Showing 135001 words to 138000 words out of 155363 words
Chapter 46 - SARAUNIYAR KYAU_Takun Farko _cmplt. By The Nainarh Kd -2-1.txt
kyau. Tofa ana zuwa kanta an rufe ƙofa. 💋
Afeefah ta kasance cikakkiyar mace mai son mutane kamar me, domin kuwa kowa nata ne, dukiyar mahaifin ta bai rufe ma ta ido ba sam ko kaɗan, gata akwai kirki kamar mene.
Afeefah ta kasance tana masifar ƙaunar Labari na *SOYAYYA* dama duk wani Abu daya shafi soyayya.
A lura da kyau Labarin soyayya nace Afeefah take ƙauna bawai soyayyar ba, domin kuwa bata taɓa soyayya ba, ita ɗin haka take, gata akwai ta da matuƙar kaifin basira da tunani sannan kuma Afeefah tana ƙaunar Ƴan uwanta sosai sosai obaaaaa.
Sannan kuma akwai ta da wani kyakyawan hali wanda shi ne kana ma ta Abu yanzu tofa yanzun zata manta, ita sam bata da riƙo ko kaɗan, sai dai kuma fah. A Lura kyau Afeefah ta kasance mace ce wacca tasan haƙin gayu obaaaaa.
Sannan duk da kirkinta bata ɗaukar raini ko kaɗan bata da girman kai amma fah akwai class highly highly. Sannan kuma ta kasance tana ƙaunar ayi surprisingly nata a komai. 💞
Lailah Abubakar Mai Kyau.
Lailah, ta kasance mace ce ita mai matuƙar tsafta da kyankyami kamar me, sannan kuma akwai ta da mugun rashin mutunci ba kaɗan ba, dan ma haɗuwarta da Afeefah ne ta raƙe wasu abubuwan.
Sannan kuma ita Lailah bata damu da harkar kowa ba, sai dai nata sannan kuma ita ba mace bace wacca ta iya gulma, sam bata iya gulma ko ƙarya ba, kai tsaye take harkar ta.
Amma fah akwai ɗan karan surutu, sannan kuma ita Lailah sam bata soyayya, ace warta ma soyayya ɓata lokaci ne kawai da shirme, amma fah a fahimtar ta ke nan.😂
Lailah tanason Afeefah sosai fi ye da son da take yi ma kanta. *_-_kunji masuyi Don Allah _-_*💫💫
Sannan Ita ma dai tana da kirkinta dai dai ita sai dai hali kawai irin na ɗan Adam.
Zinaru Abubakar Mai Kyau.
Xixi ke nan ƴar kwalisa da iya ado ga tsafta kamar me, gata ita ma akwai ɗan banzan iya yi da son asan da zamanta, ta wani ɓangaren halinta yazo ɗaya dana Zaynerb wajen iya shiga shara babu shanu, gata faɗi ba'a tambayeki ba ke nan.
Akwai surutun tsiya sannan Ita ma irin Afeefah ce, ta wani fannin domin tanason mutane babu laifi sannan kuma Abin hannunta sam baya rufe ma ta ido eheee.🌝🌚
*Wannan ke nan, Kaɗan daga cikin Halayen Ƴaƴan Mister Mai Kyau...*💅
___***
To Haka dai Rayuwar nasu ta ci gaba da lulawa ba wani farin ciki gunin ban Tausayi ta kowani ɓangare watanni tara da barin Maleek Gida aka yi bikin Nainarh da Nailah.
Yayin da ita Nainarh ta Aura wani haifaffen ƙasar Eritrea. Wanda haɗuwar social media ce, harta kaisu ga Aure.
Duk da dai kafin Auren sai da aka sha fama da Momy Rafi'at domin taƙi yadda ne.
To daga baya haka ta haƙura aka yi ba yadda ta iya.
Yayin da ita ma Nailah ta Aura wani ɗan ƙasa Nigeria haifaffen Nasarawa State, mazaunin Lagos duk da Ita ma da farko Alhaji Abubakar Mai Kyau.
Yaso ya bada matsala, ace war sa bai amince da mijin da Nailah ɗin zata aura ba, saboda Yanayin sana'ar sa, amma daga baya haka komai ya wuce aka sha shagalin biki.
- _-
Rayuwa ta ci gaba da gangarawa ta kowani ɓangare yau daɗi gobe babu, dama haka abin yake ba kullum ake cikin enjoying komai ba.
Shekarun Maleek Biyu da Barin Gida ba ko wai waye.
A lokacin ne kuma xixi ta kammala secondary school nata. Sannan ta ce ita a ƙasar france wurin Uncle Yunus take so ta ci gaba da karatunta, a can tare da Labiba ɗiyar sa wacca suke sa'anni ace war ta gaba ɗaya Gidan nasu babu daɗi tun Barin Buddy nasu.
To koda ta sama mahaifin su Alhaji Abubakar, da maganar da farko ƙin Yarda Ya yi saboda a tunanin sa Sanadin karatu a Abroad Babban ɗan sa Abdulmaleek Tarbiyar sa ta sama matsala.
Ita ma zaynerb kuma sanadin haka ta sama matsalar soyayya. Wanda nan gaba zamuji ainihin abin da ya faru da ita acan Amsterdam ɗin.
A lokacin ba ƙaramin wani hali xixi ta shiga ba, dalilin hana ta zuwa faransa domin ɗaura karatun ta na degree.
A lokacin har rashin Lafiyar ƙarya ta kwanta dan dai kawai a barta ta tafi, aikuwa daga baya Alhaji Abubakar Mai Kyau, da yaga babu sarki sai Allah, haka ya barta ta tattare ya nata ya nata ta koma faransa. Wajen Uncle Yunus ta fara sabuwar Rayuwa. Yayin da gefe guda ita da ɗiyar Uncle Yunus Labiba suka fara karatun anan wata hamshaƙiyar jami'a na ƙasar faransa.
Yayinda suke karantar course ɗaya.
Nigeria kuwa Rayuwar Ahalin Alhaji Abubakar Mai Kyau, ta ci gaba da tafiya salin alin. Yayin da aka kwashe tsawon shekaru uku hadda watanni da Maleek Yabar gida sai wannan karon ya dawo...💃💃
*Masu karatu idan nace zan ci gaba da tafiya cikin ainihin abin da ya faru a baya*.
To gaskiya ina ga har mu kammala wannan novel baza'a dawo cikin ainihin Labarin ba, saboda haka anyi min afuwa mu koma cikin ainihin Labari.
Yanzu dai kunji ainihin dalilin abin da Ya saka Maleek ya bar Gidan su tsawon shekaru uku da watanni sai wannan Lokaci ya dawo.
Kuma kunji dalilin da yasa Momy Rafi'at bata ƙaunar su Afeefah, saboda wai mahaifiyar su ta Aure mata miji.
Sannan kuma munji wani abu daga cikin ainihin dalilin da yasa Haleesat ta fara zuwa mashaya, wato Sanadin haɗuwarta dasu Zuree da Feenah da kuma Jenny.
Sannan again munji ainihin dalilin da Yasa Zaynerb ta dawo Nigeria.
Bayan kuma a Amsterdam ta fara karatu, wato dai Sanadin soyayya, kamar yadda nayi Alƙawari nan gaba zamu ji ainihin abin da ya faru da Zaynerb a can ƙasar NETH Babban Birnin ƙasar wato Amsterdam.
Haka ma Lailah munji wasu daga cikin silly. 😜 dalilanta da suka saka ta tsani soyayya, har ma da maza😕
Sannan kuma munji irin ciwon dake damun Jarumar mu.
To shin akwai maganin wannan ciwo nata ko kuma babu kudai kawai ku Biyo alƙalamin Nainarh Kd domin jin wannan ƙayataccen Novel Na musamman Wanda sai da a tsaya a Ta ce sannan kuma a tsaya aka zuba Basira wajen Taho muku dashi Labari mai Cike da sinqi sinqin chakwakiya_🤩_Cin Amana🤣_Yaudara😏_Zamba cikin Aminci🤕_Ban dariya obaaaaaaaaaa😆_Rikita Rikita🥴_____
Nishaɗantarwa🤪_Game da wa'azantarwa 😜_Buri💫_Fansa_makirci🤮_Hargitsi🤥_____
Game da Tsananin Zazzafar Soyayya Mai Ban sha'awa da Burgewa, da kuma tsindima mutum cikin Shauƙi ba tare da Da ya shirya ba. Labari Mai suna SARAUNIYAR KYAU 💋💋💋__THE GLAM QUEEN 👑💕🌹
💓💓ƚԋҽ ϝαʂԋισɳ ʂԋσɯ.💓💓
*PR£S£NT*
*Ci gaban Labari*
*_-_Masu Karatu, Ina Fatan Dai Baku Manta Ta Wajajen Da Muka Tsaya Ba, To Yanzu Dai Zamu Ɗaura_-_*
*بسم الله الرحمن الرحيم*
Bayan sun shishshiga ƙayataccen palon, Gaba ɗayan su iyayen suka zazzauna saman Royal sofa's dake zagaye da ƙaton palon, Yayin da su kuma gaba ɗaya yaran suka zazzauna a ƙasa tsakiyar palon harda Maleek wanda kansa yake ƙasa cike da yasa nin komai da ya faru baya.
Yayin da ita kuma Afeefah wacca har zuwa lokacin bata farfaɗo ba, aka ɗaurata saman doguwar kujera 3sieter Yayin da Momy Rafi'at ta zauna kusa da ita tana ma ta firfita sama sama.
Gaba ɗaya palon shiru ya ɗauka tamkar babu wani hallita mai rai ciki, sai da aka shafe kusan mintuna goma, a haka sannan Uncle Yusuf da ya kasance mutum ne shi mai bala'in sauƙin kai da kuma ƙaunar peaceble.
Gyaran murya Ya yi sannan ya kuma buɗewa da addu'a bayan ya kammala suka shafa sannan ya kalla Maleek cike da kulawa ya fara magana kamar haka.
"Yanzu kai Maleek ka dawo gida Bayan ɗaukar tsawon shekaru baka nan, shin zaka iya faɗa mana duniyar da kaje ko kuma wurin da ka tafiya ko waiwaye babu?."
Gaba ɗaya mutanen palon ne suka mayar da hankulan su kan Maleek suna jira suji amsar da zai bawa Uncle Yusuf da ya yi masa tambayar.
Shikuwa Alhaji Abubakar, babu abin da yake sai faman sauke huci kurum yana kallon Ɗiyarsa dake kwance bata ko numfashi.
Shiru Maleek ya yi tsawon mintuna uku sannan ya yi gyaran murya yana gyara Yanayin zaman sa ya fara magana cikin murya wacca dai Yanayin ta sai as low.
"Da Farko dai Bayan na Bar Gidan nan kai tsaye Airport na wuce nabi jirgin ƙasar Rasha, to koda na isa Rasha Ban tsaya komai ba. Kai tsaye na fara aiki a Babban asibiti dake ƙasar tsawon shekara ɗaya, sannan kuma na fahimci wani abu, cewar shi baturen mutum kwata kwata bashi da alƙawari.
Wato abin dai da ya faru shi ne, ina gabatar da aiki cikin gaskiya a ƙasar cikin Babban asibitin ƙasar, sai wata Rana ɗaya daga cikin manyan likitocin asibitin da yake ba musulmi bane, shiyasa bama wani jituwa dashi, daɗi da kari kuma na fahimci baya da wani hali na KIRKI..."
Katse sa Alhaji Abubakar Ya yi cikin sauri
"Okay ke nan kai ɗin wani Halin kirki ne dakai. Yanzu kaine har zaka ce wani bashi da Halin kirki?."
Da sauri Uncle Yusuf ya katse Alhaji Abubakar cikin sanyin murya Yace
"Ina ga da kayi shiru mun gama jin abin da yake so ya faɗa mana."
Alhaji Abubakar bai tsaya sauraron maganar da Uncle Yusuf Yake ba, Ya kalla Maleek cikin daka tsawa yace "Yanzu me kake nufi?, kana nufin kace ka dawo Gidan nan ne, to a matsayin wane ke nan?, ni dai nasan bani da wani Yaro na miji duka Yarana mata ne, kuma ina ƙaunar su duka."
Jin abin da mahaifin nasu yake faɗa ne yasa gaba ɗaya yaran nasa suka ɗago suna kallon sa, cike da tsananin tashin hankali.
Cike da nadama Maleek ya rarrafa kusa da mahaifin nasu ya kamo ƙafafunsa yana basa haƙuri kamar zayyi hauka cike da tsantsan nadama.
Yayin da shi kuma Alhaji Abubakar yake ture shi cikin tsananin fushi yana tuna duka abubuwan da suka faru baya tamkar yaune suke faruwa.
Maleek faɗi Yake yi "Please Daddy ka yafe min, wallahi na tuba, bazan kuma ba, domin nayi nadama highly."
Gaba ɗaya yaran kuka suke bama kamar Zaynerb da Nailah har wani shiɗewa suke yi saboda tsananin tashin hankali, tsoro suke karfa tarihi ya kuma maimaita kansa.
Ajiyar zuciya Alhaji Abubakar Mai Kyau, ya sauke a karo na babu a dadi yana kallon gaba ɗaya Yaran sa yadda suke kuka, shi uba ne dole yaji babu daɗi da ƙari ƙin yafewa Maleek da Ya yi bawai yana nufin baya ƙaunar sa bane ko kuma wani abun, kawai dai yanaso ya fahimci shin da gaske ya tuba ko kuwa.
Kallon Maleek dake hawaye kamar zararre, Uncle Yusuf Ya yi sannan ya masa umarni da ya koma ya zauna.
Komawa Maleek Ya yi kusa da ƙafafun mahaifin sa ya zauna dan Bala'i.🥵
Kallon gaba ɗaya mutanen palon Uncle Yusuf ya kuma yi sannan ya ƙara mayar da kallon sa, kan Alhaji Abubakar yana masa kallon nutsuwa, daga ƙarshe dai ya sauke idanun sa a kan Maleek.
Kiran sunan Abdulmaleek Ya yi har sau uku, yana amsawa sannan ya ci gaba da cewa.
"Yanzu dai mu a je maganar wurin da kaje gefe, a gaskiya gaba ɗaya Ahali ba muji daɗin barin Gida da kayi ba, a kan wani dalili wanda bai kai ya kawo ba, sannan kuma yanzu da ka dawo, ka dawo ka ci gaba da Rayuwa da Ahalin ka ne, ko kuwa dai akwai wani nufi a tare dakai?."
Uncle Yusuf Ya yi masa tambayar yana kallon Maleek ɗinda ya yi shiru kansa a ƙasa.
"Please Uncle ayi min haƙuri na duka abin da ya faru baya, sharrin shaiɗan ne sannan kuma na dawo gida ne saboda na ci gaba da Rayuwa cikin Ahalina kamar kowa."
Wani ƙayataccen murmushi Mister Mai Kyau. Ya yi amma fah na iya gefan fuska, domin kuwa idan ba ƙura masa ido kayi ba, to ba zaka fahimci Ya yi murmushin ba, daga yadda fuskar sa take a tsume, wani sanyi yaji cikin zuciyar sa jin abin da Maleek yake faɗa, a fili kuwa kallon Maleek dake kallon sa. Ya yi sannan yana faɗin
"Indai kanaso na manta komai da ya faru a baya, na bari ka dawo ka ci gaba da Rayuwa cikin mu. Tofa sai dai idan ka amince zaka fito da matar Aure. Idan kuma baka da budurwa ka zaɓa cikin Ƴan matan dangi, duk wacca tayi maka."
Duk wannan maganar Alhaji Abubakar ya yima Maleek ne cikin kakkausar murya da kuma bada zaɓi.
Murmushin enjoying da kalaman ɗan uwan nasa Uncle Yusuf Ya yi sannan Ya mayar da kallon sa a kan Maleek ɗin.
"Ka dai ji da kunnen ka, abin da mahaifin ka ya faɗa, saboda haka yanzu zaɓi ya rage naka."
Shima Uncle Yusuf Ya yi maganar cikin gimtse fuska alamar dai babu wasa cikin maganar.
Haka ma gaba ɗaya mutanen palon suka mayar da hankulan su kan sa hadda Momy Rafi'at da tun ganin Yaron nata bata ce komai ba.
Kai harda Afeefah wacca farfaɗowarta ke nan taji zancen Uncle Yusuf a sama, sannan kuma babu wanda ya lura ta farfaɗo domin kuwa bata nuna alama ba.
Ajiyar zuciya Maleek ya sauke yana tariyo gaba ɗaya girlfriend's da ya taɓayi kaf cikin su, baiga wacca suke tare yanzu ba, gaba ɗaya basa tare domin kuwa tunda daɗewa yabar kalar Rayuwar sa ta baya, shi dai yanzu iya tunanin sa baiga macen da zaice ya taɓa ma ta kallon so ba, ko kuma ya ma ta kallon wani abun ban da ƙawance, ɗagowa Ya yi Yana kallon gaba ɗaya mutanen palon, kamar yadda suma shi Suke kallo.
Murmushi Ya yi kaɗan kana ya buɗe muryar yadda gaba ɗaya zasuji yana faɗin
"Husnee ce wacca na zaɓa..." 💞💞
Gaba ɗaya palon dariya suka saka ganin yadda Husnee ta ɗago a firgice tana kallon sa hankali tashe.
Uncle Yusuf kuwa babu abin da yake faɗi sai
"Masha Allah dama haka ake so, lamari ya yi daɗi."
Nan kuma palon ya ɗauki hayaniyar murna da jindaɗi.
Sai da suka sama nutsuwa gaba ɗaya suka yi shiru sannan Uncle Yusuf ya kalla Husnee cikin maganar irin na manya yake tambayar ta
"Husnee Ɗiyata kin amince zaki Aura Yayanki Abdulmaleek kamar yadda shima yace keya zaɓa?."
Kallon jama'ar palon Husnee tayi kamar yadda suma suka zubo ma ta na mujiya suna kallo.😅
Cikin gimtse kyakyawar fuskar ta take faɗin
"Uncle Yusuf a bani mintuna biyar zanje yanzun nan nayi shawara na dawo."
Tayi maganar fuska ba rahama, dariya suka saka baki ɗaya, sannan Uncle Yusuf yace cikin dariyar shima
"Kinji jeki Ɗiyata ki ɗauki iya a dadin lokacin da kike so domin duka naki ne."🥰
Miƙewa tayi sannan ta zagaya ta bayan kujeru ta wuce kai tsaye bedroom ɗin Lailah, ta wuce tana shiga ta rufe ƙofar harda murza key, sannan ta dawo ta ƙarisa can gaban madubi tana kallon kanta.
Cire mayafin da tayi rolling kanta dashi tayi kana ta daka tsalle tana faɗin
"Yes, Yes, sai ni Husnee, wallahi sai ni Husnee, a gaskiya na cire tuta cikin ma ta niɗin ma mai sa'a ce cikin masu Nasara, inba hakan ba wannan Diamond boyfriend guda kamar Yaya Maleek Yace Yanaso Ya Aureni.
Haba duk inda aka ji maganar Aure ansan da akwai soyayya, Yasin sai ni Husnee, lallai dawowar Buddy Gida ba kowa Ya yi ma amfani ba sai ni, kai dole ma nayi waƙa, oh toni wata kalar waƙa ma, na iya?..."
Tayi maganar tana zama gefan bed cike da matsanancin nishaɗi highly highly,
Murmushi tayi sannan Ta ce "Yeah Wallahi na tuna."💃💃
Buɗe daddaɗar muryar ta Ta yi sannan ta fara Raira waƙa cike da enjoying Mood da take ciki rairawa take yi kamar haka.
"I'm coming home😌 I'm coming home. Tell the world, I'am coming home, 🙂 Let the rain Wash away..☔🌈 All.. the pain of yesterday😥😊 I know my kingdom awaits 💕💕 and... They've forgive my mistake"🤗💝 I'm coming home, I'm coming home Tell the world I'am coming home... { home is not a place it's feeling. }."
Murmushi tayi Bayan ta kai haka a waƙar nata sannan ta ɗauki mayafinta, wannan karon yafashi tayi saman kafaɗarta, sannan ta buɗe ƙofar ta fito bayan ta kuma gimtse kyakyawar fuskar ta.💝
Husnee ta kasance Ɗiyace ta uku wajen Hajiya Jawaheer.
Husnee, kyakyawar matashiyar budurwa ce wankan tarwatsa, doguwa ga hanci, ba zata Haura shekaru ashirin da ɗaya zuwa da biyu ba a duniya, sa'ar su Afeefah ce, ta kammala karatun degree nata anan Babbar University dake Jigawa State ta Karanci fannin Agriculture, Husnee akwai ta da san barkwanci kamar mene, gata akwai kirki da sauƙin kai, sai dai abin da ba'a rasa ba domin kuwa ɗan Adam ajizine. 😸
Komawa tayi ta zauna kusa da su Ƙarama da Mah'eesha saɓanin ɗazun da take kusa da Lailah da kuma Fateemah da Zakiyya.
Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalla Uncle Yusuf Ta ce
"Eh Uncle na amince nima."
Tayi maganar tana rufe fuska wai kunya.🤓
Gaba ɗaya fuskokin mutanen wurin idan ka kalla zaka fahimci bawai iya farin cikin dake bayyane a fuskar su bane, harda zuciyoyin su ma.
Murmushi Uncle Yusuf Ya yi sannan Yace
"hakan ake so. Yanzu sai a fara tunanin saka rana ko?."
Zuruf Husnee ta ce "Ah ai Uncle ina ga kawai tunda Already na kammala karatu na, a saka nan da one month kawai, kaga Lokacin Ya yi dai dai da lokacin da za'a kuma gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa ko?."
Tayi maganar iya gaskiyar ta kuma har zuciyarta.
Fashewa da dariya gaba ɗaya mutanen palon, suka yi cike da nishaɗi.
Lailah da bata gani bata tanka ba, ta ce
"Oh oh ikon God sai Look. Wato yanzu ke Husnee ko kunya babu kike wannan zance gaban mu ko?."
Tayi maganar cikin dariya, muryar da basu yi tsammanin jinta bane, suka ji tana faɗin
"Oh ke kuma Lailah sarkin surutu zaki ba, My Aunty to be, kunya cikin society ko?."
Cewar Afeefah tana saukowa daga saman doguwar kujerar da aka kwantar da ita.
Murmushi Husnee tayi sannan ta ce "Batta kawai dai dai nake da ita nima ae, ko tayi tunanin zanji kunyar tane?."
Gaba ɗaya dariya suka kuma yi habba daga haka kuma fira ta kuma shiga tsakani cike da nishaɗi.
Shidai Maleek shiru ya yi yana kallon Ahalin nasa gaba ɗaya sun canza sosai. Jinsa yake tamkar wani sabo cikin su, sai yaji yau ya kuma yarda da wannan maganar da ake cewa 'Duk Wanda Yabar gida, Tofa Tabbas Gida Ya barsa'. Home is not a place it's feeling for All people.💞
*KANO*
Wannan karon da tsananin mamaki ya kuma kallon