazo ya ɗauketa su tafi gida thats is all.
Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke, sai da ta nisa sannan ta ce "duk da abin da suka min banji daɗin hukuncin da aka yankewa Zuree ba, aure bashi zaisa ta nutsu ba, nasan halin Zuree gaba da baya."
Da tsananin mamaki Jenny take kallon Haleesat ta ce "ae na ɗauka zanga kina farin ciki ne, a lokacin da nake baki labari,..sai kuma kika bani mamaki...a gaskiya Haleesat bazan ɓoye miki ba, kina burgeni sosai fa over, sannan kuma zuciyarki mai kyau ce, ina alfahari dake a matsayin ƙawata, am so very proud of you, ashe akwai mutane irin ki a duniya lallai ne, yau na yadda da kalmar na 'INDA RANKA KA SHA KALLO.'
Ɗan murmushi Haleesat tayi aiƙaice sannan ta ce "Jenny kenan akwai ki da sonyin karin magana, gashi baki wani iya ba," ta ƙarishe maganar tana kuma sakin murmushi, Jenny ta ce.
"saura kuma abu ɗaya, da ban faɗamiki ba,"
"Menene shi?,"
Haleesat ta tambaya, Jenny ta ce "na sama Admission a Beijing China, acan zan ɗaura master's ɗina."
Ta faɗa cike da farin ciki, washe baki Haleesat tayi sannan ta miƙawa Jenny hannu tana faɗin.
"congratulations Dear, yanzu shikenan zaki tafi, ki barmu da kewar ki ko?."
Jenny tana dariya ta ce, "toya za'ayi duk acikin neman ilimi ne.."
Dariya sukayi a tare Haleesat ta ce "kuma fa kinyi gaskiya," tashi sukayi a tare Haleesat ta nufi motar ta shiga taja, ita ma Jenny ta nufa nata ta shiga.
HAL££SAT
Tana driving amma gabaɗaya hankalinta baya jikinta, ta faɗa duniyar tunanin hali irin na mutane zaka haɗu da mutane kala kala a Rayuwar ka sannan kuma zakaga kowa da kalar halinshi.
Horn tayi a ƙofar gate ɗin gidansu bayan ta iso, wangale ma ta gate ɗin mai gadi yayi, sannan ta shiga da motar ciki.
Saida ta daidai ta parking